Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu tàyi hakan sau biyar don bin umarnin doctor sa'adah,tuni ta hada gumi sharkaf,cikin Dauriya irin tata ta juya ta shiga dakin baba talatu da ta kwanta yin qailula bayan sun gama hira tà tadata ganin lokacin sallar azahar na qoqarin ficewa,ta farka ta dubi Fadila tana Mata sannu,ta amsa a kunya ce sañnañ ta daura tata alwalar,a falcon Tatars da baban nayin tata,itama ta zube sannan ta tayar



Baba talatu na saman kujera tana jañ carbi Fadila ta miqe tana fadin"yunwa nake ji baba sosai,kamar ba dazun nan na gama can ayabarba"
Baban ta kalli inda ta Ajjiye ragowar da ta gama ci"ai kuwa dai ga ragowar da Kuma rage can nama manta ban dauketa ba,maza ki cinye a barki ba dadi zama da yunwa,idan baki qoshi ba sai a dado miki"tayi murmushi tana dada qaunar baban,maca ce wayayya Duk d ba tayi karatun boko ba



Ta soma cin abàrta kuwa,Sam ta mance ba tayi bismillah ba saboda mahaukàciyar yunwar da takeji,ta bare ta uku tana ci hankalinta kwance,dadi ya kama salima dàke maqale tun dazun jikin window din balcony din ta fàdila,wani tsallen dadi tayi ranta da zuciyarta fes,tana qarewa surqumemen sirinjin dake hannuntà kallo cike da farinciki Wanda ya taimaketa ta gabatar da mugun aikinta



*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/28, 7:59 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*part 3*

3⃣4⃣



Kimanin awa guda yana tsayen don ko sha'awar zaman baiyi har ruwan ya qare da suri nurse din da ai bari a dakin ta taso ta cire mata ta sanya mata dayan,cikin karaya aliyyu yabi saban ruwan da ta sa mata da kallo zuciyarsa cike da fargaba,sai dai kafin ya dauje idonsa yaji an damqe hannunsa dake cikin nata tsam tsam tmkar zata ballashi,da sauri ya kalleta still idanunta na rufe,a hankali numfashinta ya sima fita da sauri da sauri,wa ni bashi ta soma mai cike da wahala



Tuni nurses din suka danna wa ni Abu,cikin qiftawa da bismillah sai ga doctor sa'adah ta shigo,kanta sukayi suka soma bata taimako,aliyyu na tsaye cike da rudani,tausayinta da qaunarta suka sake Hawa a zuciyarsa,idanunsa ya sake kadawa babu hawaye sai azabar quna da zuciyarsa keyi ganin irin gwagwarmayar d take share,idanunta na rufe amma gunji take da nishi mai ban tausayi,hannunsa dake cikiñ nata har yanzu kamar zai balle



"Doctor idan babu dama wuyarnan ta isa haka,Gwara a yimata c.s a cire mata babyn ta hira mana"ta girgiza kai"Daga take da haihuwa,don zata ita haihuwa da kanta"tana rife baki Fadila tayi wani gauron nishi mai qaraji da yasa aliyyu ya sake rudewa sai ga baby ya fado,kukansa ya cike Daki,daya Daga cikin nurse din ta daukeshi,doctor ta taba cikin ganiñ fadilan na sakeyin wani nishiñ,sai ga kukan wani yaron shima ya taya dan uwañshi callara kuka
"Alhamdulillah"doctor sa'adah ke fada tana sake dubà fadila



"Mtsweeu,inajin da wa ni yàron a cikin nan"ta soma taya Fadila qoqarin fidda sauran abinda ya rage a cikinta kasancewar qarfinta ya qare,jikinta ya soma saki,da qyar aka zaqulo dayan Maca ce,sai dai ita din wani irin kuka take baya ma fita sosai bisa dukkàn alamu taci wahala don har ta fara kashi a ciki,kam wa ni gado doctor ta dorata aqalla mintina girma sannan ta dagota
"Sa'adiyya karbi zaitun ko lotion a goge musu jiki,baza'a yi musu wa ka ba har sai gone"tace da aliyyu Wanda baima San meke gudana a dakin ba ,kacokam hankalinsa na kan matarsa



Ya kalleta"ki nadeshi kawai doctor, bamu zo da komai ba"ya maida hankalinsa kan màtarsa dake ta sakiñ ajiyar Zuciya,doctor ta Daga wayarta tayi kira tana bada umarni aje shop din cikin asibitin da yake nata ne a dauko riga unisex mai bude da showel guda uku,cikin qanqanin lokaci aka gogesu fed,doctor ta qaraso kañsu,cikin damuwa ya kalleta
"Doctor taqi motsawa fa har yanzu"murmushi tayi "kada ka damu,mun riga mun kashe Duk wani tasiri na gubar ai zata dawo hañkalinta insha Allah nan da wa ni dan lokaci,yanzu za'a gyara mata jikinta ne don tafi jin fadi,zatayi bacci na minti talatin da zarar ta farka zata koma normal,congratulations *Mr Aliyyu Salim mai tama*,ka Samu yara har uku,biyu maza daya mace"



Jinsa Kayi kamar cikin mafarki ake gayamasa hakan,wa ni sanyi ne mai dadi ke ratsa zuciyarsa,ya zaro idànu"pls doctor bama irin wannan wasan,are you serious?"
"Am serious aliyyu,lokacin da suke isowa Baka ji ba?,gasu can ai"tai masa nuni da su banda macen da aka ware a wani dan gado daban,ya zuba musu ido yanajin kamar ba haka bane
"Kada a fiya daukan baby girl din,don ta bugu sanda mamanta ta fadi,ta fisu shan wuya,zamu riqeku na three days don zamu na bata treatment"



Mai karatu fasalta irin farinciki da wannan family gida biyu suka Shiga wato familyn *Alh Abbas Abdallah* da *Alh salim mai tama* bata baki ne,godewa Allah kawai suke suka qarawa da 'yarsu ta tsallake rijiya da bakya ga kyautar kyawawan yara har uku tare da sake addu'ar samun lafiya ga Fadila dà baby girl dinta,Daki ne qato guda daya mai kyau aka ware musu aka zuba gàdajen yaran,aliyyun na zaune dirshañ gaban gadon yana jiran farkawarta ,tuni ya miqa musu yaran bayan ya tofesu da addu'a,ai kuwa dan qaramin biki aka bude a dakin,shikam yana jinsu don ta matarsa yake tukun



Cikin ikon Allah ta farka da qwari a jikinta,da fuskar mijinta ta soma tozali,ya sakar mata murmushi yana fadin "sannu 'yar albarka"ta dan lumshe idonta cike da kunya,shi da Kansa ya taimaka mata ta wanke bakinta ya hadà mata tea mai kauri ta sha,kowa sañnuñsa yake miqa mata



Dukka yaran ya Jere mata a gabanta yana dubanta"Fadeelah na kinga irin kyautar dà Allah yayi mana ko?"kasa magana tayi,cikin zuciyarta godewa Allah take mai hukunta abinda yaso,kunyar su momi take wa sanda ba su San ma suna abinsu ba,da yaga taqi dauka sai ya debesu gaba daya ya dora mata saman cinyarta ya hadasu ya rungumesu gaba daya yana jin duminsu,tuni kowa ya fice a dakin sai juyowa sukayi suka ga Wayam



Fuskarta ta dago Daga kan yarañ tana Kallon aliyyu,gira ya Daga mata yana cewa"kin yarda ni din jarumi ne ko?,Dukkaninsu da ni suke kama,baby girl ce kawai tayo kamar fatarki"sai tayi kicin kicin da fuska"ai zasu dawo kamata ne"ya tuntsire da dariya"inaaa......ai sai dai ki tara a gaba"
Gwalalo ido tayi"haba my haidar,ni kam na gama Daga wannan,wlh sun isheni"ta qarashe maganar kamar zatayi kunya
"No baby,ni Kuma wlh inason kamar haka sau shida,"fashe masa da kuka tayi,Dariya na ciñsa yana lallashinta a haka Momi ta shigo ta tadda su




*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*part 3*


3⃣3⃣


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"ta soma fadi tana riqe tamau d cikinta,cikin azama baba talatu tayi kanta tana tambayarta"lafiya?,me ya faru?"
Sai dai ina!,tuni kafin ta qarasa kanta ta rikito daya kan Kujerar da take zaune ta kifa qasa warwas kan turtsetsen cikinta cikin fitar hayyaci,da gudu baba ta qarasa gami da dagota,jirin ne ke fita ta qasanta da bakinta gami da ragowar ayabar d abata qarasa hadiyewa ba,ko kuwa babu alamun numfashi tare d ita,hakan ne y gigita baba talatu ta saki salati mai Mutuwar qarfi da nuna razana Wanda yasa salima juyàwa cikin sauri don barin gurin



Sai dai kafin Takai ga ficewa su Kayi kacibus d samira,tabi Salima da kallo ganin irin saurin da take zubawà tuni har ta wuceta,ita kuwa salatin babarne ya janyo hsnkalinta don wucewa tazo yi,da sauri ta taka tq shige bangaren Fadila don ganin meke faruwa,dai dai lokacin baba jita kokawa da wayarta don Neman mutum daya cikin biyun aliyyu ko momi,abinda Samiran ta gani yaso bata tsoro,da Sauri ta juya ta koma da baya,batayi wata wata ba ta soma qwalawa isyaku kira,sun San halin rashin Kirki irin natà don haka jiki na tmrawa ya iso
"Yi maza ka dauko Mota"



Bai tambayi ba'asi ba ya juya don cika umarninta,sanda ta shigo har baba ta gama Sanar da Momi,Samira tace"rashin maza baba mu kamata ku wuce asibiti kada ta zamar mana gawa my shiga uku gun Ali"(gaboncin magana kenan irin na samira),da ita aka sanya fadilar a Motar sai dai bata bisu ba,ta dawo tana tunanin me ya sameta haka?,dage kafada tayi don bata sani ba ta koma barandarta ta zauna tana nazarta yadda salima ta killed bangarenta tayi lakur a ciki,duk da tana jiyo tarin salatin da ma'aikatan gidan ke ta zubawa



Daga qarshe ta dauke kanta tana tsammanin shegen kishinta ne da yafi nasu ya motsa,Duk da lokaci lokaci tana tambayàr kanta me tayi a bakin window din?



Momy,Anty hauwà,farida,Anty hafiza d rabi'ah da tazo gida duk su na cikin asibitin,hankalinsu ya kai qololuwar tashi,tunda aka shige da fadilan wa ni daki har yanzu shiru babu ita babu likitocin,a lokacin aliyyu ya shi go asibitin,wujiga wujiga kamar Wanda akayi wasan kura dashi,idanun nan kyawawa farare tas sun kada sun koma jazur,kai tsaye momi ya tunkara yana tàmbayarta ina fadilan ta Samar dashi sun shiga da ita,cikin rudewa ya soma fadin"ya za'ace daga cikin bana na sai irin wannan abu ,kuma ba naquda ba,haba don Allah"



Bana talatu tace"ni kaina abuñ ya dauremin kai,muna cikin hira fa sai salatinta naji"
"Baba ko wani ya shigo,ko Kuma kun bar qofa a bude?"aliyyun ya tambayeta
"Eh,tabbas ta dn fiya barañda ta tattaka yadda likita yace da ita,to kafin ta dawo lokacin ni na shiga ciki na kanta,to ina tsammani ta manta ta bar" qofar a bude,kai tsaye ya nufi dakin da aka shigar da ita din gadan gadan Momi na ta kiransa amma ko daya kunnensa baima ji kiranba har ga Allah



Kafin yakai ga qofar ta bude ,likitoci uku ne suka fito ciki yarda doctor sa'adah,tareta Aliyyu yayi da tambayoyi barkàtài har ta rasa wacce zata amsa masa
"Cool down Mr aliyyu,my qarasa guñsu Momi",ganin tahowarsu yasa duk suka miqe suna tambayar me ake ciki?,doctor sa'adah tace"da farko dai mun gàno ayabarnan da taci tana dauke da gaba mai màtuqar qarfi"
"Gaba!"suka hada baki gurin fada banda aliyyu DA yace"what?!"cikin qaraji"waye ya aikata min haka?,tabbbas ko waye bazan qyaleshi ba"



"Calm down aliyyu,yanzu ba lokacin wannan bane,lokacine na yaya za'ayi a tseratar da ita dà abinda ke cikinta,kada su illata"ya sake tsare doctor din kamar zai dauketa gumi ne kawai ke tsatstsafo masa
"Ok doctor Meye solution?"
"Dole zamu qirqiro mata naquda tunda cikin nata dama ya isa haihuwa har yaso wuce watanninsa,mun sa mata ruwa indai ya qare aka sa mata wani yayi rabi bata haihu ba dole zamuyi mata c.s na gaggawa,sai ayi mata addu'a Allah ya rabasu lafiya"



Tuni kafin ta qarashe bayanintà aliyyu ya shige dakin,tana kwance sambal bisa gadon sai uban ciki a sama tamkar an sake turoshi,idanunta a rufe suke ruf hancinta sanye d oxygen, kayan d asibitin ke sanyawa mai naquda ne sanye a jikinta,fuskarta luf luf tamkar zata yi magana,Zara zaran gashiñ idonta sun fito reras,sai dai babu wani Abu dake motsi a jikintà,nurse biyu ne cikin dakin dayar na Gyara zanin da aka rufeta da shi Zuwa saman cikinta,dayar Kuma na tattare kayayyakiñ da sukayi magani da su



Zuciyar aliyyu ta karye gumi ya sàke yanko masa,hankalinsa ya sake tashi,ya qaraso bàkin gadon ya sanya hannunshi cikin nata yà zuba mata ido"Fadeelah waye ya yamin wannan aikin?me kuka yi masa ?,wanne zuñubi kuka aikata masa ke DA halittar da bataji ba bata gani ba,pls Fadeelah kada ki tafi ki barñi,Kiyi qoqarin ci gaba da rayuwa da ni don Allah matata,wlh idan babu ke nima babu ni"shi kadai ke zuba sumbatun nurses na kallonshi,sai da ya gaji don Kansa yàyi shiru don wadda yàkeyi don ita ma batasan yana yi ba....



*Mrs Muhammad ce*👑


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*part 3*


3⃣5⃣



a haka Momi ta shigo ta tadda su"a'ah,Ali mai Kayi mata ne?"cikin dariya yace",sai Momi don bace ina son kamar yaran nan sai shida"kunya ta lullube Fadila, daquwa momin ta wata masa "ja'iri kawai,amma dai Baka da tausayi ko?,to yanzu zan kora ka kuwa ka tafi gida"ya Daga kafadunshi duka biyun
"Momi na ba sai kun Kore ni ba ma tafiyar zanyi"sai Kuma yanayin fuskarsa ya can za"zanje na binciki yadda akayi poison ya shiga cikin ayabar nan,dolene Duk Wanda ya aikata hakan ya karbi sakamakon sa a hannu"



A hankali ta dago da kanta dake duqen"don Allah yaya kabar maganar nan,ni na riga na yafe tunda Allah ya bani ka fiya da kariyarsa,Wanda ba wayo ko dabararmu bace haka din"
"Shshshsh!,shut up, ni ban yafe ba,kada Kuma na sake jin bakinki a maganar don yanzu hurumina ce"
"Gaskiya Fadila ta fada,idan ka dage da bincike kamar ka yiwa Allah butulcin kubutar amma da iyalinka ne da yayi maka,sai dai Nima ban lamunci a qyale maganar ba saboda gaba,ya zama lallai ka qara matakan tsaro"



Koma wa yayi da baya ya zàuña yana jijjiga kai,ba yadda ya ita tunda Momi ta shigo ciki,wayarsa ya zaro yayi kira,ya soma magana inda yà Daga qarshe suka ji yana bada umarnin a kawo masa c.c.t.v camera guda hudu Daga yau Zuwa gobe(hmmmmm,a juri Zuwa rafi da tulu debo ruwa,wata rana.......)



Kwana uku Fadila tayi ragal da ita har yaran,tamkar babu wani Abu da ya faru da su,tuni haihuwar Fadila ta karade ko ina,dangi da ba dangi ba,'Yan asibiti kam sunsha kallo yawan 'yan barka dake tuttudowa a kullum yasa ta qagu a sallamesu wasu ma fadila bata sansu ba



ga aliyyu dà kulli yaumin yake bata kunya, Duk yawan mutane idan yazo baijin kunyar rungumeta ko riqeta,sai dai su bude ido suya kuwa ya fashe ya bar musu dakin



Cikin kwana na hudu ne doctor sa'adah ta sallamesu,da yake safiyya ce Daga rabi'ah sai farida dake fama itama da qaramin ciki Duk sauran ba su qaraso ba,cikin motarshi pilot suka shige shi d yaranshi,yayi da rabi'ah d farida kuwacce ta shige tata don su rabi'ah ma sunyi mota suka bisu a baya



Sai da suka kuwa Zuwa titin gidansu taga ya dauke hanya ya sauya titi,ta kalleshi"kai da zaka shiga lamido crescent ya ka canza hanya?"
"Eh ina sani"ya fada mata yana murmushi,sannu a hankali ba tare da wata tafiya mai nisa ba suka qaraso



Baki ta saki cike da al'ajabin abinda take gani,wa ni irin mansion house ne da bata taba tsammanin d irinsa a qasarnan tamu ba,tun daga makekiyar get da zata maka hanya Zuwa ciki ta fara tsinkewa da lamarin gidan,har bakinta ya Gaza yin shiru
"Habiby wai gurin wa maka zo ne?"
"Gidanki ne fadilata"ya fadi yana kashe Motar



Har ya fito ya zagaya baya Inda yaran suke ya dauki babban d mai bai màsà ya rungume a kadarsa tana zaune dirshan cikin Motar sai da ya leqa yace mata
"Mummy 'yan uku fito mana ki dauko baby girl"



Binsa kurum take a baya tana kalle kalle kamar dan qauyen da ya shigo birni,gida ne amma gari guda,duk iya yadda kàke tsmmanin kyau haduwa da tsaruwar gida to ya kai nan,fenti tiles furanni da hadi da roping da Kayi wa gidan duka fari ne,qyalli dà qamshiñ sàbuñtà kawai yake yi



Kai tsaye suka nufi daya Daga cikiñ part din dàke kewaye dà harabar gidan,qofa ce mài kyawuñ gaske suna zuwa ya Danna wàni maida ni cikin second biyu ta bude suka shige,makekeñ parlour ne Wanda ya lanqwame kujeru har set uku,mai karatu sài na kammalà rubutà littàfin nan ban gama fasalta muku shi ba,don haka na bàr mai kàratu ya fàsàlta abinsa,



Ya juyo guntà a bayan ya kwàntar da yaran ya karbi macen itama ya kwantàr sannan ya kama hannuntà ganin yadda qwayar idànuñtà sukayi raurau,baice mata komaiba ya ja hannunta tana biye d shi,ciki da bai na part din nata yake nuna mata,sama suka fara Hawa,parlour ne shima mai girma gaske sai dakunan bacci gida hudu,daya nasa ne daya nata,daya na yaran,daya Kuma safaya ne kawai,ita dai ido ta zuba,don Duk wa ni Abu na alatu da qawata gida da jin dadi babu Wanda ba'a zuba ba,dakin yaran kawai kansa abun kallo ne,dauke yake da wa su irin hadaddun gadaje na yara musu rumfuna



kowanne da drower dinsa mai zubin cupboard wadda ta kere rabin bango,cike dakin yake da Duk wa ni nau'i na kayan wasan yaran,sai many an frames masu dauke da addu'o'in tsarist maqale saman gadon kowa,idan ka dauke tulin kayan wasan babu surar photo ko daya a dakin,sai wata 'yar qaramar t.v plasma dàke manner a bangon dakin tana fidda sautin karatun alqur'ani,sai c.c.t.v dake manner quryar dakin wadda hatta fadilan bàtasan da ita ba,luf luf dakin yake dai dai da buqatar jariri



sake riqota yayi suka sauko suka ratsa ta wani corridor baya ga faluka biyu da suka wuce,dakunan bacci ne guda uku baya ga kitchen store a parlour na biyu,sai kitçhen store public toilet a parlour na farko,daki na uku da suka shiga nan ma dakin yaran ne,gira ya Daga mata bayan ta kalleshi
"Nan dakin 'yan uku zasu dawo da zata kin kuma ajjiyen wasu ukun"
Cikin shagwaba ta soma dukan qirjinsa"Baka tausayi na ko?,ba momy tà hana fàdà ba"
"Sorry sañyin idaniyata"ya fàdà yana maida hàññuñsa ya rungumetà a qirjinsa



Zaunar da ita yàyi gefàñ gadon,dà Kansa ya dingà dauko dà wadansu irin akwatuna da batà taba ganin irinsu ba,saida ya sauke 12 tana binsa d ido ba tare dà tace komai bà




*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




*part 3*



3⃣6⃣



"Kayanki ne ke da yarana"ya fadi yana bubbude mata akwatunan gami da yi mata bayani nata uku yaran ma kowa uku uku
Shaqe suke da kayan na alfarma,musamman yasa ma'aikatan company dinsa na india suka fidda taswirar design din kayan ,design ne da sai nan da shejara mai Zuwa ma zasu fidda shi,ita kam ta rasa mai zata ce,da ta bude baki zata yi masa godiya sai yayi kicin kicin,hakanan taja bakinta ta tsuke jiki a sanyaye ta tayashi rufe akwatunan



Yasa hannu ya dauko wa ni qarami dake rude daban ya budeshi,wasu takardu ya fito da su ya dorasu saman cinyàrta
"Estate ne guda uku da dake ginawa cikin garin abuja,ga takardunsu nan na mallaka wa 'yan uku,sannan akwai wasu tàkardun na company na ne da kikaje rakani budeshi na China,Daga qarshe kika gudo kikà barni"ya qarshe da sigar tsokana da ta bata kunya"na mallaka miki shi fadeelà ke kadai kikà fi cancanta ki mallakeshi,don kinsan sanadiyyar budeshi ce ta jawo kika haifamin wadannan taurarin"



Takardu guda hudu Kuma daya na shaidar mallakar motoci ne guda biyu,daya taki daya ta yaran na,ragowar Kuma ki cike min idan kin samu lokaci na central bank ne kada Kuma ki tambayeni me zanyi da su"



Zamowa tayi Daga kan gàdon ta durqusa a gabansa
"Na gode mai dear,na gode na gode,bani da abun cewa face Allah ya biya ka da aljanna ya qara budi,ya raya maka zuri'arka"tafin hannunsa yasa ya rufe mata bakinta
"Ya isa Fadeelah,nike da godiya,don naji a jikina har yanzu ban saka miki irin halaccin da haquriñ da kika yi da ni ba"
Kanta a qasa tace"alfarma daya nake nema a gunka"
"Uhmm fadeta naji,don kinfi qarfin koma a gurina"



"Wannan kyautar dear tayi yawa,kasa na zama abar zargi ,kada ina cikin zama na ka jawomin wata fitinar ta daban,mun gode da kyautarka amma pls ka barsu"
"Idan mà Momi kike ji ta Dade da samun zamansu,gani ma take sunyi kadan"
Ta girgizà kai"Sam nasan momi sosai,ba ita nàke wa ba,abokan zamana fà?"
"Ina ruwanki da su?,su Haifa mana suga suma idan ban musu ba,wannan kyautatawa ce kina yimin dole Nima nayi miki,sama na yi musu dai dai tasu,na canza musu komai na part dinsu kamar yadda na yi miki,na basu kudade,na canzà musu mota,to me kike buqata?"



Ta karyar da kanta"Duk da haka ina tsoron fitinà"sai ransa ya baci ,ya miqe ya kwashe takaddun Daga cinyarta,bai ce uffan ba ya maida cikin akwatin ya fita da su,duk sai taji ba dadi ta bishi da kallo



Kasa tashi tayi har sai da ta jiyo magana sama sama kamar a parlor din farko ta miqe ta fito,umminta ce da Anty hafiza da yaronta khalifa Wanda yaci sunàn abba su wato abbas sai farida da rabi'ah da suka Bari a baya,da sauri ta rungume ummin nata tana jin wata qaunar ta na shigarta,tunda tq haihu bata zo ba sai ya,wani hawayen dadi suka soma zuba,ita kanta ummin rungume fadilan tayi,Tasman 'yarta mai alkunya ce da zurfin ciki,tunda har ta ita rungumeta tabbas ba qaramin jin dadin ganinta tayi ba



Farida ta zauna gefan fadilan bayan ta gama zagaye dakunan da gidan
"Sister ki godewa Allah"
"Allah shine abun godiya"
"Gaskiya kam babu abinda za muyi sai godiya ga Allah da ya azurtamu da mazaje na gari"cewar farida
Hira suka dinga yi abun su mai dadi,inda daga qarshe farida Wanda babu ce kawai babu ta Dora musu abun ci,da daya da daya saiga 'yan barka ana rakosu,sai Murna ta zama biyu,ga ta samun qaruwa ga ta canza sabon gida



Qarfe uku Muhammad ya shigo da akwati yana fadin ummi taje inji abba zasu wuce,ai kuwa Fadila taçe ina ai sai ya shigo da kanta ta shigo da shi din,ya dauko yaran ya musu addu'a cike da alfahari da jikokin nasa sannan ya Ajjiye musu check na dubu Dari da hamsin kowa dubu hamsin hamsin,sai akwatin da ummin ta ciko guda biyu na kayan Barka na fadilan da na yaran,kuka kawai fadilan ta saka tana jin qaunar iyayen nata na sake daduwa a ranta,ita da farida suka yi musu rakiya har bakin Motar su



Haka Mubarak shima akwati gud ya musu,farida Kuma dinkakkun shaddodi ne da atamfofi na fitar suna ta yiw 'yaruwarta,haka Anty hafiza da ya ahmad kowa da nashi barkar,yara dai sunzo da wani irin alkhairi mai tarin yawa


_*ina labarin salima?*_


Bangaren salima kuwa tuni ta baza kunnuwa da idanu taga ko taji ta inda labarin Mutuwar Fadila zai fito kwana daya biyu uku shiru,a maimakon haka ma cikin kwana na ukun sai ta jiyo muryar Aliyyu na bawa na shiru umarni yaje company ya amso wa 'yan uku sleeping dress, da gudu ta fito tana fadin"ta haihu?"



A hagunce Aliyyu ke kallonta cike da mamakin yadda ta fito a forgive"eh ta haihu ta samu yara uku kuma duk suna cikin qoshin lfy"da sauri ta saura kanta don ganin irin Kallon da yake mata,ta waske"wlh hankalina a tashe yake tunda aka fita da ita,kai amma naji dadi"
"Eh shi yasa aka rasa Wanda zai bita a cikinku"
"Ba haka bane rudewa mukayi har suka tafi"



Tana shirin komawa ciki ya tsaidata"zan fita ki sañar da samira an jima na shiru zai zo ya maida sabon gida,ba sa8 kun dauki komai ba sai dai ko kayan sawà"ko amsawa bata iya yi bà,shim a bai lura ba don ya rigata barin gun



Tana shiga daki ta Dora Hannu aka ta zunduma ihun baqinciki da takaici
"Wayo Allah na na shiga uku Fadila kin fice ni,kin gama da ni,yara har uku bama daya ba?,wlh bazan qyaleki ba"haka ta dinga Kuka shabe shabe kamar wata qanqanuwar yarinya tare da sake cin alwashi




*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




*part 3*


3⃣7⃣




Ana saukesu a harabar gidan Samira ta fito ta qarewa gidan kallo,gida ta saki
"Allah na gode maka,kyau nice a wannan aljannar?"ta kama habarta,sai Kuma ta dubi sashen Fadila da 'yan Baka suke ta kara kaina
"Wai Matar can ta haihu ne?"tayi tambayar ba tare da ta nemi mai bata amsa ba



Ko kula ta salima bata yi ba,don ji take kamar ta shaqeta,a son samunta tana gamawa da fadila Samira ce next target dinta,sai nasiru ne dake rufe Motar yace"ta haihu gajiya 'yan uku Allah ya bayar
"Iyeeee"ta fadi tana kama baki" gaba Samira tayi abinta ta soma gwada muqullanta har ta dace era bangarenta ta bude ta shige



Sai da ta gama zàgaye bañgaren nata sannan tace bari the bangaren fàdilà taga jàriran da dai ake fada,haka nan taji t

Please Login or Register in order to submit comment