Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muna cikim gida ne fa yanzun,it can be possible wani ya fito ya gan mu a....." kanta qarasa tuni ya janyota jikinsa daidai lokacin uncle abba ya fito daga cikin gidan hannunsa dauke da carbi da alamu masallaci zashi

Sarai ya gansu amma sai ya dauke kai tamkar bai kula da su agun ba,farinciki yaji sosai cikin zuciyarsa "alhamdulillah"kawai yaje fadi cikin ransa,bisa dukkan alamu sun sasanta kansu kenan,yanzu yake ji a zuciyarsa zai iya maida fadilan gidan aliyyu,don duka alamu sun nuna na qauna da soyayyar da suke ma juna,fadila ce ta soma ganin abban lokacin har ya basu baya,ta zare jikinta da sauri tana gyara yafen mayafinta zuciyarta na bugawa tace "innalillahi" aliyu ya kalleta"lafiya baby?"
Uncle abba ta nuna masa da yatsa tuni idanunta suka cicciko da qwalla "ya ganmu wallahi,sai da nace ka bari ka bari fa"

Dariya ya saki cikin nishadi "to mene ne?,kinga addu'ata ta karbu kenan,kuma ma baby naga da mijinki ya ganki fa mene na rudewa har irin haka?" Ya jawo hannunta yana goge mata qwallar da ta soma gangaro mata "calm down my unique,don't cry again,kin gama kuka a duniya ai matuqar ina tare da ke,I will never let your tears to fall down again.....muje ma raka ki ciki"sai taga tunda abba ma ya riga ya gansu a dazun don rakata ma cikin gida ba komai bane,abun kunyar dai an riga an gama tafka shi,tayi tayi da shi ya bata jakarta ta riqe yaqi yace sai ya kaita har ciki,sai da yace idan ma ta fiya matsawa zai goyata ne ya kaita har cikin gidan,tasan kadan ne daga aikinsa,tilas ta bar masa tayi gaba yana take mata baya......

*Mrs muhammad ce*👑

📚📚📘📘✍🏻✍🏻
[10/16, 2:15 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3* 👈🏼

1⃣9⃣&2⃣0⃣

Ai kuwa sukayi kyakkyawan gani cikin parlour,momi ce da iftihal dukkansu suna zaune kan kujera sanye da hijabi da alama sallah suka idar,karatun qur'ani iftihal keyi da ka momi na gyara mata kura kurenta,kallo momin ta bisu da shi daga bisani sai kuma ta dauke kanta tamkar bata gansu ba,ya miqawa fadila jakarta da take ta Allah Allah ta bar falon kunya gaba daya ta rufeta,gogan harda hadawa da hannunta lokacin da zai miqa matan,ta zame hannun nata da sauri ta haye sama inda dakinsu yake,ya wani bita da kallo ko kunya baiji ba,sai da ta qare hawa sannan ya janye idonsa ya juya da niyyar gaida momi

Ashe idanunta na kansa take suka hada ido,sai yaji wata kunya ta kamashi,yasa tsinin key din motarsa yana sosa tsakiyar kansa irin najin kunya,yakoma gefe ya tsugunna yana gaidata yayin da tuni iftihal tayo qaura gurinsa,maimakon momin ta amsa sai tace "rasa kunya beran tanka,tashi ka bani guri,kada na kuma ganin kana takura mata daga yau,na gaya maka ka qyaleta tayi hukunci da qashin kanta,idan ba haka ba tamu ce ni da kai"ya miqe yana murmushi lokacin da yake maida iftihal kan kujerar kusa da momin,abinka da wanda bai iya qarya ba sai yace "momi ba takura mata nake ba,ai tama gama yanke hukuncin,mun gama magana da ita momi"baki sake ta bishi da kallo lokacin da ga fara tattaki zai bar falon "iye?,me kace?" 
"A'ah momi bari inje nayi sallah"shima ya fada yana waiwayo wa gami da sakin dariya wa momin har ta fice
"Ja'iri ka maida ni kakar ka ko?"
"Momi ai dama kakarsa ce ke"inji iftihal dake faman wasa da bezar hijabinta,duk sai suka bata dariya 'yar da uban,cikin zuciyarta tqna addu'ar Allah ya daidaita ya sake tsakaninsu

Kowa ya hallara a dining har aliyyu da yaqi tafiya amma qememe fadila taqi saukowa,ita kam ba zata iya ba,bala'in kunyarsu abban take ji don aliyyu ya gama kunya tata,kuma ta sani ko da ta sauko din tunda aliyun na gun ta tabbata sai ya sake kunyatata kafin a tashi,haka abban yace a qyaleta don yasan me take yiwa kunyar,sam sai yaji abincin bai masa dadi don mafi rinjayen zaman cin abincin nasa saboda ita ne,suna tsaka da cin abincin ya soma tari kamar ya qware,sai yaqi daukan ruwan dake kan table din yayi hanyar kitchen su abba na masu sannu,ganin idon kowa bai kanshi sai kawai ya haye matattakalar sadaf sadaf yayi sama,momin ce ta soma ganoshi ta dan tabo uncle abba yadda su sumayya ba zasu gani ba ta nuna masa aliyyun,dariya uncle abban ya saki shida momin duka,

Tana zaune dirshan tsakiyar gadon,gabanta system ce a bude tana faman aiki cikinta,doguwar rigar yellow din material mai santsi ce a jikinta,mai tankakken hannu ne dinkin ,babu abinda ta shafa illa man lebe da ya qarawa lips dinta taushi,sai jikinta dake tashin qamshin turaren asaal,kyakkaywan gashinta baqi sidik mai tsawo da qyalli yasha gayara ta tajeshi ta daure shi da qaramin ribbon yellow ya sauka gadon bayanta yana reto,hundred percent hankalinta na kan system din,alewar mints ce a bakinta tana tsotsa a hankali,sai da ya gama qare mata kallo iya son ranshi "unique lady"ya fada cikin ransa,komai nata mai aji ne,yanayin zaman nata bisa gadon sai ya zamewa aliyyu abun sha'awa,lallabawa yayi ya haye gadon ta bayanta,sai jinta kawai tayi rungume jikin mutum,a dan firgice ta waiwayo ya manna mata kiss a goshinta tare da sakin murmushi"me yasa kika qi saukowa kici abinci bayan kin sani bazan iya tafiya ba tare da na kalli wannan kyakkyawar fuskar taki ba"ya qarashe maganar yana shafa gashinta da ya qayatar da shi

Zumburo baki tayi kamar na shagwababbun yara tana dan kici kicin qwace kanta "haba mana dear dakinsu sumayya ne fa,suna iya shigowa su ganmu"daga hannunwansa yayi yana murmushi🤗"is ok,indai so kike na qyaleki sai idan kin yarda zaki bani hot kisses a matsayin sallamarmu ta yau"sak tayi ta kuma yo kicin kicin da fuska,murmushinsa ya dadu yace "uhm,am waiting dear"nan ma shiru,ya dora kansa saman kafadarta yana leqen fuskarta,saura kadan ya fashe da dariya yadda yaga tana zare idanu,ta gintse dariyar yaba cewa "don't mind dear,if you are not ready kinga sai muyi zaman mu a haka ko?"da sauri ta noqe kafada "no am ready,but.....Please ja rufe idanunka" "ok....ok" ya fadi yana cikata gamida rufe idanun

Shiru yaji hadi da qarar qofa,da sauri ya bude Idanun nasa,ta qarasa sa key din qofar toilet tana qyakqyala masa dariya,sai ya harde hannayensa ya zubawa qofar ido fuskar sa qunshe da murmushi"no baby,kin karya agreement,kisses sun qara nukuwa,sun zama double yanzu,ko ki fito ki bani ko in kunce gidan key din yanzun nan in shigo toilet din"dariyarnan tata mai saurin shagaltar da shi taci gaba da yi

Sai da taji sukur sukur dinshi jikin qofar sannan ya sata nude qofar da sauri,wayo dama ya mata ba wani gidan muqulli da zai kwance,ya cafkota ta fado jikinsa suna dariya,dariyar tasu ta tsaya lokacin da wayarsa ta soma ruri,ya cirota daga aljihunsa yana dubawa,salima ke kira don itace da girki dama yau zata fita,ya kara a kunnensa,da qorafi ta fara masa kafin sallama, "ok gani nan"kawai yace mata ya maida wayar aljihun,fadila tayi lamo jikinsa kishi na sukarta,ya dago fuskarta yana kallo sai yaga alamun ta dan canza,yasan dalilin hakan saboda haka dadi ne ya kamashi don yasan abunda ake so ake kishi, "oya babe,give me"ya fadi yana sake dago fuskarta gareshi,wani hot kisses ta soma bashi wanda ita kanta bata san ta iyasu ba sai yau,sosai ta rudashi har suka gagara tsaiwa suka zube saman carpet,shigowar rabi'ah da komawarta da baya da sauri shi yasa fadila saurin zare jikinta,a kasalance ya maida idanunsa kanta,kanta a qasa tana tattare gashinta da ya yamutse tana maida shi cikin ribbon,ya sake maida idonsa bakin qofa inda rabi'ah ke tsaye a bayan labulan ta yadda yanzun bata iya hangosu "yaya,momi ce ke kiranka" "bace min a gun stupid kawai,baki iya sallama ba zaki shigowa mutane daki kai tsaye?"

Sum sum ta juya tana tabe baki cikin ranta tana cewa "sallamar miliyan nawa kakeso nayi muku ,ka shiga wannan yanayin koda ganga nake sallama taya za'ayi kaji,su yaya aliyyu ashe haka aka iya soyayya?" Sai ta qyalqyale da dariya ita kadai,yasa yatsunsa ya dago da fuskarta yana son kallon qwayar idonta amma taqi yarda "I need more please..."ya fadi muryarshi qasa qasa tamkar mai rada,tuni ta shagwabe fuska tana cewa "please.....Please,na yima fa,kuma momi ke jiranka fa ma"ya yunqura ya miqe yana gyara botiran rigarshi da suka balle yana cewa "ok"sai da ya gama ya miqa mata hannunsa har lokacin tana zaune kanta a qasa "oya get up"a hankali ta dora hannunta saman nashi ya dagata,sai jirin nata ya kwasheta tuni ya riqeta don kada ta sha qasa "fadeela I think you are not well" 
"am well"
"A'ah,ki shirya gobe zan daukeki ta office in kaiki kiga likita" 
"Amma....ai zan...."ya tsansa ya dora kan lips dinsa "shshshsh...kada kice komai"shirun tayi ya leqa fuskarta "zaki rakani gun momi muyi sallama?"girgiza kanta tayi "um um"yayi murmushi "shikenan to kwanta abinki"ya zaunar da ita gefan gadon,system din ya fara kashe mata ya maida mata ita saman madubi,ya dawo inda take yana kallonta ya kama hannunta ya sumbaci sama yana cewa "good night my dear baby na,sweet dreams,I love you"a hankali ya bude bakinta tace "I love you too my dear *haidar*"farinciki ya cikashi kamar ya taka rawa,tuni saboda kunya ta cusa kanta qasan pillow tana murmushi har ya fice

Momin kawai ya tadda a parlour din yanzun ma ita da iftihal dake shimfide kan cinyarta tana baccinta abunta,a yatsine momin ta kalleshi "sannunka kaji?" Murmushi kawai yayi idanunsa na kan 'yar diyarshi,ya shafa kan iftihal din "ayi haquri momi zan tafi sai da safe" "kada naga qafarka da safe a gidan nan" da sauri ya dawo da baya ya taugunna gaban momin "yauwa momi na,Allah indai kika bani fadeelah ta ba zaki kuma gani na da sassafe a gidan nan ba,saima kin aika a nemo miki ni" dariya taso qwace mata amma sai ta kaba habarta yana cewa "o'o'o,sannu mara kunya,to anqi din har sai ta yarda da kanta" ya kama qafar momin yace "wallahi momi fadeelah ta haqura" ta dake dariyar dake cinta "kaga,mu bata gaya mana ba yallabai sai ka jira har sai ta gaya mana da kanta"ya marairaice "momi kunya fa kinsan take ji,ba zata iya gaya muku ba"momin ta tabe baki "ok,sai kai wato rasa kunga shine kazo kayi rashe rashe a gabana kake gaya min ko,don Allah tashi ka tafi gidanka ni na gaji da ganinka anan"

Kai yake gyadawa kamar qadangare "shikenan momi,shikenan sai da safe"ya miqe ya fice cikin zuciyarsa yana fadin "zan shuka tsiya kawai,komai ta fanjama fanjan,su momi basu yanda nake ji bane"uncle abba dake can tsaye yana kallonsu yqna shan dariyarsa ba tare da sun sani ba ya qaraso "haba maimunatu,ayi haquri haka nan a bashi matarsa,tunda sun sasanta kansu,ni kam na fara tausaya masa,kinsan ciwon da namiji ma na da namiji ne"ya qarashe fada cikin zolaya,dariya uncle abban ya bata sosai"shikenan tunda abun wariyar launin fata ce nima ai ciwon 'ya mace na 'ya mace ne,sai na gyara diyata nima,idan yana so jibi ko gata sai a bashi ba don halinsa ba"

Ya sunkuya yana qoqarin dauke mata iftihal daga kan cinyarta "mudai tunda za'a bamun ai shikenan godiya muke,bari in dauke miki amaryar taki,kije ki huta kema"ta saki murmushi tana cewa "godiya nake abba"ta miqe tabi bayansa tana barwa sumayya da rabi'ah dake kitchen auna wanke kwanukan da aka bata don basa barin wanke wanke ya kwana sallahun idan sun gama su kashe duk qwaya qwayai da kayan electronic na parlour da kitchen din

Tunda ya zaunar da ita a gun ta bingire ta kwanta saboda kasala,juyi kawai take tana tariyar abinda ya farun a wunin gau gana daya tsakaninsu,babuabunda take saki sai murmushi,shi din ma koda ya fito daga wanka kasa hasala komai yayi,sai da ya zauna gefan gado ya dauki wayarsa ya kirata,tana tsaka da juyin nata ne kiran ya shigo mata,ta gyara kwanciyarta hadi da rungume pillow sannan ta amsa,sallama ta masa da muryarta mai sanyi wadda ke saka susuta shi "fadeelah bazan iya bacci ba sai naji muryarki"
"But...."sai kuma tayi shiru
"But what?,pls gaya min abu daya wanda zai sani samun nutsuwa idan nazo baccina"
numfashi ta ja sosai sannan tace"i love you for all that you are,all that you have been,and all you're to be my haidar"kalaman sun tsaru sosai cikin kunne da zuciyarsa,ta kashe masa jiki da zaqin kalamansa,idanunsa na a lumshe yace "are you sure babe?" "Yes am sure,duk abinda na fada I mean it"dogon sumba ta bashi a wayar sanna ta kashe tana murmushi qasa qasa,shi kuwa mutuwar zaune yayi gaba daya tsigar jikinsa ta zuba..........

*Mrs muhammad ce*👑

📚📚📘📘✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 2:16 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

👉🏼 *PART 3* 👈🏼

2⃣1⃣&2⃣1⃣

Shi kuwa mutuwar zaune yayi gaba daya tsigar jikinsa ta zuba

⚜⚜⚜⚜⚜

Zaune take a nutse cikin office din,sanye take da shadda dinkin riga da zani rapper marun,sosai shigar ta yi mata kyau matuqa ta kuma dace da fatarta,hakanan take kullum ba dai tayi kwalliya a kushe ba,ta iya dressing sosai,hannunta dan madaidaicin cup ne cike da coffee tana dan kurba kadan kadan don babu abinda ta iya ci tunda gari ya waye,gaba daya hankalinta na gun aliyu tunaninsa take,amma idan ka kalleta a zahiri qata news paper dake gefan hannunta ta zubawa ido tamkar mai nazarin wani abu a cikinta

Yafi minti goma a atsaye bakin qofa,sam baya gajiya da kallonta,baiqi su dawwama a haka ba,tsarin shigar tata yayi masifar tafiya da shi tayi wani das tamkar fure,sai kuma aka taki sa'a shi din ma marun din shaddar ce a jikinsa

Har ya iso bata ankara ba,a hankali yasa hannu ya zare cup din coffeen dake tsakiyar tafukan hannayenta "irin wannan zurfi a tunani bai dace da kyakkyawa ba" ya fadi yana maida cup din gefe,yaja kujerar dake opposite dinta ya zauna yana cewa "nasan dai ji kike tunani ko....to gani na iso ai sai abar hasashe a koma zahiri"murmushi ta saki a kunyace tayi qasa da kanta,ya sake binta da mayun idanun nan nasa,gani yake tamkar kullum wayewar garin Allah kyau ake dada mata,ya jawo tattusan hannunta dake zube saman table din yana matsawa,ji tayi kamar wani sinadari yake zubamata cikin jikinta,ta soma qoqarin zame hannunta tun kafin yayi mata illa cikin kunya "no baby,your hand fits in mine like its made just for me,kada ki cire"

Ta dan zame dag kan kujerar ta gaidashi,noqe kafada yayi "naqi,ni ban irin wannn gaisuwar nake so ba,let me show you irin wadda nake so"kafin tace komai ya zagayoda ita zuwa inda yake zaune yayi mata mazauni kan cinyarsa,qam ya matseta,sai da ya yamutsata son ransa sannan yace "irin wannn gaisuwar nake so ko a ina muke right?"gyada ka tayi cikin jin nauyinsa,ta bishi ne da haka amma itakam rashin kunyar aliyyun tafi qarfinta "a'ah dear,ki daina min rowar sweet voice dinki,ki dinga bude baki kina magana sannan ki dinga bude idanunki sosai kina kallona,zuciyarmu ta riga ta zama daya....dubi"ya fadi yana juna mata dressing din da suka yi "baki san me zansa ba nima bansan me zaki sa ba amma saboda zuciyarmu na manne da juna mukayi shiga iri guda"

Murmushi ta saki tana kwantar da kanta a kafadarsa,"ok,I hope kin shirya,don daga nan sai asibiti,gwara muje kiga doctor sa'adah"ya fadi yana sunkutarta kamar wata bebin roba,wutsil wutsil ta soma yi da qafafunta "please my haidar,zan iya tafiya kada ka fita da ni a haka"dariya taga ya saka,ta dan saci kallonsa don bata taba ganin dariyar tasa haka ba,ya maimaita abinda tace cikin kwaikwayar muryarta sannan ya direta "matsoraciya,dama tsokanarki nake"duk da haka bai qyaleta ba sai da ya kamo hannuwanta,a haka suka isa bakin motar,ya bude mata ta shiga sannan shima ya shiga

Ko a office sai da doctor sa'adah tayi masa wayo koreshi waje da qyar don ya hana fadila sakat ,kunyar doctor din fadilan keji shikam ko a jikinshi,da zarar fadilan ta bude baki zatayi magana sai yayi sauri ya rigata cewa "doctor rabu da ita,awo na kawo miki ita,na jefa qwallo a raga" mamaki da kunya suka kama fadila haka aliyyun yake?,tamkar ba wannan aliyyun nata ba,ita kanta doctor sa'adah din tayi mamakin yadda ya sake yana ta raha har irin haka kamar ba aliyu salim maitama ba,mintina talatin doctor sa'adah ta gama duk wani bincike da gwaje gwajenta,madaukakiyar fara'a da farinciki da ta gani kan fuskar doctor din shi ya bata mamaki "congratulations fadila,naji dadi da ya zamo nice ta farko da zan taya ki murna,Allah ya albarkaceki da samun juna biyu"ta fadi tana sanya tafin hannunta cikin na fadilan

Sak fadilan tayi tanajin kunnuwanta kamar basu ji mata dai dai ba,ciki gareta da gaske?,cikin aliyyu a jikinta?,aliyyu masoyinta?, *alhamdulilahil lazi bini'imatihi tatimus salihaat*,wannan baiwa da ni'ima ta Allah da me tayi kama?,Allah kenan mai kyauta da qari,buwayi gagara misali,mai azurta bawa a duk sanda ya so,mai amsa addu'ar bayinsa,yau ga aliyyun Allah ya bata kuma ya bata dan aliyyun cikin cikinta,ya zabeta cikin matansa yace ita zata haifa,batasan lokacin da hawayen farinciki suka balle mata ba,a hankali bakinta ya soma salati ga fiyayyen halitta,sannan ta dora da godiya ga ubangiji, "na godewa Allah gwanin iyawa,doctor pls bana son ki sanar da aliyu batun cikin nan yanzu,nasan bazai iya shiru ba sai kowa ma ya ji,kuma....."

Dai dai nan aliyyu ya turo qofa ya shigo,da sauri ya qaraso a rude ganin hawaye kan fuskar fadilan,dagota yayi ya rungume yana goge mat fuskan"me ya faru ?,doctor me kika yiwa mata ta?"ya fadi cikin hade rai,dariya sa'adah tayi "farinciki ne yayiwa matarka yawa,don ance lafiyarta qalau shine don shagwaba take kuka"ta miqa masa takardar magunguna "wadan nan zata dinga sha,but gaba buqatar hutu da kulawa sosai,idan an gama lallashin ku rufe min qofar office din sir,zani inyi round na marasa lafiya,ta sanya lab coat ta fice tana musu dariya"

Ko cikin motar kanta na langabe ne jikin sit,gaba daya jikinta yayi sanyi,sai ta ruda aliyyun gaba daya ya kasa driving din dole yayi parking din motar yana tambayarta,murmushi ta saki"am fine my haidar" duk da haka sai da ya sanyata cikin jikinsa sannan ya samu ya iya ci gaba da tuqin,ga zatonta zai maidata ne gurin aiki amma sai taga yayi nassarawa da ita,cikin rashin fahimta take dubansa "nayi zaton zaka maida ni ne office ko tunda ban tashi ba"ya girgiza kai "no fadeelah,yau gidammu zamu koma"
da sauri ta dubeshi "gida haidar?,bada izinin su uncle abba ba?"
"Shshshshsh!" Yace "nafi kowa iko da ke fadeelah,na gaji da rashinki,na qosa kiyi haquri kawai idan naje gidan ni zan sanar musu,zan fahimtar da su ba laifinki bane,bare ma ba zasu ce komai ba I know"
Ta zumburo zata sake magana "tuni ya sanya bakinsa cikin nata ya hanata cewa komai,saura kadan sitiyarin ya kubce masa Allah ya taqaita ya kamo shi

Da kanshi ya bude mata part din nata don babu key din a a lokacin a hannunta,sai zumbure zumbure take ita a dole fushi takeyi da shi,shi kam dariyarsa ma yake lokaci lokaci,bai damu ba tunda burinsa ya cika,fridge ya nufa ya ciro ruwa duk da babu sanyi kasancewar wutar bangaren a kashe take,ya jawo gabanta ya durqusa,ya jawo ledar magungunan ya ballo mata,ya bude gorar ruwan sannan ya kalleta "haa" yace da ita,shiru ta masa sai da ya sake cewa "bude bakinki"nan ma tayi shiru,sai ya dire ruwa da maganin kan center ya miqe yana shirin core rigarsa yana cewa "tunda kin zama kurma inada muqullin bude bakinki" a razane ta dubeshi,bata san lokacin da tace "me zaka yimin?"yadda ta razanar da kuma yanayin yadda tayi maganar shi ya bashi dariya,ya tuntsure da dariyarsa yana maida rigarsa da ya soma cirewa har fara qal din vest dinsa ta soma bayyana,ya koma gabanta ya tsugunna yana cewa "ashe dai matsoraciya ce,baki shirya fadan ba amma kika takaloshi,oya bude bakin"bata ko sake musawa ba ta bude ya sanya mata magun gunan sannan yasa maya ruwan a baki har sai da ta hadiye

Ya miqe ya cire mata mayafin da dankwalinta,ya zare mat sarqa da dan kunneta duk tana kallonsa,ya debe qafafunta ya maida saman kujera ya dora mata pillow sanann ya harde hannayensa a qirjinsa yana duba agogon dake manne a bango "oya,maza kwanta kiyi bacci ko na one hour ne don maganin yafi saurin bin jikinki,after one hour sai ki tashi kiyi sallah ok?" Cikin shagwaba wadd ta ruda aliyun tace"amma dai kasan ban kyauta ba ace daga zuwa gun aiki ace na dawo gida na ko?"sauje hannun nasa yayi ya dawo gaban kujer ya tsugunna har yana jingina gwiwoyinsa jikin kujerar,ya koma serious sosai,yasanya tafin hannunta cikin nasa,sosai ya sa qwayar idonsa atata "fadeelah" kallon cikin idonsa tayi,yadda taga ya zama serious hakan yasa ta bawa maganar tasa muhimmanci "duk duniya babu mai haqqi a kanki daya kaini,bana so ki dinga sawa ranki damuwa kan binda yake mai sauqi ne,su momi sun ajjiyeki ne don ku sasanta kanmu da kanmu ba tare da kowa ya shiga ciki ba,sannan ni na sake gane kuskure na,to yadda suke so din duk ya faru,me kuma ya rage?uumm?,sai mu dawo gidan mu fadeelah mu shimfida sabuwar rayuwar auratayya wadda zata kuma farantawa iyayemmu rai,ina kuma fatan zan samu goyon baya daga gareki?"

Sosai take gyada kai "insha Allah mijina,na yi maka wannan alqawarin" ta dam zamo daga saman kujerar ta durqusa itama a gabansa "ka yimin afuwa ranka ya baci,ya saki qayataccen murmushi "ba komai baby na,bakya taba yin laifi a guna"ya sumbaceta sanna ya maidata ya kwantar saman kujerar,"kiyi bacci sosai,banda cewa zaki tashi kiyi aiki,gidanki babu dattin komai,don kullum sai na share miki shi"tana daga kwancen ta qwalalo ido "shara?kuma da kanka?"murmushi ya kuma saki"kina mamaki ne?,kinfi gaban haka,mene ke baki bani ba a rayuwarki fadeelah?"itama murmushin tayi "haqqina ne ai In maka har fiye da hakan" "jiniina kai yayi cikin zuciyarsa yana godewa Allah,babu shakka yayi gamo da katar da mace ta gari,wanda samuntabke matuqar wuya a wagga zamani "ina sonki my baby fadeelah har bansan adadi ba,ina alfahari dake,ina alfahari da kasancewarki cikin rayuwata"ta rufe fuskarta da tafin hannunta "ina sonka haidar dear,nima kuma ina alfahari da kasancewar ka miji a gareni har abada"wani dadi yaji ya kama shi,ya sake sumbatar bayan hannun nata yave "na gidewa Allah fadeelah,sai na dawo,zansa nasiru ya kawo miki motarki ,sannan zan daukar miki excuse gurin aiki su baki hutu na sati"bata ce komai ba don bata son ta kasance mai yawan musu da shi,bare itama zata so hakan,don tana buqatqr lokaci da zatayi wasu 'yan gyare gyare,sabida haka kai kawai ta gyada masa tana satar kallonsa ta tsakanin yatsunta har ya fice,wani annushuwa da farinciki da kwanciyar hankali mara misali taji yana ratsata

Ta janyo wayarta ta nemo number din farida,bugu daya ta dauka tamkar dama tana jiranta ne,cikin ihu take cewa "yeyyyyyy sister yaushe kuka dawo haka babu labari?"cikin murmushi fadeelah ke cewa "wayyo Allah zaki kashemin dodon kunne mana,cikin satin nan ne,kiraki nayi dama nace miki ki turo min mai gyaran jikin nan don Allah"wani ihu faridan ta sake saki cikin dariya "kai mutuniyata,wallahi da labari,tafiya tayi kyau mune winners ko?" "Kai....faridaaaa....sai yaushe zaki girma ne don Allah?" Tayi qasa da murya "kai sister,rowar story zaki mun kenan don Allah?"dariya ta bawa fadilan don tasan farida akwai son jin tsurku "hab abokin kuka ai ba'a boye masa mutuwa,zaki sha labari har sai kin gaji kin toshe kunnuwanki" "a'ah nasan halinki fa sister,zaki dai bani wanda kika ga dama,yanzu zan mata waya na gaya mata"tayi dariya "yauwa ko da yamma ne sai tazo,sau nake ta fara yimin yau don gaskiya nag ta iya" "kai sister sosai ma,ko sau daya fa ta miki sai kinga kin canza gaba daya,akinta da kyau sai tsada,bayan gyaran jiki har kitso da qunshi ma ta iya sosai" 
"to yayi,ina humairata,Allah sarki aishana,nayi missing dinta a lot" 
"Yanzu babanta ya fita da ita sitting room yayi baqi"hamma ta kubcewa fadilan har sai da faridan taji "idan sun shigo kice ina gaidasu ita da abban nata,ni zan kwanta"
Dariya farida ta saka "tabdi lallai sister,kai saidai na zo kawai" 
Katse wayar fadila tayi taba murmushi don tasan halin farida bata qi su kwana suna abu guda ba.........

*Mrs muhammad ce*👑


[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




*PART 3*




2⃣1⃣




Doctor sa'adah ta kammala rubuce rubucenta,ta dago ta kalli aliyyu "masu qaramin ciki kamar hakan suna buqatar daga qafa adinga sassauta mata gaskiya"
Zaro ido yayi kamar yaro"what?!,su waye Duke da ciki?"cikin mamaki ta sake dubanshi "oh,baka sani

Please Login or Register in order to submit comment