Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji na sake linkuwa cikin ranta,wannan shine karo na farko da suka taba body contact yana cikin saninsa,ta dinga tuna yanayin qamshi da laushin jikinsa,kamar yadda shi dinma yana zaune a falon ya kasa hasala komai ga ayyukansa nan a gabansa amma ya kasa koda sa password ya bude computer din bare akai ga batun yin aiki,tun barci ma fisgarta a hankali har mai nauyin ya saceta



A hankali ta soma ware idanunta saboda jinta da tayi tamkar tana rungume jikin mutum,qamshinsa ne ya bata amsar,a hankali zuciyarta ta tsananta bugu💓 sosai ta gwada yunqurin miqewa saidai ina ya zagayeta ne da hannayensa,ta tsammaci bacci yake ko magagin bacci ne ya sashi yin hakan saidai sanda ta sake yunqurin zare jikinta karo na biyu sai taji shi cikin soft voice can qasan maqoshinsa yace "relax,relax,am not going to do anything with you....just am feeling like am going to froze,I need to warmth my body ar you clear?" Bata ce komai ba ta maida kanta ta kwantar idanunta kan ribbon da hular sanyinta dake watse a gefe da alama shi ya zare mata su don kanshi ya tura cikin gashin yana saukar mata da dumin numfashinsa tsakiyar kanta



Ta lumshe idanunta sanda ya sake janta jikinsa sosai ya nutsa zara zaran yatsunsa tsakiyar gashin nata yana sake sheqar daddadan qamshin turaren gashi data ke fesawa kanta wanda ya cakude da na jikinta yana rarraba masa hankali,turarenda bai taba jinsa kan matansa ba,hucin numfashinsa da ta ji ya dawo sauka bisa dokin wuyanta shi ya sake rikita ta,cikin rawar murya tace "a....a....am" tsayawa yayi cak "is there any trouble?" "N....noo" bata san sanda bakinta ya fadi hakan ba,sake matseta yayi cikin faffadan qirjinsa a hankali dumin jikkunansu ya soma ratsasu,sanyin nan mai ratsa qashi ya ragu matuqa,a hankali takejin wani calmness da bata jin irinsa ba na shigarta,hakanan 2ani daddadan barci mai cike da nutsuwa ya saceta



Ya saki ajiyar xuciya jin saukar numafshinta alamun bacci ya dauketa,ya ciro daya hannunsa yana sake shafa gashin,sam ya kasa daurewa gashinta na burgeshi matuqa kasancewarsa mai son gashi,yaci gaba da shafa shi yana jin dadin santsinsa cikin tafin hannunsa har shima nasa daddadan baccin yayi gaba da shi cike da mafarkai kala kala

🔅🔅🔅🔅🔅

A hankali ta bude idanunta tadan juya bayanta ba kowa sai qarar saukar ruwa da taji cikin toilet,qarfe biyar na asuba,ta zubawa qofar toilet din ido lokacin da taji an bude ta,aliyyu ne ya fito sanye da rigar towel nan tasa mai budadden qirji,gashin qirjin san nan ya kwanta luf baqi sidik da shi,suka hada ido da shi kansa akwai moisture da alamu wanka yayi na ibada,ta lumshe ido hadi da cusa kanta cikin filo ganin yadda ya kamata dumu dumu tana qare masa kallo,shi kam kau da kansa yayi baiso ta kamashi da yin wanka ba ya dauki jallabiyarsa cumb da perfume nashi ya fice falo,sai da taji ya fice sannan ta zuro qafafunta ta sauko ta shiga toilet din don dauro alwala ta bada nata faralin

🔅🔅🔅🔅🔅

Kamar kowacce safiya tana kitchen tana hada masa break,tayi wankanta ta shirya kamar yadfa ta saba saidai yau ta gaji da sa kayan nasara din haka atamfa ta saka dinkin riga da skert da suka mata cif suka bi shape din jikinta,tana jin shigowarsa lokacin da take juya chips cikin frying pan,addu'a ta dinga yi Allah yasa wani abu yazo dauka yayi ya fice a kitchen din



Saidai addu'arta bata samu karbuwa ba don kai tsaye ya nufi ma'adanin plates ya dauki qwaya daya hadi da jawo plastic chair guda daya daga cikin biyun dake ajjiye a kitchen din ya dawo opposite dinta ya zauna,



Plate din hannun nasa ya hau miqa mata yana yamutsa fuska cikin shirin fita yake "pls help me kada yunwa ta yimin illa" sai yaso bata dariya yadda yake ta faman turo mata plate din idanunaa kamar zasu fada cikin frying pan din,tuni ta gama karantarsa akwai shi da ci ta amshi plate din ta cika masa shi da chips din sannna ta dora masa waina,dayar kujerar ta jawo gabansa tayi masa table da ita ta hada masa tea ta dauko masa ruwa da drink ta dora mishi gaba daya,ta gama hada tea din ta ajjiye masa ta miqe zata gudu don duk a atakure take jin ta don ta kasa hada ido da shi gaba daya ,rashin kunyarsa ma ita take gani kamar baiyi komai ba harkarsa ma yake free



"Thanks" taji ya ambata,cike da shakku da dimbin mamaki ta tsaya cak tana doubting anya su biyu ne kuwa cikin kitchen din nan,don bata gasgata cewa aliyyun ne ya fadi haka ba,don kawai ta hada masa break?,wace irin hidima ce mai tsauri wadda tafi wannan batayi masa ba bai taba yabawa ba ko a ido sai wannan?,sai ta yanke shawarar juyawa don ta tabbatar suka hada ido kuwa lokacin da yake kai chips bakinshi,sai ya tsaya ya fasa kaiwa bakin nasa tare da daga mata gira "yes thank you" da sauri ta juya zata fice don tana tsammanin aliyyu na karantar zuciyar mutum ne "come back,zaki broking rules dina,sai na gama kya fita"kanta a sunkuye ta dawo ta jingina jikin kantar kitchen din tana jira ya kammala

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Yadda wasu lamuran na aliyyi ke sauya salo ke bata mamaki idan yayi wani abun sai ta dinga tambayar kanta anya aliyyu ne?,shi kansa baisan ya canza ba ,sau tari sai ya tsinci kansa cikin sa'ido akan duk wani abu da ya shafeta duk wani movements nata,shi da kansa sai yayi wani abun sai ya koma yana tambayar kansa how comes?,sai kuma ya koma nazarin halaye da dabi'u nata shi kadai idan yana zaune perfect attitude nata,yakan daga kafada yace "perhaps she concern about me I think shine dalili na nima,true?"hakan zaita tambaya da baiwa kansa amsa



Sosai aliyyun yayi wani fresh yayi wata 'yar cika data qara masa kyau da kwarjini,ya gama zirga zirgarsa ya dawo gida ya tarar da lafiyayyen abinci da tsaftataccen muhalli kamar yadda yake so,ita din ma yanayin garin ya amsheta sosai don fatarta ta sake yin kyau da santsi ainihin chocolate clour mai kyau,


Tun daga ranar sai kwanciyarsu ta koma haka,koda tana wani aikin bata shiryawa kwanciya ba dole sai ta taho don yace mata umarnin likita ne ya dinga samun dumi sosai a jikinsa(lol aliyyu 😜😜),ita din ma bata damu sosai ba duk da yana sata a wani yanayi saboda tana samun dumi sosai wanda ke sata tayi bacci nutsatstse kuma mai tsawo ba kamar da da sanyin ke hanata wani baccin arziqi ba



_*ta faru ta qare*_











*to be continued*.......



*Mrs muhammad ce*😘






[10/16, 2:00 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*PART 2*

5⃣1⃣&5⃣2⃣

Qarfe bakwai na dare ya shigo gidan bayan kammala sallar magariba da kadan tuni ta kammala komai zaune take kawai tana duba saqonninta na email,kamar kowanne lokaci da sallama ya shigo hannunsa daya riqe da rigar saman kayanshi da briefcase dinsa daya hannun nasa kuma leda ce mai dauke da tambarin wani shago da suke sayar da kayan sawa na mata,ta dago idanunta don amsa sallamar qwayar idanunsu suka hadu,ita ta fara janye idanun nata don tasan idan bata janye din ba bazai fasa kallon nata ba, "wani kallo ya koya" haka fadilan ke fada ko yaushe cikin zuciyarta duk lokacin da yayi mata hakan,har wata rana bata sani ba zancan zuciyarta ya fito fili "see you tell me what you think,me zan kalla a jikinki?" Hakan ya fada still kuma yana ci gaba da kallon nata

Cikin falon ya qaraso ya zube kayan hannayen nasa saman kujera ya zauna hadi da fadin "ya Allah" sannu da zuwa tace hadi da miqewa don zuba masa ruwan sha kamar yadda ta sabar masa,baisan yadda akayi idanunsa suka bita da kallo ba,material ne ajikinta dinkin riga da skirt,sosai dinkin ya fiddo duk wani sharp na jikinta,yau babu rigar sanyin saboda yanayin sanyin da ya fara ja baya a qasar sai kawai ta kunna na'urar dumama gida ta yafa dan qaramin dankwalin a kanta,tana tsugunne gabansa ta cika cup din da lemo ta miqa masa 🍺

Maimakon ya amshi cup din sai ya hade hannayenta duka biyun da nashi hannayen,dumin tafin hannun nasa ya ratsa har ta qwaqwalwar ta,sosai yasa taji wani na yawo cikin dukkan sassan jikinta,ta miqe da alamun tafiya zatayi ko zai sakar maya hannun maimakon haka sai taji ya finciko hannunta ta fado jikinsa gaba daya tayi dirshan kan cinyarsa,suka saki cup din duka su biyun ya tarwatse saman tiles din yayi pieces

Sosai ya matseta tsakiyar faffadan qirjinsa yana cusa hancinsa lungu da saqo na jikinta yana sheqar ni'imtaccen qamshin dake fita ta jikin nata,yamutsa ta yake son ranshi sosai qamshin ke rikita shi,ya dora hancinsa bisa wuyanta hucin numfashin sa ya daketa tsigar jikinta ta tashi,a hankali numfashin nasa ke kaiwa da komowa,tuni ya soma birkita mata lissafi itama kamar yadda shi ya dade da fita daga nasa hayyacin,qirjinta ke bugawa kamar tayi tseren gudu,tuni jikinta ya mutu murus ta kasa wani motsi

Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzarinsa,duk da haka bai bata damar tashi ba ba tana jikinsa,yayi qoqarin daidaita nutsuwarsa sannan ya daga wayar "I will call you back" kawai yace ya katse kiran tare da jefata kujerar gefansa,yakalli fadilan da idanuwansa da suka canza launi kanta na sunjuye sai maqyarqyata take,sake matseta yayi a jikinsa yana ci gaba da cusa kansa jikinta kamar zai maidata cikin hancinsa,cikin kasalalliyar murya yace" da wanne perfume kike using?"karo na farko da tambayar ta silmiyo daga bakinsa ba tare da ya shirya ba, "am.....amw.....wan"jin gaba daya a gigice take yasa ya saketa, "shiryomin abinci zanyi wanka" a hankali ta zame daga cinyarsa cikin gudu gudu sauri sauri ta fada kitchen ya bita da kallo

Gaba daya jikinta rawa yake yana zaune shima a gun har ta soma debo kayan abincin yana lure da ita,ruwanshi yake sha yana bin ta da kallo,sai da ya kusa tashi da roba biyu,har barin miya tayi ta kuma taka ta santsin ya kusa dibarta kadan ya rage tasha qasa sai da ya dan riqeta hadi da cewa "take it easy"sai da ta gama jera abincin sannan ya miqe ya shiga wankan

Saman kujerar ta fada tana haki kamar wadda tayi tseren gudu,mirgina kanta kurum take,ta rasa wanne tunani zatayi daga cikin tuna nukan da suka cushe a qwaqwalwarta,me yake son canza aliyyun?ko kuma me ya canza shi din ma? Aliyyun da yace bai sonta?aliyyun da yace bazai taba qaunarta ba koda wani lokacine a anan gaba?me yasa yake son jikinta koda yaushe?bata da amsar kuma babu mai amsa matan

Sai da ya ritsata taci abincinta kamar yadda yake mata ko yaushe,ya jawo ledar da ya shigo da ita ya tura mata" I think jibi ne bikin bude company,ga kayan da zakiyi amfani da su nan" "thank you ta fada cikin sassanyar murya kanta a qasa don kallon da yake mata yana takurata matuqa

🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Da qyar yake iya jan numfashinsa saboda azabar da yakeji yana ciki,ji yake idan bai kasance da ita ba kamar zai iya mutuwa,shi kansa yaga matuqar qoqarinsa a yadda yana yin halittarsa yake,wata hudu babu wani abu yana cikin matsananciyar sha'awa?,yana cikin matsanciyar buqata mai tarin yawa,baisan sanda ya sanya hannunsa ba ya janyota a gigice ya matseta gam wanda hakan shi yayi sanadiyyar farkawarta,tayi tsam tana jin yadda yake nishi numfashinsa na kaiwa da kawowa da sauri da sauri tamkar yana shirin kufce masa,bata kawo komai ba cikin ranta illa tunanin ko ciwon cikin sa ne ya tashi?

A gigice ya birkitota sukayi face to face,lullubeta yayi cikin ingarman qirjinsa,saqonni ya soma aika mata masu zafi da tafiyar da hankali wanda shi kansa ya manta da wasu sai a alokacin,tuni saqonninshi suka girmi hankalin fadila,ganin yana neman wuce gona da iri ta soma yunqurin qwatar kanta cikin kasala saidai sam ko motsawa ta gaza yi ya aza mata nauyinsa,loko sa saqo ya dinga bi yana lashewa hadi da rabata da duk wani abu da zai raba tsakaninsa da fatar jikinta

Tamkar a mafarki take gani,sosai taga lamarin na aliyyu da gaske yake gaba daya kamar baya duniyar ya gama fita daga ainihin aliyyun ya burkice mata baya ji hakanan baya gani,tabbas yana so ya mata abinda ta dade tana tsoro da fargabarsa,ganin dan qarfinta bazai amfana mata komai ba sai ta koma magiya da roqonsa yayi haquri,tamakar da dutse take magana ko wani kurman bebe,tuni ya gama rabata da komai na jikinta sai 'yar mitsitsiyar vest da ta rage ajikinta wanda ita kadai dama ta sanya don bata kwanciya da brassiere sai tasa vest mai dame jiki, "pleeeeaaaaseeee aliyyu zaka jimin ciwo,pleeaasee kayi haquri don Allah" hannu tasa tana rufe qirjinta saboda babu wani abu da vest din ta kare na surar qirjinta,dukiyar fulaninta ta cicciko cikin vest din sunyo

Da hannunsa daya yasa ta riqe hannayen nata biyu yasa daya hannun ya tsarge vest din gida biyu ya zareta ya wurgar,tuni dukiyar fulanin ta bayyana,wani iriyar gigicewa yayi laushi da santsin fatarta ya kusa zautar da shi,bai taba karo da qirar da ta taba tafiya da imaninsa ba irin ta fadilan tuni ya sake haukacewa kamar mayunwacin zaki,kamar akuyar da ta shiga garken tumaki,magiya da roqon taga sunqi tasiri gaba daya akan aliyyu sai ga barke da kuka,a hankali ya dinga lashe duk wani hawaye da ya biyo kuncinta bai bari ko guda ya diga a aqasa ba,sannu a hankali ya dinga kashe mata duk wata gaba ta jikinta da wani irin salon soyayya da bai taba gwadashi kan wata diya mace ba,komai nata ya saki ya zare mata duk wata ragowar qarfi da kuzari da ya rage mata

Sai da ya soma aiki tuquru sanan ta soma gane kurenta,ihun kuka ta soma saki a maimakon hawaye zallah,kuka take mai hade da ihun,hawaye da majina kuwa tuni suka hada kogo bisa fuskarta,cizo da yakushi kuwa har sai da ta gaji don kanta,tuni yayi nisa cikin duniyar da bai taba koda giftawa ta kusa da ita ba,ya shiga wata duniya mai wuyar fassarawa a gareshi,tuni sukayi hannun riga da wani abu da ake kira hankali,tun fadila na fahimtar halin da take ciki har ta soma gane komai a hankali idanunta suka rufe duhu ya mamaye mata idanu,dif komai ya dauke mata ba tare da aliyyu ya sani ba

Gefe ya koma ya yashe tare da matseta gam cikin jikinsa ji yake kamar ya tsaga qirjinsa ya maidata ciki,sosai ya rushe da wani irin kuka tamakar qaramin yaro,karo na farko sa hawaye ya zuba a idanun Aliyyu haidar ta silar fadila tun bayan da ya mallaki hankalin kansa,tuni hawaye sukayi male male bisa fuskarsa fadi yake a zuciyarsa har ma a fili "alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus saalihat (godiya ta tabbata ga ubangiji wanda da ni'imarsa ne abubuwa masu kyau suke cika)ashe har yanzu akwai mata masu kai budurcinsu gidan mazajensu?ashe zai samu wannan abun mai daraja?ashe dama babbar kyauta Allah yayi masa?ashe baiwa ce babba a cikin gidansa bai sani ba?ashe gata abbansa yayi masa?ashe soyayya abban nasa ke masa ta gaskiya?....ashe din ta aliyyu a lokacin mai dama ce,nadamarsa mai tarin yawa ce,kuka yake sosai da hawaye masu tarin yawa kwance bisa fuskarsa

Wani abu mai girma yaji yana ratsa shi game da ita wanda tunda yake bai taba jin makamancin hakan ba,ya dago da fuskarta yana kallonta,wani tausayi so da qauna girmamawa da kunyarta suka rufeshi masu tsananin tasiri,ga shatin hawaye nan bisa fuskarta da suka bushe sukayi alama,sai a lokacin yaji baijin sukar numfashinta,yatsunsa ya sanya saman hancinta yaji dif babu alamun fitar numfashi,a gigice ya zareta daga jikinsa ya wuntsulo daga kan gadon da gudu yayi parlour,freezer ya bude ya dauko ruwa,jikinsa na rawa ya balle murfin ruwan ya kwarara mata kan fuskarta,wani dogon numfashi ta ja hadi da saukar da ajiyar zuciya mai nauyin gaske,muryarta can qasa qasa yadda bi jiyota sai da ya zauna tsakiyar gadon ya dagota ya mannata da jikinsa yaji tana fadin "please kayi haquri kada ka qara" qwaqumeta yayi ya dora habarsa tsakiyar kanta "relax am not going to repeat it" jikinsa shi kansa rawa yake har yanzu,ajiyar zuciyar yake saki shima a kai a kai tamkar marayam da ya ci kuka ya qoshi,kana kallonsu a lokacin dukkansu sai sun baka tausayi dukkansu sun koma kalar tausayi

Azabar da fadilan keji ya sanyata sakin wani sabon kukan mai ban tausayi,radadi sosai take ji kamar ana yankarta a gun,sake rufe ta yayi ruf da qijinsa yana cewa cikin rawar murya da ta jiki "am sorry fadila am sorry please"

Duk da tana jin jiki kalaman sun bata mamaki,aliyyu?,aliyyu ne?"a hankali yake dauke hawayen nata da harshensa yana shanayesu gami da shafa kanta zuwa bayanta alamun lallashi yana fadin "am sorry...am sorry"abunda bakinsa kawai ke iya nanatawa kenan kamar karatun sallah,sunfi minti arba'in a haka dukkansu suna sakin ajiyar zuciya,ita bacci ya fara dauka don shi kam ko alamaunsa bai ji,a hankali ya zamar da ita ,ido ya zaro ganin yadda jini yayi face face kan farin bedsheet din,tausayinta ya sake kamashi,shi kansa yasan bai mata kadan ba,ya riga ne ya fita daga hayyacinsa,hannu yasa ya yaye shi gefe ya kwantar da ita a ahankali don kada ya tasheta yaja mata bargo ya lullubeta,yasa hannunsa ya kama mata gashinta da ya yamutse gaba daya ya daure mata shi guri guda,fuskarta da tayi fayau ta bayyana a dan hasken fitilar gefan gadon

Zaman dirshan yayi yana gadinta duk wani motsi nata na kan idonsa,ranar duk qwarewar bacci kan iya sata haka ya haqura yabar aliyyu,har asuba yana zaune dirshan idanunsa na kanta tana wani wahalallen bacci

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻
[10/16, 2:03 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*PART 2*

5⃣3⃣&5⃣4⃣

Jinta kawai ruwan zafi na ratsata,a gigice ta farka saboda azabar zafi,a rude ta qwalla wata gigitacciyar qara duk da muryarta a da she take,ta riqe hannunshi sosai tana sheshsheqar kuka "calm down please,u wil get fine,pain din da kike ji zai ragu" ya fadi cikin taushin murya da kwantar da kai,ba yadda ta iya haka ta maida jikinta tayi laqwas tana jin yadda zafin ruwan ke ratsata har gun ciwonta,a hankali ta dinga jin zafin na dan raguwa sai a lokacinne kuma ta fara lura ashe haka aliyyun ya sunkutota babu komai a jikinta,hannu tasa tana kakkare qirjinta

Shi din ma tun dazun yake qarewa halittarta kallo tana ci gaba da attract nashi ji yake kamar ya maidata ruwa amma raunin da yayi mata shi kansa ya san yayi barna,hankalinsa ya bar jikinsa ne however ma baiyi zaton zai sameta da virginity dinta ba,sai da yayi matuqar kai zuciyarsa nesa kan fadilan saboda yadda surarta ke fusgar hankalinsa,ba halitta ce da zaka iya kalla sau daya ka kau da kanka ba,wanka yayi mata ya nadota a towel kamar wata baby ya maidota daki,kunya babu kalar da fadila bata jita ba yau,shi yasa mata pant har da brassiere tana ta ture hannunsa kan ya qyaleta zata sa saidai yace "am sorry ki barni kawai,ba zaki iya komai ba" ta rasa wacce iriyar rashin kunya ce da aliyyun,doguwar riga ya zira mata harda hijabi ya shimfida mata dadduma sai da yaga ta hau sallayar sannan ya shiga nasa wankan

A kwance ya dawo ya taddata kwance saman abun sallar,komawa taga yayi ya ciro wasu capsule ya zaunar da ita ta sha sannan ya tayar da sallah,tuni bacci ya sake dibarta kafin ya idar nan kan abun sallar ko azkar din ma bata samu tayi ba,cak ya dauketa a hankali don kada ya yada ta kan gadon ya maidata ya zare mata hijabin sannan ya ja lallausan bargon ya rufeta zuwa wuyanta,zaman dirshan yayi kusa da ita yana kallonta tamkar an bashi assignment a kanta,wani abu ke ci gaba da ratsa zuciyarsa,sosai baya ga qauna yake jin qimarta da darajarta na sake linkuwa cikin zuciyarsa,tunaninsa mai zaya mata a duniya tukuici zuwa ga tarin kyautatawarsa gareta?,me zaya mata wanda zai saka mata kan wannan baiwa tata yau da ta masa kyautarta dungurun gum,kyautar da bai taba katari da makamanciyarta ba?,dame zai faranta ranta da shi a fadin duniya?,she deserve anything

Qarfe takwas na safiya a gogon garin har lokacin baccinta take gashi fitar dole ta kamashi saboda yau baqinsa zasu soma isowa,dole shi zai kama masu hotel da zasu zauna andi kuma aikin da ya basu yayi yawa bare ya hada masu da wannan,ga mukhtar (abokinsa ne na kusa)bai qaraso qasar ba bare ya hada shi da aikin,don haka fiya ta kamashi dole,idan banda wannan dalilin kam baijin akwai abinda zai fidda shi daga gidan yau,ya gama shiryawa tsaf cikin suit kamar yadda ya saba sai da ya shiga kitchen ya hada mata tea ya zuba cikin flask ya soya mata chips da qwai ya hada da cups yayi dakin don kada ta tashi babu abinda taci,ya qaraso bakin gadon bayan ya ajjiye tray din kan 'yar locker din nan ta bedside yana sake kallonta,baccin take kawai ko motsawa batayi,shi kansa yasan dole ne kam tayi bacci,ya zira hannunsa a hankali ya sake maida mata gashinta gefe,karon farko cikin nutsuwarsa ya sanya tattausan lebensa ya sumbaci goshinta sannan ya maida leben nasa saman nata leben masu taushi da siranta,ya dan jima yana sheqar hucin numfashinta dake shiga hancinsa yana masa dadi yana jin kamar tana qara masa wata ruyuwar ne ta musamman

Hot kiss ya bata wanda sai da yasa tadan motsa kadan ya miqe yana sake kallonta tare da hade tafin hannunshi da nata,baya son fitar ko kadan,ya sani tana da buqatar kulawa,sai da ya qoshi da kallon nata sannan can qasan maqoshinsa yace"i will back soon" tamkar yana magana da wadda ke idanunta biyu,ya fice a dakin yana waiwayenta hadi da ja mata qofofin gidan

Cikin ayyuka yake da mutane saidai duk wani motsi da zaiyi qwaya daya tana manne cikin zuciyarsa,kaf hankalinsa na gida gangar jikinsa ce kawai a nan,har wasu abubuwan mancewa yake maimakon ya fadi sunansu sai yace "fadilah",sai kuma yace musu "am sorry I mean kaza.....",Allah Allah yake ya kammala abinda zaiyi ya koma gida saidai yana murna ya kammala sai kuma wannan ya bullo dole haka yake sake zama yayi settling

Da kanta taji ta qoshi da baccin ta farka bakinta dauke da addu'ar tashi daga bacci *"Alhamdulillahil lazi aa faani fi jasady waradda alaiyya ruhi wa'a zina li bizikrihi"*,tayi niyyar miqewa kamar yadda ta saba saidai jin yanayin jikinta da ya canza shi ya tuno mata abinda ya faru da ita jiya tsakaninta da aliyyu

Daki daki komai ke dawo mata,tana tuno moment din tar cikin kwayarta *"wanne turare kike amfani da shi?"* tambaya daya da ya maimaita mata ita sau biyu kenan a jiya,sannu a hankali tunaninta game da turaren ya soma dawo mata *"hasbunallahu wa ni'imal wakeel"* ta fadi cikin zaro ido da matsananciyar faduwar gaba,da sauri ta diro a gadon tuni ta mance wani ciwo da take,kai tsaye gun jakarta ta nufa inda taje rataye,tasa hannu ta cirota cikin rawar jiki ta soma laluben turaren ta ciroshi hadi da zuba masa ido tamkar yau ta saba ganinsa

Da sauri ta daga jakar ta zazzage ta kafataninta,dukkayan ciki suka zubo,tarkacen magunguna da suka siya ne gun fa'iza,wannan turaren da nake shafawa shine?shine wannan turaren mahadin magungunan?" Jakar ta saki qasa hadi da komawa baya ta zauna kata ta dafe hadi da sakin wani irin kuka mai cin rai, _*"saboda sha'awa aliyyu ya tara da ita ba don so ba?turare shi ya ja hankalinsa kanta ba qauna ba?me yasa nayi gaggawar baiwa aliyyu kaina ne?me yasa na amince na yaudari kaina? Tabbas aliyyu bai sona kuma ta yarda bazai taba sonta din ba"*_,jikinta ne ya burgeshi ko me? Ta ci gaba da fada cikin zuciyarta,tuni ta gama sarewa,ta gama yankewa kanta qauna da zama tare da shi,babu irin abunda bata gwada ba amma babu nasara to sai yaushe?sai yaushe nasarar zata zo mata ne? Da gaske kenan hasashen anty hafiza na zai soki fadila wataran son da bai taba tsammani anawa wata diya mace irinshi ba,ai babu *wanda yasan gobe sai Allah* ya zama mafarki........?,tana jin wannan karon ya zama dole ta zare aliyyu daga cikin tsarin rayuwarta,ya zama dole ta rabu da shi haka nan ya zama dole ta nisanceshi,ta gama yin duk abinda ya kamata tayi.....ta gama duk abinda zata iya....ta gama bashi kuma duk wani abu da take da shi,kulawa.....tattali....tausayi da soyayya......kai harma da jikinta da zuciyarta gaba daya amma aliyyun ya gaza samuwa,to me yayi saura?,bata da wani ragowar abun bashi banda ta bar masa sararin rayuwarsa itama

Please Login or Register in order to submit comment