Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ta tashe ta.
Yace ta zo sasanshi. Kwance ta same shi wai
zazzabi. Ita ce tayi ta kula dashi har ya dan
murmure.daga baya kuma abokanshi suka ba
shi shawara ya fita waje a duba shi da kyau.
Tare suka shirya tafiyar sai dai kafin su tafi sai
da ta yo ma haule waya ta shaida mata mijinta
ba shi da lafiya,ita da su danlami suka je
sannan suka tafi.wani bala'I duk da rashin
lafiyar dake damunsa wai haka kartin ke shiga
wurinshi suna aikata kazamin aikinsu. Da tace
ya bari ya warke yace ai sharadi ne kullum sai
sun aikata haka ko da baka da lafiya sai kayi
kuma sai anyi maka. Wa'iyazubillah,wannan ai
rayuwar dabbobi ce kai ko kare bama kare ba
ko alade mafi muni da wulakantuwa dai kenan
namijin su baya bin namiji. Ya samu sauki ya yi
sarai suka dawo kowannansu ya ci gaba da
aikata laifinshi.zuwa yanzun nafisa ta juku da
kudi,kasuwanci ana ta yin shi ba kama hannun
yaro,bokaye suna cin nasu rabon. Hakika
zuciyar nafisa ta kamu da ciwon som dunoya
wanda ya mantar da ita ibadarta da addininta.
Ko ramadan ne yanzun gani take yi talauci ke
sa yin ibada,sharholiyarta ce kawai a
gabanta.tabi namijin da taga dama ga kudi.
Haule kuwa likkafa ta yi gaba,hajj da umra ba
sauki duk anje ga hakoran makka an zubo
sama biyu kasa daya. Da ta hango ka tun
daga nesa zata soma washe baki,duk ko
wanda yace mata haule bai hada da hajiya ba
sai ta mishi rashin mutunci. Malam usman ne
kawai ke taka ta son ranshi don da zata yi
mishi salo zai warware ta.yauma minna ta
dauko su nafisa,suna zaune falon haule suna
dambe da kaji da kalolin juice sai ga iklima tayi
sallama,daga skul take ta zo su gaisa da haule
dama ta tambaya. Nafisa ta hada rai,iklima ta
isa gurin ta tana cewa,tuba nake 'yar uwa,wlh
ina nan sai dai ki ganni kwatsam. Nafisa tayi
dan yake tare da cewa ki sha zamanki,ai
duniya yawa ne da ita.a bariki ma ana samun
yan uwa.suna can wlh sun ishe ni zumunci.
Haule ma fuska daure ta amsa gaisuwar
iklima,ta sakko khalil ta mika ma nafisa tare da
cewa,to ga dan naki. Nafisa tace,a'a bar shi
bari dai in ganshi a hannunki,wa ya biyo? Don
ni bana daukan yara babu pampers. Iklima tayi
sororo,nafisa ta dubi yaron tace,um kama da
ke ne wannan yaron. Haule tace,ubansa ne ba
kya ganin wannan dakwa-dakwan idanun
kaman na kare an danna shi a kwata? Nafisa
bata ji dadin haka ba, ita ce ya dace ta haifi
yaron nan da mahmud ba iklima ba. Ta kauda
kai tana jin zafi a ranta,wai shin dama haka so
yake da dafi? Har boka tace ma tana so ta
daina son mahmud amma duk da irin surkullan
da ya mata ta kasa daina sonshi. Iklima ta
maida danta baya ta goya duk da tilin naman
dake gabansu ba wanda yayi mata tayi,har ga
Allah kuma ranta ya biya.tace,zan tafi. Suka ce
sauka lafiya. Ta fito tana waiwayan naman
amma duk da haka suka share ta, tayi
murmushi tare da cewa,Allah ka kai bawa kan
arzikinshi. Da ta koma gida ranar ko abinda
zasu ci ma babu sai da dare yaje gidansu ya
amso mata tuwo.
Nafisa ta nufi gidansu safina, ta samu safinan
tana bcci da kyar ta tashe ta suka rungume
juna tace shegia nafisa kinzo dunia a sa'a,
dubi ynda kike kara zama don kin gama shan
kwana. Naga wasu fitinannun shaguna da kika
sake budewa. Tai daria sanna tai juyi a tsakar
falon tace, kin sanni tn ina karamata burina
kenan, inji ance nice wance inji ana lbrina gurin
kudi, in na wuce a bini da kallo. Safina tace kin
samu Allah ya amsa. Nafisa tace matsalata
daya ynzu a dunia ita ce son mahmud, wai
yaushe wannan balain ze rabu dani ne? Duk
namijin da ze hada shimfida dani sai dai in
dinga raya ina tare da mahmud, sannan zan
samu nutsuwa. Hawaye ya soma zuba dg
idonta in sonsa ya motsa min sai inga zan iya
rbw da daular da nake ciki don na zauna dashi.
Na kashe kudi a cire min son shi ya gagara.
Safina samo min mafita, nabi duk hanyoyin da
zanja shi jikina ko da mu dinga rayuwa ne, na
kashe kudi gurin bokaye abin ya faskara.
Safina ta kama hannunta zuwa dakin bccinta,
ta xaunar da ita bakin gado ta jawo wani kwali
dg kasan gadonta cike da kwalabe tace ga
magunguna abokan shawara, da kin juye 1
cikin ruwa mai sanyi zaki manta dashi, in ma
baki manta dashi ba zata gaya miki ynda
zakiyi. Nafisa tace wannan ina ce magungunan
tari ne? Safina tace, tabdi kawata shan wannan
shine zai sa ki kara hadewa. Zaki bani lbri.
Daga ranar nafisa ta zama yar maye, sai
shaye-shaye. Tir da wannan rayuwar.
Albashin ikilima na taimakonsu matuka, dk da
hk ba a wadace suke ba. Sai dai wadatar zuci,
batayi girman kai ba tana amsar wankin jama'a
tanayi ana biyanta, yace shi bayaso tace yai
hkri rufin asirinsune. Hakan ya hkra. Matan
gidansu ma suna bata ta musu dk da yan
habaice habaicen da suke mata na cewa ta like
a gindin namiji, dk abnda take nema bata
tsinanawa kanta wata tsiya, in dai namiji ne ze
koya mata hnkl. Share batnsu tayi ta cgb da
harkar gabanta. Kullum son juna suke karayi.
Mahmud yakan ce ya yarda wani hani ga Allah
baiwa ne, ya tbbta da nafisa ce suke cikin
wannan halin dk son da take mishi da tuni ta
tada balli, amma ikilima bata taba bata ranta
ba dn yace bb, sai dai tace Allah ya kawo.
Annabi yayi gskia daya ce, "na hore ku daku
auri mai addini". Sallamar ta kasa karewa, dk
matan gidan basu nan sai ikilima ita kadai. Ta
zura babban hijabi ta fita, maza 2 ne tsaye
kofar gidan, cikin kakkausar murya tace
Alaikumus salam, wa kuke nema? Suka ce
mahmud. Tace ya fita lafia? Suka ce lfy lau,
dayan ya ciro wata letter ya mika mata gashi
inyazo ki bashi. Ta amsa ta juya farar takardar
sannan tace to. Ta koma ciki ta ajje.
Bai dawo da wuri ba don sunyi aiki a wani gida
ba'a biyasu ba,suka yi ta jira har magriba
sannan yazo yace suyi hakuri sai gobe. Rai
bace ya shigo amma ta tare shi da sannu da
zuwa,ta gabatar masa da ruwa cikin fara'a
yasha tace na ganka wani iri gajiya ce? Ya
dube ta,mun sha aiki yau muna sa ran kudi
amma bamu sa mu ba, na biyo ta gidanmu in
zo miki da tuwo muna cikin gaisawa da su
hajiya uwa sai naji yara suna a kara musu tuwo
aka ce ya kare sai a dibar musu cikin na Alh.
Ta saki murmushi.don wannan kada ka
damu,na samu wanki yau gashi nan na dafa
mana taliya. damuwata daya ta murje ce kai
kuma baka son taliyar fulawa. Yace,in kin ji ana
cewa ana cin kaza ba'a cin kaza duk cikin hali
ne. Yanzun kuwa ba mu da hali. Tace,bari ka
gani,nayi ta tayi kyau tamkar ba ta murji ba.
Ta zuba mishi ya soma ci. Sai da ya koshi ya
sha ruwa sannan yace yau kasar nan jama'a
suna cikin wani hali iklima. Yau ne na yarda da
batunki da kike cewa aiki tare da ba'a samu
kudin nan ba(ban gane nan ba sosai)kuka ya
saka yace 'ya'yansa bakwai kuma babu abinda
zasu ci yanzun haka da ya fito ko na rana
babi. Karo-karon kudi aka mishi ya auni garin
rogo. Iklima tace,Allah sarki,gaskiya mutane
suna cikin wani hali an jefa kasar tamu cikin
masifa,an talauta mu. Yace,rashin dace ne
dashugabanni na kwarai tace haka ne,sai dai
mu ma mu gyara halayenmu don kamanninmu
kamannin shuwagabanninmu in mun canza
Allah zai dube mu.Suna ta zuba sam ta manta
da batun takardar nan da aka ce ta ba shi.
Alh kabiru yana ta kai kawo a cikin
falon,tamkar karya yake ganin result da Dr ya
bashi,shine yake dauke da HIV? Zawo ne fa
kurum,to likitoci biyu asibitoci biyu kuma
kwararru sun tabbatar mishi lallai gaske ne,ko
da yake zai koma gurin likitan farko don ya
bashi shawarwari zai dinga shan magani ba
kowa bane zai iya gane cewa yana da ciwo ba.
Ya kuma ci gaba da shagalinshi kowa ma ya
samu tunda shima sa mishi aka yi,hakan kuwa
ya yi.Samari sai ayi hattara masu aikata laifin
luwadi,irin su Alh kabiru masu dauke da ciwo
suna da yawa ga kuma zunibi saboda girman
zunubin da kazantarsa in ana aikata shi duniya
sai ta girgiza da za ku ji hukuncin mai laifin
kuma sama za'a hau bene a jeho mutum. Allah
ka kare alummar musulmi.
Shi kuwa Alh jamilu wani maruru ne dan karami
ya fito mishi daga matsugunna sai damun shi
yake yi,ko zama ya kasa. In ya taba yana jin
shi amma nafisa da yace ta duba mishi tace ba
ta ga komai ba. Don haka bai yi kasa a gwiwa
ba yayi asibiti.ashe tsutsosi ne suke dam a
gurin tsugunnon,likitan yace aiki za'a masa. Ko
gida bai yo waya ya shaida ma nafisa ba,yace
ayi mishi. Sai da aka gama sannan yayi ma
nafisa waya ta zo sai dai wata sabuwar
matsalar tunda aka yi aiki baya rike kashi duk
abinda yace sai dai ka ganshi satata da ya yi
dan nishi,haka nan suka nufi egypt inda aka
yanki cinyarshi aka yi masa ciko.sannan
likitocin suka gargade shi da ya daina bari ana
taba shi a gurin.Ma'ana a daina mishi
luwadi,sai dai yana samun sauki ya dora daga
inda ya tsaya. Tir Allah ka shiryemu amin. Ita
kuwa Nafisa ko a jikinta,yawo kasashe shine a
gabanta.
Anty hajara ta sake sata a wata hanyar
madigo, inda suke diban kazantar da suke
fitarwa suna kai ma bokan yana hada musu
sihiri don bunkasa kasuwancinsu. Tsafi gskiyar
me shi, suna ganin cgb sai inda dk bokayen
suka fado shine har yau ta kasa samun wnda
ya shawo mata kan mahmud, dk bokan da taje
tasa aiki sakamakon yana zama in aikin yaje
sai ya dawo. Musamman ta yanke shawarar
samun shi gaba da gaba kmr ynda cocein din
data sha ya gaya mata. Ta tsaya da mota
kofar gidansu ikilima ta shiga sai dai kash!
Dakin na kulle ta koma gidan su, sa wa tayi
aka bi mata diddigin inda zata ga mahmud, ta
hanyar safina. Anxo mata da lbrin majalisar su
da suke hira da dare. Gidansu ta koma gurin
haule ta kwnta. Kamar ynda aka shaida mata
cewa byn isha'i hakan tayi lkcn su 3 ne a gurin
shi da muktar da wani babayo, yawanci nan
suke daukar karatunsu gurin malam ya'u. Basu
cika hirar bnxa ba a majalhsar tasu. Ta aiko
wani yaro ya kira shi koda yaron ya nuna mishi
motar be kawo ta ba a zatonshi namiji ne cikin
motar, yace to wanene wancan km? Muktar
yace kaje ka gani mana dg ganin motar can
kasan samu ke kiranka. Ya nufi motar yana
zancen zuciya.
Kofar gaba ta bude, daidai da lkcin da wutar
motar ta dallaro, nafisa ce cikin wando da riga
na wando da riga na wani jan uban sun yadi.
Zai juya sai yaga wasu samari 2 a bayanshi ta
gefe dayan ya dora mishi bindiga a kugu, ynda
ba kowa zai gane ba. Ko da ranane bare dare.
Suka ce shiga kawai muje, yace bari in sallami
abokina suka ce a'a ba jimawa zakayi ba. Wani
shahararren hotel ta nufa dasu yana tsakiyar
mutanen nan. Suka fito suka jera su 3 tana
gaba suna binta har suka iso kofar wani daki
ta ciro key cikin jakarta ta bude suka shiga. Ta
dubi mazan sannan ta ciro kudi cikin jakarta ku
jira mu can wajen shakatawa, ko a falon karbar
baki. Ta maida kofar ta kulle ga mamakinsa sai
yaga taje ta windo ta jefa dan mukullin. Da
sauri ya isa bakin windo ya leka can kasa ne
cikin swimming pool ya zunduma, ya juyo ga
mamakinsa ta soma cire tufafinta.
Ya daure fuska addu'a na cikin zcyrsa. Da in
ina yayi magana me me ki.....ke so dani da
kika kawo ni nan? Tace shine xan gwada maka
ynxu. Pant ne kawai ya rage a jikinta tai juyi
dubeni kasan ina da kyau ko? Bai bata amsa
ba ta cgb nasan kana so na, ta dafa
kafadarshi. Mahmud wlhy-wlhy dk abinda nake
so nan dunia ina samunshi, kaine kawai na
gagara samu, na kashe kudi, na zubar da
hawaye don kai kadai to na gaji dole ne ka
amince min mu dinga hulda tnda bazaka rabu
da kanwata ba.
Ya zame hannuta daga kafadarshi. Allah ya
tsareni, ya nuna ta da yatsa ki bude min kofa in
tafi ke kanki kin san kin yaudari kanki, bn
amince dake ba lkcn kina budurwa sai ynxu?
Shedaniya in dai nine kin rasa ni har abada sai
dai hawayenki su kare. Ya sake zuba mata
harara tare da cewa baki da wani kyau dama
kyan naki a fuska ne? Wlhy matata tafi ki
komai na dirin jiki, ni bana sonki ma ynxun
kwata-kwata, na kara tsanarki. Ya kaita bango
dn hk ta zabga mishi mari, tace karyane kana
sona km nafi ikilima kyau. Shima ya yarfa mata
mari gefe 2. Ga mamakinsa sai yaga ta shafa
kumatun da tafin hannunta ta sumbaci
hannun. Ko duk jikina zaka zane czan damu ba
ni dai burina jikina ya taba naka. Ta kawo mishi
runguma ya kauce ya nufi kofa yana jijjigawa
tace kada ka karya musu kofa gabanka na
yarda mukulli. Ta ko taso gabanshi zan so
kawai ka yarda ta zuge jakarta ta zazzage
masa kudin ciki yan dubu dubu ne dauri dari.
Zan baka kudi km zan samo maka aiki, in ka
amince zan fidda ka dg kunci da wahalar
rayuwa, zaka shana in fita da kai kasashen
dunia dn ka kece raini, zan zamar da kai abin
kwatance cikin abokanka da family dinka.
Ke! Ya daka mata tsawa, kinyi kadan ki aikata
dk wannan, wahala da hutu, arziki da talauci dk
na Allah ne. Shi ne kadai zai maidani abin
kwatance, in yaso in be so ba km ya brni cikin
wahala. Amma hakan ba zai sa inyi ynda kike
so ba. Tace to zaka san ynda zaka kare kanka
dg gurin yan sanda in suka sameka anan
dakin, nace dasu fyade zaka mun. Zufa ta
soma keto mishi yace ba kece ta farko da tai
wannan sharrin ga namiji ba, sai dai yi min
sharrin ze fi min sauki fiye da aikata abinda
kike so. Inyaso ni km Allah ya saka min ranar
gobe kiyama. Ta sake yo kansa da nufin
runguma ya hankadeta tn karfinshi ta zube ta
shiga kuka ta soma rokonshi da girman Allah
wai ko sau 1 ne ita tana tasan shi wanene a
rayuwarta.
Yace wlhy sai dai ki mutu. Ta mike ta nufi
jakarta ta zage zif din bayan ta ciro wata
kwalba, be taba yarda mata nashan fakalin ba
sai ranar, ta nufi water filter ta matso ruwan
sanyi ta bude kwalbr ta juye ta kafa kai ta
shanye. Tace ni da kai zamu kwana anan. Nan
ta shiga surutai wadanda bazasu fadu ba daga
baya ta zube kan gado jim kadan sai bcci. Tun
lkcn da bcci yai gaba da ita yake neman yanda
zeyi ya fita. Daga bisani ya dannan waya yai
magana da masu kawo abinci cewa su kawo
chips, lkcin da sukazo budewa ya leka ta
window yake shaida mishi cewa sistr dinshi
tayi bcci km key din na hannunta, tasha
maganine don Allah ko za a samu wani? Yace
sai dai gurin manyansu. Yace don Allah yaje
gurin masu kula da dakunan ya shaida musu.
Sai da suka zo har bakin gurin suka mishi
tmbyoyi sannan suka bude suka shigo dakin
sukayi dube-dube sai suka fita. Dama ya kalli
agogo daya saura, sun fi minti 30 da tfy
sannan ya sauka ta dayan gefen da nisa
tsakani da unguwarsu gashi bashi da sisi, a
kafa ya dau hanya.
Hnkln ikilima ya tashi matuka, rashin ganin
baban khalil ita har ta soma bcci ta farka bata
ganshi ba. Ta dubi agogo sha 2, rabonshi da
kaiwa 12 tn suna husuma dashi. Nan idonta ya
gyara har dayan dare, biyu saura sai gashi
hajaran-majaran, dama shine ke rufe gida. Ta
kalleshi cikin dmw tace daga ina yayana? Ya
sauke ajiyar zucia munje ganin wani aiki ne
motar ta lalace gashi unguwar da nisa muka
tako a kafa. Tace sannu, zo ka kwnta dk na
damu hnklina ya tashi na rasa ina zan saka
kaina. Shi kuwa shiru yayi cikin zuciar shi yana
fadin "Astagfirullah, sbd karyar da yai. Sam be
runtsa ba yana mamakin dama mata sun lalace
haka? Musamman matan aure, shin bazasu ji
tsoron Allah ba? Mace da mijinki amma kina
bin wani don son zuciarki? Ki dau cikin wani ki
kai gidan mijinki. Basa tuna mutuwa, basa tuna
kabari ba ruwansu da tashin kiyama bare su
tuna wuta.
Rywr dunia kalilan ce, ayi ta aikata zunubi. Ana
cin buri kwana suna karewa, lallai kada mu
biyewa zuciarmu don dk wnda ya bita
karshensa nadama. Allah ka tsaremu da aikata
aikin dana sani. Dk lkcin da ikilima ta farka sai
ta ganshi ido 2, dn haka itama sama-sama tai
bcci. Da safe bcci ya dauke su byn sunyi
sallah. Sama-sama suke jin ana kwankwasa
kofa, ta tashi ta bude. Baban ummi ne tsaye
yace ina maigidanki tace gashi can yana bacci.
Yace ana sallama dashi. Taxo ta tashe shi.
Singlet ce da dogon wando a jhkinshi ya fito.
Nan take ya kara wartsakewa ganin yan sanda.
Suka dube shi. Kaine mahmud? Yace eh nine
suka ce bismillah muje sashinmu zaka amsa
wasu yan tambyoyi. A hnkli yace inna lillahi wa
inna ilaihir rajiun. To bari in dauko riga. Suka ce
a'a. Sai ga baban ummi. Ya dubeshi don Allah
yi min taimako da rigata sannan ka fada ma
matata. Ikilima ta miko rigar tare da cewa lfy
dai ko? Yace ina fa lfy, yan sanda ne. Ta dafa
kirji yan sanda? Ta suri hijabi ta fita, daidai
yasa rigar muryarta na rawa ta dubi
yansandan malam lfy, meya muku? Dayan yace
ya sani inya dawo zai miki bayani. Mutane har
sun fara taruwa suka shiga mota suka tafi
dashi. Da kuka ta nufi gidansu, a waje taci karo
da musa yace antyna lfy? Tace yansanda ne
suka kama baban khalil, yace meya faru? Tace
nima bn sani ba. Yace to koma gida bari in
sanar dasu.
A daki sai kai da kawo take yi ta rasa wane
tunani zata yi, ta xauna tana so ta tuna wani
lefi mijinta yayi? Su maman ummi suka shigo
suna bata hkri tare da cewa ko meye ze zo da
sauki. Sai da suka fita suka kebe suna cewa
kila ma sata yayi don jia sai cikin dare ya dawo.
Na fito fistari na ganshi. Inji aisha. Maman
ummi tace zai yiwu kin san wasu in basu dashi
basa hakuri, sai a shiga dan hali. Aisha tace
kai, amma anyi wayon banza, za a gina jiki da
haramun. Ikilima dai ta kosa taji meya faru, ta
sake zarar hijabi ta fita suna cewa ina zaki?
Tace a'a gidan su zanje. Tana fita suka sheke
da daria wai wahala ta ganta. Tana isa gidan
ta samesu cirko-cirko, nan suka shiga tmbyrta
ynda abin ya faru. Ta shaida musu cewa ita dai
jia byn yaci abinci ya fita be dawo ba sai wajen
biyun dare. Km tnda ya dawo be runtsa ba sai
byn ya dawo masallaci. Mahaifin nashi wnda
ya shirya don tfy ofis din yansandan shi dasu
musa yace baki tmbyeshi inda yaje ba? Tace
yace min sunje ganin wani aiki ne mota ta
lalace km dama be fita da kudi ba, a kasa ya
dawo. Zasu tafi tace zata bisu yace a'a ki
zauna ynxun zamu d
awo ba musan wane
ofishin ne ba sai mun bincika tukun.
MABUDIN WAHALA 2**9
Lkcn da mahmud suka isa gurin yan sandan,
nan suka soma mishi tambayoyi akan matar
dayai niyyar yiwa fyade jia burinshi be cika ba
ya dibar mata kudi ya gudu byn ya shaka mata
abin maye. Ya jinjina kai lkcin daya ga mijin
kullin da nafisar tai mishi. Yace yallabai ba hk
bane, ina zaune da abokaina tazo ta daukeni,
sannan ita ce ta rokeni inyi zina da ita naki
sannan bn shaka mata komai ba fakalin tasha,
km bn daukar mata ko sisi ba a kafa ma naje
gida tn daga Togo guest inn har unguwarmu.
Wani ya falla mishi mari uban wanene ze ga
wannan matar yaki? Kafin su alhji ibrahim su
iso yan sandan sunyi masa ligis dk sunji mishi
ciwo.
Da alhaji ya iso kuwa yan'sandan sunce yabi
wata matane har togo guest inn yayi mata
fyade sannan ya diba mata kudi. Sunce tabbas
hakan ya faru dan ya rupe kofar ya jefar da dan
makullin ta baya, sai da ya gama abinda zaiyi
sannan ya sa akawo mishi chips daman don a
bude ne ya sulale ya gudu.
Alhaji ibrahim yace to ya ya aka gane cewa
shine? Ai tasan shi ya taba nemanta tana
budurwa kuma shima ya amsa laifukan yace
yayi. Alhaji yace innalillahi.... Ya amas? Suka
ce ya amsa, ya mike ranshi bace tunda ya
aikata shi ya sani da iyalinshi da komai dan
fitinar tsiya. Musa yace alhaji hakuri zakayi
tunda bai taba aikata hakan ba ayi maganar
belinsa. Alhaji bai ko saurare su ba ya tabi.
Musa ya dubi yan'sandan yana cewa zamu iya
samun belinsa? Sukace a'a, kotu zamu mikashi
gobe, musa yace to zan iya ganinsa? Har
sunce a'a wani ya ce ku kira masa shi ya
ganshi. Musa idanuwanshi suka ciko da
hawaye, lokacin dayaga yanda suka maida
mahmud da duka, yace yaya me yaja maka
wannan danyan aiki? Dubi yanda sukayi maka
kankanci? Mahmud yace kasan wayeni musa,
in zanyi ka sani in ma bazanyi ba duk zaka
shaida kai dai mu barma Allah.
Mura yace hakane amma sunce ka amsa laifin?
Ya girgiza kai ko kusa ban amsa ba don ban
aikataba, sune kawai suka kagamin suka kuma
amsa min. Ni saida Allah ya sakamin. Musa ya
jinjina kai, wai wace mata ce? Mahmud ya yi
shiru sannan yace bansanta ba. Shi kanshi bai
san dalilin da yasa baice nafisa ba kila don
kada haushin nafisan ya shifi ikilima ne. Yan
sandan suka tasa keyersa don mai dashi ciki,
ya daga murya ka kwantar ma da ikilima
hankali, da son samu nema kada ka gaya mata
musa ya ce to. Sai dai kash!! Kafin musa ya
iso alhaji ya ba su lbrn laifin da mahmud ya
aikata, alhaji ya ce kuma zan iya yarda tunda
matar sa tace cikin dare ya dawo jiya shine zai
yi karya wai anje nuna musu aiki, wane aikine
za'a nuna da dare? Don haka ni ba ruwana, ya
karata can ba kanshi zan kare ba tunda bashi
kadai na haifa ba. Shine babba amma kullum
matsala, iklima ta kasa motsi tana sauraron
kowa saidai ita zuciyarta taki amincewa da
batun, kaman yadda yan gdan suka kama.
Suna cewa bai kyauta ba. Musa yanufi gurinta
zo muje gdanku. Ta bishi suka fita. Su hajiya
uwa sukace sai hakuri kaddara ce.
Lokacin da suka shiga gdansu makota sun
shigo su maman ummi suna basu lbrin. Suna
shigowa makwabta suka yi mata jaje ta amsa
tare da shigewa. Musa nifa banyarda ba, yace
yauwa wlh dama shima ke yakeji, tace haba
nasan wanene mijina, nasan sharri ne yanxun
za'a bada belinsa ne? Yace a'a sunce sai gobe
zasu kashi kotu ta soma kuka yanxu cikin
bainar jama'a za'a tona masa asiri. Musa yace
kada ki damu Allah ya tare da ku, ki ci gaba da
addu'a matan gdan kuma kada ki nuna musu
ko mai. Tace to goben kowanne hukunci za'a
yanke masa? Yace sai dai goben tunda matar
tace baiyi nasarar yi mata fyaden ba sai dai
kudin da tace ya di ba ikilima tace nawa ne?
Wai dubu ishirin tace to zani gdan wancen
dillaliyar tazo ta sai kujeruna yace ni kuma ina
ganin kamar gurin mamar mu, tace a'a
hankalinta zai tashi barta. Dillaliyar tasai kujeru
dubu sha daya, tace ga gadon. Ladi tace sabbi
zakiyi ne yarinya? Tace eh gadon ta
tarkacensa ta siya dubu sha biyar, nan ta
amshi kudin cikin dare kuwa aka fita da kayan,
ta'aje katifar ta a kasa kwana tayi tana kai
kukanta gurin Allah, kan cewa ya biya mata
bukatarta wato ya sakawa mijinta.els BOOK
MABUDIN WAHALA 3**1
Tana cikin sama khalil kaya musa ya shigo, ya
dubi dakin ina kujerun? Tace na saidasu,
yanxu ni ga dubu 25 a hanuna da shida ne zan
aje dubu 1 a gurina. Yace to nima wasu
shaddodine da baba yace a kaima su kamalu
dinki soboda zuwan sallah na saida dubu 3
tunda kin san ni din dan makanta ne ba kudine
da ni ba. Sannan abokansa sun hada kusan
dubu goma sha biyer. Shima fa baba ya damu
yana ganin kamar gaskene shiyasa ya share
zance. Amma yanda yake son yaya mahmud ai
ba ma zan yarda a ce bai damuba. Kana ko yi
addua? Ta tambayeshi, inayi mana addu'a
kuwa yinta ya zama dole, koda kuwa mu2m
baicika matsala ba. Suka fita ya sao mashin
suka tafi, can abokanshi suka samesu. Bayan
alkali yazo shari'a 2 akayi kafin nasu, nafisa
bata zo ba sai lauyanta. Alkali ya saurari bayani
daga kowane bangare
bisa shedun da yasan dake dasu. Musamman
yan togo guest inn da suka bada shedar. Alkali
ya yenke masa hukuncin tara dubu ashirin
kudin daya diba kuma zaya biya. Tunda aka
fito dashi ikilima ke faman kuka saboda cikin
kwana daya dubi yadda ya koma ga jikinsa duk
jini. Ta mika ma musa ya basu nan suka hada
dubu arba'in suka bama alkali. Sulaiman ne
yakai kudin koto ta sake shi. Jama'a sukayita
masa murna, wasu kuma suna cewa Allah ya
shiryeshi ya kiyayi gaba. Ikilima tana zuwa ta
daura ruwa dan sunriga mahmud dawowa.
Lokacin da ya shigo dakin tare da abokanshi,
sai ya shiga waige waige, tamkar zaure ya fada
a ranshi, ta shimfida musu taburma sun dan
kara jajanta mishi nan sulaiman yace ikilima ga
sauran kudin, dama mu mun hada dubu 12 ke
da musa kun hada 35 yanxu ga 7. To
mungodai. Allah ya bar kauna ku bashi, inji
ikilima suka mika mishi ya amsa yana godiya
tare da addu'a. Matan gdan suka shigo suna
gaisheshi. Bayan fitar su ita ce tayi masa
wanka tare da gasa masa jiki,tanayi tana kuda
dama taba musa ya siyo mata manzafi tunda
suka dawo, ta shafe mishi jiki sannan ya sha
tea da panadol ya kwanta.
Ko lokacin da su hajiya uwa suka zo yayi bacci,
lbr malam usman yaji yazo dan ita batayi niyar
sanar da mahaifinta ba, yazo shima ya same
shi yana bacci yace kada ta tasheshi Allah ya
kyauta gaba, tace amin yace ni da'akace
mahmud yaje sata har yayiwa matar fyade
banyarda ba. Tace ai abin yarda ma daban
yake baba. Sharri ne dai kuma zaya koma ga
maishi. Kiyi ta hakur,gaskiya zata fito inji baba.
To

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment