Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka lbr ke yawo cikin garh, wasu su yarda
wasu suce basu amince ba. Mutan gda kuwa
tun daga santa aka fita da kayan da kujeru
sukejin dadi suna tsegumi. Satinshi daya ya
wartsake,masllaci kawai yake zuwa. Ya na
kwance kan katifa, ita kuma ta sauke akwati ta
zazzage zata ninke kayan data dibo daga
shanya, yana rike da khalil ya dubeta cikin
yanayin damuwa a fuskar sa. Banso kika saida
kayanki ba, ikilima ta juyo a hankali ta kalleshi
cike da mamakin abinda ya fada ta girgiza kai.
Na fada maka ka daina cewa haka,bani na
jawo ba ? Bakiga babana ya shareni ba? Ta
karkade rigarshi tana cewa wai wace mata ce?
Nifa banyarda da duk abunda akace ba, yace
wata ce. Suka danyi shiru ya ce wlh bani da
kalmar da zan gode abinda kikamin, nagodai
ma Allah daya bani ke matsayin mata, hakika
ke yar aljanna ce, dadi ya rufeta.
Daidai lokacin da ta daga wani zani ta kakkabe
letter ta fado ta dauk tana juyawa tare da cewa
baban khalil na maka laifi innalillahi, duba lettar
nan tun kusan fin sati aka kawo. Ya amsa tare
da cewa letter kuma? Ni kam wanene ya kawo
min? Tace wasu mutane ne. Ya bude itama
kuma ta tsura ma fuskar shi ido ya duba lettar
din a nutse. Ya dubeta Allah bashida abokin
tarayya, shine
maiyin yadda yaso, alokacin dayaso tace
menene? Ya mika mata letter din da bankin GT
sukayi dani tun shekara 4 shine suka turo min
cewa sun daukeni aiki, amma sai na sake zuwa
sun min iterview ranar sha hudu, yau wace
rana ne? Tace gbe kenan yau sha uku Allah
mun godai maka, Allah kasa muna da rbo yace
amin.
Washe gari yayi fes dashi cikin kana nan kaya,
ta rakoshi har bakin zaure tana cewa Allah
yasa mudace, yadubeta da murmushi yace
amin. Aysha ta leka ta yafito maman ummi ta
nuna mata so suka tallafe baki suna dariya,
tare da cewa wannan batasan waye namiji ba.
Tajuyo tagansu suna dariya dama tuni tagama
gano ko su suwaye, dan haka sai tawuce
dakinta. Suka kuma ciga da hasashe ko garin
zaya bari tunda anyi abin kunya. Aysha tace ni
itacema take ban mamaki, kan mamiji ta saida
komanta, kinsan Allah sai na mata magana,
maman ummi tace ki kama bakinki, amma!
Aysha tace ina zuwa. Tana karyawa ta sameta
itama ta zauna tace kina kari ne tace eh
bismillah aysha ta tabe baki na koshi bana cin
kwanannan abinci. Ta dubeta dama gurinki
nazo, yanzun ke baki da mai miki fada ne cikin
danginku? Kin sai da ko mai kan namiji kina
wahala kina ci daku randa fa yayi kudi bazai
saurara miki ba wata zai hararo. Cikin mamaki
ikilima ta kalleta ta mike tare da cewa Allah ya
baki hakuri in ranki baiso ba. Amma kiyi tunani
namiji dai rigar kaya ne ko kinki sai kin cire. Ta
fita ta bar ikilima baki bude. Ita dai bata son sa
ido in ta kara zuwa zatace mata batason haka.
Nafisa kuwa koda ta ko ma gida kuka ruru tayi,
yanxun batasan kuma yaya zatayi ba tasan ko
kallonta ma bazaya sake yi ba ko a hanya.
Shedaniyar zuciyarta ta ce mata duk sanda
kika tunashi kisha mayenki zaki ganshi kuna
holewa. Tundaga sannan ta kara tsananta
shaye shaye, inko tasha sai ta rinka ganinshi.
Mijin hajara jikinshi ya shiga mataki na biyu na
masu ciwon kanjamau, rama da kuraje sun
baiyana dan haka wasu suke gudunshi, lokacin
da hajara ta gane mijinta na da ciwon, sai
hankalinta ya tashe domin sau da dama in ya
kawo wani ya wtse da shi to shi wanin zai
aikata sabon zina da ita.
Tayi asibiti dan a gwada jininta, cikin lokaci
kankani itama aka gano tana dashi. Tun daga
lokacin take kuka tare da kira shiga uku, ta
danna waya takira nafisa. Nafisa ta sameta
shabe shabe ta ce lfy aunty? Hajara cikin kuka
ta ce ina da cutar kanjamau HIV dama dagaske
akwai ciwon nan? Kai ban yarda ba, ba kina
amfani da kororo ba? Hajara tace kororo zai
hana kamu da ciwon ne kema kije a gwadaki.
Nafisa tayi yar dariya tare da cewa ni ras nake
tace kada kice haka, domin kinsan munsha bin
namiji daya ni dake ba'a gane ciwon a ido.
Nafisa tayi shiru tana saurarenta zuciyarta tace
kada kije watakila ita ba kowanne lokaci take
amfani da kororon roba ba,Ke kuwa da ita kike
amfani, dan haka sai tayi gidanta, amman abin
na damunta washegari tayi asibiti jikinta sai
bari yake tun lokacin da zaa dibi jinin nata.
Ya tabbata nafisa ta kamu da qanjamau itama.
Hankalinta ya tashi ta samu alhaji jamilu da
kuka wiwi, shi dariya ma ta bashi sannan yace
to dan kina da HIV menene? Kusan dukkan mu
masu harkar luwadi muna dashi, ni ai ya
shekara bakwai a jikina. Amman kinga alama?
Ai in dai zaka qetare iyakar ubangiji ya maka
dole ne ka samu ciwon nanan sai ki soma shan
magani duk wannan baisa nafisa tayi shiru ba
ta nufo minna hankali tashe amman ta kasa
sanar da haule kwananta 2 ta juya. Tana dira
gida hajara na shigowa, cikin kuka
tace ma hajara na cuci kaina na zalunci kaina,
na debo ma kaina ciwo mara magani, hajara
tace inji wa? Ai na soma shan magani kema ki
dinga zuwa kina amsa kina sha harka kuwa ba
dainata zamuy ba, gara ma ni dake ko
haihuwar fari baki ba kina ganiyar quruciyarki
Nafisa ta sake sa kuka, kai ita ko data samu
kudin tayi kudin bata huce takaici ba kenan
kudin basuyi mata rana ba nan hajara ta shiga
lallashinta da bata magana, da kuma nuna
mata cewa yanda aka sadado aka sa musu
suma suyi ta bazawa ga duk wanda kwadayi
ya kawoshi. Shaidaniyar zuciyerta ta amince
da haka, dan haka ta bi layin masu shan
magani jama'a sai kuyi hattara ga irin su nafisa
sunfi dubu.
Ikilima tana bakin fanfo tana wanke
kayanshi,yayi sallama. Ta dago suka kalli juna,
sannan ta amsa sallamar. Murmushin da ya
sake ne ya tabbatar mata cewa anci nasara ta
nufi gurin sa tana cewa, sannu da zuwa. Ya
dafa kafadarta, kasa kasa yayi da murya ya ce
mata munci nasara, suka nufi daki maman
ummi ta bisu da ido. Taja tsaki tare da cewa,
acben tausayi. Ta shimfida masa tabarma ta
bashi ruwa sannan ta shigo mai da abinci sai
da ya ci ya koshi sannan ya ce da ita.
Zasuyi mana training na sati 2 sannan ga
takardar ka'idodinsu. Sun ce zasuyi aiki damu
na wata 9 kafin su tabbatar damu, mu zama
cikakkun ma'aikata, in mun kiyaye ba'a
kamamu da laifi.
MABUDIN WAHALA 3**2
Tace to har wata 9 baza a baku albashi ba? Ya
ce zasu bamu amma in mun zama cikakkun
ma'akata zasu biya mu kudin da muka kashe
gurin siyan kaya kinsa fa sai mun sai kaya.
Basason kaloli daga ash, sai yellow sai baki sa
blue da sky sai ko fari. Sun fison komai set har
takalmi in kuma kayan yarenka zaka sa shima
ya zama set. Tayi yar dariya tare da cewa gaka
dama maison ado shikenan sai kwalliya. To
yanzun ina za a samu kudin siyan kyan? Ya ce
nima tunani na kenan amma babu damuwa
zamuga yanda za'ayi. Tace ko na baka
ragowar kudin hanuna yace bari tukunna
yafita.
Ta debo ragowar zannuwarta na sunan khalil
tayi gdan dilaliya dasu yana dawowa tace kayi
hakuri na fita banfada ma kayi hakuri ta bashi
dubu 8 duk da kudin hannaunta tace ga
ragowar dubu 1 nan kaje ka siya da wannan
yace rantowa kikayi? Tace zannuwana na
siyar.
Ya zuba mata ido baisan kalman da zaya
godai mata ba, bayaso ya ce mata kudin baza
su isa ba dan kada ta ce zata kuma aro masa,
amma zaiyi maleji. Yace ikilima samun ki a
matsayin mata ba karamar rahma ba ne, kina
da iman, da tausayi. Tace haba baban khalil,
daina wannan zancen, shi dama zaman aure
zaman ibada ne na taimakon juna. Yace tunda
mukayi aure kece kike taimaka min bansan
sanda zan taimaka mikiba. Tace lokaci yana
zuwa ta mike tare da cewa lokacin sallah yayi.
Daga sallar isha'i gda ya wuce gurin su alhajin
shi, har yanxu alhaji bai sake da shi sosai ba,
hajiya uwa tana bude mishi abinci suna
gaisawa, sannan ya gaida alhaji ya amsa sai
dai ba kama yanda suka sa ba ba. Ya ce alh
dama gurinka nazo yaci gaba dama aiki na
samu a bankin gt. Ranar monday za'a soma yi
mana training.
Alhaji ya dubeshi cikin fara'a tare da cewa Allah
ya sa albarka a ciki sannan mu2m yaji tsoron
Allah ya tsare gaskiya da amana. Dubi abunda
ya faru dakai kwanannan, akwai kaskancin da
ya wuce kana zaune kaida iyalinka jami'an
tsaro suzo su kamaka tare da tara maka
jama'a? To dan haka ka guji son zuciya, dan
malamai suna gaya mana ko yaushe. Dan haka
ka rike gaskiya da amana,yace nagodai. Su
hajiya uwa sunyi mishi murna sannan yaje
gdansu ikilima gurin babansu ya sheda masa,
tare da cewa yana son a yi masa addu'a shima
dai yayi masa nasiha.
Aiki gadan gadan mahmud ya kama abinka da
saban ba, sai da yayi murar Ac saboda kullum
cikin raba suke fatar shi kuwa ta goge in ya
dauki wanka tamkar wani minsta. Matan gdan
kuwa sun rasa gane ina yake zuwa haka' daga
karshe aysha ce ta tambayi iklima.
Wai ina mijinki yake zuwa ne' ko neman aiki?
Tambayar tabama ikilima mamaki sannan ta
murmusa ta ce aiki ne yazo har gda ya
sameshi, don haka wani banki ya ke zuwa aiki
tace al Allah ya sanya alkairi. Ta tafi ta
tsegumtama maman ummi.
Nan kuma suka shiga nuna bakin cikin su tace
shiyasa yake iyayi, kiga ya dau gayu sai kace
dan wani da wata. Aysha tace cen zaiga wata
a bank. Maman ummi tace ni in da za'ayi haka
ma da raina kar, ba ita bace sarkin bautar miji!.
Mata kenan ya kamata maman ummi su soma
ikilima abunda kuke sowa kanku.
Tunda nafisa ta gamu da ciwon zamani duk
dare sai tayi kuka, tasan lallai batun hausawa
haka ne kwadayi mabudin wahala ne kuda
kuwa gurin kwadayi yake mutuwa. Tazo mina
gdansu safina taje ranar ta firgita ganin yanda
safina ta dawo cikin kwanaki kadan da bata
ganta ba, ta bushe ta tsotse ta rame kuraji
caba caba babu kyan gani.
Kuka ru rus suka shiga yi safina tace nafisa
kinga yadda na koma? To har gara ni da mama
zee, kwadayi ya kai mu ga halaka ni bansan na
samu kanjamau ba sai da naje matakin karshe.
Gashi mijina ya kwashe kayansa ya barmin
gdan wai in na mu2 yazo ya saida gdan, ashe
yasan yana da ciwon ya aure ni iyayena sun
gujeni dan ban musu biyayya ba, uwata ce
kuma take dan sato jiki duba ni dan babana ya
ya hana kowa zuwa inda nake, don haka nafisa
ki tuba tun kafin ciwon mazinata da yan ludu
ya sameki.
Nafisa ta sake rushewa da kuka ta ce na nawa
kuma? Nima ina dauke da ciwon safina tace to
kiyi maza ki sasanta da yan uwanki kafi kizo
irin wannan matakinh bana iya tashi nan nake
kashi da fitsari sai wanda Allah ya jeho sannan
ya taimakamin amma kije ki ga zee mama, kudi
ta baiwa safina ta fita tana kuka.
Laillai gara safina da mama zee, ita tsutsa
gabanta ke fitarwa, ko an kwashe sai su dawo
su kuma cinkusowa, itama kuka take tace
nafisa kina da damar tuba,tun baki gamu da
masifun da muka samu kanmu ba.
Ta janye zanin da aka rufa mata ga doyin da
dakin keyi ta ce irin tsu tso tsin mai gda na keyi
lokaci zuwa lokaci yana yinsu duk da wai an
masa aiki a kasar waje. Mama zee ta ce, ciwon
nan saka makon madigon da na dingayi ne
nabi hajiyoyi da kawayen banza muna bin
junanmu mata. Yau ga saka makon abin da
nayi.
Nafisa har dashewa muryarta tayi, tace nima
ina da kanjamau mun shiga uku, sauran
kawayenmu da basu bi hanyar da muka bi da
muna ganinsu basu waye ba, ga abin sona
mahmud tamkar ya kashe kansa don sona,
amma naki shi na tozarta shi. Sannan
kawayena na abuja sun sani na rarraba ma
maza da yawa. Mama zee tace ki tuba ki nema
gafarar mahaifinki, ki dinga shan magani kin
istigfari ga Ubangijin ki, kinga mu mun makara
sai abnda Allah yayi. Nafisa da kuka ta dawo
gidan su haule, tace haule dama su safina da
mama zee haka suka dawo? Tace wallahi
dama ana rade-radin suna bin maza sai ko
gasu sun hadu da munanan ciwo, ni ai tun da
naje sau daya ban koma ba. Wannan mugun
ciwo haka? Ai ko dana ne bazan iya yin
wannan jinyar ba, mutum yaje ya dauka. Gaban
nafisa ya fadi, dan haka sai ta fasa gaya mata.
Washe gari ta shirya ta koma abuja. Wani
tashin hankali ta samu sabo, Alhaji jamilu
babban kamfaninsa yayi gobara, dama duk
kwanakin cikin ciwo yake banda tsutsotsin.
Likitoci sunce yana da suga da hawan jini da
ciwon zuciya. Likitoci da malamai suna cin kudi
son ransu, cikin haka ne zaben su yazo aka yi,
yaci ya kuma hau sai dai ba lafiya, duk da ba
wai da ka ganshi bane zaka gane hakan, duk
da sabuwar daular dasu nafisa suka samu bai
sa ta cikin nutsuwa ba. Shima ko yaushe
jikinshi na kara gaba, kullum yana hanyar
kasashen turai wajen neman lafiya. Wata safiya
suka wayi gari alhaji kabiru ya mutu, lokacin da
nafisa suka iso gidan abokansu duk sunzo da
danginshi suna ta kuka, har lokacin babu
wanda ya iya matsawa kusa da gawar bare
yayi mata wanka. Hasalima tsoron gawar
sukeji. Nafisa ta dubi hajara, anty har an hada
shi ne? Tace a'a tun cikin dare ya mutu amma
bai samu mai masa wanka ba. Nafisa tace to a
nemo limamai mana. Hajara tace limaman
unguwar nan anje amma yace su samu 'yan
uwan sana'ar su wato 'yan ludu kenan masa.
Ashe kallon mu kawai akeyi duk mutane sun
san komai. Nafisa tace mun bani, to yanzun
haka za akai shi? Hajara tace yayin shi sunje
dinko likafani zasu mishi, dan basu san me
yake aikatawa ba. Nafisa lamarin ya kara
tsorata ta, yanzu dai su ya zama musu dole
kenan su mishi wankan? Hajara tace eh dan
ma yana dubo su bai zubar dasu ba, in ba haka
ba da yanzu ya zanyi da yaran nan? Tagumi
nafisa tayi, ita batasan dangin alhaji jamilu ba.
Koda yake ina ruwanta da sanin danginshi
tunda ba auran sunna sukayi ba, aure ne na
jeka nayi ka. Sai dai in yayi mata irin mutuwar
nan ya zatayi dashi? Kai duk wanda yace
kwadayi dole yayi da nasani. Haka nan
abokananshi wasu sun girgiza lokacin da
sukaje rufe shi, kabarin uwa da 'yar sai ta
matse, in sun buda sai ta matse. Karshe da
'yan uwan suka saka shi suka turbude daga
shi sai halinshi. Tir da wannan irin makoma,
Allah Ya tsare mana imaninmu , kasa mu cikin
salihan bayinka, ka tsaida mu kan halas dinmu.
Amin. Wasu cikin abokanan sun girgiza wasu
kuwa sunce ko a jikinsu. Alhaji jamilu ma duk
jikinsa yayi sanyi, sai dai bayan kwana biyu
yaci gaba da harkokin shi.
Ranar da mahmud ya soma amsar albashi,
gaban ikilima ya zube su. Me kika ga ya dace
muyi? Tace ka cirar ma baba da mama ko ba
yawa, ina nufin alhaji. Sai ka sai mana kayan
abinci. Yace sai dai alhaji da baba na gidanku.
Tunda mama bata kusa wani watan a cirar
mata. Ina bukatar waya (GSM) ko me sauki ce.
Yayi kasa da murya dai dai kunnenta, sannan
dole yau muci kaza. Sukayi dariya tace hakan
ma yayi. Ya ciri dubu daya, ke ma rike wannan.
Tace a'a nima gobe nike sa rai za a biya mu a
makaranta, duk ga lissafin da kayi kudin kuma
ba yawa na yafe, wani watan mu a bamu. Yace
shikenan Allah ya kaimu. Ya fita zuwa gidansu,
inda ya kaima alhajin abin da ya sawaka, yasa
albarka tare da sake yi masa nasiha. Ya
mallaki wayar sadarwa mai saukin kudi,
sannan ya sai musu kayan abinci. Haka nan ya
ziyarci gidan gasa kaji da tsaftatacciyar
madara ya siyo musu lokacin da ya shigo tuni
ta gama komai tayi shafa'I tayi wutiri, duk da
babu kaya a dakin ya sharu tsaf yana kamshin
turare. Tana sanye da riga da zani na atamfa
ya zauna gefen katifa, me kike shirya min ne?
Ta gane nufinshi tace komai ma yayana. Ya aje
ledar ya sake dubanta, na kwana biyu ban
kawo sako ba, saboda gajiya. Amma yau sun
isheni. Ta tashi tana dariya baban khalil kenan,
bari na kawo plate. Sunci sun sha sunyi dam
sannan suka shiga bautar Allah. Sauran
kwanakin da suka biyo baya duk cikin jin dadi
da walwala suke, haka nan koda wata yayi nisa
basu tagayyara ba, don ikilima ta iya tattali da
lura akan duk lamuransu. Yanzu kam basu da
matsalar abinci, haka nan shi mahmud duk
kayan suna a don banki yana dasu, kusan duk
budurwar da taga mahmud sai ta sake
kallonshi. Shiyasa duk lokacin da zai fita ikilima
zata rako shi har zaurensu (soro) tana bashi
amanar kanta. Baban kalil dan Allah banda
kallon mata, sai yayi murumushi sannan yace
ikilima kenan, ki kwantar da hankalinki, ko na
kalla da na tuna dake sai na gansu tamkar
maza 'yan uwana, ina nufin sun daina birgeni.
Takan yi murmushi ta bashi jakar tace Allah ya
tsare.s BOOK
MABUDIN WAHALA 3**3
Matan gdan sukanyi habaici suce ba girin girin
ba tayi mai sabon kicifi ne raka miji har zaure?
Su kwashe da dariya. Ba ikilima ba hatta
mahmud yagama gane kalan matan gdan
nasu, saidai yadda ikilima bata taba yimar
maganarsu ba haka shima din baitaba dauko
zancensu ba lamarin gbanta kawai takeyi
sannan bata taba rikesu ba koyimusu
mugunta.
Matan gida sukanyi habaici da cewa ba
giringirin ba tayi mai, sabon kicifi ne raka miji
har zaure? Su kwashe da dariya. Ba ikilima ba
har mahmud ya gama gane kalar matan gidan
nasu. Sai dai yanda ikilima bata taba yi masa
zancensu ba shima din bai taba dauko mata
hirarsu ba. Lamarin gabanta kurum takeyi.
Sannan bata taba rike su cikin ranta ba, ko yi
musu mugunta. Har izuwa yau da mahmud ya
zoma ikilima da labarin sun gama watannin su,
yanzun za'a tabbatar da sune a matsayin
cikakkun ma aikata, yace in sun tashi aiki suna
da meeting, tace to Allah ya taimaka. Lallai
lokaci ba wuya, khalil yana gudun sa ko ina, ita
kanta tayi nisa da karatunta na sanawiya,
domin tunda mahmud ya samu aiki yana musu
bukata ta koma sanawiya da hadda in ta dauki
albashi sai ya cika mata. Bayan ya dawo office
da murna ya shigo, rungumarta yayi a tsakar
gida lokacin ta zubar da shara tana dawowa
daki, ya shigo itama ta kankame shi tasan
sunyi nasara. Dan dama yana ta cewa kanwata
ki tayani da addua, kuma duk sallah in takai
sujjada ga Ubangiji sai ta sako bukatar mijin
ta. Daki suka shiga suna dariya , suka zube
kan katifa. Yayi rigingine ya daurata kan
cikinshi, khalil ya rugo shima ya fada mishi kan
kirji, tace yayana murnar me kakeyi haka? Yace
mun zama cikakkun ma'aikata, an bamu kudin
da muka kashe gurin sa kaya dana gida, da na
abn hawa. Kuma duk karshen shekara za a
dinga yi mana irin wannan biyan. Ta rungume
shi tana murna, yace kudin nan sunzo daidai
azumi ya kusa, tashi ma dai tun yanzun ki bani
biro da takarda mu lissafa duk abubuwan da
muke bukata. Ta mika mishi takardar yace sai
da ina zaton ina cikin wadanda zuwa bayan
sallah za'a turamu wani branch din zuwa wani
state. Ta zaro ido, mu fa? Yace kuna nan
mana, bari dai mugani. Ta zauna cikin jimami,
bansan ko zan saba da rashin ka ba. Yace a'a
kada kisa wannan tunanin cikin zuciyarki, ba
dole bane ma a tura dani ba, yanzun zauna mu
rurrubuta abubuwan da muke bukata. Tace
abinci, yace dama wannan dole ne, ni bari kiji
lissafina. Farko zamuyi fenti mu sai kujeru da
gado, mu sai kayan azumi da na sallah, har ma
mu sai ma mahaifan mu. Ta zaro ido, kudin da
yawa ne? Yace sai dai in sun tura min cikin
account zan gani. Tace toh Allah ya shige
mana gaba. Yace amin. Musa kaninshi ya dora
kan aikin fentin tunda shi yana yi, aikin shine
ba zai barshi ba. Ikilima tace ta zabi ranar
alhamis ta zama ranar da za ayi fentin saboda
bata da makaranta. Su maman ummi sun ga
tana fitar da kaya ita da nazira kanwar
mahmud, sai suka koma gefe suna dariya, wai
tana kwalimar daki kamar zaure. Maman ummi
tace, in ni ce ita Allah ba zan fito da kayana
tsakar gida ba, babu abn kirki cikin dakin sai
katifa. Da musa suka zo da masu fenti suka
fahimci fentin akeyi, sai suka ce alhaji ne kilan
yasa a yi musu abn arziki, dubi yana aiki
amma jiya iyau. Aisha tace sai dai kanshi yake
kashema ba kya gani ya shiga wannan ya fita
wannan, da ganin jikinshi ma kin san dadin shi
yake ci can waje. Maman ummi ta sheke da
dariya tare da cewa ya iya tsiya, ba ita ta
maida kanta sokuwa shashasha ba? Haka
suka cigaba da zantukansu na hassada. Tun
daga toilet dinta har kitchen an gama sannan
aka fente tsakar gida da kofar gida. Ladi
makociyarsu ta shigo lokacin ikilima tana
wanke wanken tarkacenta na kitchen su da
nazira, suka gaisa da ladi ta dubi aisha tace.
Aisha ana muku fenti ne haka? Tace um,
maigidan ne ya saka. Tace aiko gidan yayi
kyau, mijin maman khalil? Aisha tace a'a
sirikinta ne nake ga. Duk ikilima tana jinsu
amma bata tanka ba. Kayan sawan su kawai
tamaida dakin amma sauran tarkacen ta zuba
su cikin kitchen. Washegari da safe yana shirin
fita office ita kuma tana fifita mishi shayi,
saboda ya dan sha kafin ya tafi. Kullum haka
sukeyi saboda yanayin aikin shi, ta mika mishi
daidai lokacin daya gama daura neck tie, ya
kurba ta dubeshi ya zauna gefen katifa.
Shikenan na zauna. Tayi murmushi "Manzon
Allah ne ya hana sha daga tsaye, kuma bai
bambanta mana ba. Ina nufin bai ce ruwa ko
tea ba. Amma ga hankalin mutum ai yasan dai
abn sha din ya kamata ko menen mu zauna."
Yace haka ne, ta mika mishi bread da ta shafe
da butter kaci sannu har yanzu batayi ba. Yace
na manta ki shirya da wuri musa da kabiru
zasu zo kuje kasuwar 'yan gado da kujeru ki
zabo har da carpet, mun gama magana dasu
tun jiya. Tace baban khalil da sauri haka? Yace
to me zamu jira ? Wannan fa tamkar bashine
zan biya. Ta bata rai. Ni bana bin ka bashi,
kyauta na baka. Yace to yi hakuri nima kyauta
ce irin na miji da mata. Ta sirmiyo daga kan
katifar, nagode sosai, Allah ya kara budi da
fahimtar juna. Amin. Yace cikin murmushi, tare
da dire kofin tace to wane kala zan zabo? Yace
duk kalar da ya miki nima ina so. Tace to. Suka
rako shi har zaure ita da khalil, kamar yadda
suka saba. Yana dauke da yaron tana dauke
da jikarshi ta office ta bashi jakar ta amshi
yaron suna yiwa juna bye bye, shima khalil tuni
ya haddace yanda akeyin bye bye.
Kannanshi ya musu ihsani sannan ya ba musa
ihsani yakaima uwarsu tundaga lokacin suke
zamansu najin dadi suci mai kyau su sha mai
kyau, muhallinsu tsaf. Maman ummi ta soma
shigema ta in asha bata nan har daki take
zuwa ta ce ai aisha ta ce miki kaza da kaza. Ita
kuma ikilima sai ta ce ba komai, na yafe mata.
Bana so mu dinga cin namanta. Da maman
ummi taga ba guri sai ta daina zuwa.
Sun shiga watan axumi cikin wadata a talauce
ba'a sarauce ba yasai mashine dan zuwa gurin
aiki, cikin axumine ta soma laulayin shigar wani
cikin, ta yaye yaronta da sauri mahmud kuwa
sai dariya yake mata yace ba in nazo da
sakona ba kina cewa tsoron ciki gashi nan ya
samu, tasha jinyan ciki kafun ta samu jikin ya
danyi karfi. Kayan sallar su ta tsura ma ido
nata kala takwas, na mijinta ma haka na khalil
goma, ga takalma da sauransu, ta dinga
godiya yace ina so ayi miki dinkin zamani da
siket din nan suna bigeni. Tace haba babank
khalil zannuwan babu kasa da dubu hudu
sannan ayi siket? Nafi son zani ya ce to shi
kenan yanda kike so haka zan miki. Ran jaji
berin sallah ta kama lahadi, shi da musua suka
shiga kasuwa yayima alhaji cepane shima yayi
sai nan yasai kaji babanshi biyar babanta uku,
sukuma bakwai ga naman miya sai da aka
gyara sannan aka shigo da su.
Ranar sallah da yayi wankan sallah iklima tace
wayyo Allah baban khalil tamkar kada na bari
ka fita,kayi kyau. Yace to nagode,kema kiyi
hakan kafin na dawo yau da rana zan bada
goron sallah,kin san dai laulayin baby ya dan
takura ma sakonnina two days ko? Tace,sai ka
dawo. Ta gama dafa abincinta,nazira tazo ta
dinga yi mata rabo. Ta yi wanka ta cake cikin
shaddar da yayi musu.
Anko.da ya dawo yace"a'a cire in za mu ziyara
gobe za mu sa. Na fi so ki samun jar atamfar
nan. Tace to.sun zo da abokanshi sun ci abinci
wanda zuwa yanzun duk sunyi aure kuma suna
mutunci da matansu. Suka fita Nafiu yazo tasa
mishi na mamansu dan nazira bata san gidan
ba. Yace yaya nafisa ma tun jiya tazo.anty
Iklima dama ki bar abincinki da kyar in mama
zata karba,ta ce ka kai mata. Su maman ummi
sai yan harare-harare don su sai ma ranar idin
suka samu kajin,aisha kuwa naman shanu ne
mijin ya siyo. Ta zuba musu sosai dan ita ta
san hakkin makwabtaka tana bakin famfo ya
shigo. Ya mata wani kallo da ta gane abinda
yake nufi. Ta bishi dama khalil tun safe Musa
ya tafi dashi kwantagora gurin mamansu. Zasu
yi kwana biyu. Suka sakayo kofa maman ummi
ta ja tsaki. Aisha daga cikin daki tace lafiya
tace leko ki gani abinda aka saba. Tana ganin
kofa a rufe tace kin san yau suna hutun sallah
tunda ya samu aikin suka daina turo kofa da
rana. Maman ummi tace,ni ko wallahi sai na je
na ga kof.
Tsaya ki ga yanda zamu yi. Ta wanke kwanon
iklimar da ta basu abinci taje ta buga kofar a
bugawa ta uku ne ya zo ya bude,ta ce dama
kwano ne zan bata. Yace aje mata nan kofa
tana aiki ne,ya maida kofar har da sakata.
Suka shiga kicin din su suna dariya Tace kin
san Allah aisha daga shi sai gajeran
wando,suka ce jarababba. Kai jama'a ina
ruwanku? Me za ku karu dashi in kun gani?
Zaman aure fa suke ba zaman zina ba,shin ku
ba kwayi ne?tir da masu irin wannan mugun
halin. Shi kuwa mamaki ne ya cika

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment