Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su shi dai duk qarshen wata zai miki haka,hakanan zai kawo kudi masu kauri ya baki bayan wanda kullum zai baki koda ba ranar girkinki bace )baiji komai ba kasancewarsa mai hannun kyauta ne koda ba ga iyalinsa ba,amma ya lura barnar ta soma yawa don haka ya sake waiwayawa ga samira yace"uhm....am waiting for d answer

Ta yatsina fuska tace" kasan ni maca ce mai jama'a 'yar dangi kuma duka dangina anan garin suke ba baquwar haure ka auro ba wannan ya shiga ne wannan ya fita"salima tasan da ita take kasancewar iyayenta da danginta ba a garin suke ba a hannun qanwar mamanta take anan kanon amma ba yan garin bane,cikin hasala tace "da uban wa kike?"kamar dama jira samiran kuwa take tace da ubanki nake👉,kinji na kasa da ke ne bare ki dauka banza kawai😙 mtswee!"ai kuwa salima tayo kukan kura tayi kan samira da niyyar shaqota dama da qullin samiran a ranta

Wata gigitacciyar tsawa ali ya daka musu wadda hatta fadila dake gefe sai da ta miqe tsaye saboda razana bare su salima da suka koma sukayi zamqn dirshan ba tare da sun shirya ba,ran 'yan maza ya baci fa zuciyarsa ta tabu take idanunsa suka kada

Cikin tsananin bacin rai ya kallesu "wadanne irin mahaukata ne da baku da burin da ya wuce kuyi kokawa?"salima da ta shaqa da yawa ta nuna kanta👆🏼 tana cewa aliyyu nice mahaukaciya?" Ya dora da cewa "kun
wuce hakanne?bai sauraresu ba ya murza yatsunsa suka ce das das das ya nuna su👉� sannan yace dis is d last worning kunyi na farko kuma kunyi na qarshe dambe a agabana.....☝🏼bazan dauka ba don ni ba shasha sha bane" salima da idonta ya ciko da qwalla😢 tace"amma fa kana gani fa tana shigowa ta hau habaici daga qarshe ta hau zagina.....samirah ta tari numfashinta da cewa"tambaya kimayi na baki amsa daidai da tambayarki" shut up!" Ya sake dakawa samira tsawa ya nuna mata qofa😡👉� sannan yace da ita get out of my room,jiki a salube ta juya zata fita ya ce hey🖐🏽ta juyo ya nuna mata paper dinta👉� take your rubbish neman tashin hankalinki ya siya miki ya bita da "stupid" wani takaici ya sake turnuqeta ai kuwa buguzum buguzum ta qarashe ficewa

Ya dawo da idonsa kan salima yace"ni bani da kunne sanda tayi zagin ba zaki bari kiga hukuncin da zan dauka ba sai ke sarkin iya hukunci?,sai kuma alokacin ta soma shagwabe masa da sunan bashi haquri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu"🖐🏽dont disturb me please leave me alone"ta san bacin ran aliyu bashi da dadi do haka ta ja qafafunta ta fice cikin takaicin asarar da sira ta jawo mata na kudaden da take son karba a gunsa,yaja tsaki mai qarfi cikin ransa yace"silly girl" ya juya a hanzarce ya shige bedroom dinsa

Ransa ya baci sosai mutum ne da baison hayaniya yanzu haka qirjinsa zafi yake haka yake ko hira yayi mai tsaqo yanzu kansa zai fara ciwo shi yasa ko musu bai iya ba,ba ruwanshi da shiga wata harqalla ko abokai bai fiya tarawa ba baifi ka qirge abokansa ba da hannu,to da shi da fadilan bansan wanda yafi wani ba🤔

Mrs muhammad dinku ce
[10/16, 12:39 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*wa yasan gobe?*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Writting by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶3⃣0⃣

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya canza kayansa zuwa na barci farare ne sol masu taushi mutum ne shi ma'abocin son fararen kayan amfani ya fada bisa gadon yayi rigingine qafafunsa na qasan gadon ranshi a cunkushe yake

Fadila da ke tsaye sai yanzu ta motsa ta saki ajiyar zuciya gami da fadin Allah ya kyauta ya iya mana abinda ba zamu iya da shi ba,ta isa inda suka baje kolin abincinsu suka ci suka tashi bar kwanukan ta tattare su ta gyara gun kamar ba'a yi hada hadar abinci ba agun

Ta isa kitchen ta zubasu cikin sink ta kunna gas ta hada ruwan bununsa wanda ya wadatu da citta kanunfari da lemon grace ta saka lipton daya sannan ta rufe tukunyar,ta koma ta saki fanfo ta wanke duka kwanukan ta adanasu sannan ta juye mishi tea din cikin wani dan qaramin flask mai kyau ta dauki cups guda biyu na tangaran ta dora a saman plate ta hada masa da spoon,ta rufe qofan kitchen din ta doshi bedroom din nasa

Ta tura qofar tana dar dar don tana tsoron kada ya maimaita mat abinda ya mata dazun,ya canza kwanciyar tasa zuwa barin hannun damansa yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,qafarshi da yake dan kadawa kadan kadan shi yasa ta fahimci idanunsa biyu a hankali ta ajjiye tire din a asaman bedside sannan ta koma saman kujerar madubi ta zauna tana fuskantar bayan nasa,dakin ya yi tsit kamar ba wata halitta a dakin sai qarar agogon bango dake maqale a abangom dakin yana ta aikinsa,ita batace komai ba bareshi da tasan dama ba maganar zaiyi ba

Zuwan can ta dan ja numfashi sannan ta tattaro dukka dauriyar da ta rage mata bayan ta gama wassafa da tsara maganar da zata fito a bakinsa,tayi yar gajeriyar gyaran murya a dan tsorace sanann tace" nazo ne baka haquri game da bata maka rai da mukayi dukkaninmu mu ukun,zan ari bakin yan uwana na ci musu albasa ince kayi haquri da mu baki daya,idan ban manta ba haka Abba ya gaya maka a ranar da mukaje masa _lamarin mata sai da haquri da kuma jajircewa halitta ce maau wuyar sha'ani amma idan kasa Allah a gaba sai komai ya zo maka da sauqi_"kayi haquri da mu Allah kuma ya huci zuciyarka😔,ga black tea nan ko kana da buqata sai da safe

Ta miqe tana barin dakin ya dan waiwayo yana dan kallon ta har ta fice,yana cike ne da mamakinta dama tana da saurin sauka a fishi ne?,at least ya samu relief ainun daga damuwarsa,hakan ne ya bashi dama har ya jawo flask din ya murda murfinsa ya bude qamshinsa ya taso ya mamaye hancinsa ya dan lumshe idonsa take kwadayin tea din ya kama shi,yasa kofi ya tsiyaya ya sanya zumarshi ya kurba qamshin cittan da kanunfarin da lemin grace suka hadu a abakinsa suka masa dadi

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tana idar da sallar asuba bayan kammala al'adarta ta kullum wato azkar na sabahi wal masa wanda annabi ya koyar ta koma ta jingina da gefan gadonta idanunta a lumshe ta soma tilawa kamar yadda ta saba cikin sassanyar muryarta,sai da tai izifi biyar sannan tayi addua ta shafa,ta linke sallayarta sannan ta soma gayara bangaran nata duk da ba datti ko kadan sai 'yar qura da ba'a rasa ba wadda hadarin da ake tayi kwana biyu idan ya hado sai kuma ya zama iska mai sanyi wadda ke tashi hade da yar qura,tana kammalawa tayi wanka sannan ta shirya cikin doguwar rigar yan kanti mai roba roba red ce ta sauko mata har qasa ,daga gaban rigar wajen qirji an kamata an mata tattara yayin da ta bude sosai daga qasan aka jera wasu irin dutsuna manya guda uku masu garai garai da qyalli hannun vest ne da ita saboda haka ta sanya long sleeve shirt fara ,tayi rolling da farin mayafi wanda acucin da tayi da gashinta ta mai doughnut ya taimaka wajan qarawa rolling din nata kyau iya kafadunta mayafin ya tsaya,qananun fashion na barima farare ta saka sannan ta jawo takalminta slippers na fata shima fari ne,wayarta ta dauka ta kulle bangaran nata

Yauma da keys dinta tayi amfani ta bude gurin,shiru yake ba motsin komai hakan yasa tayi tsammanin bacci yake,hakanne kuwa ta gani sanda ta leqa bedroom din nasa cikin sanda,yana kwance tsakiyar gadon duqunqune cikin farin lallausan bargo ,gefansa daga qasa dardumarsa ce qur'ani da kuma carbi 📿akai,yayi mata kyau sosai aliyyi gwanin kyau kome yakeyi kyansa fita yake,baccinsa yake verry calmness fuskarsa tayi fresh,sai ta lumshe ido tana tuna da yadda daren jiya tayi nata baccin cike da kewa da azaba,amma shi yanzu gashi yana nasa hankalinsa a kwance har da qarin wani na bayan sallar asuba kenan,ta dauko wayarta ta kashe plasher dinta tayi snapshot din fuskarsa,ai kuwa ta fito shar zara zaran gashin idanunsa sun kwanta luf,tayi kissing din hoton sannan ta juya ta yi kitchen

*mrs muhammad ce*

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*wa yasan gobe?*

▶3⃣1⃣

Chips ta soya hade da wainar qwai sannan ta dama masa kunun gyada da ya sha madara yayi fari qal sai zuba qamashi yake,sannan ta bare indomie ta yi masa awarar indomie,nan fa qamshin abincin ya karade gaba daya falon har cikin gidan to wani ma yayi rawa bare dan makadi,fadila gwanar girki ce mayyar kitchen ce tun tana gida ma,tana saitin window inda kan famfo yake tana wanke kayan da ta bata ta ke jiyo motsi kadan kadan,windon na cikin lambun bangarenshi da ke bayan part din kowa,tana daga kai ta hangoshi qarfe yake dagawa🏋🏼ya hada gumi sosai,armless riga ce a jikinsa da shortnekeer damtsensa cike da qwanji a murde,ya ajjiye qarfen ya dau dan farin towel dake gefansa yana sharce gumin kana ya dauki bottle na ruwa ya daddaka ya rufe ya koma kan keken training kuma🚵🏻

Ta saki murmushi ta kada kai,da azama ta hada komai ta koma bedroom ta gyara masa ta wanke toilet ta hada masa ruwan wanka,ta budade ko ina da qamshin nan nata sannan ta dawo parlour ta zare rolling din kanta ta fara gyare falon shima ,yana daga can yake jiyo qamshi kala kala na shiga hancinsa da fari qamshin girki ya fara jiyowa ya bude dogon hancinsa yana shaqar sa saboda ya masa dadi daga bisanai kuma ya jiyo wani qamshin qamshin da ya kwana jiya yana sheqa,ya sauka daga kan keken shima ya dauki wayarsa da towel dinsa ya bude qofar bayan ya shigo ta cikin kitchen wanda yasa sauran kadan suyi karo,ta ja baya da sauri tana gaidashi kanta na duqe a qasa kamar kullum bai amsa mata ba dama ta zaci hakan ya dai daga mata hannu🖐🏽ya wuce

A bandaki ya tarar da ruwan wankan nasa,ya dan yi dam domin bai saba ganin hakan ba a tarihin rayuwar aurensa ba ganin tunanin zai bata masa lokaci yasa kai tsaye ya shige cikin ruwan🛀🏼yana sheqar qamshin da yake

Cikim suit ya fito baqaqe masu sheqi sunyi masifar fito da ainihin kyawunsa,takalmi ne half cover dan hasken marun kamar yadda tie dinsa yake marun da jakarsa a hannu fuskarsa saye da fari qal din medicated glass dinsa wanda bai hanawa mutum ganin kyakkyawan qwayar idanunsa,sumarsa a kwance luf baqa sidik sai sheqi take ita ba mai yawa ba kuma ba a aske ba qamshin nan nasa na musamman ke fita a jikinsa,ya dan zauna a hannun kujera yana qarasa taje sumarsa da brush dake hannunsa

👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
Afuwa afuwa 
Nayi rubutu mai yawa zan turo muku na ajjiye wayar ina dan wani uziri kafin na dawo ya goge,chargy kuma ya riga yayi halinsa,kuyi haquri da wannan ku bini bashi da yardar Allah
Na gode

Mrs muhammad ce

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:40 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶3⃣2⃣

Ganin wannan dama ya sanya fadila tayi saurin sauko da kayan breakfast din gabansa duk da cike take da fargabar kada ya gwasaleta,tayi saurin hada masa tea☕ ta daidaita masa zafinsa ta ajjiye masa sannan ta sa masa wainar qwai🍪 da farfesun kayan ciki🍲,taji dadi da baice komai ba ya sauko ya karya,bayan ya kammala ya dauki jakar laptop dinsa💼 ya ciro yan dubu dubu guda uku ya ajjiye mata kamar yadda yake ajjiye wa sauran matan ranar nasu girkin duk da kuwa babu abinda zasu siya komai diba za suyi yana ajjiye,ya yi gaba ta biyoshi a abaya gabanta na dukan uku uku bangaren samira ta ga ya shiga don haka ta ja tunga ta tsaya baifi mintina biyar ba ya fito ya shiga gun salima mintina takwas sai gasu sun fito yana gaba tana biye da shi ganin fadila na tsaye da alamum jiran fitowarsa take sai yanayin fuskarta ya sauya😠 take ta juya ta koma ciki

Har sai da ya shiga mota ya zauna sannan tace a dawo lafiya tayi saurin juyawa ba tare da ta jira cewarsa ba don tasan bazai ce din ba ma idan ma ua fadan to ba mai dadi zata ji ba,tana hango salima da ta yaye labulen falonta tana kallonsu don haka sai fadila ta qorqiro murmushi ta dora bisa fuskarta

Ta rasa hali irin na salimar mutum ce mai tsananin qyashi da hassada ga azabar sa 'ido komai idanunta na kai kamar wadda aka bata aikin yin hakan ita dai samira barta da kishi masifa da tsokalar rigima kuma kana tabata za kuyi uwar watsi agun shikenan duk da haka kishin salima har yafi na samira ita kawai tanada duniyanci da yasa take iya boyeshi ba kamar samira da ba ruwanta ko a gaban uwar waye ayita ta watse ba munafunta

⚜⚜⚜⚜

Haka fadila taci gaba da tsara rayuwarta duk ranar da take da girki zata shiga bangaren ta gyara ko ina da ina,tana kuwa fama da aikin domin tsakanin samira ko salima babu mai iya yin cangal kowacce haka take fita daga girkin ta tabar sashen a ahautsine

Tsakaninta da aliyyu sai girki ta shirya masa daddadan abinci ta zuba masa ya ci idan ya kammala ta kwashe ta wanke kana ta ja qafarta ta bar sashen sai kuma washegari idan ta shigo hada masa breakfast,da zarar kuwa kwanakinta ya qare bata bi ta kan kowa da zarar ta taso a aiki ta shiga sashenta ta qulle qofa tofa sai washegari zata sake fitowa

Wai inji hausawa sunce jiki da jini kuma mutum da zuciya cikin lokacin sai sai qyamar girkin su samira ya fara kama aliyyun ransa ya soma sosuwa da ganin sam gyara bai damesu ba,har gwara ma.salima tunda at least akwaita da son ado da kwalliya zata yi wankanta tayi kwalliyarta hakanan zata qoqarta ta dafa masa koda jallop ce albarkacin masifar son sa da take duk da bata taba girki a gidansu ,amma samira kuwa babu daya qanwar biyu daga ciki

Cikin harshensa da zuciyarsa yana jin dadin girkinta sosai dandanon da bai taba jinsa ba gun kowa ba baya ga mominsa,miskilanci irin nasa yasa ko a fuska bata taba ganin alamun haka ba,takan tattare masa socks singlet handkerchief three quarters da duk inner wears dinsa harda jallabiyoyinsa da yake sawa ta wanke su tas ta goge su sannan ta feshe su ta turare ta jera masa su to ammafa insha Allahu bayan kwana hudu ta karbi girki zata zo ta tarar da su kamar kamar ba su ba komai an hargitsa shi sai ta soma fuskantar wani abu akwai gayya a ciki ta kuma san bazai wuce su salima ba don adawarsu gane da aikin nata a fili yake qara ra wani lokacin takan jiyosu suna yan qana nan maganganu takan sharesu taqi tankawa don basu tari gabanta sun gaya mata ba bare ta kula da shashancinsu

Abu daya ke qona mata rai aishi aliyyun na gani suke batawar shin bazai tsawatar musu ba idan su basu da tunani?

Ga misali a farkon fara aikin nata kafin su soma adawarsu takan tsince kayan aliyyu ne kawai a dakin a watse takan gyara ba tare da ta damu ba tunda tasan aikin ta ne dama,da tafiya ta soma nisa sai suka dinga barin brassiere panties sleeping dress underwear 👙👗musamman salima wadda kullum sai ta tsince nata tunda samira ke fara girki sai ita wanda a qa'ida fadila ce ya kamata ta zamo mai girki a farko amma suka maida ita ta qarshe ta qyalesu duka ta zuba musu ido ,tasan da gayya take zub da kayan,zuciyar fadil na matuqar baci da hakan,a duk lokacin da ta tsinci kayan takan bata lokaci mai yawa tana qissima dalilin barin kayan daga jikin mai su wanda hakan ke qara ta'azzara kishinta ga aliyyu

Wani sabon rainin hankalin kuma sai ta fuskanci ya shigo ta soma gyaran sai ta shigo tace"☺sorry fa don Allah,jiya na mance kayana akan gado wallahi dear ne ya rudani daren jiya shi yasa da safe na manta da su ban dauka ba,kinsan shi akawai nacin abun,sai dai fa ba sauqi shima fa gwani ne😉"wannan ya bata ranta fiye da abinda tayi mata,har ta soma hasashem anya basu da masaniyar babu abinda ya taba gilmawa tsakaninsu?

Akwai lokacin da ta zube har da magungunan mata maau dauke da hotunan banza,wannan fadila maganinta tayi ta dauko mata wasu wanda wata maqociyarsu a acan gida ta bata ita basonsu take bame ma zatayi da su tunda ta bata ta jawo locker ta watsasu sai yau ta tuna da su ta qara mata tace ga wasu sai ki qara naga naki basu kai wadanan tsada ba ni kinsan bana amfani da su halitta ta bata buqatarsu komai nawa yaji ba sai da kwaskwarima ba"jiki a salube ta karba duk da bata nuna mata hakan ba,ai kuwa da ta karanta kwalin sai taga tabbas sun fi nata kyau to tun daga ranar bata sake bari ba

samira nata rashin mutuncin yafi ysakanin falo da kitchen parlour zuwa kitchen,zata dauko plates ne🍽 kofuna ne🍶 da su spoon tayi ta batawa wani abun plate din ma leda ce ta chewing gum ko biscuit zata dora akai kuma ta barshi a nan tunda ta sani cewa babu mai aikin gyara gun sai fadilan,duk da wannan neman masifa da suke ba wadda ta isheta kallo a cikinsu

Su kansun so suke ta kulasun amma ta qi basu wannan dama

Mrs muhammad

📚📚✍🏻✍🏻✍🏻

01:18 pm 05/11/1437

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*

▶3⃣3⃣

Lahadi daya daga cikin ranakun qarshen mako ne wanda yake zama ranar hutu ga ma'aikata to haka ne ya zama ga fadila hutun ya zame mata double babu zuwa office kuma bata da girki,la'asar sakaliya ta ranar ta shirya tsaf cikin doguwar riga shigar da tafi so kenan ta material ce ruwan qwaiduwar qwai dinkin rigar ya bude sosai dga qasa an mata dogon hannu tayi rolling dinta kamar yadda ta saba da jan mayafi,takddunta ta diba 📄📉📈 na aikin office da takeson dubawa zata yi wani aiki a kansu ta dauki yar madaidaiciyar dadduma da daya daga cikin matashin kujerarta ta zira takalminta ta firo harabar gidan,sai ta tarar da saluma da samira zaune kowacce a harabar sashenta bisa farar kujera plastic,novel a hannun salima📖 samira kuma na riqe da wayarta📱 tana tana ta faman danne danne,tun kafin fadila ta kai ga zama ta fuskanci zaman nasu ba na Allah da annabi bane don kuwa taba fitowa ta fara cin karo da baqaqen maganganun da auke jifan juna da shi a fakaice ba tare da kowa ya kalli dan uwansa ba

kamar ta koma ciki sai kuma ta duba agogon wayarta📱taga biyar harda rabi da minti uku bata da wani lokaci na duba takadddun idan ba yanzu ba cikin gidan kuma zafi yayi yawa sanadiyyar hadarin da keta hadowa ana yin yayyafi dan kadan wanda ke qara tada zafin garin,ga injinsu yayi tsiya yaqi tashi tun wajen uku bakaniken ke kansa yana fama da shi kasancewar ba dan qarami bane yana daukar dukka freezers dinsu heater a.c da sauransu sun riga sun saba da wuta ko yaushe 24 hours,sai kuma ta ahimfida dardumarta cikin ranta tana fadin _ina ruwan biri da gada?_,tayi bismillah ta zauna ta soma aikinta,ashe duk suna ankare da ita,minti goma bai cika ba da zaman nata samira ta soma receiving call "shegiya kina duniya?......heeeee wlh gamu a cikinsa muna gogawa.......hahahahahaha aike kinsan fa hali tun ba yau ba"ta danyi shiru sanna ta sake kecewa da dariya kamar wani gardi tace"a haba haba ke sai kace ba nice samira ba?.....k kinsan saidai a gaji aqyale mana,kowacce qaramar shegiya sai ta kama gabanta da qafafunta🏃🏽 ,salima ta bude shafin gaba na littafin dake hannunta tamkar da gsken karatun take tace"qaramin dan iska ma yaci uwatar ai yasan kansa,samira ta sake kecewa da dariya "wlh har mai share share da goge goge ita wannan ai ba wahala zata bani ba.....yo hannatu yar anacen ma ba komai bace a guna wallahi duk hasashen da take na ita wata ce a gunsa

Sarai fadila ta san da ita take amma sai taga ba mutuncinta bane tsayawa tana cece kuce da wadda batasan ciwo mutunci da kuma darajar kanta ba ,kan ta qare wannan tunani sai ji tayi tas!

Da sauri ta dago idanunta don ganewa kanta wanda ka zubawa wannan lafiyayyen marin,aikin salima ne tana tsaye a gaban samiran bayan ta kwasheta da marin tana huci,tuni samira ta katse wayar hannunta na kan kumatunta ta miqe tsaye salima ta dora mata da bayani👉shiru shirun da kike ganin ina miki ba fa tsoronki nake ba ki bar ganin kina min kina samun nasara wallahi kin kaini bango nifa ba sa'ar yinki bace don uwarki"tasa yatsanta tan nuna qirjinta👆🏼 tana cewa"ni kika mara?"😁an marekin kadan ma kika gani wata rana zaki ga abinda yafi marin ma,kina tsammaninke kaďaice tantiriyar karuwa ko?💁🏽to 👆🏼nima karuwace nayi nayi kuma yaqon duniya fiye da naki ke da kika local ma

😳😳mamaki da tsoro suka kama fadiladama har akwai abun tutiya gun mace don tayi yawon karuwanci?wannan wane irin zama nine da Allah ya kwomù da har karuwanci ya zama abun ado?ita takaici ma sai ya sata ta maida kanta kanrubuce rubucenta📝taqi kola kowaccensu tana jinsu cacar baki mai zafi ta barke tsakaninsu tamkar zasu cinye junansu 🎭

Duf taji gun yayi shiru kamar an sanya musu kwado a baki🔐,ta dago da hazari don ganin mai ya sanya su yin shirun ba tare da kowa ya raba su ba?,aliyyu ne ashe ya ahigo kuma baau ankara da shigowar tasa ba sai da ssuka soma daga hannu da niyyar kaiwa juna duka👊🏻,kowaccensu tayi sak saluma ce ta fara cewa 😢wallahi tallahi ban kulata ba itace ta fara takalatakuma ka tambayi fadila"jin sun sanyo sunanta cikin sha'aninsu ya sanyata azamar taahi ta soma linke sallayarta,daidai lokacin da ya kai dubansa😒 gun da fadilan take da salimar ke nuna masa,ga mamakinsa tana gama ninke sallayar a nutse ta duqa ta mwaahe takardunta ta juya ta shige sashen nata ba tare da ta kalli ko da daya daga cikinsu ba cikinsu ba sai aliyyu ya bita da.kallo👀 karon farko wani abu daga garetà ya fara burgeshi nutsuwarta ,sai da ta shige ta kulle qofarta sannan ya dawo da idonsa kansu tuni samira har ta gudu🏃🏽ta rufe itama qocarta cike da fargaba da tsoron fushin Aliyyu😡 a akanta don ta tabbatar In dai ya bincika ya tarar bata da gaskiya to la shakka fa kashinta ya bushe,ta ruwan sanyi yake ma hukuncin da zaka raina kankà babu duka ba zàgi bà baqar magana,ya juyo ya dubi saluma da jikinta ke rawa sai kawai shima ya gewayeta ya shige nasa part din

⚜⚜⚜⚜⚜

Kwana uku tsakaniya kamaqarshen wata ne,kamar yadda ya zama al'adar gidan fita aiyàyya a iřin lokacin don sabunta abu uwan buqata na amfanin yau da kullum
Yaune za auyi fitar farko tun bayan dawowar salima gidan gidan

Fadila ta shiryq cikin shigarta ta bare bari tana nannade cikin lafayarta ,ta kammalà komai ta kira umminta don su gaisa,hira suke sosai ta jiýo tashin horn ta tabbatar aliyyu ne don bai son jira kuma baya jira saboda haka shima bai bari a jirashi tayi saurin maqale wayar a kafada tan ci gaba da hirarta da ummin tasa daya hannunta dauki jakarta🎒ta sa mèy ta kulle sashin,ta qarasa jikin motar tana sallama da ummin ta ciro wayar daga kafadarta tana kashewa sai ga salima da samira tamakar an jehosu kowacce na qoqarin bude gidan gana ta shige don badon fadila tayi azamar matsawa ba da daita zasu yi awon gaba,ta rufe bakinta da tafin hannunta🙊 dariya na shirin subuce mata😂,cikin zuciyarta tana cewa sunan wani film *qauyawa* Allah kayi mana magani wannan ai kishin jahiliyya ne

😂😂😂😂😂

Ku biyo *mrs muhammad*

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻



[10/16, 12:41 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶3⃣4⃣

Allah ya sawwaqe tace,ta bude gidan baya ta shiga tana kallon drama,aliyu ne ya juyo don ganin meke faruwa haka ake shirin cire masa hannun mota?cikin tsawa musu su matsa masa daga jikin mota,bai wata wata ba ya figi motarsa ya barsu a gun sake da baki😦,gudu yake zubawa abinsa bisa dukkan alamu ransa ya baci,duk sai fadila tayi tsuru-tsuru don da irin wannan gudu da yake zabgawa gwara ya sauketa salun alun ,

Qiiiii...taji ya taka burki,ya gangara gefan titi ya faka motar cikin shaqaqqiyar murya taji yace"fito ki dawo gaba don ni ba driver din gidanku bane😠"bata ce kanzil ba ta dawo gaban

Yanayin zaman yayi wa fadila kusa sosai,mayen turarensa ya soma raba mata hankali,lissafinta

Please Login or Register in order to submit comment