Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da farar qwayar idanunsa,takalminsa baqi ne na kamfanin batozi sai baqar hula duk da bai sanya ta ba tana riqe ne ahannunsa,kana nazaratar fuskarsa zaka karanci damuwa a tattatare da shi,sam alh salim bai bi ta kansa ba don yasan kwanan zancan,ya sani cewa gata ne yake son ya yiwa aliyun wanda ko bayan ransa zaiji dadinsa.
A nutse yake murza sitiyarin motar har suka iso cikin gidan,alhj abbas da kansa ya fito yayi ma abokin nasa iso zuwa cikin gidan bayan sun gaisa da Aliyu suka barshi cikin motar,ya dan kwantar da kujerar motar yayi rigingine yana kallon yanayin ginin gidan,
Alhj salim ya fiddo da daurin bandir na dari biuar biyar rafa daya ya ajjiye a gaban alhj abbas yace "ga sadakin aliyu ga 'yata fadila"alhj abbas yace "amma ai a yimin kara ko ni na biya ai"alhj salim yace"ni da kai ai duka dayane babu komai wlh"alhj abbas yace"Allah to ya yiwa auren albarka yasa ya zamo farinciki a gurimmu da gun yaran gaba daya""ameen"ya amsa masa"auren zai kama nan da sati shida dai dai lokacin da zasu kammala attachment dinsu"alhj salim yace"anya ba'ayi gaggawa ba?""wani irin gaggawa kuma me zasu zauna su yimin agidan ?"to shikenan abbas Allah yasa ayi a sa'a""amin dama ban sanar da yarinyar ba niyyata dama yau ta sani amma munyi zancan da mahaifiyarta,to tunda ga sadakinta ga kuma mijin sai a kirata tasan komai""to ba laifi"inji alh salim
Tana ysaka da baccinta😴 taji ana dukan saman qafafunta,ta daga kanta idanunta cime da bacci tana kallon muhammad da ya tashetan cikin jin haushin tashin nata da yayi tace masa"meye?,ba nasha gaya maka idan ina bacci ka daina damuna ba"ya hade hannayansa 🙏🏻yace"am sorry anty,abba ne ke kiranki""abba kuma?😳"ta ta tambayeshi cike da tsoro saboda ta tuna agender su,ya gyada mata kai cike da tabbatarwa,tace jeka ina zuwa"tuni ragowar baccin da take ji ya gudu daga idanunta,ta dirgo daga gadon ta shige toilet ta wanke fuskarta tayi brush sannan ta dawo cikin dakin ta daura zani kan rigar baccin ta ta fesa turare sannan ta zira zumbulelen hijabinta mai hannu,a falo taci karo da umminta tana saka turaren wuta,ta gaidata sannan fuskarta kamar mai shirin rushewa da kuka😟 tace"ummi wai abba ke kirana"ta kalleta tace"to kije mana na ganshi da alhj salim"gabanta ya qara faduwa ta juya ta bar falon
A salube tayi sallama a sitting room din,dukkansu suka amsa mata,ta samu gefan kujera ta gaida uncle abba(hka suke ce masa)kasancewar sun gaisa da abbanta tunda asuba,uncle abba ya amsa yana mai qara nazaratar nutsuwa da ladabinta,abbanta ya kalleta yace"fadila ina son ki bani aron nutsuwa da hankalinki "tace"to abba😔""kin sani cewa shekarunki sun isa ace kina dakin mijinki tunda an aurar ma da wadanda basu kaiku shekaru ba,sannan na baki dama ki fito da wanda kikeso kamar yadda qanwarki ta fiti da shi amma har yanzu baki cemin komai ba,na qyaleki har lokacin da nabaki ya qare ban tanka miki ba duk da cewa ina da iko in zaba muku miji amma na baki damarki "ta gayada kai "hakane abba yace"fadila"ta amsa "na'am""abbanki ya nemawa yayanki aurenki kuma na bashi"wata mummunar faduwar gaba ce ta risketa tamakar an daddaure jijiyoyin jikinta taji,hakan yasa ta kasa dago idanunta ta kalli kowa bare su fahimcin halin da ta shiga,ya dora da cewa "yanzu haka ga sadakinki a hannuna"jin hakan yasa ta qarasa rikicewa sauran dauriyarta tuni tayi qaura,addu'o'i ne barakatai suka dinga zuwa bakinta tanayinsu cikin zuciyarta,shikenan na rasa aliyuna?shikenan zuciyata ta rasa muradinta?shikenan mafarkina ya zama hasashe?,abinda take jujjuyawa kenan kawai a zuciyarta,duk maganganun abba ba wanda ta ji ko ta fahimta sai maganarsa ta qarshe wadda sauran qiris ta sa numfashinta ya dauke"kije kuga juna yana falon waje duk da shekarun baya kun sanshi amma saboda tsawon shekarun zaki iya mantashi ya kwana biyu baya qasar"uncle abba ne yayi saurin cewa"a'a saurara✋🏻ina da magana ke fadila gayamin gaskiya idan bakiso kina da wanda kike so"tabbasa da zata iya da ta fayyace musu sirrin dake zuciyarta ko zasu tausaya mata su bar zuciyarta taji ma da masifar da take ciki,amma ko kusa batajin zata iya kunyata abbanta,bayan ya isa da ita yana da iko da ita fiye da yadda take da iko da kanta yayi mata komai a rayuwa ya bata dama masu yawa a rayuwa irin wadda kowane mutum ke son samu,duk ma a ture wannan gefe baza iya daga iso ta budi bakinta tace da aminin mahaifinta wanda yake tamkar uba a gareta cewa batason dansa jininsa ba,hakan yasa tayi saurin girgiza kai tace"ko daya abba na gode da zabin da kukayimin,Allah ya saka muku da alkhairi"ita kanta ta jinjinawa kanta kan namijin qoqarin da tayi na furta haka,uncle abba har zuciyarsa yaji dafi matuqa tare da sake gode ma allah da zata zamo daya dqga cikin ahalin gidansa,albarka suka sa mata sannan abbanta ya umarceta taje su gana
Takai kusan minti biyar a qofar sitting room din ta kasa shiga,gaba daya a rude take zuciyarta a cunkushe take,daga qarshe taga tsayuwar batada wani amfani don haka ta tattaro dukka nutsuwarta da dauriyarta ta kutsa kai hade da sallama kanta a qasa😔 ta lalubi kujera daya ta zauna cikin fargabar wa zata daga kai ta gani,muryar da taji ta masa mata ita ta razanata da sauri ta dago kai ta gani ahin da gaske ne ko kunnuwanta da zuciyarta ke yaudararta yadda suka saba?idanunsu suka hadu da juna👀 wanda hakan ya tabbatar mata da tsammaninta,ba qaramar razana tayi ba duk da bata nuna hakan ba,A.s mai tama Aliyyun uncle Abba?,take ta jera sunayan a zuciyarta,komai tsaya mata cak yayi,tunaninta ya kasa gaba ya kasa baya,shiru daki ya dauka ba wanda ya tankawa dan uwansa wanda hakan ya sanya fargabarta daduwa,bata kuma sake kallonsa ba bare taga a wane irin yanayi yake ciki ba,sun jima a haka sannan ta jiyo alamar miqewarsa,har ya kai bakin qofa yayi taku uku ya dawo da baya,kallon nan nasa da ta fari gani a qwayar idonsa ta kuma tsaneshi shi yayi mata sama da qasa sannan yace cikin izza da qasaita"ban iya qarya ba kuma bazan fara taba saboda ke,bazan iya tafiya ban amayar da binda nake ji cikin zuciyata ba,bakimin ba baki dace dani ba,baki ma dace da tsarin rayuwata ba,ke da kanki shaidace ce idan dq zaki iyq yiwa kanki adalci bamu dace da juna ba,baki ma da zubi da tsarin da nake so gun mace,idan banda tsaurin ido ma irin naki taya zaki hada kanki da ni?kinga nayi kala da ke?gaskiya kin cuceni,god forbid ki zama matata,kada kuma ki soma yaudarar kanki ta hanyar zato ko tsammanin nan gaba zan iya sonki harki cuci kanki ki aure ni,wannan maganan daga cikin zuciyata direct take fitowa 
Wani mugun takaici da baqinciki ne lokaci guda ya rufeta,tunda take babu wani da namiji da ya taba mata munanan furuci makamanta wannan,ta tuna uawan samarin da ke kara kaina a kanta,samari masu ji da kudi kyau nasaba isa da qasaita,ba wanda ta bawa dama a cikin su,wasunsu dama suke so ta basu koda ta friendship ne amma basu samu ba,samari da dama sun sha kuka a gabanta kan ta mallaka musu zuciyarta,amma yau wani daya daga cikin jinsin maza ke gaya mata wadannan kalaman,ji take a rqntq matuqar ta barshi ya tafi haka ba ta da ta mayar masa da martani ba wanda zai dade yana cizon zuciyarsa ba to ba shakka tayi faduwar baqar tasa"hey🙋🏻"tace da shi sanda ya sanya kai zai gice daga falon,ta miqe tsaye ta yi masa kallon sama da qasa ta yatsina fuska😏 ta tofar yawu a gefanta sannan tace"see you wane mashahurin maqaryacin ne ya gaya maka ina maraba da kai da zaka zo kanata soki burutsu,ni dinma ba yimin kayi ba don baka wuce dan aiken gidana ba a tsarina,amma ni nasan darajar dan adam banga a gidammu ana tozartashi ba kuma na iya darajatta zancan magabata na shi yasa ban tozarta mutumin da mahaifina ya zabamin ba,idan banda qaddar ina budurwa sabuwa dal a leda mai zanyi da bazawari ragowar wata..........
Wata iriyar wafta ya kawowa bakinta wanda ta tabbatr da ya sameta sai lebunanta sun fashe,da gudu ta bude daya qofar falon da zata kaita cikin gida ta baya ta shige ta bankowa aliyu qofar ta batshi tsaye zuciyarsa kamar zata fito saboda fushi,ya ga alamar akwai rainin wayo tattare da yarinyar,yayi qwafa cike da zafin zuciya ya fice,kai tsaye daķinta ta nufa ta kulle qofarta gam tayi zaman dirshan saman carpet dinta,wani irin kuka ta saki😭tayi qasa da kanta😪,ta rasa me zayayi farinciki ne ya kamaceta ko baqinciki?ta jima a zaune tana kukan tate da tambyat kanta da kanta shin dama baqinciki da farinciki na haduwa lokaći guda cikin zuciyar bil'adama?yau kam ta fahimci hakan na faruwa tunda gashi yau ta tsinci kanta a ciki
Aliyyunta mafarkinta na kullum?burin zuciyarta muradinta yau shine zai zama mijin aurenta babban burinta kenan dama anan duniya,sai dai kash yazo mata ta wata iriyar fuska da sigar da bata tsammatar mata ba,baya sonta baya qaunarta abin har ya kai tsananin da bazai iya boye qinta a zuciyarsa ba harsai da ya tsaya a gabanta ya fesar mata,baya ga haka ba ita kafaice zata zama mallàkinsa ba?zata yi sharing aliyunta da wata?ga ahi har waya ma ta rigata samunshi(maman iftihal)
Da qyar ta iya janye jikinta ta gada saman gadonta,ba abinda ke mata amsa kuwwa akunnenta irin kalaman aliyu,kafin azahar zazzafan zazzabi ya rufeta,sau biyu farida na shigowa dubata tana ganinta a duqunqune tayi tsammanin bacci take,a shigowarta ta uku ne tace"kai yaya fadila wani irin bacci ne haka tun ten o'clock har one thirty?"tasa hannayenta ta janye bargon tana fafin"ba sanyi ake ba ba komai ba kuma kin.......
maganar ta maqale mata sanda idonta yakai kan fadila ta zaro ido😳 tana cewa"kinga idonki kuwa?"ta juyar da idonta daya side din sannan tace"kaina ke ciwo"

Mrs muhammad bello

✍🏻✍🏻✍🏻📝📝📝


[10/16, 2:39 PM] ‪+234 706 914 1005‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Wa yasan gobe?

Safiyya Abdullahi musa huguma

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶7⃣

Fadila ta juyar da kanta daya barin tace"kaina ke min ciwo"farida ta gefanta ta zauna tace"kinyi dai kuka wanda ya haddasa miki ciwon kai,sis ni 'yar uwarki ce,bai kamata ki dinga boyemin wasu abubuwa da ya kamata ace na sansu ba,yadda nima bana boye miki komai bana boye miki damuwata nake neman shawar warinki akan komai,ko dan tsokanarki da nake ne yasa kikemin kallon am too young?,komai ai da tym dinsa,amma idan kina ganin na takuraki am sorry sister"ta fada tana shirin tashi,sai ta bawa fadila tausayi,farida na sonta sosai,tana damuwa da damuwarta any time,ta riqo hannunta tace"is not lyk dat sister baki takurani ba,I will tell yuh everything,but b4 den bani paracetamol nasha,and kimin alqawarin daga ni sai ke babu maijin wannan sai wanda na amincewa hakan"ta gyada kai tace "I promise sister"
To fadila dai sauqi bai samu ba har sai data kwana biyu a kwance tana jinyar jiki da zuciyarta sannan ta samu qwarin jikinta da taimakon farida ta hanyar bata shawarwari da kwantar mata da hankali,ba abinda ke sake daga mata hankali irin lafuzan da suka fito daga bakin abinda tafi so a duniyarta har yau sunqi bacewa daga dodon kunnenta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Yammacin talata ne wanda ya zamto dukkaninsu suna da abinda za suyi cikin makaranta don haka suka tafi a amota daya suka kuma dawo tare kasancewar lokaci guda kowacce ta gama uzirin da ya kaita,tare sukayi sallama suka shigo suka tadda umminsu a falo ita da muhammad dake gefanta yana ta kumbure kumbure,ta musu sannu da dawowa suma suka mata sannu da gida sannan suka haura samansu kowacce ta nufi dakinta don watsa ruwa,farida ta riga fadila kammalawa har ta sauko ta shiga kitchen ta ciko plate da couscous da vegetable soup wadda ta wadata da hanta,fadila ta sauko sanye da pakistan riga da wando irin shigar farida kenan saidai bambancin colour na fadila dark pink ne na farida kuma light blue
Itama kujera ta samu dake kusa da ummin ta zauna,ta dubin sashen da muhammad yake wanda tunda suka dawo ya musu sannu da zuwa bai qara cewa qala ba tace"ummi halan yau akwai abinda ke damun parrot dinki naji yau gidan so silent gwanin dadi ba hayaniya"ummi tace"rabu dashi,haka kawai yazo ya tarar dani ina kallon labarai shi wai dole sai ba canza masa tasha zai kalli qwallo"farida ta kalleshi"meye amfanin t.v din dakinsa"ummi tace"duk yabi ya lalata socket din dake dakinsa wai shi koyon gyara an canza masa wasu ya sake kuncesu to ba sai yaje yayi ta yi ba nidai ba mai takurani ni da falona idan mutum yaji haushi ya tashi ya bani guri"ta fadi hakane don dama ya isheta ta koreahi tun dazun yaqi tafiya,ai kuwa ya tashi ya bar fallon yana shirin sa kuka,fadila ta gimtse dariyar dake son qwace mata don tsakanin ummin da muhammad ba'a shiga tasan kuma nan da anjima shi zata lallabo tace yayi mata tausa,fadila tace"ummi mun hadu da haj barira fa?"ta juyo ta dubeta tace "a'ina?,dama tana gari ne uwar tafiye tafiye?"farida da takai lomar abinci bakinta ta karbi zancan"a danja ummi,danja ta tsayar da mu sai da tasa mukayi parking gefan titi,farida ta qyalqyale da dariya😂 tace"kai matarnan ummi Allah ya zuba mata surutu"ummi ta mata daquwa tace"ungo wannan mamarku ce,da Allah yayi ma ke farida ai da tuni ta zama surukarki"farida ta sake kecewa da dariya😂ta kama haba tace🤔"Allah ya tsare,wai shi abdus-samad ma idan banda abunsa ummi qawata fa rumana yace yqna so amma don ya raina ni yaje ya cewa hajiya ni yakeso,ni bansan ma inda tasan labarin bikimmu ba take tambayata nace mata saura three weeks,ai kauwa har zancan abdus-samad din.ma tayimin wai na dai qishi"ummi tace"ato kunya ma ta isheki"
Ummi ta juya ta dubi fadila wadda ta zubawa t.v🖥 ido tayi shiru tana sauraransu ,duk da fadila miskila ce amma ta sake zama so quiet fiye da da,ga wani rama da take dan kumarin da a da take dashi yanzu ya zabge babu shi duk a cikin kwanakin ummin na ankare da ita,abun ya dameta sosai har take sanar da abbansu,ya kwantar mata da hankali ta hanyar cewa"kada ta damu ai dama yawancin 'yammata idam aurensu ya taso gadan gadan hakan na faruwa sai tace amma ai bata ga hakan a gun farida ba yace mata ai kowa da irinshi wani ma qiba yake yi maimakon rama,ummi ta yanke tunaninta tacewa fadila"ki shiga kitchen ki sami abinci ki ci"ta dan noqe kafada "ummi sai anjima"ta bata rai😠 tace"wani anjiman kuma?,kinga tashi ki debo abinci kici tun kafin ranki ya baci"tasan ummi ba wasa don haka a kasalance ta miqe ta nufi kitchen ummi tace mata"ki taho min da kunun aya"
Taliya ta zuba da miyar kifi(haka umminsu take gwanar girki shi yasa da wuya kaje gidan ka tadda abinci kala daya a kitchen dinta takanyi kamar kala biyu dai dai yadda zasu iya cinyeshi)kusan sili dai dai fadila ke zara tana ci ummin na kallonta tayi banza da ita,yayin da farida ke mata kallon tausayi😒,
Wayar ummi ta soma ruri alamun ana kiranta tasa hannu ta qmsa hadi da yin sallama,"haj maimuna lpy lau........lpy qalau wlh........ah mun gode Allah"fadila dake gefe gabanta ta fadi ta tabbatar kiran daga mahaifiyar Aliyu ne ,ko yaya ta ji wani abu da ya danganci gidansun sai ta shiga fargaba,tana tsoron mai zai biyo baya ne a nan gaba?.
Tsinto.muryar ummi tayi tana cewa"yanzu da nufinki haj sai dai naji a gari?ai Aliyu dana ne don zai auri fadila sai na kasa zuwa rakiyar lefansa gidan wasu?ita fadilan ba'a zuwa kaiwa za'a zo kawo nata
Wata mummunar faduwar gaba ce ta shigeta,lallai ya tabbata Aliyu nasu ne ita da wata,ji tayi wani daci ya mamaye mata halshenta abincin ya qarasa ficewa a aranta don haka ta zame ta shige kitchen ta maida shi cikin cooler ta rufe,taja plastic din kujerar dake kitchen din wadda sukan ajjiye saboda zaman aiki ta zauna a kai,daganan din tana iya jiyo muryar ummin nata na mata sallama tana cewa"Allah ya kaimu goben,Allah ya nuna ma..........bata qarasa ji ba tayi saurin saka hannunta ta toshe kunnenta qwalla nabin fuskarta😢
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari gaba daya jikinta a mace yake murus ta kasa fita ko ina tana kwance a daki komai ya cakude mata,har la'asar tayi ummi ta shirya tacewa farida itama ta shirya ta kaita tana jiyo farida na mitar ita fai bazata ba ummi idris kawai ya kaiki,"kinci uwaki ja'irar yarinya to naqi idris din ya kaini ke zaki kaini idan kuma ba zaki ba bani maqullan ni nayi driving din da kaina",haka farida ta shirya babu son ranta suka fita sukabar fadila ita daya a gidan,fitarsu sai taji kamar an qara mata kasalar,kimanin awa guda da tafiyar tasu tajiyo sallama daga bakin falon qasa,ta miqe ta yafa mayafinta ta fito bakin verandar saman benan sani mai gadinsu ne yace"uwar dakina yallabai ne yazo"gabanta yadan fadi saboda wanda zuciyarta ke raya mata shine"wanne yallabai?"ta tambayi malam sani ya saki dariya😃 yace"yallabai Aliyu jan zaki"tayi jim kamar tace baxata ba,sai kuma ta tuna da maganganun da Abbanta yayi mata daran shekaran jiya ta juya ciki tana cewa"kace ya jirani ganinan zuwa"bata wani jima da yin wanka ba don haka body spray ta fesa ta dauki hijabinta ta sanya ta zura slippers din wankanta ta fito,yana cikin sitting room din bakin get,ya dan kashingide akan kujera three sitter waya yake da alamu kuma yana jin dadin wayar don har wani lumshe idanunsa yake,bata ce uffan va ta samu gu ta zauna zamanta da minti biyar ta fuskanci da wadda yake wayar jin zancan wadanda suka tafi kai.lefe da yayi,ya doshi kusa minti ashirin yana wayatsa ba abinda ya shalleshi kamar shi kadai ne a dakin sanann ta jisu suna sallama da juna cike da tsantsar soyayya,wata allurar kishi ce ta soketa ta kauda kanta gefe tayi kamar batasan budurin da yake ba,
Bayan ya kashe wayar sai shiru ya baqunci dakin,bakajin motsin komai sai qarar a.c "ke"taji yace,banza ta masa kamar ba da ita yake ba taqi ko da kallon sashinsa,taji ya sake cewa"da ke nake"ta dago ta watsa masa wanu kallo na baka isa ba,bata mai da kanta ba taji yace"baki isa na roqeki ba amma ina baki shawara da umarni kije kice bakya sona,idan ta kama ma zance miki please ko dan nima ki barni in samu peace of mind da wanda nake son aura"sai taji zuciyarta ta karye gaba daya tausayin kanta sai ya kamata lokaci guda,tabbas aliyu baya qaunarta ko qanqani,batasan sanda hawaye ya subuce mata ba,ta sake tabbatarwa da kanta so bala'ine kuma masifane,haqiqa tana cikin jarrabawa mai girma,musamman irin wannan son na SON MASO WANI,sai taji bata da wani zabi da ya wuce ta tashi ta bashi guri,ta miqe tsam ta fice tana lalauben hanya,tabbas ba shakka yau da ita ta zabawa kanta Aliyu ta tabbatar da a yau ta rabu da shi koda sonsa ai zama ajalinta,da kuna zata iya duban mahaifinta ta roqeshi ya janye maganar aurensu da Aliyu da tayi hakan
ta jima tana kuka a dakinta sanann daga baya tabi ahawarar da zuciyarta ke bata na ta nemi matemaki mana a cikin lamarinta?,ta wanke fuskarta ta shafa hoda ta zizara kwalliya a idanunta donbta rage musu kodewar da sukayi,after dress ta zira ta dauki key din motarta,tana saukowa taci karo ba daqar leda a falon,bata bi ta kanta ba ta fice,tana bude motar ta ta dannawa mlm sani horn akan ya bude mata qofa sai da tazo saitinsa sannan ta tambayeshi wa ya shigo falo da kaya?"nine yallabai ne yace a kawo miki,inata sallama ma naji ba'a amsa ba sai.........,ta daga masa hannu kawai ta fice
Cikin minrina qalilan ta isa gidan ya ahmad saboda gudun da ta tsula anti hafiza na falo ita da biyunta taganta tamakar wadda aka jeho ta zube a kujerar falon tana haki sai kuma qwalla ta fara sintiri a fuskarta,kallo daya anty hafizan tayi mata ta tabbatar ba lafiya ba ta cire yan biyu da suka zube jikin fadilan sunata murnar ganinta ba tare da lura da halin da take ciki ba,ta kiu ra maqociyarta zainab tace ta turo 'yar aikinta ta wuce dasu gidanta tayi baqi
Kusa da ita anty hafizan ta zauna ta kamo hannayentabta riqe sannan tace"lpy me ya faru haka?"fadika ta sake fashewa da kuka tana cewa"na shiga uku anty,innalillah,anty zuciyata bata yimin adalci ba ta jefana cikin mawuyacin hali,anty ki taimakamin,me yasa zuciyata ta yimin hka anty?why?why?,
Anty hafiza ta dafa kanta tana shafawa tana cewa"calm down ki nutsu ki gayamin meke faruwa?"
Tasa bayan hannunta tana share hawayen dake kwararo mata sannan ta saki ajiyar zuciya tace"anty tun kafin na San shi waye zuciyata ta dade da kamuwa da matsananciyar soyayyarsa💘,tun daga lkcn na rasa sukuni a zuciyata kwata kwata,kullum kwanan duniya qaunarsa na qara ninkuwa ne a zuciyata kamar jaraba abun,ina cikin wannan haline muka fara face to face da shi saidai abu na farko da ya fara shiga tsakaninmu fada ne,hakan ya zamana har zuwa lkcn da mahaifin Aliyu salim maitama ya nema masa arena gun abbammu ba tare da nasan shine ba,na shiga matsananciyar damuwa😣 a lokacin da ta bayyana an bada arena ga wani,sai dai sanda nayi tozali da aliyu a matsayin wanda aka bawa ni sai farinciki😊 ya mamaye damuwata
Sai dai kuma me?anty ga tarin mamaki na sai kalaman qiyayya suka zamo kalaman farko da na fara samu daga masoyina,kalaman da suka kusa tarwatsa zuciyata💔,qarara aliyu ya nunamin bai qaunata ba nice choice dinsa ba samirah ce muradinsa,meye aibuna naty?wane naqasu nake da ahi wanda ya janyo aliyu ya tsaneni?ban can can ci so bane daga gurinsa bane anty?
Aliyu yana sonki zai kuma soki fafila"ta fada tana girgiza kafadarta,kukanta ya tsaya cak sai hawaye dake shatata ta ski baki tana kallon anty hafizan da itama ido ta zuba ma ta tashiga girgiza kai tana cewa"bazai soni ba naty baya kuma sona din ya fada anty da bakinsa fa yace"kada nasan ran wata ran zai soni"anty hafiza tayi saurin tarar numfashinta tace"✋🏻ke da'alla can rabu da shi shike da kansa?WA YASAN GOBE?ai sai allah"ta karyar da kai cike da neman agaji da mafita😧"amma anty haka zamu rayu da shi?rayuwar aurece naty wadda ba yau ko gobe za'a yita a watse ba"
anty hafiza tayi murmushi😊 tace"ki kwantar da hankalinki,abu na farko da nake so gareki shine ki miqawa allah lamuranki babu abinda ya gagari allah,abu na biyu ki zamo mai juriya haquri gami da kawaici ki zamo mai controlling din anger dinki ,ni kuma insha 'allah nayi alqawatin doraki akan step na gaba,nayi alqawarin baki shawarwari na gari harsai inda burinki ya gama cika
Cikin hikima da dabara ta zauna tana bude mata babi babi na hikima da dabarun zaman tare gamida kwantar mata da hankali har fadila ta ji nutsuwa ta shigeta tace ni anty abinda ke dada tayr min da hankalin ganin yadda nake jin zallar soyayyarsa a zuciyata to shi haka yake jin zallar qiyayyata"tave cool down sister na gaya miki kada ki damu irin wananna ita take fa juyewa wata rana ta zama zazzafar soyayya ke dai ki dinga yiwa soyayyar tasa linzami kada ki bari ya fuskanci akwaita a ranki don kada ya samu jin dadi da sakewa na wulaqantaki harsai lokacin bayyanatan ya yi
Daf da sallar magariba yaya ahmad ya dawo bayan sun gaisa yake zolayarta"lpy kuwa amarya nàga tana ta qarewa haka?"tayi murmushin yaqe tace lpy lau yaya"anty hafiźa tayi saurin tare tambayar ta hanyar cewa"abban twince aì kasan fama haka na faruwa ga mutum idan aurensa yazo"ya girgiza kai xikin gamsuwa da bayaninta yace"hakane aure yaqin mata,Allah yasa ayi a sa'a"anty hafiza ta masa amin
Bayan isha'i tayi haramar tafiya bayan anty hafiza ta tsareta dole ta sata cin abinci ,antyn ta rakota bakin mota tana sake kwantar mata da hankali fadilan ta dubeta tace"anty unason don Allah ya zama sirei wannan zancan""haba fàfila kada ki damu dake da aysha daya nake daukarku(qanwarta ce aysha)fadila tace anty na gode
Tana driving tunani ne fal cikin ranta duk da tana jin ta samu relief sosai cikin ranta,ita kanta mamakin kanta takeyi tasha jin yadda mata 'yan uwanta ke yaba kyau da ajinta👰🏻 bare maza wadanda ita kanta batasan adadin masoyanta na dili da na bòue ba wadanda ke jatumtar sanar da ita da wadanda take musu kwarjini suke batin abuna zuciyarsu,wadanda ke kuka akanta bazata.iya tuna yawansu ba don ita dama Allah bai

Please Login or Register in order to submit comment