Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa nace bazan
aureshi ba don ubanki ke ki aureshi mana kin
san ni waye ai talaka ba abokin tafyata bane.
Muryar baban su ta jiyo yana cewa sannu yar
karuna ya iso ya haska su da tocila don ganin
wa take caba ma magana irin haka?ya wa take
caba ma magana irin haka?ya sha
mamakin ganin mahmud,dama kaine take
cewa baza ta aura ba? Mahmud kanshi kasa
yace nine baba. Malam usman ya jinjina kai
sannan yace ina fata ka raba katin gayyatar
daurin aure?mahmud yace kwarai muna kan
rabawa,yace to kada ka fasa kaji ko?tashi kaje
Allah ya maka albarka a kuma cigaba da
shirye2. Cikin kwarin gwiwa mahmud ya tashi
yayi sallama da yunus da ke can gefe yana
kallon duk diramar da akeyi ganin haka nfsa ta
nufi gda tana kuka tare da cewa nifa baban mu
bana sonshi fa yace nima gidan xan shigo in
na karaso kya shaida min,ya dubi iklima kema
sallami bakon naki kizo ki shiga gida kuma
haka nan,tace to,da sauri taje tace masa
malam sai da safe shima ya mike don yaji
abinda babanta yace tare da cewa mu kwana
lafiya. Malam ya shga gdan daidai nan nfsa tana
cewa maman mu ni dai wlh ba xan auri
mahmud ba kinji babanmu wai su cigaba da
shiri wlh ni kam xan shiga uwa duniya...jin
haka yasa malam usman waige waigen madoki
idanunshi suka sauka kan faskare ya isa gurin
ya dauka ya nufi dakin,saukar duka taji a
gadon bayanta ihu ta saki tare da hayewa
gado,ya bita yana cigaba da kirba mata,haule
itama cikin ihu ta rike shi tana fadin malam!
malam! yayi wurgi da ita ta tashi tana cewa
jama'a ku kawo dauki malam kada ka kashe ta
fa,iklima itama sai kuka takeyi tana cewa baba
kayi hakuri,sai da yaga ta daina ihu don wuya
lokaci guda kuma ta daina motsi ya yarda
itacen.kinyi kadan kice xaki maida ni karamin
mu2m shekera da shekaru yaron yana yin
wahala a kanki iyayansu sun zo na basu ke da
yardarki da amincewarki yanzun sai da aski
yaxo gaban goshi sannan xaki ce baki son shi?
yana huci ya nuna haule wadda ke rabe gefe
tana kuka yace ki maida hankalimki dani don
nasan ke ce mai hure mata kunne,ya fita.
Ta nufi gurin nfsa wadda numfashinta ke fita
sama sama ta dago ta jini na xuba daga
kumatunta iklima ta taimaka mata suka nufi
kyemis inda ta anshi magunguna da allura tare
kuma da gyaramata gurin ciwo suka kuma
tarairayota suka dawo da ita gida. Har gari ya
waye kuka take kuma bakinta bai mu2
ba,rantsuwa take tana karawa kan cewa ba
xata auri wanda bata so ba,iklima kuwa cewa
take ya nfsa don Allah ki bar wannan xancan
kin san baba ba xaya canxa ba gashi kin ja ya
dake ki irin haka. Nfsa tace kada ki dame
ni,adake ki irin haka. Nfsa tace kada ki dame ni,ai
ke ma munafuka ce. Cikin kwana 2 ta ware sai
plasta da ke kuma2nta.s BOOK
MABUDIN WAHALA 1***7
Sun shiga kasuwa da haule da hajiya kande
sunyo siyayyar kayan sawa da naci da gwala
gwalai har da katifa don kwanciyar
nfsa,fanka,TV,tare da kasinan kallo. Iklima
tana hada icce danta dora girkin sai ga su sun
shigo niki niki da kaya mota guda suka dauko
shata,makota sun xata kayan aure ne haka
iklima ma da ta gansu da risho da tukwane ga
xatonta kayan aure ne sun hakura sai taga
haule ta bude fos dinta ta ciro gudar dubu1 ta
jefa mata tare da cewa iklima kada ki hura siyo
lagwanin risho da kalanzir Allah ya hutashe
mu,ta saka hijabi da nikab da safa ta fita su ko
nan suka shiga gyaran dakuna su haule har da
labulaye da zannuwan gado,iklima dai tana
kallon ikon God. Suna cikin haka sai ga
sallamar mutan gidansu mahmud dauke da
akwatinsu katuwa guda1 da kit,haule ta shige
daki tana cewa hajiya kande kice su tafi ba fa
xa ayi ba,haj kande tace bar su amsar kaya ai
ba aure bane. Nfsa dama tana bayi da taji yan
kawo kaya ne sai taki fitowa illa xuciyarta da ta
cika da haushi gami da tsanar mahmud. Haj
kande sun duba kayan sun bada tukwuicin 2K
suna tafiya nfsa ta fito ta kalli akwati cikin isgili
tace wannan daki barin akwatin ai ba aji na
bane. Haule tace yanda suka kawo kayansu
haka xasu xo su dauka duk fadan baban su
wannan karon sai dai in murajiha. Haj kande
tace ke kike nuna kina tsoronshi ki xakalkale
masa haka kawai ga gidan hu2! Haule tace ke
dai gane mini hanya amma shi ana ga annabi
yana runtse ido. Haj kande tace rabu dashi in
kin bi ta tashi kya yi biyu babu. Iklima dai tana
jinsu tana jajjage.
Koda baban su ya dawo daga sallar ishai da
dare ya kira haule tana dakin yaran taxo ta
xauna tana ta wani cika da batsewa yace gobe
kafintan da naba aikin gadon nafsa yace aje a
kwashe 2nda ba lokacin damina bane sai a
jingine su a can. Haule tace malam shin wai
baxa ka hakura da xancan auran nan ba?
yarinya tace bata so amma kaki yarda yanxun
in ta tafi uwa duniya wa mukayi ma?shi ba sai
ya diba wata ya aura ba yan gidansu ma daxun
har suna wani kawo akwati. Ya dube ta kin san
Allah in dai nine uban da ya haifeta ba2n aure
babu fashi kuma ko ta shiga duniyar sai na
daura in yaso tayi ta yawon da auran sa duk
ranar da ta dawo sai ta tare haka nan in dai
shiga duniya ne taje ba kanta farau ba bare ya
kare kanta,taje ta bincika a matan da suka
shiga dunya me suka tsinta ciki? Yaya rayuwar
su ta kare? Haule tace to ni dai nace maganin
kada ayi kada a fara ya katse ta rufe min baki
mara kirki duk xan iya da ku, haule tace ni dai
da ta shiga duniya gara an fasa. Yace kin
sanni ai in kin cika matsa min da ba2n fasawa
zan saba miki kema. Ya dauki buta ya fita.
Shi kuwa ango duk da irin damuwar da yake
cki ya kasa sanar da danginsa halin da ake ciki
don haka su kam shiri suke ba kama hannun
yaro. Gidan da xasu zauna kuwa yasha gyara
da fenti. Abokananshi kuwa suma suna ta shiri
tare da yin mitin din yanda xasu hada kudin
yanmata da na walimar da xasuyi bayan
daurin aure. Amma shi ango maimakon murna
sai damuwa tare da 2nani domin 2n daga
wannan ranar da yaxo taki amsar kati bai
kuma samun ganin ta ba.
Gurin nafiu ya samu labarin dukan da babansu
yayi mata, hankalinshi ya tashi yaxo gidan ya
aika fiye da shurin masaki amma sakon da
take aiko masa dashi duk ba masu dadin ji
bane duk ya rame ya fita daga hayyacin shi
Ya sani abin kunya ne yanxun ya 2nkari wani
da wannan ba2n domin babu wanda bai gaya
masa gaskiya ba game da yarinyar sai ya
toshe kunnuwansa tare da kauda kansa yaki
sauraron kowa sai gashi yanxun nfsa xata
kware mishi baya. To in auran nan bai kasance
ba kila sai dai ya bar garin domin ko
mahaifinshi babu lallashin da bai masa ba ya
nemi wata amma ya kafe.
Nfsa ta daga wayarta ta tashi xaune da sauri
ganin lambar Alhaji jamilu jiki na bari tace
Alhajin Allah ya garin ne?yace gamu a kofar
gdanku tace to gani nan xuwa da sauri ta mike
tana kwala ma mahaifiyar kira,ta shigo lokacin
nfsa na murza hoda da 2rare tace yaya akayi
ne yarinya mai tsada? Ckin zumudi nfsa tace
Alhaji jamilu a kofar gida,haule tace maxa
maxa kada ki tsaya sanya. Cikin wata
dirkekiyar mota suka xo ta nufi gurin cikin
takun kasaita ta isa bakin motar cikin
murmushu tace sai ga ka?yace wallahi ki shigo
mana. Nfsa ta shiga ta lafe kan lallausar
kujerar motar,sanyin AC ya ratsa jikinta,
kamshin 2raransu suka doki juna. Alhaji jamilu
ya kai dubanshi ga gidan yace gidanku kenan?
ta dan taba baki tare da kallon gidan tace ka
sha mamaki ko?gidan ma ba namu bane na
haya ne,ni kaina ina takaicin kamar ni nan
muke zaune. Yace gaskiya sam ban xace ki a
irin nan ba,ya ciro magazine din bikin kalle ki a
nan fa,babu wanda ba xaya zaci cewa ke yar
wani kusa ce a gwamnati ba. Ta rausayar da
kai gefe ka bari kawai ina takaici sosai nasan
xaya yi wuya ka aure ni,yace sam wannan ba
xai shafi auran mu ba don kuwa ina sonki sai
dai dole ne in canza muku gida kafin lokacin
saboda yan daurin aure.
Nfsa cikin murna tace kai aiko mun gode da ta
2no da waye baban su sai kuma ta dan daure
fuska tace ina shakkar baban mu da kyar in
xaya amshi kyautar yace saboda me?tace
yana da tsatsauran ra'ayi sannan kuma yana
son aurar dani ga wani da bana so. Alhaji
jamilu yace kada wannan ya dame ki kudi suna
saka mai tsatsauran ra'ayi nfsa tace to Allah
yasa ya yarda. Yau fa sauran kwana 9 ya
daura min auran kana ganin har xaka aure ni
xuwa wannan kwanaki?bana son in rasaka.
Tayi kwal da ido tamkar xatayi kuka yayi
murmushi bari in ga tsohon naki komai xaya
daidaita yana ciki ne?tace a'a ya tafi sarkin
fawa xaya dauko doya amma gobe kaxo baya
xuwa ko'ina saboda juma'a yana gida yace to
xan samu masauki xan dawo. Ya xamu dan fita
ne kiyo shopping?tace to bari in shiryo da
murna ta shiga gida ta shaida ma haule yanda
sukayi a gaggauce ta shiryo haule tace ki xabo
min leshi don Allah jiya na manta ban saya ba
nfsa tace to,iklima ma ko takalmi ne xan sayo
mata. Da sauri haule tace kyale ta kada ki sai
mata ita nan da samu kudi ba ubanta ta baiwa
ba. Nfsa tace ta bamu zannuwa ki dai bari in
sai mata. Iklima dai bata da ra'ayin saka ko
dankunnan da xa a samo daga mu2min nan
wanda xuciyarta bata yarda dashi ba duk da
bata taba ganinsa ba. Sun zaga duk wani kanti
da ya ansa sunansa da ke cikin garin minna.
Siyayya ba a magana sannan ya dawo da ita
gida a xatonta in sun fita xay nemi suje
masaukinsa sai taga sam shi ba irin haka
bane.
Masu tsaron shi yasaka su kayi ta shiga mata
da kayan cikin gida inda shi kuma suka cigaba
da hirar in an daura auransu ya sai mata gida a
nan ko tafi son Abuja?da sauri tace haba
darlind dina kai ma kasan ba wanda xai bar Abj
kaf cikin naija sai dai in waje xaka fita yayi
dariya to shikenan. Sai ga Mahmud kamar an
jeho shi da yake gilasan motan masu duhu ne
bai san tana ciki ba ya jingina da bangon gidan
yana jiran dan aike, yazo ne don ya tambayeta
a ina abokanshi xasu gana da kawayan nata?
in ta ga dama ta fito. Ta dubi Alhaji to kaga fa
wanda babana yace xai bani don Allah anyi
min adalci?kalle shi fa ka dube ni. Alhaji jamilu
ya xuba ma mahmud idanu to ai bashi da
makusa,tace yana da makusa kuwa 2nda
bashi da aikin yi kyan siffar xanci a gidanshi?
Alhaji yace kema kinxo da uxuri,yace to kije
gurin shi mu xamu tafi tace Allah ba xani ba
kan shi fa har dukana babana yayi, Alhaji jamilu
yace to kira min shi,tace da xakaji tanawa da
ka bar shi. Ya daga waya ya kira bodyguard din
shi guda daya yace kaje ka kira min wancan
yaron. Mahmud yana xaune yana ta hamma
mu2min yace yane? Mahmud ya dube shu
lafiya lau,kana neman taimako ne? Ya daga
kafadunshi alamun wuce nan,oga na ke
kiranka ina xaton xaya taimaka maka
ne,mahmud ya kai duba ga motan da 2ni yake
kallonta ga xatonshi babu kowa cikinta yace
ina ogan naka?ya nuna motar. Mahmud ya
mike tare da kakkabe wandonshi ya nufi
motar,murfin motar ya wangale ga mamakinsa
sai idanunsa suka sauka kan nafsa kishingide
kusa da kyakyawan mu2min wanda daga gani
ya jike da hu2. Wani abu ne ya taso ya tokare
mishi a kirji numfashinsa na fita da sauri
kamannin shi suka sauya idanunshi suka ciko
da kwalla tamkar xasu zubo. Ya nuna ta da
yatsa nafsa ni xakiyiwa haka?dama kudin
wannan mu2min ne yake rudarki?amanata
zakici ko? Tace kai wa ma kake?ni dama nace
ina sonka ne?dole xa ayi min. Kanshi ya soma
juyawa don furucinta cikin karfin hali yace
gaskiya ne nfsa kudi babu abinda basa saka
mu2m yau kece da bakinki kike cewa dama
can ba sona kikeyi ba dole akay miki ko? Dole
kice haka 2nda kin tsiyata ni kije na barki da
Allah kuma ki rike a ranki wata rana xaki neme
ni in nadama ta riske ki...ta katse shi naji don
Allah ni dai kuxo ku kwashe komatsanku. Alhaji
jamilu ya dubi mahmud kaima dan saurayi kayi
ganganci ya dafa kafadar nafsa wannan xubin
manya ne da ita ka hakura in ta karya maka
jari ne xan dora ka,daga # 1mil ha10 mil,kaje
kayi naxari kafin jibi don in ma ka cije to baxa
ka same ta ba kuma babu kudin. Mahmud ya
katse shi da cewa baxan amshi ko sisinka ba
koda ba xan same ta ba saboda ban san asalin
kudin ka ba, kai ba maka da wani abu da xaka
bani wanda ubangiji ba xaya bani ba ya juya
xaya tafi. Alhaji jamilu yace kada ka yanke
hukunci da sauri,na baka xuwa gobe zan
amshi numbarka gurin gimbiyata zan kira ka
inji kayi hakuri na sani rabuwa da masoyi da
zafi. Ran mahmud yafi da baci ya dubi nafisa
ko a jikinta tana ta taunar cingam tare da yin
kwai tana tauna shi kas-kas,ya juya ya tafi
xufa na tsiyaya daga jikin shi duhu yake gani
duk da kasancewa rana ce. Duk da horn din da
mai mashin din ke masa bai ji ba sai da ya
bangaje shi har ya fada cikin wani
kwalbati,mu2m biyu ne suka taimaka masa
gurin ciro shi duk da bai ji ciwo ba yayi dumu
dumu cikin kwata,ya dubi jikin shi bakin ciki
tamkar ya hadiye kanshi.
Wani mai 2ra ruwa yaxo xaya wuce aka tsaida
shi inda aka soma diddila mashi ruwan a jikin
shi,shi kam kasa motsi yayi. Ya isa gida inda
yana shiga ckin gdan hankalinshi ya sake tashi
ganin dangin mahaifinshi da ke sokoto sun xi
biki gefe juma ga kannenshi suna ta gwada
dinkunan ankon su. Hajiya rabi tace a'a ango
daga ina haka jiki sharkaf?yayi karfin halin
cewa mashin ne ya 2ra ni cikin kwata ya nufi
bayi ya sake ma kanshi shawa ba tare da ya
cire kayan ba,ya jiyo muryar kanin sa musa ya
leko yace musa dauko min jallabiya ta a daki
musa yace to,cikin karfin hali yayi wanka ya
fito. Ya xube kan katifa ya rasa wa xaya gaya
wa wannan kayan bakin cikin da takaicin?
Sulaiman ya shigo da sallam ya zauna kan
kujera tare da mishi kirari ango kasha kamshi
daga gani 2nanin amarya kakeyi to kayi hakuri
ta kusa zuwa. Mahmud tamkar ya tashi ya
naushi sulaiman don bakin ciki amma babu
dama shi kuma ba abin ya gaya mishi abinda
nfsa ta mishi ba domin duk sun gaya mishi
gaskiya yaki sauraron su. Sulaiman yace na
ganka wani iri ya dai?dan tsaki yaja sannan
yace bana jin dadi ne,sulaiman yace na lura to
kasha magani?ya daga kai alamun
eh,sulaiman ya sake cewa Allah ya saukaka
yanxun ina xamu ga kawayanta? Mahmud
yace don Allah ka bar su in sun matsu su neme
ku sulaiman yace shikenan bari in barka ko
xaka samu bacci ya fita. Mahmud yana dai
kwance ne amma kwakwalwar shi tana dawo
mishi da duk abubuwan da suka faru yau itace
ranar nadama a gurinshi domin ansha bashi
shawara ya rabu da ita amma yaki alhalin
hausawa sunce in so cuta ne hakuri magani ne.
Abokan shi sukayi ta xuwa don suga yanmatan
amarya amma sai dai su samu ango kwance
ba lafiya hakan ya kara daga hankalin shi kafin
dare doke akayi asibiti dashi.
Musa kanin shi ne ya nufi gdan su nfsa ya
shaida mata ba tare da sanin mahmud ba
2nda basu san me yake faruwa ba. Bata nan
sai mahaifin ya samu dawowarshi kenan xaya
shiga gida suka gaisa ya shaida masa,malam
usman yace assha Allah ya bashi lafiya in na
shiga na shaida musu kayi masa sannu sai
nazo,wane asibiti ne? Musa yace babban
asibiti. Ita kuwa nfsa lokacin da mahmud ya
tafi wani gefe na xuciyarta yana kokawa
yayinda mafi rinjayen yake tayi mata murna, da
zasu rau da Alhaji bayan siyayya jakar ranar
nan ce ya bude mata yace ta diba. Cikin
xumudi ta shiga jidar sabbin yan dubu dubun
sai da ta dibi dauri 12 ta kalle shi tace sun isa
nagode. Yayi murmushi tare da jinjina kai cikin
zuciyarsa yayi ma2kar mamakin son kudi irin
na nfsa wannan ta dama shi ta shanye kan son
kudi,ta runguma ta nufi gidan su.
klima ta xaro eyes lokacin da taga nafsa ta
shigo rungume da kudi tace "A'uzubillahi"
nafsa tace shaidan kika gani?kaji iskanci fa.
Haule,haule fito kixo ki gani da gudu ta fito
itama 2rus ta tsaya tare da dafa kirji tace ni
haula2 me xan gani haka?tace Alhaji jamilu ne
yace in diba niko na jido. Haule jiki na bari ta
amsa sukayi daki tace kuma yace xai sai ma
Baba gida sai dai ina tsoro da kyar ne baba xai
amince. Haule tace ya siya in yaki amincewa
mu sai mu koma,kina tsammanin xan yarda in
sha wahala ga saauki yaxo min? Nfsa tace ki
adana su dasu xamu siyo kayan daki haule
kam duk ta rude nafsa ta shiga koro mata
yanda sukay da mahmud suna ta sheka dariya.
Ranar ma yini sukayi lissafin abinda xasu saya
na daki ita dai haule fadi take waya zaki fara
sai min wannan karon. Lokacin da malam
usman ya shigo gdan da nafsa ya soma cin
karo ta fito wanka yace yauwa kinji yaron nan
mahmud ba lafiya yana babban asibiti ko? Ta
danyi dim sannan tace ban sani ba,yace to ai
ya 2ro kanin shi ne ya shaida miki muka ci karo
ya juya. Cikin rashin damuwa tace Allah ya
sauwake yace amin sai kuje ke da yar uwarki
ku gaida shi. Ina iklimar? Nafsa tace to iklima
an aiketa,ta dai amsa ne amma ba don xata je
ba.
Lokacin da malam usman yayi xaman cin
abinci kan tabarma sai yayi mamakin ganin
sababbin kuloli yace daga ina?2nda yasan
daidai da cokali in ba saya yayi ba haule baza
ta siya ba koda kudin xaya kashe ta ne. Ya
buda kular maimakon 2won garin masara
yasan suke dashi sai yaga farar shinkafa da
taliya na miyar kuma sai yaga ferfesun kaji
ne,2ni kamshi ya cika hancinsa yawun sa ya
tsinke amma duk da haka ya ruufe murafun ya
kalli jug din ruwan shima sabo ne. Ya koma ya
kishingida tare da kwala ma iklima kira da sauri
taxo gani baba, yace kira min mamanku. Haule
ta iso sanye da sabuwar atamfa wadda ba shi
ya saye ta ba. Yace xauna ina son xamu yi
magana,ta xauna cikin fargaba amma a xuciya
tana raya yau kam sai dai suyi ta in dai ba2n
mahmud ne. Yace haule ina aka samu
wadannan kwanukan tace saya nayi,yace me
kika saida kika samu kudi?tace daga Allah
suka xo ya bude kulolin wannan girkin fa?tace
duk ni nayi,ya nuna zanin jikin ta wannan xanin
fa?shima ke kika saya?ta ce eh ya kafe ta da
idanu tare da cewa gaya min inda kika samu
kudi ya rike habar shi yana kallonta bayan ya
2re kulolin gefe,tace mai son nafi ne yaxo ya
bani, ckin sauri yace ya shigo min gda bana
nan?ckn sauri itama tace a'a ita ya aiko.
Malam usman yay shiru xucyar sa na tafasa
har sai yaushe matar nan xatay hankali?an
kusa auran yarinya kuma tana amsar kudin
wasu?ita kuwa haule jin yayi shiru ta xata yayi
ladab ne don haka ta cigaba yana ma son
ganinka ya ma ce xaya saya maka gida,ya
xuba mata eyes cikin takaicin kalamanta amma
da yake dare ne bata fahimci haka ba,ga nata
xaton ya yarda ne 2nda tasan a rayuwa bashi
da burin da ya wuce gidan kanshi sabida
wulakancin masu gidan haya, tace yana da
kudin sosai ko yau daurin kudi 12 ya bama
nfsa kuma duk yan dubu dubu. In ka bashi
hadin kai wallahi har jari mai tsoka xaya baka
kaga kana sauke motocin doya shi gurin shi
kyautar kudi ba wani abu bane. Dubu dari fa
sau 12 ya ba....
Ke da Allah yi min shuru ballagaxar uwa mara
hankali,haba yanxune na gane dalilin da yasa
yarinyar ta soma 2burewa maganar auran
dama me kudi kuka gani?ya tashi tsaye tare da
yin kwallo da kular miyar yace ina nafsa?ta fito
da sauri ya nuna ta ya nuna haule yace baku
isa ba kunyi kadan ku maida ni tsohon banza
ku saka ni in saba alkawari har xaki xauna kina
shaida min yace xaya saya min gda Allah yasa
gari xai bani ko duniya da kayan cikinta ba xan
canxa ra'ayi ba,kudi kuwa in yaso ya baku
world bank shi ne dai bankin duniya ko? Haule
tay karfin halin cewa malam banda abinka wa
yaki hu2?tsaki yaja sannan ya fita yana fadan
cewa in bakay dace da mace ta gari ba hkika
kana ckin wani hali. Manzon Allah(SAW) yayi
gaskiya da yace mu xaba ma yayayenmu uwa
ta gari. Su kuwa yana fta nfsa tace ni ko a
jikina ina kan bakana haule tace barshi kinji ke
dai abinda xance miki duk wuya duk runtsi ki
jajirce. Nfsa tace har ma sai an fada min?
yaushe xan yarda inyiwa kaina black stomach?
haule tace a to gane min hanya.
Da safe Malam usman ya shirya ya nufi asibiti
don dubo mahmud yaci sa'a zuwan mahaifin
mahmud kenan gurin suka gaisa ya duba mai
jikin da yake ta bacci yace da musa kanin shi
idan ya tashi ka shaida masa ina gaida
shi,musa yace to xan gaya masa. Malam
Usman suka jero da Alhaji Ibrahim suna
tattauna ba2n daurin auran nan da kwana7.
Sukayi hannu a bakin titi tare da yin
sallama,malam usman ya tare mashin ya hau.
Shi kuwa mahmud da ya farka musa yace
masa baban su nfsa yaxo yace a gaishe ka da
jiki ya samu baba a nan,mahmud yace nafsa
fa?musa ya taba mouth nikam ban ganta
ba,mahmud yayi shiru can yace xata xo amma
koda wani ya tambayeka kace taxo musa yace
to. Mahmud ya lumshe eyes yana naxarin
yanda mata suke juyawa tamkar wahainiya. Ya
sani nfsa tana ma2kar sonsa amma ta amince
ta sadaukar da son saboda kudi 2ni ta manta
da son da yake mata da dukkan dawainiyoyin
da yayi mata ita da mahaifanta a can baya.
Nfsa ta kira wayarshi Alhaji jamilu ya daga tace
yawwa kaxo in kana kusa baban mu yana nan
yanxun, Alhaji jamilu yace to,kusam 30mins
yaro ya shigo da sallama haule ce a tsakar
gida ta amsa yace wai ana sallama da mai
house din tace to,ta daga murya ta kira nafiu
ya amsa daga cikin daki sannan ya fito tace
kace da baban ku ana sallama. Malam Usman
Yana fita kofar gida ya shiga waige waigen ina
mai sallamar dashi?mota kawai ya gani ba
kuma ya xaton cewa da wani mai mota da
xaya xo gurinsa bai gama 2nani ba motar ta
bude masu lura da lafiyar shi ne suka fito daga
gaba sannan suka bude mishi bayan motar ya
fito. Sanye yake da shadda irinta karshen kudi
yar ciki da malun malun mai ruwan blue
takalmi,hula n sandarsa duk bakake ne. Ya
nufo Malam Usman yana dogara sandarsa ba
don yana dingishi ba sai don kawai gayu da
kuma giyar kudi,kasancewar shi fari shigar ta
amshe shi.
Ya mika wa malam usman hannu sukayi
musabaha sannan yace nine mai son ganinka
malam usman yace to Allah dai yasa lafiya?
Alhaji jamilu yace lafya lau in sha Allah ko
xakaxo mu shiga mota?malam usman ya
girgiza kai ba xan shiga motarka ba bari in
saka yaro ya kawo tabarma,ya leka ckin gdan
ya kwala wa nfiu kira yace ya kawo tabarma.
Ya shimfida sannan yace bismillah bayan shi
ya xauna ga mamakin malam usman sai yaga
masu tsaron nashi sun daga but din motar sun
ciro wata kujera sun xo sun bude ta ya zauna.
Ya kalli malam usman yace baba barka da
warhaka anyini lafiya?malam usman yace
lafiya lau Alhaji jamilu yayi gyaran murya yace
baka sanni ba ko?malam usman yace eh Alhaji
jamilu sunana ina aiki ne a Abuja kuma naga
nafsa ne ina so shine nake son in 2ro
waliyaiyna. Yayi shiru yana sauraron malam
usman wanda ranshi ya baci to ko ba auranta
xa ayi ba yaushe xaya yarda ya ba wannan
yarshi?sam bashi da tarbiyya. Yace Allah sarki
gashi kuma anyi mata miji yau sauran kwana 7
bikinta. Alhaji jamilu yace nasan haka ina so a
bar xancan yaron 2nda tace bata so in ma
kana 2nanin abinda yaron ya kashe ne xan
biya fiye da abinda ya kashe kai kuma xan
saya maka gda a cikin unguwar 2rawan
garinnan in baka jari naira 5mil tare da kujerun
makka 10 danginka kuma in.....hannu malam
usman ya daga mishi sannan yace noman kudi
kuke a gidanku?ya mike tare da nade tabarmar
yana cewa in sayanta xaka yi to albarka bata
saidaawa bace ya nuna shi da yatsa bana
bukatr sake ganinka a kofar gidana baxan ci
amana ba. Alhaj jamilu yace malam da ka
amince da lalama domin nan duniya ban taba
neman abu na rasa ba,malam usman yace
wannan karon kasa a ranka cewa ka fara in dai
nine ubata ya juya xaya shiga gida. Alhaji
jamilu yace in ka canxa shawara ka sanar da
ita xata shaida min. Lokaci kadan xaka shiga
sahun masu rufin asirin unguwar ku. Malam
usman yace kai sakarai hala kai jahili ne?kai ka
isa ka azurta mu2m? Allah shi ne kadai me iya
azurta bawa ya buga kirjinshi yana cewa ni nan
da ka ganni Allah ya bani arxiki saboda ya bani
wadatar xuci. Alhaji jamilu yace kai matsiyaci ni
kake xagi?in kayi wasa xan sa a tsare ka har
abada kuma in auri yar taka in ga yanda
xakayi. Ya juya fuuu!!! Mamaki ya hana malam
usman motsi har suka tada kura suka bar
layin..,.
Ya shiga gida yana kishingide bakinciki da
takaici sun ki hana shi sukuni,iklima tayi
sallama ta shigo gidan duk da kayan
makarantar boko ne a jikinta kafarta sanye da
safa,fuskarta rufe da nikabi malam usman ya bi
kamilar yartasa da kallo duk kokacin da ya
kalle ta yana alfahari da ita,ita kuwa bata lura
dashi ba sai da ta gota sannan ta ganshi ckin
sauri ta dawo baya ta tsugunna tace baba
lafiya kuwa?yace bana jin dadi ne yau duk ban
fita ba cikin tausayawa ta xauna tare da cewa
yaya jikin me ya same ka ne? Yace zazzabi ne
tace Allah ya sawwake kasha magani ne?

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment