Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

layi duk da tana da
wata shi bai san tana da waya ba kuma kudin
shine na shago. Yau ta bashi kyallen
shadda,gobe leshi jibi atamfa ko material masu
tsada tace suna da biki. Itama haule ko yaushe
nafiu yana hanya gurin amso omo, sabulu da
madara. Wannan lamarin yana ma2kar bata
ran ikilima shi yasa koda haule xata dake tane
sai dai ta dake ta amma bata xuwa amso mata
sabulu ko wani abun.
Lokacin da yar tata ta dao sai ta shaida mata
cewa ga hukuncin da babanta ya yanke. Nfsa
tace sunyi ta banxa don ba dai dani ba to ko
kudin gaisuwar safina dubu 50 ne bare ni in ba
a kawo min 100 ba ai sai dai nima a bani 50
din,amma dubu 5 sai kace dan tsako. Haule
tace ashe kin fara hankali yanxu kyale shi
2nda ance sai kin gama makaranta ki karta
mishi rashin M har yayi xuciya ya daina xuwa
sannan kiyi ta dora mishi nauyin abinda bashi
dashi duk abinda kika sanyafi karfin shi shi
xakice ya sai miki. Nfsa tace ki bar shi sai mun
karya shagon kema ki dinga aikawa kina amso
sabulu da omo haule tayi dariya tace xan ko
dinga aikawa. Hakan ce ta kasance,tashin
farko ta sake bijiro masa da ba2n waya jiki na
bari ya siyo mata har da layi duk da tana da
wata shi bai san tana da waya ba kuma kudin
shine na shago. Yau ta bashi kyallen
shadda,gobe leshi jibi atamfa ko material masu
tsada tace suna da biki. Itama haule ko yaushe
nafiu yana hanya gurin amso omo, sabulu da
madara. Wannan lamarin yana ma2kar bata
ran ikilima shi yasa koda haule xata dake tane
sai dai ta dake ta amma bata xuwa amso mata
sabulu ko wani abun.
***
Rayuwar ikilima abin sha'awa ne ga duk wani
mai hankali yarinyar tana kara2 sosai yanxun
ne take aji 6 na makarantar primary islamiyya
kuwa suna ajin sauka ga kuma hadda tana
xuwa yanxun haka tana da haddar izfi 30.
Mutane da dama yan layin su ma sun manta
da kamannin fuskar iklima saboda ko yaushe
koina xata sanye da babban hijabi da kuma
nikabi ga safa. Malamansu na islamiya
koyaushe suna yin alfahari da iklima usman
tana da zazzakar murya shiyasa duk lokacin
da xa ayi gasar kara2n alkur'ani da wasu
makaran2 iklima na daya daga cikin masu
gasa kuma tasha xuwa musu ta daya. Yanxun
ma da ake shirin yin na kananan hukumomi
itace suka yanke shawarar turawa don haka
mahaifinta malam usman na alfahari da ita
kuma duk lokacin da taxo mishi da wani bukata
game da makaranta yana biya mata. Haule
kuwa tana kallon iklima a wawiya yar kauye
shiyasa ma basu cika shiri ba kullum tana ckin
yi mata fada duk da cewar biyayyar da take
mata nfsa bata mata ga uban aikin gidan duk
ita ce ke yin shi. Ita kuwa nfsa yanxu tana
ma2kar juya mahmuda duk sun karya shago
har sai da ya saida mashin dinsa ya kara jari
amma ina suma 2ni sun tafi. Wannan al'amarin
ya 2nxura mahaifin shi in da ya kira shi ya
tsare shi da son ya sanar daa shi inda ya kai
kudin 2nda ba abinci yake saye yana ci ba ba
kome ba. Shiru kawai yayi bayan ya gama
mishi fadan ya sake bashi kudin amma kafin
watanni 3 suma sun kare. Kai hatta kannanshi
haushinsa suke ji domin su sun san gindin
nafsa ya tare, shi kuwa burin shi ya faranta
mata, ga nfsa kuwa yanxun wata sabuwar
rayuwar take fantamawa haka nan cikin
xuciyarta koyaushe kara son mahmud takeyi
sai dai har yanxun bata gama yanke xata aure
shi ko ba xata aure shi ba domin duk lokacin
da wani yaxo gurinta ba mahmud ba takan
samu kanta da jin kunci amma in mahmud ne
ko ta daure masa fuska xuciyarta ta kan
sanyaya tare da jin nishadi. Xuwa yanxun ta
gama yarda mahmud ne kawai farin cikin
rayuwar ta sai dai matsawar bai samu aiki ba
to ba2n autan su yasha ruwa kenan.
Iklima ta shga ckin ma2kar farin ciki ta samu
haule tana firar doya ta xauna tare da cewa
mama yau dai mun gama jarabawar mu ta
sauka sai walima ya rage mana,iklima 2nda
wani malami ya taba yi musu nasiha kan cewa
babu kyau yaro yana fadar sunan mahaifin shi
ta daina kiran sunan haule. Haule tace na mki
murna kinga kin huta da wannan ziritin xuwa
makarantar kome ruwa kome sanyi, iklima ta
dubi haule mama kara2 yanxun muka sa kafa,
haule ta taba baki ai sai kiya tayi kin ga ni ban
iya abinda kika iya ba tashi ki hada min
murhu,cikin sauri iklima ta tashi ta cire hijab da
nikab ta shiga kitchen. Ckin kwanakin Alhaji
ibrhm ya kira mahmud ya saka shi gaba da
fada a gaban hajiya uwa uwargdan shi yace
uwa yanxun ki duba mahmud shagon sa ya
sake lalacewa da ina xaton yana da hankali
ashe ba haka bane dubu dari shida na xuba
mishi kayan sun narke,mashin ya saida na
sake bashi dubu dari3 suma sun rushe to me
yakeyi da kudin? Hajiya uwa tace kasan
mahmud da kyauta, Alhaji ibrahim yace daina
gaya min wannan ba2n don yana da kyauta
sai ya rabar da kayan?nifa nafi xaton cewa
mata yake nema...da sauri mahmud ya dubi
mahaifinsa, hajiya uwa tace haba Alhaji kada
kayi masa mummunan xato ba halin mahmud
bane. Alhaji ibrahim yace to caca yakeyi
kenan? Hajiya tace babu ko daya ka dai daure
ka kara mishi, Alhaji yace Allah ya tsare ni nayi
rantsuwa baxan kuma bashi ko sisi ba kuma
baxanyi kaffara ba tashi ka fita ka bani wuri.
Mahmud ya dubi mahaifinshi yace kamin
afuwa yanxu xan gyara, Alhaji yace kada ma ka
gyara tashi ka fita,mahmud ya nike tare da
cewa Allah ya huci xuciyarku, Alhaji ibrahim
yaja tsaki tare da cew sakarai batun aure kaki
har kasa sana'a itama kaki to ni yanxu na xuba
maka idanu. Ckin daknshi ya shiga yana ta
ziri2 yana kai kawo shi kanshi ya sani ya
cancanci fada kai har duka ma gata dai mai
suna gata mahaifinsa ya nuna masa ya sani
duk cikin yayan mahaifin nasu ya fi son shi
maimakon ya mu2nta kanshi ya jawo
kannanshi ya lura dasu don wata rana in babu
mahaifinsu shine xai zama mahaifin nasu. Ya
kasa gyara kanshi duk dalilin son nafsa to
anjima xayaje ya sameta ya gaji hakanan in ba
xata aureshi bane ya hakura alabasshi son
nata ya kashe shi. Bayan sallar ishai ya aika
aka kira mishi kabiru don ya tsare mai shago.
Mahmud yayi kyau ckin bakin wandon jeans da
jar t-shirt mai gajeran hannu,ya fesa mayan
turarenshi sunshine ya saka takalmanshi ya
fita. Yana tsaye nafiu ya fito mahmud ya kira
shi nafiu ya gaida shi sannan yace yaya nafisa
suje biki bata nan yce jeka xan je in dao
shagonshi ya koma sai tara saura ya kuma
nufar gdan tare da adduar Allah yasa ta dao.
Yana tsaye iklima ta dawo haddar dare bata
san shi bane yace malama kin dawo? Cikin
natsuwa ta nufo shi don ta shaida muryarsa
sallama ta masa sannan tace ya nafisan bata
nan ne ko baka samu dan aike ba ne? Yace
daxu naxo wai sunje biki shine na dawo yanxu,
iklima tace to bari in shiga sai na 2ro ta ta tafi
tare da cewa sai da safe shi ko da kallo ya bita
yarinyar ta samu yabo a kafatannin unguwan
su tana da ma2kar nutsuwa shi kanshi ya
manta kamannin fuskarta, ina ma haka nfsa
take? Koda dai shi yana son mace wayayya,
nfsan ce ta katse mishi 2nani da cewa my
sweet ga alama yau kana son ganina ance ka
xo dazu wallahi mun je biki ne.
Baice kala ba,ta kai hannu xata kama nashii su
xauna sai ta 2na yanxunnan sa iya yin rigima
kan hakan don haka sai ta fasa tace mu xauna
mana my sweety darling. Ya xauna sai dai ta
lura fuskarshi babu annuri tace wai shin yau
me yake faruwa? Yace ni dai gaskiya na gaji
yau naxo ne muyi ta ta kare, tace name? Yace
na aure, bakya duba uxuri na sai naki ni kuma
na fada miki ina bukatar mace kusa dani ni ba
maxinaci bane gashi mahaifina ya kosa inyi
aure. Tace to yanxu me kake nufi da ayi ta ta
kare?cikin xafin rai yace na shirya rabuwa dake
domin na kasa gane kanki ta raxana tare da
xare idanu,mahmud xaka iya rabuwa dani?
Taci gaba da magana muryarta na rawa,dama
kenan ba son gaskiya kake min ba?ta mike
xata tafi tana cewa shikenen nagode. Kukan ya
kwace mata sosai,da hanxari ya mike ya cafko
hannunta lokaci guda kuma yace a'uzubillahi
tare da sakin hannun ta. Yasha gabanta baki
fahimce ni bane nafsa ba nufina in bata miki rai
ba,nafi son ko xamu rabu muy rabuwar
mu2mci ta sake fusata barni na wuce in yaso
son naka yayi ajalina dama na jima ina zargin
ba sona kake yi ba. Nan take ya daburce ya
shiga lallashinta,kuka takeyi rurus da kyar ya
shawo kanta tayi shiru. Ckin sarkewar murya
irin ta wanda yaci kuka tace mahmud dama
akwai ranar da xataxo kayi 2nanin barina?
Yace come on beby nace mu wuce gurin ko?
tace a'a mahmud kasan son da nake maka
kuwa?wallahi gara na rasa raina da na
rasaka,me xaisa ka dinga baraxanar rabuwa
dani?
Ya sake matsowa kusa da ita xuciyata ke gaya
min cewa xaki yaudare ni, raina xaya fi
kwanciya idan mukai aure in na xama naki
kema ki tabbata tawa ni1. Ta sauke ajiyar heart
wallahi na fika son in ga wannan ranar,to kayi
hakuri mana 2nda baifi wata shida mu gama
ba. Yayi shiru yana 2nani itama 2nanin take yi
nata naxarin in ma xata aureshi to xata cigaba
da huldarta da wasu alhazan,to kuma bata ba
shiga katon gda da ka2war mota?sai yaushe
kenan ta cika burinkanta? Ya katse ta da cewa
shikenen zan kara daurewa tace nagode
masoyina don ma in na baka wata shawara
baxaka yarda bane yace fadi mana in xata
amfane mu. Tace xata amfane mu sosai
mana,yace ina jinki. Tace 2nda aure xamuyi an
riga an baka ni in ma kana jin xaka takura sai
inxo dakinka mu dinga rayuwarmu tamkar
ma'aurata...ya katse ta da cewa A'uzubillahi
kina nufin muyi zina?tace to an riga an baka ni
shi ne zina?
Yace ke daina furta wannan kalmar mara dadin
ji duk wanda yace miki don an baka yarinya ba
a daura aure ba ya kusance ta ba zina bane to
ki ce masa karyaa ne. Nafsa ko an kai
sadakina gdanku ba xan take ki ba bare ba a
kai ba,ni aure nake son inyi mai tsafta na
sunna ba jafwalgwalo ba, sannan in haifi yaya
suma wasu can su lalata min su don haka take
duk wanda yayi zina da yar wani haka xa ayi
da tasa,nfsa shawararki bata yi ba ke a duk
lokacin da irin wannan 2nanin ya bjiro miki kice
a'uzubillahi,ya mike tashi ki shga gida sai da
safe ta kasa tashi,ya tsuganna menene kuma?
tace duk abinda nace sai kace banyi daidai ba
ni banga wani laifi ba kowa fa ba matsala don
muna hulda. Ya fusata kina da hankali
kuwa,kin san me kike fada?to gurin Allah ba
karamin laifi bane. Sannan xaki iya samun ciki
me xaki ce da iyayenki?me xaki ce da mutan
unguwa?me xaki ce da ubangijinki?sannan me
xaki ce da dan koi yar?kinga dai na farko cikin
da akayi auran sunna ni xan dinga doki kema
haka dangina ma haka haka danginki. Sannan
yaron xai tashi ckin dangin mu kowa na sonshi.
Amma in muka yishi ta hanyar zina ke a boye
ba kwanciyar hankali danginki basu san a
sani,dangina ma kila su karyata suce ba nawa
bane,nima in naga xanji kunya in zuke ince ba
nawa bane,yaro in ya taso gori gurin yaran
unguwa a karshe ya rsare ki don ki fito mishi
da ubansa ga dinbin zunubi gurin Allah. Kin
gane nufina? A sanyaye tace na gane kuma
haka ne. Yace yauwa nafisata nafi son in
bareki daga leda. Gabanta ya fadi ta mike tare
da cewa to sai da safe,yace mu kwana lafiya
kiyi mafarkina kinji?tace to,cikin sanyin jiki ta
nufi cikin gida.
Lamura sun dagule mata,mahmud yasan cewa
2ni wasu suka bare ta a leda?kenan in bai
same ta a ledar ba xai gane?lokacin da ta
shiga gida mahaifinta ya fito bayi yace sai
yanxu kika shigo?nifa ban son doguwar hirar
nan 2n ana fadin gaskiya har karya ta shigo
ciki. Jeki taso Danlami ya rufo gidan,daga yau
kada 10 ta kuma yi miki a waje. Nfsa dai tace
to ta shge dakinsu ta samu iklima tana kara2n
Al"urani,ta fada gurin kwanciyarta ta shiga
2nani gashi kuma iklima ta dame ta sai dai
tasan koda wasa baxa tace mata tayi shiru ba
domin idan baban su yaji xata kwana da tabon
duka. Iklima ta gama kara2nta tayi addua ta
kwanta,nfsa ta dube ta iklima ina cikin
damuwa kin sanni in xance na cina bana iya
rikewa labari xan baki ba shawara nake nema
ba. Iklima tace ina jinki don tanaso su dinga
hira amma nfsa taki hakan. Nfsa tace yau
mahmud yaxo min da wani shirme wai xai rabu
dani,iklima tace saboda me?nfsa tace in ban
yarada munyi aure yanxu ba kai ba2n ya
girgixa ni bai san irin sonsa da nake bane.
Iklima tace to yaya nfsa banga amfanin xaman
haka ba 2nda bakya xuwa makarantar ba sai
kuyi auranku ba?ta katse ta da cewa nace ba
neman shawara nake ba. Iklima tace na manta
ne,nfsa tace duk sonda nake masa kuwa
banjin xan aureshi a haka inje babu lafiyayyan
abinci bare sutura. Iklima tace da kinyi
bu2lci,nfsa tace a,ai in na auri wani din na
wawuro sai naxi muyi aure kin san ni burina
babban gda da babbar mota. Iklima tace yaya
nfsa kwadayi fa shi ne mabudin wahala,ba
kyau bawa yana kallon na saman shi. Manzon
Allah(S.A.W) yace duk wanda bai gode kadan
ba ko ya samu mai yawa ba xai gode ba,don
haka in kin raina arzikin mahmud ko kin samu
babban gda da babbar mota baxa ki gode
ba,xaki hari wani abinne. Sannan Allah ba xai
bar cin amanar da kikayi wa mahmud ba ku
dubi yanda yake dawaiyniya damu cikin
gidannan,sutura...nfsa ta katse ta da cewa
malama kiyi min shiru kin cika min kunne an ce
miki irin rayuwarki xanyi kullum a lullube shi
yasa gashi har yanxu baki da saurayi. Iklima
tace ba shine a gabana ba sai da safe,ta
kwanta tare da jan mayafinta ta bar nfsa tana
ta masifa tare da yi mata gore gore.
Washegari da ta sanar da haule yanda sukayi
dashi haule tace nifa bana ma so kina wani
zancan mahmud wannan ai an gama babin shi
2nda yanxu bashi da ko taro shagon ma ya
tsiyace. Nfsa tace shiyasa yanxun duk wanda
yaxo fita xanyi ko a gaban shi ne,haule tace
yauwa yarinya mai tsada kyan ki babban gida
da babbar mota Hajiyar Allah. Nfsa tace amma
ikli dana bata shawara wai irin nima yaruwa
sai ta shiga zuga ni tare da kawo min
hadisai,haule tace nace ki daina shiga harkarta
iklima me ta sani na rayuwa?nfsa tace ai babu
kari. Ana gobe su iklima xasuje gurin gasar
kara2,malam yunus yana kara musu bayani
musamman saboda shigar da xasuyi yace
ba2n hijabi fa tabbas kowannan ku yasa kalan
na makaranta,suka ce to banda iklima wadda
babanta bai sami dari taran saya mata yadin
ba. Bayan malam yunus ya sallame su ita ta
tsaya bayan sun tafi ta dube shi,malam ina
ganin kila ni baxan samu xuwa gasar ba yace
saboda me?cikin mata dake muke takama,tace
babana bashi da kudi yayi duk yadda xa yayi
ko bashi bai samu ba so kaga bani da hijabi
kenan. Yayi shiru sannan yace je gida ki kwana
dai da niyar xuwa.
Da dare yaro ya shigo yace wai ana sallama da
iklima,nfsa tace inji wa?ko dai nfsa?yaro yace
haka ni dai yace min. Haule tace iklima kixo
kinyi kasuwa,suka sheke da dariya,ta taso ta
saka hijab da nikab,nfsa tace kai shegiyar
yarinyar nan ra'ayi ya miki yawa tadin ma kin
rufe fuska gashi sai uban kaurin hayaki kike
yi,iklima batace kala ba ta tafi,sai dai nata
2nanin kila yan ajinsu ne,ga mamakinta sai
taga malam yunus ta gaishe shi cikin
girmamawa ya amsa ya miko mata leda; to
iklima ga hijabi don Allah ki shirya da wuri
sannan ki sake duba littafanki,tace na saka
dawaiyniya malam yanxun ban san ma me
xance da babana ba sai ko ga baban ya taho
tace yauwa gashi nan xuwa. Malam yunus ya
gaishe shi sannan tace baba wannan malamin
mu ne ya sai min hijabinne ka ganshi baba
yace to to Allah ya saka maka da alkhairi naso
kwarai in sai mata hijabin amma Allah bai bani
iko ba,malam yace ba komai shi xaya tafi nan
sukayi sallama. Washegari 2n safe su ikli aka
shiga yin aiki da ta san itace me yin shi don
kada ta makara koda ta gama ta shiga shiri
dama koda ta dawo daga kiran malamin su ta
nuna ma su haule hijabin tsaki suka ja,ta
shirya tsaf suka dau hanya.
MABUDIN WAHALA 1***4
Kusan duk wanda ya halarci taron gasar iklima
ta burgeshi da zazzakar muryarta. Haka nan ta
amsa duk wasu tambayoyi da akayi mata babu
gyara karshe dai itace taxo ta daya don haka
ta samu damar xuwa gasa ta jihohi wadda za
ayi a jihar sokoto. Murna gurin ta da babanta
da yayyenta maxa sai ka gani,nfsa kam baki ta
taba,haule kuwa cewa tayi ni dai 2nda ban ga
kudi ba ba a birgeni ba,nan ko ta samu
kyautan litattafai harda kudi wadanda aka
gayyata sun bata amam sau ta mika su ga
babanta 2n a can tace kada ma ya sanar da su
haule. Shi kam dadi gurin shi da yake ji har
kwalla sai da yayi,lokaci da take kara2n kusan
dukkan mutanan da ke gurin shi mata albarka
suke yi tare da cewa mahaifanta sunji dadi.
Hakanan makaranta sun sake ji da ita tare da
kaf kaf da ita musammamln malam yunus
wanda ya fito ya nuna mata son da ya jima
yana yi mata,yaki nunawa ne kawai don yana
malaminta,itama ta aminta dashi don dama ko
yaushe burinta Allah ya bata saurayi mai
ilmi,mai tsafta kamar malam yunus. Matan
ajinsu sun sha nuna masa so amma sam shi
baya ko sakar musu fuska,ko yanxun da ya fito
da son da yake ma ikliman yace mata wannan
sirrinsu ne haka nan baya so yan makarantar
su sani don haka in sunxo makaranta duk
abinda zai ma sauran daliban itama haka yake
mata kai ko dukan duka aji baya tsallaketa don
haka babu wanda ya gane sai dai in yaxo tadi
yace tayi hakuri duka da ya mata daxun shima
yaji zafin a jikin shi. Babanta ya aminta da shi
dan haka yana xuwa tadi sau daya a sati kuma
minti 30 yake tafiya. Nfsa kam dariya take yi
ma iklima wai ta rasa wanda xata aura sai
malami,ita dai bata kula ta ba,haule ma ko
yaushe yazo sai tayi mita.
***
A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah su
nfsa anyi jarabawar fita lokacin iklima tana js2
kuma wannan lokacin ne suke ta shirin tafiya
gasar kara2 ta kasa. Nfsa kam ko a dakin
jarabawa sai kallon silin da cixon biro,to bata yi
kara2n ba balle tasan me xata rubuta lokaci na
cika aka amshi takardun suka fita amma
saboda tsabar karya da salo har da buga
kalanda da memo tare da yin party wai an
gama secondary school. Ta gayyato
kawayanta yan karya tare da samari da kuma
wasu maxan da take kiran su
abokanta,mahmuda ma yaje sai dai xuciyarsa
tana cike da mamakin inda nfsa ta samu kudin
yin wannan shagalin da kuma 2nanin ina ta
roro wadannan kawayan?shi kan shi gurin da
akayi partyn yasan dubu30 ake kamawa don
haka ya kosa a tashi don ta amsa masa
tambayoyin sa. Yanmatan da suka halarci
gurin gaba daya ba kawayanta na kuruciya
cikin su daga mama zee sai safina sune kawai
ya sani,su kuwa yanmatan sai zundan nfsa
sukeyi suna mata dariya wai wannan talakan
tilis din take so sai dai dayawansu sunce
kyawun dirinsa gami da kwarjininsa ne ke
rudinta. Bayan an taso ya wuce gda yaxo da
dare bata nan dole sai washegari shima din ya
ritsa ta ne ta caba ado zata fita,nan take ko ta
daure fuska gami da ce mishi ita fa unguwa
xasu je ana jiranta ne. Yace ina kenan?ta
zafga mishi harara da manyan idanunta masu
kara tsuma shi, cikin taunan cingam tana kas-
kas dashi tace sai kaji?yace to ni kuma naxo
da magana,tace lafiya?tana girgiza kafadu in ta
dame ka maganar ka zo da dare. Ya bita da
kallo cikin irin tafiyarta tamkar ana mata kida
ranshi bace ya juya shi kanshi yana jin haushin
kansa irin cin kashin da take masa ya kasa
watsi da ita.
Yaxo bata dawo ba sai kusan tara yana zaune
har xata wuce yace nfsa ta dubi inda yake taja
tsaki sannan ta iso sai da taxo kusa dashi
sannan tace naci yace to ki gaya min in kin
daina sona ne in hakura tace don ina sonka sai
kuma ko yaushe kana like a kofar gidan mu?
kaga nifa na soma gajiya da wannan
tadin,yace to kinga dai 2nda yanxun kin gama
kara2n sai na 2ro ta katse shi da cewa ka 2ro
ina?ai wlh baxan yi auren da nasani ba auran
da iyayena xasu saida akuya ta dawo tana ci
musu danga ba yayi shiru can ya mike yace to
shikenan Allah ya hada kowa da rabonsa cikin
isa da izza tace amin. Lokacin da ya isa gida
ko ganin gabanshi bayayi kafin wani lokaci
zazzabi ya rufe shi sai dai yasha alwashin
koda son nata xaya xama ajalinsa ne sai dai
ya mu2. Ita kuwa ta shiga gda tana murnar ta
yarda kwallon mangwaro ta huta da kuda,cikin
ranta tace ana harkar arxiki waka ba2n tsiya
yanxun da haka kudi ne cikin jakarta naira 20K
saurayin mama zee ya basu 40K ita da safina
suka raba kuma cikin masu sonta da xasuyi
fatin nan daga mai 100K sai mai 50K amma shi
ko ko taro,dakin haule ta shiga ta samu baban
su bai shigo ba don haka ta zube mata kudin
suna kirgawa suna farinciki tana kuma sanar
da ita yanda sukayi da mahmud,taji dadi sosai
tare da sa mata albarka. Sai dai me?lokacin da
taje kwanciya sai zuciyarta ta bijiro mata da
son mahmud din tare da kawata mata suffofin
shi kyawawan lebunan shi masu jan
hankalinta,nan take ta birkice taji baxa ta iya
rabuwa da shi ba 12 na dare 2ni an rufe musu
gida ta sadada ta bude ta fito ko gyale babu ta
isa kofar dakin shi cikin sa'a kofar tana bude
ne 2nda ya shigo ya fada kan katifa bai samu
damar tashi ya rufe ba ta 2ra ta shiga sannan
tayi sallama.ovels BOOK
MABUDIN WAHALA 1***5
Bai jita ba duk da ba barci yake yi ba idanunsa
suna kallon silin ta xauna gefen katifar tare da
cewa mahmud yayi firgigit ya kalle ta ya tashi
xaune cikin daurewar fuska. Me kika zo yi
kuma?tace hakuri naxo baka na sani ko cikin
mafarki ban isa ince xan barka ba kai dai
dinnan kaine i love you so much don Allah kayi
min afuwa yanxun muyi maganar auranmu, ya
mata banxa nan ta shiga kuka wiwi ganin
daren kara yi yake yace to na hakura tashi ki
tafi tace to zo ka raka ni tsoro nake ji,yace to
sai dai ki kwana don bazan fita ba,ga mamakin
shi sai gani yayi ta matso tare da cewa dan
matsa mini,da sauri yace in matsa miki kiyi
me?tace in kwanta da asubahi sai na koma
gida lokacin baba na ya tafi masallaci,ya mike
tsaye duk da zazzabin da yake damun sa muje
in rakaki don nasan hakkin addini na har kofar
gda ya kaita sannan ya dawo,taxo xata shiga
daki babansu ya fito daga bayi yace ke nfsa xo
nan daga gidan uban wa kike?tace na'am a
bayi zan shiga yace karya kikeyi ina daga bayi
ina jin motsinki kina rufe gida ya nufi gindin
murhu ya suri itace jikinta sai bari yakeyi yace
zo nan, ta soma bashi hakuri yace inda kika
fito karfe daya kawai xaki fada min tace kirana
akayi mahmud yace karya kikeyi mahmud ko
goma baya kaiwa ya matso ya cafketa ya shiga
aza mata itace ta shiga kurma ihu dukkan
mutaan gidan suka fito
. Haule tana ta cewa don Allah me yarinyar nan
tayi maka kake dukanta?yace duk wanda ya
matso nan xan targada shi ya jibge ta son rai
da kanshi ya hakura ya kyaleta ya shige daki
haule tazo ta kama ta ta nufi dakinsu da ita
iklima ta kauce ta basu hanya sai kuka take.
Haule na lallashi a hankali don kada ya jiyo su
danlami suka wuce dakin su itama iklima taxo
ta koma makwancinta tana kallon su, haule
tace wai me kika masa ne?ckin muryar wanda
yayi kuka ya gaji tace kirana fa kawai akayi na
fita shi ne ya zi ya hau ni da duka,haule tace
mugunta ce irin wadda ya saba ki barshi Allah
zai saka miki. Iklima tace haba mama yaya
uba zai hukunta yarsa kice... Ta jefa mata fulo
akai rufe min baki yar iska,iklima taja abin
rufarta tayi musu shiru tana jina su suna ta
aibata mahaifin nasu har dai bacci ya
kwasheta bata ma san lokacin da haule ta fita
ba. Washegari kasa fitowa nfsa tayi,tayi
dankam ta doku ranar kam babu yawo sannan
bata daina kuka ba shi ko mahaifin lokacin da
haule ta dawo daki fada ta yayi da fada sannan
yace ya gaji aurar da ita zayayi sadaka, da
sahe kuwa ya tashu danlami yace maza ya kira
mishi mahmuda,ya isa dakin mahmud yayi
sallama ya amsa tare da cewa shigo,suka
gaisa danlami yace baban mu ke neman ka
yace to kace masa ina zuwa. Tafiyar danlami
ba dadewa ya isa gidan sai ga nafiu ya dawo
siyan sugar yace baba yana nan?yace yana
nan, mahmud yace kace ina jiransa a
nan,shigar nafiu ba jimawa baban ya fito.
Mahmud ya zube yana gaidashi baba yace ka
2ro min manyan ka yau,mahmud yace to.
Haka kuwa akayi ya samu mahaifinsa ya
shaida masa sakon surkin nasa, Alhaji ibrahim
yace ka kuma shirya auren ne yanzun?ko ko
dai wani shirmen zamu kuma zuwa muji?
mahmud yace Alhaji ina jin ba2n auran ne dan
ta gama kara2n,yace shikenan zan masu Alhaji
mustapha magana.
Lokacin da waliyan nashi suka je sun gana da
malam usman yace maganar aure ne ta taso
suna so wannan satin ne ko za asa wata daya?
Sun mika sadaki 10K sannan zasuji daga bakin
mahaifin yaron da shi yaron in sun shirya
shikenan. Lokacin da sukazo ma Alhaji ibrahim
da wannan ba2n yace a kira mishi uwargida
hajiya uwa yace kinji ba2n auran mahmud
suna so mu tsaida lokaci shi sakaran ma bance
ya tanadi kome ba,tace a kirashi dan abinda
yake dashi sai

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment