Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bude dukkanin qofofin ya tura daya wadda a samanta aka rubuta da wani dan siririn katako mai kyau *bedroom* ya shige,ta miqe itama a gajiye ta shiga public toilet cikin sa'a ta tadda a kwai heater kunna ta tayi ruwan ya dan yi zafi sannan ta kunna famfo na zafin da na sanyin ta saisaita su yadda zai mata dadin alwala,falon ta dawo saidai bata san ina ne gabas ba don haka ta kintaci inda taji hankalinta ya fi karkata ta tada salla

Minti goma ta kammala magrib da isha'i har ma da shafa'i da wutirinta,batabar kan carfet din ba tana duqunqune cikin hijabinta wanda dama yana cikin jakar hannunta haka al'adarta yake ko ba zata sanya hijabi ba to bata rabo da shi cikin jakar ta,a hankali tana duqunqunen idanunta suka soma mata nauyi da radadin bacci tamkar an watsa mata tsakuyoyi a cikinsu gajiya da bacci suka yi mata tarom dangi suka murqusheta bata san sanda ta bingire da bacci ba agun

Cikin sabon shiri yq fito yana sanye da jibgegiyat rigar sanyi mai gashin dabba daga ciki trouser ne da long sleeve shirt duka baqaqe kansa hular sanyi ce ta gashi mai azabar kyau qafafunsa boot ne mai dan tsawo 👢ya sanyawa hannayensa safofin hannu ya saye idanunsa cikin gilashin nan nasa na ko yaushe👓 cikin hanzari ya fito da niyyar fita don sama musu abinda zasu ci idanunsa ya sauka kanta tsakiyar centre carfet din dake tsakiyar falon ta cure guri guda

Ya san sanyin garin ne ya soma addabarta shi kansa da ya saba zuwa abroad cikin irin wannan yanayin wannan karon sanyin ya dameshi balle ita da bai tsammanin ta yaba zuwa,ya dawo da baya a hankali ya isa ga makunnin na'urar dumama daki ya kunna ta ya sake juyawa ya zuge gami da rufe duk wasu qofofi windows da labulaye dake abude na gidan sannan yasa kansa ya fice hadi da sa key ya kulle gidan

A hankali ya soma bude idanunta tanajin yanayin dakin ya sauya mata,sanyin da ya takura mata dazu da zata kwanta ya ragu sosai da sosai,ta kasa tashi illa idanunta dake bude tayi zuru tana jin yadda cikinta ke qugin yunwa,idan bata manta ba rabonta da abinci tun a nijeria sai drink da take ta sha har acikin jirgi

Wanka a qa'ida take da buqatar yi da ruwa mai zafi don ta samu ragowar gajiyar ko zata sake ta amma rashin ganinsa afalo yasa take tsammatar yana bedroom din,kasa kunnenta tayi sosai bata jo motsin kowa ba don haka ta miqe akasalance,cikin sanda ta tura qofar bedroom din ,babu kowa ciki daki ne babba yalwatacce ba wani tarkace cikinsa cupboard ce sai dressing mirror hadi da dressing chair sai sofa qwaya daya madaidaicin gado ne mai rumfa wanda aka kafashi daga jikin window sai center carfet da center table daga gaban gadon kenan,komai na dakin shima farine kamar dai falon hatta da kalan furniture din zuwa ga bedsheet

Ta sako kanta ciki bayan ta tabbatar babu kowa akwatunansu na saman gadon a ajjiye nashi akwatin ne ta gani a bude kayan sun dan hargitse kadan da alama ya bude ne ya debi wasu abubuwa,gefe ta zauna ta fiddo da duka kayan nasu ta shirya su cikin cupboard,nashi ne auka cinye fiye da rabinta ta tsaya tana kallon yadfa kayan suka tsaru ita kanta sun burgeta ta karkade hannayenta ta rufe qofofin sannan ta shige toilet din bayan ta ciro kaya kala daya da zata sanya

Ta fito daure da towel wanda ya sauko mata qasan gwiwarta yayin da ta yafa qaramin saman kanta tana goge ruwan da ya dan taba mata shi da wanda ya shigar mata kunne,sam bata yi tsammanin ya shigo dakin ba shi din ma haka yana zaune ne kan bedside hannunsa riqe da lemon kwali yana dan zuqa kadan kadan ,gabanta ya fadi sosai don ta tsorata da ganin nasa,da azama ta juya don komawa toilet din garin haka towel din kata ya zame ya fadi qasa kanta zuwa kafafunta suka fito sarari,gashinta ya kwanta luf bisa dan dogon wuyanta zuwa gadon bayanta wanda ruwan da ya tabashi ya sake sashi kwanciya,da sauri ya dauke qwayar idanunsa ita kam ko ta kan towel din bata bi ba ta koma hadi da tura qofar

Ta hudar dan maqulli take leqensa tana gani ya daga lemon maimakon shan ganin dama irin na dazu dai taga ya daga kwalin bai sauke ba saida ya daddake shi tas sannan yayi cilli da kwalin yayi qas da kanshi yafi Minti guda ahaka sannan ya miqe da sauri ya five a dakin,sai da tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri ta sawa qofar key sannan ta shirya cikin doguwar riga mai dogon hannu cotton ce sosai ta yane kanta da mayafi ta duba jakarta don dauko turarenta na shamsul imarat da blue lady

Kaf jakar ta lalube da hannunta ta nemi su sama ko qasa ta rasa,cikin shakku ta zazzage jakar gaba daya babu babu blue lady din babu shamsul imarat din sai wani da ta gani cikin kwalba cikin takaici take kallonsa tasan dai ita ta sayeshi amma ta manta a ina?,ta zumbura baki tana maida kayan da ta zazzage din cikin jakar,ta dauko shi shima zata maida saita shanshana"ba laifi shima qamshinsa"ta fadi haka tana ajjiyeshi a gefanta

Kuyi haquri da aliyyu kudai kuci gaba da bina komai daki daki yake a rayuwa😂😂😂
Na gode🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Mrs muhammad ce 👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:53 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

3⃣1⃣&3⃣2⃣

Ta dade a tsaye tana takaicin rashin sako turaren nata da batayi ba don gaba daya tayi tsammanin ta sako su,taja tsaki yafi a qirga ita ba sanin gari tayi ba hasalima yau ta soma shigowa qasar ko da ta sani din ma ai dole sai dai ta yiwa aliyyu magana wadda ita kuma hakanne bata so,to idan kuwa haka ne bata da zabi illa saka wannan turaren tunda sam bata son zama a rayuwarta ba tare da taji jikinta na tashin qamshi ba haka take qamshi a jininta ya ke,ai shima wannan din turarene,sam fadila ta mance aikinsa tama manta a inda ta sayeshi tunda abun bai gabanta tunda ta wulla shi a jaka ta manta da babinsa

Ta kammala shafawa tana lumshe ido gami da cewa "hmmmm" saboda yadda qamshin nasa ya yi mata dadi sosai,qanshi ne mai sanyi ya karade jikinta da ma dakin gaba daya,ta maida shi cikin jakarta ta rataye jakar a abun rataye jakankuna ta jawo qofar dakin ta dawo falo,yana zaune a gaban laptop dinshi 💻(agogo sarkin aiki😏)cewar fadila cikin zuciyarta,aliyyu hardworking person ne komai yasa a gabansa yakan zama serious akai har sai ya kai ga cimma burinsa,yana jin fitowar tata amma bai daga kai daga abinda yake ba bare ya dubi sashenta

Sannu a hankali qamshin ya soma karade falon ya soma kuma fisgar hankalinsa,ya rasa daga inda qamshin ke fitowa,sannu sannu kasala ta soma rufeshi idanunsa suka soma lumshewa,ya daga kansa ahankali ya dubi sashen da take waya ce a hannunta📱 tana danne dannenta saqonni take dubawa da suka shigo mata,ya maida ido runtse sosai yana qaryata kanshi game da feelings din da yake ji,ya sani tun usul haka halittarsa take yana daga cikin mabuqata,gaba daya ya mance da wannan matter din sanda zai taho aiki ne kawai a gabansa da kuma tsaftar inda zai zauna da abincin da zaici

Cikin lokaci kadan mood dinsa ya canza sosai he needs something really, idanunshi sun jima a rufe aikun da yake ya gagareshi saidai still mood din da yake ciki bai canza ba,ya sake kallonta karo na biyu bata san ma me ake ba har yanzu wayarta na hannunta tana latse latsenta,"take dis bags ki samin nawa a plate ki dauki naki

Juyowa tayi don jin muryar tamkar ba tasa ba,amma sai taga latse latse yake bisa laptop idanunsa na bisa screen din,bata ce komai ba ta ajjiye wayar a gefanta ta debi kayan ta shiga kitchen,shawarma ce da Chinese spaghetti sai roasted chicken ta saka kowanne a aplate din ta hada masa da ruwa da lemo ta jawo dan side table gabansa ta dora masa akai,zuwanta gabansa ya sake sa qamshin ya cika masa hanci,ya sake runtse idonsa hadi da qanqame hannayensa gu guda cikin wani irin lust moode,sam bata lura ba ita dai ta kammala hada masa ta dauki tata ledar ta koma mazauninta,duk yadda ya kai ga son cin abincin haka ya dinga tsakurarsa a kasalance girman kai kuma ya hanashi ya sake koda duban sashen da take

🔅🔅🔅🔅🔅

Ta sake duban agogo karo na uku kenan sha daya da rabi na dare🕦,tuni bacci ya sake cika mata idanu kamar ma batayi shi dazun ba duk da dama ba wani jimawa tayi ba ta farka,tunaninta daya ko ina makwancinta? Tasan dai ko giyar wake ta sha bata tafiya kai tsaye su hada dakin kwana da aliyyu ba bare ya yarfata

kasa daurewa baccin da take ji tayi saboda haka ta ware mayafinta ta lullube kafadarta zuwa qafafunta ta ja filin kujera qwaya daya ta tada kanta da shi tunda shi kam lura aikinsa yake tuquru hadi da amsa kiran dake ta shigo masa wanda dukka da harshen turanci yake maganar hakan ya tabbatar mata yan qasar ne masu kiran,batasan yayi hakanne bane ko zai samu feeling da yake ji ya sake shi shi uasa ya takura kansa da aiki,ba abunda yake sai faman dirkawa cikinsa coffee flask guda ta hada masa amma ya kusa tafiya abun har yaso bata tsoro

Tsaye yayi a kanta baccinta take sosai,bai taba qarewa fuskarta kallo ba irin yau,gashin gaban goshinta ya sake kwanciya kamar relaxer ta shafa masa komai nata medium mai kyau tamkar ma ba baccin take ba,a hankali abun nan da yake son ya danne ya ci gaba da taso masa,ya tabbatar idan yaci gaba da kallin nata a yanayin da yake ciki din nan zai iya aikata abinda yame ganin ita din ta masa kadan ta iya daukarshi gane yake zai iya nakastata,ya janye ida nunsa daga kan fuskarta yana maida numfashi,yasa hannunsa ya zare filon da take kai kanta ya sauka saman kujerar

Firgigit tayi ta farka don ta dan tsorata ya kalli idanunta wadanda bacci da ta soma da tsoratar da tayi yasa su sukai wani kyau ya dauke kansa gefe guda zuciyarsa na dan bugawa da sauri, ganinsa tsaye bisa kanta yasa ta dan sukuyar da kanta "idan kinga dama ki koma bedroom ki kwanta"ya fada yai gaba hannunsa dauke da cup da flask din tea

Ta dauki a qalla minti talatin a zaune tana doubting din aliyyu ne kuwa ma ya tasheta?idan shi din ne ma ya zata iya kwana daki guda da aliyyu? Aliyyun da yaqi jininta? Bai sonta bai qaunarta?,wani benefit nata kawai yake so tayi masa girki da shara ba wai ainihin ita fadilan ba,ganin babu mafita ga wani sanyi da yake sirarowa falin saboda kashe na'urar falon da yayi ya sanyata miqewa jiki a salube ta njfi bedroom din

Kamar wata munafuka ta tura ta shiga,ga mamakinta yana kwance ne aqasa saman dan qaramun carfet din nan na gaba gado mai dauke da center table ya sauke center din shi kuma ya maye gurbinsa,trouser ne kawai ajikinsa da singlet,yayi ruf da ciki,hannun hagunsa da damansa duka pillow ne ya jajjerasu ya kuma matsesu ajikinsa,faffadan bayansa mai cike da siffar qarfi ya bayyana,ta dauke kanta cikin sanda ta zagayeshi gami da hayewa kan gadon tana mamaki cikin ranta shi kam wannn baijin sanyin garin nan ne?

Ga kuma sofa a dakin doguwa amma bazai hau kai ba?bata da courage din da zata magana don haka ta maida gulmarta ciki ta tattara tafukan hannayenta tayi addu'ar bacci ta shafe ilahirin jikinta da ita ta jawk bargon ta rufa tayi matashin kai da hannunta kasancewar duka filon dake kan gadon aliyu ya kwashesu zasu taya shi kwana😜😜

Idanunta fes a kansa tana gain yadda yake ta mutsu mutsu cikin ranta take munafuncin haka yake wai baccinsa ne shi,tun tana kallonsa har bacci ya rufe idanun nata,taso tayi daddan bacci mai tsawo a a lokacin saidai saidai hakan ya gaza samuwa don ta tashi yakai sau nawa saboda rashin sabo duk kuma tashin da zata yin idanunta na kan aliyyu sau uku tana ganinsa yana canza gurin kwanciya ana hudu ne ta ruskeshi yana qiyamul laili tuni ta miqe don ita din ma lokacin tashi yin tata sallar yayi

Aliyyu na bisa darduma yaga tashinta a zatonsa fitsari zata yi sai yaga bayan ta fito ta tayar da sallah shi da zuciyarsa yaje gulmar isha'i ne bata yi ba kota tsammaci asuba ce tayi?,shi kadai ke kida da rawarsa ita kam ta kafu gaban ubangiji,har ta idar idanunsa na kan fejin qur'anin dake hannunsa yana karantawa yana shafin qarshe ne cikin suratu anbiya'i,kusan yare suka sake miqewa suka tada sallar asuba kowa yayi tasa,yana so ya samu falalar jam'i sai dai girman kansa bazai barshi yayi mata tayi ba,bata jima da soma azkar dinta ba bacci ya sureta ko gamawa bata yi ba

🔅🔅🔅🔅🔅

Sanda ta farka ta duba agogon dake ajjiye kan side drawer tayi mamakin yawan baccin da tayi,ta yunqura da niyyar tashi sai ta ganshi shima kwance kan abun sallarsa yana baccinsa cikin nutsuwa da alama shima surarsa yayi bai shirya ba kamar yadda yayi mata,ta dan zubawa kyakkyawar fuskarsa ido wanda da idonsa biyu bata isa ba🙊,fuskatsa tayi mata kyau tayi wani fresh,ta dan girgiza kai ta miqe tsaye ta soma gyara gadona a nutse cikin taka tsantsan don kada ta sheshi sai da ta kammala tayi mopping ta wanke bandaki duk da baiyi komai ba ta sake kintsa falo,ta koma ta buda jakarta ta fiddo da turaren wuta ta jona abun turaren wuta mai amfani da wutar lantarki ta zuba cikin qanqanin lokaci gidan ya dumame da qamshi har ya leqa moqata ma,cikin sanda ta koma dakin gadon tayi saurin shiga wanka tun kafin aliyyu ya farka ta kasa sakewa

Shigar shadda tayi pink dinkin riga da skert ne sun mata cif sun zuna das ajikinta babu inda yayi kwarara kai ka rantse a jikinta aka dinka su,hida lip glosses sai kwalli kawai ta saka ta taje dogo kuma baqin gashinta ta kameshi da ribbon pink,ta ware dankwalinta tayi daurinta na zamani wanda ake sokeshi(ture kaga tsiya)hakan ya bawa jelar gashin nata damar zubowa ta qasan daurin,rigar sanyi ce wadda ko ciki bata rufe ba mai gashi dogon hannu ne da ita ita ta sanya light blue,ita kanta sai da ta juya ta sake kallin kanta duk da ba wani make up tayi ba amma ta zuba kyau

ta dauko turarenta ta shafe lungu da saqo na jikinta,har ga Allah tana jin dadin qamshin turaren yayi mata ta maida shi sannan ta koma kitchen din shirya break

Mrs muhammad ce👑

📚📚📝📝✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:56 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

3⃣3⃣&3⃣4⃣

Tun acikin baccin ya soma jin qamshin na ratsa qofofin hancinsa,duk zuqar numfashi daya da zaiyi yana zuqarsa ne tare da qamshin,qamshin yayi masa,tun yana tsammanin ko amafarki ne har ya soma gasgata cewa a zahiri ne ido biyu ne,sannu a ahankali idanun suka ci gaba da buduwa ya soma zagaye dakin da idanun nasa 👀,ko ina fes sai qamshin turaren wuta ke tashi da na wannan turaren nata da har yanzu ragowar qamshin bai bar dakin ba

Komai na dakin a kintse neat " I like it" ya fada can qasa,hakan yakeso ko da wani lokaci area din da yake rayuwa ta kasance,ya dan miqa hannunsa ya jawo wayoyinsa da ya dora kan center ya duba agogo,lokaci ya gani ya ja sosai din kuwa qarfe goma sha daya agogon china qarfe shida agogon gida nijeria,ya duba call logs nan ya tadda missed call na mr lin,babban dan kasuwa ne dan qasar china saidai sananne ne a qasashen duniya hakanan yana da companies anan gida nijeria sai missed call din andi biyu sai na salima guda biyar da ya biyo baya,duka baiji ba don a silent wayar take mantawa ma yayi bai kasheta ba don baya kwana da waya a bude saida babban dalili

A hanzarce ya miqe ya watsar da fulallukan da yake kai ya nufi toilet,as usual tun a gida a nan ma haka ya tadda ruwan wanka ready cikin bathtub shigewa yayi kawai abinsa,mintina talatin ya kammala wankan a gurguje ya fito ya shirya kansa cikin baqaqen suit harda baqar safar hannu saboda sanyi sunyi matuqar haska farar fatarsa yayi kyau kamar wani bature tabbas aliyyu badai kyau ba

Da hanzarinsa ya wuce kitchen kai tsaye kamar yadda ya zame masa aladarsa shan ruwa cup guda da safe kafin yaci komai,tun daga falon qamshin girki ya marabceshi,hancinsa ya bude sosai yana sheqar qamshin son ransa👃🏻😋,cikin kuzari ya qarasa kitchen din tana tsaye gabn gas tana kwashe chips don shi kadai ya rage mata dama ta kammala,bayanta yake bi da kallo tayi kyau kamar wata 'yartsana don kayan sun mata cif cif ajiki ya bi gashinta da kallo wanda ke reto a bayanta sai ya tsinci kansa cikin birgeshi da hakan yayi don shi kam ma'abocin son gashi ne tun yana qarami,ya dauke idonsa ya maida kan freezer bayan ya budeta yana jawa kansa kunne

Sam bata san da shigowarsa ba qarar rufe freezer din ita ta ankarar da ita,ta dago ta dubeshi yana shirin ficewa ya dan lumshe idanunsa sanda yake qoqarin barin kitchen din saboda feeling da yake ji sosai irin na jiya da ya hanashi sukuni da bacci mai dadi,bata ce komai ba ta biyo bayansa,har ya samu hannun kujera ya zauna numfashinsa na fita da sauri da sauri,cikin hanzari ya balle hancin gorar ruwan ya kai bakinsa ya soma daddaka

Bai ajjiye ba har sai da ya shanye tas ya wurga robar cikin dust bin dake kusa da shi yana maida numfashi bayan ya rufe idanunsa

"Your breakfast is ready"yaji muryarta kusa da shi tana fada,a hankali ya bude idonsa bai ganta ba don tuni ta wuce sai ragowar bayanta da ya gani sanda take qarasa shigewa kitchen,bai sake komai ba illa wucewa dining da yayi don gwada cin abincin

Ta zuba masa komai hatta tea ta hada masa a cup ya sanya cokali yana motsa shi,mamakin kanshi yake yana kuma tambayar kanshi *meke faruwa?* da shi,ta fito daga kitchen hannunta dauke da dan qaramin cup data hada black tea☕ta zauna cikin falon tana kurba a hankali qamshin ne yaci gana da buwayarsa ta hanyar iska dake kado mishi shi

Ya maida hankalinshi kan tea dinsa yana kurba kadan kadan,comfortably yake jin zamansa kan dining din shi daya,ya debi chips da pork ya kai bakinsa yana ci gaba da monitoring movement dinta da idanunsa,"hey" taji yace ta dago da kanta ya dan dago hannunsa ba tare da ya dubeta ba"come here"ya kirata sai taji ban barakwai,ta ajjiye cup din hannun nata a hankali ta qarasa dining din,ya sake kurbar tea din idanunsa na kan ruwan tea din da yake sha "sit" yace da ita,ta ja kujerar gami da kasa kunne tana sauraran mai zaya ce mata

Bai ce komai ba har ya kammala breakfast dinsa,qamshin da yake ji ne ke rudashi ya rasa wanne irin mayen turare take amfani da shi ya zaro tissue daga cikin tissue dice box yana dan goge hannunsa inda ya bacin "as from today kada ki sake kawomin abinci ki bar gun har sai na kammala understand?"(nikam cewa nayi hmmmmm,fadi gaskiyarka na daure.......) "mutum sai shegen mulkin tsiya ba haka nake masa ba a nijeria wani lokacin bai taba cewa don me ba sai yanzu?wato zai fara fidda sabon salo don yaga ba'a gida muke ba"cewar fadila ita da zuciyarta,a fili kuwa gyada kai tayikata na a qasa "hey" ya sake cewa ta dago ta dubesa ta sake sadda kai "open ur mouth u r not a bruise" to tace masa cikin qosawa da zaman

Har ya ja kujerarsa baya yana niyyar tashi don ya tabbata ya sake qara wasu mintina a gaba bai bar gun ba tabbas bazai iya mallakar kansa ba,abunda yake ji a cikin gangar jikinsa is very strong feeling,yana so yace ta daina amfani da perfume nata amma girman kai ya hana, yana ganin idan ya fadi mata zatayi tsammani ya damu ne da wani abu nata,he feel he can sustain whatever zaici gaba da ji,wayarsa da ta soma kadawa cikin tattausan ringing ita ta dakatar da shi daga tashin da yayi niyya

Mrs muhammad ce 👑

📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻
[10/16, 1:57 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

3⃣5⃣&3⃣6⃣

Ya ciro wayar ya duba mai kiran ya dan saki ajiyar zuciya kadan sannan yayi pressing ok,sunan da taji ya ambata ya sata gane da wadda ya ke wayar,salima ce,hira take yi masa sosai yana dan biye mata,hirar da tasa fadila kasa jure zaman gurin ,satar kallonsa take ta qasan ido gaba daya launin idanunsa sun canza muryarsa ta sake zama so cool

Idanunsa na kan fadila lokacin da ta miqe don basu guri don zuciyarta ta samu salama daga mugun kishin dake taso mata,ya dan daki table din da hannunsa wanda yasa fadila daje shirin sauka juyowa suka hada ido da shi,fararen idanun nan nasa da sukayi returning zuwa ja ya lumshe su sannan yayi mata alama ta koma ta zauna,kamar ta zura da gudu tabar gurin haka taji saidai ba yadda ta iya ta koma din

Minti biyu tsakani yayi sallama hadi da kissing wayar sau uku,lumshe nata idanun tayi tanajin wata dalmar kishi na digar mata cikin zuciyarta,bata bari shaidan ya kitsa mata komai ba ta soma karanta *hasbunallahu wani'imal wakil*,wani gumi ta gani yana tsatstsafo masa ya maida jikinsa ya jingina sosai da makarin kujerar idanunsa a rufe wani weakness yake ji sosai cikin jikinsa

ya dauki aqalla minti goma sha biyar a haka kafin mood dinsa ya dan saisaita ya dinga sakin 'yar qaramar ajiyar zuciya a jajjere,har a lokacin fadila na satar kallonsa tana mamakin meke damunsa haka mood dinshi yayi bala'in canzawa within few minutes,ya sauke doguwar ajiyar zuciya lokacin da yake bude idanun sa,caraf ya kamata tana kallonsa sai yayi wani kicin kicin da rai yana ganin kamar tasan meke damun sa,sunkuyar da kai tayi shi kuma ya zark handkerchief ya share ragowar zufar fuskarsa

Sauka yayi a ahankali daga dining area din ya shige bedroom,tana zaune a gun ya sake fitowa wannan karon yellow and coffe din suit ne ajikinsa da alama kaya ya canza koma wanka yayi ne oho wa yasan masa😜😜😜,hannunsa riqe da brief case yana amsa wayar mr lien a hanzarce yake tafiya ya sanya hannu ya bude pocket din sa ya zaro yuan dari ya ajjiye mata(five thousand kudin naija) kana ya dago suka sake hada ido dukkaninsu sunji jiki ita ta sunkui da kai shi kuma ya fice a hanzarce,ta kalli kudin ta tabe baki "ne me zanyu da kudin qasarsu?tabdijan" ta fada a fili amma qasa qasa kamar mai gunguni

Yana fita lukas da andi na qofar gida cikin motar kamfaninsa da yake shirye shiryen budeshin *maitama group of companies* haka yake kowa yasan da su,da fitowarsa suka sara masa kamar wani soja sukayi handshake kamar yadda yake a al'adar sa don dabbaqa value ba addininsa a ko ina yake,lukas ya bude masa qofar zungureriyar motar ya shiga suka rufa masa baya

Driver din ya bawa umarnin yabi ta lujing road huangtian street zasu fara shiga yueyang hotel yana son ganin ramzan dan india ne wanda yana daya daga cikin wadanda ya bawa contract na ginin factory din nasa,factory ne babba na qashin kan aliyyu wanda ya narkar da maqudan kudade gurin samar da shi,factory ne da zai dinga manufacturing kayan babies blouses na maza da mata

Wunin ranar cikin zirga zirga mai yawa yayi ta ahiga can fita nan,hakan ya taimaka masa sosai gurin rage masa abinda yake ji cikin jikinsa,yayin da a daya bangaren fadila ta wuni kwanciya sai bayan ta idar da sallar la'asar sannan ta shiga kitchen,pepe chicken couse couse da miyar qwai sai mutuminta lemon kwakwa da ya wadatu da madara da flavour wannan shine jadawalin abincinta na dare

Nan da nan ta gama kasancewar gas din nata mai hudu ne,ta turare gidan nata da turaren wutanta bayan ta zuge duk wani glass da window dake gidan,sai gidan yayi wani dumi mai dadi daya gauraye da qamshi,cikin ruwa mai zafi sosai tayi wanka saboda sanyin dake damunta na garin,riga da wando tayi shirya kanta ciki wandon dogone har qas pencil rigar kuma da kadan ta rufe cikinta jacket ta saka mai kauri

Please Login or Register in order to submit comment