Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko mahmud
na ckin gidannan kamin sallama dashi? Musa
ya gane surkinsa ne don haka yace ga dakinsa
nan,yace to yi min sallama dashi musa yace
shigo kawai baba,yace ayi haka?musa yace ba
damuwa. Malam usman ya shiga da
sallama,mahmud dake xaune ya xabga uban
tagumi ya amsa sallamar ganin baban su nfsa
sai ya mike da sauri,malam usman ya mika
masa hannu su gaisa amma ya noke tare da
nuna masa kujera bismillah xauna baba,yace
da ka bani hannu mun gaisa ba karamin lada
bane ga kankare xunubi ga musulmi masu yin
musabaha. Shi dai mahmud kanshi yana kasa
suka gaisa ya sake tambayar shi jiki.malam
usman ya kalli musa wanda ke shirin fita yace
wannan ba kanin ka bane?mahmud yace
danuwa na ne,malam usman yace to dawo ka
xauna musa ya dawo ya xauna. Malam usman
ya koro musu duk abinda nfsa ta mishi sannan
yace ya yafe ta cikin yayan sa sannan yace
naxo maka da albishirin baka iklima kuma xa a
daura auran ne a ranar da akasa kai da nfsa.
Mahmud ya dauki rigarsa dake kan katifa ya
shiga share xufa sannan yayi karfin halin cewa
baba mu bar ba2n iklima don kanwa ta na
dauketa,nfsa kuwa na hakura haka Allah ya
nufa xaya faru. Malam usman yace kada kayi
saurin yanke hukunci kaga lokaci ya kure yau
saura kwana4 daurin aure kayi shawara da
magabatan ka. Shawara ta gare ka kada kace
xaka ki iklima tafi nafsa komai,riba kaci don
samun mace mai ilmi da addini ba karamin
falala bane samun mace mai addini shine cikar
mu2ncin da namiji. Mahmud yayi shiru,malam
usman ya mike yace to duk yanda ake ciki naji
xuwa da safe,mahmud yace mai sonta ina
2nanin ba xaya ji dadi ba,malam usman yace
kada ka damu da wannan saboda
magabatanshi basuxo gurin mu ba ya fita yana
cewa Allah ya sawwake ina sauraron ka. Musa
yace to mun gode baba,xanxo da safen,malam
usman yace to kwa iya yin shawara da
magabatanku. Ya fita
Yana fita musa ya dube shi yaya kayi naxari in
dai yana nufi yarinyar nan ce mai sanya nikabi
mutane dayawa na sonta har dani,a ganina
dami ka tsinta a akala yarinyar da taci gasar
kara2n Al-Qur'ani mai girma na kasa yanxun
haka xata tafi ta duniya gaba daya a kasar
saudiya ranar asabar dinnan mai xuwa in an
daura auranka da kwana1 nasan ka sani da
gaske ne kalmar mahaifinta riba kaci. Mahmud
yace son fa?ina son nfsa sosai wlh ban san irin
son da nake mata ba sai yanxun da na rasa ta
bana bacci. Musa yace ka amince in so samu
ne ma baba kada muyi mishi bayani sai
ranar,kayi kokarin ganawa da ita. Mahmud
yace xanyi kokarin yin istihara yau da dare xan
roki Allah in da alkhairi yasa min son lamarin
cikin raina amma yanxun dai ko sunan mace
ban son ji. Musa yace yauwa sai kabawa Allah
xabi sai dai ina 2nanin Alhajin mu. Mahmud
yace shi da bashi da burin da ya wuce na son
inyi aure bana jin xai ki yarda don kasan baya
son nfsa,musa yace haka ne yanxu dai bari in
barka. Sukayi wa juna sai da safe ya fice.
Daren ranar babu wanda ya runtsa cikin mu2m
3. Malam usman yana sallar nafila ne yana
gaya ma Allah matsalar shi wato inda alkhairi
auran iklima da mahmud Allah ya
tabbatar,iklima itama zabin Allah take
nema,shima mahmud haka.
Nfsa kuwa dai dai wannan lokacin tana can
akan tafkeken gadonta na gdan matar abokin
Alhaji jamilu tana ta sharar bacci har da
mafarkin ana yin bikin su ita da mahmud yana
bata tsire a baki ita kuma sai narke masa take
yi. Lokacin da gari ya waye ta tashi sai 2nanin
mahmud ya dawo mata sabo tare da sonsa
mai tsanani. Ta janyo filo ta manna shi a
kirjinta tare da lumshe eyes tana rayawa kan
faffadan kirjinda ta dora,kai dole ne ma in ta
fizgi abinda xata fisga ta koma ta aureshi. Ta
lura ba xata taba jin dadi ba matsawar bata
tare dashi damuwar ta Allah yasa kada yayi
auran huce haushi da wata,koda yake tasan
bashi da kudin yin aure yanxu,2na hakan shi
ne ya dan kwantar mata da hankali. 2nda ya
dawo daga sallar asubah yaji ya samu
natsuwa kuma yana ganin mafi a'ala shi ne ya
amince da ba2n mahaifin nafsa domin yin
hakan shine xaya kara yi masa shamaki da
nfsa domin yanxun in da akwai wadda ya tsana
to kuwa bata wuce nafsa ba. Sun zanta da
kanin shi musa in da ya kara cusa masa
ikliman kuma sunyi cewa xai je gurinta don jin
bakinta.
Iklima duk saurin da takeyi sai da taso tayi
latti,ko kamun bata sha ba don ko karyawa
bata tsaya yi ba. Yanke tabi bata son tabi layin
su mahmud sai dai dogon lungun da ta shiga
daidai xata fita daga lungun mahmud da
abokanshi xasu shiga ta lungun suma.
Gabanta ne yay mugun faduwa domin ta gane
shi ckin frends ta ckin nikab tana ganin kowa
mutane ne basa gane ta,gefe ta rabe suka
shige lungun shima ya gane ta amma sai yayi
tamkar bai ganta ba,sai dai yayi gaba ya juyo
itama daidai lokacin ta juyo,da alma daga
motsa jiki suke in ta lura da kayan dake jikin su
da takalman su. Tana tasowa ko gda bata
shigo ba ta wuce islamiyyar su don bita da
takeyi saboda gasar kara2n su da xasuje ranar
sati manyan malamai ne suke taruwa suna
kara yi mata gyara. Sai 5 ta shigo gdan da
alamu har yanxun mahaifiyarsu bata dawo
ba,cikin damuwa ta shiga ta ajiye jakarta ta
soma aikin gdan tare da girki. Danlami ya shigo
da sallama ta mishi sannu da kasuwa sannan
yace mama bata dawo ba?iklima tace walh
bata dawo ba ina xaton ko dai baba baije
gurinta bane, danlami yaja kujera ya xauna
yana cewa walh sun je jiya dasu baba malam
idi abokinsa yace ya maida ta tace bata maidu
ba ita baxa ta dawo ba,tana gdan hajiya baba
kawarta nima daxun da xan tafi kasuwa na
biya tace min xata dawo ashe ba dawowa
xatay ba,iklima tace basa bata shawara ne yan
gdan da taje. Danlami yace xugata fa sukeyi ai
duk shegiyar yarinyar nan nafsa ce taja
mana,iklima tace Allah ya shiryeta yasa ta
kuma gane da wuri amma in munyi sallah muje
gurin mama muji ko xat yarda ta dawo
Danlami ya dubi mahaifinsu yace baba xanuje
gdansu mama inda maman take yace da
kkunyi hakuri domin maman ku tayi nisa bata
jin kira ni dai naje na sanar da ita na maida ita
tace min baxa ta dawo ba,iklima tace xamuje
mu gani yace to kuje kuji ni dama don ku ne da
kuka matsa da baxan damu da dawowarta
ba,har da aminu suka tafi suna fita shima ya
taso nafiu suka fito waje su dan sha iska. Suna
fitowa sai ga samari guda3 yayi musu sallama
suka amsa ya basu hannu suka gaisa mahmud
ne kamar ko yaushe ya make hannun shi,ya
gyara tsayuwa kunxo gurina ne ko?ya juya bari
in dakko tabarma, sulaiman abokin mahmud
yace aa baba mun xo ne mu gana da iklima
cikin jin dadi malam usman yace oho to ku dan
yi jiranta yanxunnan xata dawo sunje nan ba
nisa ita da yanuwanta,suka ce to,suka xauna
shi kuma ya tafi. Su kuwa su iklima suna xuwa
gdan hajiya baba kofar falon suka tsaya suna
ta sallama amma su haule sun kaure da suru2
suna cin food suna kallon fim tare da wasu
kawayensu irin su fati dillaliya da mairo uwar
adashi. Suna jiyo muryar mahaifiyar su tana
cewa niko ina sha'awar shiga wasan hausa
dinnan ina ma xan samu na shiga?uwar
adashe tace kin san Allah in har kina so ni ko
xan miki hanya,haule tace Allah xanyi, hajiya
baba tace kuma xaki karbu suka sheke da
dariya suka tafa. Tace ai Alhaji jamilu yana
xuwa gobe suka kaini gidan da ya sai min aka
gama bikin nafsa kawai kawata ki hada ni da
wanda xai kai ni fim din.
Iklima kunnuwanta basa son jin kalmar don
haka ta kuma dagewa tace "salamu alaikum"
lokacinne suka ji suka amsa ganin yaran sai ta
daure fuska,hajiya baba tace aaah yayana ne
sannunku ku shigi. Suka xauna suna kallon
mahaifiyar su kowanne da abinda yake
kimsawa ckin ransa kaji ne a gaban su da
kwalaban fanta. Iklima ta kara yarda
mahaifiyarsu bata damu dasu ba haka nan
sakin da baban su ya mata na gargadi bai
xamar mata darasi ba,ta katse mata 2nani da
cewa lafiya yayan baban su me kuka zo yi?
Danlami ya fara gaidasu sannan yace munji
shiru ne kince xaki dawo kuma baki dawo ba.
Iklima tace mama 2nda baba yace ya maida ki
a musulunce ke matarsa ce don Allah ki dawo
mama,aminu yace ni dai ko baki dawo ba kada
ki shiga fim,tace lah kuji mu da yaro dama 2ro
ku yayi ku labe mana?sukace a'a tace ke kuma
magana daya kice Allah yace annabi yace
musulunci yace to ban maidu ba inma 2ro ku
yayi ba yace xai rike yayansa ba nfsa ce yar
banxa ya bar ma duniya to ni xan rike ta ta
yata daya tamkar dubu don hausawa sunce da
taron yuyuyu gwara daya kwakwara.
Ni gobe war haka ma ina sabon gidana da mijin
nfsa ya sai min an gama gyaran shi yau gobe
xan tare in an gama xuba min kaya. Ckinku
waga ni uwarsa ce xai xauna dani yaxo wanda
kuma ya xabi xama a gidan jar kasa bulon
kasa babu ko fulasta ya xauna.
Nan yaran suka shga yi mata magiya, amma ta
ce kada wanda ya ishe ta fa,haka suka taho jiki
ba kwari,kowa xuciyarsa na kisima masa
yanda rayuwar gidansu xata koma,in suka yi
la'akari da itama iklima aure xatayi wa xai kula
da gidansu,musamman ta fannin girki.
Suna isowa kofar gdan iklima ta samu bakinta
suna hira kasa kasa har xata gota muktar yace
wannan ba iklima bace?ta isa gurinsu tayi
musu sallama ckin girmamawa da sanyin
murya suka amsa dukkansu,ta gaidasu ckin
ladabi sannan tayi shuru tana sauraransu.
Suleiman ne ya soma magana da cewa iklima
kin sanmu?ta daga nikabinta ta saka shi a
kanta kasancewar gurin da duhu baxasu iya
ganin fuskarta ba tace nasan yaya mahmud ne
kawai,sulaiman yace very good kuma nasan
kin san halin da ake ciki game da ke dashi ko?
ta sauke nunfashi sannan tace na sani. Yace
yauwa to yanxun mun xo muji naki tsarin su
wanene kawayanki saboda mu basu kudin
sha'aninku muna nufin musan shagalin da
xaku yi. Mukhtar yace saboda lokaci ya tafi
sosai,ta gyara tsaiwa sannan tace bani da
wani tsari sai na sunnar manxonmu (SAW) a
musulunce walima ce kawai muka sani in
mu2m yayi aure ko ya samu karuwa.
Don haka kada ku damu kanku kuyi walima
kawai domin ranar daurin auran da yamma
xamu tashi xuwa saudiya inda xamuyi gasar
kara2n alkur'ani ina neman addu'arku ta
numfasa. Sannan tace inna dawo xanyi tawa
walimar gaba 1 da fatan hakan ba xaya sosa
raku ba.
Sulaiman yace ai mu murna muke Allah kuma
ya taimaka,ba2n kawayanki babu kenan? Ta
ce wannan shine gaskiyar magana,suka ce
shikenan ba damuwa. Mahmud dai kanshi
yana duke kuma yana sauraron su.
Mahmud yace muje kawai ai duk abinda xance
kun riga da kun fada,ya mike iklima tace to
Allah ya bamu alkhairi nagode,ta nufi gda.
Mahmud yayi dan tsaki tare da cewa sam
yarinyar nan bata yi ba,mukhtar yace me ya
hanata yi?sulaiman yace in dai nutsuwa kake
so da hankali wallahi yarinyar nan ta wuce da
2naninka. Mahmud yace kun kasa gane
xabina,ina son mace yargayu mai kwalisa
wannan koyaushe a lullube,addini ma fa ya
bani damar naga irin matar da xan aura. Haka
dai abokanan suka tafi suna karfafa masa
gwiwa,yangidansu ma da su muktar sukace
gara ya fada ya shaida musu sai kowa ya
sshiga murna,kannanshi mata suka shiga
alfaharin yayansu xai auri wadda suke jin
kara2nta cikin waya. Shi kam da yayi xugum
ckin daki mamaki yake yanda abokanshi,dangi
nsa da kowa hatta mahaifinsa murna suke da
wannan canji,mahaifinsa ne ma da yaso yaki
yace duk a hakura dasu saida su Hajiya uwa
sukayi masa bayanin yarinyar sai ya amince
tare da murnar alkhairi.
***Ranar Alhamis dangin malam usman suka
iso daga jalingo maxa da mata bos 2,lokacin
da ya karanto ma kannansa abinda ya faru
bayan tafiyarsu sun sha mamaki,baba hamza
yace lallai nfsa ta cika yarkanta walh yaya ka
barta ne baka karya shegiya ka xubar tsakar
gida ka kuma daura mata auran in yaso tayi
jinyar can a gidan mijin.
Baba sale yace gara da ya barta duniya ce ta
ishi kowa riga da wando itama xata haifa
domin manzon Allah (SAW) yace ku yiwa
iyayanku biyayya yayanku xasuyi muku
biyayya. Kun ga yaya irin biyayyar da ya ma
magabatanmu amma yarsa tayi masa haka,to
ita yaya nata yayan xasu mata? Malam usman
yace xatayi nadama lokacin da bata da amfani
iklima kuwa ba xan daina alfahari da ita ba
suma suka ce Allah ya shi mata albarka.
Duk yanda ya kamata a ga gdan biki haka
gdan malam usman yake cike da mutane ana
ta girke girke ga makota da yan uwa da
abokan arxiki amarya kuwa tana ta shirin tafiya
gurin gasa,karfe 3 jirginsu xaya tashi karfe 1
aka daura aure.
Daurin auren ya samu halartar mutane da
dama ciki har da manyan malaman kasar
nan,abokanan ango sun xo tare da ango,bayan
an gama daurin aure sun xo ne don suy
sallama da amarya,danlami ne ya same ta ta
fito wanka tana sallah yace da kanwar baban
su in ta idar kice mata angon yaxo don suyi
sallama tace to baxayashigo ba mu ganshi
mamudan? Danlami yace inta fito ta shigo
muku dasu ya fita. Ta gama shafa mai dama
kwalliyar ta bata wuce mai da hoda ,anty iyami
matar baba hamza tace banda abinki amarya
yau dai kamata yayi ace kinyi yan shafe shafe
kina amarya,iklima tayi dan murmushin yake
sannan tace Anty iyami yau bani da lokaci ina
son in xama ckin shiri yan mintina ne suka rage
mu tafi,ta ciro mata shadda ckin akwatin auran
baxa wannan amarya,ta kalla tace kai gara dai
ku bani atamfa,suka bata atmfa yan Ghana
dinkin kuwa tamkar dama kayan ya xauna
mata tace sun saka hijabi ma kuwa? Anty iyami
ta dago tace kin ganshi nan guda1 ne sai
gyalalluka ne. Iklima ta kalli hijabin tace
wannan ya min karami sai dai ko in na xaman
gida,danlami ya sake yin sallama yace iklima ki
xo mana suna ta jira,ta saka hijabin ta sabo da
ta dinka don xuwagurin gasar ta daura nikabi
ta fita.
Lokacin da ta daga labulan buhun kofar
gidansu ta fito har yanxu akwai ragowar people
yan daurin aure,idanunta suka sauka kan
mahmud da abokansa kusan su 10,yana sanye
da farar shadda yar ciki da malun malun yayi
kyau da hularsa kube ta isa gurinsu ckin
natsuwa sannan tay musu sallama duk suka
amsa illa mahmud da fuskarsa ta nuna rashin
jin dadin ganinta ita kuwa tana kallonsu duka
ta ckin nikabinta,tace ina yinin ku?suka amsa
lafiya lau amarya. Ishak yace har yauma da
rufin face xa a xo mana?bata ce kome ba,
mukhtar yace sallama mukaxo yi,sulaiman
yace ya kamata ace da ango xa ayi tafiyar,
iklima ta gyara tsaiwa tace lokacin ne ya kure
domin daga gefena mu2m 1 xaya je da kanin
baban mu aka shirya tafiya. Sadi yace to mu
dai muna nan xamu kasa mu tsare a gaban tv
Allah sa ki xama zakara,tace amin nagode.
Sukay ta suru2 kafin daga bisani mukhtar ya
dubi mahmud ango kai har xuwa yanxu bamuji
ta bakinka ba ina ganin yanuwa mu basu guri
ko?sukace hakane,to amarya yanxu sai dai
muce Allah ya dawo daku fyn tace nagode
sukay gaba tamkar ya bisu don bai san me
xaya ce da amaryar tashi ba,abinda kawai ya
sani yarinyar tana da irma a idanunsa batay
kama da wadda xa a wulakanta ba saboda
ilminta,yace malama ana ta yin shirin tafiya
ko?tace in sha Allah nan da 30mins ko 1hr
xamu tafi,yace to Allah ya taimaka tace amin
na gode da adduarka,duk sukay shiru na dan
lokaci sannan yace xamu koma tace na xaci
sai kaga tashinmu?yace naso hakan nima sai
dai abokaina sun kira walima kuma sunyita ne
don ni bai dace ace bana gurin ba tace haka ne
to sai mun dawo,yace Allah ya tsare. Ta tafi ya
bita da kallo yanxu yarinyar nan matarsa ce sai
dai bai san wa ya aura ba saboda nikabi. Uku
daidai jirginsu iklima ya dauki hanya.
Nfsa bata da labarin auren iklima da masoyinta
don haka 2ni itama ta diro minna don shagalin
nata auren da Alhaji jamilu kai tsaye gdan da
Alhaji jamilun ya saima haule nan direban ya
sauketa da tata motar sbuwa dal ta kudi
kimanin 4mill
Kuma ckin yan kwanakin da tayi gdan Anty
hajara ta iya mota don dai ckin gari haka
saboda tana da karambani,kudi ne iyaka kudi
ya xube mata,akwa2na kuwashago mafi tsada
suka xaga a garin Abj ta darji akwa2nan da
takeso tare da kayan ciki,gwala gwalai kuwa
sai da tace mishi ya barsu haka don shi da
kanshi yay ta xabansu,cewa yayi ma don
lokaci yaxo a kure ne da dubai xasu da indiya
da china don kawai hado lefe. Haule kam da
kawayanta da wasu daga danginta sai murna
sukeyi da ganin kayan lefen duk da cewa ba
wani nashi bane ya kawo direban shi ne.
Kai ckin bkin baya ga abokinshi Alhaji kabiru
babu wanda sika gani kuma basu damu su
gani ba duk kawayanta shine ya saya musu
anko na shadda wanda aka hada da leshi
dinkin mutanan sanagal N20K haka ya dinga
jidar musu.
Ranar daurin auran kuwa 2n safe masu kidi
suka kafa tare da hana kunnuwan mutanan
layin sakat ita kuwa sai rawa suke tana canza
kalolin kaya,xuwa karfe 1 aka daura auran su a
wani masallaci karkashin waliccin kanin haule
kawu idi amma sunyi wa limamin masallacin
karyar cewa shi kanin mahaifinta ne. An daura
auran bisa sadaki N500K duk wanda ya halacci
daurin auran kuwa xaya baka labarin irin garar
da ya diba ga kyaututtukan kalandu jakukkuna
masu dauke da hoton ango da amarya duk
wanda ya kalla kuwa xakaji yana cewa kyau na
dukan kyau yayin da wasu ke ganin nfsa ta
gama morewa a duniya. Koda yake itama haka
take gani
A ranar asabar dinne dai da dare mahmud yana
zaune gaban mahaifin sa wanda yake masa
nasihar cewa ya rike kyautar da Allah ya bashi
da amana wato iklima sannan yace xaya kara
masa jari don gyara shagon sai shi kuma ya
nemi kudi don xuba kaya a ciki sai yace ai
maman su ma tace xata bashi daya filinta yayi
jari.
Alhji Ibrahim yace hakan baxai yiwu ba saboda
ba kai kadai ne dan da ta haifa ba kayi maneji
da wanda xan baka in naga shagon naci gaba
xan kara maka kudi amma yanxun kam kada
ka sake inki labarin ka kuma saaida mata fili.
Mahmud yace nima fa nace ta barshi itace ta
dage yace a'a xan ganta mahmud yace
shikenan nagode Alhaji, Alhaji Ibrahim yace
kada ka damu ni matsalata kaine babba in har
ka xama nagari nasan kannanka ma xasu
xama haka ka rika tunawa kaine ubansu
watarana.
Mahmud yace xan kiyaye insha Allah. Alhaji
yace to Allah yayi maka albarka yasa abokiyar
arxikin ka ce ina kara horonka da ka rike ta da
amana domin yarinyar itace xabin Allah a
gurinka. Mahmud yace insha Allah xaya kula
ya fita ya nufi gurin mahaifiyarsa da danginta
inda babansa ya bar musu ainihin sashen sa
har a gama biki.els BOOK
MABUDIN WAHALA 1***10
Bayan ya fito ne ya samu abokansa suna
jiranshi a bakin dakin sa na waje suka shiga
dakin suna hira,mukhtar ya kunna tv don son
yaga labarai sulaiman yace sai dai kaga
newsline yau asabar ka manta?kafin ya bashi
amsa idanunsu suka shagala da kallon dinner
din da ake nunawa live.
Shahararran dan siyasan nan ne Alhaji Jamilu
a ke nuna auransa da nfsa yace a'a har auran
nafsanka yaxo ne mahmud?dukkan su suka
tsura ma tv idanu daidai lokacin da suke rawa
anai musu ruwan naira kan mahmud ya sara.
Yace mukhtar kashe talbijin dinnan kada ka
min fami ba xan manta cin amanar da nafsa
tayi min ba kuma xan manta cin amanar da
nfsa tayi min ba kuma xan rubuta labarinta don
kawai ya xama darasi ga wadansu maxajan
masu xurfafa so irin na gaskiya da aka hore mu
da muyi so saisa saisa don in karasa abinda
kake so din sai kayi tawakkali.
Mukhtar ya kashe kowa yace kada ka damu,
Allah ya maka mafificin canji yace ni na karaya
nawa ganin duk halin mata daya ne. Sulaiman
yace Allah ya hana kudin goro akwai da yawa
nagari. Ni yanxun damuwata yanda xan xauna
da yarinyar da tsakanina da ita gaisuwa sai ko
kira min yayarki,abokanshi suka ce wannan
baxai xama matsala ba domin akwai wadanda
basu taba ganin juna ba sai a matsayin mata
da miji kuma sunyi xaman mu2nci da juna.
Haka sukayi ta bashi shawara tare da kwantar
masa da hankali.
Ita kuwa nfsa daidai wannan lokacin 2ni suna
Abja inda jirgin sama ya debe su,katafaran gda
ne mai dankaran kyau duk shige shigen
gdajenta na masu kudi bata gama xaga gidan
ba kuma ganin dare ta mishi kai hatta da
kawayenta sun rude haka danginta. Safna tace
kawata kin debo mai xafi,mama xee tace ai tayi
babbar sa'a mu kam gani nake maxajan mu
basu fi yanaikin ku ba,ita kuwa sai daga kai
tare da salo ga magungunan mata da take ta
dankara tana fadi yanda ya gigitata da kudin
shi haka nan itama take son gigita shi a daran
farkonsu.
Yato mata waya cewa su shirya xa a xo a
kwashe su xuwa dinner wadda ake nunata su
mahmud suka kalla,duk son kudin nafsa sai da
ta firgita da irin wadanda ake likawa domin
daloli ne ba ayi amfani da ko 1K ba ckin kudin
mu na kasa,sannan taron dinner din kusan duk
kusoshin kasar suna gurin inda ta kara yarda
tayi babban kamu kenan.
Sai dai dinner babu mata dayawa kamar yanda
ta xata sai maxa matasa da yawan su sunyi
irin shigar nan ta wizee wandon kuwa ass
down ana ganin wandunan su na ciki,an shi
ansha a gurin dinner an watsa kudi har kusan
3 na dare sai dai wasu sunyi tatul da giya inda
ranta ya dan sosu kenan har tayiwa angon
nata korafi da cewa darling me yasa kuka
shigo da giya gashi duk wasu sai maye suke
yi? Yace kada ki damu mu mun san yanayim
mutanan da muka tara ne wani in bata ba xaya
xoo ba. Koda suka koma gidan ta xata xai
nemeta a sashin shi saboda mutane basu tafi
ba amma taji shiru,kai har ta kirashi ckin waya
tace taxo?yace a'a ta tsaya gurin kawayanta
ba damuwa.
Bata so haka ba domin itama abubuwan da
tasha sun sata matsuwar su kasance da mijin
nata don haka bata damu ba lokacin da yan
rakiyar tata suka soma shirin tafiya bayan sun
gama karyawa da kaji da sauran kayan dadi da
xaki wani abin ma basu taba ci ba,sannan aka
xaga dasu cikin dankareren katafaran gidan
suka ganshi,ba kawayanta ba har ita kanta ta
amince cewa sunanta ya bita babban gida
babbar mota duk ba wanda bai rude ba,da
xasu tafi yayi musu alkhairi mai yawa tare da
basu direba ya kaisu har gida.
Iklima wadda ke ckin farincikin isarta kasa mai
tsarki don gudanar da gasar kara2 komai yana
tafya yanda ya kamata,tsawon sati1 suka
dauka suna gasar,kwarai da gaske iklima tayi
kokari don itace taxo ta biyu.
Sun samu kyaututtuka na kurani da litattafai
ga kudi duk da ba itace 1st ba amma ta
samu,bizarsu ta kwana10 ce don haka
kwanaki ukun da sukayi mata saura ta kashe
sune gurin yin ziyarori da ibada da adduoi.
Tasha mamaki yanda kasar su ke karrama
mahaddata kur'ani duk inda xata shiga da
masu tsaronta,ranar da xasu dawo kuwa ji tayi
tamkar kada ta baro kasar,kano suka sauka
inda sarkin musulmi suka tare su tare da
manyan malamai.
Gwamnatin kasar nan tayi mata tarba tare da
yin walima gareta,mahaifinta da mijinta da
wanta sun samu halatta aka bata kyautar
motadaga gwamnatin kasa sannan suka nufo
minna gdan mahaifinta tare da kyaututtuka har
da motarta,farinciki baya misaltuwa bata bata
lokaci ba tace da mahaifinta tana son ya sai
gida ne da kudadanta motar kuwa a samu
wurin ajiye mata kafin tay nazari,mahaifinta
yace shi kam yana son duk dangi da makota
suma su shaida don haka xaya basu nasa su
sa albarka mota kuwa taba mijinta. Tace a'a ya
raba in kudin basu kai na gda ba sai ya saida
motar a cika nafi so ka daina biyan
haya,kannan mahaifinta suka ce hakan
yayi.ranar ce kuma aka kai ta dakin mijinta
gdan mahaifinshi da ya bashi ciki da fao sai
bayi da kicin daga waje sannan da akwai yan
haya mu2m 2. Bayan yan kawota sun tafi
kasancewar bayan magrib ta fito tana kallon
falon kayan da mahaifinsu ya siyo ne domin
nfsa yarta kujeru ne guda 5 sai ledar tsakar
dakinta da labulayanta duk kalar ja,a talauce
ba a sarauce ba ta sani mahaifinta yayi kokari
ga kuma,ckin dakin baccin kuwa gado ne 6 by
6 yaji katifa da mudubi gami da durowoyin sa
sai yan kayan girkinta sune ma take ganin xata
karo don ta gansu babu yawa 2nda baban su
yace itama dole ta amshi wani abu ta rike in ta
amsa ta kara abubuwan da take so.
Gidan da xa a siya ma ya kafe kan cewa nata
ne da sunanta xa a siya saboda halin rayuwa.
Can kusan 10 sai taji sallamar su Mahmud da
abokanshi ta amsa da sauri tare da shigewa ta
sako hijabinta da nikab duk suka xauna kan
kujeru wasu kuma a kasa,sulaiman ya dubi
ango yace kira mana amarya mu gaisa mu sayi
baki,mahmud wanda ke sanye da shadda light
blue yayi kyau sosai ya sake hade fuska shi fa
sam har yau iklima bata kwanta mishi a rai
ba,mukhtar yace ta ango xo mana mu gaisa
iklima ta fito hannuwanta rike da plate guda2
shakare da cin cin da alkali ta aje musu
sannan tace ina yininku?suka amsa Basiru
yace to amrya yau dai ai a cire murfin guskar
mu gaisa aga juna ko?tace kada ku damu a
musulunce hakan shine yafi alkhairi a tsakanin
mu,mahmud ya sake jin haushin abinda tace
dama fitowarta da nikabin ya dada shakar
dashi,ta kawo musu ruwa suka mata murnar
dawowa lafiya duk da cewa bata zo ta daya ba
sun jinjina mata,tace nagode Allah ya saka
muku da khairan,ta koma ciki sun kusan minti
30 suna hirarsu ta abokai irin da an rako aboki
dinnan,wannan yace masa ka dage gobe mu
samu yan2,sai mai cewa banda zalama duk
dai bai tanka su ba kalma1 ya furta inda yace
ina ma ace nfsa ce yau da babu wanda xaya
kaini farin ciki. Sulaiman ya dube shi da sauri
sannan ya kalli kofar uwar dakan ya sani cewa
iklima taji don haka ya mike tare da cewa
abokanaina ku tashi muje suma suka mike duk
basu ji dadin jalmar shi ba ya biyo su don yin
rakiya nan ko sukayi

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment