Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in ta dafa ma kanta haka
zata tara su,in tazo wankewa tayi ta mita wai
bari ya dawo ya nemo mata yar aiki,ita ba za
ta iya yin wahala ba.watarana ta mishi waya
wai ita fa tana son zuwa saloon ba ta da
kudi,sai ya ce ta amsa gurin ikilima.A haukanta
sai ta za ci kila mai kudin shi ne a gurinta,don
haka da taje wai ikilima ta bata dubu daya in ji
beby.Ikilima tayi shiru,don daga ita sai dari
takwas,sai ta tuna da kudin musa,ta shiga ciki
can karshen dakin ta kira shi,suka gaisa ta
ce,musa zan iya aron kudinka?ya ce, eee.ki
dauka ba yanzu zanyi amfani da su ba.ta ciro
dubun tabata.Ashura ta amshe cike da isa,ta
tafi tana cewa,lalle wannan dan raini wayon
wato matarshi ya ba wa ajiyar kudi ya ce min
ba shi da su?Tun daga ranan kullum tace dari
biyar,ban dari biyu.ikilima bata taba cewa babu
ba, zata dauka cikin kudin musa ta bata sai de
tana rubutawa da lokaci da rana,da kuma
nawa ta amsa.Hudu saura ya kira ikilima wai
ya fasa zuwa,ta ce, too tasan zolayarshi ce da
ya saba yi.Ashura kuwa da ya ce haka sai a ja
tsaki ta ce,ina kaga dama ka daka dawowa ta
kashe wayar ta mike ta shiga kichin inda
ikilima ke ta hada hadar kammala komai kafin
ya shigo,don tunda ta ji ya ce haka ya kusa
shigowa garin kenan.
Ashura na mitar kada ka dawo din mana,ni dai
kayana na sani wallahi wanda aka kwasar mini
da akwatina in ko ba a kawo mini ba za,ayi
rigima.ta dau kofo tayi gidan sakina.Ikilima ta
ce a ranta,yau za ta ba shi kayansa,don haka
taki amfani da su.ta gama komai tayi wanka
ita da yaranta ta wadata gida da turaren
kamshi.hudu da kwata ya shigo suna daki ya
kwankwasa ta ce khalil abbanku.da gudu suka
tafi ta dauki ummita ya daga khalil ya hada su
ya rungume suna dariya.Ta zare jikinta ta
ce,sannu da zuwa.ya mika mata jaka ta ce, ba
nan ne masaukinka ka ba, ka manta ne? ya
nufi dakin ashura,khalil ya bishi.kofar ya ji a
kulle,ya ce ina take?ikilima ta ce, yanzu ta
shiga makota kira wayarta.nan take ya daure
fuska ya ciro waya ya kira ta ke ina ki ka je na
dawo ba kya nan?ta ce,too ba ka ce ka fasa
ba?tsaki yaja ya kashe wayar,ikilima ta koma
cikin dakinta .Ahura ta shigo ta bude daki suka
shiga ciki.Ya ajiye jakarshi ya zauna,itama ta
zauna kusa dashi tare da cewa,kasha hanya
shi ne ka ce ka fasa?ya ce, Ashura don na ce
na fasa shi ne ki ka tafi yawo,ina ki ka je?ta ce
nan makota na shiga gidan sakina.Ya soma
cire takalminsa,ta faki idonsa ta harari khalil da
sauri yayi waje,mahmood yana ta cewa zo
mana babana,tuni ya kai dakin mamanshi,ita
ko sai ce ruwan khalil ya kasa sabawa da ni.ya
dubi ta baki ja shi a jiki ba ne ko?yaron nan da
saurin sabo.ta ce um,ta canza zancen ban
gabka da kayana ba.ya dube ta.ko ruwa baki
bani ba kina min zancen kaya?ta tashi ta nufi
kichin ta dauko pure water leda daya ta zo ta
miko mishi.takaici ya cika shi,ya mike bayan ya
cire takalmin ya fita zuwa dakin ikilima yayi
sallama,suka amsa tana zaune lana koya
musu alifun.
Ya zauna kan kujera,yunwa nake ji ita waccan
ko ruwa don wulakanci bata bani ba ta soma
tambayana kayanta?ikilima bata tanka ba, ta
nufikichin.ta shirya masa komai gabansa nan
ya manta da bacin rai ya shiga diban girki.suna
hira.ya koshi dam,sauran wanka za,ayi mini
taimako ne.ta ce,ai dakin amarya ka ke,ka je ta
maka.ya yi dan tsaki taje bayan durowarta ta
janyoakwati daya aka dinka leshin sai shadda
wadda aka yi wa aiki ba a hada ba,ta dire
gabanshi.ga kayanta ka bata,dama ni ba zan
saka ba.ya hade rai ba na ce ki dauka
ba,yaushe kika fara gardama ? ta zauna kusa
dashe,ban isa na maka gardama ba baban
khalil,don Allah kabata kayanta nina ci
girma.Ashura ta turo kofa bako sallama,ta
dube su amma de ba,a mini sati daya na da
musulunci ya ba ni bako?aka zo akayi shiru a
cikin daki,ke kina nuna Allah a fili daman ranki
ba haka bane?Zai yi magana ikilima tasa tafin
hannu ta rufe mashi baki,don ta lura ba alkhari
zai fada ba.Ashura ta hango akwatinta,ta
shigo da sauri.haba ashe ga inda aka kawo
mini kayana,lallema mahamood kun cika
isassu kai da matarka,baki dama ku ka had?ta
ja kayanta tana cewa,Allah yakama ku.ikilima
ta hana shi magana,sai kallonta suke yi har ta
fita.ikilima ta ce,shi kenan daman nafi son ta
dauki abinta.
Ya ce, ita ta siya to?ta ce, da sunnanta amma
ka siya.ta ce gaba ta fika gaskiya, sannan don
Allah koda kaje dakinta kada ka tado da
zancen pls,to wai ke so ki ke in zuba mata ido?
Dubi fa yanda ta yi mana ,ita ce ya dace ta
bani abinci amma bata yi hakan ba,nazo nan
kuma ta biyo ni da rashin kunya.Ikilima ta ce,
to kayi hakuri,in dai na isa in baka shawara in
kaje dakin ta kada ka tada komai kuma laifinka
ne ya zaka ce ka fasa zuwa ita kuma bata son
tsokanarmu ka ke yi ba,nasan da zata shirya
maka wani abu. ya ce, ba wani, kina kare ta ne
kawai.wannan ya nuna min bata damu da ni
ba, ke bana manta ranar farko haka nace miki
na fasa zuwa san da na zo na samu komai is
ready.ikilima ta ce, too mubar zancen kaima
don Allah ya wuce.ya ce, shi kenan,yanzu bari
naje nayi wanka da bayan isha,i sai na zo amin
lissafin bashinna in biya shi ko? ta ce, too. ya
ce,Allah ya miki albarka.ta ce amin.Da ya shigo
dakin ashura ta baje kayan kan gado ya ce,ina
son yin wanka ta ce,to ka shiga mana.ya ce,
ba za,a taimaka a min ba?ta ce,, me yasa ba
ayo maka a can inda aka baka abinci ba?ya
ce,na ce amin an ki ne.Haushi ya kama ta shi
ne ni ga marainiyar wayonku kaje ka kwanta da
ita ni kuma na zo na wanke maka kazantar ko?
To wallahi bazan yi ba.yayi murmushi,shi
kenan.ni bari naje na wanke da kaina.ta taso
da gudu ba a bayi naba.ya shiga tabishi ya
kunna ruwa yana tarawa cikin baho wanka ta
tsaya tana cewa,mallam zo ka fita.
Ya jayo ta ya tura cikin baho shima ya
shiga,nan ya mantar da ita komai.tana shafa,i
da wuturi ya shigo,ya zauna ta idar tana mishi
sannu cikin fara,a,ya ce a fada min bashina, ta
mika mishi littafin da ta rubuta,ta ce dubu biyar
da dari uku ashura ta karba,ya ce me ta yi da
su?saloon tace zata nace ki bata dari biyar ta
ce sai dubu na ce ta karba.Ikilima ta ce, too ni
dai gashi nan.ya mike mai kikayi da dubu
biya,in ji wa?ya ce, gurin ikilima. tace, bai kai
ba,sau nawa ni na amshi kudi?too in ma na
amsa meye dubu biyar a tunanina nafi karfin
dubu dari ma a gurinka bare dubu biyar.bana
harkar talauci wallahi,ai kasan gidanmu.Ya ce,
to ban ce miki kuma ni mai kudi ba ne koo?kin
kuma san gurin aiki na bare kice na miki
karya,don haka bana son irin wannan,shi yasa
kake bata ajiyar kudinka wato ni in ka bani zan
kashe ko?Ya ce, ehh. ya fita. ikilima ta ce haba
baban khalil,mainene zaka bita kuma har daki?
baice komai ba ya dubi takardan ya ce,to ni
kuma da zan tafi na amshi dubu uku,ke kuma
nawa kika kashe?ta ce, wannan dai zaka
bada,wanda ta amsa,wanda na kashe ko na
mota bar su kawai nawa ne. bai ce kala ba, ya
saka hannu aljihun ya ciro yan dari
bibbiyudauri daya ya ajiye a gabanta.ki cire
dubu biyar dinta kema ki cire adadin da ta
dauka,sannan sauran ki cire wanda na ranta da
wanda ki ka kashe.
Tayi tayi ya bar shi ya ki, daga karshe ma ya
tashi ya fita ma tare da cewa sai da safe,haka
yaye kwana biyun shi ba wani jin dadi,tun
kafun aje ko ina ya soma gane kuren shi na
son mace mai tsananin wayewa.da za ya koma
ya ba su dubu bibbiyu tunda komai yara da
kudin mota ikilima kuma dubu uku.nan fa ta ce
bata yarda ba ya zai bata dubu biyar ita dubu
biyu?haka ya tafi da damuwa.Nafisa tana tsifar
kai ikilima tayi sallama ,hama tana zaune tana
dinkin hula,haula tana bakaican masara,duk
suka amsa itama ta sauke ummita ta
zauna.nafisa ta ce, uwargida sai yau?ikilima ta
ce,ina fushi da yen gidan nan baba hama,ba
wanda ya zo bikin mijina har ke anti
nafisa.hama ta ce mai zai kawo mu cikin yara?
ikilima ta kalli nafisa kuma mamarki tayi tayi ta
ce ita ba zata ba.ikilima ta kalli nafida,to
saboda mai?nafisa ta ce,haka nan.ke ba ki ma
da hankali,in ni ce mahamood ya isa yayi aure?
Ikilima ta ce, to ai lokaci ne,ba isa ba ce.haula
ta ce,kuna de zaman lafiya ko?naga duk kinyi
kashin wuya,ko har an soma gasa ki ne?ta ce
lafiya muke,ai ya samo yariyar kirki.nafisa ta
ce, kada dai kiyi saurin yabon dan kuturu,sai ya
girma da yatsu.
kilima ta ce, mu dai muna lafiya,kuma baban
khalil yana da adalci sosai.nafisa ta tabe baki
tana cewa,kar dai ki cika baki,hama ta ce to ai
alamar karfi tana ga mai kiba.mahamood
yasan abinda yake yi.haula ta ce Allah yasa
kada ya chanza yanzu.ikilima ta ce
amin.nafisa kuwa shiru tayi,don bata son a
cika tadin mahmood,yanzu a fama mata ciwon
sonshi.Ta dan jima sannan ta yi musu ihsani
ta tafi,nafisa ta rakata ta hau machin suka
rabu tana yi ma nafisa mitar to ta zo taga
gidanta,ta ce zata zo.wannan satin ma dai
haka ya yi shi ya kuma tafida damuwa,yana
lura da irin abunda ashura ke yiwa
yayanshi,yana lura da cewa ikilima ke komai
na gidan,hatta abinci.ita da ya mata magana
kai tsaye ta ce,ba zata iya ba sai dai ya dauko
mai aiki tunda yaga gidansu,kuma yasan bata
gaji wahala ba.shi kuma ya ce ba zai dauko
ba.tun kafun ya tafi yake ma ikilima in ya dawo
gurinta zai sauka,ita kuma ta ce a a sauran
kwana daya ya gama yiwa amarya
satinta,sannan ma ita ai ta kara mishi
kwanakin.ya ce shi fa baya so.too ranan
alhamis ma kiranta ya yi da dare ya ce gobe
ina hanya ina son tarba sosai fa.ta ce,too ka
gaya mata ko sako nein fada mata?ya ce wai
wa?ta ce amarya.ya ce ke ni fa na gaji gaskiya
ki tambaye malamanku ban amince da wannan
fatawar ba, ace bana gari sai sati zuwa sati
biyu nake zuwa amma ko yaushe dakin amarya
zan sauka har sai nayi kwana bakwai?vels BOOK
MABUDIN WAHALA 3**9
Ta ce, ehh,haka ne kaima ka tambaya.to wai
kai menene matsalar kai da ke da sabon inbox?
yaja tsaki mata da yawa suna zaton kwanciya
da su ne kawai abin da muke bukata?ikilima ta
ce,to da mai kuke bukata bayan wannan?ya
ce,irin kulawar da kike bani.sai da kulawa
sannan sha,awa take zuwa.too yanzu kai
menene damuwar ka?ta tambaye shi?bana
samu kulawa gurin ashura ,sai ta kwanciya.ta
ce,too zan baka sauran kulawar,ka ci gaba da
kwana da ita har zuwa lokacin da zaka ji a
ranka cewa ikilima ta bani gudumawa.ya ce, na
gode.kafin ya iso tayi duk shirin da ya dace ta
gyara gida.ta samu ashuracikin dakinta,zaune
take tsakiyar gadonta wanda ke hargitse da
kayan da ta cire,da kuma kayan shafa kuma ta
ce gurinki na zo.ashura na ci gaba da yin 2go
dinta ta na cewa ina jinki.ikilima ta ce,shawara
zan baki akanmaigidanmu,kin san shi namiji
kullum tamkar yaro yake,dan son kula ne.Ta
hada rai tare da daga mata hannu,shi ne ya ce
miki bana kula dashi?ikilima ta ce, a a nasan
kina yi,nufina ki kara.ina son ne na fada miki
abubuwan da yake so da wandada ba ya
so,don ki kiyaye.Ta aje wayar
hanunnuta,malama ban son salo kece za ki
gaya mini abinda yake so ko shi ne zai fada
min?ikilima ta ce,da za ki daure ki saurareni da
kin kar..........ashura ta katse ta don Allah fita
malama,bazan saurare kiba.kada kiga kina da
yara ki raina ni,ba kin girmai ni bane nima da
ace ban tsaya karatu ba da nayi uku ma ba
biyu ba.sannan kiyi kadan ki hada kanki dani a
wayewa.ikilima ta ce,kada kiyi girman kai,yana
daya daga cikin tushen zunubi ki
saurareni.tsaki ashura ta ja.ke na ce ki fita
,bana son shisshigi don Allah.ikilima tace shike
nan tafita.
Ta ciji yatsa,lalle wannan na lura so take ta
raina min wayo,itace ma zata koya mini zama
da miji?jahila irin ta,a gurin wadda ko
secondery bata gama ba. ita kuwa ikilima ta
zauna a dakinta tana jin zafin yanda ashura ta
ki sauraronta.lokacin da ya iso ya samu
ashura zaune inda ikilima ta barta tana aikin
2gota ajiye wayae tana mishi sannu ,ya dubi
koina na dakin a hargitse.ya ajiye jakarshi ya
fita.Dakin ikilima ya shiga,suka mishi oyoyo ita
da yara.ya shiga wanka,kafin ya fiti ta tanadar
mishi komai da tasan zaya yi amfani dashi.ta
taimaka mishi gurin shafa mai da kaya,sannan
ta shirya mishi abinci suna ci suna hira.farin
ciki a ranshi kamar me,sai da suka gama ya
ce,madam albishirinki?ta ce, goro.ya ce,bana
son goro,sai dai in za ki min iri jus din shinkafa
da kika min wacan satin.ta ce zan maka.ya
ce,an maido ni abuja wannan satin.tace kai
amma nayi murna.ya ciri kudi daga aljihunshi
kayan dakinki da kayan sawan wanne zan fara
sai miki?kin san alkawari ne bashi ne a
kaina.ta ce, a a ni dai ka bari su nan gaba ya
ce, a a yanzu zan biya.ta ce,tooduk wanda
kafara don ta sanshiin zata shekara rokonshi
ba zai yarda ba,don ta ce ya abr shi ba zai
bashi ba.ya ce,shi kenan,gobe za muje
kasuwa.ta ce Allah ya kai mu.da ya koma
dakin amarya ta hada rai har da kuka.ya ce ba
kya iya kula da ni dole naje in da za,a kula
dani.ta ce,tunda nazo gidan nan ka taba
nemana naki?
Ya ce, ba a nan matsalar take ba.kada ki dauki
damuwata kawai na kwanta da ke ne a a
,wannan ya yakan fita kaina amma ba
kulawa.ki dubi yanda ikilima ke tatalina,ko ta
fanni abinci ita ke min wanka, ke ni fa ban san
yanda ake cie takalmi ba sai da na fara zuwa
kaduna.Amma ke ko yaushe kina nade a
gado,ko kina makota.ta ce,daman ina so in
fada maka, ka samo min yar aiki wahala bazan
iya duk wannan ba.yaya ma batun aiki na?ya
ce,yana nan,hajjiya kuma ta mini
magana.Akwa fin bankaina ga kila litinin su
neme ki.amma gaskiya ki chanza hali.Ta
ce,too da suka zo kwanciya,ya ce, ta gyara
shimfidar gadon sai ta ce a a suje dakin shi
tunda ta zo gidan ba su taba kwana ciki ba.ya
ce, a a sai randa ya zuba kayan shi tukunna
nata kwashe wa za,ayi.ta kuma jin
haushi.Washegar i kuwa suka gardama da
ikilima, ya ce ba ya son karin tun da yayi satin
shi kenan,ita kuma ta ce a a,har yayi fushi ya
fita kofar gidan.ta ciro wayarta ta yi ta kiran shi
yana kofar gida amma ya ki daga wayar,tunda
ya lura ita ce.Ta rubuta mishi text tana bashi
hakuri,sannan ya dawo.ta tsuguna gabanshi
tana cewa,ya yafe mata bata yi ba ne don ta
bata mishi rai,ya ce ya sani.kuma shi ya yafe
mata tun kafun ta roke shi.can nisan dare tana
bacci shi kuma tunani yake,ikilima ce yake
gamsuwa da ita,ashura kam tun da yake
kwanciya da ita kara mishi kwadayi take,ko zai
kwanta sau uku da ita cikin dare baya jin
nutsuwa,ko haka mata suke?kasa daurewa
yayi.Da safe suna kari ya chanza maganar shi
zuwa turanci don kada khalil su ji,ya ce wai
mata daban daban ne?Ikilima ta ce mai yafaru?
ya ce,baya gajiya da ashura,don bai samun
nutsuwa ita kuma yau ya samu nutsuwa da
ita.amma bai yawan kwadayinta.
Da sauri ta rufe mishi baki,ta ce,ba kyua ga
baban khalil,ba kyua ka tona sirrin matarka.ya
ce, too ai ba wani gurin naje na fada ba,kema
don naga mun zama jini da hanta ne.ta ce, duk
da haka ba kyua.shi yasa ake cewa ku ke hada
gidanku a yi ta rigima.nata kowacce da
kalarta,sirrinka ne ka bar ma cikinka.ya ce, shi
kenan.sun je kasuwa ya darzo mata atamfofi
da lesuka da shadda,har da yara,ya ce, sauran
gyaran daki.An maido shi abuja,matsala daya
ikilima ke fuskanta yanzu,ya fi son kwanciya da
ashura kuma wani lokacin yana nuna mata
hakan karara.Da farko har zata dau fushi sai
kuma taga ya dace ta nemi shawara.Tuni har
ashura ta samu aiki kuma tasa shi ya samo
musu mai aiki don itama yanzu bata
zama.haka nan yana jin maganarta,jininsu ya
hadu da luba,luba na kawo mata shawara,don
haka itama sai ta nemi luba shawara.Don
yanzu sai yazo dakinta ya bar dakinta bai nuna
sha,awarta ba.luba ta ce,duk yanda akaye
tana amfani da kayan mata.ikilima ta ce,mai ke
nan?nan fa luba ta rike baki tana mamaki
dama akwa matan da basu san gyaran jiki ba?
Ikilima ta ce, gani.luba tace, tafdi!to ke ko
lokacin bikinki ba a miki ba ne?ta ce,wallahi ni
bikina da ba shiri?koda shirin ma wa zai mini?
nasan ana fada.Da an ci gaba ma wata rana
sai ya nemi ki bar gidan.luba ta ce zo muje ki
gani.
Ta bude wata durowa ta soma fito da rabobo
tana mata bayaninsu.ikilima ta ce ba sa
cutarwa?kin san da addinmu bai yarda mu sha
abin da zai cutar damu ba.Luba tace ni nake
hada kaya na da kaina,duk abubuwan mu ne fa
su aya su dabino,su cukui su ayu,furen zogale
da sauransu.Ta kuma janta gaban wani fridge
duk kayan itatuwa ne dangin kankana,lemon
zaki,rake,da sauransu.ta ce amma zo mu fara
tanan.suka shiga bed room ta janyo galan ta
ciko ta tsumi,sha wannan.ta amsa ta
shanye.ta ce, ke luba,na tuna da dandanon
abin nan,mamanshi ta taba bani lokacin da
muka je ina amarya.luba tayi dariya ta ce
shanye duka.ko yaushe zaki dinga zuwa kina
sha kafin ya dawo.ta ce,wannan satin guri
ashura yake ma.luba tace,za mu samu damar
yin aikinmu da kyua kenan.cikin satin ikilina ta
nace ma gidan luba,har ta shida mata luba
kayan da ya siyo mata.Luba ta ce,mijinki na
kula wayayye ne,yana son gayu shi ne dalilin
shi na auro wannan kodaddiyar,ki kawo na ba
telana ya fito mini da ke sannan dole na hada
miki sabulun don gyaran jiki kuma mu shiga
kasuwa a siyo mai.ikilima ta ce,ba na son
bilicin fa.luba ta ce to nu dubi fatata,nima
bilincin din nake yi?gyaran fata kawai,ke har fa
kananna kaya zamu siyo.ikilima ta ce kai
luba,sai na tambayo malamai na sun tabbatar
min da cewa ba haramun.Ta ko tambaye
malam kabir ya tabbatar mata cewa shi ne ma
tsari,tayiduk kwalliyar da take sodon ta birge
mijinta,ta canza hallitarta daga baka zuwa
fara,shi ne aibu.amma don ta shafa wanda
zata yi laushi ko tayi kyua ba matsala.Ta ce, to
kaya fa?mallam ya ce duk nau,i kayan da kike
so ko mijinki ke so kya iya sawa,in dai gidanku
ku kadai ne.Nan fa ikilima ta kwaso dinkunanta
ta kawo ma luba.waya tayi aka kawo mata mai
dinki har gida don su zabi wanda zai dace da
ikilima,duk da ba gurin ikilima yake ba sai da
ya kasa daure kyan da tayi.Ranar ta saka daya
daga cikin lasunan da ya siyo mata,an dinka
shi riga da siket tamkar a jikinta aka dinka
su.ya ce,kanwata kin yi kyua,ke ce kuwa?
Kodai ummita ta samu kanine?tace a'a bana
sallah ma ni yanzun,yace waya miki dinkin nan
gaskiya kinyi kyau,tace to na gode,telan luba
ne yace gara da bai miki riga da zani ba. Kafin
wani satin ta kara tsumuwa tare da gogewa da
darussan da luba ke koya mata ga girki iri-iri
ita kam bata ce da luba kome sai godiya.
Ranar da xai dawo bayan kitso har da lalle luba
tasa a xuba mata sai kace amarya tayi masa
girki da kalolin jiice ta gyara gidan ta wadata
shi da kamshi. Lokacin da ta tabbatar ya kusa
isowa ta shirya cikin wani riga da wando yan
kanti da lubar ta amshi kudi ta siyo mata su
kala kala dama musa yaxo ya tafi da khalil,ta
kwanta kan kujera tana kallon tashar ikra'a ya
turo kofa....
Sai ta samu kanta da jin kunyar mikewa dan
bata saba ba. Shi kuwa sakin jaka yayi yana
kallonta,yace come on taso kizo na ganki
kanwata ce kuwa?ta mike yace wow dama
haka kike shine kike boye min hakkina?ta rufe
face. Rigar da wandon sun bi jikinta dam sun
fitar da surarta ya mannata jikin shi yana
shakar kamshinta,ta zame tare da cewa ina
zuwa. Ya zauna idanunshi dai suna kanta ta
zura hijabi yace ya haka kuma?tace kicin zanje
ina zuwa ta shirya kome a gabanshi yace don
Allah cire hijabin nan. Ta cire yace ina kika sai
kayan nan?tace gidan luba,yace da wasu
kalolon in sai miki dan duk lokacin da zanzo su
nake bukata ki saka min. Tace sai dai ka sai
mana mu 2 yace keda wa?tace da amarya.
Yace ai kece amaryar dubi lallen nan naki duk
gidan luban kika yi shi?tace eh,yace kai kin
dace da makociya Allah yayi mata sakayya ta
alkhairi,nayi murna da abotar ku,tayi dariya.
Kafin ya dawo sallah tayi sabon wanka da
sabon ado na kayan bacci ,masu shegen kyau
kalar jan ra'ayi yace kai yau dai kanwata ba
sauki duk kin rudani. Ya dauki Ummita dake
bacci kan gadon ya gyara mata kwanciya kan
kujera tare da cewa gobe kayankii xanje in siyo
wadannan a kai su dakin yara su fara kwana
can. Tace ya ka dauke min yarinya?yace
sakona na yau bashi da sauki bata kara
magana ba. Lallai shi da ita duk sunga canji.
Ya rasa inda zai sata yace tasha wani abu ne?
tace a'a menene?yace akan kome yaga canji
tace ita dama haka takenuna misi tayi shine
dai ya shiga rudu. Har da safe yaki barinta
sukuni,tana kicin shima yana manne da
ita,ranar ya hana ta xuwa islamiyya wai shi dai
ta zauna gida yayi ta kallonta. Tace baban
khalil nice fa,baka sanni bane?yace iklima kin
canja inda haka kike yi min baxanji sha'awar
kara aure ba. Tace a'a dole kayi auren so donni
auran mu kusan na dole ne xance ko na
biyayya don haka dama ni ina sa ran xaka iya
yin aure duk lokacin da kaga wadda kake so.
Tana xaune gaban madubi take maganar shi
kuma yana bakin gado,zuru yayi yana kallon ta
ya hade fuska, iklima don Allah fada min me
xanyi ki yarda ina sonki?wlh ina sonki sai daga
baya na gane ke nake so ba Nfsa ba. Ita Nfsa
sona kawai take ni ina sonki don ko lokacin
kullum dake nake bata misali ince ta dinga koyi
dake. Iklima tace ba ita ba, Ashura ba sonta
kake ba? Yace sonta nike tace to nufina kenan
so daya tak yake,yace to ke nake mashi tayi
dan murmushi ban yarda nasan dai kana
daraja ni. Yace wlh sonki nake kece ma nanaga
tamkar ba kya sona. Ta dube shi me yasa kace
haka?
Yace dubi fa aure nayi amma ko a jikinki tace
ka jika to don ina sonka xakayi aure sai nayi ta
hauka ko me?abbinda na sani ina sonka so na
hakika kuma ina tayaka son abinda kake so
matsawar bai kauce shari'a ba. Yace nima ina
sonki ta marairaice ina son kullum da safe kace
kana sona ya iso gurinta tare da dago kanta in
na miki hakan zaki gamsu ina sonki?ta lumshe
ido sannan ta daga kai alamun eh. Yace to xan
fara daga yanzun,iklima ta ware idanunta
manya tana kallon shi cikin idon shi,ina sonki
ya subaci kuncinta sannan ya rungume ta. Shi
da musa suka shiga kasuwa ya xabo mata
gado da kujeru ya siyo tafkeken TV ya saka
musu a babban falo. Nan fa ashura tace sam
bata yarda ba an cuce ta,ya xa ace ya canza
mata kome?yace alkawari ya cika amma sam
taki yarda har ya tafi suna tsiya. Haka suka
cigaba da zama iklima tana koyan abubuwa a
gurin luba,dabarun jan ra'ayin miji cikin sa'a ko
yaushe ya dan samu dama xai kirata a waya
yana fada mata I Love You,in ko yazo a ranar
girkinta yana nuna mata so tamkar ya cinyeta.
Ita kuwa duk abinda ta san xaya birgeshi
yanzun shi ne aikinta haka kuma kara2nsu ya
dau xafi dole ta bar koyarwa dan yanxu lamura
sun mata yawa.K
MABUDIN WAHALA 3**10
Cikin haka Ashura ta samu ciki nan fa suka
soma tsiya tace sai ta cire yace bai yarda ba.
Tsiya tayi tsiya har sai da ya 2ra ta gdansu
hajiyanta ta goyi bayanta da cewa ciki xai
hanata aikinta kuma yasan aikin yanda yake
don haka dole su cire ciki shi dai yace bai
yarda ba. Kawayenta suka kara xuga ta da
cewa kada ta yarda ta haihu yanxun taje ta
tsufa a banxa ta bari ta ci xamaninta,taje ta
cire cikin yace xai sake ta iklima tayi ta rokon
shi a karshe taje ta hada shi da su Hajiya Uwa,
Baban shi naji yace kul ya fara 2nda wayayya
yake so gata nan,dole ya maido da ita suka
cigaba da xama haka.
***

Nafisa gurin shan magani suka hadu da wani
Mustapha irin samarin nan masu leke leke yaje
ya jangwalo ciwon suka daidaita kansu nan ya
2ro mahaifanshi aka sa lokaci. Likitoci sun
basu shawarwarin da suka dace har xuwa
lokacin da xasu haihu kuma sunce xasu iya
samun yara marasa ciwon in dai sunbi
dokokin,mustapha iyayan shi sunji dadi. Baban
shi dan kasuwa ne a babbar kasuwar Minna
shi ma nan yake taba yan harkokin shi
mahaifin ya basu gida dan madaidaici aka
gyara shi in anyi biki su xauna. Mahmood yayi
murna lokacin da iklima ta sanar dashi yace
Allah yasa ina gari xa'ayi bikin domin bankin
mu sun 2ra ni lagos tare da karin girma. Lallai
mahmood likafa tayi gaba don kuwa 2n da ya
koma lagos suka warke sai dai baya xuwa
kowanne sati duk lokacin da ya ya samu dama
xaixo in kwana2 ne kowa dai dai in kwana
daya ne kuma sai ya kwana gurin daya yace in
ya dawo xai sauka gurin daya. Yaana son
tafiya da iklima kara2nta Ashura kuma aiki,da
kaga mahmud xaka san lallai ya samu sukuni.
Yayi yar kiba da dan tunbi fatar nan shar ta
goge ya sai mota ya sa Musa ya koya ma
Iklima saboda khalil ya shiga makaranta ga
makarantar ta. Nan ma Ashura ta tada balli
itama yace ya koya mata kafin wani lokaci sun
iya. Amma dan gudun rigima ya dauki driver
yace ya dinga kaisu.
Anyi bikin su Nfsa mahmood baya gari amma
ya 2ro da kudi masu dama iklima ta sai mata
kayan daki kuma duk zirga zirgar da akayi
iklima ce ke dawaiyniya da motarsu. Hakan ya
kona ran Ashura take ganin kamar gadara
iklima keyi da mota. Ita ko ganin sati da lahdi
ne Ashura bata da aiki shi yasa bata dawo da
motar gida ba,take barin ta gidan Mahaifin
shi,an tashi biki lafiya. Iklima tana kwance a
dakin shi dan 2ni yasa Ashura ta kwashe
kayanta tasa a dakin yara maxa dake kusa da
dakinta sai tayi fushi ta saida su ya shirya
dakin sosai tare da xuba kayan alatu. Haka
babban falon suda

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment