Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma gefen hajiyar shi da
gefen baki. Ashura saboda xuciya da tayi tace
baxat taba xuwadakin shi ba sai dai shi in ya
matsu yaxo nata dakin, ako haka suke. Iklima
duk jinta take ba daidai ba,2n ana bikin Nfsa
karfin hali kawai takeyyi ko bata je asibiti ba
tasan cewa ciki ne da ita taji bata marmarin
komai sai taliyar murji ta fulawa ta mike ta nufi
kitchen tana 2nanin ina xata samu? Hijabi ta
xura ta nufi gidan Luba
Suna gaisawa tace luba ina xan sau taliyar
murji?luba tace bari a kira A'i me aikina kila ta
sani,dan taliya muka samu kenan?tace wlh ina
xaton ciki ne dani luba. Luba tace ai ummita ta
sha miya,iklima tace haka babanta yace ranan
wai shi fa kada na yarda nasha wani
magani,ashura ma da take sha ya fada mata ta
daina ba da yawunsa ba tace ita bata shirya
haihuwa ba yace ita ta sani shi 2nda yana da
yaran shi. Luba tace saki jiki ki haihu kawata
lokacin da kike sunbulo ma mijinki yara lokacin
yake kara sonki iklima tace hakane. A'i ta dawo
daga siyan taliya iklima ta shiga gida.
Tana cikin dafa taliya khalil na kofar kicin yana
shan dudu Ashura tazo shiga kitchen tace kai
tashi a hanya dan iskan yaro kuna ganin
mutane matsiyatan yara baxa ku matsa ba.
Iklima abin ya soki ranta tace haba Ashura ki
daina zagin yara na yan iska gara in sun miki
laifi ne ki dake su bana son zagi bana yi bana
so yarana su tashi dayi. Ashura tace na xaga
koke sai in xaga bare su,su din banza?gidan
miji na ne,ran iklima ya baci sosai bata saba da
fada ba tace to ai suma gidan uban su ne ko?
Ashura tace gidan uban manya dama uban ya
damu dasu ne to uwarsu ma cuso ta akayi mun
san komai yarki ya nema taga kudi ta guje shi
aka manna mishi ke ba sonki yake ba,ita kuma
ta kwashi kanjamau. Iklima ta tsura mata ido
sannan tayi karfin halin cewa wa ya fada miki?
Ashura tace wa kika sam xai fada min?don
haka bar ni na sake soyayya tasa aka auro ni
kuma da xaran na shirya haihuwa xan soma
zubulbulo yayan soyayya. Iklima ta lumshe ido
in ma shi ya fada miki xai dawo ya same
ni,ashura tace shi ne ya fada min kuwa don
haka ki san matsayin ki bar gani ina raga miki.
Daki iklima ta shige tare da kama yaronta tayi
shiru akan gado.
Tabbas Mahmood shine ya fada wa matarsa
sirrinsu domin babu wanda ta sani a garin da
xai bata labari,a saninta sakina makociyarsu
itace kawar ashura kadai kuma bata xaton
tasan labarin 2nda ba unguwar suke ba,ta
gama duk 2naninta ta gano cewa in ba
mahmood ba ba wanda xai fada mata. Ranta
yayi ma2kar baci kenan ita da mahmood ba
sirri?ta xata sirrin shi nata ne haka nata nashi
ne ashe ba haka abin yake ba?ranar dai kasa
cin taliyar tayi yini tana daki. Ashura kuwa an
sami abinyi shiga goma fita habaici,waka,wai
matar cushe bata daraja. Iklima tayi kuka har
ta gaji da dare luba ta shigo ta ganta kwance
tace jikinne har yanxun?iklima tace wlh amma
dole xan gyagije gobe Asabar ina da jarabawa
a makaranta. Luba tace kuma yayan naki baya
kusa bare kiyi shagwaba,sukay ta hira luba ta
tafi bata fad ma luba komai ba domin sirrin
gidanta ne.
Washegari tayi shirin islamiya ta fita ko duban
inda motar take batayi ba ta nufi taxi,su khalil
suna gidan luba. 2n jiya kome na mahmud yasure mata hatta wayarta ta kashe don bata ko
son jon muryarshi ya kira ya kira yayi text shiru
ya tambayi Ashura iklima fa? Tace ita tana daki
bata san ko tana nan ba
yace ta duba ta tace ta kunna waya,ko
motsawa batayi ba da ya sake kira sai tace ta
fita 2ni gurin magrib ya sake kira Ashura tace
bafa ta dawo ba don sharri,kawai ya cika da
mamakin ina taje?washegari ma duk bata a
ntwk ya damu sosai. Ta dawo islamiyya ta
shiga kitchen tana kokarin dora girki sai ga A'i
mai aikin luba da uwar kula cike da 2won
shinkafa miyar ogun,iklima tace kai jice da luba
Allah ya biyata sai nazo, Ashura na jinsu ta hau
wakar habaici wai kwadayi mabudin wahala ga
roko an bani dai. Iklima dai tayi daki cikin ranta
tace bada ke xanyi ba da wanda ya daure miki
gindi xanyi bari yaxo garin. Uku saura suka bar
office da yake yanxu ya xama babba har sati
yana office daga office jirgi kawai ya hau xuwa
airport sai dai ya kira wayar direbansu mabde
yace yaxo ya dauke shi,iklima na kwance tana
sauraron kaset din wa'azi na Sheikh Aminu
Daurawa (siffar mace ta gari) ya shigo da
sallama banda sanin muhimmancin sallama da
baxata amsa ba sai dai a ciki ta amsa,sannan
ko motsi batayi ba bare ta dube shi ya iso
gabanta ya sabule jakar daga kafadar shi
iklima ta dube shi irin duban da bata taba mishi
ba shi kanshi yaga kallon tsana ganin idonshi
yace lafiya?tace kalau cikin muryar rashin
ladabi,al'ajabi ya cika shi.
Ya sauke ajiyar heart ya kika kashe wayar ki 2n
jiya ina ta nema?tace bana son damu ne na
kashe,yace tashi wai meke faruwane?yau ban
gane miki ba kinxo da bakin dabi'u,taja ajiyar
heart lokacin da ta soma 2no xantukan ashura
tayi mata gori dasu sai kuka,duk ya rude xai
taba ta ta tashi xaune tare da cewa kada ka
taba ni ta sauka daga kan gadon binta yake da
ido cikin mamaki tace Mahmood! Ya xaro eyes
bai taba jin sunan a bakinta ba taci gaba cikin
kuka dama jiranka nake yi kaxo ka sallame ni
in tafi gida,bai san lokacin da ya iso ya daga
hannu ya wanka mata mari ba sannan yace
anki a sallame ki kin san me kike fadi?ta dafe
kunci tare da fashewa da sabon kuka ni ka
mara?ni ka daka?ta janyo hijabinta daga kan
kofa xan tafi gidan makwadaita. Yace iklima in
kin fita kofar gida Allah ya isa ban yafe ba ta
tsaya cak sai ta fashe da sabon kuka tana
cewa ka cuci xuciyar da bata taba 2nanin cutar
ka ba,kaci amana ka kuma tona sirrina don ka
birge abin sonka ta dube shi ni yanxun kimarka
ta ragu a idona. Yaxo ya tsugunna kusa da ita
ki fada min lefina kin tsorata ni,yaya kike gani
xanyi wata rayuwa mai dadi in baki?haba
iklima me yasa xaki yanke min hukunci da xai
xamar min tamkar na kisa?wannan ba halin ki
bane ina kika samo bakon hali?
Wlh iklima keme hakuri ce ke me biyayya
ce,keme adalci ce kuma kece rufin asiri na ta
dube shi gefen da ya mare ta idon gefen har ya
kumbura amma kai me yasa baxaka rufe nawa
sirrin ba?mahmood na sani baka sona kuma
banga lefin xuciyarka ba don bata soni ba
2nda mahaifina yayi maka tayina ya 2ra maka
ni da ka sani baka karba ba,tausanta ya cika
xuciyar shi dole akwai wani abu yaxo ya
kamata ya rungume tsam,fada min me aka ce
miki nayi?tace ka fada wa matarka cewa baka
sona da yarana dama auren dole akay maka
dani yayata kake so ita mai kwadayi tabi mai
kudi gashi nan ta dibo kanjamau....ta fashe da
sabon kuka yayi shiru ya rasa bakin magana
don al'ajabi,ya sake ta ya fita. Ashura dake
labe ta jiyo takunsa ta ruga ta shige kicin ya
duba dakinta yana kia Ashura! Ashura!! Ta
amsa daga kicin yace zo nan,tana fitowa ta
biyoshi iklima na zaune kasa suka shigo ya
tsugunna kusa da ita,tashi ki xauna kan kujera
ya kamata ta tashi,yace Ashura me kika ce
mata? Tace na me? Yace kada ki kawo min
raini. Ya dubi iklima me tace miki?iklima ta
harare shi abinda ka fada mata,tace kace dole
ka aure ni shi ne nekeso ka sallameni,kace
iyayena kwadayayyu ne,yayata kaso ta auri
maikudi tana da kanjamau duk ina ta san
wannan in ba kai ka fda mata ba?ya fusata to
ke Ashura ina kikaji wannan xancen?tace ina
kuwa xanji?kai ka fada min kace dole kake
xaune da ita har yaranta kace kyamar gidan su
kakeji saboda kanjamau. Bai san lokacin da ya
daga hannu ya wanka ma Ashura mari ba.yar
sharri a ina na fada miki?ta dafe kuma2 shine
ka mare ni dan ban fadi sauran ba?ta nufi kofar
fita kace iyayanta talakawa matsiyata,kai kake
ma Babanta dinki kuma kai kayi ma yarta
kayan daki....
Ya nufo ta da sauri ta fita,kan ikilima ya sara ta
ji zuciyanta na tashi.ta shiga bayi da gudu
tana sheka amai.ya biyu ta yana tsaye yana
mamakin sharri irin na ashura,ta gama amai ta
yunkura zata mike jiri ya debe ta da gudu ya
shiga ya dago ta can zuwa kan gado,ta ce
ikilima don Allah kiyi hakuri,wallahi ta fada ne
don kawai ta hada mu.ikilima tayi ajiyar
zuciya,mahamood so nasa mutum yayi abinda
yafi haka,kana sonta zaka iya fada mata.maza
nawa ne suke zagi matansu suka tozarta
matansu a gurin budurwa ma ba mata ba?Don
ka fada mata ba wani sabon abu bane.ya ce
ikilima ta ce bana so ka musa,don na tabbata
duk sharrinta ba za ta kalli idonka ta maka
ba,gashi duk abinda ta fada an yi.Gurinwa taji?
wa muka sani nan unguwar?ya ce zata fadi in
da ta ji.nafi son ki nutsu ki kwantar da
hankalinki,dubi yanda ki ka yi.ke jaruma ce na
sani kina jure abubuwa,ki jure wannan.Ta
yunkura ta tashi zaune,ta soma magana
hawaye na bin kumatunta.zan jure duk wani
abu da zaka min,zan jure abunda matar zata
min.amma ka sani ba zan taba jure abin da zai
shafi mutuncin iyayena ba... kuka ya sarke
ta,ta ci gaba da magana.Don iyayena koda
hannu suke karawa a gaba don talauci ban da
kamarsu,kuma zan tsare musu mutuncinsu,in
ma tambaya ka?ya ce,Babana ya taba zuwa
rokonka wani abu?taja numfashin a a,ta ce zan
karba maka.ya rugumai ta,ba ke ba ko ni ba
zan bari wani ya ci mutuncin mahaifinki ba. kiyi
hakuri zan bi diddigin maganar nan.Ya dace
zuwa yanzu kin san abin yi,kin san sharri da za
a yi min,ta ce an sha fada min cewa namiji ba
shi da tabbas ina musawa,ya ce kici gaba da
musawa,kada kuma tabbas miki haka.Nan dai
yayi ta lallashinta kin san wanda bai saba yin
fushi ba,ina yayi ba kyua.da kyar ya shawo
kanta,lokacin magariba ta gota,yayi wanka a
dakin yayi sallah,itama tayi sallah ya ce ina
yaran nan?ta ce suna gidan luba.ta dauki
wayarta ta kunna tana kiran luba,suka gaisa ta
ce,a"i ta kawo su khalil,baban su ya dawo.luba
ta ce yanzu?ikilima ta ce,ehh,luba ta ce to ya
jikin naki?tace da sauki.luba ta ce naji
muryanki duk ta shake?ta ce,eh,kaina ne ke
ciwo.
A"i ta kawo su khalil,sun ci sun koshi har an yi
usu wanka,suka ruga suka makale jikin
babansu.a"i ta sauke kulolin da ta zo dasu,ta
ce ya jiki?ikilima ta ce da sauki,ki ce mata na
gode.taje ta dauko plate ta zuba mishi sinasir
da miyan kaza,taje ta kawo mishi kunu
aya.Ashura na lekenta bata so haka ba,tayi ne
don su yi ta gabza fada,ya ce rabona da abinci
tun break fast kema kina jin yunwa?ta ce,a
a.ya ci ya koshi sannan ya yi isha:i,bai fita ba
laptop ya jawo ya shiga harkokin aikin shi har
lokacin bacci.ita tuni ma tayi bacci,ya aje
komai ya kwanta a bayanta,ya nutsata
jikinshi,zafin jikinta ne yasa shi hakura da
bukatarshi.da safe kam bayan asubahi kasa
jurewa yayi,don satinshi uku rabonshi da
gida,don haka duk da bata jin dadin jikinta ta
fahimce shi,don haka sai ta saki jiki ta mishi
duk abinda yake so.bayan sun karya ya kira
musa a waya ya ce yazo zai aiki shi gurin
mahammod.ya nufi dakin ashura,rufda da ciki
tayi tana ta chatting,ya fizge wayar ya duba da
wa take hira,namiji ne suke hirar ya ce wanene
wannan?ta ce dama can da abokina ka
ganni.ya kashe ya saka wayar cikin aljihunsa
ta ce ban wayata.ya ce bazan baki ba,a ina ne
nake fada miki zantunkan da ki ka fada ma
matata?ta mike tana hura hanci ba kai ka fada
mini ba.ya ce a ina ki ka ji?ta ce,zancan duniya
yana boyuwa ne?ya ce to me yasa ki ka zabi ki
mini sharri ki ka ce ni ne na fada miki?ta dube
shi don nasan haka ne zai fi yi maka zafi.ya ce,
tashi muje ki karyata kanki,tayi mishi wani
kallo.wallahi in mun je gabanta zan fadi wani
abin,kuma ba zan canza ba.ya yi shiru yana
kallonta,ya fita yayi shiru akan kujera yana
tunanin yanda zai mata. kilima ta fita ta zauna
kusa dasji lafiya?ya dube
ta,ikilima za ki yarda da duk abin da zan fada
miki? ta ce fadi naji,ya shaida mata duk yanda
suka yi da ashura.ya ce,na baki dama ki je ki
tambaye luba kawarki ba mata masu irin
wannan makircin?ta kuwa shiga gidan lubata
shaida mata komai.Luba ta ce,tabbas akwa
matan da sun dama ashura a sharri,dan ke ba
kya shiga jama,a sosai shi yasa ba za ki san
wadannan abubuwan ba,shawarata ki saurari
mijinki kuna da fahimtar juna ke da shi,shi yasa
ake son mata da miji su fahimci juna duk
matsalar da ta taso muku ba za ku sha wahala
ba gurin magance ta.sannan in zai auro mata
uku dole su biki a baya,don kin san mijinki fiye
da kowaccan su.ki share ki yarda da abinda ya
fada miki.ikilima ta ce to ni mamaki na ina ta ji
zancen?luba ta ce,ke ki barmakiyinki,duk inda
za taje ta lallabo zata je,a yanda ya damu ma
za ki san cewa ba shi bane.Ikilima ta ce she
kenan,na amince.Ashe tura ta gidan luba da
yayi hukunci zai yi,tana shigowa ta soma jiyo
ihun ashura sai jibgarta yake,ta fada dakin da
gudu ta kama shi ta karfi ta rike yana barta
yarinyar nan in koya mata hankali,in za ki yiwa
sharri?ki hada ni da matata,ke ban da arzikinta
ma da ki ke ci ta hana da tuni ban yarda ke na
huta ba?Ikilima ta ce to ya isa ka bari ba kyua
dukan mace,Manzon Allah bai taba dukan
matan shi ba.ni dai aka yi wa laifi ko?to na
yafe.ta dubi ashura kiyi hakuri ashura,da ke cin
kuka tana zage zage ta ce ba zan hakura
ba,munafuka duk ke ce ki kasa ai ya duke ni
kuma wallahi sai na dauki mataki.ya ce,ki
dauka.ya ciro waya ya kira yayanta abubakar
abikin shi ya sanar da shi komai,abubakar ya
ce baka zane yar iska ba?mahamood ya
ce,mun kaita ga haka ai yanzu.abubakar ya ce
da kyua kuma wallahi tazo gida sai na karya
mata kafa,batun waya kuma kada ka barta da
ita,in ma zaka ji tawa aikin ma ka ce ta aje
tunda kana mata komai.vels BOOK
MABUDIN WAHALA 3**11
Mahmud ya ce,tunanina kenan kawai ina duba
yanda hajiya zata dauki batunne?abubakar ya
ce, kai ke aurenta ko hajjiya?kawai ga abinda
ka ke so in zata zauna ta zauna in bai mata ba
tsarinka kenan.tazo ta zauna da
hajjiya.mahamood ya ce na gode ya fita.Ikilima
ta bishi a daki ta nuna mishi bacin ranta na
duka ya ce bazai kara ba.da dare ya same ta
har lokacin sai kuka take,ya ce bata da
waya,kuma karta kuma fita sunan aiki.nan ko
ta shiga hada kayanta,ta ce ba dole.da safe
yana tafiya itama ta kama hanya.Hajjiya ta
daure mata gindi,shi ko share su yayi lokacin
da ya ji labarin cikin ikilima yayi murna sosai
tamkar wannan ne lokacin na farko,da aka
soma yin ciki a gidan shi.Tattalinta yake ita da
yaranta,ya canza mata mota ya dauka mata
yan aiki itama ta na kula da shi tarea da yin
duk wani abu da tasan zai so ko zai birge
shi,insuna hutu takan bishi lagos .zuwa yanzu
mahamood lamura sun bude,karin girma a kan
aikin shi,don haka ya zama bango mai kwari
ga danginshe da mahaifanshi.Ashura kuwa sai
waya take,ya bata takardarta,da ya yi yunkuri
zai bata sai ikilima ta hana ta ce ba zai sake
taba,ita dai tafi son yaje yayo bikonta shi kuma
ya rantse cewa ba da shi ba.yayanta abubakar
da cewa ya yi shima wai ya sake ta,ikilima ta
ce sam bata yarda ba.ya ce shi kwnan kuma
ba zai bi ta ba randa ta ji cewa zata iya zama
da shi ta dawo. Duk da ikilima ta nuna bata son
bidi,a wannan
haihuwar mahamood ya kekashe ya ce,lokacin
abu ayi shi.aka dace lokacin yana hutun
karshen shekara,ta sintalo yaronta shima dai
yan uwanshi ya biyo,duk suna kama ne sak da
mahmood.Wa ya ce da ni ba ni ba sweety kin
duba yaron nan da wa yake kama?ikilima ta
ce,kana mini wayo baban khalil.ya ce,ki kara
himma kin ji kanwata?tun da kin haifo
mahmood ki samo min ikilima in fa tayi kama
da ke.Ikilima ta ce,bar ni da labari wata
haihuwa yanzu ban gama gyagajewa ba.ya
ce,na bari.ya yi ma dan shi huduba da
mahamood,hidima kuwa tun ranar da suka
dawo asibiti aka kada sa dangi ko ta ina sai
barkowa suke yi suna kuwa tana bata son taro
bata son taro gida sai da ya dinke da
jama,a,aka yi ta girke girke.su luba sune masu
rabon abubuwa,nafisa kam tunda ta zauna
bakin gado ikilima bata iya tashi ba kallon
dakin take tana kukan zuci ga kanwarta ikilima
ta zama babbar mace hakima.da ka ganta
kaga matar manya kamshi dakinta ma dabanne
kaya da gwala gwale ba a magana shi ko
mahamood yanda yake shiga yana kiran ikilima
yana ji da ita shi ne yasa nafisa tunanin cewa
kila dama can ba sonta yake ba ikilima yake
hari.Abokansa su muktar bai yada su ba,da
abokansa na yanzu ta shirya walima an ci an
tashi kowa na san barka.washegari nafisa tazo
gurin aikin nama,tana gidan yayi wa ikilima
albishir da cewa ta shi gudumawar shi da ita
da mamanshi za su je umarah,nan da sati
hudu har da jaririnsu.duka da ikilima ta taba
zuwa lokacin gasar karatun su tayi murna
sosai,don tsalle tayi ta rungume shi tana
murna.
Nafisa ta kara yin dana sani da bata bi son
duniya ba, gashi yanzu tayi asarar abib
sonta,har abada ta raina zrzikin sa gashi yau
Allah ya daukaka shi.dukiyarsa ta halas
guminsa ita ko ga ta ba dukiyar ba kuma
lafiyar.wai ita taga da kyua ma kenan a kan
mama zee tunda ta tuba kuma har gashi tayi
aure tana saran samun dan kanta,don tayi bari
ma kwanan baya,ita kam ta dau darasi a
rayuwa,ta kuma yarda kwadayi mabudin
wahala ne.Hajjiya su ashura ba lafiya, ciwon
kansa za,ayi mata aiki kusan miliyon biyu,duk
su saida komai sun biya mata aikin amma ba a
jima da yin aikin ba ta ce ga garinku.Ikilima taji
rasuwar lokacin da mahaood yayo mata
waya,ya ce zai zo asabar amma kaduna zai
wuce,ta ce ya biyo mata su tafi tare.haka kuwa
aka yi gidan cike da mutane don ranar ce
uku.Ashura taji mamakin ganin yanda ikilima ta
koma cikin shekara daya,shima ta ji mamakin
shi,daga ganinsu kasan kudi su zauna.duk da
tasa hijabi da nikab a kamshinta da yadin
hijabin ma zaka gane ta kere sa,a,sun yi
gaisuwa da zasu tafi kannen hajjiyar su tayi ta
bashi hakuri wai ya maida ashura,ya ce ai shi
bai kore ta ba ita ce ta tafi in taga lokacin yayi
da zata iya zama da shi to tana iya
komawa.Nan dai suka tafi bayan sun sauke
musu buhun shinkafa sadaka da dubu
hamshin,abubakar yanata godiya.dangi suka
yi wa ashura caa kan cewa tayi wa kanta fada
ta koma ta ce in fa ina son shi amma yanda ya
dauki matar nan sai ka ce uwarshi komai
ita.itama komai shi in mutum na son zaman
lafiya sai de yabi su dukansu.baba amina
kanwar hajjiya ta ce,to ai durkusawa wada ba
gajiyawa bane,daga ganinta zata yi hakuti ba
zata yi son fitina ba.Ashura ta yi shiru don
tasan duk sharrinta ba za ta ce ikilima
mafadaciya ba ce.
Matar yayanta abubakar ta ce,kiyi koyi da
halayanta za ki samu shiga gurinsa.domin
komai ki ka gani halin mutum ke ja mada.baba
amina ta ce haka ne dama son mace ta zama
sirrin mijinta,ta bi mijinta su zama tip da
taya,ita da shi yanda duk wadda ta zo sai dai
ta biyo ta.Wata kawar hajjiyar ta ce,ko de asiri
ne?baba amina ta ce ko daya,ba asiri,hakuri
ladabi da biyayya tsaf ta kare sirrin mijinta,kula
da hakinshi kula da dukiyashi,tausaya mishi in
yana halin damuwa,ki ji cewa damuwarshi taki
ce,ba shi shawara mai kyua.kyuata ga
daginsa,duk iri wadanna ki ka haro mijinki da
su,to shi kuma zai bauta miki tamkar bawa.shi
namiji tamkar yao yake.Ashura dai ta dage
musu kan cewa sai in ya zo da kan shi ya ce ta
koma,suka ce shi kenan ta zauna suka barta.
Ikilima taja dalleliyar motarta zuwa gidan su da
gidan surakarta don yi musu sallama saboda
daran yau za su tashi.ta shiga gida suna da
gurinsu maman ummi duk sunji kunya don ba
su zo mata barka ba.suka shiga kame kame ta
ce ba komai kada su damu,dama sallama ta zo
musu za su tafi umra.Nan suka shiga murna
tare da cewa,baban khalil ne ya biya miki?ta
ce,ehh,yanzu kun yarda cewa akwa maza yan
goyo?shawarata ku kama kawunanku kuyi
hakuri ku rike Allah ku rike mazajanku da
gaskiya da amana Allah zai baku fahimtar juna.
Ikilima tana ki tana komai mahood ya ce ta sai
ta sako hakorin makkah,don shi yana so ta ko
sako,wayooo Allah!sun zama taurari,duk mata
kawayenta so suke su koyi halinta don su
mallake mazajen su bata tare da boka ko
mallam ba.sakina ta doka ma ashura waya
cewa sun dawo sai gata cikinsa,a yana gida.ya
ko hada rai ko gaisuwarta bai amsa ba.ikilima
dai ta sauke ta sauka ta girmamawa,tana kuka
tan ba ikilima hakuri tare da neman
gafaranta,ta kuma shaida mata cewa dama
sharri tayi ma mahamood bai fada mata komai
ba,kuma don Allah ta nemar mata gafara a
gurin shi.ikilima tasa yan aikin ta suka sharre
ma ashura dakinta, tare da gyara shi,ta ce ta
zauna ba koma ba. wasa wasa sai mahood ya
shiga fushi da ita,kan ta ikiliman wai don me
zata sauraro ashura?Hankalin ikilima ya
tashi,amma ya ki sauraront,ya ma yi tafiyarshi
lagos,ta shirya ta bishi ya ce sam shi fa ashura
bata yi hankali ba.ikilima da kyar tasha kanshi
ta dawo saboda makaranta ,ta tura ashura.bai
san ta turo ta ba sai dai ta kira wayarshi ta ce
ya taro ashura,sawa yayi aka zo aka dauke
ta,duk da haka ta kusa sati tana rokon shi
sannan ya kulata.bayan ya kafa mata
sharudda wanda in tayi wasa da su zata bar
gidan shi.sharuddan duk kusan saboda ikilima
ne,tun daga lokacin ta kare sanin ikilima ta
wuce da tunaninta..Zamamsu gwanin
sha,awa,ashura ma ta haifi yarta yasa mata
sunan hajjiyarta.likafa tayi gaba. yanzu
mahamood fita waje kamar nan ya maida ta,ya
ci gaba sosai.yayinda ragamar aikinshi ke
hanun uwargidan sarautan mata,hajiya ikilima
karatu bai hanata yin duk hidimar da ya sakar
mata ba.na dagin shi da gidanshi suna godiya
da sa albarka.amma shi bai san ma me aka yi
musu ba,in ko yazo gari haka zai ta ji makota
da yanuwa suna ce mishi sun ga sako sun
gode. Wani abun da yafi ba shi mamaki,wani
azumi
yana gari yaje sallah masallacin layinsu,yaga
an kawata masallacin kuma an gina islamiya
maza manya ya ce da makocinshi gurin nan ya
yi kyua,sai ya ce ai gaskiya ka kashe mishi
kudi.ya ce ni?mijin luba ya ce, mai ne mana sai
kuma ga yan kwamitin masallaci sun zo suna
godiya.ya yi murmushi cikin zuciyashi ya
ce,ikilima kenan!shi yasa komai nashi baya iya
boye mata duk takardunshi masu muhimmanci
suna hanunta tasan duk abin da ya mallaka
dan yasan tana da gaskiya.Yanzu su nafisa da
dagenta suma a gurinta suke hutawa,bata da
rowa bare kyashi.iyayanshi na sonta don ta
tsaya gurin kula da shi yan uwana mata kuna
koyi da halin ikilima don mallake mazajanku?

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment