Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi,iklima
tace yayana baki muka yi ko na fada maka
kayi hakurin dare. Yace kwano ne in ji matar
gidannan,nace ta aje miki nan waje.iklima tace
wlh ba zanyi kaffara ba tsegumi ne ya kawo
ta,ni kana bani kunya fa. Ya zauna kusa da ita
bani kunyata to. Tayi dariya Allah in na fita suyi
ta kallona.haka yan gidannan suke. Yace ke
baki da wayi,tunda suna kallonki sai kiyi
alfahari da mijinki yana sonki ko kin fi son in
nemi na banza a waje? Ta kwanta a jikinshi
kayi hakuri ajizanci ne ke sa ni sonyi maka
gaddama. Wajibina ne in amsa gayyatarka cikin
kowane hali matsawar bai ci karo da abinda
musulunci ya haramta ba kamar misalin haila
ko biki. Yayi dariya,ya malam kenan shi yasa
kullum kike kara shiga raina,nagode Allah da
ya ban ke. Da dare ya shigo da waya cikin
kwali tana kallon labarai ya zauna tace yayana
kashe-kashe ua soma yuawa a kasarmu dubi
yanda wai aka shiga gidan wannan mutumin
aka yi masa yankan rago. Yace na gani dazun
a gidan mukhtar in dai mai kisan yayi hakuri da
wanda zaya kashe ma ya mutu tunda ko ba su
yanka shi ba ba zaya wuce ranar ba. Tace
hake ne Allah ya saka masa. Ya dube ta,bani
goron albishir yanzunnan. Tace me kake so?
Yace sumba daya mai kyau.
Ta san yanda yake nufi dan haka ta zura
harshenta cikin bakinshi. Ta zauna tana dariya
ganin yanda jikinshi yayi laushi. Ya dora mata
wayar bude ki gani, ganin wayan tayi tsalle ta
fada jikinshi. Yace ke kada ki zubar min da dan
yarona fa, baiyi kwari ba. Sukayi dariya, ya
koya mata. Washegari suka nufi ziyara bayan
sun dauki wankan shadda iri daya, sai dai tashi
ta dan fi tata duhu kalar makuba, hijabinta yau
bai kai can kasa ba, da tace ita bazata sa. Shi
kuma ya ce ai ya rufe jikinki. Bata daura nikabi,
yace yanzu haka zamu fita yau sallah ki hakura
da nikabin nan mana. Tace a'a fuskata da
adona kai daya ke da ikon gani sai wadanda
Ubangiji ya amince wa, wato muharramaina.
Bai ce komai ba suka fito, su maman ummi
suna raba abinci lokacin da ta fito shi yayi waje
ita kuma ta nufi gurinsu dan yi musu sallam
suka ce ga abinci tace Allah ya amfana zamu
fita ne. Ya tada mashin ta dafa shi ta hau yace
kyan shi ace yanda kika yi kyau dinnan
gyalenki kika yafa yafa kalar jakar ki da
takalminki, da sai kinfi bada ma'ana. Tayi dim
domin duk lokacin da yayi furuci mai kamar
wannan sai ranta ya sosu. Sai da suka dauki
hanya sannan tace baban khalil ban san me
yasa ba, sam baka kishina. Yace bana kishinki
fa kika ce? Kin san me kike fada kuwa? Tace
nagani ne maza da yawa suna son suga
matayensu suna irin shigar da nake yi, amma
basu samu ba, kai kuma shigar tawa bata birge
ka. Yace ra'ayina ne kawai ba wai kishinki ne
banayi ba, ki daina fada min haka. Tace Allah
ya baka hakuri. Suka tsaya a kofar gidan suka
shiga, duk yaran gidan sun tafi yawon sallah,
suka shiga dakin hajiya uwa. Tace alhaji na
nan cikin dakinsa. Suka shiga suka gaishe shi
cikin jin dadi da fara'a ya amsa tare da cewa
khalil yana kontagora ko? Suka ce eh, ya shi
musu albarka, ta mike ta fita dakin hajiya rabi
ta shiga suka gaisa sannan ta koma dakin
hajiya uwa. Sun dan jima ya fito shi da alhaji ya
miko dari biyar gurin hajiya uwa yana cewa
gashi a bata ta aje ma khalil goron sallar shi.
Ikilima tace dama ya barshi, tunda baya nan.
Hajiya uwa ta ciro kudi a gefen kujerarta naira
dari ce tace duk da ya gudu dan kada ya bamu
goron sallah, gashi ba dinkin sallah nima ga
nawa. Ta hada ta ba ikilima suna dariya
dukansu. Tace angode Allah ya maimata
mana. Rabi ma ta miko nata tana cewa mara
cefane ne ba. Suka fita suna dariya. Alhaji ya
ce kada ka manta ku bi ta gidan alhaji jinjiri da
alhaji ado tunda sallah ce zaka same su gida
suna yawan tambayarka. Yace to zamu biya.
Abokin alhajin ne duk basu da nisa suka shiga
suka gaisa yayi musu ihsani, suma sun bada
goron sallar khalil, yace yanzun can gidan zan
kai ki? Tace eh, da dare sai kazo mu tafi. Yace
a'a biyar zaki dawo don ni ba zan samu zuwa
bama. Tace kai dan Allah, ba ka ganin bani da
lafiya? Yace in dai biyar tayi banzo ba ki dawo,
tace shikenan. Gobe sai naje mu wuni masu
baba. Yace eh, bayan ta sauka yayi parking
mashin din suka shiga. Nafisa ce kwance a
palo tana amsa waya, bata san ma su waye ke
sallama ba, ta dai amsa. Suka zauna. Ko
yaushe ikilima tazo gidan tamkar bakuwa
takeyi, ta kasa sabawa. Nafisa tace, duba anty
hajara ni na gaju kawai ba zan dawo ba nake
ganin sai dai in debe kayana, sa san shi fa wari
yake yi dan masifa koyaushe sai na dau G na
roban nan na tuttura muishu ni kuma ya tilasta
ni sai na kwanta ya min, ga wari har fa da
tsutsa wani sa'in ni bazan iya ba. Hajara tace
ai kinyi kokari ma in nice bazan yarda ka rabeni
kana wari ba. Ta tashi zaune tace kinji dalilin
dawowata. Abn duniya ya isheni. Ta sauke
idanunta kan mahmud wanda idanun shi ke
kallon TV kuma yana sauraron duk abn da take
fada. Sai dai bai fahimci me kalaman nata ke
nufi ba, wayar hannunta ta subuce ta fadi kan
kujera, abubuwan da suka faru cikin hotel din
suka dinga kai kawo cikin zuciyarta. Ikilima ta
katse ta da cewa yaya nafisa mama fa? Cikin
in-ina tace tana...tana kicin. Ta mike tare da
kallonshi. Yaya bari na kira ta ku gaisa. Yace
to tare da kallon agogo. Kiyi sauri dan zamu
fita dasu muktar ne. Tana fita nafisa tace don
Allah mahmud ka yafe min, wallahi alhakinka
dana babanmu sai bina yake yi, na cuce ka da
yawa. Baiko kalle ta ba, don shi gidan bakikirin
yake kallonshi. Ikilima tana shigowa nafisa tayi
shiru, mama ta fito suka gaisa. Yayi mamakin
sakin fuskar maman har da ce mishi ina khalil?
Har da godiyar abincin sallar da aka kawo mata
daga wajen shi.
Bayan ta fita ne ikilima ta raka shi har gurin
mashin dinsa saidai sam babu walwala cikin
fuskanshi, shi kuwa sharrin data masa ne har
gaban alkali ke cizonshi. Ikilima ta ce habba
baban khalil, sai inga kana daure fuskan ka in
kazo nan gdan. Dan grman Allah ka yafe musu.
Yabuga mashin dinsa batare da yayi magana
ba. Ta tsura masa ido har saida ya bace
sannan tako ma gda. Kuka sosai tasamu
nafisa tanayi haule tana tsaye kanta tana fada.
Kin soma kular dani kan batun yaronnan. Shin
mai yafi sauran maza zaki damai ni da cewa
kin cuci kanki kina sonshi maisa kika ki shi?
Nafisa ta ce mama ke kika zugani ke kika
kasheni da kanki. Ta dubi nafisa sha sha sha
to da kin aure shin wannan gdan da yanxu
muna cikinsa? Koko daular dakike ciki da
yanxu kina cikinta?.
Nafisa tasake fashewa da sabon kuka tace
kazamar daula, daular da bata Allah da Annabi
ba dana aureshi da ban hadu da ciwon zamani
ba, ban zama yar maye ba..... Kuka yafi
karfinta maganar ta doki zuka tan haule da
ikilima, a tare sukace yar maye? Wanne ciwo
kike dauke da shi? Nafisa bata tanka ba saida
tayi kuka mai isarta, ikilima ta cire hijab ta a
jiye hannunta yana rike da hankacif saboda
zubar da miyau. Haule ta katse shirun da cewa
nafisa ina tambayarki wanne irin ciwo kike
dauke da shi? Ikilima ta matso kusa da ita
yaya nafisa dan Allah ki daina wannan kukan
ni na auri mahmud ne don fitar da baba da
kuma ke daga zagin da jama'a zasu yi muku
sannan kuma in shirya barakar dake tsakanin
baban mu da maman mu. Ban da kina da aure
zan iya neman mijina ya sahale min ya aure
ki... Ta daga ido ta kalle ikilima da sauri cikin
wani sabon kuku ta rike hanunta gam.
Na sani yar uwata kina s tuntuni nice dai
ba...bakiyi da ce da yaya ba inaso...so ina so
ki sani ko banida aure mahmud yayi mini nisa
bazai saurare ni ba dan na cutar dashi kuma
na cuci kaina ikilima tace zan tursasashi sai ya
yafe miki,tayi saurin katseta babu tursasawa a
yafiya. Ta mike ta soma kai kawo a tsakar
falon. Bazanga laifin mahmud ba dan yace
bazai yafemin ba. Ya taba baki lbrin ni ce na
hadashi da yan sanda har kotu? Ta fashe da
kuka kafun ta tsahirta ta ci gaba nice na bada
kudi aka sama shagonsa wuta, dan kawai na
jefashi cikin kunci. Ikilima ta zaro ido tana
kallon nafisa, batakuma san lokacin da bakinta
yana tambayar saboda mai? Bata dubi ikilima
ba saboda soshi. Haule tace dama nafisa kece
hajiyar da'akazo ana lbr? Bata amsawa haule
ba taci gba da kallon iklima bansan ina son
mahmud ba sai lokacin da'aka kaini gidan alh
jamilu yadda naga rana haka na raya daran da
kuka.
Randa alh jamilu ya shgo dakina ranar na
soma nadamar auransa domin ranar nasan
cewa shi dan luwadi ne na aura... Numfashin
iklima yakusa daukewa dakyar ta janyoshi
sannan tace ludu? Nafisa ta kwashe komai ta
sanar dasu sannan tace sakamakon kwadayi
yau gani da ciwon kanjamau. Haule sai da ta
zube kasa, iklima kuwa kuka ta saka haule
tace amma nafisa Allah ya isa naturaki zina ko
aure? Nafisa ta dubeta duka kika turani domin
ke bakida burin da ya wuce kudi, gurinki na san
kwadayi. Ta dubi ikilima wadda ke fatan ace
duk wadannan abubuwan cikin mafarki ne, cikin
raunanniyar mury tace kin tuna ikilima lokacin
da mama take ce mana muna da kyau kada
mu saurari takaka? Kin tuna lokacin da ta ke ce
mana babban gda babbar mota? Lokacin kika
ki sauraronta nice na biye ma zuciya da
kwadayin duniya. To yau gani cin nadama
mama kin cucen kinci amanata, kin zalunceni
kin turani ga hakaka...
Tasake fashewa da kuka haule ta mike tana
cewa kin dai cuci kanki nace kiyi zina? Ki
tattara ki koma dakin mijinki ni banzauna da
mai kanjamau ba.
Ikilima cikin matukar sanyi jiki tace yaya nafisa
gaskiya kin tafka babban kuskure ki soma
neman gafarar Allah hakika kin gafala da yawa.
Nafisa ta matso kusa da ita tace ta ina zan
fara yar'uwa ta? Wlh har sallah nadaina yi,
bazan tuna ranar danayi sallah ta karshe ba.
Wa'iya zubillah iji iklima. Iklima zufa ya shiga
tsatstsafo mata daga dukkan wata kofa ta
jikinta, kinyi kuskure babba banyi mamakin
laifukan dakika aikata ba, domin duk wanda ke
barin sallah daga lokacin tama Allah ya fada
azaba ta tabbata gareshi , bare wanda
ya barta. BOOK
MABUDIN WAHALA 3**4
Ikilima ta taba nafisa tare da rada mata cewa
ta gaishe shi, sannan ta soma neman gafarar
shi. Koda tace baba ina kwana? Bai tanka ba,
tace dama nazo ne ince ka yafe ni, wallahi na
gane kuskuren da nayi. Ya girgiza kai, baki
gane kuskuranki ba tukunna, lokacin bai yi ba
da saura. Haule tace don Allah malam kayi
mana aikin gafara. Ya dubeta "ni bansan laifin
da kuka min ba. Mahmud yasa baki da cewa
baba ba kai ba, ko mu mun san laifin da tayi
maka, ta gane kurenta dan Allah ka yafe mata
taji da lalurar da ta ke tare da ita. Mal usman
ya gyara zama , to inda wanda aka cuta aka
zalunta ai kai ne, don haka kai zata roka.
Mahmud yace baba ai tuni na yafe mata kafin
tazo. Domin in na ci gaba da fushi ban gode
ma wannan baiwar da Allah yayi min ba. Ya
fadi haka yana nuna ikilima, sannan ya cigaba
da magana.
Canjin da Allah yayi min ya bani ikilima baiwa
ce don haka ka yafe su baba. Yace mahmud
basu dauki darasi ba tukunna, ko na yafe musu
in dai wannan mai kwadayin ce..." Ya nuna
haule, da wannan magajiyar tata sai sun yi
wanda yafi na yanzu. Ikilima tace wallahi baba
sun dauki darussa. Nan ta shiga baiwa baban
labarin mijin da nafisa ta aura da halayan shi
da silar dukiyar shi. Ba mal usman ba hatta su
danlami sun girgiza da jin batun. Don ma bata
shaida mishi irin shagalar da nafisar tayi ba.
Nafisa kuka wiwi ta rinka yiwa ikilima godiya
sannan haule tace ni dai nafison ta koma
gidanta, tunda ance ciwon nan daukarshi ake,
ikilima tace ba'a dauka sai ta hanyar haduwar
jini ko ta hanyar da ta samo. Nan ne ma akafi
saurin dauka.
Biyar daidai ya kira wayarta , abnka da sabon
shiga tayi ta zumudin dauka, yace ki taho ina
jiranki zan baki sako. Tace zan taho amma
maganar message sai a hankali, don ina cikin
wani hali. Gani nan zuwa yanzunnan. Ta soma
shiri, hauke tace ki zuba abnci kici mana tunda
kika zo baki ci komai ba, amma mama dan
Allah kada ki nuna mata tsana. Taski haule tayi
tare da cewa, bar ni inji da kaina.
Tunda ta shiga daki take aikin kuka, ko a
mafarki bata taba zaton irin wannan
kwamacalar zata faru cikin zuri'arsu ba. Ciwon
kanjamau da suke jin labarin shi can nesa har
ya matso kusa yazo gidansu kuma a dakinsu.
Mahmud ya shigo duk da yazo da uzurinshi
amma halin da ya same ta aciki ya shafe nashi
uzurin, nan ya rungumeta yana son jin
damuwarta. Dolen ta ta fada ko dan halarcin
yayi mata, inda wani ne yayarta tayi sanadin
zuwanshi hannun hukuma yaci duka kan ta zai
zo ya sauke. Amma shi bai ko fada mata ba, in
ma tana son lamuran su warware dole sau yaji.
Tace mahmud. Ya dube ta da sauri don bai
taba jin sunan daga bakinta ba. Ta katse mishi
tunani da cewa dama yaya nafisa ce tayi
sanadin kai ka gurin hukuma? Yace inji wa?
Tace in jita, nan ta shiga zayyano mishi duk
yanda lamuran suka faru, daga karshe tace
yanzun haka tana dauke da ciwon kanjamau...
Maganar ta tsorata shi, lallai wannan abn jaje
ne. Ikilima tace yaya nafisa taki amince wa ne
kawai tun farko na sanar da ita duk wanda
yace shi ba zai tsaya inda Allah ya ajiye shi ba,
karshen shi nadama. Don Allah baban khalil ka
yafe mata. Allah yana yafewa bayinsa masu
yafiya. Shiru kawai yayi yana tuna artabunsu a
hotel, da yabi son zuciyarshi da yanzu yana
dauke da ciwon shima. A fili yace Allah na gode
maka da ka kare ni, ya dubi ikilima ni tuni na
yafe mata. Allah zata roka sai ko mahaifinta.
Ikilima tace baban khalil ina rokon wani arziki,
yace na me? Tace kai zaka jagorance mu zuwa
gurin babanmu, don ta nemi gafara. Yayi shiru
tace don Allah. Ya dube ta yaushe? Tace da
safa. Ya dan rausayra da kai ba tare da yace
komai ba. Har garin Allah ya waye ikilima bata
iya bacci ba, juyi kawai take yi. Abubuwan
suna zuwa mata tamkar cikin mafarki. Da safe
yana kwance ta gama duk shirye shiryenta
sannan shima yayi wanka suka tafi lokacin da
suka iso gidan haule tana zaune a falo cikin
tagumi ta daga ido tana kallon ikilima. Cikin
sanyin jiki tace lafiya da sassafe? Ikiilma tace
lafiya lau, daidai nan mahmud yayi sallam ya
shigo. Tace a'a tare kuke? Ta sunkuyar da kai
tanai musu sannu da zuwa. Yau ce rana ta
farko da hauke ta soma jin nauyin mahmud.
Suka gaida ta, ikilima tace una yaya nafisan
ne? Ta nuna dakin da nafisan kan sauka in
tazo. Tana nan ciki. Ikilima ta shiga, haule ya
dube shi, baka zauna ba ka zauna mana, ya
zauna tace don Allah duk naji abnda ya faru
gurin nafisa, dan Allah ina neman gafararka ka
yafe mu. Mahmud ya dube ta tamkar zata
zubda hawaye yace bakomau mama, ya wuce.
Tace nagode. Daidai nan suka fito. Nafisa
zubewa tayi gwiwa biyu tana rusa kuka tare da
neman gafararshi. Yace ya wuce in dai nine na
yafe miki. Ikilima tace mama zamu je ne da ita
gurin baba don neman gafararshi. Mahmud
yace kamata yayi ace har maman za aje don
an fa bata mishi rai ba kadan ba. Haule ta mike
bari muje din. Ya buga mashin yayi gaba.
Tsaye suka same shi kofar gidan shi da nafiu,
su kuma sunci karo da danlami da aminu, don
haka tare suka dunguma.
Yau ce rana ta farko da nafisa da haule zasu
shiga gidan. Yana shan shayin da matarsa
Hama ta hada masa, ita kuma tana ninke
kayan nafiu suna 'yar hirarsu cikin nishadi, sai
sukaji sallama. Ikilma ce a gaba tace a'a haj
ikilima ce da sassafe? Tace mu ne mama, koda
malam usman ya daga ido ya sauke su kan
nafisa sai ya kware.
Kwaruwa mai tsanani har sai da mahmud da
danlami suka rike shi, ya dan lafa sannan ya
nuna nafisa yace wannan ta fita daga gidana,
bata cikin ahalina. Nafisa ta soma kuka
mahmud yace yi hakuri baba, ka dubi girman
Allah ka saurare mu. Ya kalli mahmud tamkar
zaiyi magana sai kuma ya fasa. Hama ta
shimfida musu tabarmi suka zauna, hama dai
tsakar gida ta fita ta kama 'yan aikace aikacen
ta.
Ikilima ta taba nafisa tare da rada mata cewa
ta gaishe shi, sannan ta soma neman gafarar
shi. Koda tace baba ina kwana? Bai tanka ba,
tace dama nazo ne ince ka yafe ni, wallahi na
gane kuskuren da nayi. Ya girgiza kai, baki
gane kuskuranki ba tukunna, lokacin bai yi ba
da saura. Haule tace don Allah malam kayi
mana aikin gafara. Ya dubeta "ni bansan laifin
da kuka min ba. Mahmud yasa baki da cewa
baba ba kai ba, ko mu mun san laifin da tayi
maka, ta gane kurenta dan Allah ka yafe mata
taji da lalurar da ta ke tare da ita. Mal usman
ya gyara zama , to inda wanda aka cuta aka
zalunta ai kai ne, don haka kai zata roka.
Mahmud yace baba ai tuni na yafe mata kafin
tazo. Domin in na ci gaba da fushi ban gode
ma wannan baiwar da Allah yayi min ba. Ya
fadi haka yana nuna ikilima, sannan ya cigaba
da magana.
Canjin da Allah yayi min ya bani ikilima baiwa
ce don haka ka yafe su baba. Yace mahmud
basu dauki darasi ba tukunna, ko na yafe musu
in dai wannan mai kwadayin ce..." Ya nuna
haule, da wannan magajiyar tata sai sun yi
wanda yafi na yanzu. Ikilima tace wallahi baba
sun dauki darussa. Nan ta shiga baiwa baban
labarin mijin da nafisa ta aura da halayan shi
da silar dukiyar shi. Ba mal usman ba hatta su
danlami sun girgiza da jin batun. Don ma bata
shaida mishi irin shagalar da nafisar tayi ba.
Yayi shiru, Allah ya sani bai kai fasikancin
mutumin nan har haka ba, ana shi zaton
mutumin ma'aikacin gwamnati ne barawon
gwamnati kenan, ashe abn ba haka bane. Yace
to yanzu me take so in mata? Ikilima tace
yafiya take nema. Yace in yafe mata taje ta
cigaba da zama dashi ko in yafe mata ta rabu
dashi? Da duk abn da ya mallaka? Duk suka
dubi nafisa wadda har dashewa muryarta tayi,
saboda kuka tace baba ai na bar shima ba zan
sake komawa inda yake ba.
Yace to da sharadi guda 2 zuwa 3, na farko sai
dai in silai nashi dake gurinki zaki maida mishi,
sannan uwarku ta dawo nan ta hakura da
kadan da Allah ya bani, don ba zan kuma shiga
wannan gidan ba, na karshe kuma taje ta
baiwa 'yan uwana hakuri ta nemi gafararsu. Ba
tare da dogon zance ba tace na amince baba,
zanyi duk yanda kace indai zaka yafe min.
Yace na yafe miki, sai ki tattara kazamar
dukiyarshi ki maida masa, ko bai nan ki ajiye
masa. Danlami yace yaya za'ayi da kantinan
da ta bude mana? Mal usman yace duk ta
tattara ta maida masa, domin kudi ne ba masu
tsarki ba, haramun ne kuma Manzon Rahama
(SAW) ya shaida mana duk jikin da ta ginu da
haram bazata shiga aljanna ba. Ki kuma zo ki
duka neman gafarar mahaliccinki. Haule ta
dube shi, mal dan Allah nima ka yafe ni, zan
dawo nan din sai dai zanso a raba mana gurin
kwana da nafisa don tana dauke da cutar
kanjamau....
Da sauri ya kalli nafisa, domin a wannan
lokacin ciwon bai yi yawan da za a ce ai wane
na dashi wane ma yayi ba, ciwon a wannan
lokacin duk me shi zai kasance cikin kyama,
tsana da tsoro gurin mutane kuma zai zama
abn gori da zuri'arsu , musamman ma in wanda
ke gidan miji yasa mata. Yace ya akayi kika
san cewa kin da wannan ciwon mai karya
garkuwar jiki? Cikin rawar murya tace anyi min
gwaji. Yace shi kenan dole kuzo neman gafara
tunda kin samo ciwon mutuwa, Allah ya kyauta
suka ce amin. Suna fitowa mahmud yace muje
gida mu karya kin dawo nan din, su kuma suka
nufi can gidann. Nafisa ta dubi mahmud ya
dauki iklima sun tafi, ta lumshe ido cikin kunan
rai, hakika ta cuci kanta. Haule dai tayi gaba
dan ta tattara kayanta, cikin ranta kuwa cewa
take ba komai zata bata ba, boye gwala-
gwalai zatayi.
Isar su gdan sai ga yan sandan ciki nan take
sukayi ciki dasu sai abuja, tuhumarsu alh
jamilu yake da cin kudinsa tunda tace bata
aurenshi, to ta dawo mishi da komai nashi.
Washe gari yan sanda suka tasa keyarsu har
minna ta kaisu kantunanta, a gda kuwa ko
kayan sawa basu bari sun dauka ba sukace
shegu alh yace komai shi yake siya muku,
kantinanta na abuja kuwa dama tuni yasa an
amshe, dole suka dawo gdan ikilima karkashin
malam usman din ba komai a tsiyacansu. Sai
ma ciwon nafisan ke dauke dashi, iklima ce
tasai musu katifu madaidaita, dakyar
maganarsu da alh ta mu2 ya bata saki.
Haka suka ci gaba da zama, haule ko tsakar
gda saidai alwala, abinda yakara sa nafisa
nadama, yanda haule ke nuna tsanarta karara.
Ko dakinta batason nafisa ta shiga, mamaki ta
dingayi. Lokacin baya kadan da ya wuce kafin
tasan nafisar tana dauke da ciwon, ji take da i
ta tamkar tsoka daya a miya. Duk daular da
taci ta manta, wannan damuwar da rashin
shan maganainta kusan sune suka taru suka
sa mata ciwon kai mai tsanani, wanda sai da
hama da babansu sukazo kanta. Sai kuma
zawo kafin kwanai duk ta rame, malam usman
shine ya nemo wani yaro mai kemis yadan yi
mata karin ruwa. Duk iklima batasan halin
da'ake ciki ba domin tundaga ranar bata koma
ba, ga islamiyya, sallah na wucewa suka koma
da zafi zafi.
Tagama girki kenan ta shirya khalil zata kaishi
gdansu mahmud daga can ta wuce islamiya.
Sai ga nafiu, suka gaisa tace yau bakaje
makaranta ba? Yace mune fa zamu zana
jarabawar j.s.s. Kin manta? Tace au ranar
litinin kenan zaku fara? Yace eh, yanxu ma fa
jikin yaya nfisa ne bata jin dadi har anyi mata
karin ruwa shine naga baki zo ba na ce bari
inzo in sanar dake. Cikin Damuwa ta ce, to in
na dawo daga makaranta zan biyo, zan kira
baban khali a waya in shaidamasa, yace to.
Nafiu ya juya ya tafi, duk jikin ikilima yayi sanyi,
tana tausayawa yar'uwarta. Suna tashi daga
islamiyar ta kirashi, ya daga yana tsaka da
aiki, tace zan biya gdan mu in duba yaya
nafisa, yace, minti nawa? Kinsan nakusan
dawowa, bana son in zo gda bakya nan. Tace
awa daya, yace a'a minti talatin, karki wuuce
haka, ina tare da bakine ya kashe wayar, tayi
dan murmushi ta maida wayar jakarta.
Na tsorata da irin ramar da yaya nafisa tayi,
cikin kuka nafisa take fadawa ikilima irin rashin
kulawar da haule take mata, tace kinsan dai
mama itace ummul'aba'isin shigata wannan
halin ko? Kuma lokacin dana samo wannan
kazamar daulan tafi kowa ci, amma yanxu tafi
kowa tsanata, matar baba ma tafi lura dani da
kuma tausayamin, hatta baaba duk da irin laifi
da nayi masa yana tausayamin tare da bani
kulawa. Ta nuna mata wasu zannuwa
wadancan falle biyvn ma jiya ya siyo min su,
bayan wadanda kika kawomin. Ikilima itama
cikin zubar hawaye tace, kiyi hakuri yaya
nafisa, ba'ance ana bada maganin shi a
babban asibiti ba? Nafisa ta share hawaye tare
da cewa maganin da tsada yanzun banida
wanda zai saimin. Ikilima tace baban khalil ya
cemin kyautane duk karshen wata,yakamata
gobe ki fara zuwa,zan tambaya in ya yarda
zanzo na rakaki. Nafisa tace, ikilima
nagodai,amma bazan so muje dake ba tunda
duk garin nan nasan yanxu sun san inada
ciwon nan, kar nagoga miki bakin jini.
Zan zo in har ya barni, don Allah ki daina ma
fadin haka. Ikilima ta kalli agogo , minti talatin
ya bani, bari in sallami su mama duk yanda
tayiwu dai gobe kije asibitin, tace to. Takawo
dari biyar ta bata, ki rike wannan a hanunki.
Kibarshi, kina dawainiya dani iklima. Come on,
amsa yaya in ban miki ba in yi ma wa? To,
nagodai Allah ya bar zumunci.
Ta fita nafisa ta tsura ma kudin idanu. Ta tuna
wasu kwanaki da suka shude , dari biyar bata
maida ta kudi ba. Duk da bata sadaka, haka
zaka gansu a dakinta, in kuwa canji ne ya rage
bata karba don gani take tamkar naira biyar ce.
Yau ga ta an bata tana murna, kai ya kamata
jama'a muyi hattara da kwadayin abn duniya.
Ikilima ta sallami su mama, dari bibbiyu ta
basu. Sannan tace da mama "gobe zanzo muje
asibiti da yaya nafisa ta soma amsar magani,
in kuma bai bar ni ba to mama kuje tare don
Allah. Wa!! Ba in da zani, na tura tata debo
ciwo? Kema ina gargadinki ki rage shige mata,
in kin kwasa ke kika sani. Ikilima bata ce komai
ba, ta fita don taga zatayi latti, cikin sa'a tana
fita baba zai shigo suka gaisa a gurguje ta
shaida mishi batun magani, yace yi zamanki,
haule ce ta dace suje tare. Ikilima tace in ya bar
ni zanzo muje. use Facebook in Free Mode. OK
HAUSA Novels BOOK
MABUDIN WAHALA 3**5
Ta fita nafisa ta tsura ma kudin idanu. Ta tuna
wasu kwanaki da suka shude , dari biyar bata
maida ta kudi ba. Duk da bata sadaka, haka
zaka gansu a dakinta, in kuwa canji ne ya rage
bata karba don gani take tamkar naira biyar ce.
Yau ga ta an bata tana murna, kai ya kamata
jama'a muyi hattara da kwadayin abn duniya.
Ikilima ta sallami su mama, dari bibbiyu ta
basu. Sannan tace da mama "gobe zanzo muje
asibiti da yaya nafisa ta soma amsar magani,
in kuma bai bar ni ba to mama kuje tare don
Allah. Wa!! Ba in da zani, na tura tata debo
ciwo? Kema ina gargadinki ki rage shige mata,
in kin kwasa ke kika sani. Ikilima bata ce komai
ba, ta fita don taga zatayi

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment