Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa caaa kowa na nuna
masa cewa abinda yayi bai dace ba.
Bala ya mika masa ledar kajin da kayan tea
yace ka gani ta kan sauri har zan tafi da cin
hancin da xa a bawa amaryar. Mahmud ya
amsa ya koma ciki. ME ZAI FARU?
Daidai wannan lokacin nfsa tana kwance kan
tsalelen gadonta tana sanye da kayan bacci
masu santsi da ta kalli kanta a madubi sai taji
sha'awa ta sake bijiro mata taja tsaki a fili take
cewa ace ranar da aka kawoka mijinka yayi
tafiya?danginta yan rakiya da kawayanta suna
tafya shima ya shigo yana bata hakuri cewa
xai tafi america don Allah tayi hakuri. Ranta ya
baci sosai tace suje tare yace babu halin yin
hakan kada ta damu sati1 kawai xayai ya dawo
amma hashi yau 10 days yadai ce gobe xai
dawo shi yasa ma da ta aje kayan matan da
take dirka sai yau ta ciro tana sha saboda gobe
xaya dawo.
Wayarta ta soma ruri ga xaton ta shi ne amma
tana kallon fuskar wayar safina ce tace
soyayya ta rufe jinki da ganinki kawata ko ki
kira mu kiyi man ban gajiya? Nfsa tace yi hakuri
safina kina raina ya gajiya na fa gode. Safna
tace ba damuwa kin san Allah kawata kin dace
duk ckin kawayanmu babu yake,inaga fa kashe
auran nan xanyi na rabonan ko xan samu
shigen naki don samun irinsu sai sa'a. Nfsa ta
saki dariya sannan tace baxan so kiyi ma Alhaji
sani haka ba,nfsa tace nafa gaya miki
matsolilinsa 2nda ya kai ni gdansa aka gama
amarci ke bamu ma gama amarci ba ya watsar
dani yaci gaba da bin matansa. Kudinshi kuwa
sai dai in nagani na sata,sisin shi ya daina bani
in kuma in na satan yaxo yayi ta bala'i rannan
har da marina. Mari inji nfsa?safina tace kinji
kadan. Nfsa tace lallai to kiyi dai mai yiwuwa
safina tace ai shi ne nake son yi yanxun xan
dai kiraki. Amma abubuwan da kika sha nasan
kin rikita angon ko?
Nafisa tace, kuna tfy aka kira shi mitin America,
gobe zamu soyewa sai dai kin san wata
matsala? Safina tace sai kin fada, tace samun
kaina danayi cikin gidan nan in ci, in sha in baje
a gado ya dawo min da son mahmud sabo dal.
Safina tace, ke dai sakarya ce, dubi motocin
daya nuna mana yace naki ne guda 5 duk
manyan motoci me zaki tuna wani mahmud?
Kin ma san yayi aure ko? Nafisa ta mike tsaye
ta ce, "Aure kuma? Ina..." wace ya aura...
Santa yake? Na shiga 3! Safina tace nima ina
gida lbri yaxo min ynda aka ce min ikilimarku
ya aura..." sam bata san lkcin da wayar ta
subuce daga hannunta ba, ta dora hannuwanta
akai tana zaga dakin, komai ya dagule mata
kai wannan mummunan lbri Allah yasa mafarki
ne. Tabdi! In ko ya auri iklima ya kasheta
domin hakan yana nufin sun rabu tnda sun
zama surukai. Hawaye ya shiga sintiri akan
fuskarta. Da tayi kukanta ta gaji sai km zcyrta
ta shiga saka mata cewa kila karya ne, dn
haka taxo inda ta yar da wayarta ta dauka ta
kira mamansu cikin kuka tana tambyrta wai
haule gaske ne iklima ta auri masoyi na?"
Haule don ta kwantar mata da hankali ta ce, ke
karyane, ikilimar da naga an nuno ta suna
gasar kara2 a saudiya! Nafisa ta sauke ajiyar
zucia tace har naji dadi. Haule tace ke da ke
gidan wani ina ruwanki da shi? Nafisa tace tab!
Har gobe ina son shi, sannan ta kashe wayar.
Ta zauna ta zuba tagumi ina ma yana da waya
da ta kirashi taji muryar nan tashi mai taushi.
Kai ranar dai nafisa b barcin kirki, kwana tayi
tana juyi cikin mayen son mahmud tare da
begen shi game da tsantsar sha'awar sa.
Washegari uku daidai alhaji jamilu ya shigo,
tana sanye da riga da wando irin masu rawa
din nan dama gashi ta kware wajen juya jiki,
bata sa komai ba sai wadannan kayan ta zubo
gashi baya.
Da gudu taje ta rungume shi, amma ga
mamakinta sai ya cire ta daga jikinshi, ya dube
ta fuskar shi da murmushi yace na sameki
lafia? Tace lfy lau, ya nufi sashenshi ta bishi,
biye dasu km yaranshi ne dauke da jakarsa.
Kayataccn falon ya bude suka shiga, yau ita ce
ranar farko data shigo gefen nashi, gurin kam
ya tsaru. Ya zauna kan wata kujera wadda ita
kadai ce kalarta daban a cikin falon, tamkar ta
zinare. Yaran suka shiga dakin bccnsa suka
ajje jakar sannan suka fita tare da cewar mun
brka lafia yallabai. Ta dube shi za a kawo ma
wani abu ne? Da murmushi yace "je ki huta" ya
danna wani guri sai ga makel shugabn kicin
kenan. Makel yai gaisuwa, alhajin ya amsa
sannan yace hna son abu mara nauyi da mai
sanyi. Makel ya fita tare da cewa "To". Dk
nafisa na zaune a hannun kujerar dake kusa
da alhajin tana kallonsu. Ya dawo a jikin
kujerar ya danna wani guri sai ga tebur ya fito
na gilash nan ya shiga jera abincin, ya gama ya
fita. Tace in in baka? Yace ki huta madam, ke ai
yar hu2 ce. Yasa hannunsa ya ciro hakoransa
guda 4 na gaba, ashe dk na roba ne ya aje su
cikin wani abu.
Da ta dube shi sai taga ya bata tsoro, ya cgb
da cin abincin sa ya gama ya maida su ya mike
tare da cewa bari inyi wanka. Tace "ko nazo
muyi ne? Nan ma yace ta huta. Ta zame kan
kujera ta zauna tai jugum ta zabga tagumi,
ynda ta ganshi ba hakoran gaba din nan dk sai
taji ya sure mata. Abinda yafi daure mata kai,
da dare takai kanta gurinshi yana zaune yana
waya sanye yake da kayan bcci, itama cikin
kayan bccn take irin masu mannewa a jiki tare
da fidda surar jiki. Dole ne dk lafiyayyen namiji
inya ganta hnklinsa ya tashi. Amma shi sai
yace bakiyi bcci ba? Tace "Eh" yace ya kamata
ki kwnta. Ta xuba mishi idanu tare da cewa
jikinka zan kwana, yayi murmushi "au bn sanar
dake ba ko? Ya iso kusa da ita, ni ba namiji
bane. Ina nufin bazan iya amfana ma mace
komai ba Gabanta ya fadi ta dafa kirji shine ka
aure ni?
Dama dn kawai ka kalle ni ka aure ni? Yace,
kwarai ina son zan tsaya takarar dan majalisa
to kinga be dace ace bani da iyali ba, ya iso
inda tayi mu2war tsaye yace karki damu kudi
dai masu suna kudi zan jibge musu ga babban
gida da manyan motoci a zatona baki da
matsala? Ta girgiza kai, kayi kuskure dk mace
mai lfy tana bukatar namiji musamman wadda
ta samu hu2 iri na, dn haka kawai ni ka
sawwake min". Ya kyalkyale da daria me karfi
sannan yace "yaro be san wuta ba sai ya taka"
ya ciro wata doguwar takarda a tsakiyar littafi
"Ga wannan lissafa, ina zaton in kinbi a hnkli
zaki gano lissafin daki-daki, ki maido min da
kudina sai na sake ki kawai
Total din ta soma kallo, taga an rubuta miliyan
dari uku da dubu 6 da dari 7 da hamsin. Nan
take ta soma ganin jiri tare da kallon shi yace
ki lissafa naira daya bn kara ba, lallai baku da
hankli da kike ganin tamkr bn san ciwon kudina
ba, ko da nomansu nayi ko hako su nayi dole in
san ynda xan kashe su. Amma rannar farko
dana fara ganinki anyi miki tayin kudi kika dibi
miliyan daya bb dubu dari, yayi yar daria
sannan yace tn lkcin nasan ke ba karamar
muguwa bace a fagen son kudi" ya cgb da
cewa "ynxu ina so kije dakinki ki lissafa ki gani
sannan ki zabi daya, zaki zauna ko zaki biyani
kudina ki kama gabanki? Ta dafa bngo ta juya
shi km cikin murmushi yace "kwadayi mabudin
wahala". Ta zube a tsakar daki cikin
matsananciyar dmw, zufa tana kwaranya dg
jikinta dk da karfin (AC) din dake dakin. Abin
al'ajabi alhji jamilu ya soma lissafi ne tn daga
kudin daya lika mata har xuwa na man motar
da aka maida danginta gida lkcin dasuka yo
mata rakiya.
Kudin daya bata da gidn daya sai ma mamanta
dk suna cikin lissafi, hatta likin dayayi a bikin
su, mai hoto da na bidiyo duk kowanne da date
da time, da km kudin da aka kashe har da
rasitai ma ga sunan. Nafisa ta ajjiye takarda
tana ta shiga 3 ni nafisa, ta dau wayarta ta
shiga kiran layin haule. Cikin zumudi haule da
daga wayar, numfashinta ya nemi daukewa jin
nafisa tana rera kuka. Tayi saurin jawo shi
sannan tace wace kyauta ya miki mai dadi har
ta saki kuka? Nafisa tace "kinji fa haule, ashe
alhji mugunta ce tasa ya aure ni, shi ba namiji
bane, wlhi baya iya amfana ma mace komai, ya
raba ni da masoyina" ga mamakinta sai taji
haule tace "To ke ina ruwanki, kin huta ma da
damu". Nafisa tace "bazan zauna ba, ya dai ce
mu dawo mishi da dk abnda ya kashe mana
daidai da ruwan sha da aka siya na bikin ya
lissafa kudinsa miliyan dari 3 har da
dubunnai". Haule tace "to ke bnda hauka irin
naki baga kudi ba? Kwntr da hnklinki kici inya
mu2 kin haye. Nafisa tace ni dai ki harhada
kudi gurinki ne baxan xauna ba xanxo ne in
auri mahmud dina" haule tace "duba nan
nafisa, ki samu nutsuwa, mahmud fa ynxu
baku da aure don gskiyar magana ya auri
ikilima tn kafin a daura naku..... Da karfi tace,
"ikilima? Na shiga 3. Ta yar da wayar da
takardar, sannan ta zube kan gado tana rera
kuka.
Alhji jamilu ya shigo yana daria. Madam dama
baki san masoyinki ya auri kanwarki ba? Ya
xauna kusa da ita, "sakamako kenan na
toxarta shi da kikayi. Ko lkcn da kika ce auren
dole za a miki dashi naji ki ne kawai don ina da
lbrin dawainiyar daya muku. A ynxu lkci ya
kure, gara ma ki zauna ki huta yar hutu. Ga
babbn gida ga manyan motoci, a sanina
burinki be wuce wannan ba. Amma ki bari gobe
xan kaiki gidan hajara matar alhji kabiru ta baki
shawara". Ya miki tare da cewa sai da safe yar
hu2. Ta bishi da kallo har ya fita ta sake
fashewa da kuka tare da fadin "Na shga uku!!!"s BOOK
MABUDIN WAHALA 2***1
A DAKIN AMARYA
Ya shigo da sallama cikin dakin,ya xauna kan
kujera sam bata ji ba tana cikin dakin tana
ninke hijabinta ta gama ta fito don kwashe
plate din da ta kawo ma abokan ango cin cin
sai ta ganshi xaune kan kujera shi kam bai ma
san ta shigo ba yana duniyar 2nani. Sam
baxaya iya fassara yaya yake jin lamarin
ba,muryarta ta katse shi da cewa sannu ka
dawo?ya daga idanunshi masu cike da
damuwa ya xuba su kan fuskar iklima yarinya
mai kalar madara in an hada shi da bournvita
idanunta farare tar masu kalar tashi daga bacci
duk da basu kai girman na nafsa ba amma sun
fi nata ban sha'awa daga ganin fuskar xata yi
laushi ba irinta nfsa ba da man bilicin yasa
mata kuraje,lebunant a yan yala yala hancin ta
bashi da tsawo amma ya dace da fuskarta mai
dan tsawo. Yace sun tafi tace kaima na xuba
maka cin cin
din?ya girgixa head tare da kishingida ta koma
ciki tayi alwala a bayi taxo ta tada nafila gami
da shafa'i da wuturi sannan ta canxa kayanta
xuwa doguwar rigar bacci wadda ita kadai aka
sako cikin kayan lefen ta saka ta kwanta tana
gama addua bacci yayi awon gaba da ita,shi
kuwa ya jima idanunshi basu daina ganin
hoton fuskar iklima ba duk da ba xaya ce sonta
yake ba,ba xai ce bata da kyau ba kyawunta
irin sassanyan nan ne matsalarta rashin
wayewa,sam bai san lokaci ya tafi ba,sai da ya
dubi agogon hannun shi 2 na dare xufa duk ta
jika shi saboda yanayin xafin da garin minna ke
da shi duk da cewa damina ce. Ya tashi yana
son watsa ma jikinshi ruwa sai dai baya son
shiga bedroom din nasu dama ya kawo kayan
shi ne da ya kunna fanka da yaga bashi da
yanda xayayi sai kawai ya danna kai cikin
bedroom din.
Idanunshi suka sauka kanta,tana baccinta
cikin kwanciyar hankali fuskarta tamkar tana
murmushi, gashin kanta ne ya fi daukar
hankalinsa ya bazu kan filo wasu kuma sun
sauka kirjinta. Ya 2no nfsa nata iyakarshi
dokin wuya amma birge shi yake yi ita wannan
nata har kirji sai dai shi ba ya kyalli irin na
nfsa.
Ya jima yana kallon kirjinta xuwa hips dinta
yana ganin kamar tafi nafsa jki sai dai nfsan
tafi ta sarrafa jikin ganin tayi motsi ne yasa shi
nufar bandaki don kada ta tashi ta gane tsaye
kanta.
Lokacin da ya fito tayi juyi ta koma rigingine ya
sake xuba idanunshi kanta yana tafiya har yaci
karo sannan ya fita,rataye kayanshi yayi ya
kwanta daga singileti sai gajeren wando
(Boxer) ya kasa runtsawa domin gizon da take
mishi.
Da ace nfsa ce yau kam yasan baxaya barta
ba,ita ce ma xata taimaka burin shi ya cika,ita
ko wannan kila ma in yace ga abinda yake so
gareta ta raina shii 2nda ba wai son shi takeyi
ba, tada sallar da masallacin kusa da su suka
yi ne ya tada shi daga baccin mai cike da
mafarkin yarinyar wadda ke matsyin matar sa
yanzu.
Ya dan ja tsaki domin ya xamar masa dole yayi
wanka gashi bai kawo suturun shi ko1 gidan
ba dole sai dai ya shiga daga shi sai singileti
din da boxer in ya fito ya saka kayan shi ya
rataya rigar a kafada yayi ciki tashin ta kenan
tana xaune a tsakiyar gadon shigowar sa yasa
ta rufe jikinta sannan tace mun makara ne?
Yace a'a yanxun aka tada sallah ya shige toilet
din,ta bishi da kallo. A ranta tace suffar shi ta
asalin jarumai maxa masu lafiya da kuxari
daga ganin shi kasan ba rago bane. Tayi maza
ta canza kayanta kafin ya fito yana fitowa ya
saka rigar shi ta shadda yana rike da singletin
da boxer din ta amsa tare da cewa kawo,ya
bata sannan ya fita falon ya saka wandon sa
ya nufi masallaci ita kuma ta shiga don yin
alwala tare da saka kayan nashi ckin wani
bokiti.
Tana kara2n kur'ani mai girma lkcn daya dawo,
ya xauna nan falon da ta gama tayi addu'a ta
tashi. Shi dayake falon ma ji yake tamkar kar
tayi shiru, da dayake jin kara2n nata cikin
wayoyin mu2ne da redio yin jama'a ya xaci an
goge ne cikin computer an sirance muryar,
ashe tata ce. Hakan nan shima mata da maxa
suna son kara2n. Ta fito sanye da hijabi itama
ta xauna kan kujera tace, "yaya mahmud ina
kwana"? Ya amsa ba tare daya kalleta ba
sannan fuskar sa ba yabo ba fallasa. Tace mun
kwana lfy? Yace "Alhmdlh". Ya miko mata ledar
gefenshi ta amsa tare da budewa ta leka, kazar
jia ce da kayan tea da bread. Ta dubi fuskar shi
"bari na hada rishon, sai dai kalanzir ne
matsala. Yace bari na dauko hita a dakina" ya
mike tace to ka dawo lfy. Ya sake dubanta
sannan yace Allah yasa. Kafin ya dawo ta
wanke bayinsu ta gyara gadonta tare da share
dakin ta goge. Ta duba cikin akwatinta ta ciro
turare ta dinga fesawa a dakin, duk da cewa na
jiki ne. Tazo kasan gado tana ciro kayan
girkinta. A fili tace, gaskia ina da bukatar kayan
aiki. Ta hada risho sannan ta fitar da kofunan
roba da jug dinsu, ta fita ta wanke su ta dawo.
Sauran matan gidan duk suna cikin dakunansu.
Ta bude kicin din shima ta share sannan ja
zuba kayan girkinta ciki. Sai gashi ya shigo, ya
dube ta, "tsakar gidan ma har da wani uban
hijabi? Cikin xuciarsa yayi maganar. Sai dai ta
lura da ynda yadan hada rai. Da sauri ta amshi
jakar hannunsa tare da cewa "sannu da xuwa"
yace "yauwa. Ya juya. Ya sake shigowa da
akwatin kayansa ya shiga dasu ciki, tace kazo
da hitar ne? Yace "eh, gata can cikin ledar can
har da dutsen guga na soma rago kayana ne.
Nan ta jona masa ruwan wanka dayayi xafi ta
juye cikin buckt ta kai bayin ta sirka masa,
sannan tace ga ruwan wanka kafin ka gama
wannan yai xafi". Ya dubeta "na gode" kafin ya
fito ta shirya kayan tea cikin wani tire da flask
din ruwan zafi. Ya fito ya shafa man shi wnda
yaxo dasu cikin jaka, ya saka kananan
kayansa blue jeans da jar riga, yayi kyau. Yasa
turarukansa masu kamshi. Mahmud akwai
tsaftar gaske. Ya fito tana ciro takalmansa
daga cikin wata leda baka dayazo dasu, ta
gama curowa tasa kyalle tana goge su, ta
shigar masa dasu ciki byn ya dau wnda zai
saka. Ya shinfida darduma ya zauna kasa yace
yafi son cin abinci yana zaune kasa. Yace "to
zo mu karya. Tace ni ynxu zanyi wanka ne, in
na gama zan karya" yace "okey, bari in jira ki.
Taxo ta zauna "ra'ayinka za'a bi, bari mu karya
din. Tasa karamar wuka tana yanka mishi
naman kazar byn ta hada mishi tea din. Ya
dauki kofi shima ya hada ga zatonta zaya ce
baya son wnda ta hada ne. Ya gama sai taga
ya miko mata yana murmushi. Ta karba tare da
cewa na gode. Kadan-kadan take kurba don
tana jin nauyinsa. Dakin ya tsit don basu saba
da juna ba yace "kinki ci bread din, ga naman
ma" ta dube shi "nafi son lipton. Ya kalli kofin
ashe ko madara baki so, meyasa? Tace na'a-
na'a kawai nake sawa. Ya dubeta meye
wannan? Ta danyi murmushi, wani ganyen
shayi ne muke amfani dashi sbd yana gyara
mana murya gurin kara2, bama samun
matsala.
Ya kurbi shayin "kin san mun taba musu da
nafisa nace ina zaton ana goge karatn ki a
computer tace min a'a wai muryarki ce" ta dire
cup din tare da hamdala sannan tace "dayawa
mutane haka suke cewa, amma ba hakan
bane" ya dire kofin sa "bari inje xan turo yara
da kalanzir din. Zan tattara kayana guri 1 in
kawo in bazan takura miki ba sai ki dafa mana
wani abu ko? Cikin idanunshi manya masu
yalwar gashi ta kalla fuskarta dauke da
mamaki tace "umarni kawai ya dace ka bani ba
neman taimako ba, me kake son a dafa? Yace
duk wanda kika so, sai dai ina zatn su muktar
zasu zo. Tace to bb dmw, sai ka dawo" ya fito
ta biyoshi har bakin kofar daki tace sai ka
dawo yace to
Tayi wanke-wanke lkcn matan gidan sun pito
bakin pampo suna aiki,ta gayshe su suka
amsa cikin sakin puska tayi wanka tare da
kwallia ta saka wani yadi riga da wando cikin
kayan akwatinta,ta shapa turare. Sallamar yara
taji ta pito sukace aunty ina yini? Tace lapia
lau sukace yaya ne ya aikomu suka mika mata
kalanzir da kayan miya da nama da kipi,ta
basu cincin da alkaki tare da tambayan
sunayensu,suka gaya mata tare da cewar sun
tapi tace to ta goday su gayshe da mutanen
gidan. Yaran suka pito suna murna tare da
yaba halin auntien nasu. Nan iklima ta para
tunanin me xata para dapawa a matsayinta na
amarya shirya musu talia tayi ta wadata ta da
kipin da naman da kuma kayan lambu wanda
ta bada kudinta aka siyo mata ta xuba,gidan
ya cika da kamshi 2 dai dai suka shigo lokacin
ta gama komai ta xira hijabi ta pita ta shirya
musu komai sannan suka gaysa ta koma ciki.
Tana jiyosu suna ce mishi,ai wannan tapi ma
napisar da kakeso kyau gata kamila. Shi kuma
yace ina be yadda ba napisa tana da kyau ga
wayewa ga kuma son da yake mata. Dik suna
batun ne a hankali amma kuma dik sunaji,sai
dai dik da ba sonshi take ba bataji dadin
abinda ya pada ba. Tana kwance tana tinanin
cewa kenan xai xauna da itane yayarta na
xuciarshi alhalin itama tana da wanda takeso
kuma ta hakura? Muryarshi ce ta katseta inda
yace mun wuce suna ta miki sallama. Tayi
ajiyar xucia,sannan tace to sai ka dawo su
kuma tace mun gode ku gayda gida. Sukace
sune da godia,daganan bai shigo ba sai bayan
sallan isha'i ya shigo da kankana da lemo da
abarba. Tana xaune a parlour tana karatun
Qur'ani, tayi mishi sannu da xuwa sannan tace
ko xaiyi wanka? Yace ehh. Dama ta dapa
ruwan sai kawai ta sirka kapin ya pito ta hada
mishi kayan itatuwan da yaxo dasu cikin plate.
Cikin shirin bacci ya pito palon ya xauna tace
ga tuwo da aka kawo mana daga gidanku yace
xanci kadan dama sun sanni da son tuwo
shiyasa suka aikomin. Ta xuba masa yanaci
sai yace itapa ? Tace ta koshi. Ya daure puska
tare da tsareta da ido kinason ace bana kula
dake ko? Dik yau ruwan lipton kawai naga
kinsha tace naci abinci daxu yace oyah! Matso
kisa hannu mu ci,dama nima yayi min yawa
dama shi ba gwanin daria bane,ya tsare gida
gashi yana da kwarjini matuka yanda baxa ka
iya jan musu dashi ba dan haka sai ta matso
ta saka hannu. Ya kalli xara-xaran yatsunta
meyasa bakiyi lalle ba? Tayi dan murmushi ban
sami lokaci bane saboda shirin tapia da mukayi
a lokacin yace hakane, na manta ban miki
jinjina ba,sai dai naso ace kece ta parko ina
nupin ta 1. Tace ta biyun ma ban saka rai ba
dan dik nice karama cikinsu kuma suna da ilimi
sosai yace haka, kinyi kokari. Ta tashi da
dauko mishi ruwan wanke hannu ta dire a
gabansa tace kyauta ya dace ka bani ya dan
murmusa ki bini bashi tace ina wasane pa yace
nikam da gaske nake xan baki wata rana tace
nagode ya sake dubanta cikin idanu tin kapin
kiga kyautan kin para godia? Ke kam kina da
yawan yin godia. Ta murmusa tare da tattare
kayan ta kai kitchen ta kulle itama tayi shirin
bacci.
Yau ma tamkar jiya falo ya kwanta yana ta
sakar zuci shi kam mabuqaci ne amma girman
kai yana so ya cutar dashi yanda ya lura da ita
sam ba zata yi taurin kai ko wahalar
sauraronshi ba. Ita kuwa ta fi tunanin kaninta
nafiu da mahaifinta,bata san me girka musu
abinci ba,gashi nafiu bai zo gurinta ba bare ta ji
labarin baban nasu,Allah ya dai turo mata
keyarshi,haka suka kwana.
Nafisa zaune tsakiyar gadonta hawayenta sun
kasa qafewa.kenan haka zata yi rayuwarta ita
daya? Kai da sake! Ita ba zata iya ba domin
ubangijinmu bai halicci mace don tayi rayuwa
ita daya ba wannan ma wani nau'in azabtarwa
ce da Alh jamilun yake son yi mata. Sallamar
anty hajara ce ta dawo da ita cikin tunanin.
Hajara ta shigo sanye da doguwar rigar atamfa
'yar holland fara mai ratsin ja,gyalenta da
takalmin da ta saka ma duk jajaye ne. Ta
zauna. Kusa da nafisa tana murmushi ta ce
"kanwata kukan ne dai?" Nafisa ta matso ta
kwanta jikin hajara tana cewa, anty hajara ki
taimake ni na saba ma mahaifina na ci amanar
masoyina na haqiqa gashi tun kafin aje ko'ina
na soma yin nadama. Hajara tana dan
bubbuga bayanta tana cewa "yi shiru ki tashi
muyi magana,nima abinda ya kawo ni kenan"
ta share hawayenta ta gyara zama ta dubi
hajara ta ce "dama alh jamilu ba namiji ba ne?"
Hajara ta ce eh,ta ce wlh da ya fada min ba
zan aure shi ba. Hajara ta ce duk kin damu
kanki,budurwa wadda bata san ya ya namiji
yake ba bana zaton zata damu kanta. Nafisa
cikin damuwa ta ce "ba zan boye miki ba anti
hajara nasan da namiji"
Hajara ta ce "to ki kwantar da hankalinki kiyi
zamanki domin ba zai sake ki ba sai kin ba shi
kudinshi in ko kin zauna a jikinshi ma sai ki
tara ki bashi abinsa ki huta. Kuma yanzun ne
ya dace ki saki jikinki ki kwashi kudin in ki ka ci
gaba da kunci ba zai sakar maki ba,ni kaina
ina da tawa matsalar in kin nutsu za ki fahimci
komai ke kusan duk wata mace da ke zaune
garin abuja ko bata da matsala to tasan wata
ko maqociya me fama da shigen tamu
matsalar. Nafisa ta ce "anty fayyace min" ta ce
sai kin kwana biyu kin soma gano lamuran
yanzun dai ina so ki saki jikinki kada ki fada ma
kowa hatta mahaifiyarki. Nafisa ta ce,har kuwa
na fada mata. Anty hajara ta ce,kash kinyi
gaggawa to me ki ka ce mata? Ita kuma me ta
ce? Nafisa ta ce, na fada mata cewa shi din ba
namiji bane. To me ta ce? Nafisa ta ce,cewa
tayi wannan ba matsala ba ce da zata sani na
bar daular da nake ciki har ma tayi ikirarin tsine
min in na ce dole sai mijina ya sake ni. A
cewarta bata da kudin biyansa,kuma ta soma
sabawa da daula ba za ta iya hakura ba,a
karshe ma cewa tayi sai na biya ta nononta in
har nayi mata asarar zuwa aikin hajjin bana
wanda Alh jamilun yayi mata alkwari.Anty
hajara tace,to kin ma ji mahaifiyarki,sai dai
koda za kii ga ko ki ji wani abun nan gaba
wannan sirri ne tsakaninki da mijinki kada ki
fada ma wani.
Nafisa ta ce,shi kenan. Hajara ta ce "yauwa,ki
kwantar da hankalinki,duk abinda ya shige miki
duhu ki fada min zan bude maki haske. Nafisa
ta ce to.tun daga ranar Nafisa ta hakura,kudi
kuwa sai dai ya nuna mata in da zata dauka,in
dai karamar bukata ce in kuwa babba ce zai
tura mata cikin account. Damuwarta da abinda
ke sa ta kuka kullum shine rasa
masoyinta.Motoci luwa duk wadda take so
zata hau,'yan aikinta ne dai suna ganin
wulakanci da iya yi. Kullum dare in ta kwanta
kewar kasancewa da masoyinta ke hanata
bacci don haka maimakon kyau sai ta shiga
rama.Alhaji jamilu kuwa ba shi da lokacinta sai
dai ta waya.haka nan ya tsani taje mishi sashe
har da maigadin gurin,tun tana jin haushi har
ta hakura. Yau gidan anty hajara tayi niyyar
zuwa sun gama gaisawa ta dauki ummi tana
cewa "kitsonta ya yi kyau,itama kuwa tana son
ayi mata kitso" anty hajara ta ce,ummi kira ladi
mai aiki in aike ku.Da ta kira ta, ta ce. Suje su
ce ma mai kitso in layi ya ragu tazo zata yi ma
baquwa kitso. Suna fita ta dubi nafisa ta ce
kanwata naga duk kin fige ya ya ne? Nafisa tayi
rau-rau da idanunta hawaye suka soma zirara
a kan kumatunta ta ce anty hajara ba zan iya
zama ba gaskiya ina da bukatar abokin halitta
ta,ke mace ce na san kin san cewa duk macen
da ta zama cikin hutu lamuranta basa cika sai
da da namiji.Ni kuwa ina mamakin ya ya za'a
ce ina da miji daga ka ganshi mai kyau da
kuzari amma ace ba shi da amfani a gurina.
Hajara tace "to ya ki ke so ayi? Shi dai ba za
ya iya

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment