Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda kike so ba" nafisa ta ce"ina
tsoron kada in fada zina ne,kin san zuciya bata
da qashi" hajara ta gyara zama tace bari in
wayar maki da kai. Sai da ta sake gyara zama
tare da numfasawa sannan ta ci gaba da
magana a nutse.
Ni hajara tunda na taso na kasance mai son
hulda da masu kudi,duk da iyayena masu
karamin karfi ne.Lokacin dana zama budurwa
duk kyau baya sharaba ne,saurayi in ba shi da
mota bana fitowa,cikin haka muka hadu da
alhaji kabiru lokacin na zo abuja tare da wata
amarya makociyarmu dana rakota biki.Muna
haduwa ya soma yi min barin kudi,nan fa na ce
naga miji.Lokacin ina (SS3) ai ko tuni na saki
makaranta muka yi aurenmu.An kashe kudi
kamar tsiya,don duk unguwarmu a keffi ba a
taba shagali da barin kudi kamar na bikina
ba,tunda aka kawo ni mijina baya kula ni har
kusan wata na yi masa magana sai yace min
ba shi da lafiya kamar dai naki din nan. Muna
nan zaune a haka saboda kudin da nake samu
wata rana naje wani super market siyayya sai
naga wani dan saurayi mai kyau nan take naji
sha'awar shi don haka sai nace masa suna da
motar kai ma mutane kaya gida? Yace in an
siya da yawa ba. Na ce shi nake son fa ya kai
min don na kula yana da nutsuwa.yace sai dai
in ma Ogansu bayani. Ta dubi nafisa ta ce kina
fahimta? Nafisa ta ce,"eh" hajara taci gaba da
cewa na yi ma ogan nasu bayani sai yace ba
damuwa. In gaya miki Nafisa nan nayi ta lodar
kaya aka cika mota. Muna zuwa suka yi ta
saukewa suna shigar min dasu to dama da
cikon kudi na ce ya zo ya karba,ni kadai ce
lokacin Alh kabiru yayi tafiya. Yana zaune falo
nace mashi ya sunansa? Ya ce bello nace ina
zuwa bari in kawo mai kudin ko? Na yi dabara
na kulle falon nan koma daki na cire kayana na
fito.(Wa iyazubillah) Ya tsorata ya tashi zai
gudu amma kofa a kulle nace mishi ka nutsu
ka biya bukatata zan baka ko nawa kake so
tace in takaita miki Nafisa sai da na dire mishi
dubu dari sannan ya yarda. Daga nan muka
saba da bello har kwana yana zuwa yayi,Na ce
ma 'yan aikina kanina ne. Nafisa ta ce Alh
kabiru kuma bai gane ba? Hajara tayi
murmushi bai gane me ba? Ai kin Allah daga
baya har kudin da zan ba maza yake bani
kuma cikin Ummi ina zaton na bello ne. Alh
kabiru shi yayi komai saboda ba ya so
danginsa su san baya da lafiya,ya ce min zasu
yi masa dariya amma cikin Abba ban san na
wanene ba,tunda lokacin na samu samari da
yawa"
Nafisa tai zugum cikin matukar al'ajabi, sannan
tace, "km har yau kina hulda da maza? Tace
"sosai ma, ynxu da likafa ma tayi gaba ina
xuwa dubai sarin kaya, kin san ina da shago
nima inda na dora bello yana kular min dashi,
can nake holewata da duk namijin da yai min,
jm in gaya miki dk abokansu hk suke basa
amfani da matansu". Nafisa tace "dk aboknsu
fa kika ce? Hajara tace Eh, gashi km suna
dayawa, kowanne matar shi hoto ce. Amma bai
damu tabi wani ba. Hk nan suna rike yayan da
dk matan suka rero a waje". Nafisa tace "kai
nidai bazan iya aikata zina ba da aurena. Wnda
nayi da ma ina neman gafara. Hajara tace gara
ma ki huta in ba hk ba kya tsufa dn shi ba
sakinki zai yi ba hakanan in kin haihu zai fi
sakar miki kudi fiye da ynzu. Nafisa tace ni
mamakina ma ace dk group dinsu basu da lfy,
to ya akayi hk? Hajara tace su dai suka sani,
ke dai kiyi hrkar gabanki". Tnda nafisa taji
wannan batun, hnklnta yai mu2kar tashi, data
dawo gda ma sai tufka take tana warwarewa
amma da yake son abin dunia ya rufe mata
idanu ta kasa tsaida tunaninta ga ynda zata br
gidn alhji jamilu, tafi maida kai ga tunanin ynda
zata samu wanda zasu aikata laifin.
Yau satinsu 1 da tarewa, dk da bb abnda ya
shiga tsakaninsu na auratayya, suna mu2nta
junansu. Mahmud a ganinshi iklima bata da
matsala illa rashin iya kwalliya da salon mata
gurin jan ra'ayin miji, sai dai zuciarshi tana
yawan shaida mishi cewa kada yayi saurin
yanke mata hukunci, ya bari zama yai zama.
Ita kuwa nata gefen tana fassara mahmud a
mu2m mai saurin fushi, miskili. Sai dai yana
burgeta gurin kula da ibada, da km tsafta ga
iya sa tufafi, uwa-uba kasancewarshi mai yin
komai cikin kuzari, hakan na birgeta.
Ya shigo da sallama hannunshi rike da leda ta
tashi da sauri ta aje fiqhun da take dubawa,ta
amshe shi tare da cewa "sannu da zuwa ka
dawo lafiya?" Ya fadada murmushinsa ya
ce"lafiya lau ya ki ka yini?" Ta ce fyn. Ya
murmusa tare da baba muke fa,zai zo nan
muka hadu na taso shago. Tace "yana ina
yanzun?" Yace yana zaure (soro).ya dauki
tabarma ki zo ku gaisa. Da sauri ta sako dogon
hijabinta ta dauki jug da ruwa da kofi ta nufi
zaure gefen tabarma ta zauna cikin fara'a tace
sannu da zuwa Baba nayi miss naka. Cikin
shagwaba tayi maganar.
***Ya murmusa sannan ya dubi mahmud
wanda ke tsugune gefe ya ce,Malam mahmuda
ya ya harkokin? Ya ce lafiya lau Baba. Iklima ta
gaida mahaifinta tare da tambayr nafiu bai zo
ba. Yace kasuwa muke zuwa dashi,daga can
yake zuwa makaranta in sun taso ma can yake
wucewa. Haka nan lokacin islamiyya. Iklima
cikin damuwa ta ce Mama fa? Yace tana
gidanta. Yayi saurin kauda maganar da cewa
iklima kuna lafiya ko? Ya dubi mahmud "lafiya
lau muke" yace maigidan naki shima lafiya? Ta
dubi mahmud din shima ya kalle ta suka
murmusa. Ta sunkuyar da kai tace lafiyan shi
lau Baba, yace to madalla. Mahmud zai mike
yace zauna,da farko zan soma da yi muku
nasiha da kuyi hakuri da juna,ku kashe ku rufe
tsakaninku Allah yayi muku albarka da abinda
zaku haifa. Mahmud yace Amin sun gode.
Yasa hannu cikin aljihunshi ya ciro kudi sababi
yan 500 yace bismilla kirga min wannan mal.
Mahmud. Mahmud ya amsa ya kirga su dubu
hamsin. Ya sake ciro wasu yan 100 ya mika
mashi ya gama kirgawa dubu ashirin. Yace to
kinga abinda yayi saura cikin kudin gida da aka
samu,gidan naira miliyan biyar da dubu dari
tara an saida mota sannan na bawa mutane
dangi da makota duk sun sa albarka.malaman
kuma duk an basu. Sannan neman taimakon
da masallacin makarantarku ke yi mun saka
maki dubu dari sadaka. Iklima tace nagode
baba,to kai ma ka dau wani abu, ya ciro 30k
yace gasu nan na dau 30k Allah yayi muku
albarka. Suka ce amin. Ya dubi mahmud gida
kuma yana matsayin nata ko bayan raina nasa
an rubuta takardu da sunanta. Nan take ta
hade fuska, baba ni fa kai na bawa kyauta
naka ne. Yace a'a iklima hajji dai naje Allah
yasa munyi karbabbiya amma gida fa naki ne
za dai mu zauna mun huta haya. Ta dubi
mahmud don Allah Yaya kasa baki.
Mahmud yayi murmushi sannan yace kiyi
hakuri da yanda baba yace in kin lura da
bayanansa sun riga sun gama komai,ta karyar
da kai gefe tare da cewa shi kenan.ya mike
tsaye,to ni zan tafi. Tace Ba ka fa sha ruwan
gida na ba.yauwa baba ina ku ke samun
abinci? Ya yi 'yar dariya,saye muke yi. Tace
baba don Allah kayi duk wani kokarinka don
mama ta dawo, yace ta ki iklima yaya zanyi da
ita? Su su hamza ma tuni sun zo min da batun
wata mace da mijinta ya rasu,'yar jalingo ce,sai
dai sun ce bata haihuwa amma tana da
matukar hakuri.iklima tayi kici-kici da fuska,to
yarda kayi Baba don Allah? Yace iklima su
hamza kannaina ne amma ba zan watsa musu
kasa a ido ba,dole nayi aure ko don girki yanzu
da haka ranar juma'a za'a daura auran. Sune
suka biya sadaki.iklima ta tabe baki sannan
tace shi kenan Baba sai an kwana biyu. Yace
to iklima a dai yi hakuri naga ranki bai so ba.
Suka fita da mahmud ita ko sai data koma daki
sannan lamarin auren mahaifinta ya dagula
mata lissafi.
MABUDIN WAHALA 2**3
Harara haule ta zabga mata "nayi kama da
matar babanku ynxu? Ta xaro idanu "ba
danginsa sun aura mishi daidai shi ba? Na
wuce da ajinsa". Ikilima tayi dim. Sannan tace
ki daiyi naxari mama, ki dawo sbd ke da baba
baxaku taba samun kamar juna ba, mu yaya
kuke so muyi? Haule ta sake xabga mata
harara tare da cewa in kika cikani xan tashi na
zane ki ba ruwana, laifina ma kike gani? Shi ya
sake ni ko ni na saki kaina? Haka nan bani da
kmr nafisa dk cikinku km dk wnda yace
bayason nafisa nima makiyi nane
Iklima tace,mama dukkanmu muna son Ya
nafisa,matsalarsu da Baba ni ce na kasheta da
na auri wanda Baba ke so.shi kenan tazo
kawai ta ba Baba hakuri ke kuma dama a cikin
musulunci in mutum ya saki matarsa saki daya
ko biyu in dai bata yi idda ba yace ya maida ta
to ta maidu kuma kinga tuni baba yace ya
maida ki. Tace,"ban koma ba me shegen tsarin
tsiya,yaushe aka haife ki da har zaki ce min
musulunci yace kaza? Ni ai kin san tuba nayi
da zaki ce min a cikin musulunci. Iklima tace yi
hakuri. Yaro ya shigo da sallama,haule tace kai
wa kake nema ne ka shigo min gida ba notice?
Kazamin yaro dube shi dan talakawa kawai.
Iklima ta zaro ido tana kallon mahaifiyarta.
Yaron yace wani ne a waje yace iklima tayi
sauri ko ya tafi. Tasan mijinta ne don haka tace
ma yaro "kaje kace gani nan zuwa.Haule tace
ke da waye? Tace mahmud ne ya ce in
gaisheki. Ta ja tsaki,shine yaja tunga a waje ko
ya shigo,ina ruwana dashi? Har yake zai tafi.
Mota ya siya ya kawo ki? Tace a'a a kafa ne.
Haule ta sheke da dariya "ba dai kinji kin gani
ba,haka zaku kare rayuwarku. Kowa yana abin
arziki ban da ku. Iklima tace mun tafi
mama.amma kiyi nazarin maganganuna.tace
nace miki fa ba zan yi ba koda baban naku
yace ya maida ni ban koma ba.iklima ta wuce
ranta a bace. Mahmud ya dube ta kin shanya
ni. Tace,yi hakuri. A gidansu ya barta gidan yai
mata kyau,matar baban nasu mai tsafta ta
amshi iklima hannu biyu.
Ta sauke abinci ta zuba ma iklima,Nafiu ya
dawo makaranta yana tamurnar ganin ikilima.
Daga ganinshi ka san yana samun kulawa tsaf
dashi.da suka yi sallah tace da iklima tsefe kai
in maki kitso. Iklima tace kan nawa ma a tsefe
yake. Nan kuwa matar baban nasu ta yarfa
mata kitso kanana yayi kyau.Tana ta godiya
tace ina ma zan samu wadda ta iya lalle da ta
zana min. Matar baban ta ce "Nafiu in kasa
kayan islamiyyar shiga nan makota ka gani
yarinyar nan naja take ko wa? Nafiu yace eh
sunanta Naja tana yin fulawa sosai bari na kira
miki ita Ya iklima. Tace to. Naja kam ta zana
mata fulawa mai kyau ta biya tana ta yabawa.
An soma kiran sallar magriba,babansu ya
shigo. Cikin murna take mishi sannu da zuwa
shima da fara'a.yace iklima ke ce? Ta ce,"eh,ai
nan na yini" yace lafiya dai ko? Ya ya ba kije
gida ba? Tace zai zo mu tafi yace min. Baba
yace,to madallah,hakan ya yi kyau dama baki
san uwar taki ba,itama tana taso nafiu ya
rakota bai san gidan ba,tace" to baba da kai
baka raka ta ba? Yace bari muyi sallah sai na
zo mu gaisa sosai. Iklima tana lura da duk
yanda matar Baban nasu ke gudanar da
lamuranta. Bata tsinke ba sai da taga yanda
take karrama babansu gami da girmama
shi.lokacin da tazo ma kayan baban ta samu
tana wankewa dana nafiu,tun daga mam ta
san cewa ko mamansu ta dawo dole ta gyara
zamantakewar su in ko ba haka ba sai dai ta
zama yar kallo. Don shi namiji dan son
tarairaya ne da kula komai tsufansa. Tunda ta
taso ko babansu bashi da lafiya bata taba
ganin mamansu ta wanke mishi kaya ba,sannu
da zuwa kuma in kaga ta mishi to ta hango
leda a hannunshi cike da cefane. Bayan sunyo
sallah sun dawo nan suka zauna suna ta hira
tare da cin tuwo miyar kuka.sai bayan isha'I
sannan mahmud yazo.Sun gaisa da su baba
sannan suka tafi. Baban yana ta sa musu
albarka. Mahmud ya yaba kitson da lallen
sosai har sai daya biya kudin da aka yi su.
Zaman su kam ba laifi suna kula da juna zuwa
yanzun iklima tana ganin bata da kamar
mahmud,sai dai shi yana ganin akwai abubuwa
da yake so mace ta ringa mishi ita kuma bata
iya ba.don haka nashi ganin rashin wayewarta
ce matsala in ba haka ba sai yace tayi.
Nafisa tana tsaye bakin kofar motafta tana
kallon yaron, matsahi yana loda mata kayan da
ta siya a cikin boot yayi mata kama sosai da
Mahmud dinta, illa manyan ido da Mahmud din
ya dan fi wannan saurayin, hatta sajensu daya
ne.. Yace an gama hajiya. Ta dybe shi da
murmushi. "Ya sunanka?" Yace "Timo". Ta
sake dubanshi "Kai ba musulmi bane?" Yace "
a'a". Tace "kayi kama sosai da musulmai"
yace "haka mutane suke cewa." Ta ciro yan
dubu dubu guda biyar ta mika mishi. Ya yi ta
godiya, ta shiga mota ta tafi.
Cikin kwanakin shedaniyar zuciyarta ta gama
saka mata yanda zata shawo kan Timo, amma
tana tsorin Alhaji Jamilu ya sani ko ya gani,
sao dai Allah ya sa shima irin mijin Anty Hajara
ne ko ya gani ba ruwanshi. Ta a cikin wannan
tunanin a lambun shakatawarsu sai ta hango
wadansu samari biyu za su shiga falonsu. Ta yu
kura da nufin yi musu magana, idonta ya
sauka akan Alhaji Jamilun, shima ya tasanma
shiga falon, ta koma ta zauna tana mamakin
yanda samari ke yin safa da marwa a cikin
gidan, matsawar yana gari, koda yake yace
mata aiki yake samar musu. Ta jima tana
tunani, sannan ta mike ta shiga ciki.
Falonshi ta nufa don ta manta ma yayi baki, da
baza taje ba tunda y sha sanar da ita cewa in
yayi baki ta daina zuwa don yana da kishi.ta
shiga falon kanta tsaye, wani irin nishi ta jiyo
daga dakinsa.. Gabanta yana faduwa ta nufi
dakin ta tura. Numfashinta ya dauke tare da fadin
"innalillahi,
A'uzu billahi! Me zan gani?" Ta fada ta tashi
zata fita da gudu, yace da na tsayen, "riko min
ita" wanda ke tsayen ya cafko ta sannan ya ce
"kulle kofar ka cire key din.
Nafisa ta zube tana wani irin kuka, a gabanta
ya aikata alfasha da dayan, dukkansu da ya
gama sai da yasa wani farin kyalle ya kwashi
wani abu a al'aurarsu, sannan ya duko wannan
jakar tashi ya ciro daurin yan dubu dai dai ya
basu dubu dari dari, sannan ya zira jallabiyarsa
suka yi sallama tare da ce masa sun gode.
Ya juyo yana kallonta "leke lekenki na tsiya ya
sa kin leko abinda yafi karfinki, to bakinki kanin
kafarki.". Ya jawo wata dirowa ya ciro bindiga
ya nuna mata, "zan iya karar da danginku kaf
da wannan in na samu labari gurin wani, haka
nan zan kashe duk wanda kika gaya na
wannan sirrin ko da uwarki ce. Sannan bazan
taba sakinki ba, taimako daya zan miki in kinga
wanda kikeso ki kawo shi ki kwana da sbi ba
matsalata bace." Cikin kuka tace "kaji tsoron
Allah ka tuna zaka mutu ka tuna da
kwanciyar..." Ya dauketa da wani makahon
mari har ta gigice. Yace "baki da hurumin yi
mun wa'azi, kudi kika gani kudi kika aura, kudin
kuma nake baki." Cikin kidima tace "kudin ludu?"
Yasa kafa ya
shure ta sannan ya take ta da kafsrshi "in kin
sake magana sai na karar da numfashinki."
Shiru tayi don tayi mutukar tsorata da shi. Ya
jata ya fitar da ita daga sasanshi ya yar tare da
cewa "ina jaddada miki ki iya bakinki." Ya fita
abinshi. Ta ja jiki ta nufi dakinta, kan gado ta
zube. Ina
ma ace iyakarshi bai da lafiyar ne kawai ba
wannan mummunan kazamin laifin yake
aikatawa ba. Lallai tayi mutukar da ta sani a
rayuwarta, yau tga lidi da idonta, abinda take
jin labarinshi.
Ranar kwana tayi kuka, daga bisani ta
dangana. Washegari ta nufi gidan Anty Ajara
tana kuka, amma ta kasa gaya mata abinda ya
faru saboda mijinta ya gargadeta. Amma ga
mamakinta sai taji anty hajara tace "na jima
ina sa ido ki zo min da wannan kukan amman
sai yau"
Nafisa ta dube tq "ban gane ba" anty hajara
tace "nutsu in ganar dake." Nafisa ta share
hawayennta tare da jan hancinta tace "ina
jinki." Hajara tace "Duk mazanmu sirrinsu
kenan na siyasarsu da harkokinsu. Shine yasa
basa iya amfani da mata sai dai ludu, ko bashi
kika gani ba?"
Nafisa tace "Wa'iyazu billahi! Na shiga uku!"
Hajara ta bata rai, "ke don Allah dakataa min, a
zamanin nan in dai kika ce kwadayi ne to fa sai
kin ga haka. Babbab gida kike so da babbar
mota, kin samu. Don haka dole ki jure ki zauna
da shi, in ma kin nutsu in ma baki nutsi ba,
tunda kika ga sirrin shi dayan biyu ne, ko ko
zauna dashi ko ki rasa baki, in har an barki da
rai kenan. Zaki daina magana kwata kwata
don kada ki tona sirrin. Nasan ya fada miki ko
mahaifiyarki baya so t sani ko?"
Ranar kwana tayi kuka daga bisani ta
dangana.washegari ta nufi gidan anty hajara
tana kuka amma ta kasa gaya mata abinda ya
faru saboda mijinta ya gargade ta. Amma ga
mamakinta sai ta ji anty hajara tace na jima ina
sa ido ki zo min da wannan kukan amma sai
yau. Nafisa ta dube ta"ban gane ba? Anty
hajara tace nutsu in ganar da ke, nafisa ta
share hawaye tare da jan hancinta tace ina jin
ki. Hajara ta ce duk mazanmu sirrinsu kenan
na siyasarsu da harkokinsu,shine yasa basa
iya amfani da mata sai dai ludu ko ba shi kika
gani ba? Nafisa ta ce"wa'iyazu billah,na shiga
uku" hajara ta bata rai,ke don Allah dakata min
a zamanin nan in dai kika ce kwadayi ne to fa
sai kin ga haka. Babban gida ki ke so da
babbar mota kin samu. Don haka dole ne ki
jure ki zauna dashi in ma kin nutsu in ma baki
nutsu ba tunda ki ka ga sirrin shi yanzun dayan
biyu ne ko ki zauna ko rasa baki in har an barki
da rai kenan.zaki daina magana kwata kwata
don kada ki tona sirrin. Nasan ya fada miki ko
mahaifiyarki baya so ta sani ko? Nafisa ta daga
kai,hajara ta ce "to kiyi ceton ranta don yanzun
duk lamuranki za'a sa ido a kansu. Nafisa tayi
kuka har ta gaji har dare sannan ta koma gida.
Da yake itama shedaniyar kanta ce kafin sati
shedan ya gama toshe mata basira. Hajara
tazo har gida ta sake yi mata famfo,alhaji
jamilu ya sake sakar mata kudi tare da bata
damar yin hulda da dukkan namijin da take so
har yake ce mata har da masoyinki mahmud in
kina so. Tana mamakin yanda yasan mahmud
masoyinta ne. Ranar nan fa har dawainiyar da
mahmud din yayi mata sai da ya fada
mata,wannan ya nuna mata Alh jamilu yasan
komai nata kenan kuma yana bin diddigin duk
inda taje.
Nafisa bata yanke shawarar bin wani namiji ba
duk da tana son timo,albarkacin kamannin shi
da mahmud.cikin dan lokaci Hajara ta fita da
ita cikin sauran matan abokansu idanunta suka
kara budewa da ganin yanda matan ke
fantamawa da kudi.wata rana sun je birthday
party din yar Alh hashimu abokin su Alh
Jamilun ne shima.matarsa laila irin fulanin nan
ne mai kyau. 'Ya'yanta uku,Nafisa tace da anty
hajara "yanzun wannan ma ba yar Alh hashimu
din ba ce? Hajara ta ce duk wanda ki ka gani
cikin grp din nan ba yayansa ba ne.Sai dai yan
kadan daga ciki masu yara yan shekaru sha
biyar zuwa sama.to manyan yayan su ne kafin
su shiga kungiyar,amma duk wanda ya shiga
to fa shi kenan. Nafisa tace mamkin da nake ji
ki ga suna ta ji ya'yan. Hajara tace iyi to ai
hakan shi ne rufin asirinsu shi yasa ki kaga
suna kiran yan jarida don su nuna ma duniya
cewa suna da ya'ya ba za'ayi musu wani zato
ba. Lokacim da taro ya ragu sai matan abokan
suka hadu suna ba juna labarin lamurransu.
Nafisa sai raba ido tana sauraron abubuwan
tamkar almara.Sima ce ta ce,hajara zuwana
dubai din nan naji dadinsa,sauran suka ce kun
samu kaya kenan? Sima tace,yaushe ma ni
nabi takan kaya? Tun a jirgi idanuna suka
kyallo wani bawan Allah zuciya kuwa ta
kwadaita dashi duk na kasa sukuni shi kuma
daga ganinshi kamili ne sai Allah yasa (hotel)
daya zamu sauka dashi.da dare na dan fito
shan iska sai ko na hango shi yana zaune kan
wata kujera irn mai lema din nan na nufi
gurinshi da biyu.na isa da sallama cikin
mutunci na zauna na tambaye shi yace bismilla
zauna mana. Sima tayi yar dariya tare da
cewa,kun san abinda ya kara birge ni da
wannan mutumin? Suka ce"a'ah. Tace ina
danna waya tamkar me neman wani abu shi ko
iyalanshi ya kira. Hankalina na gurinshi suna ta
hira a bashi yaransa suka gaisa sannan suka
ci gaba da hirar soyayya da matarsa. Yana
gaya mata I miss u,I luv u,I need u da
sausaran hirarrakinsu na miji da mata. Sai naji
zuciyata ta kwadaitu dashi,tashi nayi naje
dakina ina ta shiya yanda zan has kanshi don
daga ganinshi kamili ne. Tace can na dawo na
same shi zaune har lokacin wayar yake nace
"bawan Allah don girman Allah zo ka min
taimako wani abu a dakina ba zan iya fitar
dashi ba. Ya dube ni kamar zai ce ba wani
kwaron da zai shiga nan(hotel)din amma
ganin yanda na rude sai ya biyo ni. Muna zuwa
na nuna masa cikin bedroom yana shiga na
kulle kofa na jefar da dan key din na cire kaya
na bishi daidai lokacin da yake cewa banga
komai ba." Juyowar da zai yi na rungume shi
tare da samun sa'ar bakinshi na saka nawa,ya
yi kokarin kwacewa amma shidan ba raggo
bane ya dafa min,in gajarce muku nan muka
aikata wannan laifin sai da komai ya kammalu
ni ina murna don mutumin ya kai namiji shi
kuma sai naga yasa kuka wai na cuce shi shi
bai taba aikata zina ba.N WAHALA 2**4
Laila tayi tsaki,don kalaman kawai? Hajara
tace maganar gaskiya laila mace yar son
soyayya ce,mu kuma duk cikinmu wacece zata
ce mijinta ya taba ce mata I luv u tun bayan
aurensu? Kowace tace ina,gaskiya ita sai tayi
wata bata ganshi ba. Hajiya Samira tace,sai
dai inji yana ce ma katti in suna aikata laifin
amma ba ni ba.Nafisa
Sabon shiga tace,ni kuma wanda nake so
yanzun an aura masa kanwata na rasa yanda
zan shawo kanshi ya dinga debe min kewa ta
basu labarin yanda alamuranta suka faru ta
kara musu da cewa "ita in tayi yunkurin aikata
laifin sai kuma ta tuna da mutuwa da hisabi sai
ta fasa. Nan suka yi caa a kanta suna bata
labarinsu Marsy tace kudi zaki sakar masa ga
ki da kyau ai baki da matsala. Laila tace ki
daina tuna mutuwa kafin ta zo kin tuba.(Kamar
sun san sadda mutuwar za ta zo) sima tace
sannan ga wani sirri ki dinga yawaita aikin
alkhairi in kin ci sa'a sai ya shafe zunubin ki.
Nafisa dai cikin zuciyarta tace bamu isa mu
yiwa Allah wayo ba,don ya san abinda ke cikin
zukatanmu amma a fili sai tace hakan zanyi.
Koda suka dawo gida zuciyarta sai mamakin
labarurrukan matan abokan Alh Jamilu take yi.
Ta tuno sa'adatu da tace ita mijinta kullum zai
kawo wani ya yi dashi a gabanta sannan in sun
gama sai ya umurci saurayin ita kuma yayi
zina da ita,a haka tana da yara uku bata san
wanene asalin baban yaran ba. Wa'iyazu billah.
Nafisa dk tmkr cikin mafarki take ji da ganin
abubuwn, ta roki alhji jamilu iya roko kan cewa
ita wlh bazata iya wannan rywr ba, don Allah
ya saketa zata rufa asirinshi, amma sai ya bata
tsoro cewa ta iya bakinta inta matsa mishi za a
batar da ita.
Alhji jamilu yaje gidansu hajara ya samesu
suna dinner, ya zauna shima za shiga sahu.
Suna ci suna hira, yace hajara kin kasa saka
tawa matar akan hanya, sai damuna takeyi.
Alhji kabiru yace "na zata an wuce wannan
babin. Hajia hajara tace taurin kanta yai yawa,
amma ka sani ne kabiru, ka kai yara gidanku
sai ku shirya mana fita waje ko dubai ne, nasha
muku alwashin in mun dawo zaka ga canji.
Suka ce shikenan. Alhji jamilu yace ma nafisa
ta shirya zasu fita dubai ita da hajara su dan
siyo takalmansu na sawa da turaruka. Tace,
to. Hajara tasan lbrin timo da nafisa take gaya
mata cewar yayi kama da masoyinta, dn hk ta
same shi ta xuba mishi kudi tare da mishi
bayanin abnda take so yai mata. Cikin
kwanakin suka kammala shiri, a airport suka
hadu dasu timo, nafisa tai mamakin ganinshi
su da wani saurayi. A zatnta tafiar su daban
sai taga sun hau jirgi tare sun sauka tare. Ashe
ma dakinsu daya ne. Nafisa tace ma hajara
meyasa wadannan suke biye dasu? Hajara
tace tare muke, su dan taya mu shakatawa.
Har nafisa ta soma fada, hajara tace ma timo
sai fa yayi aikinshi sannan zata cika masa
kudinsa. Nan ko ya iske nafisa a bayi tana
wnka, ya soma yi mata kaxaman wasanni
shedan ya rura wutar suka taru suka kifar da
dan guntn imanin dake zuciar nafisa, hr ta
soma ganin wautarta da taso taki. Shaidan ya
kawata mata zinar hr taji bb rywr data kai
wannan sugar. Tir! Allah ka tsare mana imanin
mu.
Cikin kwanakin nafisa ta xama gwaska, sati 3
sai taga tamkar kwana 3. Da suka dawo kam
alhji jamilu yaga bambanci, ynxun ta sake ta
daina kunci da takura kanta cikin daki. Sannan
ba ruwanta da batn harkar nashi zunubi. Timo
kuwa har kwana yakeyi a gidan. Harka ta balle
tuni ta sake kullewa da matan abokanshi tana
daukar wasu darussan. Allah ya tsare mu.
Iklima suna tsakar gida suna aiki da makota da
dangin me jego, daya matar gidansu ta haihu
yau aikin kunu. Tana sanye da riga da zani da
hijabinta na xaman tsakar gida, iyakarshi
gwiwa. Suna xaune ne suna tace kullin kunun,
wasu suna kicin gurin ruwan kunun. Sai
zancenta suke wai waccan amaryaryar haka
take yini da hijabi? Wata tace tnda akayi
haihuwar nake xuwa amma ko yaushe da
hijabi. Maman ummi daya matar gidan kenan
tace a ynda kuka ganta din nan hk take. Sam
bata xama sai da hijaba, sai kace wani abu tafi
mu. Wata tace iya yine. Suna ta dai tsegun-
gumansu ita kam bata ma sani ba.
Mahmud ya shigo da sallama ta

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment