Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa ai ni na zata kema yana kawo
miki.ta ce, ku kai mata, nasan nima zai siyo
min.hajjiya hauwa tasa hannu ta ciri lashi biyu
atamfa biyu, shadda biyu,komai ta diba har da
kayan shafa ta zazzagebabbab akwatin na
farko ta zuba mata kayan.zata yi magana ta
hanata,ta ce musa dauki ka kai mata
gida.hajjiya uwa ta ce,ko dai a bar su nan a kai
dinki,kin san ta bashi zata yi hajjiya hauwa ta
ce,hakan ne, ta dube shi ka bada kudin dinki.ya
ce, too.zuciyarshi cike da zukkumi kayan da
aka diba,kuma kalolin da shura tafi su,gashi
har hajjiyar su ashura sai da ta nanata mishi
cewa kada ya sake a taba kayan.koda suka
dawo gida taguni yayi,ta dube shi ka bari in har
sun bani zan baka.yayi sauri cewa,a a ki bar
su dama zan sai miki ba komai,ta ce, a a ,
wadannan sunyi tsada da yawa sai
amarya.kalmar ta duki shi,ya ce ban gane ba,
ke ma ai irin su daman zan sai miki.ta ce, ni na
yafe,in sun kawo ko bayan biki ne zan bata
kayanta, Allah sa alkhari.ya ce, a a na ce ki sa
daman zan sai miki.ta danne hawaye da ke son
fitowa,ta ce a a kayi hakuri ba jajajja zan yi da
kai ba,lefenta ne nima an min.ya ce,to naki ai ai
ba irin wannan ba ne, tayi dan take,too auran
so ne wannan ba irin nawa ba, kaga kowa da
matsayinshi. ta tura bayi ta shige.duk da
kokarinta sai da tayi kukan ta maiishi,yanda ba
zai ji ba dole ta yo wanka don kada ya
gane.shi ko maganarta ta saka shi cikin
rudu.da ta fita ta shafa mai,ya ce ikilima! ta
dube shi zaune bakin gado, ta ce na,am. yanzu
ta ji dan sanyi cikin ranta saboda kukan kishi
da taye.
kishi kumallon mata,ya ce ni nace bana sonki?
ta sunkuyar da kai,wallahi ikilima ina sonki,ba
zan yi aure ne don na muzguna miki ba.bata ce
kala ba,ya ce gobe ne nake ga ya dace mu
koma sabon gidanmu,ko ya ki ka gani?nida
zaka ma barni anan nafi so.ya ce, a a ki sa su
hajjiya su tsire ni kenan,kiyi hakuri ban dai sai
mana sababbin kaya ba,yanda na ci
buri.amma in sha Allah in komai ya lafa zan
siya.ta ce, too ai wadannan ma ba suyi komai
ba,zaman duniya Allah na tuba sun ishe ni.shi
dai haka ya koma ranan lahadi tare da yan kai
lefe, sun samu tarba sosai, sai dai ba su samu
tukuici ba, saboda lura da suka yi ba babban
akwatin tare da sauran kaya.bayan
tafiyarsu,ashura ta tada balli har da
kuka.hajjiya kuwa ta tsare shi lalle sai ya fadi
ina suke?ya ce, ya ba matarshi saboda bai
samu halin yi mata kaya ba.daga ashura har
hajjiya suka rufe shi da fada,me yasa bai dauki
masu arha ba?bai samu sakar ba sai da ya
sha alwashin biyanta bayan biki.hajiya ta
hakura amma ashura sai masifa take
yi,wannan yar kauyen banzan me ta sani da
zata kwasar mata kayan masu tsada?nan take
ya daure fuska tare da fita daga gidan.
Ikilima sun tare, koina fes koda ba sabbin kaya
daki suka sa ko ina ya birge mutane.hajiyan
shi ma tana gidan don dama da gefen da ya yi
na saukarta,sai coridor,cikin coridor din aka
shirya dakunan bacci,ga na ikilima.na yara
manne da nata.sai na marya manne dana yara
maza,gefe na mahmood sai hayar
kichin,kowanne da toilet ciki.shi kuma dakinshi
ma kulle yake don ba ko katifa.duk gidajan
biyu fannin ango da amarya ana ta shiri bare
ma gidan amare.da yake ita dole ta aje aiki
tunda ba za a bari suyi aure karkashin banki
daya ba,sai dai ya sha mata alwashin sama
mata a wani banki.kyua iya kyua ashura
tayi,jiki ya gogu da dilka,kafafu sun sha lalle
sai kamshi take,ga magungunan mata da ta
dirka na tsiya.ango dama yana garin saboda
aiki ranar juma,a abokan shi suka diro,ranar ce
kuma za,ayi mothers night.
Sun hallaci gurin,kyan da amarya tayi ya
firgitata acikin jikinshi yake tamkar ya manna ta
a cikin jikinshi don sha,awa, goma daidai aka
tashi daga shagali.suna harabar ta arewa
house suna ta daukar hotuna da kawayanta da
abokanshi,tamkar kada ya bar gurin,abokin
aikinshi ya sauki su muktar.shima can zaya
kwana,sam ya manta da ikilima,don yau ko
sau daya bai kirata ba.sai da ya kwanta
abokanshi suna ta masa tsiya wai ya rage
rawar kai ko kunya baya ji,sai uban zumudi
yake ga dangenta suna ta yi maka dariya,ya
ce, ka bari wallahi na kosa a gama bikin
nan.muktar ya ce, in ko kaje kana wannan
rawar kan nan a gaban ikilima zaka kure
hakurinta.gaban shi ya fadi, sam ya manta da
ita yau,ya mike ya shiga toilet ya ciro wayarshi
a fili ya furta cewa,Allah sarki saboda ganin
missed calls dinta har guda uku.ya soma kiran
layen.suna kwance da yaranta,ta dauki waya
taye guntun murmushi takaici,sannan tayi
sallama.ya amsa yace daita.Don Allah kiye
hakuri kanwata,wayar na silent ne.dama na ji
shiru ne ba ka kira ba, na ce hausawa sun ce
ka gaida mai gaisheka ka,shi yasa na kira.to
na gode,ina yara? ta ce, sun yi bacci. kin sami
dinkunanki? ta ce, ehhh.to mai kuma kuke
bukata? ba komai.har ni?ya fada cikin
marairaice murya.taye murmushi.kai ko ina
bukatarka ka min nisa yanzu.to ko in zo ne?a a
sai da safe.har kin gaji da hira da ni?kada na
takura maka ne,kana cikin hidima.duk hidimar
da nake ciki kin sha gaban hidimar.uhmm.ta
fada cikin wani yanayi.ba ki yarda ba ko?to ya
zan yi,ba dole in yarda ba. to bari na barki ki
huta masoyiyata.ta ce, hummm!ko da bata
yarda da abinda ya ce ba a kalla ta ji dadin
yanda ya nuna kulawar shi,shi ko ana shi
bangaren gani yake bai kyuata mata ba.
washegari tun safen jumaa,a ke tururuwa
gidajan biki , kide kide kuwa gidan da amarya
suke ita da kawayanta ba dama ne. karfe daya
daidai aka daura auren,suma can gidan ango
dam da kawaye da dangi,ikilima tana sanye da
atamfar da babanta ya yi mata kala biyu da
zanin gado,danlamin su ya sai mata
kuloliabinci sababbi,matan abokan shi kuwa sai
surutu suke yi suna fadin ai maza maciya
amana ne, kowa ya ce namiji uba ne zaya mutu
maraya.waye waye.ta ce,ba haka bane.wallahi
ni ban ga laifin namiji ba, Allah ne.suka yo
mata caa.kannashi har suna cewa,ai ga shi
nan kayan fadar kishiya sai da aka kwatar
mata.ta ce, to ai ba addini ba ne,ba wata aya
ko hadisi da ya ce don miji zai aure sai ya
maka kaya.sai dai kyuatatawa yana da
dadi.suka sake mata caa akan ta fadi
haka,kowa da abinda yake fada mata.wannan
su ce wawiya,wannan su ce sakarya,wasu su
ce ta rako mata.karar wayarta ne yasa ta ce ku
saurara min ga ango nan ya kira,ta nufi toilet
da gudu,suna ta mata tsiya,tayi sallama ya
amsa cikin zumudi ya ce da ita.kanwata an
daura aure fa. wani abu yazo ya tokare ta a
kirji,kadan ya rage numfashinta ya dauke.ta
danne ta ce,to madallah, Allah yasa
alkhari.Amin, nagode.ki fadawa su
hajjiya,sannan su jamila su share dakin
amarya,kun dai dora,musu abinci ko?don
yanzu zamu dauko hanya ta kasa amsa
shi,saboda kuka da ya subuce mata.tasa hanu
ta toshe bakinta don kada ya jiyo ta,sai da ta
hadiye kukan sannan ta ce kana ji na?
ehh,yanzu ina jinki. na ce kun dora musu
abinci?ehh zamu de dora yanzu. yayi dif don
ya ji muryarta na rawa.yayi kasa da
murya.kuka kike yi ikilima?
MABUDIN WAHALA 3**8
A a. sai kuwa kukan ya subuce,taye maza ta
kashe wayar.sai da ta sha kukanta mai isanta
sannan tayo alwala ta fito tana cewa da su.
too duk mai niyyar sallah lokaci ya yi,ta dauko
hijabi ta tsada sallah lokacin ya yi.ta ji sanyi.da
ta idar ta ce,to an daura aure fa jama,a ku taya
ni da adu,a.ta nufi inda su mahaifiyar shi da su
hajjia uwa ke zaune ta sheda musu sakon shi
cewar an daura,sannan ta shiga hada kayan
miya don yi musu girki.da guda suka shigo,
misalin biyar na yamma.gaban ikilima ya shiga
faduwa,sai kama anbaton sunayen Allah
SAW,ta shiga yen zikiri cikin ranta.suka je yi
dankin su dakin amarya fa ya ji kaya masu
tsada,gado ma saiti biyu ne,dayan sai suka sa
dakin shi.kichin kuwa sai suka tattara yan
komatsanta gefe suka danke shi da kayan
kicin masu aiki da naurar lantarki.aka gabatar
musu da abinci,da guzurin su nan suka fito da
naman kaji da kalolin lemuka suka shiga
ci.kawayan ikilima sai surutu suke yi,wannan
ta ce lallai kin ma zama raba danni kenan,sun
danke dakin miji da kichin.ta ce, arziki ne,
amma a ranta ta ji mamaki.kiran sallar
magariba yasa kowacce tattara komatsanta
don zuwa gida.wannan ta ce, na bani har
magariba tayi ban ji ba,gashi ya ce hudu ta
mini a gida.haka dai suka yi ta surutan su
suna shiri kafin wani lokaci shiru ba kowa su
watse,dangin shi ma duk masu aure, sun
gagga dakin amarya sun kama gabansu.ikilima
ta share dakinta ta turo kofa taye sallah
tayewa yaranta wanka, tana musu shirin bacci
sai gashi yayi sallama,tun da suka zo ma bata
sa shi ido ba.ya ji wata danyar shadda sai
kamshi yake, dama shi gwanin tsafta ne.ya
shigo ta mishi sannu ya amsa, idanunshi na
kanta,ya zauna kusa daita.Ikilima kin sani cikin
wani hali,mai yasa ki kuka dazu?ta dube shi,ta
ce ban fa yi kuka ba.ya matso ya rungumo ta
jikinshi nayi miki abinda mata basa so,na sani
ban kyuata ba ki yafe mini.ta kasa tare
hawayen idanta,dole ta bar su su zuba.ta ce,
ba ka mini laifi ba ni.ya dago fuskarshi yana
share mata hawaye.yi hakuri, Allah yayi miki
albarka.ina alfahari da ke.kin ga khalil na kallo
mu kada ya zata dukanki nayi.ta mike tsaye
ina maka murna cikar burinka,Allah bada
zaman lafia.ta dauki ummita zo mu je kuye wa
hajjiya saida safe..
Ya ce, wanka zan yi, kuma zan so ne ki min.ta
dubi fuskarshi,ina zuwa. zamanta tayi suna
hira da su hajiya,ya gaji ya tashi ya shiga
wanka har ya fito yana cikin sa turare ta
shigo.wani shegen yadi yasa fari tas tas,mai
laush da tsada.sai kamshi yake.ya dube ta ta
ce,kayi kyua.sallamar su muktar ce ta hana shi
magana.ya dubi ikilima,to ga su nan za su min
rakiya,ko za ki zo muje? A a saida safe. Allah
ya kai mu. ya fada yana mata
murmushi,sannan ya fita.ta kulle kofarta ta
key,ta tsaya tsakiyar daki rike da haba,Oh ikon
Allah!ta isa gado ta kwanta,ta lumshe idon
tana asu,o i,ganin baccin yaki ta mike ta dauro
alwala ta tada sallah,sai taji duk wasu lamuran
duniya ta zubar su tunda ga ta gaban
ubangejinta.ta yi kusan raka,a takwas kafin ta
soma karatun qurani.sai guri uku da rabi bacci
ya soma zuwa mata,don haka ta kwanta,sallar
asubahi ne ya tashe ta,da ta idar ta nufi kichin
don hada abin kari ta da wuri saboda
baki.Turus tayi ganin yan komatsanta a gefe,
taje ta kwashe ta kai dakin yaranta tunda ba su
soma kwana ba, ta kunna risho ta shiga
aikinta.su kuwa ango da yaga su sulaiman za
su dauko doguwar hira sai ya ce su kama
kansu,kawaye ma suna gefen baki,nan suka yi
musu nasiha sannan ya raka su.Sun ci kazar
su mai dadi da madara mai sanyi, ya duba text
din da ikilimata turo mashi, cewa kada ya
manta da sallar ma,aurata.Ya dube ta ya
ce,muje muye alwala ta ce ni nayi sallah.ya ce,
na sani. ta kashingida.to kuma ta mai zamuyi.
Ta godiya da Allah da neman zaman lafiya,ta
taba baki.har yayo alwala ya fito tana zaune
can dai ta mike tana tsaki da mitar cewa ita
duk ta gaji.suna idar da sallah ya dafa kanta ya
yi mata adu,a sannan aka bude shafin
soyayya.magungunan mata data dirka sun
riketa shi,don haka bai san budurwa ba ce ko
ba ita ba ce,illa dai kusan kwana yayi yana
bata sako,wannan ya ja musu makara sai a
daki yayi sallah bayan yayi wanka.lokacin da
suka fita kusan goma saura,kawaye da yen
uwanta duk sun shirya suna jiran fitowar su shi
ne suyisallama,ikilima ta gama abin kari ta
wadata kowa ya koshi,tayi wanka tasa dayan
zanin na gurin babanta,ta dauki littafinta
muwadda ta zagaya bayan dakinta tasa kujera
tana dubawa.sai dai kun san kishin ranta sai
zafi yake,ta ji har mahmood din ta tsana,kuma
bata son kowa ya dame ta yana fitowa dakinta
ya shiga,ba kowa. ya nufi gurin su hajjiya zaton
shi tana can, suka gaisa bai ganta ba,khalil
yazo ya gaishe shi ya ce khalil ina mamarka?
khalil ya ce ta na dakinta.mohmood ya ce a a
bata nan.ya mike ya koma dakin bata nan, ya
kira wayarta dama ta kashe,duk ya firgice ya
soma zaga gidan.khalil ne sai can ya tuna da
gurin da take karatu,ya ce abba na san inada
take karatu.ya rike mishi hannu sai ko ga su.ya
jingina da bango yana kallon yanda ta tsura
ma takardar idanu yasan ba karatu take ba
tunani ne kawai.khalil ne ta ji ya kwanta a
bayanta.
Firgigit! tayi,sannan ta ji kamshshin
turarenshi,nan take ta daure fuska tamkar bata
taba dariya ba.ta kuma ki kallon inda take
zaton yakr ta kai hannu da dafa khalil tare da
cewa.ba na ce kaye wasa da ummita ba?bana
son a damai ni karatu zanyi.ni da abbana ne.ta
dan bude murya sama kadan.na ce karatu zan
yi ko?oya koma gurin su hajiyakaye wasa da
ummita.ta sake maida kanta ga littafintatamar
tana karatu.ya iso ya tsugunna kusa da ita
yayin da yake kokarin yi mata tattausan
murmushi da yake zaton zai sanyaya mata
zuciya.
Barka da safiya ranki ya dade,ba tare da ta
dube shi ba tace mishi.an tashi lafia breakfast
dinku na kichin dinku too kalle ni mana.ya ce
da ita.yi hakuri ina karatu ne,ta fada a
tausashe.wayar shi ta soma ruri,yana dubawa
yaga ashe amarya ce.daga inda take zaune
tana jin muryarta,ta ce beby ka zo sun gama
shirrin tafiya.ya ce, ina zuwa my.sai kuma yaye
shiru don ya tuno a gaban wanda yake.abin ya
kunnata,ta sake hade rai.yayi shiru sannan ya
mike.ina zuwa,ya ce, ba sai ka dawo ba,ina
bukatar kadaici ne.ya kara yin zuru yana
dubanta,sannan ya wuce.ta rufe littafi tare da
dora kanta bisa gwiwoyinta,gaskiya kishi ciwo
ne.ta furta hakan a fili.lokacin da yaje yan
uwanta suka ce,ta ina ne dakin mahaifiyar shi
mu kaita.ya nuna musu lokacin su hajjiya uwa
sunzo,bayan sun gaisa,sai suka ce ga fa
yarinya amana,in tayi ba ga daidai ba a kwaba
mata.hajiya ta ce,to.su uwa wannan aikin ku
ne,in dai ba a nan nake ba,hajjiya uwa suka ce
insha Allahu,Allah dai ya basu zaman
lafiya.Hajjiya uwa ta ce,ku kai ta gurin abokiya
zaman tata ku dan musu nasiha.mahaifiya shi
ta ce kuma kuyi wa yarku nasiha sosai,mun
san halin uwargidanta akaw kawaici.
Suka ji haushi,wata cikin su tace too muma
tamu batada matsala.suka mike fuu,ba su
samu ikilima a daki ba, ya ce su zo gata
nan.har sun ce a a ya kai ta da kan shi ya
hada su, sai ya ce su dai kaita din. ganin su ta
fadada fara,a tare da sakin fuska,ta ce su je
dakin mana suka ce a a sauri suke yi daman
dai su kawota gata nan amana a zauna
lafiya,ta ce ba komai.suka ce mun wuce,ta biyo
su tana musu adu,a Allah ya sauke su lafiya.ta
nufi girki rana a inda tasa kayan girkinta.ya
shiga gurin amarya ta ce,mai zaka basu zasu
tafi?ya dube ta ba ni da kudi,dubu bakwai ne
dani kuma kinga gobe ko jibi da asubahi zan
tafi,dole ne na bar muku wani abu.Ta hada
rai,yanzu don Allah shi kenan kuma yan uwa
nawa suzo su tafi hannu rabbana?gaskiya
wannan abun kunya ne. ya ce,ashura ba ni da
kudi kin sani.dubu hamsin na dauki hayar
motocin da dangin ki suka zo zuwa da
dawowakwana daya,ban da motar kaya.ta ce,
in dai ba zaka ba su ba shi kenan kawai.ya
ciro kudin to ga dubu uku ta zaro ido dubu
uku?bar su gaskiya.su raba nawa nawa?
Ya ce,to ga hudu,nima mamana an jima zata
tafi.ta amsa rai bace ta bi su ba tare da mishi
godiya ba.ya nufi dakin ikilima,bata ciki.ha
hangi khalil kofar dakin da yake matsayin
nasu,ya nufe shi sai ya hange ta ciki tana
yanka albasa,ya nufi ta da mamaki.me ki keyi
a nan?ta ce.girki.ya ce.kichin din fa?ta ce,
bazai ishe muba, kayan ta sun cika,yayi
shiru,sannan ya nufi kichin din da kyua da
tsaruwa da kichin din yayi bai ga amfanin shi
ba,matsawar ikilima ba zata amfana da shi
ba.ya dawo gurinta,ya ce ki koma kichin kiyi
amfani da kayanta.ta dube shi da murmushi ai
ba zai yiwu ba gaskiya,ba haka ake yi ba.ka
barni kawai na dinga yin nawa anan.ya ce,sam
gidanki fa kichin dinki ne in har ba ke ce za ki yi
amfani da shi ba gara ba a gina shi ba.ya
soma diban kayan yana maida su kichin ya
kwashe wasu kayan ashura ya tara mata su
gefe yasa na ikilima dole ta koma kichin.bayan
ashura su hajjiya uwa da maman shi suka
soma shiri tafiya.lokacinne suka shiga
ganindakin amarya,gado ne dan italiya kujerun
leda,ta kai su dakin shi hajjiya hajjiya ta ce nan
ba dakin shi ba ne?ashura ta ce,eh, ai gadon
shi ne.hajjiya tace,to ai ba zaya yiwu ba kuma
kisa kayanki a turaka shi ne zai siyo yasa
tunda ba ke kadai ba ce.
Ashura taye turus,hajjiya ta dubi
mahamood.lalle a cire kayan nan.ya ce mata
too. dubu uku yabata ta ce a a ita tana da
kudin motarta,ya ce shi dai ta karba ta amsa
sannan ta hada ashura da ikilima ta musu
masiha.ta kuma ja wa ashura kunne kan dole
ne tabi ikilima.ashura fa an kaita bango,don
haka suna tafiya ta shiga daki tana ta rusa
kuka.da ya shiga ta ce,ita de zata tafi gida don
baya sonta danginshi basa sonta.ya
rungumaita ta wa ya ce bana sonki? yayi ta
lalashinta da kyar tayi shiru.da dare ikilima
taye abinci tasa tasa musu shi ne yakai
musushi da amarya.ta kalli abincin ta yatsina
baki,wai ita ba zata iya cin wannan abincin
ba.kuma yiunwa take ji.ya ce, to me za ta ci?ta
ce indomie .shi da kanshi ya shiga kichin yana
dafa mata.ikilima ta shiga kwanukan da suka
ci da yarantata ganshi,bai so ba ta ce Ah,ba ku
koshi bane ?ya ce, a a ita ce dai take sonci wai
bata son cin shinkafa.ta tsura mishi ido,sannan
ta ce,hummm!ta nufi dakinta.
Ya ce,don wahala? ki barsu a gida
gamu.ashura ta ce,ni fa ba zan zauna ba, mu
dan fita mana naga yanayin garin naku.ya ce,
to.ikilima ta koma dakinta ta dauko jaka da
nikab ta goya umminta tana daura nikab suka
sake fitowa,ta yafo wani dan gyale sai kace na
yan yara.yazo kusa da ikilima.ranki ya
dade,ina makullen gidan?ta dauko mishi yasa
hanu ya zaro ummita daga bayanta.zo muje
mamana.ta ce, da ka barta baban khalil,kada
ta bata muku gayunku.ya dubai ta sai kuma
yaji nauyin yi mata magana.wane bata gayu?
ya dube ta kina da kudin mota ne,don wallahi
in zan tafi ma ban san ina zan samu na mota
ba,na yi kaf.
Ta ce, ina da shi,sai na dawo.ta maida zanin
goyon ta rufe dakinta.ko yau a makaranta bata
da nutsuwa,tana dai yin adu,a saukin ta ma
kenan yau ma malaminsu sai da ya sake yi
mata nasiha dan ya lura bata maida kai sosai
kamar da.da suka fito juwairiya ta ce, ki nutsu
ikilima,ke yarinya ce kada ki jawo ma kanki
hawan jini da kuruciyarki.ranar bikin nan yan
makaranta suna ta yabon ki,don Allah ki
nutsu.ta ce, humm,kishi da zafi juwaira,yanda
yake zumudi kanta da yanda yake rawar kai ke
ban tsoro.yau fa shi daya suka fito sannan ta
ce su fita taga gari,ko musu yace too.jawaira
ta ce,ki dauke hankalinki,ki kama girmanki duk
da naga wannan ta girme ki amma ki rike
girman ki don Allah ya dora miki.shawarata da
ke kenan,kin san ita amarya ko ta buzuzu ce
sai an yi dokinta.ita da shi duk ki cire su
gabanki.
Ikilima ta ce,too juwaira,na gode,ni ma da kishi
ne matsalata,sai dai ina ta yin adu,a.juwaira ta
ce,shi ne kawai zakiyi.sanda ta koma gida a
waje ta same su shi da yarann suka mata
oyoyo,ta daga khalil ta sauke sannan ta daga
ummita. sannu da zuwa mallama.ta daga
nikab sannu,har kun dawo? ya ce, ehh,
tuni.suka nufi kichin, amma ashura tana daki
kwance tana bacci.haka da dare ta ki cin abinci
yau ma,washegari yayi shiri da wuri,ya shigo
dakin ikilima tana karatun ku,ani ya zauna gefe
gadonta,ta kai aya sannan ta gaishe shi.ta
tsuguna yayi kissing din yaran,ya ce zan tafi
don Allah ki ta hakuri kin ji,sannan ba kudi
gurina ko zan sami dubu biyu gurinki?ta tashi
ta bude zif din jakarta,ta ciro dubu biyu kudin
da ya ba hajiya shi ne zata tafi ta bata,ta ce ,
ga dubu biyu. ya kalle ta kina da wasu don yan
matsalolin gida da zuwanki makaranta?ta
ce,Allah zaya rufa asiri.ya ce amin. ta bashi ta
na cewa,ka dauki komai ko?ya ce,ashura ta
hada.ta ce, to Allah tsare, ka sauka
lafiya.Ashura na tsaye kofarta sanye da kayan
bacci ta mika mishi jakar ta ce beby sai mun yi
waya.ya dubi ikilima sannan ya ce to don Alllah
kuye hakuri da juna.ashura taye cikin
dakinta,ikilima ta rakashi har waje,ya tafi yana
mata byy.tun tafiyar shi ashura bata fito
ba,koda ikilima tagama abin karin kumallo har
daki ta bita ta buga ta bude,sannan ta ce
lafiya?cikin wata yatsinar fuska,ikilima ta daure
fuska don bata son raini.break fast
dinkine.daina sa abincinki da ni,ni na ji ci zam
fito in yi nawa.inji ashura.ikilima ta ce ok.ta
juya ta tafi.tsaki taja ta maida kofar,tana jin
haushin ikilimar nan don ta kula mahamood na
ganin darajanta.don ta tuna yau da asuba ya
tashe ta wai ta hada mishi kaya ta ce ya bar ta
tagaji,wato bari ya je ikilima ta hada mishi,shi
ne ta tashi da sauri tana hadawa.ta lura ikilima
taga shgwaba shi ne,komai sai ya ce yi min
kaza ita kam gaskiya ta gaji kamar dole?Shi
kuwa daman daga nan office ya wuce,sai da ya
taso sannan ya nufi gida,ranar ne fa ya fara
gane ashura daban ce,da ya bude jakarshi
kayan ba gyara,duk a hargitse wani ma riga ce
babu wando babu neck tie kayan shafanshi su
mai zuwa turare duk babu sai makilin ta saka
babu brosh.
Ya rike kai,dan canjin hanunshi shi ne ya je ya
siyo duj abin da babu,don haka zakuwar shi
yana tunanin bai ga ta zuwa gida wannan satin
ba dole sai sati na sama,lokacin wata ya
kare.ya dan samu wani abu.Sai da ya kwanta
ya dauki waya sai ya soma tunanin waya zai
soma kira?duk da ashura sau biyu tana kiran
shi yana office ya ce mata ta bari zai kira text
din ikilima ne ya shigo,a in da take cewa da
shi.ango nasan yanzu kana nutsu,ina fatan
kana cikin kwanciyar hankali.ni da yara munyi
kewarka,kayi bacci lafiya.da yagama
karantawa,sai ya yi murmushi a fili ya ce,ikilima
yar aljannan ce.ya soma rubuta, Nima ina cikin
kewarki yar aljannan,ba zan iya manta
karamcinki ba. Zuciyata tana girmama ki tare
da jin nauyi ki.gangan jiki tana jimain rashinki
kusa,sakonnina sun rasa masaukin su na
asali.Ina fata za,a share duk wani tsohon sako
na da kafin na dawo.sai dai ina ga za ki ci
gaba da hakuri tare da rike gidan na har zuwa
sati na sama,don ke ce halifata in bana
nan,saboda matsalar kudi zan bari sai karshen
wata.i
Ikilima tayi yar dariya bayan ta gama
karantawa,sannan ta rubuta kada ka damu,zan
lura da gidanka da dukiyarka har da
masoyiyarka,ina nufin amaryarka.sai dai kada
ka manta ita masoyeyarka ce zata ci gaba da
karban sakoninka har zuwa lokacin da zata
cinye kwanakin amarcinta,wato kwana bakwai.
kayi kwana biyu kafin ka tafi in ka dawo kayi
biyu,in ka muma dawowa haka in ka sake
dawowa ne zaka yi daya.too sai dai zan yi
maka aibishir dama lokacin aurenka ban baka
gudumawa ba.A matsayina na ta hanun
hagunka na yarda kayi ta sauka dakin
amaryarka duk lokacin da ka dawo har zuwa
lokacin da zaka ji da kanka cewa ka gamsu da
gudumawata.Yana gama karantawa ya hade
rai kamar tana kusa dashi,ya kira layinta.ta
daga ya ce,ke in ji wa ya ce miki zan yarda da
wannan shirmen naki?to bana son
gudumawar,kina cewa kece ta hannun hagu
karna sake ji.ikilima ta ce asalin kashin
hakarkarin,sannan duk wandda zan so,sonta
yana bayan naki ne,ta ce,to Allah ya baka
hakuri,amma mu da aka yi auran hadi ba shiri
fa in ka tuna yanzu ko so ya hada........... ya
katse ta da tsawa,wai ba na ce ki min shiru ba
ne?ta ce,too na yi me sona,na ji kana sona kayi
hakuri.ya kashe sannan ya share sakonta na
karshe.
Ya kira kayin ashura ta daga cikin sigar
shgwaba ta ce,beby sai yanzu zaka kira ni don
Allah.ba sai na fada miki ba,kin dai san
yanayin aikinmu. na sani, amma yanzu nasan
kana kwance ne kawai,ya ce, ehh, kanwata na
kira tukunna.tayi tsaki to ina ruwana da wata
kanwarka?ni kaina na sani.niko kinga inada
ruwa harda tsaki da ita.taja tsaki aje wannan
topic din,kayi missing dina?ya ce a lots ma
kuwa.ta ce,nima haka .ji nake kamar na janyo
week end wallahi.Gashi sai na sama in mun
samu wani abu sannan na dawo,yanzu ba
kudi.ta ce, cikin shgwaba,haba bebyna,gaskiya
ka sama min aiki a nan kadunan ba zan jure
rashinka kusa ba.ya ce, a a bamu yi cewa
kaduna ba.ta ce, to ina dai maka tuni da
kayana da aka diba gidanka in kasamu kudi
kasan shagon kuma kasan kudinsu.gaskiya ba
yanzu ba,ina da al,amura sama da wannan sai
na gama su.sai da safe.ya kashe wayarsa nan
take ta kira mahaifiyarta suna gaisuwa ta ce,
hajiya mahmood za su yi albashi,ki ce masa ya
sai min kayana,ni na mishi magana wai ba
yanzu ba,ta ce,too zan masa.
Shi kuwa kwanciya yayi yana so ya daidata
halin ikilima da ashura sai yaga sam ba za su
hadu ba ma.zuciyarshi ta ce,zabin Allah bashi
da mahadi,ikilima daban ce.haka suka ci gaba
da zama ashura ko ummita ta rarrafo ta taba
mata kofa da tsawa take koranta,bare
khalil.duk ikilima kauda kanta tayi,alwashi ta
sha ba za ta taba kula ashura suyi sa in sa
ba,nata ganin in haka ta faru ta ci
baya,girmanta kuwa zai fadi.amma in ta kame
kanta dole ne ashura take shakkarta.Da ranar
da zaya zo tazo tun safe ikilima ta shiga gidan
makociyarta lubabatu yar birnin kebbi ce,mijin
ta ma,akaci ne a abuja yake aiki,sun fi sabawa
da ikilima ta ce, luba don Allah bani aron a,i me
aikinki ta siyo min kayan kosilo.luba ta ce,ina
da su bari na dibar miki.ikilima tace,ko dai bari
ki satar mini?luba ta ce, sata kuma? ikilima ta
ce,too ai kyauta da kayan miji baya nan sata
ne,in bai sani ba.har sai in kin nemi izininshi
sannan zaki bada.luba ta ce, to shikenan na
daina.a,i zo ki siyo mata.yau baban khalil na
hanya kenan?wallahi, na rasa ma kalar jus din
da zan masa?ki masa na shinkafa mana.inji
luba.ban iya ba.inji ikilima too kuna da
shinkafar tuwo eee muna da ita.luba tace,too
jika rabin gwangwani zan shigo.
Ikilima ta koma gida ta shiga masa fred rice,ita
kuwa ashura dama gidan sakina nan ne gurin
zuwanta,ita ma makotansu ne amarya ce daga
abuja aka kawo ta,irin yayan masu kudi din
nan ne ga salo hali dai yazo daya.kullum in ta
shiga gidan sai dare take dawowa.ko sharar
dakinta bai dame ta ba bare cikin gidan,ashura
daidai kayan girkinta

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment