Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din Abban hannunta dauke da doster da alama goge goge ta gama,fadila ta gaidata tana qoqarin tashi tace"abba zan tafi"ya dubeta sannan yace"ai banga kin ci komai ba haka zaki tafi?""abba zan karya a capteria idan na..........
Ummi tayi saurin katse ta da cewa"yi mana shiru wlh abbansu idan taje ma bacin take ba farida ai ta gaya min wai ba zata iya cin abinci a waje ba,wannan yarinya na rasa meke damunki anya lafiyarki qalau kuwa?",abban yayi murmushi yana dakatar da ita"dakata umminsu,fadila lafiyar ta qalau,kin manta yawon asibitin da muka dinga yi da ita tun tana qarama?,haka dai halittarta take"ya juya ga fadila yana tura mata cup din da ta hada masa kunun yace"maza zauna kici wani abu kada ki qara bata ran umminki kinji ko?"tamkar zata sa kuka😟 ta zauna tana cewa"to abba"yaci gaba da cewa"gashinan fadila tafiki abin arziqi shi yasa ta rainaki tana ganin kanku daya,ummin tace sai rawar kai da gwanintar yin girkin amma saidai wasu su ci mata,abban yayi murmushi yana kallon yadda take tura abincin kamar magani😣
Kafin ta kammala muhammad ya shigo don haka abban ya sallamesu suka fita tare,suna mota muhammad ya dameta da surutu,ta daga masa hannu ✋🏻hadi da cewa kaga malam bafa aku na dauko ba🐔idan kuma kai aku ne ka gayan"ya qyalqyale da dariya😂 yace"anty ke dai ba dama mutum yayi hira dake sai kice ya dameki shi yasa yaya farida ke burgeni ke halin ya ahmad kikayo kun fiya kwafsawa wlh,ta harareshi sannan tace"ai da itan da kai duk zamuce ta tadda mujemu idan mutum baiyi surutu ba baya burgeku,kada Allah yasa mu burgekun muyita kwafsawar,idan ka qara magana kuma sai na saukeka anan" take ya rufawa kansa asiri yayi shiru🤐
Taso makara saboda ajiye muhammad da tayi don ita ta saba da wuri take zuwa don ta samu sit din gaba,bata da wata qawa bare ta tarar mata hakan ya jawo batayi parking din motar ta daidai ba ta nufi ajin cikin sauri
Lacture din ta daukesu awa uku har da mintina,kanta ya dauki chargy sosai,don haka da fitowarta ta samu wani guri dake nesa kadan da ajinsu bashi da yalwar jama'a sosai yafi kusa da inda suke ajjiye motocinsu idan sunzo,gurine mai wadatar shuke shuke ita kuwa ma'abociyar son tsirrai ce
[8/8, 3:24 PM] LOADING......

gun na burgeta saboda son tsirran da take dashi,tamkar a cikin iska ta ke jiyo qamshinsa,gabanta ya tsananta faduwa,ta gefan ta ya wuce saidai bayansa kawai take iya gani,ahigar suit ne a jikinsa masu dan karen kyau da sheqi,kayan baqaqene sai tsintsiyar hannunsa da ta gani wadda yake daure da agogon fata baqi,gefansa wani ne ke biye da shi riqe da takardu da brief case,sam sai ta kasa dauke idanunta daga kanshi👀,hakanan gabanta yaci gaba da faduwa cikin zuciyarta take fadin inna lillahi wa inna ilaihir raji'un"har ya danyi nesa da ita sai taga ya waiwayo,cikin wani irin sauri ta dauke kanta tayi wani sashen da shi zuciyarta kamar ta tsinke ta fado,ganin yayi gaba tayi hamdala da Allah yasa bai lura da ita ba,tana tsammanin jikinsa ne ya bashi ana kallonsa👀,a sace taci gaba da kallonsa har ya bacewa ganinta,taja ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kallon hanyar ta jawo jakarta ta zuge ta fiddo da wayarta tana danne danne,ta doshi kusan minti aahirin a gunbtana hutawa sai sannan ta tuna zata fa gidan ya ahmad,da sauri ta miqe tana gyara yafen gyalenta,atamfa ce ajikinta dinkin riga da skirt ne,atamfar England ce dark green mai ratsin yellow,sai mayafinta da takalminta agogo da jakar hannu duk yellow,fadila ba qarya ta iya daukan wanka don duk munin atamfa takai aka mata dinki ya saka komai kushe da hassadarka baka isa kace batayi kyauba haka Allah ya bata wannan baiwar,tana tattare komatsanta tana sanyawa a jaka taji ana kwada mata kira,a nutse ta dago tana neman daga ina wannan kiran mafarautan ke fitowa?,wata class mate dinta ce binta auwal fadila taci gaba da binta da kallo har ta qaraso,"fadila abbas yaufa kinyi tabargaza"abinda ta soma cewa kenan,fadila tace"kamar ya fa?"tana dubanta tace kinyi wrong parking kin toshewa A.s mai tama hanya"ta sake dubanta cikin rashin fahimta tace"waye haka kika bi kika rude?'binta ta zaro ido😳 tace"kar dai kice min baki san a.s mai tama ba,hadadden guy din da duk nigeria bama kano ba ansan da zamansa"fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa"na gode"taci gaba da mayar da kayanta jaka
Iya dube dubenta ba wanda ta gani sai mutum daya👀,a tsammaninta idanunta ke mata gizo,sai dai har ta qaraso gun shi din dai ta gani,yana tsaye hannayensa harde a qirjinsa fuskarnan a murtuke,ta qaraso ne da niyyar bashi haquri sai dai lura da irin kallon qasqancin da yake mata mata yasa tayi banza da shi kai tsaye ta nufi motarta ta bude,ta zauna a seat din tana qoqarin jan murfin ta rufe taji an dafe murfin motar,ta dago ta dubeshi,yana tsaye yana mata irin kallon dazun,cikin qasaita taji yace"baki da ladabin bada haquri ga wanda kika aikatawa laifi?"duk da yadda zuciyarta ke sake ninqaya a zuciyarta,muryarsa mai sanyi ta kwanta a zuciyarta,amma ta dake gami da cewa cikin zuciyarta"duk da dumbin qaunar da nakeji taka a zuciyata hakan bazai sa na bada girma da jan aji irin na 'ya'ya mata,ta dauke kanta sannan tace"ai shi wanda akawa laifin baisan darajar bil'adama ba"ya saki murfin motar hadi da watsa hannayensa yace"ok,ba laifi"ya saki murfin motar,cikin wata iriyar gaggawa taga ya amshi key din tasa motar daga hannun wanda suke tare ya bude motar sa ya shiga cikin gwaninta ya take motar ya kurda ya matse motar fadilan ta yadda itama bata isa ta fita ba harsai da ya gogeta,ya kashe motar ya zare maqullin ya rufe motar ya fito yana cilla maqullan yana cafe wa ya danyi tsalle ya haye bayan motar ya zauna,da hannu ya kirashi yadan yi masa rada ya amshi tak ardun hannayensa shi kuma ya juya da sauri ya bar gun
Sarai fadila ta fahimci abunda yake nufi saboda haka ta zaro wayarta ta nemi number farida ta kirata"hello farida kin shigo school?"tace"eh ya akayi?""kizo ina parking space ki daukeni mu wuce"farida tace"me ya sami motar ki?""kinga idan zaki zo kawai kizo malama""ok sister gani nan"
Cikin 'yan mintina sai ga farida horn tayi mata ta miqe ta fito ta kulle motar ta gabansa ta shige ta nufi farida,dai dai lokacin ta jiyo saukowarsa daga bayan motar,wata yar qaramar mota ce tayi parking a gabansa kusan tare suka shige motocin,ta madubin motar farida suka hada ido ta sakar masa tsaki hadi da murguda baki,cikin zafin nama ya balle murfin motar ya fito da sauri tacewa farida"yi sauri ki bar gurinnan,tamkar kuwa tasan meke faruwa ta figi motar ta bar gun

Muje zuwa
[10/16, 12:21 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wa yasan gobe?

Safiya Abdullahi musa huguma

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶4⃣

Sai da motar ta saitu akan titi sannan tace mata"gidan ya ahmad fa zamu"ok" inji farida,"sister wai me ya faru naga kamar wadda aka biyo a guje?"taja tsaki tace"wani dan rainin hankali ne yaso wulaqantani bai san bana daukan wulaqanci ba"ta bata lbr yadda sukayi da shi akan toshe ma juna hanya da sukayi,me farida kuwa zatayi idan ba dariya ba,"kefa 'yar wulaqanci ce shi yasa ban fiya saki cikin lamarina ba,a yar madaidaiciyar harabar gidan sukayi parking,kai tsaye suka nufi falon gidan,ba kowa cikin falon da alama matar gidan na ciki don haka suka dinga kwada sallama,daga kitchen matar gidan ta fito anty hafiza kenan kyakkyawar bafullatana,tana ganinsu ta saki fara'a😊 cikin barkwanci tace"lallai yau baquntar tamu ce"suka saki dariya😀dukkaninsu suka gaidata cikin girmamawa ta amsa musu cikin kulawa tana tana tambayarsu ummi,suka ce tana lpy tana gaidata,fadila ta zaro packet na chaculet tace gashi injita a baiwa twince,wai ni ina suke nema anty?""tace yau ai ranar school ne suna can amma suna hanya don bala ya tafi dauko su,""na manta wlh"ta fada tana qoqarin kwanciya bisa doguwar kujera"anty hafiza tace"ah ya haka ina murna kuku tazo kuma naga tana neman bin lafiyar kujer?"fadila ta dan murmusa 😊tace " anty yau saidai amin afuwa yau kasala nake ji""na miki"inji anty hafiza,farida dake canza tasha a t.v tace"qyaleta anty muje na canjeta yau tsokano fada tayi sauran kadan taci na jaki badan Allah ya kawoni na ceceta ba""tab wucenan wlh wa ya isa yayi gangancin taba mana ita?😳""fada mata dai anty😏"cewar fadila,suka shige kitchen nan suka barta a falon
Gyara kwanciyarta tayi don taji dadin yin tunaninsa,shi wa?,idan bata manta ba A.S mai tama binta tace da ita,A.S mai tama ta shiga maimaita sunan ita da zuciyarta,"to me A.S mai tama take nufi?"A dai duk inda aka zaga farkon sunansa ne,to ahmad ne ko ko abubakar ko abdul?,oho itama bata sani ba,wani murmushi ne ya subuce mata😊 sai tunaninta ya dawo kan abinda ya faru tsakaninta dashi dazun,sassanyan muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunnenta,kyawawan idanunsa yanayin zubinsa da tsarinsa,sai ta tuna sanda ya fito a fusace lokacin data murguda masa baki ta harareshi,nan ma dariya ce ta subuce mata,"lafiya kuwa?"ta tsinci muryar farida na tambayarta,ta hade rai tace"lpy lau me kika gani?"farida ta dan tabe baki tace"hmmm tun dazunfa kike murmushi har da dariya ke kadai kamar wadda ta fara soyayya"da sauri fadila ta kalleta tace"lallai yarinyar ni kikewa wannan titsiyen?to gyada na zama na soye qarewar soyayya"anty hafiza dake zaune saman kujera bata sa baki ba sai yanzu tace"um um yaya fadila wannan fa sign ne na falling in love😜"fadila ta miqe daga kwanciyar tana cewa"kai anty,please kada ki biyewa shirmen farida,ita 'yar sa ido ce komai ta gani idonta na kai,kuma sai ta sanya ma question mark😏",ta gyada kai sannan tace " alright idan tayi wari maji,Allah yasa alkhairi ne""amin amma ba abinda zaiyi wari ma anty",nan gidan suka wuni har 'yan biyu suka dawo suka yini tare da su,suna son yaran sosai ko dan su kadaine jikokin gidan nasu,sai bayan magariba sukayi sallah sukaci abinci har yaya ahmad ya dawo ya tarar da su,bayan sunyi shirin tafiya ne ya ahmad ya baiwa ko wacce 4000 anty hafiza kuma ta basu turarurruka.
to daren ranar sam fadila bata samu bacci ba,kusan kwana tayi tunanin A.S maitama,duk da ta danji dadi don aqalla tasan yanzun yasan da fuskarta a duniya,koda bazai iya shaidata ba bare tana tunanin mawuyacine ace yayi saurin manta ta ko dan irin karon da suka yi,har washegari da taje school bai janye motar tasa ba,sun dauki aqalla sati guda a haka sannan taje ta tarar ya cire,a gida tace ne kawai tana tana garage ana duba mata ita
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin wannan yanayin suka soma attachment,ranar laraba aka turasu domin tattaunawa da wani fitaccen dan kasuwa,ita da abokiyar karatunta ne hafsat sai wani ma'aikacin gidan radion khalid da zasu tafi tare qarfe hudu na ranar larabar.
cikin yellow din atamfa ta shirya mai zanan blue din qananun taurari,skert ne rafa da riganshi wanda dinkin yayi mata cif a jikinta kamar don ita aka qera atamfar,ta maqala qananun fashion na dutse masu kalan blue,ta daura dan siririn agogo na fata ,qafanta blue din hill shoes ne mai madauri sai mayafi data yafashi a kafada bayan ta soka daurinta wanda ya fito da dogon gashinta ta qasan daurin,jakarta ta dauka 'yar madaidaiciya wadda ake maqaleta a gwiwar hannu ta feshe jikinta da turaren shamsul imarat,shigar ta haska fatarta sosai ta fito dagwas da ita,farida dake nade a tsakiyar gadon fadilan tana charting ta dago ta dubeta"gsky yaya fadila kinyi masifar kyau,tsiyar abun daya da baki kula kowa,sai ance anasonnki kuma ki kama mita bayan laifinki ne saiki yi shiga ta janye hankali kuma kice ba wanda ya isa ya kalaki"banza tayi mata ta dauki wayarta dake kan dressing mirror ta fice,farida ta dan daga murya yadda zata jiyota tace"a dawo lpy antyna Allah ya hadaki da mannau ya biyoki har gida😜"bata dai ce mata ci kanki ba ta wuce dakin ummi don tasan a wannan lkc tana daki tana azkar,daga bakin qofa ta tsaya don ta kusa makara tace"ummi zan tafi""to Allah ya tsare hanya ki kula sosai kuma kuna kammala abinda kukaje yi ki taho gida kada ki yadda kiyi dare a waje"tace insha Allah ummi",acan gidan radion suka hadu,bata shiga ba ta yiwa su Hafsa waya su fito su wuce don a motarta suka tsara za suyi tafiyar,Hafsa na zaune a baya yayin da khalil ya shige gaba,tsaf fadila ta gama karantar manufarsa saidai tayi banza da shi tamkar bata fuskance shi ba,tun zuwanta gidan yake rawar qafa a kanta saidai ya kasa furta mata kamar sauran maza da yawa,tana da wani irin kwarjini ne a idanunsu ita sam baya burgeta,ya fiya surutu shi yasa sam bata son ko aiki ne a hada ta da shi,kamar yanzun ya takura mata sai zuba yake shi ala dole sai ya burgeta,Hafsa na baya tana ta tuntsira dariya 😂don tasan halin kayarta sarai,daqa qarshe c.d plate ta dauka tasa sannan yayi shiru
A hankali suke binkwatancen har suka gano gurin,qaton get din gun aka bude musu gu ne a tsare ahankali aka dinga nuna mata inda zata bi har taje inda aka tana da don ajiyar motoci tayi parking suka fito,ta jingina jikin motar tata tana qarewa gun kallo,tamkar ma'aikata gun yake saidai ya tsaru sosai komai neat,khalil ya qarso gunsu bayan yaje yayi tambaya yace muje can sunce mu jirashi yana fitowa,wani dan gune da ka qawatashi da flastic din kujeru da teburinsu kowanne yaja kujera guda ya zauna
sun dan dauki mintina har fadila ta soma qosawa da zaman jiran
Tun daga nesa da ta hangoshi qirjinta ya hau luguden bugawa,ji tayi tamkar ta tashi ta bar gurinsai kuma taga idan tayi hakan ta bada kanta,don haka sai ta basar ta zarme da bude jakarta ta soma fiddo da kayan aikin da zasu buqata,qashin mayen tutarensa da taji ya mamaye gurin shi ya tabbatar mata da qarasowarsa,sallamarsa ta same tabbayr mata da hakan dukkansu suka amsa saidai ita ta kasa dago ido ta dubeshi ta fake da laluben jaka,ya .iqawa khalil hannu sukayi musabaha hafsat ta gaidashi,sai a sannan ta dago kanta caraf suka hada ido👀 saidai ga mamakinta dauke kansa yayi tamkar bai taba ganinta ba,a hankali ta radawa hafsa"da wa za muyi hirar ne?""gashinan a gabanki a.s maitama "inji hafsat"take taji ta dan rude amma cikin dabara ta gayyato dakiya da nutsuwa ta yafawa kanta,kasancewar Ita ce mai tambayoyin jfsat da khalil na tayata da rubutu dolenta ta jawo kujerarta ta sake matsowa daura da shi ta sanya 'yar qaramar recorder dinta a tsakiyarsu suka sake zama verry close aunyi face to face sosai,wani yanayi ya dinga shiga zuciyarta da gangar jikinta wanda hakan ya haifar mata da kasala,tanason tayi.masa tambaya ta farko saidai ta kasa,har sai da hafsat ta dan dungure sanna tayi ta maza ta dago ta fuskanceshi👀,saidai ga mamakinta hannauensa na harfe ne bisa qirjinsa yana mata wannan salon jallon rainin nasa😏,da fari munason muji ainihin cikaken sunanka,ta fada yayin da ta mayar da dubanta kan radio dinta taga tana nadar sautin yadda ya kamata,shiru taji har yayi yawa ta dago ta sake dubansa a karo na biyu,saia taga ya saki hannunsa ya dauke idonsa daga kanta ya kalli khalil yace"ko zakuyi musayar aiki ita ta ta karbi rubutun kamar ba zata iya aikin ba"khalil ya dan rusuna yave ranka ya dade zata iya haka tsarin aikin yazo"ya kalleta cikin gatsali yace"zaki iya?"batayi qasaaqwiwa ba tave aisai an gwada aknsan na qwarai"ta mayat masa da irin yanayim yadda ya yi mata tambayar,cikin ransa yake jinjina rashin kunyarta tare da fafin nasan maganinki" a zuciyar sa ya fadi hakan

Ku biyoni muje......





[10/16, 12:21 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
▶5⃣

Ya dan gyara zamansa cikin isa ya amsa mata"Aliyyu salim maitama shine cikakken sunana""sunan ya dace da maishi"ta fadi a ranta,cikin nuna qwarewa da gwaninta ta shiga jefa masa tambayoyi daya bayan daya,sai da suka kwashi kusan awa guda sannan ta saurara masa,ta katse abun recording din nata ta jefa a jakarta,ta miqe tayi gaba abinta,saidai can qasan zuciyarta farinciki ne fal ranta,yau ta zauna daf da shi ta shaqi qamshinsa ta saurari muryarsa son ranta,shi kam bin ta yayi da kallo cike da mamaki da takaicin raininta don a gurinsa wannan raini ne.
Zaman ta tayi cikin mota tana dakon zuwansu hafsat
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Dukkaninsu suna gidan alh salim,kasancewar yau ake birthday din iftihal,rabi'ah sumayya farida da fadila anty hafiza sai anty hauwa'u(babbar yar haj maimuna)duk suna bedroom din momi,fadila na kwance bisa gadon momin,dakin ya kaure da hayaniya amma banda ita,sam gun ma baya mata dadi,tun jiya da Abba yayi mata da ya ahmad suka yi masu magana ita da farida kada su kammala attachment dinau ba tare da sun kawo mijin aure ba,farida kam ko ajikinta tunda dama irin wannan damar take jira ita da masoyinta mubarak
Ta sake juya kwanciyarta hannun damanta kanta yayi mata gingirin zuciyarta a cunkushe,anty hafiza ta juyo ta kalleta "fadila ki saki ranki don Allah kiyi addu'a shine kawai mafita "fadila ta lumshe idonta hadi da sake qanqame pillow tana sake jin nauyi cikin qirjinta,anty hauwa tace "me ya sameta ne tun dazun na lura bata cikin sukuni",anty hafiza ta gaya mata hadi da cewa"na rasa irin farida kwata kwata bata kula kowa,nan da kika ganta bata da wani gwani"farida tace " anty itama fa da laifinta ya za'a ce duk mazan dake mutuwar sonta ace babu daya da ya mata"a fusace fadila ta kalleta😡"anty kinganta ko ko da ita ake magana?😫"dama zuciya kusa a kusa sai hawaye wani na bin wani😭"anty hauwa'u tace"duk ku tashi ku fita ku bamu wuri"tsam suka fice dakin ya rage daga ita sai fadilan sai anty hafiza,anty hauwa'u taja ajiyar zuciya tace"sai nake gano dacewa tsakanin fadila da Aliyyu Abban iftihal ba don kada nayi muku shishshigi ba da na hada wannan alkhairin"gabanfadila yayi matsananciyar faduwa💔 jin an ambaci Aliyyu,inama ace shine aliyyun da anty hauwa'u ke magana akai?,ina ma ace shine zai taho da neman soyayyarta?,ina ma ina ma.........taci gaba da zancen zuci
Anty hauwa taci gaba da cewa"shima anyi anyi da shi ya fidda mata tayi aure ya qi,sai jiya ya kawo wata yarinya mai zubin yare ba alamun tarbiyya a tattare da ita wai ita yake son aura,hafiza yarinyar bata da maraba da matarsa ta farko,amma sai ya kakkareta da cewar wai zaman cikin yare ne yasa aka ganta haka amma da nutsuwarta.
Fadila tayi hanzarin tashi don batason zancan da anty hauwa'u ta dauko yayi ma wani nisa,tayi qasa da idonta😪 tace"anty ba wai inason watsa miki qasa a ido bane a'ah,bansan ya Aliyu ba sani na da shi tun ina qarama ne wanda a yanzu na manta shi gaba daya,shima kuma nayi imanin ba sanina yayi ba,ba ta wannan ba anty a zamanin nan auren soyayyar ma ya aka cika bare auren hadi,matar cushe anty ba ta daraja,kawai ku tayani addu'a Allah yayi min zabi mafi alkhairi"suka amsa da amin suka kuma bar maganar suka shiga wata badan maganar ta bar ran anty hauwan ba
Kwana biyu da yin maganar anty hauwa na juya maganar cikin ranta sai ta kasa hadiye maganar har sai da ta niqo gari ta dawo gidan don tattatunawa da abba"tana zaune gaban abban bayan sun gama taba hira tace"abba nazo maka ne ne da wata muhimmiyar magana"abban ya bada dukkan hankalinsa kanta sannan yace"uhm ina jinki maijidda"ta dora"abba kasan fadila 'yar abba abbas tafida?"yayi murmushi irin na manya yace"banda abinki maijidda idan ban san su farida ba ai kuma bansan kuba,"tayi dariya ita da momi tace hakane abba"tiryan tiryan take gaya masa halin da yanzu fadila ke ciki game da zancen fiddo da miji,sannan ta dora"abba inason ne na haska muku abinda tuna nina ya hasko min game da wannan lamarin""uhn"cewar abba,anty mai jidda ta dora"abba Ali ya kawo muku yarinyar da azahirin gaskiya baku yadda da halaye da nagartarta ba,ali abba ya riga ya fada soyayyar yarinyar wadda da zarar kunce zaku hana shi auren ta dama ce tq zo masa ta yaci gaba da zama babu zancen aure,zai kafa hujja da cewa ai tun tuni ya kawo ku kuka qi abun"abba ya gyada kai cikin gamsuwa maijidda ta dora da fadin"to abba mai zai hana ku bashi damar ya aureta amma abba ku hadashi da fadila?,abba kai ganau ne ba jiyau ba ka fini sani kasan fadila kasan irin kyakkyawar tarbiyyar da suke da ita,mai zai hana muyi kwadayin hada zuri'a da su abba?,abba kada mu bari ta subucewa family dimmu saboda fadila macace ta gari wadda nake da yaqinin samun alkhairai masu tarin yawa da zuriyya dayyiba tattare da ita?"
Shiru sukayi gaba dayansu bayananta na ratsa su tabbas duk abinda maijidda ta fada gaskiya ne,sun gamsu matuqa da bayananta,abba yaji dadi matuqa sosai tare da sawa maijidda albarka gameda zurfin tunanin da tayi akan makomar rayuwar dan uwanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari alh salim da kansa ya taka ya nufi gidan amininsa alh abbas tafida,suna babban falon sa bayan sun gam gaisawa alh salim yace"abbas nasan zakayi mamakin ganina ko da daddarennan bayan jiya da azahar ma muna tare"alh abbas yayi murmushi yace ai nasan akwai dalili,kuma ma mene a aciki don dan uwa ya ziyarci dan uwansa aduk sa'adda da yaso?"alh salim ya gyada kai yace"hakane dalili ne kuwa babba ya taso da ni"alh abbas ya vyara zama yace"ina jinka Allha yasa lpy"alh salim yace"danka Aliyyu nazo nemawa auren'yata fadila"alh abbas yace"fadila?"ya gyada kai qwarai fadila ko anyi mata miji ne?"alh abbas ya girgiza kai yana murmushi yace"ko daya wlh,rigimar da nake ma da ita kenan a 'yan kwanakinnan kenan akan sai ta fito da miji,maganarka alh ta yimin dadi sosai wlh,amma ina fatan da amincewar alin?"a'ah ko daya wannan hasashe nayi na son hada zuriyya da aminina"alh abbas ya saki dariya yace"yayi wlh wannan tunani naka yayi kyau qwarai da gaske,domin samun nagartacce kamar Aliyuna a wannan zamanim abune mai matuqar wuya qwarai da gaske,fadila'yar ka ce halak malak kuma ko wani kaso bata wlh zaka iya bashi bate aliyu,na bawa aliyu ita har abada abokina"alh salim yace"a'ah abokina kada kayi saurin yanke hukunci ba tare da kaji ta bakin ta ba ka bari su gana taga idan har yayi mata"alh abbas yace"haba salim Haba salim yaya zaka ce haka bayan kasan yarinya budurwa ubanta ne ke da ikon zaba mata mijin aure ballantana duk yaron da zata zaba mawuyacine yakai nagarta da ingancin aliyyun,ai magana ma ta qare dama dab suke da kammala attachment dinsu nafison ace da zarar sun kammala su tafi dakunansu"
Alj salim yaji dadin maganar yace"amma fa wani hanzari ba gudu ba,akwai yarinyar da aliyun zai hada su ya aura tare,to ya kamata a sanar da ita kasan yaran yanzu basa son abokiyar zama kaga ya kamata ta sani kafin ayi"alh abbas yayi dariya yace"shirmen banza ne iri na 'ya'yan yanzu zan sanar da ita kada ka damu,bamu buqatar duk wasu kaya na bidi'o'i"alh salim yace"a'a kaima ka sani momimta haj maimuna ba zata yarda ba yadda za'a yiwa dayar itama sai an mata"suka sa dariya gaba dayansu cikin farinciki,cike da godiya bisa karamcin da amininsa yayi masa"alh abbas yace ka daina godiya da Aliyu da fadila duk daya ne a gurina"alh salim yace"na sani amma duk da haka godiya ta zama dole duk wanda yayi ma jininka kyautar da sukutum da guda ai ba qaramin masoyi bane,cikin girmamawa da mutuntuna juna sukayi sallama

Safiyya(mra muhammad bello)
[10/16, 12:22 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wa yasan gobe?

Safiyya Abdullahi musa huguma

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶6⃣

Cikin daran alh abbas ya sanar da mai dakinsa,tayi murna qwarai don tasan amincin dake tsakanin mazajan nasu da irin tarbiyyar dake gidan alhj salim,sai dai tace wani hanzari ba gudu ba alhj ba lallai yaran su so junansu ba fa?,abba yayi dariya yace"duk soyayyar yqnzu shirme ce,ina soyayyar take zuwa?daga anyi auren ta mutu sai ki rasa ranar da tayi musu,wani auren hadin ba yafi qarko da albarka ba,ga auremmu ya isheki misali sai da aka kawo ki muka ga juna ko kin manta,gashinan haryau shekara kusan talatin da biyar ba fada bare yaji"ya dan kalleta ta sigar tsokana yace"nasan dai abu daya kikayimin kin shanye ni na kasa qaro miki abokiyar zama"kunya ta kamata tadan rufe fuskarta da tafin hannunta🙈tana cewa"kai alhaji"shina dariyar yayi😄 yana bude mata fuska yace"ai gaskiya ne"

Misalin goma na safiyar washegarin ranar alh salim da kansa ya sanya aliyu a gaba ya tuqoshi zuwa gidan aminin nasa alhj abbas don kawo sadakinsa,aliyun yayi kyau abinsa cikin shadda gezna dinkin tazarce farace qal sai maiqo take,ya saye idanunsa cikin farin glass wanda bai hanaka tozali

Please Login or Register in order to submit comment