Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fadila wani faduwar gaba taji amma ta maze don bata son fadilan ta fuskanci ta razana da ganin da ta mata,maimakon haka ma sai ta mata wani kallon raini na sama da qasa sannan ta janye idanunta ba tare da tace kanzil ba

Bata ma lura da kallon ba tana qarasowa cikin falon ta yiwa kanta matsugunni bisa tattausan carfet din da ya malale dakinta jingina jikinta da kujerar dake bayanta,wani abu ke tsunkular zuciyarta game da kishi duk da ta godewa Allah da ta tarar samirah bata fita da komai ba sai farar fata don ta tsammaci aliyu zai so matar da ta fi samira ne ba kamar samiran ba cikin ranta take cewa lallai so hana ganin laifi,to ganin samiran ko sashen da take bata kalla bayasa itama ta dauke mata kai sai ma ta zaro wayarta ta shiga latse latse

To shima Aliyun sai da ya kammala abinda yake ya shiga bedroom dinsa ya dan jima sannan ya fito ya samu kujera daya ya zauna ai kuwa tsam samira ta bar gurinta ta dawo jikinsa ta lafe kamar mai shirin komawa cikin sa ta gefan ido take satar kallonsu wani abu mai daci na damunta,amma a haka idan ka kalleta sai ka rantse da Allah batasan Allah yayi ruwansu ba don bata fasa danne danne a wayarta ba

Da bismillah ya fara yayi salati ga fiyayyen halitta yaja dogayan addu'oi wandabhar samira ta fara nuna masa tafa gaji,fadila ita mamakin yadfa Aliyu ke zuba addu'a take tamakar ba daga bakinsa suke ba(hmmm fadila kenan bakisan waye Aliyu bane😜)ya kammala sannan ha shafa,ina godiya ga Allah bisa ni'imomi da ya yimin a rayuwata tun daga haihuwata har kawo yau,ya kalli samira yace ga abokiyar zama nan Allah ya qaddara tare zan aureku sai kj zauna lpy bana buqatar hayaniya ko tashin hankali a gidana kowacce ta kama kanta ta tsaya inda Allah ya ajjiyeshi....
Ya dan sarara sannan yace idan da mai magana bismillah ya koma ya jingina da kujera yana jiran cewarsu,samira ta saci kallon fadila tana jiran taga zata tanka sai taga ma Sam idanunta bai kansu ta aza su ne bisa carfet,ta gayara zama cikin iyayi da kisisina tana kuma yatsuna 😏 tace"to nidai bana son shishshigi kuma bana son raini ehe.....kuma kowa ya kwana lpy shi yaso,sweet banji kayi rabon kwana ba?"ya daga kafada yace"its un 2 u ai"tayi wani fari da ido🙄tace"zamu raba kwana dai dai ne yayi aiko?"ta tambayeshi ya sake faga kafada yace taakaninku ai nikam ban iya yawon bin bangare bangare ba,"hmmm shegen girman kan tsiya"fadila ta fada a zuciyarta,duk da idan ka kalleta zakayi tsammanin bata tare da su,yauwa sweet ina kuma da buqatar masu aiki do.....cikin dakiya ya tari numfashinta,ba'a gidannan ba☝🏼,inji aliyu,ta narke murya,please sweet pls mana"bani buqatar roqo✋🏻ra'ayina ne"shiru tayi don tasan Aliyu idan yace eh babu mai sashi yace a'a,bare ita da take lallabawa tasan har yanzu lamarinta bai saki zuciyarsa ba

Dakin yayi shiru har ta gama kidanta tayi kuma rawarta ita kadai,ba wanda ya nemi jin ta bakinta Aliyu ya rufe da addu'a,ita din ma bata zaton ko sun ce tace dinma zata tsinka wani abu,suka shafa addu'ar ta miqe ta fice ba tare da ta cewa kowa komai ba,samira ta bita da kallo ranta cike fal da kishi saboda komai hassadarta bata gano abun kushewa tattare da fadilan ba

Shima kallon gun da ta tashin yayi yana dan mamakin sauyawarta yayi tsammanin za susha artabu ne kamar yadda suka saba a gida sai kuma yaga b sabanin hakan

A bangaranta fadila dana sanin zuwanta tayi gun sosai don bai qareta da komai ba sai hanata bacci da ya yi duk yayin da ta runtse ido da niyyar baccin sai hoton fuskar Aliyu ya bayyana cikin duhuwar idanun nata,wata iriyar soyayyarshi ke mamaye ruhunta cikim tsakiyar daren kewa ta kamata ga kadaici da ya hanata sakat,so ne da bata yaba jin irinsa ba a rayuwarta qauna ce ta musamman,hakanne ya zama sanadiyyar karyewar zuciyarta duj yadda takai ga bawa kanta qwarin gwiwa,kuka ne matsananci ya sarqeta,daren tayi kuka mai yawa a kwancan tana tausayawa rayuwarta da makomarta,tasan tabbasa son Aliyu na daya daga cikin jarabobin rayuwarta,tanajin sa a jiki jini jijiya da ruhinta

Cikin taimakon Allah bata manta da ambatonsa ba hakan yasa bacci yayi nasarar daukarta

👏🏻👏🏻👏🏻 ayimin afuwa a danyi haquri da wannan sai Allah ya kaimu gobe

Mrs muhammad bello ce

✍🏻✍🏻✍🏻📚📚📚📖
[10/16, 12:31 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶1⃣3⃣

Kwanakin da suka baya ta yisu ne cikin kadaici da kewa,ita kadai ke wuni a bangaren nata,bata da aiki sai wanka da sallah da shi dama abinci ba gwaninta bane saidai tayi ta jiyo muryar baqin samira da har yau suka qi qarewa,wani lokaci kuma ta kira farida su sha hirarsu

Ranar da ta cika kwanaki bakwai a gidan ranar tana kwance a falo hannunta riqe da littafin sahihu muslim mujalladi na daya tana karantawa da yake mayyar hadisi ce ita ta jiyo ana knocking din qofarta ta dora littafim a saman kujerar taje ta bude

Anty hauwa ce da yaranta bilkisu kausar Ibrahim sai qaramin su muhammad sai kuma madina qanwar momy da yaronta hamid sai iftihal,farinciki sosai fadila tayi don tasan yau babu wunin kadaici,nan falin ya kaure da hayaniya su suna hirarsu yana na nasu,ta shiga kitchen ta hado musu kayan motsa baki sannan daga bisani ta nufi kitchen don dora girki iftihal da bilkisu suka bita zasu tayata don sune yan manya madina ma binsu tayi aka bar anty hauwa da ragowan yaranta suna kallo fadila tayi tayi madina ta bari amma taqi don haka tare suka kammala komai,tare suka ci a babban plate guda yaran ma aka hada musu anti hauwa ce tace ayi haka kada a bata mata kwanunka,bayan sun gama madina ta hada kan kwanunkan ita da su bilkisu suka gyara mata komai,ganin ba kowa a gun anty hauwa ke tambayarta ina fatan dai baki da matsala da Aliyu ko dan kishiya wannan kam ita ba'a rasa ta da matsala saidai haquri ,dan murmushi fadilam tayi tace"ba wani matsala anty lpy lau muke"ta jinjina kai tace to saidai a yita dai haquri don kinsan zaman aure ya gaji yau fari gobe tsumma,tayi mata nasiha sosai tare da bata shawarwari masu gamsarwa fadila sosai taji dadin maganganunta hakan ya sake qara mata qwarin gwiwa da nutsar mata da zuciya

Bayan sun idar da sallah ne ta la'asar wajan biyar da rqbi suka soma haramar tafiya,iftihal tace da naty hauwa mummyn kausar nidai anan za'a barni ko?,antu hauwa ta girgiza kai tace a'ah ai ba haka kukayi da mummy ba,bazan iya da wannan rigimarba tate zamu tafi da ke,ta soma diddira qafa tana maqale kafafa tana cewa nidai anan zan zauna mummyn kausar gaskiya,fadila tace da anty hauwa"anty don Allah ku barmin ita mana dama ni kadai zaman ba dadi wlh"anty hauwa ta zaro ido😳 tace"wai rufamin asiri ai mummy bazata iya zama ba iftihal ba ko na barta da kanta zatq zo ta dauki abarta baki ji yadda aka kafa mana sharadi ba kan a bamu mu taho da ita kamar tasan za'ayi haka"jin haka yasa fadila ta haqura

Ta tako.musu har waje bakin part dinta yara nata tsalle kowa da packet na chaculet dinsa a hannu ta bawa su anty hauwa turarurruka da qyar ta karba tace ita lpyrsu kawai ta zo gani,ganin suna shirin yin gaba ba tare da sun shiga gun samira ba tace"antu baku leqa gunta ba kun gaisa"anty hauwa tace o'o'o ni kam tun shigowarmu muka gaisa da ita a harabar gida ta rako baqinta sai dai ko madina ita da yara,madina ta tabe baki tace nima bani zuwa anty ina kallo fa sanda muka shigo tana ganinmu tayi saurin sallamar baqin ta juya ciki kema sai da kika kirata kusan sau uku sannan ta amsa miki,sai dai su kausar maza kuje ku gaidata ku fito mu tafi ungoshi bilkisu ga hamida ma aje da shi ai ya wakilceni

Suna tsaye suna jiran yaran sai kuwa gasu jiki a salube sun dawo Ibrahim sarkin zuciya hadda guntun hawaye madina na amsar hamid daga hannunsu tana tambayarsu me ya samesu,bilkisu tace anty koromu tayi wai ba mun gaisa a waje ba meye kuma na wani biyota,ibrahim da ya fisu shekara yana kusan 12yrs yace"har tsawa fa tayi mana wai masu qwala qwalan ido sai kallonta muke wa ya sani ma ko turo mu kayi mu cinyeta"iftihal kam fuskarnan a turbune tqma kasa cewa komai,anty hauwa tace ya 'isa haka is ok bata mata rai baqinta suka yi ku wuce muje,sukayi gaba fadila da mamaki ya kamata tana biye da su mamakin samira take sai kace wata mahukaciya yara zata tsaya tana gayawa irin wadannan magan ganun sai ka ce wasu manya,suna gab da get suka ji ana kwararo horn mai gadin ya tashi da azama ya bude wawakeken get din wata farar motace sol qirar range rover ta shigo ta samu gun parking ta tsaya da gudu iftihal ta kwasa tayi bakin motar

Ya bude motar ya fito sanye yake da suit masu bala'in kyau baqaqe sunyi masifar yi masa kyau da kwanciya lif a farar fatarsa tas da shi kamar yanzu ma yake ahirin fita aikin ba wai ya dawo bane,iftihal na qarasawa ya cafeta ya daga ta sama ya jujjuyata yayi kissing kumatunta sannan ya direta ta tsugunna da alama gaidashi tayi,madina tayi dariya😀tace "oh uwar wayon tsiya wai har motocin Abbanta ta sansu wannan yarinya "anty hauwa tace"ke ai iftihal da wayinta aka haifeta don.mummy tace duk cikin jikokinta bata ga mai wayonta ba"da hirar iftihal da suke suka qarasa gurinsu ,cikin motoci fadila ta dan rabe bayan wata mota tana ganinsu tana kuma jina binda suke cewa,ya dago yana masa sallamarsu.lokacin da yake tambayar iftihal"ashe tare kuke mummyn yara"anty hauwa ta mayar masa ta sigar da ya fada"😊mummyn yara tun dazu tazo kuma yanzu zasu koma"ya juyo yana kallin madina yadan hade rai yace"au da waccar kima zo"anty hauwa dake danne dariya tace"eh duk tare muke"tasan yar tsamarsu da Aliyu don tun ranar da take fadin ita babarsa ce tunda qanwar mummy ce bata san yana gun ba suke yar tsama ya daina sakar mata

Ya miqawa su ibrahim hannu suna musabaha haka halayyarsa take dama yana dan tsokanar ibrahim din kasancewar sunan kakansu ne shi kuma ibrahim na murmushi ya karbi hamid daga hannnun madina yana duban anty hauwa yace ba wanda ya rakoku ne?,anty hauwa tana dube dube tace tare da fadika muke ina tayi ne?,fadila data dora hannayenta saman motar tana game a wayarta har dankwalin kanta ya zame bata sani ba ta dago jin an ambaci sunanta idanunta suka fara sauka kan aliyu cikin sa'a suka hada ido harara taga ya balla mata wani abu taji ya caki zuciyarta ta lumahe idanunta am ta kasa budesu wani sinsa taji na mamayar zuciyarta da gangar jikinta kamar ana zira ra mata ruwan sanyi bugun zuciuarta ya sake qaruwa,bata san me tayi masa ba yake harararta,sai tq sunkuyar da kanta😔 tana kallon yatsun qafarta dake saye cikin slippers,sai da iska ta watso mata gaahin kanta gefen fuskarta sannan ta gane ma'anar hara rar da aliyu ke mata don bata manta ba rabi'ah ta taba fada mata ya aliyu baison yawo a waje ba dankwali idan ya ganki kuwa kin shiga uku,da sumauri ta jawo mayafin data yafa ta lullune kanta sosai

Duk daga idon da zatqyi a rayuwarta ta kalli aliyu sai taji an qara manna mata sonshi ji taje kallomsa ma kawai jaraba yake zamewa rayuwarta sai dai koda tayi niyyar qin kallon nasa sai ta kasa jure haka domin zuciyarta bata lamunce mata ba,ba abinda ke sata nishadi irin kallon kakkyawar qayatacciyyar fuskar tasa

To fadila za mu wuce sai an kwana biyu kuma,cewar anty hauwa tana dan murmushi😊 ta taso daga jikin motar da niyyar sake yi musu tattaki suka sake hada ido da shi sanda tayi niuyar satar kallonsa wata hararar mai zafi ya sake watso mata wadda ta sata tsayawa daga nan cak,yaram suka taho suna kama hannunta suna cewa anty bye bye,itama ta daga musu hannu✋🏻 tana dan murmushin yaqe😇 tana cewa"bye"sai kuma iftihal ana su taho ta ja tunga ta tsaya ita allan katafar ba zata bisu ba aliyu dake karbar takaddu daga hannun nasuru ya juyo yana tambayar meke faruwa anty hauwa ta masa bayani,kallo daya tak yama iftihal din tabi bayansu jiki na rawa

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣4⃣

Bata sake sha'awar kallon inda yake ba don ta gaji da ganin wanna hararar tasa da kallon qiyayya da yake jifanta da su sai ta juya da sassarfa don barin gurin "ke"taji dakakkiyar muryar Aliyu,batason irin wannan kiran sam don haka tayi banza bata juyo ba bata kuma amsa ba kuma bata daina tafiyarta ba ya sake daga murya yace"dake nake"sai ta tsaya cak saboda tsoron da ya bata muryarsa ta canza tayi fakare tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,da tsawa yake mata magana bayan ya sha gabanta"ki baki isa a kira ki ba kenan ki tsaya"tamkar tace wani abu sai kuma taga bai kamata ba tunda a harabar gida suke wani zai iya zuwa giftawa ya jisu

Aliyu ya kafeta da ido yana huci a zuciyarsa yana fatan ta tanka masa ko zai samu ya huce mata haushinsa amma ko kallon fuskarsa taqiyi hasalima sadda kanta tayi qasa,ganin da ya yi bata da niyyar ko alamun tanka masa sai ya dora mata baqar leda mai dan matsakaicin girma bisa qafarta yaja tsaki gami da hura mata hucinsa akan fuskarta ya wuce,sai sannan ta dago tabi bayansa da kallo tana sheqar iskar wadda ke bada qamshin lemon fresh na mouth fresh,ta kauda idonta sai kuma ta hango samirah na tsaye bisa varender dinta ta zuba musu ido don haka sai ta saki murmushi ta kuma yi saurin dauke ledar tayi bangarenta tana qara hasko fuskar aliyu qamshin turarensa maganarsa komai nashi unique ne mai tsari ba baunda tafi buqata a yanzu irin aliyum saidai tasan samun nasa ba baune mai sauqi ba wanda zata cimmawa cikin qanqanin lokaci
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Kamar ko yaushe a irin wannan lokaci tana kwance kam dogowar kujera a main parlour kunnenta maqale da earpiece tana sauraron suratu baqara cikin qira'ar sheikh Abdurrahman assudais taji ana mata knocking kafin ta bada izini tuni an bude an shigo,ga tarin mamakinta samirah ce ,ta tashi zaune tana qoqarin cire earpiece samirah ta qaraso tana kallon yadda take qarewa parlour din kallo zuciyarta cike da kishin yadda parlour din fadilan yafi nata tsaruwa da kyau,fadilan nata biye wa wanna ba ta nunawa samirah gun zama tace bismilla ga guri zauna😒"ta wani tabe baki tace"ba zama na zo yi ba don nima gidana akwai gun zaman "jin haka yasa fadila ta gane ba mutuncine ya kawota badon haka sai ta koma tayi kwanciyarta kamar yadda take da ta kuma maida earpiece dinta kunne ba tare da taci gaba da sauraron karatun ba

Da samira taga haka sai ta yatsine fuska sannan ta fora da cewa"nazo ne don na tuntubeki bakiyi shirya fara zuwa turakar miji bane?,sai tambayar ta bawa fadila mamaki ta kuma ji wani bawai tana daga kwancan ta dubeta"kamar ya?,me kike nufi ne?"samira ta juya ido👀 tace"a....to gani nayi har yau baki fara zuwa ba shi kadai yake kwana nima ba zuwa nake ba tunda lissafe kwanakin amarcinki ne"mamaki ya sake kama fafila don ko a lbr bata taba jin ko ganin raahin kunya irin wannan ba wato ma idonta na kanta kenan
Tilas ta miqe ta zauna sosai don nuna wa samira ba ita ce kawai mara munya ba itama ta iya barikancin nan,"da farko baiwar Allah ajiyata aka baki?,ko kuma da mai gidan kukayi maganar bana zuwa gunsa?,to idan ajiyata aka baki ina mai baki shawarar kiyi gaggawar maidawa wadda ya baki ajiyar don wannan aniyar tafi qarfin ki wlh ba zaki iya ba idan kuma shi mai gidanne ya gaya miki bari na sake tambayomiki shi.....,ta fada tana jawo wayarta tana shirin shiga contact cike da barazana don bata tsammanin ko number dinsa akwai cikin wayarta😜
Ganin da samirah tayi da gske kiransa zatayi kuma ta san sarai halin Aliyu bare tana cikin case har yanzu lallabawa kawai ake sai tace"dakata ni ba gangami nace kiyo ba magana ce iya kacina da ke"ta juya tana shirin barin falon fadila ta dan daga murya tace"ai da kin tsaya an sake jin ta bakinsa ko kinga maji dadin qarasa maganar,mu amarci muke mai lasisi ba irin naki ba"bata ce uffan ba ta fice ta ja mata qofa,wani takaici ya kama fadila taja wani dogon tsaki tana cewa"banza ballagaza ko angaya miki ke daya kika iya bariki ne kina ganin kin girmeni ko,da auren so mukai da aliyu wlh kallonki ma kace yayi sai yaji an hada shi da aiki"ta koma tayi kwanciyarta yadda take taci gaba da bin karatunta

Kwanaki nata tafiya da fadila cikin gidan,ba wani qiba da zaka ce ta qara sai fatarta da tayi lumi lumi ta sake fresh saboda zaman guri daya
Watanta biyu kenan da sati yakwas kwankin da take jinsu kamar waau shekaru saboda zaman kadaici,Allah allah take sakamakonsu ya fito bata da sha'awar komai illa ta fara fita aiki,ta jawo wayarta ta soma neman nafisah classmate dinta ce suna gaisuwar mutunci da fadila don har bikinta tazo tave cikin zuciyarta bari ta kira ta tambyaeta ko sakamakon ya fito saidai nata sameta ba number dinta a kashe don haka ta maida akalar kiran layin anty hafiza sunsha hira aosai ta kuma yi mata qorafin sunqi leqota ba ita ba yan biyu gsky tayi fushi tace tayi hqr insha Allah zasu zo su yinin mata,bayan sun gama sai ta kira hafsah da aukayi attachment tare sun gaisa sosai take tambayar hafsa ko result ya fito tace yana dai hanya da ya fito insha Allah zata sanar mata tayi mata godiya suka kashe wayar
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Zaune take alambun dake bayan part dinta kan kujerar siminti under wear dinta take wake wa su brassiere pant da skert gun tsit yake shima kamar yadda gidan nasu yake saidai ahi akwai kadawar ganyayyaki da kuma kukan tsintsaye jifa jifa wadanda take zubawa gero shi yasa suka dadu kuma suka fi yawa alambun nata fiye da ko ina a cikin gidan tana son gun sosai saboda yawancin lokuta yakan zamo daya daga cikin abinda ke debe mata kewa ko da yaushe gun luf yake dauke da inuwa mai sanyi
bata barin undies dinta wanna ma kwana biyu ne da bata jin dadin jikinta dama cutarta ciwon kaine ko ciwon mara shi yasa suka taru haka ita dama can ko a guda da wahala kaga kayanta cikin kayan wanki ko za'a mai saidai kaga na fatida tafi ganewa tana cire maya ta sabesu ta shanya sannan ta shigà wanka,tana cikin shanya ne taji takun taviya sai tayi sak don dai tasan ita kadaice a gun kuma ta kulle sashen nata da idanunta take bin gun da kallo don gane daga ina takun yake,Aliyu ne ke taho wa hannayensa harde a qirjinsasanye yake da jar t.shirtmai gajeran hannu sai dogon wandon jeans mai kalar black blue sau ciki ya sanya balck blue idanunsa saye cikin glass dinsa na qa'ida fari qal zuwa lokacin fadila ta soma tsammanin medical ne bana gayu bane,tayi saurin dauke idonta dag kansa zuciyarta na wani das das das har ya qaraso gabnta ta kasa moysawa tamkar ta nutse saboda irin kayan dake jikinta ta tabbatar babu mai shigo mata ne don ta kulle qofarta shi yasa ta saka su rigane da akery sosai sai dai maau roba ne iya qibarka iya yadda zasu fidda shape dinka gashi gaba daya hannayen ta da skrt din anbi an tsaga ko ina babu inda ya tsira wuyan rigar mai fafi ne son ana hango saman qirjinka sosai kanta kuwa ba dankwali sai tafkeken ribbom da ta saka ta mate gashinta ya sauka mata a kafada duk da ya danyi tauri sabida raahin zuwa saloon kwana biyu

A dabarance take duba jikinta tana sa hannu tana gyara inda hannunta fuk yakai saidai ina duk In da ta sa taja ta rufe sai wani gurin kuma ya bayyana shikam hannàyensa na harde ya jinggina jikin qarfen da ta ware tan shanya kayan idanunsa duka ya zuba mata duk dabararta na tattare jikinta sai da ya ganota shi sai abin ma yaso bashi da riya duk da a fuaka sai ka ranyse rufeta ma zaiyi da duka"bari nayi maganin yarinyarnan'ya fadi haka cikin zuciyarsa"ni da waye a gun kiketa wani aikin rurrufe jiki?,gabanta ya fadi kunya ta sake kamata sai taji ya ja tsaki wanda yasa ta dago ta kallo shi ba tare da ta dubi qwayar idanunsa ba don tana kaucewa hakan bataso au hada ido sam don tana tsammanin yana da wani asiri ne cikin qwayar idanunsa aduk sanda qwayar idanunsa auka hafu da nata takan kwana ne ta wuni cikin begensada kuma aAbar aonshi da take ta yaqin ganin ta bunneshi cikin babin rayuwarta,wa ya gaya miki an damu da jikin naki da kiketa qoqarin killaceshi ne?...... Ba wannan ba na duna store naga yadda aka Uba kayan abinci haka suke ba'a taba ba kamar wadda ka bai wa rancansu sannan fridge ma haka yake abu qalilan ne suka ragu mekike nufi? Salon kija min bala'i ko?wannan wankin kuma da kika hafo na meme?duk masu wankin gidannan suma basu miki ba ko gulmar azo a tarar kina wanki ace wuya kike sha?burinki dai kawai na zama mai lafi

Ya tsagaita da fadan ya kafeta d ido ko zata ce wani abu amma yaga ba alamu duk da zuciyarta ta baci da yadda aliyu ke mata a cikin gidan ba dama inuwa daya ta haasu sai fada tsakaninta da shi?cikin zuciyarta taja tsaki gami da cewa"shikenan kuma sai akace mutum bàshi da aiki sai dirkar abinci kamar tsohon jaki?kuma ma wane aiki nake don na dwbo yan kayana na wanke da hakan zai zama laifi agun wannan mutumin?

Bata tsammci a fìli tayi maganar ba sai da ta ji yace"duk basu zama laifi ba amma ki shirya duk ranar da aka tuhumeni da wani laifi akanki kisan yadda zaki kanki don daukar ki zanyi cancankat nakai musu ke"ya maida kansa gun agogon dake daure atsintsiyar hannunsa 😠 yace"me dame kike da buqata?a gajarce tace masa"ba komai"yayi tattaki ya sake qarasowa gabanta ya ajiiye mata kudi kamar yadda ya saba ya rabe ta gefanta ya wucè tana sheqar daddadan qamshinsa wanda yaja mata kasalar da ala dole ta tattara ragowar da bata wanke ba ta maida ciki

Mrs muhammad ce

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻




[10/16, 12:33 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


▶1⃣5⃣

Washegari misalun takwas na dare tana zaune a falo tana kallon wani film gabanta plate ne ta yanka kankana apple da gwanda tana sha dama abincin bai wuce ire ire wadannan qwaqwaso qofar taji anayi ta dauki hijabinta dake gefanta wanda ta idar da sallar isha'i da shi ta zura sannan ta miqe tana tambayar wane?ki bude mana,taji ance bata dau murya ba amma ta gane maca ce,ta bude ba yare da ta kauce daga hanya ba,samirah ce tsaye cikin kwalliya rakacau a fuskarta tana sanye da doguwar rigar atamfa tayi rolling dawani siririn mayafi sai uban turare data bulbule jiki da shi tana taunar chewing gum qas qas qas, tana wani ya tsina fuska tace sweet yace ki fito zamu siyayya,fadila tace😏 waye sweet kuma?,ta wani juya ido tace my aly,

Tabe baki fadila tayi tave kice bani buqatar komai,bata jira cewarta ba taja qofarta ta rufe,wani kishi ne ya motsa mata ita kanta tasan tana da tsananin kishin aliyunta amma ya ta iya?,ta jiyo muryar samirah na masifa"aikin banza wa ma ya damu da ke 
?kada Allah ubangiji yasa ki je din dama sho ya takura ayi kiranki waishi mai adalci toga abinda ya jawo mana nan wulaqanci agun wadda bata isa ba"fadila dai murmuahin uaqe tayi wanda akace yafi kuka ciwo,ta dauki plate dinta taci gaba da cin fruit din ta ba tare da tana jin dadinsu ba kamar da
Knocking ta sake ji ana mata ta maida plate din kitchen sannan tazo ta bude yana tsaye a bakin qofar hannayensa zube cikin aljihun jeans dinsa fuskarnan kamar hadarin dake shirin zub da ruwa😠ba tare da ya dubeta ba ya kalli agogon hannunsa kana yace"nan da minti biyar ki sameni a mota,abindabya fada kenan ya juya yayi tafiyarsa,cikin qanqanin lokacin kuwa ta shirya kasancewar ita dama

Please Login or Register in order to submit comment