Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kasa kushesu yaran sun mata sosai,turare qal da su tamkar diyoyin turawa,qaramar tasu ce kawai mai dan duhu,sai gashi ta dauki kusan minti tàlàtiñ kafin ta baro bangaren

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tun ranar da aliyyu ya Baro bangaren nata bata Kuma ganinshi ba,Tun tana dan guntà hakan da yawan jama'ar dake wuni zirga zirgar barka a shashen nata hàr ta qaryata hakan,don ko kiranshi tayi baya Dagawa,a ranar ne Momi ta kira ta tana mata nasiha me yasa zata maida hannun kyauta baya,ta bata haquri ka ba zata sake bà



Qarfe takwas na dare baba talatu ta gama Gyara yaran tsaf cikin wasu irin hadaddun kayan bacci na jarirai turare qal duk iri daya sai qamshin turaren yaran su ke,itama shirye take cikin kwalliyarta wadda tafi zubi da amarya ba mai jego bà,ta goye qaramar a bayanta,sai ta rasa yadda zata sanar da baban



da qyar ta daure tace"baba Zani in Kai masa su"
"To.....to amma kada ki Dade,don dazun ma ya shigo da kansa ya gansu"yana shigowa kenan ya gansu idàñ bata kusà,ita dince bai nema yana nufi yayi fushi ne da ita



Sannu a hankali ta qarasa cikin Sa'a kuwa shi kadai ta taras cikin falon yana nutse cikin lausasan kujerunsa,falon lufluf yake sai qmshin freshner yake,sanye yake da jallabiyya blue black da tayi matuqar haska farar fatarsa,idanunsa saye da farin medicated glass dinsa



Ya dàgo fararen idanunsa yana amsa sallamar tata,sai ya Kasa zama ya miqe ya karbi biyun hannunta ,ta sauna tana niyyar kunto masa ta bayan,tuni itama Yan karbe abarsa ya jerasu reras



Ya cakuli wannan ya taba wancan tamkar mai wasa da màñyan mutane,ido kawai ta zuba musu tana Kallon tsantsar kamar da sukeyi,sai da ta gaji da shariyar tasa don tun gàisheshin da tayi ya amsa yayi mata dif
"ranka ya dade ina màgana"
"uhm......me kike fada?"ya tambaya ba tare da yà dubeta ba
"hankali ka nake so pls"
"Ai kunne ke ji ko?"ya sake fada bai dubetan ba,sai zuçiyàrtà ta raunaña,da sauri ta rungumeshi ta baya tasa masa kukan kissa



Sai ya tsaya cak yana ajiyar zuciya,bata sani bane amma yà fita shiga kewa,bai ita daurewa ba sai da ya rungumeta tsam a jikinsa yana lashe hawayen
"I missed you to much "yake fada cikin rudewa,tuni ta lura ya soma fita daga hayyacinsa,tsoro ya kamata tayi qoqarin zame jikinta,sai a lokacin suka ji kukan yarinyar,tare suka kai hannu don daukarta,aliyyu ne yayi nasarar daukartà ya soma lallashinta har tayi shiru



Cikin lokaci qanqani suka shirya Kansu dama ance *fadan masoya hutu*,dama aliyyu màzewa kawai yake
"Baby hassan din nayi nayi masa huduba d Muhammad, usainin Kuma Ahmad, qaramar tasu Kuma khadjà"tayi dariya tace"masu manyan suna ne ya kamata a basu nickname"
"As you wish my queen"
"To Muhammad Muslim, Ahmad aslam,khadijah Islam"tafi yasa mata
"Very good, that's my unique, komai naki mai kyau ne kin iya zabe,Muslim aslam Islam,Allah ya raya mana su"
Tayi fari d ido tace"ameen"



Kudi masu yawa ya bata yace ta riqe a hannuñta ,kada Kuma ta wahalar da kowa duk wani Abu naci ko na sha ko na rabo suna nan a shirye za'a kawoshi nasu yin amfàni da shi kawai,bata dà ikon cewa koma sai addu'a cikin zuçiya don godiyar ma ya hana




*Mrs Muhammad ce*👑



📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/28, 10:50 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*part 3*

3⃣8⃣



Mai karatu fadar irin shagalin sunan da aka sha bata baki ne,sai dai an ci ansha masu guzuri sun diba har suka suka bari,abunci indai na qasar Hausa ne babu Wanda ba saka samu ba,an rabar gidan kurkuku d na nakasassu d masu rangwamen gata,masu kinsan qwarya a ranar da yawa sun samu rabauta,don aliyyu bai yadda maza sun shiga musu cikin hidima ba,hatta da masu hoto video coverage mata ne



Atamfofi,set na food flask da na jug,jakankuna na mat ra purse masu axabar kyau,agoguna na hannu da na bango,gyalulluka coolers kai kayan dai gasu nan barkatai har yawa sukayi,ka dibi son ranka Kayi gaba,guri na musamman aka warewa *HUGUMA novels reade*,sunyi kyau a gun cikin shiga ta alfarma,kowa sai tambaya yake su waye wadannan?,aka karramasu,sun Kansu sai yau sukà sake kashe qwarqwatar idonsu suka San wace Fadila a gun aliyyu



Cikin ikon Allah taro ya water lafiya,salima na bangàranta zazzabi mai zai na bakin Ciki ya rufeta *huguma novels readers* sun so ganinta nace kada kuje Ku qarasa ta Ku zo mu tafi,



Jaridun washegari kuwa shafin farko hotunan yaran ne an rubuta da manyan baqi *'YAN UKU KYAUTAR ALLAH,DIYOYIN HAMSHAQIN DAN KASUWA ALIYYU SALIM MAI TAMA*

*** *** *** ***


_*RANA DUBU TA BARAWO*_…………


Misalin takwas ne na dare bayan ta gama shirin kwanciya,haka ta shirya yaran yadda ta saba cikin kayan baccinsu,kuwa ne t bashi nono ya qoshi,cikin lokaci anqani bacci yayi a won gaba da su,ta saka kuwa ne cikin gadonshi ta ka musu net din dake saman gadon



Kasancewar ranar ba ita ke da aliyyu ba yasa suka su na samun har baba talatu,ganin sunyi bacçi yasa ta jà musu qofar dakin ta shiga dakin baba talatu don suyi hira kafin lokacin baccinsu yayi



Sadaf Sadaf ta dinga takawa har ta nisa ga jerin dakunan baccin su,ta Kasa kunnenta sosai ba motsin kowa hakane ya tabbatar mata su na sama,cikin dakiya qarfin hàli da son cimma buri ta kama step din ta haye,kai tsaye ta nufi dakin yaran,ta tura qofar a hankali farinciki ya cikata ganin ta taki sa'a babu kowa cikin dakiñ



Jikinta na rawa ta qarasa bakin gadon ta Ciro muslim ,hannu tasa a wuyanshi ta kwatanta shaqeshi,sai kuma ta tuna zai iya tsala Kuma fa,ta jawo blanket din da aka lullubeshi ta wurgashi bayanta ta Goya shi,ta kifi daya gadon ta zari aslam ta sabashi a kafadar hagu,ta sake gaba ta dauki Islam cikin sassarfa ta fice daga dakin tana waige qirjinta na dukan uku uku har ta samu nasarar zagayawa can bayañ gidan inda tafkeken swimming pool dinsu yake



Dai dai lokacin fadilan ta fito zata komàwa dakin yaran ta dauko wayarta da ta mance kan gadon aslam,tayi mamakin gañin qofar dakin a bude,bata kawo komai a ranta ba sai tayi zaton aliyyu ne ya shiga,don wani lkcn idan ba ràñar girkinta bane kafin ya kwanta sai ya zo ya gansu ya daukesu daya bayan daya ya rungume Yadi da kissing nasu



Ba Aliyyu cikin dakin wayam Kuma babu aslam bisa gadoñshi,cikin sauri ta soma dune dube,wasa-gaske sai ta rasa Islam da Muslim,a gigice ta fito tana qwalawa baban kira,ta fito tana tambayarta lafiya,a rude take gaya mata
"Jeki gun babansu ko shi ya daukesu"
Duk d bata jin hakan don aliyyu baiso a dinga fitowa da su cikin sassarfa qirjinta na wani irin bugawa ta sauko qasan ta nufi sashen aliyu



Samira taga giftawar mace da goyo Zuwa bayan gidan nasu,tayi mamakin wace haka cikin dare,sannu a hankali take binta sai taga Muslim ne Ashe a goye a bayanta,da sauri ta tàko don ta cimmata,saidai kafin ta qaraso din ta daga aslam ta cillashi cikin swimming pool din,yaron ya canyara qara iya qarfinsa yayi qasa,abunda ya razana Samira Batasan lokacin da ta saki razananniyar qara ba cikin firgici



aliyyu dake zaune cikin balcony dinsa yana jiran samiran ta kawo masa file din da ya aiketa tà dauko masa file cikin mota qarar ta ratsa kunnuwansa,da sauri ya miqe ya nufi inda yake jiyo sautin,fadila da taza gurinsa taga wucewarsa ta rufa masa baya gabanta na ci gaba da biyu



Da sauri ta warce Islam da take qoqarin jefawa,cikin razana Salima ta juyo ta kalleta don batayi tsammanin akwai mahaluqin da ya ganta ba
"Ashe ke tsinanniya ce azzaluma,muguntar taki har ta kai da zaki iya kisa"ta fada cikin tsoro da firgici gami da mamakin taurin rai da Zuciya irin nata



Yana qarasowa idoñsa ya kai Kansu,wata iriyar mummunan faduwar gaba ce ta ziyarci Fadila ganin Muslim goye a gun salima,Islam a Hannu samira
"Yauwa don Allah kayi sauri ka shiga cikin ruwañnan ta jefa aslam ci........"
Kafin ta qarasa fadi tuni ya tsunduma ciki cikin wani irin nau'in tashin hankali,minti biyu kacal ya ciro yaron,



Suna tsaye cirko cirko Fadila na rungume da Muslim Hawaye ne kwance male male bisa kuncinta ,yayin da Islam ke a Hannu Samira,salima kuwa na tsaye tana bari kamar wadda aka sheqawa ruwan qanqara a tsakiyar hunturu,tuni fitsàri ya gama bata ta,Kallon da aliyyu yayi mata yasa a take wata gudawa mai dumi ta balle mata,zuciyarta ta nemi tarwatsewa saboda tsananin tsoro da razani





*Mrs Muhammad ce👑*



📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:51 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 3*


3⃣9⃣




Wani lafiyayyen mari ya sakar mata wanda yasa jinta da ganinta ya dauke na wucin gadi sai gata ta zube a qara warwas



Babu numfashi ko alamarsa a tattare da aslam,hankalinsu idan yayi dubu ya tashi,asibitin doctor sa'adah tana masa gyare gyare saboda haka suka wuce kai tsaye d shi *get-well women and children hospital* dake rijiyar zaki,asibiti ne mai kyau saboda haka suna Zuwa aka rufu.kan yaron,sun kasa zaune sun kasa tsaye,Zuciyar Fadila tayi rauni matuqa,qauna da tausayi irin ta da da mahaifi ta dinga taso mata,Hawaye ne kawai ke sintiri kan fuskarta ta kasa controlling din kanta,tana jin wanne irin laifi ta yiwa salima har haka da zata yi mata irin wannan hukuncin?,me ta state mata a duniya?,don kawai sun hada miji daya?,Samira ce mai dan bata baki



Aliyyu kam bai ma tantance a wanne halin yake ba,mintina talatin doctor ya fito,d sauri suka tunkareshi Tun kafin ya kai ga qarasowa
"Doctor ya ake ciki?"
Ya danyi Jim sannan yace"saidai Kuyi haquri,munyi iyà bakin qoqarimmu,amma Allah bai qaddara........"
"Doctor! Doctor!, numfashinsa ya dawo"cewar daya Daga cikin nurse din,da azama likitan ya juya ya koma cikin dakin,Kasa jurewa aliyyun yàyi ya riga masa baya



*Zakaran da Allah ya nufa da cara* cikin ikon Allah suka samu ya far fado numfashinsa ya daidaita,nan suka bashi gado dakin mutum daya,kafin lokàciñ tuni salima ta jima cikin cell



Duk Wanda ya zo dubiya sai yayi mamakin rashin imani irin na salimar,domin ana zaton wuta ne a maqera sai aka sameta a masaqa,tuni jikin samira yayi sanyi matuqa,Duk iskancinta abunda salimar tayi yayi Mutuwar dau4e mata kai,don a zahirin gaskiya ba zata iya koda kwatanta hakan ba



Lokacin da salima ke musanta abinda ta aikata aliyyu baice komai ba,na'urar c.c.t.v din ya dauko,inda take Adana bayanan ta ya shiga,tiryan tiryan har shigowarta cikin dakin ta bayyana har yunqurin shaqe muslim,wannan ya zama hujja mai qarfi a gurinsa,mataki mai tsauri ya dauka a kanta,inda yasa aka sakaye ta babu Wanda ya isa ma yàje ganinta,babu yanda iyayenta ba suyi da shi ba yasa a fito da ita ko kotu ne suje akan ajiyar da yasa aka yi mata amma yace ina bai da lokacinta,koda zaiyi shari a da ita a yanzu ma to sai yaronshi ya warke,don Tun ba yauba take yin yunqurin kisan kai tun Daga kan 'yarta iftihal



ya tabbatar ita tayi poisoning din fadilar a baya,ya sake gasgata hakan fada masa da Samira tayi ganin da ta yi mata a bakin window din fadilà,ya sake hada hujjarsa da irin firgicewar d yaga tayi lokacin da yake Sanar da haihuwar fadilan



Tun suna bashi umarni cikin gadara har suka dawo lallashi amma fir yaqi sauraronsu sai suka dinga biyowa ta gun Momi da suka fuskanci abun na yi ne,
"Babu ruwa na don bani na Haifa musu dan ba,haqqinsu ne ba na wa ba"haka ta sanar da su,suka yita Neman uncle abba da suka ga babu nasara ta bangaren Momi to shi bàya qasar ma ya tafi turkey duba company dinsa na yin carfet dake can



Duk wuni gu Wanda suka San za'asa aliyyu ya fidda salima sunje amma abun yaci tura *sawun giwa ya take na raqumi*,ba su da dukiyar da zasu kara da shi,bai bari an saketa ba sai da yasa tayi attachment na wata uku cikin gidan yari😂,zama ne na azaba da aiki mai tsanani,ta Fige ta palace kai Baka ce Salimar nan bace,nan ma cewa yayi shari'a zasu fara uncle abba yace ya barta hakan ma ko don 'yarsu iftihal,Kuma Allah ai ba azzalumin bawansa bane,zai musu sakàyyà walau a duniya ko a lahira



Cikin station din da aka dawo da ita ya barsu,yana shirin bude motarsa ta tareshi,yaja da bàya saboda wani shegen tsami da take bugawa,ta zube a gabansa tana ya yafe mata sharrin shaidañ ne"
"Ta riga ta wuce,idan ba hakan ba ai da baki isa ma ki tsaya haka a gabana ba,Kuma shaidan din dake zugaki kinga ai Abu yayi kyau kenan ko?,abinda zan baki shawara kada ki kuskura ki sake yin gaba da gaba da ni,idan takàdarki ce kuma already na danqawa d.p.o babu Kare bin damo"



Kafin ta sake ce wa wani Abu tuni ya shige motarsa ya bule mata idanu da qasa ya wuce abinsa,a take a nan ta sulàle ta fadi sumammiya ,bata tashi farkawa ba sai a gadonn asibiti,ta farka tana surutài da buge buge
"Ni aliyu zaiwa haka akan Fadila da tsinannun yaranta?,to wlh sai na dau fañsà"sai da aka zurkuda mata allurar bacci aka samu sa'ida

*** *** *** ***


Rayuwar gidan ta soma sauyawa,wata nutsuwa ce ta zowa samiran, son yaran take sosai,Tun Fadila na Dari Dari har ta sàkar mata jiki,cikin lokaci qanqàni tad fuskanci babu abinda ya cuci samirar illa tsantsar jahicin ilimiñ addini da shàidanun lqawaye dake zugata,amma baya ga haka bata da wata illa



Aliyyu kam ya daukewa Samira wuta matuqa da gaske,don yace itàma bai yarda dà ita ba,Mara baki ma ya aikata ina ga mai baki,kuka ta dinga yi masa tana rantsuwar wlh ko kaza ba zata iya kàshewa ba,har tausayi ta bawa fadila,ta dinga masa mita kan ya dainà yi mata haka,ita ta sashi ya siyowa samirar littattàfan addini ta samu lokaci tana karanta mata,tun daga kan su ahlari,qawa'idi,iziyya,arba'una hadith,umdatul ahkam,usulus-salasa dadi makamantañsu qananu wadanda za suyi mata sauqin fahimta


*_SHIN MENE MAKOMAR RAYUWAR SALIMA ANAN GABA?_*


*_SHIN YA RAYUWA ZÀTA KASANCE TSAKANIN SAMIRA DA ALIYYU?_*



*_RAYUWAR GIDAN ZATA DORE A HAKA_*


*_amsar sai 'yan mutan huguma,kuci gaba da haqurin bibiyarta mun kusa da yardar Allah_*



*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:52 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*part 3*


4⃣0⃣



Cikin ikon Allah ta soma fahimtar rayuwar da take abaya rayuwa ce mai cike da jagwalgwalo da qazanta,tabbas rashin ilimin addini ciwo ne da bashi da magani,makanta ce da ka iya yima mutum jagora Zuwa ga halaka,haka nan duk ilimin zamanin da ba'a hada nemansa da na adidni ba sunansa kwado ko Kuma ince jahilci,sannu sannu kuma zai iya kaika ga ramin da zaka gaza fitowa,ilimin dadi ni gaske ne da kullum yake zamowa dan jagora ga rayuwar bani adam

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Da aliyyu ya ga Fadila na Matsa masa kan Samira sai ya shirya musu tafiya su d yaran,da tayi magana sai yace honeymoon zasu da ya alqawarta mata kafin ta haihu,qasashe biya suka je,suka fara da saudiyya,Turkey, Egypt, Spain suka qarqare da u.k




Honeymoon kam an shashi babu qarya,jiki da Zuciya duka sun huta,watansu hudu a can alokacin su aslam na da wata biyar suka dawo,ba 'ya'yan ba hatta da iyayen sunyi bul bul fatarsu ganin sha'awa,aliyyu aslam da Muslim da suke farare sun sake haske tamkar ka taba su jini ya fito,Fadila kuwa da Islam fatarsu wuni lumi lumi ta sake yi,da wuni dan haske na hutu da jin dadi



Sosai yaran sukayi wayo,sun San ummin su sunsan abbansu,idan ka ga su sai ka rantse sun ninka watanninsu,bula bula da su,ga wuni she gen kyau da kwarjini da su ke dashi,hakan ya sanya su ke da farinjini,duk inda suka shiga kaga ana sha'awarsu da son daukarsu,maman ni su daya saka su ukun,babu ta inda suka baro aliyyu photo copy dinsa ne illa Islam da ta biyo fatar babarta,sun samu uwa gwanar iya tsàfta son qamshi da kwalliya,zanso mai karatu ka ga wannan family mai ban sha'awa

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Ranar da suka dawo da daddare bayan ta yiwa yaranta wanka itama tayi sun shirya su Kayi kwanciyarsu nan cikin dakinta kan gadonta,baba talatu Tun randa suka tafi tace itama zata gida,babu yadda Aliyyu baiyi ta zauna ba tace LA,LA,LA,



Ya turo qofa dakin ya shigo da sallama yana hararar fadila,ta ams masa tana Daga gira alamar mene ne?
"Kinbi kin kwashe min yara,kun barni ni kadai kamar wani màraya,ko tausayi na baki ji"
Ta danyi dariya cikin lanqwasa murya
"banda abunka gun matarka fa zaka,Meye na Neman yara,me za suyi maka,abinda tun dazun sukàyi baçci"
Harara ya manna Mata mai dauke da salon so,ya soma qoqarin haurowa kan gadon yana ce wa"bari ni na kawo kaina tunda ni baqin jini ne d ni ba'a nemana,bayan nima in buqatar a rungume nin,ba su Islam kadai ke so ba"



Zuba masa ido tayi bayan tayi kicin kicin da ranta,sarai ya lura da ita amma ya share ta don yasan tatsuñiyar tazo bata wuce ta qoqi,ya janye Islam dake kwance saman qirjinta ya ajjiyeta kusa da 'yan uwanta shi Kuma ya maye gurbinta
"Abbu(wani lokaci haka take kiransa,saboda haka tashi yaran sun fara gwarancin kiransa),me yasa kake son yana ka zama haka bayan da ba haka kake ba,yaushe rabon samira d kai,nifa tsawon wata hudu muna tare,me yasa kake son janyomin zargi da zagi n........."
Ya katseta ta hañyàr fadiñ
"Masu zagin naki suje su yita yi,tunda ba su isa suyi a gabanki ba kinga Kansu suke batawa lokaci"Daga haka ya hana ta furta komai

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Da safe shi da yaran na zaune a living room Duk sun karade gun kai kace wasu masu shekaru ne,dukkansu tsaf suke sai qamshi suke kamar yadda gidan nata ma baki daya yake kasancewarta wadda bata wasa da tsafta,cikin kitchen take tana hada musu breakfast don sun saba basu karyawa da wuri



Samira ce ta shigo da sallamarta,sanye take da atamfa dinkin riga da zañi,kanta lullube da mayafi,tsaf da ita duk da babu make up tàmkar ba ita ba,ta qaraso ciki aliyyu aliyyu na riqe da hannun aslam suña ta qyaqyata dariya yayi dama dama da yoghurt har fuskarshi



Kallo su take cike da sha'awarsu,ta karbe Hannu aslam Daga gunsa ganin ya rasa yadda zai da shi yaron akwai hanzari,gashi yana ta qwalawa Fadila kira tayi banza da su ya sani fushi take tun jiya,gyara masa jiki tayi tas,ta dawo tayi zaune cikinsu tana masa wasa yana bangala mata dariya



Ta dire kwanukan abincin bayan ta fito Daga kitchen din tana Kallon yadda suka bararraje su na biyewa yaran,sai taji ma kunyar samirañ ta kamata
"Lallai kam,sannunku kun samu aiki fa"
"Ina ruwa wuni,tunda mudai bamu ce ya zo ya taya mu ba"Tasan tsokana yake sonyi sai taqi Kallon Duk da nacin son ganin qwayar idonta d yake,ta maida kanta gun Samira su na Gaisawa,har ga Allah taji dadin ganin canji sosai gun samiran,don kafin tafiyarsu bata bari karatunta ya yanke ba,da kanta taje *Darul hadith* ta yanko mata foam bangaren kayan aure weekend kawai Tun Daga aji daya



A nan ta sauko musu da break din sukayi tare,samiran ta tayata suka gyara gurin har kitchen ta bita ta tayata suka wanke kayan suka dawo parlour din,tana lura da yadda aliyyu ke ta jifan fadilar da kalloñ qauna tana share shi,addu'a take cikin ranta Allah ya bata haihuwà ko ta samu kwatar son da aliyyu ke wa fadila(hmmmm,batasan abun Daga Allah bane)




*Mrs Muhammad ce👑*



📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:52 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*part 3*


4⃣1⃣



Ya miqe bayan ya kwantar da Islam da tayi bacci aslam da Muslim nata wasan su gun Samira
"Madam tazo a shirya ni ko, zan fita"ya fada Kansa tsaye yana wuce wa cikin bedroom sonta,share shi tayi taci gaba da hirarta da Samira don ta fuskanci so yake ya bata kunya,bata Ankara ba sai ji tayi anti sama da ita sai bedroom, zillo ta yi ta dira daga hannunsa



Cikin harara take ce wa"mene haka abban islam?"cikin gintse dariya yace
"Lallai yarinyarnan,ni zan kira ki ki wani jamin aji?,zaki San da Ali haidar kike"yayi guntà gaba daya,ba zata ita hana mishi farincikinsa ba don haka ta qyaleshi ya share budirinsa,bayan sun fito wanka Kuma ya tsareta yace babu inda zata sai ya gama shirya wa sa fito tare
"Amma fa mun bar su Muslim da mummynsu a falo ko?"
"Basa nan"kawai yace da ita yana ci gaba da shirinsa tayi zaune kuwa taqi taya shi sai kumbura take



Tana kallonshi yana kici kicin saka socks da takalmi,dariya ta so qwace mata amma ta maze, ta gama shagwabashi koma ita ke masà a yanzun bai iya koma ba,ya lura da ita d9n haka ya lakuto cream mai yawa ya yaba mata a kumatu,ta juyo tana sake hade rai kamar gaske
"Kin bata ni da yauwa,shirya ka ina ma yanzu gagara ta yake,ke Kuma kin zauna kina min dariya ko?"bata San lokacin da ta fas he kuwa da Dariya ba ganin yadda ya wani màrairaice mata,sai ta hau shirya shi kamar yadda ta saba



Da suka fito falon babu kowa,aliyyu ya leqa dakin yaran sai Islam kawai da ke ci gaba da baccinta nisa gadonta,da a lama su na gun samirar,har Mota ta raka shi kamar yadda ta saba,yace su shirya anjima idan ya dawo zaya kàisu su Gaida momi,ta ams masa na siru ya ja Motar suka fice,sai da ta leqa sashen samira ta tabbatar suna can tace"yauwa mommyn su aslam,tunda su na nan bari nake na fidda kayan tsarabar can"
Murmushi tayi "ba Matsala idan kin gama sai Kiyi kirana ,dama ina son ganinki,sirrin tsafta kwalliya da kula da miji nake so a bani"
Murmushin itama tayi mata"to shikenan ba Matsala"ta juya ta fice tausayin Samira na damunta tare da jin rashin dadin yadda aliyyun Yaqui sakewa da ita



Momi ta rasa inda zata sai jikokin da surukan nata,iftihal 'yammata Duk ta rude anga qanne sai ta dau wan can ta Ajjiye ta dau wannan,Daga momin har uncle abba sunyi mamakin sauyawar Samira,suka sake addu'ar Allah ya kade fitina yaci gaba da hada kansu,tsaraba sosai ta yiwa Momi da iftihal har da uncle abba,sai goma na dare suka tafi



ya ajjiye mata yaran ya fiya da niyyar bada umarnin a kulle gida,tuni kafin ya dawo ta kulle sashenta,Tun yana danna bell har ya dawo bugu tayi masa biris,wayarta dama a kashe take tilas ya haqura ya koma,da safe tana Kallon yarda yake aiko mata da saqon harara,ta share shi kawai tana dariya,don idan bata yi masa haka ba sai a shiga haqin samira,Daga qarshe sai da yasa yadda yayi ya biyota kitchen taci zalinta"gobe ma ki kuma"yace da ita



Wannan karon ziyarce ziyarce sukai har Maiduguri gurbin hajja gaña,farida ta so Zuwa saidài babu dama sanda tsohoñ cikin da take dau ke da shi,sai humairà ta bada aka tafi da ita,tayi Sa'a kuwa ya zo a daidai bikin diyar qanin abba,aka sha biki da ita,kuwa sha'awar Fadilan yàke,Duk inda ta gifta sai ta fita daban cikin mutane,wanda ma ya Dade bai ga Fadila ba yau ya gañta har da 'yan uku,don idan Baku manta ba farida dama na mata tsiyàr kafin rijiyà ce,ba Zuwa take sosai ba faridan ta fita zuwà




*Mrs Muhammad ce*👑



📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:54 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺
*_CONTINUATION_*4⃣1⃣


Da qyar ta cinye kwana biyar aliyyun ya azalzaleta ta dawo shikam ya gaji haka nan,gidan ya zama masa kango,haka suka dawo cike da farinciki don ta faranta wa danginta sosai su Kuma suka cikata da tsaraba



Rayuwa mai kyau da inganci mai cike da tsaftatacciyar Soyayya ce ta kewaye aliyyu d iyalinsa,tana ita bakin qoqarinta na ganin ya saki jiki sosai da samirar sai dai har yau bata kai ga cimma ga ci ba,Duk da ya rage wasu abubuwan

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Cikar Muslim aslam da Islam shekaru biyu samira ta hada musu gagarumin birthday party,ita kam fadilah nata kallo don tuni suka maida ta 'har Kallon,wannan Abu na daya Daga cikin abinda ya s aliyyun

Please Login or Register in order to submit comment