Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana kudundune kan gado sam bata
son su hada ido sbd wata matsananciyar
kunya, ga surutn daya dinga yi tana tuno su.
Yaxo ya xauna bakin gado "tashi kije kiyi
wanka kanwata" ta tashi tana nade jiknta da
zanin gadon, sai dai kanta na duke data mike
kuwa hannu tasa ta kare fuskarta dashi. Shi
kam daria yayi mata ynda ta cukwi-cukwiye
jiknta da zanin gado. Tana zaune cikin baho
tana tuna abubuwn da suka faru, ynxun nan.
Shikenan ynxu ta xama mace sosai, haka nan
batayi bakinciki ko jin haushn abnda mahmud
din yai mata ba, sai ma take ganin ynxun zaifi
bata daraja da kulawa. Ta leko ta gefen kofa ta
hange shi kwnce rigingine kan gado, idanunshi
suna kallon silin, yana sanye da boxer. Tunani
yakeyi na abinda ya faru ynxunnan, kai gskia
auren sunna yayi, ya kamata duk musulmi ya
gode ma Allah, ynxu da zina ne memakon
farinciki sai bakinciki da dinbin zunubi. Sannan
dk wnda ya aikata zina boyewa yake kar a
ganshi, in km ciki abokiar zinar ta samu
shikenan ta shiga gararin ryw, danginta su ki ta
shi kanshi saurayin yace banashi bane
danginshi ma suce anyiwa dansu sharri. Dan
ma in an haifa kila a yar, inya girma yaji cewa
shi dan tsintuwa ne bakinciki yasa shi gararin
ryw, in ma ta rike shi inya girma wataran dole
yace ina dangin babana? In bata nuna mishi ba
ya tsaneta. Kai akwai wanda ya shake uwarsa
kan cewa sai ta nuna mishi ko hoton babansa
ne.
Muryarta ce ta katse shi da cewa "dan miko
min zanina yaya. Firgigit! Ya kalli gurin bayin,
yace me kikace kanwata? Tace zani zaka bani
cikin shagwaba tai maganar, ya kwaikayi
muryarta tare da cewa to yar kanwata,
amaryata" ya dauki zani akan akwatinta ya
mika mata, ya dora mata kan hannunta sannan
ya sumbaci hannun. Da sauri taja hannun ciki
tare da cewa "yaya bana so" yace sako ne
shima wannan din na baki kanwata" ta daura
zani ta fita ta rufa da tawul dinsu na wanka,
zanin gadon ta saka cikin robar wanki, idonta
rufe da tawul din ta fito. Yana tayi mata daria
game da tsokanarta cewa bari ruwan saman
ya tsaya inje in fada ma baba in ce...." ta katse
shi da sauri "kace me? Tare da cire tawul din
dg fuskarta. Yace "yee! Naga fuskarta me cewa
yaya kayi hkri zan tsaya" ta sake rufe fuskarta
dn ta gane wayo ya mata, zolayarta ma yakeyi.
Daya fito ya samu ta saka kaya ta dan saci
kalln shi tana dan murmushi yace kanwata
amarya bari inxo in hada mana tea dole yau na
nemo miki kazarki dakika ki ci ranar daren
amarci. "tagumi tayi tana mamakin shi sam
bata yi zaton yn mgn ba da lkcn da yake zuwa
gurin anty nafisa, kai ko ynxun da akayi musu
aure bata zaci cewa yana daria ba.
Shine ya hada musu tea tace ita b ynxu ba, ya
dinga tarairayarta hatta da gyaran daki shine
yayi ranar ta dinga mamaki dama maxa abnda
suka fi so kenan ko me? Sai kusan biyu ruwa
ya tsagaita, dama shine ya musu limanci
sukayi sallar azahar. Da ze fita yace kanwata
kada kiyi girkin komai ki huta kiyi bcci zanje
shago. Me zaki ci in shigo miki dashi? Ta dube
shi "ka dawo lfy yaya ni bana son komai. Ya
matso ya dago kanta ya sumbaci goshinta,
idanunta a lumshe sannan ya fita cikin farinciki
da annashuwa, wnda ada yafi xaton samun hk
dg nafisa. Allah knan me juya lamarinshi ynda
yaso, ita kuwa cak ta mike ta kwnta kan gado
tare da rungume pillow. Yanayin yai mata dadi,
Allah yasa su dore cikin farin ciki tare da duk
wasu ma'aurata musulmai.
Nafisa wadda ke ta kai-kawo cikin dakinta,
zuwa yau ta soma tunanin ko kudi zasuyi
maganin komai to bazasu iya yin na so ba, ga
kudin ta soma jukuwa amma sun kasa mantar
da ita son mahmud, dama shi wayayyene data
jawo shi jikinta ta sakar masa kudi suci gajiyar
soyayyarsu. To ko zata gwada xuwa minna ne?
Ta sani ma ba son ikilima yakeyi ba, abnda ma
ko dama ba shiri suke wani yi ba, km ynda ta
san shi miskili km tasan irin abubuwan dayake
so tasan matar dayake so ba xai kula ikilima ba
dn bata dace dashi ba. Ranar hk ta kwana
zullumi ko alhji jamilu zai brta yau sati 3 da
biki? Sannan inya brta mahmud ze yrda km ze
amince suyi soyayyarsu cikin jin dadi? Wata
xuciar tace da kamr wuya. Ta kira shi yau
kwananshi 4 wai suna south africa, tace tana
son xuwa minna ne ta duba mamanta, in ze
bari. Sai da yayi yar daria sannan yace "nafisa
kin kasa fahimtata, ni mu2m ne wnda yasan
yancin dan adam, kada ki damu dk inda zaki
kije inda kike so a lkcin da kikeso, kiyi abnda
kike so, kici abnda ranki yaso, ba matsi. In ina
son mgn dake xan kiraki ba sai kirani ba. Ynxu
xaki iya jan motar ko da direba zaki?
Tace xan gwada xuwa in gani ko xan gane?
Yace tukin nake tunani, kada ki gaji. Tace xan
iya. Yace shikenan, xan sa a tura miki kudi sai
ki musu tsaraba. Tace "to na gode. Yace ki rufe
tsakanin mu kada ki yrda kiba wata kawa ko
mahaifiyarki lbrin cewar ni ba namiji bane. Tace
kada ka damu ba me ji. Yace "Good, zakiji alart
in kudin sun shigo, sai na dawo. Tace, to. Bata
samu wata matsala ba dg abuja xuwa minna
sbd motocin gaske ne. A gjy ta isa gidan
mamansu. Ta samesu suna ta hira da shewa
ita da kawayenta, nan fa suka shiga murna ga
hajia nafisa ga hajia nafisa, sai cewa suke dubi
ynda tayi bul-bul, jiki lumi sai dai tayi rama.
Hajia baba tace kun san maxannan ba dama, a
sa samu yarinya bare wannan yar kare ta
diddirki kayan mata ba dole ne ya makale mata
ba? Kin ko san wannan harkar tana sa rama.
Sauran suka ce, haka ne. Waya sani ma ko
ynxun da ciki? Nafisa dai sai dan yake takeyi.
Haule tace anya da cikin nan kuwa? Wata tace
kin san yayan zamani ba kowane yake son ciki
da wuri ba. Ita dai jaka ta balle ta shiga rabar
musu da kudi. Can gurin karfe 1 tace bari taje
gdan kawayenta dk da ba yau xata koma ba.
Gidan safina ta soma xuwa, suka rungume
juna da murna. Nafisa tace ina ta xuba idon
ganinki shiru? Safina tace ke dai xauna in kawo
miki abin sha, sannan musha lbri.
Suna cin dambun nama da hollandia suna ta
lbri. Nafisa tace kawata alhji sanin ya gane
kurensa ne ynxun ko? Safina ta dafa nafisa tare
da cewa wannan dan iskan mutumin ne ze
daina halinsa? Nafi tace hkri kike yi kenan kiyi
xaman kudinshi? Tace kudi fa kika ce? Ta
yatsina mouth, ai karamin me kudi ne wannan
ba irin naki ba, dama kudin nasa dk a wajene.
Tnda ya bani na amarci ya daina. Mafita na
samo ma kaina, mama zee ma ynxun da hk ta
amshi shawarata asirinmu a rufe . Nafisa tace
to nima ku fadan shawarar ko zata amfane ni?
Safina tace, ke ni kin wuce nan, mu dan mu
samu kudi muke yi, ke ko kina da kudi. Nafisa
tace fada min. Safina tace alhazai muke bi.
Nafisa tace a'uxubillah! Safina da auranku fa!
Safina tace da auren fa! Mata dubu nawa ne
masu auren suke km bin mazan? Kudi ba karya
bane, ke kin samu ne shi yasa.
Nafisa tacn to maxanku sun sani? Safina ta ce
dube ki da wani sabo, ya za'ayi mu bari su
sani? Iyaka da sun fita mu ma mu fice. Wancan
satin har abujanku, ya min karya yai tfy aka ce
min yana nan wani hotel da karuwai, ni km
wani dan majalisa ya daukeni mukayi abuja,
dubu dari ya bani gobe ma ze dau mama zee".
Nafisa tace wnda ya daukeki din ne km ze dau
mama zee? Tace eh, ina ruwana mijinane?
Wata kwngila ce ya bni kawata, wai in samo
mishi matan aure 40, dk guda daya ze bata
dari, ni km yan dubu hamsin. Nafi tace meyasa
yake son matan aure km har adadin arba'in?
Safina tace, Oho mishi, kila wani asirin ne dn
najh yace in ya gama da arba'in din xan samo
masa kananan yara yan sha daya. Nafi tace
"Innalillahi! Don Allah kada ki cuci yara. Safina
tace ke ni fa kudi!! Ba karya a cikin kudi.
Shegia kema ai kudin kika gani. Nafisa tace
"um ni naga kudi! Amma zuwa ynxun sun soma
fita kaina, dk da bn jike sharkaf ba. Ta tsura ma
safina ido, ta ce wlhy kawata ina cikin wani
hali, son mahmud tamkar ynxun na soma kllm
cikin tsananin begensa nake kwana. Safina
tace "gashi ya auri kanwarki, ya knan? Nafi
idanunta suka soma kawo hawaye, cikin
shesshekar kukan take cewa, ko yaushe
tunanina kenan, km dalilin zuwana minna
kenan ynxun. Safina tace don Allah ki haka
rami ki binne son mahmud, ga mijinki me kudi,
mai kyau dashi, me mahmud zaya miki wnda
alhji jamilu be miki ba? Nafi tace akwai, safina
mijina ba namiji bane, ina nufin baya iya komai
dani. Ya aureni ne kawai dn ya kare kansa
daga suru2n yan siyasa.
Safina ta saki baki tana kallon nafisa sannan ta
girgiza kai tare da cewa "tirkashi! Gaki da
rashin hkri ina nufin kina cikin mata masu
sha'awa. Nafisa tace ashe kin gano kawata,
kina ganin rayuwa zata yiwu a haka? Safina
tace ina fa! To ke ki kaso auren mana? Nafisa
tace yace sai na xube masa kudinsa, ina xan
samo su? Ni da xuwa nayi mu jone da mahmud
ba tare da ikilima ta gane ba, kin san fa shi
bagidaje ne. Safina tace "shegia nace muna
bin alhazan zakiyi min salo, kice kema irin
harkarmu ce ta kawo ki? Nafisa tace da
bambanci, nifa matsala gareni. Safina tace
kawata bb wata kwaskwarima da xakiyi,
zunubin mu 1, bambancin kina bada kudi ne dn
aikata laifin mu km mu ake ba. Nafi tayi shiru,
can tace "zunubin ne in na tuna sai naji gara in
hkra. Safina tace kin yi lkcn da kina gida, dn hk
gara ki cashe kawata, a laifukan dunia me kika
yi ma? In yaso daga baya se ki tuba, ke da kike
da kudi ma sai ki ta yin alkhairi dn ki fanshe
laifinki. WA'IYAZU BILLAH!
Safina da nafisa kuna nufin zakuyiwa Allah
wayo ne? Hakika matan aure da dama suna
cikn wannan halakar. Nafisa tace haka zanyi
km kin san Allah safina, zo kije abuja ki soma
ganin masifu iri-iri, mata da dama suna cikin
irin wanan harkar. Ga masu madigo, ga masu
ludu, safina tace to nima kwanaki wani dubu
dari biyu ya bani wai in samo masa namiji dan
shekara 14 naki, nafi tace na shiga 3! Mutane
na tsoron kwncyr kabari kuwa? Safina tace mu
br xancen tnda kin soma kiran kabari, mu ma
masu lefi ne ynxu dai tashi muje gurin mahmud
masoyinki, tn kafin jikinki yai sanyi kice kin
fasa, gashi za'ayi gwarzon namiji shine ma ze
iya da fitinarki. Ita ke jan motar har suka shigo
layin, safina ta dubeta gidanshi zamu? Nafi ta
sakar mata harara. Ba can zamu ba, me zanje
nayi? Kin san Allah safina, dk da nasan ba
sonta yake ba gani nake da mun hadu da ita
shake wuyanta zanyi sai ta mutu. Safina tace
ina ruwanki da ita, nasan dai ba kulata ze yi ba
tnda ance ranar bikin ma fuskrshi dk a daure.
Lkcn da suka tsaya a kofar shagonshi sam be
lura bama, shi yana ta harkoki da abokan ciniki
masu siyan siga, madara da sauransu
Cikin takun kasaita suka nufo shagon, kmr
ance dago sukayi ido 4 da nafisa tana sanye
da riga da skirt na wani tsadaddan material
tmkr kayan su fasa jikinta don matsewa. Dan
siririn gyale ta yafa a kafadarta. Tai kyau jikinta
luwai-luwai, hutu ya soma ratsawa. Nan take
mahmud ya daure fuska dama gashi gwanin
dakewa, sannan ya kauda kai tare da cgb da
harkar gabanshi. Nafisa suka kalli juna, safina
tace salamu alaikum" be tanka musu ba. Nafi
tace mahmud gurinka mukazo, har sallama
gashi munyi maka amma kayi mana bnxa. Ya
dube su rai bace yace "A'uzu billahi minassh
shaidanin rajim. Me kuke nema anan? Nafi tace
ynxu mahmud sbd mu kake ta'awizi kmr kaga
shedanu? Yace kunfi shaidan shedanci da
shu'umanci, dole in nemi tsari daga sharrinku.
Miyan bakin nafi ya kafe, tai ajjiyar zucia
sannan cikin in...ina tace kayi hkri na sani nayi
maka lefi, ina fatan komai ya wuce. Be tnka ba,
tace don girman Allah in ci albrkacin
soyayyarmu. Ya sake dubanta cikin harara
yace sai dai don Allah da kika ce da kuma
albrkacin ikilma bare bn ma shirya yafe miki ba
sai ranar da mahaifinki ya yafe miki. Kiyi
gaggawan barin na gurin. Ta soma hawaye, ni
kake kora? Yace na kore, ki br nan na tsaneki.
Safina zatai magana yace ban son jin komai,
ku br nan kawai. Safina taja nafisa tana kuka
rurus suka shiga mota. Safina tana bata baki
tare da cewa tuka muzo gidana mu canza
shawara ta ina xamu bullo mishi
***Shi kuwa takaicinsa daya ta zo ta tada mishi
da gyanbon sonta,alhali shi ko iklima ta mutu
ne ba zai aure ta ba. Ranshi yana zafi ya rufe
kofar shagon duk da cewa ga 'yan siyayya nan
tsaitsaye ya nufi gida suna kallonshi.iklima
tana cikin nika kayan miya zata dora abinci ya
shigo,ta dube shi tare da cewa "sannu da
zuwa" umhum kawai yace ya nufi ciki ta bishi
da kallo don hakan bata taba faruwa a
tsakaninsu. Ta mike tare da ajiye injin nikan ta
bishi.yayi rigingine kan gado,kafafunshi suna
kasa ya dora pillow kan fuskarshi.tasa hannu
zata zare pillow'n tare da cewa yayan...tsawa
ya daka mata."Ke da Allah can kada ki dame
ni" taja baya da sauri tare da razana. Ta daure
ta sake cewa kayi hakuri dama ina son in ce
baka da lafiya ne? Yace asibiti ne ni? Ta zaro
ido tana kallonshi sai ta fita jiki babu kwari
idanu suna kawo hawaye. Taci gaba da
aikinta.Maman Ummi matar gidansu tazo tace
"amarya ga wukarki" tayi saurin kakaro fara'a
tace "to maman ummi,ta amsa tana share
hawaye tare da cewa "albasar nan tana da
zafi" maman ummi tace nima yanzun na gama
fama da tawa. Ta gama dora komai amma ta
kasa shiga dakin don tsoro. Kusan minti talatin
sannan ya shiga bayi ya sakar ma kanshi
shawa.Yana tsaye kusan 4mins ruwa na
sauka a jikinshi sannan yasa sabulu sama-
sama ya fito ya canza kaya,zata shigo daki zai
fito da sauri ta koma gefe tare da firgita tamkar
ta ga abin tsoro har tana bigewa. Bai ko kalli
inda take ba ya fita.ta sauke ajiyar zuciya
sannan ta shiga ciki ta zauna a falo tare da
cewa "Ya salam,me yake shirin faruwa dani
ne?Allah kada kasa shaidan yaci galaba
tsakaninmu.
.
Shi kuwa yana fita gidansu suleiman ya nufa,ya
ko same su har da mukhtar. Suna ganinshi
suka ce "angon nan yaya ne yau?" Bai tanka
su ba,sai da ya zauna sannan yace hum Allah
ya isa tsakanina da nafisa. Suka hada baki
gurin cewa,"wace Nafisa?" Yace,in nace muku
Nafisa kun san wadda nake nufi. Nan ya
zayyane musu duk yanda suka yi,ya kara da
cewa,shi yasa naji iklima ma haishi take bani.
Mukhtar yace, ita wannan 'yar aljannar ina
ruwanta? Mahmud yaja tsaki tare da
cewa,Gaskiya mata ba su da kunya,ba su
santa ba ma. In ba haka ba dubi cin amana
gami da cin zarafin da ta min,amma har ta iya
zuwa inda nake. A tunanina nan gaba sai ta
shekara goma bata iya hada ido dani ba.
Suleiman yace,to kunya gare ta ne? Kai dai
ghara daka yi mata haka.Amma matarka kada
kasa ta cikin matsala. Mukhtar yace,gashi har
kayi kyau,zamanku ne ya sani sha'awar yin
aure,Suleiman yace ko ni wallahi. Nan suka yi
ta ba shi shawara har zuciyarshi ta sauka,ya
kuma bayyana musu abinda yayi mata tare da
cewa yasan yanzun tana can cikin damuwa.
Suka ce "don Allah yaje ya kwantar mata da
hankali. Yace,su zo suje tare su ci abinci. Nan
suka nufi gidan lokacin ta gama abincin amma
ta kasa ci taje toilet ta watsa wanka ta fito.
Gama sa kayanta kenan suka yi sallama. Cikin
sanyin murya ta amsa,duk suka zauna falo har
da shi. Ta fito cikin tsoro daga ka ganta kasan
a firgice take,fuskarshi ta soma kallo har
yanzun tana daure da sauri ta kauda kai tare
da gaida su mukhtar. Mahmud yace "ki ka ...."
Maganarshi ta katse yanda yaga tayi wata
razana har ma abin ya bashi dariya.Amma sai
ya dake.
Ita kuma maganar ce ta ji ta a sama dama
wanda ke a tsorace haka ne. Ya dube ta abinci
nace da sauri tayi kicin.Suleiman yace,kai dai
mugu ne,duk yanda akayi dukan yarinyar nan
kayi. Mukhtar yace,tunda muka shigo duk a
gigice nake ganinta. Yace,dukan lafiya?wlh ko
zagi. Ta shirya musu abinci da komai ta koma
daki ta cire hijabin ta hau gado har suka gama
suka fice,tazo ta gyara komai. Da dare dama
baya dawowa da wuri,sai gurin sha daya ko
sha biyu yake rufe shago. Tana kwance tamkar
mara lafiya ta kasa bacci shigowarsa sai ta
lumshe ido tamkar mai bacci,tasan har yanzun
da matsala tunda bai aiko an karba mishi
abinci ba.ya tsaya kanta yana kallonta,tausay
inta yaji ya san baccin cikin damuwa tayi shi.
Ya zauna bakin gadon yana shafa kumatunta
gami da kiran sunanta a hankali,"ikeelee
kanwata! Ta bude idonta a hankali ta zuba su
cikin nasa. Yace,sry na tashe ki daga bacci. Ya
kara yin kasa da fuska har suna jin numfashin
juna. Ban baki sako ba kika yi bacci bayan
kinsan ba zan iya aje shi har sai gobe ba ko?
Ta tashi zaune tana murtsuke idanunta. Baccin
damuwa nayi Yayana,baka aiki an daukar
maka abinci ba.yace,koshi nayi.Ta sunkuyar
da kai,don Allah ka yafe min laifin da nayi
maka dazu. Ya mannata jikinshi ta baya,baki
min komai ba,can ne a shago aka bata min rai.
Ta sauke ajiyar zuciya,sannan tace kayi
hakuri,Allah yana tare da masu hakuri,sannan
manzon rahama yace mu daina yawan
fushi,damuwarka ta sani cikin wani hali,don ko
abinci duk yau na kasa ci. Ya dada manne ta
"yi hakuri kanwata tashi ga namanki da
yoghurt ki ci. Tare suka ci naman suka sha
yoghurt suka koshi,yace muyi wanka saboda
zufa sai ki amshi sakon ko? Tace to tare suka
shiga bayin hakan lokacin da yake bata sakon
sai tana mamakin a duk lokutan da zai bata
sako shi baya gajiya ne? Don sakon nashi kan
dauki lokaci. Sai dai tana jurewa tare da daukar
wa kanta alkawarin ci gaba da jure amsar
nauyayyan sakonninshi.
Nafisa kam dakyar tayi shiru a gidan safina
kuka take rurus wai ita mahmud zaya ce ta ci
albarkacin iklima.Safina tace,don ki ji haushi ne
yace haka,ni a nawa ganin ki nutsu ki sakar
mishi 'ya'yan banki tsaf zamu shawo kanshi.Ai
dama ba farat daga zuwa zamu ci galabar shi
ba,sai kace bai san ciwon kanshi ba,abin da
kika mishi fa ba duk bane zai jure. In wani ne
ma dukanki zaya yi. Da kyar ta sha kanta suka
ci gaba da shirya yanda zasu sha kansa da
kudi amma sai ta sake zuwa. 2 days ta tafi
cikin damuwa.Sam bata leka mahaifinta
ba,bata san ma sun tashi ba. Washegarin
dawowarta gidan anty hajara ta nufa,suna
kwance kan gadon antyn suna hira tace tana
son tayi dinkuna don Allah anty hajara ta
hadata da telanta. Tace zan ko hada ku ga
yaron ya iya dinki.bari in kira shi ince yazo
gobe sai in sa driver ya kawo shi, nafisa tace to
washe gari driver'n mai suna bashari yazo aka
kawo shi ta bashi dinkuna tare da kudin da ya
sara mata babu ko ragi.
Wata biyu kenan da auran su ikilima koyaushe
tana son yi ma mahmud batun komawa skul
amma tana shakka,don ba wai anyi yarjejeniya
bane.yanzun dai da ta lura yana cikin nishadi
suna karin safe sai ta dube shi tace"Yayana
tunda na shigo gidannan ban taba fita ko nan
da can ba" Ya dube ta ina kike son zuwa? Tace
gurin babana,ban san matarsa ba sai
mamanmu in je? Sannan ina son inje skul.ta
dubi fuskarshi don taga ya ya ya amshi
batunta.Sai taga ya sha kunu. Gabanta ya fadi
tace "Yi hakuri in ranka ya baci" Yace wace
skul? Boko ko islamiyya? Tace duka wai
da,yace to sai nayi tunani,gida kuwa ki bari
zamu fita tare gobe ki shiga gidanmu kije gurin
mahaifiyarki ki fito sannan gidan babanku dan
can zaki yini,zan zo mu dawo. Tace,nagode
yaya. Bai ce komai ba yaci gaba da karinsa.
Hakan ce kuwa ta faru,washegari suka shirya
ta ciro safa da niqab yace,wai ke duk uwar
ranar nan da ake yi sai kin rufe fuska? Ta dube
shi "ba zan iya fita haka ba" Ya taba baki tare
da cewa manzon Allah dai yace imani yana
zuciya" ta dube shi ranta ya dan sosu ta jima
da lura da shi baya son irin shigar da take yi
tace"amma yaya hijabi cikar kamala ce da
mutunci,ya kamata ka lura da bambancin da
ke tsakanin mace mai sanye da hijabi da kuma
mara shi. Yace ni ki min sauri ba dogon tarihi
na tambaye ki ba. Tace Allah ya baka hakuri.
Suka fita tace da matan gidan sai mun dawo
suka ce to. Da ta fita kuma sai suka dasa
zancanta kun san mta. Maman ummi
tace,Aisha kin Allah,amaryar gidannan suna
bani mamaki,ita da mijinta.Aisha tace na me?
Maman ummi tace, na jaraba,koyaushe da ya
shigo sai kiga an karo kofa.Aisha tace,ashe kin
lura,ni haushin da take bani cikin gida da hijabi
sai kace mazan mu suna da lokacin kallonta
ne.mu kuma me zamu kalla a jikinta wanda ba
mu dashi? Maman ummi tace shi na gani. Ita a
dole mai ilimi,shi fa mijin ma da take wannan
rawar kafa ba fa sonta yake ba.Aisha ta tare ta
da cewa,to waye a ung nan bai san cewa Yarta
yake so ba,taga kudi ta ki shi shine uban ya
lika mata mishi kanwar. Suka kwashe da
dariya.Aisha tace,kina nan wata rana zai gara
mata,sai an gama amrci da abu ya hada zai ce
abinda ba sonki nake ba.
Ikon Allah! Ko ina ruwansu maman ummi?
Wannan shine ana kayan zunubinka kai kana
kayan na wani, dama mata muyi harkar
gabanmu dn kowa tashi ta fisshe shi. Zaman
gulma ba abinyi bane. Allah ka shiryemu mu
daina Amin.
Gidnsu mahmud suka soma shiga sannan suka
wuce gidan maman tasu don bata san gidan
ba. Yaja tunga daga can nesa yace "minti
talatin" ta dube shi "kai bazaka shiga ba? Yace
kema dole ce tasa, don dai uwarki ce km baxan
rabaku ba, ki wuce kina cin tym dinki ne. Bata
ce komai ba tai gaba. Yau ne ranar farko data
soma zuwa gidan, ta tura gate din gidan ta
shiga, flat me kyau, ta kwankwasa kofar can
aka bude ta daga nikabinta, haule ta tabe baki
ta koma ciki. Ikilima tabi ta falon yaji kayan
alatu gwanin sha'awa ga sanyin a.c. Mamansu
fa tayi kiba jiki shar dole ta guji babansu. Ta
zauna kan kujera itama ikilima ta xauna tare da
cewa mama ina kwana? Tace lfy. Ta cgb da
cewa ai na zaci kin cnxa sbwr uwa ne ke da
nafi'u, ku ne baku taba xuwa gidannan ba sbd
bakinciki. To ynxu meya kawo ki? Tace naxo
gaisheki ne dama haule tace dama kin rike
gaisuwarki, dk abinda kuke ciki lbri na xuwa
min daya byn daya. Ance ubnki yai ma
mahmud huce haushi da ke. Km kinje gasa kin
samu kudi kin sai ma ubnki gida. To ni da baki
bani sile ba duban ni ki gani mena rasa na jin
dadi? Nasan duk kyau da girman gida dakika
saima uban naki bnyi zaton yakai wannan ba.
Ikilima tace ni dai mama don Allah kiyi hkri,
auren mahmud nayi ne dn na daidaita ku da
mahaifina, ba wai dn baba ya huce haushi ba,
gda kuwa danku na siya. Tayi shiru jin maman
bata ce komai ba, ta cgb da cewa don Allah
kiyi hkri ki koma gurin baban mu.ls BOOK
MABUDIN WAHALA 1***3
Da safe bayan ya gaida matan babansa yayi
sallama kofar dakin mahaifin nasa,Alhaji
Ibrahim kwantagora ya amsa,mahmud ya shga
ya xauna ckin grmamawa yake gaida baban
nasa shima cikin farin ciki ya amsa. Mahmud
yace Alhaji mahaifin nafsa ne yace in sanar da
kai ake sai dai ni kamar yanda na gaya maka a
dan tsahirta min saboda yanayin harkokin
kasuwar ta tsaya 2kunna. Alhji Ibrahim yace
banda abinka mahmuda ni bance kayi kome ba
a hidimar auranka nine xanyi maka kome,yace
ni nafi soxuwa gaba ne kadan. Alhaji Ibrahm
yace to shkenan ban san nufinka da haka ba
amma xan sanar da Alhj mustapha(kanin shi
kenan) in sunje sai a ce a jiramu,yace to
nagode. Koda su Alhaj mustpha sukaje gdan
malam usman sun bada kudn gaisuwa kuma
ya yanka musu sadaki 5K sunce a sauraresu in
sun kawo sadaki asa rana. Sun roki alfarmar
suna so yarinyar ta karasa kara2 malam
usman yace amma shi yaron yasan da wannan
magana?suka ce shine ma yace su nema masa
alfarma,malam usman yace ba komei shekara
biyu ai kamar yau ne gurin ubangiji sukace
hakane kam. Sai dai shi malam usman da yake
yasan halin yarsa ko shakka bayayi yasan ita
ce ta matsa mishi. Lokacin da ya shga gda ya
kira haule sai da ta xauna sannan yace iyayen
wannan yaro mahmud suka xo ta daure fuska
shi kam ba tare da ya kalle ta ba ya cigaba da
cewa ga kudin gaisuwar su nan kuma xasu
kawo sadaki sai dai sun roki a bari ta karasa
kara2 duk da nasan ita tace dashi hakan.
Haule tace to malam nawa kace sadakin?yace
dubu 10 da sauri ta dube shi tamkar ya watsa
maya wuta dubu 10 malam sai kace wata
kaxa? Yace mu albarka da alkhairin aure muke
nema ba tsawwala sadaki ba,sannan ki min
shiru haka naga dama. Ta mike ta fita ba tare
da tace kala ba.
Lokacin da yar tata ta dao sai ta shaida mata
cewa ga hukuncin da babanta ya yanke. Nfsa
tace sunyi ta banxa don ba dai dani ba to ko
kudin gaisuwar safina dubu 50 ne bare ni in ba
a kawo min 100 ba ai sai dai nima a bani 50
din,amma dubu 5 sai kace dan tsako. Haule
tace ashe kin fara hankali yanxu kyale shi
2nda ance sai kin gama makaranta ki karta
mishi rashin M har yayi xuciya ya daina xuwa
sannan kiyi ta dora mishi nauyin abinda bashi
dashi duk abinda kika sanyafi karfin shi shi
xakice ya sai miki. Nfsa tace ki bar shi sai mun
karya shagon kema ki dinga aikawa kina amso
sabulu da omo haule tayi dariya tace xan ko
dinga aikawa. Hakan ce ta kasance,tashin
farko ta sake bijiro masa da ba2n waya jiki na
bari ya siyo mata har da

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment