Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sake dan saukowa d samirar,don su Kansu yaran sunyi Matuqar sabo da ita

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Suna gadon baccin su bayan sun gama komai na shirin kwanciya,duka yaran na gun samira don yawancin lokuta idan ranar Fadila ce to ita ke kwashesu tace zasu tayata kwana



Envelope aliyyu ya miqa mata bayan ya hade girar sama da ta qasa,ga bata ya fadi tabi envelope din da kallo,cikin sarqewar Murya tace"n......na meye.....wannan?"cikin tsawa yace "bude mana ki gani"cikin rawar jiki ta sure ta ta farke,dan qaramin ihu ta saki,ta Daki tsalle ta daneshi,Duk ta rude,shikam dariya yake ta mata har da qwalla wait da har idan guntà sun fito waje sunyi hudun na su Muslim,Sam bata bai ta kan tsiyar da yake mata ba,foam ne na jami'ar Bayero university degree na biyu zata yi kan mass comm



Ya dubeta bayan ta natsu"ki dai na yimin godiya my life,har yau inajin ban saka miki irin tarin alkhairi da haqurinki gareni ba"haka an aliyyu yake mutum ne mai rama alkhairi komai qanqantarsa,cikin nasara karsashi qarfin gwiwa da nishadi ta soma karatunta
,bata da matsalar koma,yaran samira ke kula mata da su,idan lecture ta fado a weekend itama samira na da Darul hadith sai su taba ita ta dau biyu ta bata daya,ganin haka ma sai Aliyyu ya niqi gari da kansa ya tafi gombe ta tattago baba talatu da taqi dawowa,d year ta amince ta biyoshi,don tace bata son zama tsakiyar rayuwar auren yara



Ganin haka yasa cikin gidan Daga can baya aka zuba fasalin irin ganin gidajammu na ga gajiya mai tsakar gida da dakuna aka yi mata nata gidan Duk da ce wa akwai part din da salima ta bari da Kuma wani spare daban amma tace bata sonsu sun mata zamani da yawa,dariya Fadila da samira suka dinga mata tace eh ta ji

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Cike da nasara Fadila ta kammala karatunta,ta fito da kyakkyawan sakamako cikin makarantar,hutun sati daya kawai tayi aliyyu ya baro musu tafiya China,bata ga passport din samira ba a ciki dama tuni baba tace ba zata ba ita kam indai ba Garin ma'aiki ba,da ta matsa masa da tambayar na samiran ko ba'a buga mata visa bane,sai yace ai ba wuni dadewa za suyi ba,ka ita zaiyi ta diba kamfaninta na can da ya bata,sai wuni daban da zai bude a kwana daya



Tubure masa tayi har ganin samiran,murmushi tayi babu damuwa a tartare da ita"Kuyi tafiyarku abba Islam rabu da ita,ranar da zaki tafin ma Samu fara jarrabawa,kinsan Samu shiga s.s one mun zama seniors ba raini"



Sai ta bawa fadilan dariya,har yanzu fadar magana kai tsaye da calikancin samira na nan tare da ita,sai dai wannan karon yana tafe ne da burbushin ilimi


*_INA SALIMA NE?....._*


Ku biyo ni masu karatu............


*Mrs Muhammad ce👑*



📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 3*

4⃣2⃣

*ina salima?*



Qunci da baqinciki babu Kalar Wanda bata ji ba shi cikin zuciyarta,na farko rabuwa da abinda tafi so Duk duniya wato aliyyu,na biyu Kuma rashin cimma burinta na raba fadila da 'ya'yanta daga sheqar iskar duniya,gash a yanzu babu wata kafa da zata sadata da cikar muradin nata



"Akwai mana"shedaniyar zuciyarta ta gaya mata
"Kiyi auren kinsan wuta kawai sai ki koma gidan ko ta gajiyar asiri ne ya maida ki ko bai cikin hayyacinsa"
Tashin farko ta nemi auwal tsohon saurayinta sukayi yarjejeniyar auren wata guda kacal,da sharadin ba zai kusanceta ba(kaji wata kwamacala)



Ba tare da ta gama idda ba aka daura mata aure,tun daren da aka kaita ta soma gane kurent,kwana auwal yayi yana Abu daya,Duk bakin tsiwa da rashin kunya ya mutu murus,haka nan tana ji tana gaji ya gama budurinsa,dama auwal ya dade yana sha'awarta,taqi bashi hadin kai ne Tun farko saboda tana ganin ta zarta ajinsa,sai kyau ya samu cimma muradinsa



Wata daya na cika ta same shi da zumudinta ta tunasar da shi lokacin rabuwarsu fa ya cika,wata mahaukaciyar dariya ya bushes da ita sannan yace
"Amma bansan ke daqiqiya bace sai yau,in banda ke mahaukaciya ce kina tunanin zan sake ki ne?,to ki sani Kinyi kuskure,auremmu kuwa mutu ka taba takalmin kaza"



Miqewa tayi a fusace tace"tabdi,lallai auwal ka ga dama ta,to wlh bari kaji,ko Baka qaunar Allah sai na bar gidanka,ai Kaine babban mahaukaci,banda haka ai ko makaho ya Shafa ni ya shafaka yasan nafi qarfinka wlh,ni ba'a halicceni don nayi zàman aure da kowa ba sai aliyyu jar......."
Gif!,tashi a bakinta,kafin ta qarasa tuni auwal ya dunqule Hannu ya Daki bakin,tuni gurin ya haye ya suntume jini yace salami alaikum,bata gama tantance barnar da yayi mata ya bita ya turmushe ta da duka tamkar wanda ya samu qato dan uwansa



Tun tana qoqarin ramawa har ta dawo sai zagi,qarshe bakin ma ya mutu,sai da ya gaji don kansa sannan ya qyaleta,ya dago yana haki
"Shegiya qaramar 'yar iska,ke har kin isa ki bude kice na sakeki ki koma gidan wancan dan iskan da na sha wuya a hannunsa saboda ke,to gobe ma idan kin cika 'yar iska ki Kuma yimin makamanciyar wannan maganar,ke da fita daga gidan nan sai dai a fidda gawarki"ya tsallaketa ya fice abinsa



Sai da taci kukanta ta qoshi sannan ta ja jikinta sannan ta hada kayanta a trolley tayo waje,sai da tazo har soro saidai abun mamaki tayi tayi ta fita ta Kasa kamar wadda aka daure da Sarqa,a ranar dai tayi yunqurin fita ya kai sau ashirin amma da zata ta zo soro sai tashi kamar an riqeta,qarshe ta fas he da kukan baqinciki ta zube a soron tana hango wajen amma ta kasa fita,



Anan ya dawo ya tarar da ita,dariya ya fashe da ita"yarinya kin makara,ai ba zaki ita fita ko ina ba ba tare da izini na ba,hakanan babu Wanda zaki ita ga yauwa halin da kike ciki,wuce don uwarki ki bani abin ci na,idan Kuma ba Kiyi ba ki dafa min yanzu yanzu ko ki ci ubanki wlh"



Cikin wata biyu ba izayar da salima bata gani ba,gashi ko Karen gidan su Yaqi Zuwa,bata sani ba auwal ne yasa aka kadar da hankalinsu,ko tunaninta basu yi



A hankali cimar gidan ta canza sai qarma qarma kawai,auwal a qarqashin wini alhaji sabo Alfa dake cikin kasuwàr kantin kwari yake,ya dade yana cutarsa ta hanyar sace masa manyan kudade yasa an rufe masa ido bai gane ba,auwal bin malaman tsubbu gunsa ko mace ta shafa masa lafiya,da kudadeñ yake burga cikin Garin tamkar ubansa wani ne,daga baya da Allah ya yake alh sabo ya gane ya koreshi kudin Kuma da ya sata din da yake ba ta hanyar halal aka samesu ba maimakon ya tattala sai yaci gaba da harkar banza da holewarsa da su har suka soma qarewa



Allah qadiran Ala may yasha'u,cikin hikima ta Allah sai ga cikin auwal jikin salliman,sai Allah ya dora mata son cikin,tana son ganin gudan jiñiñta a yanzu tunda ta fuskanci rayuwar na dab da juya mata baya,sai dai inaaa.....ba'a yiwa Allah wayo,domin a baya taqi cikin a lokacin da uban dan keson abinsa,to a wannan karoñ Kuma sai ta so cikin a lokacin da uban cikin bai buqatarsa



Har gida auwal ya dauko wani inyamuriñ likita har da kayan aikinsa,ya danne masa salima yayi mata allurar kashe baki,tana ji tana gani aka zurmuqa mata qarfe aka zuqe cikin,kai qarshe ma yasa aka gutsire mata mahaifar ma dungurun gun,a cewarsa bai da buqatar wata haihuwa,ta rasa lokacin da zata fara haihuwa sai lokacin da ya fara fama da kansa.......




*Mrs Muhammad ce👑*



📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*_continuation_*4⃣2⃣


Saura qiris salima ta bar duniya amma da yake akwai sauran shan ruwanta a gaba sai ta warke,tayi kuka tayi nadama da Dana sani maras iyaka,taso kashe Fadila da 'ya'yanta sai gashi ita tana eaten amma tayi Mutuwar tsaye,taqi ta Kuma wulaqanta kyautar da Allah yayi mata lokacin da ya bata cikin iftihal,aliyyu ya biya da lallashi sai ganshi yanzu da uwarta da ubanta aka bai aka zage sannan aka qwaqule cikin ,maimakon ma ya dauki iya ajiyarsa sai da ya hada da ajiyar Allah yasa aka guntile mata mahaifa



"Ashe dama haka rayuwa take?,Ashe Wanda yaqi zaman gidan aurensa ya rains matsayin da yake kai ya butulcewa ni'imar Allah yaqi daukar ixina ta ruwan sanyi duniya zata biyar da shi?



A yanzu take sake qaunar gudan jinin nata qwaya daya tilo iftihal,Ashe ita ka dai ce qwanta a duniya?,ta yima aliyyu addu'a sosai da ya tsaya tsayin dauka ya hanata yasar da cikin iftihal din,da tuni ta tashi a tutar babu kenan?,qaunar 'yar take sosai sai dai ta sani babu qaunarta ko daya a Zuciyar yarinyar Wanda ita ce sula ita ta haifar da hakan,wannan shi dake kira da Dana sani qeya ce

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Wannan ce rana ta qarshe Kuma company na qarshe da aliyyun zai qarasa bude wa ,dukkanin yaran nata uku sanye suke cikin sutura iri daya sai dai su maxan na maza ne Islam Kuma na mata ne haka aliyyu ke sawa ana musu,tuni Muslim da aslam suka saje cikin fararen fata su da abbunsu,Fadila kuwa shigar babarbariyar usuli tayi (kanuri)cikin lafiyayyar laffaya maroon tayi mata kyau matuqa,sosai ta burge mutanen sin har wata Daga cikinsu mr.shengping ta Kasa shiru har sai da ta yaba family din na su



Ahankali bai sake yiwa kanta ba sai da aliyyu ya anshi microphone
"A kyau ina farinciki gabatar muku da mata ta,farincikin rayuwata,zuciya ta jinin jini na,Fadeelah aliyyu Salim"
Tafi suka sa kowa so yake yaga fadilar nan da wancan karon ta ruda Mr aliyyu,dai dai da dai dai take ba wa Matan hannu suna musabaha maza Kuma su na gaisawa ne kawai ta wuce,kallonta aliyyu yake kawai ganin yadda take sarrafa harshenta tamkar haifaffiyar qasashen turawa,bata fiya yiwa yaranta magana da harshen nasara ba don suna yi a maka ranta,tafi yi musu larabci ko barbanci,shi Kuma ya musu fulatanci don su tashi da ainihin yaransu na uwa da uba



An tashi taro lafiya baya ga kyaututtuka da suka samu masu tarin yawa Daga abokan kasuwancin aliyyu,direct gidan mukhtar (abokinsa)suka wuce,a can suka ci gaboncin dare,Fadila na tare da matarsa Aisha suna hirarsu abinsu,Islam tayi bacci ita da Muslim,aslam Kuma na gun abbansa a parlour su na lissafe lissafe kan company din Fadila da irin ribar da aka samu



riba ce mai tarin yawa,da Kansas mukhtar ya shiga ya kirasu fadilan,sun soma mata baya nin irin ribar da aka samu,Tun tana dauka har kanta ya gaza dauka,sai ta sai kuka irin kudaden da dake ambato mata sunfi qarfin kanta,ace kamarta ba 'yar wani ba ta mallaki irin wadannan kudaden a matsayin riba.......



*Mrs Muhammad ce👑*



📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 3*

4⃣4⃣



Ya duba littattafansu na makaranta dayake wuni lkc shike dubawar,ya taimaka musu sukayi assignment, da suka bude na Arabic don son ya tsokaneta sai yace"kai kai 'yan uku wannan yafi qarfina,wannan ai sai balarabiyar mamarku,Ku kai mata maza"
Suka kwashi littattafan sai aslam ya noqe jikin abba nasa don tsoron zuwan yake ji,



Ta kalle su ta dan zare musu idanu
"Yalla Ku tafi gun abbu ya qarasa muku,Nima ban iya ba"suka juya gunsa din kuwa,yadda ta musun sai ya sosa ransa,sai da suka gama ya musu brush ya suya musu kayan bacci ya raka aslam gun samira sannan ya dawo
Tsaye yayi a kanta hannayensa harde saman qirjinsa"me kike nufi da abinda kika yiwa yaran nan?"



Ta dubeshi,sai ta Dakota da shan fruit salad dinta
"Me kuwa nayi musu?"
Sai yaga ta ma raina masa wayo,cikin hasala Zuciya ta tunzura shi yace
"Kinga malama,idan Kema baki sonsu ki fito ki gaya min,ina da inda zan kaisu dama ni na saba ganin hakan,ba kanki farau ba"
Za can ya qona mata rai,cikin gatse tace"shikenan,ka kaisun inda kake so din"taci gaba da shan fruit salad dinta



To Ashe bata sani ba ta tada masa tsohon miki,don haka ransa ya dugunzuma,ya ranqwafo wait in fuskarta"oho......alright, to wa ya sani ma ko ke kika hana kanji sake dauka ciki tsowon wadannan shekarun don wadannan ma baki sonsu ko?"
Wani wal tayi da idanunta ,batasan lokacin da bowl din fruit salad din ya subuce Daga hànnunta ba,mai aliyyu ke nufi?,zarginta yake yi ko me?,a guje tayi bedroom dinta saboda wani kuka da ya qwace mata



Yana tsaye a gun ya bita da kallo,jikinsa yayi sanyi,sai yace jin baiyi furucin da ya dace ba,sautin kukanta da ya soma ji sama sama ya sashi zabura ya nufi dakin,saidai kafin ya kai gareta amai yabqwace mata,ta kuwa dinga kwarashi,Duk sai da tayi aaman fruit salad din da taci,gaba daya ya rude fadi yake"am sorry my queen, sannu kinji"shi ya gyàra gun ya sai Mata ka6an bacci,Duk fuskàrshi ta canza kamar zai sai mata kuka,haka shim a ya gama nasa shirin baccin ya jawota ya manna ta da jikinsa,



Kalaman ban haquri yake ta jeranta mata,sai dai taqi ce wa kanzil,kai Daga qarshe ma sai ya juyata yaga ashe tayi bacci,ya sauke gajiyar Zuciya ya sake rungumeta yana jin rashin kyautawarsa har cikin zuciyarsa




*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:57 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*CONTINUATION*4⃣4⃣



washe gari asabar ce bai tashi da wuri,hakanan bai fita da wuri sai kusa da wajen azahar,don haka ta lallaba ta gama aikace aikacenta ta fice gun baba talatu wadda ta dawo a Daren jiya,nan suka shiga hirarsu tana bata labarin tafiyar da tayi



Ko da ya farka bai ganta ba yasan tana can,sukuku ya shirya don ya saba ita ke masa komai,wuraren daya ya daga Waya ya kira nasiru yace yaje ya dauko masa su Islam daga gidan momi wadanda da sassafe suka addabeshi sai da aka kaisu,Fadila na jinsu bata ce musu komai ba a lokacin



Hannunta riqe da kwanon zogalen da da baba ta kwadanta tana ci suna hirarsu cikin nishadi har da dariya, ganin shigowarsu kawai tayi suna rigen rigen fada wa cinyarta banda aslam da ya rakabe,batayi tsammanin dawowarsu haka da wurwuri ba,sai yaron ya bata tausayi amma sai ta dauke kai,don kaxa na take ranta ne ba don bata sonshi ba don ta koya masa darasi ne, duka yaran suka gaidata suka Kuma gaida babar kamar yadda ta saba musu Gaisa babba,shima aliyyu suka Gaisa yayi mata sannu da hanya tare da tambayarta mutan garin



Sai ya kalli baban yace"baba Zuwa mukayi ki taya mu roqo,'yarki muka yiwa laifi Kuma taqi yi mana afuwa"
Baban ta kalli Fadila"a'ah,ni kam na San 'yata bata da riqo,ba shakka laifinku mai girma ne,me kuka yiwa diyata?"
Da sauri Fadila ke girma aliyyu inkiya da ido na yayi shiru don Allah amma Sam sai yaqi kulawa
,"baba,aslam ta daka har jikinsa yayi shatin bulala,Kuma suka shige ciki suka barshi a waje,to nayi fada ne har ya wuce kima,na gane kuskure na na bada haquri amma anqi yafe mana,sai ake mana horo da halin ko in kula"



"Ashsha,ashsha,ya akai haka ta farun?"ta maida tambayar ga fadila,cikin raunin muurya tace"baba yanzu ace fisabililahi kamar aslam idan yayi laifi baza'a hukuntashi ba?,yaron nan sau hudu yana fasamin wayoyi,rashin jinsa duka ya zarta na 'yan uwanshi,ga raini,ya raina Muslim,har fa sai yasa hannu ya dakeshi,haka Islam ma bata tsira ba,dan qanqanin Abu zata masa yasa hannu ya maketa bayanshi babu mai dukanshi wai baya son raini"



"Sannan da ance za'a hukuntashi baban ya hana,to don kawai fa rannan na hukuntashi suka dau fushi ya kwashe kayanshi ya maida gun mominsu,qarshe ma harda cemin wai wa ya sani ko......"sai ta kasa qarasawa hawaye ya subuce mata,ai bai san lokacin da ya isa gareta ba,hannayensa ya sanya yana dauke hawayen,sai baba ta yunqura ta miqe ta fice tsakar gida,don ta lura abun nasu salon maganar nan ce da ake cewa *fadan masoya hutu ne ko sunyi zasu dawo su shirya*



Yayi Kane Kane ya hana hawayen zuba"kada ki yimin haka mana Fadeelah ta,na riga na yima ka ina alqawarin fa ba zaki sake zub da hawayenki ba,kinsa alqawari na ya karye?,jiya Kiyi daya kyau kinyi,ina jin zuciyata cikin qunci duk sa'ilin da naga hawaye a fuskarki,pls ki yafe mana,ni da 'ya'yana bamu saba ganinki haka ba kina hukuntamu"
Sai ya juya gun yaran ya kira su da hannu"Ku zo mu bawa mamee haquri"ai kuwa suka yaso da saurinsu duk suka durqushe a gabanta yadda suka ga abbun na su yayi



Muslim yace"pls mamee kiyi haquri kinji mamin mu"
Islam tana riqe da kunnuwanta tace"sorry mamee,pleaseeeee"
Aslam ya taso ya kama qafarta"mamee na na dai na bazan sake ba,kince annabi nabda haquri Kema Kiyi maker pls,I promise bazan qara ba,Duk abinda kika ce nayi zan dinga yi kanji"
Sai suka suka bata tausayi,ta Miqa musu hannayenta suka taso Muslim a hagu aslam a dama Islam ta dane cinya,ta dinga shafa Kansu tana cewa"na yafe muku,Allah yayi muku albarka"
"Ameen maman mu mana sonki"
Ta saki murmushi"Nima ina sonku yarana"



Aliyyu dake kallo su cike da sha'awa ya Matso yana turo mata kansa"Nina mamee a samun albarkar"cikin hararar Soyayya take kallonshi
Sai ya kwabe fuska shims kamar tarin"kunga maminku taqi shafa min kaina ko?"
Nan suka rude da ce wa mamin mu a shafawa Abbu shima,dariya tayi shima ta shafa masan



*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 9:57 AM] My Mom: * 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 3*

4⃣5⃣



Sai lokacin baba ta dawo,taji dadin ganin sun sasanta kansu ,nan taja hankalinsu su duka har yaran,cikin gamsuwa sukayi mata godiya
Ya kalli fadilar cikin marairaicewa"to ataimaka azo a yimin Garin pepper chicken din nan mana mai dadi, ni da abokaina duka zamu tayaki aikin"
Ta noqe hancinta tace"a dauri kashi ko a bata igiya,babu abinda kika biya sai qara wa mutum aiki"da sauri Islam ta kalli mamin nata tana nuna kanta da yatsa"banda ni ai ko mamee?"
"Har ke mana"jin haka yasa su Muslim suka qyalqyale mata da dariya,sai ta kwabe fuska ta soma diddira qafafu kan Dariya da su Kayi mata,aliyyu ne ya taba fadan ta hanyar daukarta ya sabata a kafada aka tafi yin paper chicken din baba talatu ta musu a dawo lafiya bayan sun mata tayi Zuwa tace lazumi zata yi sai sun dawo,islam tace zata kawo mata qashi,Duk suka sa dariya



Haka suka cikata da surutu cikin kitchen din,ba ga yaran ba ba ga babansu ba,aiki dai na surutu kawai suka tayata ta,har ta samu ta gama ta tura musu,ya tasa yaranshi a gaba bayan kowannnensu ya wa ke hannu suka soma ci cikin plate guda



Sai da suka ci kusan Rabi sannan ya dubeta tana zaune gefensu tana lura da yanayin can abincin yaran nata,Duk Wanda ya gutsuro kafin ya ci sai ya miqawa abbunsa, yaran na da matuqar son iyayensu
"Ke baki ci ne mamee?"
Ta zumburo baki "sai da ya rage saura qasusuwa wannan za'a yimin tàyi?"
Sai suka soma rige rigen bata a baki,kuwa yana ce wa nashi zata ci



Murmushi ta saki tace musu duka ta gode,Allah ya yi musu albarka ita ta qoshi,taci zogale gun baba,aliyyu yayi qasa qasa da Maurya bayan ya dubeta"anya baby na lafiya qalau kike?,ina lura dake rashin son cin abincinki ya qaru akan na ainihi,fruit salad kawài kike bawa muhimmañçi,anya ba wani cikin gareki ba?"



Kai tsaye ta Daga masa gira tana murmushi,cikin zumudi har baisan sanda ya daga murya ba yace"are you serious baby?"
"Yes"tace da shi cikin wata iriyar murya mai taushi
Ya lumshe ido a fili yace"alhamdulillah,alhamdulillah"
Sai ya tara yaran yana fada musu sun kusa yin qani,ihun murna da tsalle suka dinga yi abbun na su na biye musu,ta saki murmushi bayan ta dau ke idoñtà daga Kansu
Gaba daya aliyyu ya maida yaran abokanshi"

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Rayuwa mai cike da jin dadi amunci da qauna suke yi cikin gidan,tuni ganin gidan rediyon Fadila yayi nisa,Wanda bai da nisa da qatuwar islamiyya da dake gana wa samira wadda totally yanzu ta can a idan ka gantà zakayi mamakin yadda ta sauya,ilimin addini sosai ya ratsatà



A nurse aliyyu ya zauñàr da Fadila yayi mata ba yamin abinda yasa yake ma Samira haka duk da a yanzu ya soma daidàità lamuran,yana son ya gane turban muzuru tayi ko na gaske,saboda canza mutum haka lkc guda sai Allah,zata iya zama da shi cikin kowañne irin halin kamar yadda ita fadilan tayi a baya?,ta Kuma shirya can a tsarin rawarta ta xamo ta dace da ra'ayinshi da tsarinshi?,
"Hakan ya tabbata ai tunda ga zahiri kana gani ko"
Tace da shi



Cikin ikon Allah Fadila ta dauka lafiya,ta samu qatotoñ lafiyayyen yaronta Wsuna yaci su na *ABUBAKAR ASSADDIQ*,don su abba ba masu damu wa da wani takwara ne ba




*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 10:01 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*CONTINUATION*4⃣5⃣



_*BAYAN SHEKARU GOMA*_



dukkaninsu Fadila,aliyyu,aslam,muslim,islam ,saddiq,umar,usman,iftihal,suna cikin filin wasan da aka tanada cikin gidan domain wasanin motsa jiki,sanye kowannensu yake da kayan sport farare qal,table tennis ake ta bugawa tsakanin Fadila Islam iftihal da Kuma team din aliyyu da ya qunshi aliyyun kanshi muslim aslam,faruq da sadiq ne a gefe su na tilliqa dariya ga duk wanda aka ci,basu da bangare



Ganin dai da gaske su aliyyu na shirin basu kashi yasa ba shiri fadila ta radawa iftihal yake tavtaho da mommy(samira) don itama gwanar table tennis ce,sai kuwa gata tsaf a shirye cikin kayan sport din,su aslam suka sa dariya,aliyyu yace"Duk Ku gama taron danginku,kun sani mune winners ba yau aka fara ba"
"Wlh kuwa abbu"inji aslam



Cikin ikon Allah sai su Fadila suka cinyesu,gufa ya rude iftihal tace"shikenan daddy,mume da ikon zabar qasar da za'aje hutun qarshen shekara"tavfadi tana yiwa su Muslim dariya don ra'ayinsu ya ban bata,haka suka haqura da akaxo dinner suka zaba,wannan karon a Africa za suyi don haka iftihal ta zabi South africa,samira ta zabi Ethiopia tana son taje taga garin da sarki najjashi ya mulka,suka tsara tafiyar kuwa da tafiyarsu saudiyya sauke farali



A Daren aliyyu yasa Fadila ta kira farida tace"gobe driver ya kawo humaira ta tayi da passport dinta za'a buga mata visa din qasashen da zasu,tunda tuni abbanta ya buga mata ta saudiyya,jinin aliyyu ya hadu da na yarinyar sanda kama da takeyi da fadilansa,shi yasa duk hutun da su ke fita da ita ake tafiya,ko unguwa fadilan zata wani lkc ta fita da humairar da Islam sai ayita dauka humairar ta Haifa ba Islam ba,don ita Islam da abbanta tayi kama



Duka family ukun da su aka saukre faralin bana,yarda Anty hauwa da iyalinta,scan ne Fadila ta so lura kamar amai wani Abu tsakanin iftihal da Muhammad(qaninta)sai dai bata tanka ba,ta barwa ranta ne idan lokaci yayi zasu nuna kansu



Daga saudiyya suka wuce hutunsu na qasashe biyun Hutu Kayi mai dadi sosai,Hutu ne da Iyalan suka dinga ji dama kada ya qare,ciki yarda samira domin tuni aka 'yantà ta,sai dai ta riga ta sani ta Kuma saddaqar Fadila ta riga ta yi mata fintikau,tayi mata zarrar da ba zata iya kamota ba ta kuwa ne ganin,saidai ita kanta tana jin dadin yadda tayi wata ta canza,Allah ya nufe ta da gane gaskiya tun lokaci bai qure mata ba irin yadda ya qurewa salima,tana Kuma sake yin addu'a ga Fadila don kaso casa'in na gyaruwar rawarta ita ta bada gudunmawa



To Tun a can Fadila ta soma jin canje canje a jikintq,sai dai tayi shiru da bakinta,suna dawowa gida duka sai suka kwanta ciwo ita da samiran,til as doctor sa'adah ta ziyarci gidan,bayan gwaje gwaje ta shaida musu *duka su biyun suna dauke da ciki*,kuka Samira ta dinga yi haiqan tana gode wa Allah cike da yabo na yadda bai dubi halàyenta ba na baya da kurakurenta ba ya azurtata da samun qaruwa



Kasa zama Fadila tayi Duk da jirin dake dibanta sai da ta taho bangaren samiran,ta rungumeta cike da farinciki,jin sumbatun da samirar keta yi ya sanya ta hanata magana tace
"Shi Allah babu ruwansa,Mutuwar Kayi tuba tuba mai kyau to zai gafarta maka zunubinka komai yawansa ko da shirk a ce indai Baka mutu kana aikatawa ba"
Tsananin farinciki ne ya rufe aliyyu,Duk da yaran dake gabansa amma ninkinsu yake buqata,taga kulawa Daga kuwa wadda bata taba katarin gamo da irinta ba


*Mrs Muhammad ce*👑


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 10:01 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




Please Login or Register in order to submit comment