Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan tsaya mshi
a rai . Lokacin data rako shi ya rike
hannunta.宄歵a sai munyi waya:
Abban Khalil don Allah ka kauda anka daga
haramun顏� Ya kale tad a son jin dalilinta na
cewa haka Tace tunatarwa ce kawae. Kana da
yara mace da namiji kai ne zaka tsare musu
mutuncin ta hanyar tsare naka Ya fuskance ta
yace in nasi in fahimceki kina nufin zuciyarki ta
soma raya miki ina neman mata ? Auzubillah!
Kullum zuciyata tana kyauatata zato a kanka
tunatarwa ce Ya girgiza kai. Maganar tad an
tsaa mishi a rai.
It kuwa tunda yatafi tana cikin damuwa, koda
sunye waya bata taba nuna mishe Ba, haka
yanzu ta koma adu,a ko matar banza ce ya
hadu da ita Allah yarabasu. Sannana ta Kara
Zage damtse gurin ye mishe duk wani abu da
zai Sa she cikin farin cikin Tare da kare
mutuncin she. She kuwa zuwa yanzu Yagama
shagala da son ashura, burinshi kawai ya
aure,Yana son mace yar gayu, sai dai Yana
ganin iyayenshe bazasu yarda Ba, sannan
Yana tsoron ikilima ta sani, don yasan tana
tana da zafin kishi. Sai dai fa shi zai shanye
komai in dai zaye samu ashura.
Nafisa dai suna nan suna Shan magani labarin
mutuwan mama zee da safina ta samai ta,
tsakaninsu kwana daya. Nafisa
Taye kuka tareda nadama. In tana tuna kanta,
shekaru biyu baya tana shan mamaki, bata San
yau zata zo mata a haka Ba, koda yaushe tana
gane illar son zuciyarta da taye, ta dinga
gantali zina don kawai ta samu abun duniya.
To yau gashe shekara biyu jal da yan watanni
ba kudi Ba mutunci, ba kuma lafia, ciwon da
kowa ke gudun ka sai dolenka, Wanda kuma
take mutukar so ya zama ba
Rabonta ba, mutane na kyamarta ko Islamiya
taje sai ayi ta matsawa daga kusa da ita.
Mahmood yana zaune gaban mahaifinshe a
wani hutu dayazo,so yake ya gabatar da batun
Asurah,amma mahaifin nashe sai ya tareshe
da batun gini,kan cewa yaye kokari ya karasa
sai yace too, ai kwanan nan zaya gama.
sannan ya ce,daman kan batun wata yarinya
ne da yake so, shene iyayenta sukace ya turo
manyanshe.ya tsura mashe idanu,sannan yace
Aure ? Aure yanzu ?baka samu ka kammala
gininka.yace Alhaji zancen nakeson a gama
komai in an tsaida rana saina karasa ginin
kafun bikin,Alhaji yace, madalla, to a ina
kasamu matar?Can kaduna ne gidan da nake,
kanwar aboki na ce. shekenan amma baka
ganin kaye gaggawar sake aure?
Mohmood ya sunkuyar da kai tareda cewa,
Allah zaya rufa asiri Alhaji.yace shekenan zan
samu su alhaji mustapha sai mu ji lokacin da
za a tafi din.Duk wananna shirin ikilima bata da
labari,haka nan mahafiyarshe dasu hajiya uwa
sun bashe shawara yace shede su tayashe da
adu,a.Matar muktar itace ta soma tsegumtawa
ikilima batun auren mohmood, har an saka
rana ikilima taye murmushe yake tare da
cewa,ai ta sani.matar muktar tace she a
gidanmu yace baki sani ba,don Allah karna
fada miki.ikilima tace wasa yake miki
nasani.bayan tafiyarta ikilima ta zame ta
kwanta.tambayar kanta take wani irin mugun
hali ne da ita wanda har mijinta mijinta zai
boye mata batun aurenshe?Don ita a hagenta
nesanta mugun hali ke sa miji ya boye wa
matarsa don gudun fitina.
Ta shiga daki taye ta kuka sosai don tana
kishen mijinta,amma hakan bazai sata bijirewa
Allah ba,tasan kisheya babu dadi amma Allah
yace a yi.farko ma da biyu ya soma,sannan
yace uku,ko hudu.sai inkana tsoron baza kaye
adalci ba ne aka ce kaye daya.Da an doge da
biyun da duk wanda zai ye aure biyun zaya
yi,matsalarta boye matan da yayi,tunda ba ya
so ta sani ita ko tasha alwashin ba za taba yi
mishi zancen ba.
Ashura dai tana rabonta,don ko kayan Akwati
tare suke zuwa su siya.musa ne da yaje
kwantagora ya shaidawa mahaifiyarsu,nan ko
ta fusata,dama shima musa ba son auren yake
ba.
Ta ce kira mini shi ,ya kira shi ta ce, too duk da
ban isa shawara ba don za ka yi aure in ka
gama ina neman ka, don ban amince da batun
aurenka ba. Duk yaushe ka soma samun kudin
da har zaka sakawa matarka da kishiya? ka
manta wuyar da yariyar nan tasha kanka.ko
dadin kudin ba ta soma ji ba zaka debo wadda
kila ma kudin ta gani zata aure ka.shi dai shiru
yayi tamkar ruwa ya cinye shi, ta ce don haka
ina nemaika.
koda yake nasan ban isa ba,ta mikawa musa
wayar ya kashe.ranan juma,a daga kaduna kai
tsaye kontogora ya wuce,da kyar ta amsa
sallamar shi don tasan muhimmancin
sallama.tsuke fuska taye yanda bai taba
ganiba daure fuska irin haka ba.jikinshi babu
karfi ya shiga,cigaba taye da aikinta ta share
shi,saida ta gama komai ta shigo.yana zaune
ya zabga tagumi ta zauna tana ninke kaya ba
tare da ko ta kalle she ba.ina wuni hajjiya da
kaushin murya ta ce,kaga alama ai tunda aiki
kaga ina yi ba a kwance ka ganni ba,kaga lafia
kenan.wallahi bana ki sheda miki ba ne,daman
zan zoo.....ta ce rufa mini baki,baka maida ni
bakin komai ba har a sa maka rana ban sani
ba?don bani da abunda zan baka ko kai kayi
kudi!ya zuba gwawoyinshi a kasa yana
cewa,don Allah ki yafe ni naye laifi,amma ba
don baki da shi bane,ni wallahi aure kwai nake
son karawa.saboda matarka tana maka mai?ta
katse shi.ya dube ta wallahi ikilima tana min
duk wata biyayya,in ma nace bata min sai Allah
ya kama ni,ni de ina son ashura ne.don Allah
hajjiya ki sa min albarka cikin auren nan.Bazan
saba naji ance baka son ikilima ta sani,adalci
kenan?
cikin in ina yace a a a ta sani,ai ita ce ma ta
karfafa min gwiwa fa.ka ji karya.yana ta share
zufa hajjiya taye shiru, can ta ce yarinyar
kirki.to shi kenan, ai zan zi minna din.nan dai
ya kwana da safe ya zuba mata kudi ya nufi
minna.ikilima tana kwance ba lafiya,tunda
matar muktar tazo mata da labari auren mijinta
karfin hali kawai take yi,su maman ummi sun
samu labari,sai dariya suke suna Allah kara,tun
suna habaicin cewa ai daman duk shegiyar da
ta rike namiji uba zata mutu marainiya,har dai
suka samaita har daki suka ce wai an ce
baban khalil zai kara aure?Ta ce ehh Aisha
tace,kizo in kai ki gurin aminyata ta kai ki gurin
bokanta ta tarwatsa abun.maman ummi tace
ce ,ke ko nan gurin malam na ketare aka kai ki
tuni zai wargaza lamarin.
Ta ce A'uzubillahi! A wargaza sunnar manzo
(saw)? bana cikin wannan layin, ban ce bana
kishi ba amma ba ni da abin yi sai adu,a Allah
yasa abokiyar zaman arziki ce Allah yasa mu
zauna lafiya.aure inkun yi tunani sunna ce,
Allah da kan shi da biyu ya ce su fara, don
haka kuma mijina fatan alkhairi nake mishi don
na rike shi uwa uba.jiki ba karfi suka fita suna
taba baki, Aisha ta ce, don Allah kyale ta,karfin
hali ne gashi nan duk ta rame? maman ummi
ta ce,in ya sake ba sai kuma muga ta kaudi
ba,ai dama su maza haka suke, daga sunyi
kudi sai sake aure,sai kuma saki.muna nan zai
sake ta.su khalil da ummita suna gidan su
mahmmod,ranar ma nazira ce tayi mata aiki ya
shigo da sallama,bacci ya soma daukanta.ya
nufi bed room, nan ya same ta kwance ya
sabule jakarsa ya aje ya tsura mata idanu,ya
tsorata da ramanta. ya kai hannu ya shafi
kasuuwan wuyanta,sun fito rada rada firgigit!ta
farka ganin shi ta kirkiro fara,a ko na yake.ta
yunkura zata tashi ya zauna da sauri tareda
rungumota ta zuwa jikinshi dunib jikinta ne ya
firgita shi,ya ce ikilima tun yaushe ba ki da
lafiya? tashi muje asibiti.ta ce zazzabi ne kawai
,bari na kawo maka ruwa.mai zaka ci na dafa
maka?ya tsura mata idanu,sannan ya kwantar
da ita ya canza kayan shi da sauri ya dauki
key din mashinsa tare da zura mata hijabi.tashi
muje.ba don taso ba, dole ta mike suka nufi
asibiti. duk gwaje gwajen da likita yayi hawan
jini kawai yagani,shima ba ta'azzara ba ne, ya
dai ba su shawarar su kiyaye duk wani abu da
zaya sa jininta din ya kara sama.Hankali
mahmood ya tashi sosai, koda suka dawo gida
yasa ta shi lallai ta fada mishi damuwarta, ta
ce ba komai.ya tsargu, ko dai ta samu labarin
auren shi ne? ya ce, ikilima ko an zo miki da
labarin game da ni?
Ta dube shi "na me?" Yace a'a am...na zata
dai ko ni ne na bata miki? Tace ko daya, me za
kaimin? Yace to kila yaran da kike koyarwa ne
hayaniya shi yasa nace ki daina koyarwa kiji
da karatunki. Ta dube shi kayi hakuri, inason
karatuna da koyarwa. Yayi shiru kawai yana
tunani, in kuma taji batun auran shi sai yaya
kenan? Kila jininta ya kara sama. Kafin
washegari tana ta samun sauki, yana kula da
ita, hatta wanka shine ke mata. Maimakon ta
tafi lahadi da yamma yadda ya saba, sai
washegari litinin yayi asubanci, a cikin mota
kafin ya sauka ma ya kira ta yafi sau goma. Ko
ashura bai saurare ta ba a wannan zuwan
kamar yadda suke hira cikin internet in yazo
gida. Bai samu sukuni ba har sai da ya samu
tabbaci daga kannan shi cewa taji sauki, don
shi ko tace da sauki sai yaga kamar fadi ne
kawai dan kada ya damu. Duk lokacin shan
maganinta zaya kiraa yace mata tasha yana
jiranta har ya kan ce ta kara wayar yaji shan
ruwanta, sai ta tsokane shi tace amma gara ni
ba sai an jika a cokali ba, yace eh naji sha dai
ina jinki.
Ranar wata asabar sai ga mahaifiyar mahmud
tamkar an jeho ta. Taci sa'a yana gari. Tunda
nazira tazo ta shaida masa zuwan hajiya
gaban mahmud ke faduwa, yana keta zufa.
Yasan yau ba makawa ikilima zata san abnda
yake boye mata, ta gama abinci kenan zata
aika mata sai ga ta, tayi sallama shima yana
wanka yana sauri ya fita don kada tazo ta
same shi. Suka gaisa da ikilma tace "dama
yanzu zanyi shirn makaranta ne in zo mu
gaisa". Ta gabatar mata da abinci. Hajiya tace
a'a a kai min can tunda kika ganni gidanku
kinsan ba zuwan kowa nayi ba naku ne, ina shi
wannan yaron? Tace yana wanka. Ya fito jiki
ba karfi, ko turare bai sa ba ya zauna yana
gaishe ta cikin yake da fargaba. Duk suna
zaune ne a kan carpet, tace ikilima kwanaki
musa yaje min da batun auran mijinki, har yake
cemin shi mijin naki yace baya so kisani, shi
kuma da yazo yace min kece kika karfafa mishi
gwiwar yin auren, haka ne? Ta dan dakata
yayin da take bin ikilma da kallo da idanunta,
alamar tana son fahimtar wani abu a tare da
ikilimar. Kafin ikilima ta bata amsa, sai kuma
taci gaba. Don ni ban kama zancen shi ba,
shiyasa nace sai nazo naji daidai lokacin yana
garin, ba ruwana da munafurcin maza.vels BOOK
MABUDIN WAHALA 3**7
Ikilima ta kalle shi duk yayi zufa, yasan hajiya
na jin cewa ikilima bata sani ba, batun auran
ya rushe, gara ma ya fada da kanshi kafin tayi
magana. Yayi saurin cewa gaskiyar magana....
Hajiyar ta katse shi 'ban tambayeka ba, ke 'yar
nan fada min gaskiya, kin sani? Ikilima ta
danne bakin cikin da ya taso mata tace na
sani, ni ce ma na karfafa mishi kamar yadda ya
shaida miki. Cikin mamaki ya tsura mata ido,
tana kallon shi sai yayi maza ya sunkuyar da
kai, kunyarta mai tsanani yaji. Hajiya wadda ta
kasa magana don jin wai ikilima ita ce ta daure
wa mijinta gindi yayi aure, ta nisa sannan tace.
Yau ne na yarda 'yan nan baki da kan gado,
hankalinki daya zaki ce mijinki yayi aure? Kin
san kishiya kuwa? Kin san halin maza kuwa?
Ban da rashin hankalinki in shi ya manta wuyar
da kuka sha ke ai bai dace ki manta ba.
Yaushe ne ma kuka samu rufin asirin? To ki
sani ita kishiya cikin dayan biyu ne take zuwa,
ko ta kore ki ko ta mulke ki. Shi ko in bai juya
miki baya ba to saki ne zai biyo baya. Ta dubi
mahmud nasan sakinta zakayi wata rana. Duk
suka kalle ta yace saki? Haba mama.
Ikilima zufa ya rufe ta, dama daurewa tayi ta
sake cijewa tace mama kiyi mana addua,
nasan ba zaya min haka ba. Tace Allah yasa.
Bari in tashi, na lura kece kika bashi fuskar yain
auren. Ikilima tace ki sa mana albarka mama,
bakinki yana da fa'ida ga auran. Ina nufin
albarkar ki. Tace um Allah yasa alheri. Ta dube
shi kai sunkuye sai kace munafuki. Tace wane
shirye shirye kake nagam ginin? Yace ai mama
har an rufe, tiles ake sawa sai painti. Ta taba
baki ta dube shi. Yaushe ne auren? Ya dubi
ikilima suna hada ido ya sunkuyar da kai
"kwana arbain da daya ya rage. Tace to a nan
kake aje lefen? Yace yana gurinta, in mun siyo
sai ta aje saboda nisa nace ba sai anje kaiwa
ba an huta. Ikilima ta danne wani abu da ya
taso mata tare da maida hawayen idanunta.
Hajiya tace tabdi! Auren bariki zakuyi? To ba
da ni ba, ka amso kayan ka kawo daga nan
za'a kaisu , ina ka taba jin ance amarya ta tara
kayan lefenta? Kai ka raina danginka ko? Yace
a'a zan karbo. Tace ita ma ikilima duk abnda
kayi ma waccan shi zaka mata, butulu. Har ka
manta wahalar da tayi dai? Ikilma tace don
Allah mama kiyi hakuri, ni yaji da amaryar da
kuma gininshi. Mama kisa albarka. Hajiya tace
bai isa ba yace ba zai miki komai ba. Da sauri
yace duk abin da take so zan mata ai. Tsaki
hajiya taja tare da mikewa. Ikilima ta kallo
agogonta, nima lokacin makaranta yayi, ta
mike tace mama bari na dauko miki abincin mu
wuce tare. Yace hajiya sai na shigo. Bata amsa
ba ikilima ta sabi jakarta ta dauko kwandon
abincin hajiya, ta dube shi tsananin kunya tasa
shi sunkuyar da kai, ikilima tayi murmushi tare
da cewa sai na dawo. Duk abn duniya ya damu
ikilima, tana zaune cikin aji. Duk wanda yaji
batun auran sai yace ta tashi tsaye, to tayi me?
Menene tashi tsaye? Hatta maman shi sai da
tace ki nemi tsarin jikinki, 'yar bariki ce. Tsaf sai
ta raba ki da mijinki. Haka mamanta tace ke
sarkin gaddama, to yanzu sai ki dage ki nemi
mallaka. Ki mallake shi in ba haka ba wata
tazo ta koreki. Nafisa kuma kuka tayi ta yi,
wanda ikilima ba zatace ga dalilin kukan ba,
sai dai ita tana yi ne saboda rashin masoyi da
tayi.
Tasan har duniya ta nade baza ta daina son
shi ba. Su haj uwa ma duk ce mata sukayi ya
tashi tsaye. To wane tsaye zata yi da ya wuce
adduoin da take yi? Sam tayi nisa cikin tunani
bata san me akeyi a ajo ba, bata san an tashi
ba sai dai juwairiyya usaini ta buga tebur
sannan tayi firgigit. Juwairiyaa tace tunanin me
kikeyi haka? Hawayen da take makewa suka
saukar mata, juwairiya ta zauna me yafaru?
Ikilima tace um, bansan me mutane suke nufi
da cewa in tashi tsaye ba, kowa tsorata ni yake
da cewa matar da mijina zaya auro zata zo ne
don ta kore ni, ban samu mutum daya da ya
ban shawarar kwantar da hankalina ba.
Juwairiyya dama duk wadda mijinta zaiyi aure
sai ta tashi tsaye? Kafin ta amsa malamin su
ya shigo kwasar littatafansa, sai yagan su.
Lafiya ikilima kike kuka? Juwaoriya tace
malam tana da matsala ne. Meke faruwa da
ita? Malam ya tambaya da saurin shi. Nan
ikilima ta shaida mishi cewa mijinta ne zaya
kara aure bai fada mata ba, sannan kowa yana
bata shawarar ta tashi tsaye, ma'ana ta shiga
malamai.
A'uzubillah. Inji malam kabir. Ya kausasa
murya, koda wasa kada ki kuskura ki dauki
wannan muguwar shawarar, ba kya yin adduoi
ne na tsari? Tace inayi, yace ki tsaya akansu,
su kadai sun isar miki. Azkar din safe da
yamma. Wallahi ba mutum ba ko aljan sai ya
barki, kuma duk abinda kika ga ya same ki sai
kaddara daga Allah. Ya gyara tsayuwa. Abin da
mata ku ke kasa fahimta, kishiya ba abokiyar
gaba bace, 'yar uwa ce. Sunna ne mu aje ku ku
hudu, duk matar da take yakin bata son kishiya
fada take da Allah da yace a yi, don haka ki
nutsu kiyi wa mijinki addua, kada ki zama cikin
matan da ke cewa namiji ba dan goyo ba,
namiji kaza namiji kaza. Da zaki bukaci jin
dalilin zagin namiji, zakiji duk kan batun kishiya
ne, don haka ki nutsu. Ikilima tace to malam,
nagode. Yace ki dinga tashi cikin dare, misalin
ukun dare ko biyu daidai lokacin ubangiji yake
cewa ina mai bukata ya roke ni, ni kuma in biya
mishi? Kiyi nafila ki gaya wa Allah damuwarki.
Amma bakije gurin wani makaryaci ba ya
amshe miki kudi ya rabaki da imaninki, kuma
wasu malaman har zina suke yi da matan
mutane. Tir! Da irin wadannan mutane.
Ikilima tace to malam in sha Allahu zan kiyaye.
Tace malam babu wata addua da mutum za
yayi yayin da kishiya tazo masa? Yayi
murmushi yace ikilima shi kishi halitta ce da
dan adam ba ko dabba yana da ita musamman
ku mata. Ki dai rike zikirin Allah cikin zuciyarki
yana wanke damuwa ko yaushe. Ki dinga
la'ilaha illah ko subhanallah, walhamdulillah,
wallahu akbar. Ko istigfari. Ki ringa yinsu kala
kala. Kin iya malama ikilima zaki samu
nutsuwa kuma Allah zai sa miki sanyi cikin
zuciyarki. Ta mike to malam, zan rike duk na
iya su. Adduoin tsari fa? Yace nasan kina
ayatul kursiyu, falaki, nasi da kulhuwallahi uku
uku. Asubahi, azahar, la'asr magriba da isha'I
dai dai? Tace inayi. Yace ba abn da zai same
ki, ki tsare adduoin bacci nasan duk kinayi ko?
Tace eh, yace Allah yaja mana gaba. Ta
gidansu ta biya, tayi dace samun mahaifinta
inda yace dama yana so yazo gurinta, domin
duk yaji batun da mata sukeyi a gida na game
da auran mahmud. Yace da ita. Ikilima na
sanki na san halinki, don Allah bana son ki
canza don za'ayi miki kishiya.
Ki zama mai biyayya da son abn da mijinki ke
so. Kiyi zama na tsakani da Allah da abokiyar
zamanki, kinji ko? Tace to baba in sha Allahu
zan zama abin kwatance a gurin sauran mata,
zan bar misali. Yace Allah yayi maki albarka ke
da 'ya'yanki. Tace amin baba na gode. Tana
shiga gida dakinta a rufe, mahmud ya fita.
Tasa hannu ta ciro key din a gurin da suke
ajiyewa ta bude kofa ta shiga. Tun lokacin da
malamin yayi mata nasihar take zikiri cikin
ranta, don haka sai taji rayuwarta fes. Nazira
da ta kawo su khalil itace ta tafi da abincin
hajiya na dare. Mahmud kuwa har taran dare
ya kasa shigowa gidan. Suna fita shima cikin
sanyin jiki ya bar gidan, gidan su sulaiman yaje
yana neman shawarar shi game da abinda
zaya fada ma ikilima inta dawo. Bayan ya
sanar dashi duk abubuwan da suka faru,
sulaiman yace Allah ya kara maka, sai da na ce
kasanar da ita tuni ka ki, to gashi yanzun ta
sani lokacin da baka shirya ta sanin ba, ta
kuma rufa maka asiri, don haka sai kaje ka
bata hakuri. Suleiman ba zan iya kallontaba,
ina jin nauyi. Don Allah muje ka raka ni.
Tab! Wallahi ba zan je ba, kawai ta zo tana Jin
haushen na a banza? Mukhtar ma nan ya
same su, amma shims cewa yaye bazai je ba.
Lokacin da ya shigo ikilima tana wanka,falo ya
sauna cikin fargaba tare da tunani in ta fito
Kilauea ta balla Mishi harara ko ta ja mishi
tsaki,wata zuciya tace in ma haka taye maka
da sauki,kila da hauka da zai tare da ce maka
munafuki maci amana. Haka dai yaye ta tufka
yana warwarewa har baije fitowarta ba.ta
shirya cikin Kayan barci tasa turare,bata san ya
shigo ba ta dubi ago go tara ta gota,don haka
sai ta ce Bari ta shirya masa abinci kafin taye
shafa"i da wutiri kada ya shigo taye bacci ko
tana sallah.taja ta tsaya saboda ganinshi
Zaune ya rafka tagumi.a hankali ta ce sannu
da zuwa,firgigit yayi sannan ya ce yauwa,um
hum.duk ya rude.tayi guntun murmushi,sannan
ta nufi kichin ta dauko mishi abinci ta shirya
mishi ko ya kasa kallonta,ta zauna ta cewa
tuwo" na maka, na San ka da son tuwo.ya ce,
"EH, ai gara tuwon ne." ya soma ci duk da ba
ya Jin yauwa saboda damuwa.
Ganin yana duk ya kasa sukuni sai ta nufi ciki
ta fara sallah.yau dakin tamkar bakon shi,ya
kasa shiga. Can dai ya yanke Shawara yasame
ta ya bata hakuri ya huts da Jin nauyin nan
dake damunsa.yasan kuma Zara hakuri don
tana da matukar hakuri.lokacin da ya shiga ta
soma barci,don haka ya kwanta amma ba don
bacci ba.ya shiga tun daga ranar da ya kwanta
ciwon bakin ciki da nafisa ta dasa mishi zuwa
lokacin da mahaifinta ya ba shi kanwarta
ikilima. Ya dubi yaran su guda biyu mace da
namiji,ya sauke ajiyar zuciya.sannan ya soma
tunani a tsawon zaman nan ko zaa tuna mai
ikilima ta Fada mishi na bacin rai? Yayi ya yi
amma ya kasa tunawa,Kirkinta ya shafe..ina
ma ta taba mishi ya shiga tuno halayanta na
kware.ya tuno lokacinda itace ke ci yarda su
da dan albashinta, ya yi ta tuna abubuwan daki
daki har zuwa yau da ta kare shi gaban
mahaifiyarshi.ya juya ya zuba mata idanu, ya
sani ya yi Dacen mata,Allah yasa ya fita
hakkinta.baya ga son da yake wa ashura da
tuni ya shafe babinta,abin nufi ya fasa.uku
saura ta fara,lokacin ya soma bacci amma
motsinta ya farkar dashi,sai dai ya yi shiru ta
dauro alwala ta shiga nafilfili, sai jikinshi ya
sake mutuwa yaga tamkar bai mata adalci ba
ne take Kai karar shi gurin Allah.
Don haka da safe ma kasa mata zence ya yi.iia
zugum da ya yi yana tuna lokacin da ta dawo
alwala a jiyan da dare ta shafe mishi jikinshi
tsaf.tana cewa " nasan baban khalil sakaci da
wuya in ya yi adu,a. Sam bata Canza mishi ba,
yanda ta saba kaf kayan kunya har ya
tafi..lokacin da ya dira garin kaduna yafita
wanka yaye shirrin bacci, abubakar na rokon
shi don Allah yasa kaya manya suje malali
gurin budurwanshi.ya ce, na gaji ka Gaida ta,
kasan gajiyan tafiya..abubakar ya ce,ka cika
raki,in Kai ke jan motan sai yaya? Ashura ta
shigo da tire abinci a gaban mahmoud,fuskarta
a daure ta koma gefe ta zauna.abubakar ya
fesa turare ya jefa kan katifa tare da cewa" ni
na wuce. Ya ce, " to in kayi dare zamu rufe
gidanmu ne," abubakar yayi dariya tare da
cewa, sai na hauro katanga." ya maido duban
shi ga ashura.ranki ya dade ina yini? Ta sake
Cuno baki ya ce " to nayi laifi kenan? Tayi fari
da matsakaitan idanunta tare da cewa, " au, ba
ka ma sani ba kenan? Na lura in ka tafi garin ku
share ni ka ke yi,
Kuma da ai ba haka kake min ba,ko dan
chatting Bama yi yanzu. Jiya fa har kashe
waya kayi.yace, to nutsu in Fada miki
uzirina,haba my love, ta ce, na ji." ya ce kin ga
kwana Bihar fa mukeyi kullum muna hira,amma
ita kanwarta kwana biyu jal yana da kyua mu
lura da hakkinta? Ta tabe baki, ni wannan ba
matsala bace." na Kai ma tella dinki anko har
da nasu hajjiyaduka yaye mini lissafi dubu sha
biyar.sannan zaka bani kudin gyaran jiki dubu
sittin.ya zuba mata Ido tare da cewa,dubu
sittin ashura? Gaskiya bani da halin ba ki
su,kin fa San gurin aikinka.so ki ke na shiga
diban kudin Jama,a. Ta daure fuska," to ya
za,aye yanzu? Ya ce, kin San na ce miki da dan
karashen aiki a gidan da zamu zauna.kanwata
ban sai mata komai ba,lafe ba a gama hadawa
ba,duk fa ni kadai ne.ki lura da wannan." ta
ce," kana nufin na hakura da gyara jikin,don Kai
fa zanyi?ya ce, wai wani Irin gyara bane? Ta ce,
gyaran fata ne zuwa lalle da za a zana min." ya
ce, " too zan bada rabi dubu talatin,kince na
dinki dubu sha biyar, anko har guda nawa ne?
Uku ne, sai na hajjiyata da kawayenta su biyu.
Too naji, zan bada arbain da biyar ke nan ko?
Ta ce, um, too yaushe za,a karasa kayan
lefan? Ya ce, " kafin na tafi gida sati na sama
da su zan tafi sai su kawo." ta ware idanu shi "
da su" ya ce," eh," amma ai da ba haka muka
yi ba da Kai ba,ya za,a Kai mini kaya can? " ya
ce, na Canza ne,dole na Kai sai dangina su
kawo,zai fi daraja koo? Kema zaki fi kima a
idon dangina.ta ce" to gaskiya ba za,a Kai min
kaya Kauye ba suje su kwashe. " ya daure
fuska " garin namu ne Kauye? Ya kauda Kai " ki
zauna da shirrin zan tafida su Koda garin mu
daji ne.fuu ta fice tana kara kumbura fuska,ya
Fada kan katifa a baya tare da lumshe ido.ya
ciza dan yatsan shi na tsakiya, wannan lokacin
ne yasan matsalar aure daya so nafisa wanda
son ya rikide ya koma na ikilima,ko zanin dubu
uku babu.shaddar cikin ce kurum ta dubu biyu
da dari biyar. In zai tuna atamfofin da suka
siyo kawai kowace daya dubu ashirin da biyu
ce guda biyar,ga lesuka da shadda duk masu
tsada gaske,kudin shi na wannan shekaran kan
ashura suka kare.yaja tsaki gashe bata San
darajan shi ba,kuma yana ganin da kyar in
Zata yi biyayya.
Ta wani bangare sai yake ga kamar ya cutar da
ikilima don bashi da karfi sai musu iri
daya,komai ya dauko wayar shi ya dubi lokaci
sha daya yasan tayi barci,ya rubuta:
NA SANI NA MIKI LAIFI, DON ALLAH KI YAFE NI
INA JIN NAUYENKI.Ya tura mata, sannan ya
kwanta yana karanta addu,a wanda in gida ne
ita ke shafa masa.da safe taga sakon
shi,murmushi taye.koda wasa ba zata nuna
mishi taga sakon ba,bare yaga amsa.ya ko sa
ran ganin amsar sai dai shiru ta bashi
labari.saboda ya samu a karasa gidan duk sati
yake zuwa.wannan lokacin ko da ya zo da
kayan lefen gidansu yakai duk zuwa in sun siyo
sai ya zo da shi ya gama gidan amma bai
samu halin canza ma ikilima komai ba.yanzu
ma da ta zama surukarshi,har sakonnin shi
sub dame shi amma baya iya tunkararta,ita
kuma sai take ga dan zaya yi aure ne ya
chanza mata,ya daina kawo sakon tunda gashi
zaya yi sabon inbox.sauran sati daya biki,
hajiyar shi tazo da kannanshi taga lefen
amarya,amma bata ga kayan uwargida ba,don
haka ta kira shi a gaban babanshi ta ce,ina na
ikilima?ya ce, wallahi zai sai mata ko bayan biki
ne,wallahi kudin shi duk sun kare kayan dakin
zai chanza mata.hajjiya ta ce, ina, wannan ma
labari ne.ta tura musa ya kira mata ikilima,ta
ce darji wandanda ki ke so.su hajji uwa
msukace ta diba.ta dube shi ya sunkuyar da
kai ta ce, ba lefen amarya ba ne?
hajji uwa ta ce, ki dauka ya za,ayi ace ke ba a
miki ba?dubi

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment