Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasuyi dn hk gaba suka
sa ta suna mata sannu dn dare ya tsala.
Sai kusan karfe hudun asubahi sannan danlami
ya nufi gidan su babasu. Malam usman yana
cikin alwala yaji bugun kofa, sai daya saurara
da kyau ya tbbtar nan ne sannan ya nufi kofa
cike da fatn Allah yasa alkhairi ne ya kawo
koma wanene. Sai daya tmbaya danlgmi ya
tabbtr mishi shine sannan ya bude. Danlami
cikin dmw yace mamanmu ba lfy tn ciki dare,
ciwn ciki, ban zaci xata kai yanxu ba.
Sai kusan karfe hudun asuba sannan danlami
ya nufi gidan su babansu. Mal usman yana
cikin alwala yaji bugun kofa sai da ya saurara
da kyau ya tabbatar nan ne sannan ya nufi
kofa cike da fatan Allah yasa alkhairi ne ya
kawo ko ma wanenen.sai da ya tambaya
danlami ya tabbatar mishi shine sannan ya
bude. Danlami cikin damuwa yace mamanmu
ba lafiya tun cikin dare,ciwon ciki ban za ci zata
kai yanzun ba. Mal usman yace subhanallahi
to bari in dauro alwala muje. Ya koma yayo
alwala ya sanar da mai dakinsa sannan yazo
suka dauki hanya. Shima ya tausaya mata
yace bari suje sallah sai ya roki makocinsa
cewa ya taimaka masa da mota.hakan yayi
sun kai ta babban asibitin minna.sunga likita
emergency an tura su gefen scan sun dawo
likitan ya duba sakamakon tsakuwar ciki
ce,yace musu aiki za'a mata a kwashe amma
sai sun fara bata magani sun taru guri daya
zuwa gobe. Kuma 30k ne kudin aiki. Mal
usman ya dubi likitan da sauri,30k dana?
Likitan yace,eh baba. Mal usman yace asibitin
gwamnati fa. Likitan yace baba suna ne kawai
ace asibitin gwamnati amma ba kayan aikin
komai. Kasan dai shugabannin kasar tamu ba
tausayin talaka. Sun fi son kansu fiye da
kowa.ba sa bamu kayan aiki albashinmu ma
sai an kai ruwa rana muke samu. Kudin
kasarmu suke kwashewa su fita da iyalansu da
kansu waje don karatu ko neman lafiya ko
kuma shakatawa. Mal usman ya nisa yace
haka ne to zanje na bubbuga mu gani. Danlami
yace,mu baba da kudi a shagonmu sai dai
kudin nafisa ne. Mal usman bai tanka shi ba
don shi baya son jin ko sunan an ambata, ya
fita. Yana tafiya Aminu yace ma danlami kirata
ne kawai in ta ce a dauka sai a dauka tinda da
kudin. Danlami ya kira lokacin bata tashi barci
ba,ba ma a gida ta kwana ba. babban hotel
din abj suka kwana ita da wani saurayinta.
Tana daga wayar tace,yaya danlami ya ya ne?
Yace,mama ba lafiya sosai aiki za'a mata
muna babban asibiti, ta mike tsaye da sauri.
Anyi aikin ne? Yace sai gobe,yanzun ma ba
kudi a kasa shine muka ce ko mu cira cikin
naki? Tace,baba fa? Yace ba kudi
gurinshi,amma ya ce zaya buga-buga.
Tace,yaya danlami ku dibi kudi ku canza mata
asibiti na kudi wanda za su yi mata aiki yanzun
nima ina tahowa yanzun. Waye gurinta? Suka
ce su ne,tace ina iklima? Danlami yace bata
sani ba,tsaki taja sannan ta kashe wayar,gida
ta koma ta shiga shirin n minna.
Su kuwa nan suka shiga shawarar yanda zasu
yi. Aminu yace,muje mu dibo kudi kawai mu
canza mata asibiti,ni dama wannan asibitin bai
min ba,ina ganin ba su san aikinsu ba,in ba
haka ba kuna ganin mutum cikin wani hali ku
ce sai gobe? Danlami yace,amma ba ga shi sun
mata allura har ta samu bacci ba? Sannan sun
ce don stones din su taru guri guda ne shi yasa
suka bari sai gobe. Aminu yace to me ka ke
nufi. Danlami ya gyara tsayuwa tare da
dubanta sannan ya dubi aminu. Muje mu
shawarci Baba.Aminu Yace,da mun kyale shi
kana ganin da muka ce ko a kirata banza yayi
mana. Danlami yace,duk da haka dole ya sani.
Gidansa suka koma,sun samu yana karyawa
da koko da kosai,ganinsu ya fadar mishi da
gaba. Yace,ya ya ba dai jikin ba? Suka ce,a'ah,
nan suka zauna sannan suka gaida matarshi.
Suma ta dire masu kwanon koko da
ludayi,basu kalli kokon ba,danlami ya zayyano
mishi komai,kala bai ce ba. Aminu yace,ba ka
yi magana ba? Ya dubi aminun,yanda yake
wani dacin rai,sannan yace shiru ma magana
ce,ya rage naku ku fassara. Aminu ya mike.zo
muje don Allah,lokaci yana tafiya. Danlami ya
yi jim don yasan babansu ba da son ranshi ba
ne,ya mike tare da cewa,baba mun tafi. Yace to
Allah ya sauwake. Suna fita danlami yace da
nafisa,da za ta ji shwara da ta bari,baba ranshi
bai so ba da batun canjin asibitin nan. Aminu
yace,to in ranshi bai so ba ya ya zai yi? Shi fa
ba kudi ne da shi ba,don Allah kada ka kira ta.
Danlami yace,yana da kyau nafisa ta nemi
sulhu da baba. Aminu yace yanzun ba wannan
lokacin ba ne,yanzun batun ciwo muke yi. In ba
zaka canza mata asibitin ba ni na canza mata,
shi fa baba da ka lura ma bai damu da
mamanmu ba ne,in ba haka ba dubi yanda ya
dawo gida yana cin abincinsa don yaga yana
da wata matar.
**Danlami yace wai kai me ke damunka ne? Za
ya kasa karyawa ne don ciwo? Ya soma kiran
layin nafisa,tana dagwa tace,ya ya jikin dai?
nima gani nan ina shiri. Yace da sauki dama na
kira ne in ce maki ko zamu bar Mama anan
asibitinne domin ran baba bai so ba..." Ta
katse shi,don Allah ya danlami bana son in
rasa uwata,ku canza mata asibiti in don ra'ayin
nan na baba ne sai ta mutu yana nan yana
kaza yake so kaza ke bai so. Danlami yace shi
kenan. Sun kaita asibiti mai tsadar gaske inda
aminu yaje ya dibo kudi suka zube kafin kace
hka kuwa kuwa tuni sun mata aiki sun fito da
ita. Daya saura nafisa ta iso. Nan tasa suka je
store dinta suka yi ta jido kalolin juice da ruwan
sha. Ta tura su gidan abinci mafi tsada suka
yo musu oda,tana bacci suka yi ta ci tamkar
suna gida. Ita kuwa iklima bata sani ba,can
matar babansu ta tuna ta kira nafiu tace,maza
ka je ka sanar da iklima. Tana kokarin shiga da
kuloli daki ta gama kwashe abinci kenan ya
shigo. Tace,nafiu shigo,kai ne da rana haka?
Mahmud na bakin gado ya dawo cin abinci
lokacin nafiu yake cewa,mama ba lafiya tana
asibiti za'ayi mata aiki. Iklima ta dafa kirji tana
cewa,aiki? Mahmud sai yaji kamar nafiu
yace,baba ba lafiya don haka da sauri ya fito
yana cewa,baban za'ayi wa aiki? Iklima duk ta
rude ta kasa magana. Nafiu ne yace mama na
ce. Mahmud ya ce,ayyo sai na ji kamar kace
Baba. Ya koma ciki yayi zamanshi har
zuciyarshi ya ji da sauki tunda ba Baban ba ne.
Yanda yayi abin yayi ma iklima ciwo,bata so
yanda yake nuna ma mahaifiyarta ko cikin
magana ne in ana batun iyaye sau da yawa in
ta ce "mu ma haka mamanmu kaza" sai ya yi
tsaki musamman in ta fadi wani abin kirki na
maman tasu, ta zuba ma nafiu abimci yaci
sannan tace ina nan zuwa wane asiniti ka ce
ma? Yace ban san asibitin ba,baba ne kawai ya
sani. Tace,to zan zo ta gidan in ji. Bayan
tafiyar nafiu ta shiga dakin fuskarta daure,ta
jera masa abincin sannan ta dawo falo ta
zabga tagumi. Ya gama ya watsa ruwa ya fito
har zai fita sai kuma ya dube ta. Lafiya ki ka yi
wani zugum? Ta dube shi hawayen da take
makewa suka zubo,ta ce a zatona mahaifiyata
mahaifiyarka ce. Yace,to me aka yi? Ranta ya
sake baci,tace ba'ayi komai ba. Ya zauna,kin
san dai bana son bacin ranki ko? Ta dube shi
cikin kukan shagwaba ta ce,sanin kanka ne ba
ka min adalci akan mahaifiyata,bana son
yanda kake nuna tsanarta karara.albarkacin
auranmu komai tayi maka ai ka yafe mata.
Ya riko mata hannu"ban tsane ta ba,don bata
min laifi ba."ta matsa mashi hannu,"meyasa
ka nuna ko in kula da kaji an ce bata da lfy?"ya
saka dayan hannunshi yana share mata
hawaye tare da cewa,"shi kenan yi hakuri,kiyi
wanka muje tare,zan amso mashin din
Hamza.hakan yayi maki?"Taye dan murmushi
tare da daga gira.Mashin din Hamza ya amso
ta shirya suka fita,ya dauke ta a mashin.Ko
yaushe za su fita yakan so tayi ado,amma ita
koda tayi a don sai ta rufe jikinta ruf,sannan
tasa nikabi.Yasan a musulunce ta fi shi
gaskiya,shi yasa baya magana.
Gidansu suka je,matar Babansu ce ta shaida
musu sunan asibitin,don lkacin da Danlami ya
dawo ya shaida mata asibitin da suka canza
mata Baban ya fita. Mahmud ne ya gane
kwatancan asibitin,don haka suka dau hanya.
Za su shiga Aminu za ya fito don Nafsa ta aike
shi ya sai mata kati,shi ne ya nuno masu dakin
daga nesa ya wuce. Suna tura kofar da Nafsa
suka soma tozali,dukkan su sai da gabansu ya
fadi. Ikilima tunda Nafsa ta bar gida kafin
auransu sai yau ta kara ganinta
Nafisa tana rike da waya me shegen tsada, tayi
kyau ta kara kiba ta xama hajiar sosai, jikinta
sanye da wani leshi me tsadar gaske. Sai da
ikilima taci tuntube dn faduwar gaba. Mahmud
yayi saurin taro ta xuwa jikinshi tare da cewa ki
lura da kanki mana my baby". Wayar dake
hannun nafira ta subuce ta fadi kan kafafun
haule dake kwnce sharkaf kan gado, idanunta
sun tsayu kan mahmud shi kuwa tmke fuska
yai tamkr be taba daria ba. Ikilima ta isa kusa
da ita ta dafa ta tana cewa sannu anty nafisa.
Firgigit tai kafin ta kalli ikiliman, sannan ta
daure fuska. Ikilima tace ina yini anty nafisa, ya
jikin mama? Nafisa cike da masifa tace Yini bn
ganshi ba, jiki km gashi nan ki tmbyeshi. Ta
sake kallon mahmud, wnda fuskarshi ke daure
yana kallon ikilima.a kauda kanta gefe, yaxo ya
janyo kujera ya kamata ya dorata akai ta
xauna, yai kasa da murya yace, bana so kina
dmw kanwata, ki zauna zanje na dawo tnda
tana bcci. Ikilima ta dube shi da murmushi, to
sai ka dawo. Ka kular min da kanka kaima. Har
ya kai bakin kofa zai bude sai ya kuma
dubanta. Ya dawo ya sunkuya ya sumbaci
lebunanta tare da shafa cikinta ya mike ba tare
daya kalli ko inda nafisa take ba ya fita
abinshi.
Nafisa ta diro dg bakin gadon cikin tsananin
kunan rai, ta shiga sintiri a tsakar dakin ji
takeyi tmkr ta shake ikilma ta kashe. Dukkan
abubuwan da mahmud yai ma ikilima ynxun
nan su ne suke yawo cikin idanunta da
kwanyarta. Ta dubi ikilima tana hura hanci. Ta
nuna ta da yatsa "ke maci amana, macuciya.
Ta soma hawaye. Kinci amanata kin auri
masoyina, kina so ki nakasa rywta. Ta matso
gabanta kinyi karya, lkci be kure ba ki rabu da
mijina. Ikilima ta dubeta cikin harara, mijinki?
Mijinki fa kika ce? Itama ta mike tsaye mijinki
na can inda kika baro shi, mahmud nawa ne
har abada. Ta sake zama kan kujerar, ta cgb
da cewa bn cuce ki ba, kece kika cuci kanki
kika yaudari kanki, kika br abin sonki kika auri
kudi.
Nafisa ta sauke mata mari mai karfi a kunci,
daidai lkcn aminu ya shigo km marin shine yai
sanadiyar farkawar haule dg bcci. Ikilima ta
dafe kumatu, ni kika mara yaya nafisa, me nayi
miki? Aminu ya isa gurinta yana cewa nafisa
meya faru ne? Bata kula shi ba ta cgb da cewa
baki ma san me kikayi ba ko? To ki sani dole
ne ki bar min mahmud din yar iska kawai.
Ikilima tace ni ba yar iska bace, km da ace
farkon auran mu kikaxo da wannan bidi'ar kila
in yarda, amma ynxun da sakonninsa suke
yawo dani a sararin samaniya, Allah daya bani
shine kawai zai iya raba mu da juna ba dan
adam me kashi ba. Nafisa ta sake zaburowa,
aminu ya riketa. Kiyi hkri kece babba. Ya dubi
ikilima, baki da kunya ko? In tashin hnkli ya
kawo ki mu ba shine a gabanmu ba, tashi ki
kama gabanki. Tai shiru bata ce komai ba.
Nafisa sai zaginta takeyi tare dayi mata
mugayen kalamai.
Nafisa ta sauke mata mari mai karfi a kunci,
daidai lkcn aminu ya shigo km marin shine yai
sanadiyar farkawar haule dg bcci. Ikilima ta
dafe kumatu, ni kika mara yaya nafisa, me nayi
miki? Aminu ya isa gurinta yana cewa nafisa
meya faru ne? Bata kula shi ba ta cgb da cewa
baki ma san me kikayi ba ko? To ki sani dole
ne ki bar min mahmud din yar iska kawai.
Ikilima tace ni ba yar iska bace, km da ace
farkon auran mu kikaxo da wannan bidi'ar kila
in yarda, amma ynxun da sakonninsa suke
yawo dani a sararin samaniya, Allah daya bani
shine kawai zai iya raba mu da juna ba dan
adam me kashi ba. Nafisa ta sake zaburowa,
aminu ya riketa. Kiyi hkri kece babba. Ya dubi
ikilima, baki da kunya ko? In tashin hnkli ya
kawo ki mu ba shine a gabanmu ba, tashi ki
kama gabanki. Tai shiru bata ce komai ba.
Nafisa sai zaginta takeyi tare dayi mata
mugayen kalamai.
Aminu sai lallashinta yake yana bata hkri,
dayake ance me kudi bashi da wa sai kani.
Ikilima kuwa sai kuka takeyi domin haule ma
da take kwnce tana mgn da kyar fadi take
mugun halinta irin na ubnta ne, don Allah ta
fitar mata bata son ganinta. Nafisa na cewa ki
rubuta ki ajje sai mahmud ya dawo hannuna
sai kin wulakanta... Daidai nan mahmud din ya
shigo. Bakin kofa ya tsaya idanunshi kan
ikilima, km yaji maganganun da nafisan ke
gaya mata. Ranshi na zafi ya isa gareta. Tashi
muje gida. Ya mikar da ita, ta share hawayenta
da bayan hannu sannan tace ka gaida mama
ta farka. Ya dubi gadon, yaya jiki? Banza tai
dashi, nafisa ce tace ana gaisheki. Haule tace
da sauki. Ikilima ta kalli maman mun tafi
mama, sai na sake zuwa. Bata tnka ba, ya
kama hannunta suka fita.
Nafisa ta bisu da ido, wani tukuki take ji cikin
zucia, ta daga labule windon tana kallon ynda
yake share mata hawaye tana kuka, sannan ya
taimaka mata ta hau mashin din, ya tada suka
tafi. Ta runtse ido wasu zafafan hawaye suna
zuba. Shedaniyar zuciarta ta shiga raya mata
cewa, ta raba su ko ta halin yaya. Ta xauna
kan kujera tare da share hawaye, aminu yace
nafisa ki daina damun kanki kan wannan
mahmud din, har ynxu fa yana nan ynda kika
sanshi bai kara komai ba sai ma kara
tsiyacewa da yai. Ta kalli aminu, ai ynda ban
aure shi ba itama dole ta barshi sbd ina son shi
ynxun.
Gidansu haule ta koma ta kwnta dn samawa
zuciarta mafita, abinda take yawan tmbyr
kanta shine, ynxun mahmud ya daina sonta?
Ko ko yana so ya rama abinda ta mishi ne?
Wata xuciar tace ikilima yake so da baya sonta
ba zai yi mata ciki ba, dubi ynda koyaushe
idanunsa ke kanta, kalli kulawar da yake mata.
Ta tuno irin sumbar da yai mata a gabanta,
abinda taso yai mata tuni yace sai sunyi aure,
gashi yana yiwa kanwarta a gabanta. Da yake
hausawa sunce laifi tudu ne, ka take naka ka
hngo na wani. Sai ta furta a fili cewa mahmud
kaci amanata, ka cuce ni. Zuciyarta tace A'a
kece kika cuci kanki, gashi ynxun kina dana
sani. Dubi ynda yake nuna so da kulawa ga
yar'uwarki, kin zabi kudin da bana halak ba ga
zunubin ludu da zina su kuwa suna cikin ryw
me tsafta.
Wata zuciar tace zafa ki same shi in kin dage,
ynxu ki nemi mafita ne ta ina zaki fara? Tai
shiru tana son ta tuno ta ina zata fara din.
Shedaniyar zuciarta tace to bari in tsara miki
ynda zakiyi in dai zaki bani daki-daki, to zaki
cimma burin rywrki. Ta sake rungume filo dn
saurare tare da hawa dokin zucia. Zuciar ta
cgb da sheda mata cewa kisa a kona dan
shagon da yake takama dashi, sai ki bude
mishi ido da kudi, ki nuna masa su zunzurutu
hr ynxun yana sonki zai aureki sai ki kashe
auren ke in hk bata samu ba ma ki kai shi gurin
bokanku mana. Ta sheke da daria, tabbas dk
wadannan mafita ce km shawara ce amma
zata fi so tasa yan daba ta basu kudi su kone
shagon ko don ikilima ta kuntata.una?
MABUDIN WAHALA 2**6
Har suka shiga daki ikilima hawaye take
zubarwa, don dai idanunta na rufe ne cikin
nikab shi yasan kuka take sbd yana jin
shessheka. Ya rungumo ta zuwa jikinshi. Haba
ikilima, nasan kin saba da halin nafisa, don
tace sai na rabu dake na aureta sanin kanki ne
tatsuniya take yi. Wlhy ko mata sun kare bazan
aure ta ba, ynxun na daina sonta kece nake so.
Ya cire mata hijabi ya cusa hannunsa cikin
zaninta yana shafa cikinta. Kece uwar babyna
da kannansa. Ya soma share mata hawaye.
Haukanta take yi kada kisa komai a ranki.
Ikilima ta dube shi, har fa marina tayi. Da sauri
yace mene? Mari? Matata? Ya mike sai na ramo
miki. Tace ai na yafe ka barta kawai. Ya
rungumeta tare da cewa alkawari ne sai na
gargadeta kar ta kara, dk lkcn da muka hadu.
Ya zaunar da ita akan kujera tare da cewa, bari
in nemo mana na karin safe tace to Allah ya
bada sa'a.
Kusan hudun dare yake jin bugun gida sama
sama. Lkcin daya fito dukkan mazajan gidan
sun fito tare suka nufi kofar kowa yana kissima
dalilin bugun kofar. Shi dai mahmud yafi raya
babanshi ne ko maman su ikilima. Suna bude
kofar sai gasu musa kannanshi suka ce wuta a
shagon shi. Nan suka dunguma, tsayawa
kawai sukayi suna kallon wutar, sai ci takeyi
har ta soma kama gidan da shagon yake.
Mutane ne sukayi ta gudunmawa da ruwa har
dai yan kwana-kwana suka zo. Cikin sa'a aka
kashe wutar, sai dai ta lashe komai har ginin ta
rusa, tnda da fridge a shagon kun san gas. An
km rasa musabbabin wutar, sai dai anfi ba
wutar nepa. Gida ya dawo su da mazan gidan
nasu suna jajanta masa, har lkcin ikilima tana
bcci gashi wasu masallatan sun tada sallah.
Yayi alwala, sannan ya tasheta shi km ya nufi
masallaci. Tana azkar ya dawo, ta gaishe shi
ya amsa, ya zauna shiru. Tace au, na manta
bari in tashi in shirya zamu asibitin kuwa? Ya
dube ta a sanyaye, Eh, zamuje. Tace baka jin
dadin jikinka yau ne?
Yan jaje suna ta zuwa, babanshi ma har gidan
yazo, yace yazo da dare yana nemansa. Haka
nan babansu ikilima yazo har yake ce mata na
shaida ma mamanku danaje asibiti dazun.
Ikilima tace to. Abokanshi sun hada mishi dubu
goma, kowa dai dai don ma wasu basu da kudi,
yai godia sosai dasu ya sai musu kayan abinci.
Sannan da dare yaje gurin mahaifin nashi.
Alhajin ya sake jajanta masa, sannan ya soma
da cewa, na kira kane don muji yaya za'ayi?
Tnda kaga nima ynxun lamuran sun danyi
tsauri, sana'ar tamu ba kasuwa irin da. Mun
rage yin tafiye-tafiyen ma, don fatun ma in mun
kai su sai dai bashi, ynxun da hk motata ta
tsaya dk lamarin na kudi ne da sai a gyara
shagon amma kai yanzun menene tunaninka?
Mahmud yai shiru dn dama shi da mahaifinsa
kawai yake takama, km hakika ya tbbtr
mahaifin nashi ba kamar da bane. Ya nisa
Alhaji sai dai mu cgb da addu'a, Allah zaya
kawo mafita, domin uwar da ribar duk suna
shagon, hatta kayan abincin mu suna ciki. Alhji
ya jinjina kai tare da cewa "Allahu Akbar, to
zamu ga ynda za'ayi. Tashi kaje amma ka
shiga gurin su hajia su auna maka shinkafa ka
dibi doya yace a'a abokaina sun hada min
dubu 10 na siyo kayan abinci, yace to madalla
tashi kaje Allah zai bada ynda za ayi.
Lkcn daya shigo gidan ikilima tana zaune kan
sallaya tana addu'oi, ta shafa ta mike tana
ninke sallayar tana kallonshi da murmushi tare
da cewa, sannu da shigowa. Yace yauwa. Ta
kawo mishi abinci ya zabga tagumi, ta zauna
tana zuba mishi cikin filet, yace yayi yawa fa,
tace ni sai ka cinye, tnda abin nan ya faru baka
wani cin abinci, meyasa kake dmw ne? Ya dube
ta, ikilima na tsani yinin nan da nake a gida ba
abin yi, in na fita sai dai gurin abokai.
Ta koma kusa dashi ta kwntar da kanta a
kafadar shi, niko ina son inta ganin gani ga ka
koyaushe, yauwa zan baka wata shawara zaka
samu abinyi, ci abincin tukunna. Haka tayi ta
jan ra'ayin shi har yaci ya koshi, sannan yace
to fada min. Tace zan fada maka sai munje
bcci, ynxu yi wanka dai ga ruwan can. Da yake
madafa yake nema ranar da wuri ya kwnta, tayi
ta jan shi tare dayi mishi abubuwan da suka sa
shi kai mata sakonnin shi domin tnda ya shiga
wannan halin baya iya yin wani abu na nishadi,
sai da suka nutsu sannan yace ikilima ba zaki
fada min shawarar ba? Tace, yauwa ynxun
zaka fi fahimta ko? Ta cgb, ka kwashe fridge
dasu T.V duk kayan wutan mu dai ka saida
kaja jari. Yace to ai ko gyaran shagon bazasu
isa ba. Ko yaushe na kalli cikinki ina dmw, ba
mu sayi komai ba. Ta rungumeshi "Allah zai
kawo. Da safe ta matsa mishi ya amso mashin
suje asibiti taga mamanta, yace a'a tace to in
bazaka ba ni ka bar ni inje ko a kafa ne. Jin dai
ta dame shi hk nan ya aro mashin suka tafi.
Haule taji sauki dn har ta soma dan cin abinci,
ba da wata kulawa ta ishe su ba ta dai yiwa
mahmud jaje. Nafisa ta shigo ikilima ta
gaisheta da kyar ta amsa ta zauna bakin gado
ta bude jakarta ta ciro daurin yan dubu dai-dai
guda 2, ta dubi mahmud ya akaji da abinda ya
faru? Ya hade fuska, ikilima tace yaya tana
maka mgn. Yace da godia. Ciki ciki yai magnr.
Ta mika mishi kudi, ga tawa gudunmawar,
Allah ya kyauta gaba. Ya dube ta cikin matukar
daure fuska, kin samu lbrin ina neman taimako
ne? Cikin daburcewa tace A'a, amma ko dn
ikilima kanwata ai zan baka gudunmawa.
Yace to bana so. Hatta ikilima bataji dadi ba,
ta dube shi, ka amsa mana yayana yace kin
nemi wani abu kin rasa ne? Ta girgiza kai.
Haule tace bar kudinki dama sai dana ce kada
ki bashi. Ta dube shi kin san talaka bai iya
iskanci ba inya tashi yi. Nafisa ta katse ta,
mama ba ruwanki nace don Allah. Ta sake
duban mahmud din to zan nemo maka aiki, ka
fahimta? Don ikilima zanyi. Ba tare daya kalleta
ba yace ikilima in xaki tafi tashi muje in km naje
na dawo ne to? Ta ce jeka dawo din. Ba tare da
ya sake magana ba ya fita. Dakin yai shiru na
wani lkci, haule ta sake cewa, matsiyaci, ko an
sa shi a tandun mai haka zai fado fari kwal.
Tnda yace baya so ki kyaleshi. Ikilima tace
yaya nafisa mun gode. Zan shawo kanshi a
hnkli. Nafisa tai shiru xuciarta na zafi, wlhy da
ba don ikilima yaruwarta bace sai tasa an
kashe ta. Amma ynxun tnda tana neman sulhu
dashi har ta samu ynda zasu dinga hulda dole
sai tabi takan ikilima.
Ta dubi iklima,kanwata duk abinda ya faru ina
fata ya wuce? Iklima tace ba komai,dama ban
rike ki ba domin na san aikin shedan ne.
Tace,to ina muku jajan abinda ya faru. Sannan
na tausaya mishi yanda su Aminu ke bani
labari. Iklima tace,wlh. Nafisa tace yanzun me
ku ke bukata? Tace sana'ar dai ce in ba ita ba
bamu da matsalar komai. Nafisa tace,zan fi
son ya kawo takardunsa in nemar masa
aiki,wlh in CBN yaje so zan samar masa kuma
babban matsayi. Iklima tace zan lallaba miki
shi insha Allah zamu zo tare. Nafisa tace,likitan
ma yau zai sallame mu da dare in ya yarda
gobe sai ku zo don jibi zan wuce abj. Tace to.
Ta mika mata daurin kudin guda daya,ga
wannan kwa dan ringa batarwa ko. Iklima ta
amsa tare da godiya. Dama ba mu da ko sisi
cikin dakin,in na lallaba shi zai amsa. Nafisa
tace,ba komai. Daf da magrib ya dawo,bai
shigo ba wata ma'aikaciyar shara ya aiko ta
kira ta,nan tayi musu sallama ta fito. Nafisa ta
biyo ta da harara ita kuwa haule tsaki taja tare
da cewa,dukkanku haushi ku ke bani,an taba
abu dole. Tunda yace ba ya so ai babu dole a
ciki.
Tunda suka dawo ta rasa ta ina zata soma yi
masa zancan.har ya soma bacci tace,don
Allah tana son suyi magana. Ya tashi zaune,ta
ce dama kan wannan ne am.ya katse ta da
cewa"ki mun magana mana bacci nakr ji. Ta
kama hannunshi,yaya nafisa ta ce ka kai mata
takardunka zata samar maka aiki ta hanyar
mijinta ni a ganina ba wani abu ba ne.ya
kamata yanda ta bar komai kaima ka bari
dazun har hakurin abinda ta yi min rannan ta
bani. Ta kalle shi sam tana ta zuba bata san
ya cika yayi dam haka ba tamkar ya doke ta
yake ji. Ta daga filo,ga ma wannan tace muyi
cefane dama ba mu da sisi a dakin nan. Ya
tashi zaune da sauri ranshi bace ya suri filo ya
fita ya bar ta zaune da kudi a hannu. Ta biyo
shi ta zauna gefen kujerar da ya kwanta.
Yayana don Allah ka. Ya katse ta da cewa ke
mara hankali,in kin sake min magana zan
kashe miki fuska da mari. Ki gaggauta fitar min
da kudin nan daga dakina ko in bala'in bata
miki rai. In har zan kwana a dakin nan to kuwa
kudin nan ba za su kwana ba. Ta yi shiru cikin
jin haushi,me yasa shi sam ba ya fahimta ne?
Nata ganin bai dace yayi gaba da danginta ba.
Cikin zumbura baki ta ce,to ni yanzun ya ya
zanyi da wannan kudin? Yace,oho miki,ni dai
ba zasu kwanar min a dakina ba. Ta saka
hijabi ta fita dakin maman ummi ta kwankwasa
mijin ya bude ya fito tace daman gurin maman
ummi na zo. Yace,to. Yaje ya taso ta,iklima
tace,yi hakuri na tashe ki daga bacci.don Allah
kudin nan zaki dan adana min zan amsa da
safe. Ta ce,to nawa ne? Dubu dari ne. Inji
iklima. Ta juya duk da hakan da iklimar tayi bai
sa mahmud sakin fuska ba. Nashi ganin iklima
bata da hankali,a ganinta Nafisa ba da biyu
tayi mishi wannan kyautar ba. Koda zuciya
daya ne baya so. Dama bata san darajar ta ba
ne yasa shi jure miyagun kalaman da
mahaifiyarta ta gaya mishi ba. Har zuwa washe
gari bai kuma shiga harkarta ba. Da safe kuwa
ko karyawa bai ba,yana yin wanka ya fita sai
dare ya shigo, nan ma sallama kawai ya yi,
sannun da ta mishi sai da ya gimtse fuska
sannan ya amsa.
Ita kuwa Nafi jin su shiru basu zo ba sai tasa
Aminu ya kawo ta gidan bayan magrib. Iklima
ta idar da sallah kenan ta zabga tagumi tana
tunanin yanda zata shawo kan mijin nata. Sai
yanzun itama ta ga wautar ta,tun a can

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment