Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a harhada a hada lefen basu
suka cinye kudin nashi ba? Alhaji yace kada
kiga laifinsu shi ne ya bada. Akayi kiran
mahmud yazo ya zauna tare da gaida
mahaifan nasa cike da ladabi, Alhaji ya
zayyana masa halin da ake ciki, mahmuda
yace ina ganin a saka auran wata 5 or 6 kafin
lokacin mu shirya cikin tsanaki yanzun wallahi
bani da komai,hajiya uwa tace hakane kaga
zai je ya sanar da mahaifiyarsa don itama ta
shirya yanzun taji ance biki sati ko wata baza
ta ji dadi ba. Alhaji yace watan sha daya kenan
in an barshi wata biyar?sukace eh yace to
shikenen nima lokacin nake saka rai da zuwan
wasu kudi sai afi jin dadin yin sha'anin.
Lokacin dasuka samu malam usman da ba2n
ba haka yaso ba son shi ayi auran cikin satin
amma ba dama ya nuna yarshi ko matarshi
basu da hali don haka sai aka sa rana
wata5,ko su haule bai sanar dasu kome ba sai
da aka kawo kayan sa rana sannan sulka sani.
Nan fa haule ta shiga masifar cewa ita bata
amince ba ya za ayi ba a shawarce taba za a
saka rana?shi kuwa maigidan yace wannan ba
damuwarshi bace sannan shi baya ma so ta
amince. Ita kuwa nfsa ranar ta rasa me zata ce
don damuwa,tasan tana son mahmud amma
haka zasu zauna cikin babu?kowa fa yasan ta
da son babban gida da babbar mota,a halin
yanzu kawayenta ma sun koma kiranta babban
gida da babbar mota xata sha kunya gurin
kawayanta. Sun kebe da haule sun yanke
shawarar cewa su nuna sun yarda in yaso
kafin bikin sai ta fito da wani mai kudi ta
tubure. Ga mahmud murna ba a magana ranar
da yaxo gurin nfsa cikin murna itam bata nuna
mishi komai ba sai da aka kwana2 ranar taje
gurin wata kawarta a poly taga rayuwar yan
makarantar sai ta kwadaita ma kanta don haka
yana zuwa ranar tayi kici kici da ranta,yaso jin
dalili tace tana son shiga poly ne,gabanshi ya
fadi yace ki bari sai munyi aure tace ni dai
yanzu nake so daman nasan baza ka iya
daukan dawaiyniya ta ba kamar yanda kace,2n
yaushe rabonka da yimin wani abin arziki?
shiyasa nake shakkar yiwuwar auranmu. Nan
take ya daburce yace to yanxun ina ta jigilar
hada kayan auran mu ne fata yamutsa fuska
tare da cewa dama ka daina hada kaya don ni
yanzu gaskiya poly zanje,to yaya ma za ace
kana hada kayan aurena ba zaka zo muje
kasuwar tare in zaba ba?don fa ni ba auran
duhun kai zanyi ba. Ya danne damuwarshi
yace to yanzu yaya za ayi? Ta yarfa hannaye
dabara ta rage ma mai shiga rijiya ko ya bi ta
kai ko ta kafa nifa vazan yarda in wahala
ba,wallahi kaji na rantse ina da masu kudin da
yanzun innace su fito zasu fito kuma in
university nace ina so zasu kaini,ya shiga
share zufa yace shiyasa nace ki kawo mana
shawara,ta mike ta kakkabe zaninta bani da
wata shawara illa ince na baka 2wks in babu
ba2n makaranta kafin form dinsu ya kare zan
canja sheka eh ni bazan cuci kaina ba kai babu
sana'ar kirki ni babu ilmin da zan taimaki
yayana. Zan2kan suna soya ranshi wata
zuciyar ta shiga mishi fada kan dole ne auran
me yasa ba zaya canza da wata ba?duk irin
matan da ke nuna suna sonshi saboda ita ya
bata da duk abokanshi don sun gaya mishi
gaskiya ita ba yarinyar kirki bace ya rabu da
ita. Ya dube ta in da take tsaye kanshi tana
cewa kai nake sauraro dan gida zan shiga,yace
shi kenan za a nemi form din amma baku fa
amshi result ba tace kai kasan shi ni nayi nan
Ranar mahmud bai runtsa ba ya rasa inda zaya
saka kanshi ya saka wannnan ya kwance
wannan 2naninshi ina zayaje ya samu kudi ya
sani duk kudi sune matsalar nfisa inda yana da
su da 2ni sunyi auran su,ya yanke shawarar
xuwa kwantagora gurin mahaifiyar shi yasa xat
bashi wani abu,yaje ya sanar da ita cewa dama
yaxo ne ya fada mata ba2n auren nashi tace
ansa ne?yace ansa wata 5 gashi shago ba
kasuwa ba kaya ma dai xance Alhaji yana
iyaka kokarin shi shi ne nake son in sami
abinda xan tada jari mama tace nafisar ce dai
har yanxu?mahmud ya dube ta ita ce mama ta
gyara xama tare da dan jan tsaki ni dai
wannan yaron da ka hakura da nafisar nan
domin na samu labarin su ita da uwart ba
mutanan arziki bane,kawata hajiya hauwa dake
bayan layin ku ta sanar dani kome game da
yarinyar wahala kawai xaka dibar ma kanka
yace ki daina sauraron zuga mama kuma ma
yanxun an rigaya manya sun tsaida magana
sai ince na fasa?tace guda nawa akayi haka?
ya sunkuyar da kai tare da cewa ki dai min
addua tace ko yaushe muna kanyi tace to sai
dai in sai da Sa na guda 1 ko filina dake nan in
baka yace gara dai filin mama zaya fi,tace shi
kenan, da zai tafi ta kawo takardun fili ta bashi
yaxo ya samu dillalai aka saida 300K ya
dankara kayan shago sauran kuma ya shiga
fafutukar nemar ma Nafisa poly.s BOOK
MABUDIN WAHALA 1***6
Daga baya ita ce ta samo gurbin kara2n Daga
baya ita ce ta samo gurbin kara2n da
kanta ta hanyar kawarta da ta hada ta da wani
lecturer wanda sai da ya gama lalacewar sa da
ita shi kuma mahmud yana ta barin kudi. Kai
wanda yayi nisa baya jin kira mahmud ya kasa
gane wacece nafisa,tana dai xuwa makarantar
ne don kawai ace mata yar poly,shigarta gurin
ta kara zama wayayyiya a ganinta sai dai cikin
kwanakin ta soma kasa gane kanta sai amai
da kasala,mahmud yazo suje asibiti amma da
kasala,mahmud yazo suje asibiti amma sai
haule tace ai shawara ce ba sai anje asibiti ba
xata dafa mata huntu,ya dai jibgo lemo da
ayaba kullum kuma zai zo sau 3 a rana. Nfsa
ta damu kwarai a zubar da cikin da likita yace
3 months 2naninta in mahmud ya san3 months
2naninta in mahmud ya sani
shikenan sun rabu har abada don koyaushe
burinshi randa zai bude littafinta ba,bai sani ba
2ni wasu sun bude har sun karanta ba. Haule
tace wa iklima in taji zancan a wani guri sai tace
wa iklima in taji zancan a wani guri sai ta
kashe iklimar 2nda ba a kanta aka fara ba
kuma dama Allah ne ya kaddara mata haka
tsautsayi ne don wannan ba halin nafisar
bane,iklima tace mama ki daina cewa Allah ya
kaddara ma ya nafisa domin shi ba azzalumin
sarki bane sai wanda ya zalunci kansa inda
fyade akayi mata sai ace ba laifinta bane,
haulke tace ke dai kika sani mu gobe ma war
yanzun mun fidda abin banza mun huta. Wa
iyazubillah inji iklima mama kada kuyi haka
laifin zai zama 2,yaya zaku ce da Akkah ranar
gobe kiyama?me zaku ce da ran da kuka
kashe in ya tambayeku dalilin kashe shi a
rankashe in ya tambayeku dalilin kashe shi a
ranar
sakamako? Haule ta jefe ta da murfin kwano yi
min shiru shegiya ai ke nan gaba ma kila kice
mu kafirai ne ba wanda ya isa yayi wani motsi
yanzun kya ce ba haka musulunci yace
ba,kada ki manta mune muka haifeki laifi
wanene baya yinsa illa muy istigfari, iklima bata
daddara ba ta sake cewa ni nafi son kuji tsoron
Allah fiye da mu2m,ina so mu shiga gidan tsira
tare daku. Nafisa da ke kwance tana ji da ganin
abinda ke faruwa tace kyaleta haule,so take inji
kunyar duniya kuma bazan ji ba,iklima tace
kema kina cikin matanan da suke cewa da
kunyar duniyya gara ta ta lahira,kun san
kunyar lahira kuwa? Haule tace tashi ki fita
daga nan! Iklima ta mike cikin takaici tasan ba
mahmud bane abokin lalacewar nafisa shi ya
shanya baki zai auri budurwa. Sunyi nasarar
kwakwale cikin duk da tasha wahala tazo taci
gaba da jinya har ta warke sarai tamkar batayi
jinya ba,sannan aka dora daga inda aka tsaya,
Allah ka shirye mu.
Iklima yau ce ranar tafiya gasarsu wannan
lokaci har sabon dinki baban su yayi mata da
hijabi da takalmi. Goma daidai aka soma
gabatar da gasar,lokacin da aka zo kanta taje
cike da kwarin gwiwa don malam yunus in
yazo zance girinta bitar kara2 sukeyi yana
mata yan gyare gyare,cikin ikon Allah wannan
karon ma iklima usman tana kokarin zuwa ta
daya,ga zazzakar muryarta in tana kara2 gurin
tsit yakeyi tamkar kada ta daina,suka rage tsit
yakeyi tamkar kada ta daina,suka rage ita
da wani yusuf Adam dan kano state a karshe
tazo 1st shi kuma 2nd,iklima si ta samu kanta
da yin kuka da kawayenta lokacin da al'umma
suka shiga daukanta hoto yan jarida suka
baibayeta yan agaji suka shiga bata kariya ta
musamman,mahaifinta ma sai da yai kuka don
dadi nan take aka shiga raba kyautuka ga
dalibai da sukai nasara. Iklima ta daya an saka
mata alkyabba kyauta daga sarkin
garin,gwamnan jihar ya bata kujeran makka ga
tsabar kudi 300K a sai mata kayan daki in ta
tashi aure banda littatafai na addini ga kuma
kyautuka daga wasu mutane daban. Kafin kace
kobo gidajan radio sun shiga labarta yanda
abin ya kasance talbijin kuwa nunawa
sukeyi,nan makota suka ta shiga yiwa haule
murna daga nan aka wuce da iklima islamiyyar
su tare da sauran daliban. An sake tabbatar
mata da cewa ita xata wakilci kasar nan don
yin na duniya,an sanar da haule harda
rungume iklima sai murna take yi tasu ta samu.
Nfsa ma sai murna sunji ba2n makka tace
haule ya kamata kice ta baki kujerar makkan,
haule tace ai dama in ta kuma cin wata gasar
taje,iklima dai tana jin su bata ce komai ba.
Koda makaranta suka bata duk abubuwan da
ta samu,yunus ne ya bata shawara ta dan ba
makaranta wani abu, 100K ta bada sannan
sauran komai ta mallaka wa mahaifinta shi
kuma yace ta ciri wani abu ta bari a hannunkuma
yace ta ciri wani abu ta bari a hannunta
sai zannuwan da ta samu daga wasu yan
kasuwa ta bawa su haule da nfsa itama ta
dauka duk haule bata damu ba don iklima bata
bata kudi ba don koyaushe burinta naga
kujerar makkan nan. Sai dai bata san lokacin
da aka bukaci passport ba 2ni iklima tace
mahaifnta yaje yayo ya bada sannan ya dawo
ya shaida ma haule nan ta bude faifan bala'i ta
shiga zagin iklima. Bayan baban ya fita tacshiga
zagin iklima. Bayan baban ya fita tace ai
dama 2ni nasan ba sona kikeyi ba kin fi son
ubanki dani matsiyaciyar yarinya ilminki bai
kare ki da kome ba 2nda ko musulunci sai da
ya kira uwa sau 3 yace uba. Allah ya jikan nfsa
badan ta mu2 ba da ace ita ce ni zata ba,iklima
ta lankwasar da kai tace ayya mama baki
fahimce ni bane in na sake samu ke zakije
malamai na ne suka ban shawara kan cewa in
bawa baba 2nda shine shugaban mu a gidan
gaba daya kudin kuma ya kara jari 2nda shi ke
dauke da nauyin mu in Allah yaso ma sai ki ga
dalilin haka wata rana ya kaiki...ta katse ta
dalilin haka wata rana ya kaiki...ta katse ta da
ke da Allah rufe min baki ai su malaman naku
dama nasan munafukai ne bare wannan yunus
yake ko wane?da ganin shi kaga mako ya dafo
dan wando yana sunne kai to aniyar ku ta biku
munafukai kuma ko kin samu din bana so
nafisa ta kaini. Lokacin da nafisar ta dawo
haule ke labarta mata abinda ya faru,nfsa tace
kwantar da hankalinki haule Hajji da umra sai
kin gaji da zuwa haule tace ai ko da bakya nan
ma na fada shi yasa ko yaushe nake saka miki
albarka kuma tana binki. Cikin kwanakin iklima
tana fuskantar cin zarafi daga yaruwarta da
mahaifiyarta hakuri ta dinga yi dasu har suka
gaji suka dan raga mata.
***
Nfisa ta shiga makarantarsu rungume da
litatafai jikinta sanye da wani yadi mai ruwan
kasa takalmanta masu tsananin tsini ne iri
daya ne da jakar tana tafe cikin taku na isa da
kasaita da dama suna yi mata kallon yar wani
kusa ne a gwamnati yayin da wasu ita ce da
kanta tace musu uban ta minista ne wasu
kuma tace musu jakadan nigeria ne a england
babu wanda bai gaskata ta ba saboda la'akari
da irin tsinannun motocin da ake kawda irin
tsinannun motocin da ake kawota
cikinsu,nfsa bata da wani takaimaiman fannin
da take karantawa don bata shiga aji kuma
koda ta shiga sai dai tayi ta zare idanu in anyi
dariya itama tayi domin in za a shekara ana
2ranci bata san me ake cewa ba,itama 2rancin
nata irin dan na tsintan nan ne amma ko kai
waye baza ka gane ba,ta isa gurin kawayanta
nan suka shiga koda shigar tata tare kuma da
yi mata tafi ita kuwa ta shiga yi musu juyi
kamar me yin paret, abokansu maza sukace ta
shiga gasa da za ayi ta sarauniyar kyau anan
makarantar tace haba?sukace Allah matan ma
suka shiga zugata,guda daya ce mai suna
jamila tace nafsa kada ki shiga sai kace ba yar
musulma ba? Nfsa tace dakata min malama!
ban kasa da ke ba ni nan da kika ganni ko gida
ba a matsa min ba kuma ni zan iya saida rai in
nemo suna,jamila tace zadai ki saida mu2mci
ki nemo suna to Allah ya ganar dake,tace
jamila sunanki kowa?don Allah dan maida min
hankalinki kinji ko?duk gurin suka fashe da
dariya jamila ta mike ta kama kanta. Zuwa
yanzun ko a gaban mahmud nafsa tana yin
waya da samarinta kuma in yaxo ya kan same
ta da wasu ko in yana tare da ita wani yazo.
Sun yi fada sun shirya yafu a kirga don ya lura
baxa ta canza ba ko da kuma yaki zuwa zata
bishi ta lallaso shi. Irin san da ya ke mata har
haushin kansa yake ji kafatanin kannansa basu
kaunar ta basa dokin auran yayan
nasu,iyayansa kuwa adduar zabin alkhairi suke
masa don kowa yasan yarinyar ba mai
natsuwa bace,shine kadai so ya
makantar,lokaci na tahowa ango ne kawai ke
hidimarsa dan buga bugarsa in yayi ya sai
kayan lefe don mahmud yanxu har aikin gini in
ya samu yana zuwa tunda shagon ba kayan
kirki.
Satin da zai kama nafsa suna da bikin safina
ita da mama zee sune manyan kawayan don
haka suke ganawa da abokan ango wadanda
ke ta yi musu barin kudi tamkar basa so,jikin
nfsa har tsuma yake yi saboda irin kudin nfsa har
tsuma yake yi saboda irin kudin da
ake musu bari ga dinner na garari,nan cikin
abokan mama zee ta samu nata angon da
dama sun kai hari ga nfsa taki amincewa duk
don son mahmud in da soyayya kawai xa ayi
xata yarda to duk ba2n aure suke mata. Bayan
wata1 da yin auran safina suka sha na mama
zee nan ma sunga barin kudi fiye ma da na
safina abinda ya dada firgita nafisa jibgegiyar
motar da safina ta shigo mallakinta ga wani
kyau da tayi suka gama bikin mama zee nfsa
tana nazari. Wata rana taje gdan safina ta
same ta tana ba yan aikinta umarni kicin dinta
ga girki nan kala kala wai mijinta zaiyi baki,
suka shige uwar dakin safina suka fada kan
gado nafsa tace kin ganki kuwa hajiyan Allah?
duniya tana kai muku. Safina tace kece kikaso
gashi cikin satin nan zamu tafi subgashi cikin
satin nan zamu tafi subai
shakatawa ni da mama zee don mazan mu
suna da meeting zasu tafi france kin suna da
meeting zasu tafi france kin san
abokai ne kuma aikin su daya,nfsa tace kai
kawata ina ganin xan yada ba2n so din nan
nima in shigo sosai safna tace xama ki dao
hanya in kin ki to kije kiyi auran so inyaso hanya
in kin ki to kije kiyi auran so inyaso in
mun cire kaya mun baki ki saka. Nfsa tace
xanyi 2nani,yini tayi zugur gidan da zata tafi
kayan shafa na iyayan kudi har da turmin
holland ta bata yayin da Alhaji sani ya dire
mata 20K sannan suka sa direban su ya kawo
ta gida. Da dare sna cin balangun su ita da
haule suna labari iklima kuwa tana gefe tana
kallon su tare da sauraron irin labarin da
nfskallon su tare da sauraron irin labarin da nfsa
take baiwa haule na daular da kawayanta ke
ciki,haule tace a to kin dai gani kema ki sa kafa
ki shure ba2n wannan dan iskan yaron da kika
nace ma mu huta,nfsa tace ai ina zaton
wannan karon zan jure in share shi baba kawai
nake tsoro,haule tace shima share shi ana
shiga daula zai manta daina tsoro zan tsaya
miki. Iklima tace haba mama bai dace kiyi
mana nuni da mu bijire daga umarnin
mahaifinmu ba. Haule ta kwabe mata baki da
bayan hannu tare da cewa uban wanene ya
kasa dake da zakiyi caraf ki kwashe?iklima ta
rike bakinta nafsa ta shiga yi mata ruwan bala'i
a karshe tsakar gida ta fita ta bar musu dakin.
Biki sauran sati2, 2ni abokan ango sun fito da
katin daurin aure da na biki,ka2nan sun birge
mahmud don haka ya kosa dare yayi don yaje
ya shaida mata cewa gobe za a kawo lefe
sannan ya bata katin da ya isa gidan bata nan
wai suna bikin wata yar ajnsu inji nafiu,zuwawai
suna bikin wata yar ajnsu inji nafiu,zuwan
shi uku iklima ta fito suka gaisa tace misshi uku
iklima ta fito suka gaisa tace mishi
suna biki ne xasu kai amaryar Abuja sun ma
tafi can xasu kwana,yayi shuru gashi bashi da
waya bare ya kirata ya dubi iklima yace to
shikenan sai da safe. Cikin dakin shi ya zuba
ma ka2nan idanu haka kawai yake jin gabanshi
yana faduwa a duk lokacin da ya kalli ka2nan
sai yaga kamar auran ba zaya yiwu ba in ya
2no hali irin na nfsa da mahaifiyar ta game da
son abin duniya. Yanzun haka da karma karma
da taimakon dangi ya hada akwati babba daya
da kit ya san rainawa zasuyi to amma yana
dogara ga Allah da kuma son da take mishi,
fatanshi dai ayi lafiya a gama domin yanzun
wani sonta ne mai tsanani yake kara shigarsa.
Nfsa suna bikin fati wata kawarsu ce itama Nfsa
suna bikin fati wata kawarsu ce itama dai
irin nafsa ce wato yan cika poly ko yan garirin
nafsa ce wato yan cika poly ko yan garari
cikin makaranta wai su a dole dalibai. Nafisa ce
babbar kawa cikin kawaye.
Fati ta auri wani kusa ne a gwamnati dattijo ne
mai shekaru kusan hamsin haka nan
abokananshi kuma 2nda aka soma biki
abokanan suke ta kai hari gurinta sai dai
hankalinta yafi tafiya kan Alhaji jamilu dukku na
farko ta kula ya dan fisu kuruciya ga kyau
tamkar ba mu2m ba sannan uwa uba ya
lillinka su kudi 2nda aka soma bikin yake
canjin mota in yaxo da wannan yanxun anjima
da wata xa ka ganshi, sam shi bai damu da
yanmata ba nafsa ce take yawan shige masa.
Yau da ya kasance ranar dinner kwalliya sosai
ta xauna gaban madubin amarya tana
yi,burinta Alhaji dukku ya taya,wani yadi ta
saka ja mai adon kyallin ruwan gwal,riga ce saka
ja mai adon kyallin ruwan gwal,riga ce da
skirt sun matse ta iyaka matsewa da kyar take
sauke numfashi,takalminta mai tsini ne sai
jakarta pos, gashinta da ya kone da mai ya
sauka gadon bayanta,rabin kirji da bayanta a
bude, net aka nada mata gwagwaro ta dora shi
bisa kanta duk kawayen sun ga kyan tsarin
adon ta tare da jinjina wa telanta. Lokacin da
suka isa gurin dinner guri yayi guri makada sun
cika gurin da sautin zamani,nfsa shedaniya
jikinta har nari yakeyi saboda jin sauti ko gurin
zama bata nema ba ta nufi gurin kidan cikin
tafiyarta mai jan hankalin mazaje ta shiga yin
wata irin rawa,juya jikinta takeyi tamkar babwata
irin rawa,juya jikinta takeyi tamkar babu
kashi ita kadai ce ke rawar don haka ta zamar
wa mazan gurin tamkar T.V ko kuma a club
nan kuwa alhazawan birni suka shiga yi mata
ruwan nera. Alhaji jamilu shine karshen likin
inda yayi ta yiwa nafsa liki da dala hakan ya
dada firgita ta yayin da mai wakar ya cigaba da
yi mata waka. Mai abin magana ne ya sanar da
makadin cewa su tsagaita za a soma gudanar
da dinner. Alhaji jamilu ya amince nafisa tayi
daidai da tsarin sa, don haka baiyi kasa a
gwiwa ba yace da bodyguards dinsa su
tanadar ma yarinyar abun zama sannan su
kawo masa ita. Sun sha mamaki don maigidan
nasu mata basu ishe shi kallo ba, nfsa tana
zaune taji an dafa mata kafada ta waiga yace
xo muje,tayi mishi wani kallon kai gaja yace
maigidan mu ne ke son ganinki tace wa kenan?
ya nuna mata shi. Zaraf ta mike tare da cema
sauran kawayan nayi kasuwa cikin irin salsauran
kawayan nayi kasuwa cikin irin salon
takunta na musamman ta isa gabanshi ya dubi
kujerar da ke gabanta tare da cewa kya iya
zama. Ta zauna tare da kafe shi da idanunta
gwarza gwarza da take jan hankalin maza har
ma da mata yace sunana Alhaji jamilu ina
zaune nan Abj,malamar fa?nafisat usman ina
zaune a minna. Ya jinjina kai haka yayi kyau ke
daliba ce?tace eh ina kara2 a poly yace good
me kike karantawa ne?tace uhm tana dan sosa
keya accounting nake karantawa. Ya zuba
mata idanu kin shirya aure?donni daga nazo fa
aure za ayi,cikin tsananin doki tace ai kada kaji
komai nima dama kai nake jira kuma gakkomai
nima dama kai nake jira kuma gaka
kazo,yayi dan murmushi. Ya salam!tace cikin
ranta saboda kyan da da ya kara,namiji har da
dimple.
Yace to ya xaayi in san gidanku a minna?tace
me sauki ne in zan tafi sai muje tare yace a'a
zan hada ki da yaro daya cikin yarana ya kaiki
tace duk ba damuwa. Tayi shiru xuciyarta cikin
takaicin kasancewarsu talakawa ko dai ta
kaisu wani gida ne? To wane gida dangi ma
babu mai silalai kowa fdakara'u,2naninta ya
katse lokacin da wayarshi ta shiga ringing ta
kai duba kan teburin wayoyi ne wadanda ko
cikin mafarki bata taba ganin irinsu ba. Kai
ranar saboda tsabar rudewa duk kwadayinta
da nama kasa ci tayi don murna ruwa ta iya
sha kadai. Daya saura suka tashi shi ne ya
saka daya daga cikin yaranshi ya kai ta gida
yayinda masu tsaranshi suka rufa masa baya
sai kace shine shugaban kasa. Kawayanta kam
sai murna suke mata a gidan amarya tayi
babban kamu, da zata gida kuwa suna sallama
cikin motarsa akwati ya bude mata makil da
kudi yace ta dibi son ranta,yan dubu dubu ne
sabbi fil tayi ta wurga idanu yace kada kiji
komai ki diba yanda zaya isheki. Sai da tayi
ma jakarta dam,sannan ya hada ta da wanda
zaya kai ta har gida ta dibi sauran kudin suka
nufi gida cikin murna. Shi kam Alhaji jamilu 2n
da yaga yanda ta dibi kudi yan dubu dauri 9
yasan cewa lallai wannan yar hannu ce,shi
dama yafi son mace da zata saki jiki taci kudin
shi son ranta ba wadda zata tsaya nuku nuku
ba. Bayan yayi waya da direban cewa sun
sauka lafiya,yace ta dubi hanyarsa jibi, tacsauka
lafiya,yace ta dubi hanyarsa jibi, tace
ton gara kam yazo don akwai wata yar
matsala...
Lokacin da ta shiga gida haule bata nan don
haka ta shiga dakin su,iklima ce ke rubutun ta
na hadda tayi mata sannu da dawowa nafsa
cikin fara'a ta amsa tare da cewa ina haule?
Iklima tace ta tafi gdansu na saman layi.
NfsIklima tace ta tafi gdansu na saman layi. Nfsa
ta zauna kan shimfidarta jiki na bari ta ciro
jakarta daga kafada ta zuge zif ta ciro kudadan
ta zubesu gabanta. Iklima tana kallo ta fiddo
dukkan idanunta tare da cewa Ya nfsa wannan
kudin fa?ckin dariya tace Alhaji jamilu kenan
sona yake jakar kudi ya bude min na diba
kadan na dauka dubu dari 9 da na kara dauri 1
miliyan kenan.iklima ckin tsoro tace miliyan?ke
yaya nfsa kin san in da ya samo kudinnan ya
baki su har haka?tace ke rufa min baki da
Allah,iklima ta mike ta fita tana cewa ki dai
Allah,iklima ta mike ta fita tana cewa ki dai yi a
hankali. Lokacin da haule ta dawo har da rawa
da taga kudi suka shiga shawarar yanda za ayi
dau, haule tace mu sai kayan abinci da nama
da kaji mu sayo freezer nfsa tace kuma muyi
dinkuna da zai yiwu ma mu gyara gidannan
don kada yazo yaga yanda gidan namu yake.
Haule tace baza mu gyara gidan haya ba bar
shi haka muci kudin mu ai ke yake so ba gidan
ba. Nfsa tace haka na mu sayi gwal mu sa ma
kunnuwan mu,haule tace mu bari sai da dare
maje kasuwar. A ranar da dare mahmud yazo
gurin nfsa suna zaune suna lissafin abinda
xasu sayo ko magrib basuyi ba bare ishai,nafiu
yazo kiranta taja tsaki ni wallahi har na mance
dashi ashe kudi yana shafe soyayya?yanzun
kam sai dai ayi rigima amma baxan auri
mahmud ba haule ta sheke da dariya sannan
tace in na zai ce a biyashi hidimar da ya miki
ne nasan Alhaji jamilu tsaf zai biya shi tace da
nfiu ce masa ina zuwa zanzo muyi ta ta kare.
Mahmud yana zaune a kan dan dakalin da
suke hira,can gefe kuma iklima ce da yunus
dinta suna hira irin ta masoyan da ke da ilmi.
Nfsa ta fito babu ko dan gyale dankwalintNfsa ta
fito babu ko dan gyale dankwalinta ne
ta rufa da shi ta tsaya a gabanshi kerere yaxo
da nufin nuna masa jin haushinsa ta tafi bikda
nufin nuna masa jin haushinsa ta tafi biki
bai sani ba,don haka shima sai ya shareta.
Tace malam in baka da magana in koma yace
amma ai kya yi sallama da kikaxo ko?cikin
isgili tace ya ma akeyi?ban iya ba ya mike
tsaye wannan kuma Allah kikeyi wa isgili. Ya
ciro ka2nan gasu kuma gobe za a kawo lefe,2n
shekaranjiya suke son xuwa amma kin tafi
bikshekaranjiya suke son xuwa amma kin tafi biki
saboda kin isa da kanki ko in sani,tace kai
dakata! ta daga mishi hannu wannan katin
menene?yace saura kwana 12 sannan kice
katin menene?ta shiga tafa hannu tare da
dariyar renin wayau tace mahmud kenan don
Allah ka sanar da yan gidanku su huta ba sai
sun kawo ba,don kada su sha wahalar xuwa su
dauka,ka sni baxan auri talaka irinka ba,sai
yaushe xan samu babban gida da babbar
mota?kwashe ka2nanka Allah ya hada kowa
da daidai dashi.
Kafafunshi suka shiga karkarwa dole ya
xauna,muryarshi na rawa yace kada kiyi min
haka nfsa baki min adalci ba. Ckin daga murya
tace ban san adalci ba yaya ma ake yinsa?aure
ne dai na fasa. Iklima da suke jin duk me eke
fadi tace ya nfsa lafiya kike daga murya haka?
sam matakin da kike shirin dauka hakika bakiyi
masa adalci ba,nfsa ta kai mata mari ikli ta
kauce nfsan tacigaba da

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment