Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tagar da tayi "sama fa qasa ya kalleta sannan yace "๐Ÿ˜ baki da kunya ko?,ni zaki buge ki wuce kenan?"tafin hannunta tasa ta kate fuskarta tana ci gaba fa kukanta shi kuwa ya zuba mata ido ba tare da ya sake cewa komai ba, sai da ya gama ikon nasa don kansa ya kauce tare da wucewa ya bar gurin


Da gudu ta fice tana ci gaba da kukan ta wuce bangarenta,dispenser ta kunna tayi heating gurin sannan ta koma bisa gadonta ta kwanta tana maida ajiyar zuciya,me ta masa?ma ta tsare masa banda tsabar cin zali kawai don ta rabe zata wuce sai ya mata wannan muguntar?" Ta danyi qwafa kadan a ranta tana ayyana zata rama

โšœโšœโšœโšœโšœโšœ

Su biyar ne zaune cikin office din fadilan sai fauziyya fa'iza aisha da halima dukkaninsu abokan aikinta ne matasa ne son saidai duk sun girmemata aqalla zasu bata shekaru uku zuwa hudu,amma nutsuwa da kaifin hankalin fadila yasa ta saje cikinsu suna jin dadin zama da ita sosai duk da miskilace saidai akwai karamci da mutunta mutum


Hira suke gaman da zamantakewar aure irin hirarmi dai mata da aka sani wadda matuqar mayan aure suka wuce biyu aka hadu sai an yita,hira ce ta qaruwa ba banzar hira ba wadda bata kamata ba,duk da haka fadila na gefe don bata da abun fadan saidai jifa jifa takan ce wani abu


Hira tayi nisa fa'iza ke basu labarin wata maqociyar yayarta 'yaf nijar dake saida magungunan mata masu kyau na gargajiya wadanda basu cutarwa,dukkansu suka ce ayi kiran matar suna so fadila kawai ta rage,fa'iza ta kalleta"ke ba ki siya fadila wlh maau kyau ne"murmushi tayi tana neman qaryar da zata gilla musu,don ko ta siya me zata yi da su,ta kalli fa'iza "to a hado da ni ga nawa kudin"ta nude zif din jakarta ta fito da kudin,fa'izan ta kuma cewa idan ma bakiso akwai wani hadin tutare mai tada sha'awar mai gida sai a kawo miki shi"cikin basarwa fadila tace"a hadomin duka kawai"(kaji fa mai karatu kamar gasken tana da buqatarsun ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ)


Take fa'iza ta kirata ta sanar mata,ta kaahe wayar tana dubansu tace kun taki sa'a don gata nan ma anan kusa don tana ja'en,cikin minti talatin sai gata kowacce ta karbi nata ta sanya ajaka


Qarfe biyar ta soma hada kayayyakinta tana sallama da su zata wuce gida don ta kammala aikinta ,wayarta dake aljihun bayan jakarta ta dauki qara alamun ana nemanta *sister ta* ta gani bisa screen din hakan na nufin farida ke kiranta,da sauri ta daga hadi da yin sallama,"sister ki taho kiga baby girl mai kama da ke kamar copy naki akayi na haihu yanzu haka ina gida"wani tsalle fadila tayi hadi da qaramin ihun farinciki sam ta mance a office take ba a gida ba sai da taga su fauziyya sun taso suna tambayarta mai ya faru sannan ta tuna ta maida wayar tana dariya cikin doki tace junior sister na ce ta haihu wlh"suka mata barka hade da dariya suna cewa saura ke kenan,murmushi ๐Ÿ˜Škawai ta musu ta saba jakarta tana cewa"Allah ya bamu alkhairi"ta kama kumatun yarinyar fauziyya tana mata wasa har ta fice yarinyar nata kuwa bangala mata dariya don fadila akwai son yara yarinyar ta soma sabo da ita yauma sa'a akaci bata sa kuka ba da zata tafin


Da dokinta ta shiga motarta da niyyar wucewa gidan farida kai tsaye,har ta kunna motar ta tuna cewa sai fa ta sanar da aliyyu,take
murnarta ta ragu tamkar an zare mata laka ta kashe motar,ta jawo hand bag dinya dake kusa da ita ta ciro wayarta ta bude sannan soma searching number'n sa cikin contact dinta wadda yayi mata serving da kansa ranar da bata da lafiya,tayi attempting din kiransa yafi sau goma ta kasa,sai ta fara dialing sai ta katse da kanta,bata san answer da kuma result da zata samu ba


Daga qarshe taga hakan bazaiyi mata amfani ba sai kawai tayi shahada ta kira din,yadda wayar ke qara yin din din haka zuciyarta ke bugu,idanunta a rufe gam tana jiran wayar....



Mrs muhammad dinku ce๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘



๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป




๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ
๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ๏ฟผ๐ŸŒบ



*PART 2*



7โƒฃ~~8โƒฃ



"Assalamu alaikum" dakakkiyar muryarsa ta doki dodon kunnen fadila,numfashinta ya dan dakata na wucin gadi,komai da ya danganci aliyyi jinsa yake har cikin jininta da bargo komai qanqantarsa kuwa,"hello waye ne?" Ya sake maimaitawa, "idan mai kira baida abun fada zanyi rejecting I have a lot to do"dadi muryar tasa ke mata har can qasan zuciyarta,zata so ta dawwama tana sauraren muryar idan da halin hakan,din din din da taji sau uku shi ya tabbatar mata ya katse wayar kamar yadda ya fada tun farko,ta saki wani dan murmushi da ya tsaya a kuncinta tana kallon fuskar wayar tata,tazarar minti biyar ta bayar sannan ta redial din number tasa


Tana daf da tsinkewa ya daga wannan karon ita ta fara yin sallamar ,yayi dan dum sannan ya masa a daqile sanan ya dora da "who's on d line?"cikin in ina ta soma magana don gaba daya dakiyarsa ta rudata "nice" "kewa"ya maida mata da tambaya,"fad...fadila"ya sake shiru na yan sakanni har tana tsammanin ko baya kan layi ta duba wayar sai ta ga yana nan


"What's going on?"ya sake tambaya,wani abu ya dan taba ranta da gaske bai ganeta ba har sai da yayi analysing a qwaqwalwarsa,"sister farida ce ta haihu" "uhm labari kike ban kenan?"ya fadi cikin watsar da muhimmancin batun a gunta,tambayar ta quleta hakan yasa tayi shiru,"me kike buqata ne ina fa da aikin yi"ta daure tace "baby nake son inje na gani" "ban amince ba"ya fadi kansa tsaye,din din ya katse wayar,wani hawayen takaici ne ya sulmiyo mata,tayi wurgi da wayar kujerar gefenta,cikin takaici ta figi motar sai gida


Danja na tsaida su tana ganin wani wani saurayi dake gefan tata motar yadda ya zuba mata ido da alama yana mamakin me ya sanyata kuka ne,ta kawar da kanta gefe cikin zuciyarta tana ayyana in banda babu kyau fita babu izini tabbas da sai tayi wucewarta gidan farida saidai aliyyu yayi tsirenta,ta share hawayen sanda danja ta sake su ta sake figar motar,tana kallon yadda saurayin ke sa mata signa yana son tsaidata tayi banza da shi ta qarawa motarta speed,ita kanta bata san tayi gudu haka ba sai da ta iso gida agogon wayarta ya harba taga yan taqitattun mintocin da suka kawo ta gida,tana qoqarin shiga gidanne bayan mai jire bakin qaton get din gidan ya dage mata qofa ta soma shiga taji wani horn din,ta glass ta hangota motar samira ce wadda take cin ubanta da hawa ta tabbatar da motar mutum ce da tuni ta dade da guduwa,ba samiran ba hatta qawayenta sai suzo su ari motar su wuni sur suna cin ubanta ko a daddoke mata ita su kuma dawo su yasar mata ita ce mai kudin banza ta gyaro ta zuba musu mai gobe su dawo su sake ara ita kuma ba lissafi ta basu saboda tsabar neman suna irin na samira,shi uasa tayi nacin aliyyu ya canza mata mota qememe yayi buris da ita don yana sane da abinda takewa tatan



Mrs muhammad ce



๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป



12:36 pm 22/8/2016
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*WA YASAN GOBE?..*
๐ŸŒบ??๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ






*PART 2*



9โƒฃ~~1โƒฃ0โƒฃ




Ta ajjiye motar a parking space ta kashe ta tana mai dauke idanunta daga kansu samira zuciyarta na tur da irin halayen mutanen da samiran ke mu'amala da su,hakanan ko yaushe zaka gansu cikin shiga ta banza da rashin da'a,yanzun ma qawayenta ne su uki ta dauko cikin motar kowacce kuma cikin shigar tasu dai ta dabi'ar da suka dorama kansu ,tana jin shewarsu sanda take rufe motarta kasancewar suna bayanta ne tsaye jikin motar samiran su basu shige ba hakanan basu komacikin cikin motar ba,sun saba yi mata haka tun ba yau ba kula su ne sam bata taba yi ba don bata kallonsu ma a matsayin cikakkun masu hankali,tana ganin idan ya kula su ma tamakar ta basu wata martaba da daraja ne,kallon tsiya ma basu isheta ba bare su sa ran wataran zasu samu na arziqi bare fadilan dama miskilar kanta ce sai ka gama cin kashinka a gabanta idan bata ga dama ba quda bazata kore maka ba


Kamar ko yaushe yauma har ta bawa banza ajiyarsu tayi gaba abinta maganar da ta jiyo suna fada ita ta sanyata dawowa da baya ta tabbatar ya zama dole yau ta yiwa tufkar hanci bare yadda take cikin takaicin hanata zuwa gidan farida da aliyyu yayi shewa suka yi sanda take yin gaban sannan daya daga cikinsu tace"badi'a (sunan daya daga cikinsu ta kama)saiki dinga fakewa da fita aiki ana yawo a kwararo


Da baya ta dawo sannan ta fuskancesu,dubansu tayi daya bayan daya up to down ta saki wata 'yar siririyar dariya tace "๐Ÿ˜ ai karuwanci iyawa ne kuma karba karba ce,๐Ÿ’๐Ÿฝwata hajar sai ta qaraci zamanta a kasuwa tasha qura tayi futu futu kullum kuma sai an fito da ita an kasa amma sai kiga ko kallonta al'umma basuyi bare su baqaci siya,kinga kenan inda wani yayi rawa aka bashi kudi wani idan yaje yayi dan banzan duka zaici


Ta sake watsa musu kallon raini sannan ta dora"ku ba abokan yina bane don ban hada sabga da ku ba wannan.....ta nuna samira da key din mota dake hannunta "itace abokiyar yina,ita din ma zata gaya muku inuwarta bata isheni kallo ba bare zahirinta,but.... well zan baku shawara guda daya hade da gargadi mai kama da jan kunne,shawara ta farko itace ku rufawa kanku asiri ku samu ku raba jikinku a dakin aure kafin a rasa mai kwasar ragowarku......๐Ÿ˜‚๐Ÿ™Š au am sorry na manta yanzun ma fa hakance ta faru da ku fa shi yasa kuke gararamba da yawon kwadayi da maula agidajen matan wasu



And gargadina shine kada wadda๐Ÿ‘‰ ta sake bude rubabban bakinta da niyyar shiga gonata don nikam duk cikinku babu wadda tayi isar da zan shiga gonarta,saboda haka nima akiyaye shiga tawa gonar๐Ÿ‘‰"ta kama kunnenta daya da hannunta tace"idan kunne yaji......gangar jiki ta tsira"ta saki hannunta ta juya da niyyar shigewa dukkansu sunyi mutuwar tsaye don nasu taba tsammanin ta iya magana haka ba a yadda samira ke basu labarinta,samiran ce tayi yunqurin nuna jarumtarsu tasha gabanta ta kama qugu tana cewa"ke qaramar 'yar iska mu kike nufin zakiyi wa rashin mutumci?"


Murmushi fadila tayi tace"๐Ÿค— a'ah sanin kanki ne fa ni ban iya hayagaga ba ke zaki fara baiwa wanda bai sani ba labari ,to kuwa akan wadancan๐Ÿ‘ˆ๐Ÿผ shashashan bazan fara ba"ta gewayeta tayi wucewarta,tana jiyosu suna ci gaba da kuri da cika baki kala kala akanta har suka wuce sashen samira,cikin ranta take fadi Allah ya bawa daya daga cikinsu sa'a tace zata biyota taga yadda ake rashin albarka


Wanka tayi don taji sanyin zuciyarta tuni ta watsar da batun su samira don basu gabanta hasalima bata daukesu wani abu ba don tasan baya ga tsabar jahilci dake damunsu rashin tarbiyya na bibiyar rayuwarsu,tana mamakin tsarin rayiwa irin tasu sam basu damuwa da yanayin da rayuwarsu ke gudana,falo ta dawo ta hada yoghurt mai sanyi da fura ta dama ta koma saman kujera tana diba da cokali a hankali tana sha zuciyarta sam bata gidan,kira ne na anty hafiza ya soma shigowa wayarta tana neman farida ne tayi ta kiran wayarta busy shine ta kira ko suna tare ta bawa faridan,nan da nan ta tabo mata miki basu gama sallama ba ta kashe wayar don bata son taji kukan da ya qwace mata,kamar kuwa hadin baki yan uwa ke kiranta suna cewa ita zasu yiwa barka itace uwar 'ya,hakan ya raunana zuciyarta sosai tasha kuka,sister faridanta guda amma wai a hanata ganin 'yarsu?


Har magariba jikinta amace yake,sai sannan ta tuna bata kira umminta ta mata barka ba,jin muryar ummin bayan ta daga sai ya karyar mata da zuciya kuka ta saki,a tsorace ummin tace "meye haka lafiyarki kuwa?"cikin kukan tace "ummi ya hanani zuwa ya hana ni inje inga baby ummi"ummin ta saki ajiyar zuciya sannan ta ja tsaki"wlh harkin tayarmin da hankali na zaci wani abune ya faru ko ya sameki?" Ta sake marairaicewa cikin muryar kuka tace "ummi wani abune mana sister farida fa ummi" "to sai me idan baki je din ba?,idan kinje ma me zakiyi mata iyakaci kije kuyi ta surutu,tunda Allah yasa an sauka lpy bashi kenan ba abunda dama ake buqata kenan"ta sake sakin kuka tace "ummi ki masa magana don Allah idan ba haka ba baza ni ba"kama haba ummin tayi kamar fadilan na gabanta tace"๐Ÿค”lallai bansan haryau quruciya na damunki ba fadila,to ba da ni ba wannan shiriritar,bana som sakarci ki maida hankalinki fadila kada na soma jin wani abu kuna jina ko?" A sanyaye ta gyada kai ta sani ummin bazata so ace bata je ba amma bazata taba bata goyon baya ba,halin ummimsu ne a gidan aure maca ce mai tsananin biyayya ga abbansu ko layi uaja yace kada ta tsallake to insha Allahu ba zata tsallake din ba hakanan kaf yaran babu wanda zata bari ya tsallaka hakan ne yasa har yau har gobe har ma jibi inji shi abban nasu yake alfahari da kuma ji da ita


Ta saki ajiyar zuciya bayan ta kashe wayar tana jan majina hadi da son maida kukan ta,alwala ta daura tayi sallar magariba ta zauna kan sallayar tana jiran a kira isha,hakanan fadila take tana da kwadayin wannan garabasa da ake samu ga duk wanda ya idar da salla bai kuma tashi daga gurin ba,jira ne baifi na awa daya da rabi ba aka tada isha'i ta gabatar da ita duka harda shafa'i da wutiri sanann ta sake zama ta karanta subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azim,don kanta ta gaji da zaman ta ninke abun sallar ta maida shi muhallinsa ta baro dakin sa hijabinta a jiki don dumin cikin hijabin ya mata dadi


Cartoon ta maida tana kallo kan tashar m.b.c 3,lokaci lokaci tana sakin ajiyar zuciya saboda kukan da tayi,sannu a ahankali ta soma jiyo qamshinsa ,ta daga fararen idanunta ta maida su bakin qofar shigowa falon,cikin nutsuwa da sallama ya shigo yana sanye da jacket black blue sun haska farar fatarsa,sunyi amsarsa matuqa da gaske adorable structure dinsa ta fito sosai,sassanyan kyawunsa din nan ya bayyana cikin kamilalliyar tafiyarsa ya qaraso falon hannayensa sarqe a qirjinsa,can qasan maqoshinta ta amsa sallamar carelessness ya samu hannun daya daga cikin kujerun ya zauna ba tare da ya dubeta ba


With bounded face yace"ki fito na miqaki kiga baby"tamkar tayi banza da shi ko tace ta fasa sai taga idan ma tayi hakan ai kanta ta yimawa ba wani ba don shi kam bashi da asara,ta miqe kamar marar laka ta shige bedroom dinta tana qunquni qasa qasa"sai an ma gama qonawa mutum rai sannan za'a wani tasa shi a gaba akaishi kamar wani dan qanqanin yaro" "idan baki zuwa ba saiki zauna ba ke ya shafa"ya fada a tsawace,baki ta rufe da sauri ta qarasa shigewa bedroom din don batayi tsammanin ya ji ba,lallai shi kuwa wane irin kaifin ji gareshi take mamaki cikin zuciyarta




*NOTE*: assalamu alaikum masoya littafina saqonninku nata isheni da maganganunku game da littafina,duk da cewa na sani nayi muku bayani tun a farko na yadda rubutun zaici gaba da kasancewa sakamakon shirin fitar da shi kasuwa,na dauka tuni mun wuce gun saboda banyi zaton zanci gaba da baku shi littafin ta watsapp bama amma yanayin yadda kuke nuna qauna gameda da shi din yasa naci gaba da rubuta mukun duk da na rage yawansa kamar yadda na fada,
To amma naga rashin fahimta na son shiga ciki,na farko har ga Allah yadda wasunku ke min bana jin dadi yana bata zuciyata,saboda bani da wani uziri da zai taso min a matsayina na yar adam a gunsu abunda kullum suke buqata shine nayi musu kawai typing na turo musu,sannan wasu babu yabawa saidai qorafi da zarar sun gama karanta wanda na samu na turo,hakan da suke yana kashemin gwiwa ne,maimakon suyi abinda zai qarfafa min gwiwa ko saboda gaba kada ku manta hannu ne keyi ba fada muke wayar na rubuta mana,kuma yau da gobe ai sai Allah,ni 'yar adam ce gsky da bana son abinda zai dameni ko ya samun damuwa a zuciyata nakan haqura da abubuwa da dama matuqar zasu jawomin damuwa,don Allah ina roqonki ku tsaya kuyi duba na fahimta game da ni,ni ba budurwa bace matar aure ce ku duba kuga yanayin hidimomin gida na kullum dake kan matar aure baya ga wadanda ka iya taso mata wadanda bata tsara da su ba a rana,ku dinga adalci kuna hukunci na gaskiya,mu fahimci juna don Allah wannan shi zaisa ni daku muci gaba da jin dadin alaqar dake tsakaninmu,wlh akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a rayuwata da nake yi kulluma da kafin fara muku rubutu amma a yanzu sun gagareni yi saboda rubutunku,na sani harka ta mutane sai kayi haquri tunda yadda muka banbanta a halitta haka Allah s.w.a ya ban banta mu a halaye da dabi'u,na gode Allah yasa mu dace๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป


Na biyu kuma masu ganin abunda aliyyu yake yayi yawa kada kusa gaggawa a lamarinku kuma kada ku manta shi haquri shine jagoran kafatanin lamuran mu na duniya bare haquri ga 'ya mace kuma acikin gidan aurenta hanyar shiga aljannarta riba ce ba kadan ba,ina so ne yan uwana mata muyi koyi da halinta koda cewa ba irin auren ta kikayi ba amma nasan baza'a rasa matsala daya ko biyu da kike iya fuskanta ba daga mai gida wadda shigen halin da aliyyu ya taba nunawa fadila ne to ga yadda ta shanyeta ga kuma ribar da ta samu,na godewa masoyana gana daya ,Allah yayi mana sakamako agidan aljanna ya hadamu dukkanmu a cikinta in kuma ci gaba da zama marubuciyarku ta gidan aljanna ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€๐Ÿ‘๐Ÿป


Mrs muhammad din[truncated by WhatsApp]

4:50 pm 23/8/2016
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*WA YASAN GOBE?..*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ





*part 2*



1โƒฃ1โƒฃ&1โƒฃ2โƒฃ






Powder kawai ta shafa a fuskarta ta shafawa kyawawan labbanta lip glosses,atamfa ta zaro cikin kayan nata dinkin doguwar riga ne mai umbrella ta bude sosai an mata dogon hannu simple style ne,ta ware dan madaidaicin mayafinta ta yafa shi har saman kanta kamar yadda ta saba yafenta sannan ta fesa turare ta fito


Yana tsaye a wajen motar yana amsar calling yayin da salima ke tsaye kusa da shi hannunta harde a qirjinta tayi kicin kicin da fusaka,sallama fadila tayi mata sai taga ta dauke kai don haka sai ta ja tunga itama tayi banza da ita,ya gama amsar kiran ya kashe wayar hannunsa na kan mabudin motar salima ta kalleshi tace"please dear"kai ya gyada yana cewa"dont mind" ya bude gidan gaba kusa da kujerar mai tuqi ya zauna ta bude baya itama ta shige,nasiru ya gaida ta cikin girmamawa a mutunce ta amsa sannan ya tada motar suka fice


Tafiya ce kamar ta kurame sai ka rantse bata cikin motar sai shi da nasirunne ke hira jefi jefi galibi ma bai wuce zancan kasuwa,idanunta na kan titi yayin da zuciyarta ta lula duniyar tunani


A bakin get suka dakata bayan mai gadin ya dage masu get aliyyu yasa nasiru yayi masa magana ya rufe ba shigowa za suyi ba,fadila ta tabe baki cikin ranta tana gulmar aliyyun,nasiru ya gyara parking din sannan ya fice daga cikin motar,fadila ta sa hannunta a kan mabudi zata fice "twenty minutes"haka ya fada cikin carelessness,ba abunda tace da shi tayi ficewarta "ko baka gaya min ba ai na sani uban masu tsari da qa'ida na duniya๐Ÿ˜™"tayi zancan cikin zuciyarta


Da yake takwas na dare ma ta dan gota gidan ya samu sararawa daga cincirundon 'yan barka mutum hudu ta tarar Amina da mariya qannan mubarak ne sai maqociyarta guda daya sai kuma wata dattijuwa inna jummai wadda mahaifiyar mubarak ta kawo mata ita saboda kula da mai jegon da kuma jaririyar,alokacin da ta shiga ma tana kitchen tana kwashe tuwon da ta yiwa faridan,fadila nata qyalqyala dariya ganin inna jummai nata loda tuwon a flask tana ce mata"inna zanso naga dambarwar ku kam da farida don ba abincin da taqi jini irin tuwo,dama dai ni kika baiwa"innan da yake macace mai kirki da saurin sabo da jama'a tace"ai duk qinta kuwa da tuwo yanzu ya zama abokinta dole ta cishi tunda jego ya zo"


Tayi sallama ta shiga falon faridan dukkaninsu suka amsa mata cikin fara'a suna dariyar hirar fadilan da inna jummai,farida kam ture kayan jarirai dake gefanta take tana cewa sister taho nan daya hannun nata kuma cup ne cike da tea tana sha sai hada gumi take inna kuma taqi ma a kunna fanka bare a.c saboda wai jego faridan zatayi irin na da,fadilan ta qaraso tana cewa "๐Ÿค”sister farida mai tsokana da yawon gidan qawaye yau gata dq baby" dariya ta basu dukkaninsu harda faridan,idanu fadila ta baza tana neman baby tace nifa baku nazo gani ba wlh ina 'yata ku bani ita naji duminta"yarinyar na hannun maqociyar ta ta nannade cikin farin shawul mai taushi ta miqe tana miqawa fadila ita hadi da yi misu sallama ta ajjiyewa faridan 1000 kudin barka ta mata godiya ita kuma ta fice


Ta kammala shanye tea din tas ta dire cup din tana kallon fadila tace "sister da fa har nayi fushi kece ta farko da kika fara sanin haihuwarnan baya ga abbanta amma sai yanzu zaki zo mana tun dazu baby ke son ganin mummynta bata zoba sai da aka rigata gane mata ita" "hmmm lallai yarinyarnan kukan dadi fa kike da yaya yanzun ma ya barni tare ma fa muke"cikin zolaya wadda attitude din farida ne tun usulinta tace "wow kice har an fara boyonki lallai soyayya ruwan zuma"fadila ta harareta tace "wlh badan kin mun abun kaiba kin bani baby mai kama da ni ba da sai na bubbuge bakinki"su amina suka qyalqyale da dariya sannan suka miqe suka ce bari dai mu baku guri kada a buge mana anti a gabammu"dariyar suka bawa fadila su kuma suka fice kitchen gun inna jummai


Fadila ta sake zubawa yarinyar ido tubarkallah masha Allah qatotuwa da ita lallai kam wannan photo copy dinsu ce ta kalli farida tace sister sannu"farida ta ya da kai gefe tana tuno wuyar da ta sha"hmmm ke dai bari sister ansha gwagwarmaya ni kam dan ba qara"fadila ta sake rungume yarinyar a qirjinta tana sake jin qaunarta na shigarta bata qi ace tata bace,ta saki dariya tace "yanzun fa aka fara farida me akai da maza daga ihu daya sai kuma murya ta dashe?๐Ÿ˜œ"ta qarashe ta sigar tsokana yau dai ta maida raddin tarin tsokana irin na farida da take mata ko yaushe,ko da can dama fadila Allah ya zuba mata son yara,sanda suka tashi muhammad ne kawai yaro a gidansu to har gidan maqofta take shiga dauko yara duk da yanayin unguwarsu irin unguwan nin nan ne da ba ruwa na da kai kowa na qulle shi da ahalinsa cikin gida amma haka fadila ke shiga ta taho da su,miskila ce ako ina magana bata dada ta da qasa ba amma banda kan yara hakanan zaka ga ta sasu a gaba suna ta wasansu,farida kam dama idan taga dama idan suka zo neman anty fadila sai ta korasu tace bata nan zasu zo su dameta ne


Farida ta girgiza kai da sauri tana juya ido tace "kai sister is hardly in sake ko zan qara sai after five to ten years,nikam na barmiki ki taba kiji"dariya ma ta bata ganin duk yadda tayi laushi duk rashin tsoro da dakiya irin na farida,murmushi fadila tayi tana ci gaba da kallon yarinyar tayi kissing dinta agoshi,"ina aliyyu ne sister?"๐Ÿ™„af yana waje " farida ta miqe daga kashingidar da tayi tace "kada dai kice mun kuna tare yaushe ya aliyyu boss ya fara kai matarsa unguwa"fadila tace"saboda ya bata min ya fara ta kaina yau kina gani fa kamar gidqn nan yace min wai twenty minutes?"farida tace "wlh am serious ya aliyyu ko salima matarsa ta farko bai taba kaita wata unguwa ba idan ba monthly shopping naku ba(farida ta fi fadila sanin halinsa ne kasancewar tq fita

Please Login or Register in order to submit comment