Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

latti, cikin sa'a tana
fita baba zai shigo suka gaisa a gurguje ta
shaida mishi batun magani, yace yi zamanki,
haule ce ta dace suje tare. Ikilima tace in ya bar
ni zanzo muje.
Ta soma bacci ya tashe ta, tayi mika tare da
cewa menene? Yace wai ke don Allah ikilima
yanzu baki da lokacina ne? Kin banni da
sakonnina tun fa sallah. Ta tashi zaune "baban
khalil ba ka ganin ina cikin damuwa ne? Yace
toh shikenan. Ya dauki filo ta mike ta bishi,
yace me kuma kika zokimin? Je kiji da
damuwarki, Allah ya yaye. Kayi hakuri, gani
nazo. Allah na hakura, kin san ba zan juri
wulakanci ba kan hakkina. Tun yaushe nake
bin ki? Abnda ya faru ya riga ya faru, zaki cire
mata ciwon ne? In kuma saboda ciki ne ai da
cikin khalin baki min wannan horon ba. Kina so
inje inyi zina ne? Da sauri ta rufe bakinshi, cikin
rawar murya tace ka yafe min. Ta durkusa , ba
zan zama daga cikin matan da suke tura
mazansu ga halakar zina ba. Ta sabule rigar
baccinta, yace wlhi na hakura. Ta mike ta
shiga daki, shi yayi bacci amma ita ta kasa
runtsawa.
Yana cikin kari, duk da bashi da wata walwala
bai dai daure mata fuska ba, tace yauwa
yayana zanje zan raka yaya nafisa asibiti, don
ta soma karbar magani kamar yanda kace. Ya
dube ta, duk baku da wanda zai je asibitin da
ita sai ke? Tayi shiru yace in da akwai wadda
ta dace suje bata wuce mamanku ba, don haka
ban amince ba, ban yafe ba ma. Ya dire kofin
ba tare da gama karin ba, ya suri jakarsshi ya
fita. Tayi sororo a zaune, nata ganin menene
na fushi? Ba zata ba, simple. Taci gaba da
aikinta ta gama, nafiu yazo wai baba yace
kada tazo da mama zasu. Tace to.
Ta so ma da ta dawo makaranta ta biyo amma
ba za ta tambaye shi ba tund ga irin rabuwar
da sukayi. Hatta da matan gidansu taji suna
tsegumin cewa yau dai su wance an kwashi
tsiya ne tunda muka ga ba a rako shi ana salo
ba sai kace kanta aka soma aure. Aisha tace,
ae ni na gama karantarsu.iN KIN GANTA
SUKUKU kamar kazar da kwai ya fashewa a
ciki to ya tsula mata tsiya, kuma kin ga ai da
kunya ta fito tace tunda an fada mata halin
maza taki ji. Sai ma nan gaba " Maman Ummi
ta ce "bari ya dawo zaki ga ba za ta zo tarar
shi ba "Suka sheke da dariya
Ta cika da mamaki, to yaushe da yaushe ma
suka yi fadan? Hu'um, in ma sunyi ita kam ta
manta, ko yaushe tana mamakin irin wannan
lamarin, kai ba ka damuu da mutum ba amma
shi ya damu da kai. Wallahi duk zamanta a
gidan ba zata iya cewa ga yanda suke zaune
da mijinta ba, tana dai musu kyakkyawan zato
kamar yanda musulunci yace mu kyautata zato
ga junanmu. Ta kammala komai kafin ya dawo
kamar yanda ta saba, jikinta da dakinta
kamshi. Taa cikin balle ma Khalil botirin riga,
taji shigowar shi da mashin da yake ciki yake
shigo dashi
Khalil ya kwace ya zura da gudu, shi a dole ya
gane babash ne ya dawo. Ta biyo shi daidai
lokacin da ya gama kafe mashin dinsa. Ya sur
dan nashi ta iso gurin. Ta sabi jakarshi daga
kafada da kot dn shi dake daya gefe. Ya
dubeta da murmushi. Ina mamakin wayon
khalil , har ya gane karan mashin dina? tayi
dariya, " kai ya biyo ae shima ya dan dara. Kina
nufin nima ina da wayo? Ta ja hannunshi " Zo
muje daki in fada maka" Suka jera suna dariya.
Tasan en leken asirin suna nan suna kallo, duk
ma a inda suke Tabbas haka ne, dmin kuwa
suna ta window din dakunansu suna leke. Tir
da irin matan nan masu sa ido a harkar da
bata shafe su ba
Ikilima kuwa suna shiga ya zube kan kujera shi
da danshi, ita kuma ta sulale kasa tana cire
mishi takalmi da safa. Ta tura safunan cikin
takalmin ta mike yana motsa yatsun kafarsa.
Madam baki fada min wayon me gare ni ba? "
Tace zan fada maka, ka bini bashi" Ya ce
shikenan" Ta tsiyaya ruwan da ta dire masa
cikin kofi ta mika masa" Sha wannan yayana"
Ya dire kofin daidai lokacin da take cewa Abinci
ko wanka? " yace "Abinci sai anjima don mun
hadu da Mukhtar na rage masa hanya zuwa
gida, daga shiga mu gaisa da Rahama suka
tsare ni sai naci abinci, dole babu yadda zanyi
sai da naci"
Ta mishi hararar wasa " Kaje kwadayi ko?"
yace banci da yawa ba kanwata. Zanci anjima"
Ta nufi bayi ta hada masa ruwan wanka ya
mike yana mika don son samu ne wankan ma
ayi min wallahi. Nazira kanwarshi tayi sallama,
suka amsa ta gaida su cikin ladabi sannan
tace " Inji Hajiya wai gashi tsarabar kauye" Ta
miko mata tsintsiya guda biyu. IKILIMA ta ce "
Yau ta dawo? Nazira tace "Eh" Ikilima tace
"Nagode" Ta dauki naira goa ta ba Nazira
"kema ungo wannan nagde" Nazira tayi godiya
ta tafi tana murna
Kyautar Ikilima tasa kowa sonta "Khalil ya
shiga ihu zai bi Nazira, Mahmood ya kwala
mata kira ta dawo ya ce " Dauke shi kutafi.
Amma kada ki bari ya bata jikinshi" Tace "To"
Suna fita ya dubi Ikilima ya dan marairaice
murya zan samu wankan?' Muje " Ta tura kofar
dakin, kan gado ya zube wai ta cire masa
kaya. Karshe sai da ya bada sako sannan aka
je wankan. Bayan isha'i, suna cin abinci ya
tuna, ya tashi zaraf ya nufi cikin daki. Jakarshi
ta Office ya ciro wata takarda ya dubi Ikilima
"Ranki ya dade na manta. Bankinmu ta tura ni
reshenmu dake Kaduna" Ta zaro idanu "Can
zaka koma "yace " Eh" ranan litinin kin ga tun
lahadi ya kamata ace ina can.saboda in samu
matsuguni"
Ikilima tace "Wayyo Allah!Ya ya zanyi in saba?
yace Ni kaina damuwata kenan. Kin ga shaf
tunda na dawo gida kin mantar dani,
yanzunnan kawae abinne ya zo min kwatsam!
ya dauko wayar shi ya soma kiran layin
Abubakar, wani abokinshi ne suka yi bautar
kasa tare.
Bayan sun gaisa yace "Abubakar dan Allah ina
son dakin haya ne nan unguwoyin dake kusa
da GT Abubakar ya ce " Sun dawo da kai ne
nan kaduna? ya ce sun dawo dani wallahi " Ya
ce tunda muna Alkali Road, kazo mu hade a
dakina kafin ka samu"
Mahmood ya ce To na gode, sai na shigo ranar
lahadi "Ikilima ta dube shi, "Har ka samu
masauki? Ya ce Na samu "Tace TO , amma mai
masaukin naka yana da kirki koh? Yace
Abubakar mutumin kirki ne , a sanina dana
mishi da "Suka yi shiru ta zabga tagumi ya ce
"Ikilima bana so ki damu" Ta dube shi "iNA JIN
LABARIN KADUNA, INA TSORON MATAN
KADUNA, ANCE SUNA KWACE MAZAN
MUTANE" Ya ce" inji wa? Tace "wasu "yan
ajinmu naji suna labari, dayar tana cewa mijinta
yana aiki a kaduna wai yanzun ya koma
neman matan banza.
Dama a nan din ma yana yi tun kafin ya koma
can" Ya gyara zama"Look Ikilima, duk mutumin
da ya je wani guri ya shiga neman mata a garin
su ma yana yi a boye, ban yabi kaina ba amma
wallahi ba halina ba ne : ta ce "To ni dai ka
daina kallon mata" Zan kiyaye, ki wantar da
hankalinki" Cikin sauran kwanakin kafin
lahadiduk sunyi ne cikin bankwana. Ya je
kwantagra ranar asabar in da ya shaida ma
Hajiya Hauwa Mahaifiyarsa komai, tasa
albarka sannan tayi maasa nasiha.Duk
abokanshi ya sallame su
Ranar lahadi da safe yaje ya sallami
mahaifinshi kafin ya fita da Malam Usman duk
sunyi masa nasiha da sanya albarka, sannan
ya dawo ya samu Ikilima ta gama komai, ta
zauna tayi uban tagumi tare da tsura ma Khalil
idanu ko yaya zai yi in ya daina ganin shi? Ya
dube ta, "Ikilima tunanin menene kike yi haka
har baki ji sallamar da nake ba ? Uhum, tunanin
tafiyarka nake yi" Ya zauna tare da kallom
agogo. "Dag yanzu zuwa uku na yamma duk
lokacin ki ne, muyi sallama sosai." Don kan shi
ya shimfidan da khalil din, suka bude shafin
soyayay, ita ce ta shirya masa akwatin
kayanshi na ciki, singileti da boxers ta zauna ta
goge su duk abinda yake bukata ta shirya
masa
Sannan ta shiga zubar da kwalla,ya rungumeta
yana lalllashi tare da share mata hawayenta,
har gidan su ta raaka shi bayan yayi masu
Maman Ummi sallam, dama tun safe yayi
sallama da mazajensu, ya sallami yan gidansu
Musa ya goya shi a Mashin din ya kafe a gidan
tare da bawa Ikiilima makullin. Bayan ya sauka
tasha, sai ya tsare mai Mashn zuwa Alkali
Road, da waya suka yi ta amfani har ya iso
gidan su Abubakar, ya shiga sun gaisa da
mahaifiyar su Abubakar. Wayayyiyar mace ce
mai kirki da fara'a baban daki ne mai hade da
bayi yana dauke da katuwar katifa, ga kayan
kallo ya ajiye kayan shi ya shiga wanka. Ahura
kanwar Abubakar ta dire masa abinci ta fita.
Da ya fito Abubakar ya ce Ga fa abinci" yace
sai sun yi sallah. Dare ya tsala idanunshi suna
lumshe amma ba bacci yake ba. Ya dauki
wayarshi ya kira layin Ikilima amma yaki shiga.
Dole ya hakura
Da safe ya gama shiri kenan Ashura ta shigo
dauke da tiren karin kumallo. Tana sanye ne da
cikin wani dan uban sun yadi kalar ja dinkin
riga da siket, sun dame ta tsam. Cikin salon
magaa ta ce "
Ta ce "Mamun an tashi lafia? "Ya dube ta lafia
lau. Amma tun jya nace miki Mahmood " Ta ce
Na fi jin dadin Mamun n in ka gama sai mu
wuce kasan nima GT nake"Ya ce Haka
Abubakar ya gaya min jiya. Da ya bude jakarsa
don sa kaya, wani kamshi ne ya ziyarci
hancinsa sai kum wata yar leta da ya gani.
Tare suke zuwa da Ashura kullum su dawo
tare. Ashura fara ce doguwa mara jiki, fara ce
yar gayu.Koda yake "yan banki yan gayu ne fari
da salo da fi'iligurin Ashura karshe ce, hatta
Hausa iin tana yi sai ka tsaya kallonta bare
trani
Bare turanci. Ya kwanta rigingine akan katifa
ya ciro yar takardar data zamar mishi abin
karatu kullum, yan kalamai ne Ikilima ta rubuta
ta saka cikin jakar da ta shirya masa kayan
bayan ta feshe ta da turare.Yauce rana ta hudu
da zaya sake karanta yar takardar, kawae
cewa tayi . "INA FATA KA SAUKA
LAFIA.ZUMANA,ICE CREAM DINA, LIPTON
DINA, MAI CIKA INBOX DINA DA SAKONNI
MASU DINBIN LADA. INA SONKA SOSAI.
Ya juya rigingine,dama Ikilima na sonshi? Ko
yaushe ya sake karanta yar takardar sai ya ji
tamkar yayi tsuntsu ya je gida. Ya fidda
wayarshi ya rubuta"INA SONKI SOSAI,ABIN
NISHADINA. INA SO RANAR JUMA'A KIYI
DELETE DIN KOMAI NA CIKIN IBOX DIN NAN,
ZAN ZO DA ZAFAFAN SAKONNI, LADANSU
KUWA ALLAH NE KADAE YA SANI" Ya tura
mata yana murmushi duk da lokacin da ya
maimaita takardar sai ya tura mata sakon salo
daba daban. Ikilima tana kwance taji shigowar
message, lallai yar takardar tata ta tabi
zuciyarshi. Ta gama karantawa, salon shi a
yau ya burge ta har ta rubuta cewa: "Tun
yanzu na rubuta delete all" Ta tura mishi, yayi
dariya , irin haka ce suke yi duk dare. Yafi son
suyi text da ita fiye da call don ya fi jin cikinta.
A waya bata iya mishi magana irin haka. Ranar
jumaa day a cika sati biyu it ace ya shaida
mata ta soma duban hanyara shi, tun daga uku
dan daga office in ya taso juma zaya
wuto.dole ta tayi murna sati biyu kenan basu
ga juna ba. Tun safe tasa Musa ya siyo mata
kaza da kayan salad, ta shirya mishi fara
shinkafa da miyar kaza, ta hada mishi juice din
abarba da coconut da dabino. Tayi gayunta
cikin shadda. Shima khalil ta masa har hudu
da rabi shiru bashi ba labarin shi gashi ta kira
shi amma wayar taki shiga . Damuwa tay ta
samu guri ta zana tare da zabga tagumi ,
wayarta ta soma ruri tayi zaraf ta daga dn ta
san shine. Yace kanwata kiyi hakurii b azan
samu daan zuwa ba sai wani satin kila Tayi
dim, yace shiru? Sai ta kasha wayar ta
dawo palo ta zauna, idanunta suka cko da
kwalla .
Ya daga labule ya shigo tare da sallama, ta
mike tsaye da sauri tana dubanshi ,
hannuwanshi ya ware said a ta mishi duka a
kirji sannan ta fada ya rufe dukan su suna
dariya
Ya daga Khalil sama yana sumbatar shi a
ko'ina, suka zube kan kujera ta zamo tana cire
mishi saa a takalmi, ya dube ta "Kin san nasha
wuya kafin na saba da cire takalmi da safa? Ta
dube shi da murmushi "ya ce , kin shagwaba ni
dayawa ko gurin shafa mai ina gane kurena.
Ta ce Allah yasa kada ciwo ya same ka a can
yanda baka son magani. Da sauri ta cude shi
tas. Wagambari ta ciro mishi rigar 3 kwata sai
yaba shi take yi wai kaduna ta amshe shi, yayi
kiba yayi kyau. fatar shi ta goge yace a'a shi
ya rame ne saboda.........
Saboda rashnta kusa. Ta ganatar mishi da
abinci yace dama ina jim kamshin tuni ya cika
min hanci. Yana cikin dibar girki sai gasu
sulaiman nan ta karo musu suka ci suna mishi
tsiya wai ya kara wayewa. Ranar dai hum....!
Sakonni ba a magana, da safe yace lolipop
dina gaskiya na yarda kinyi delete din inbox din
all. Allah ya bada lada" Darya tayi tare da rufe
fuska.Ya fita don zuwa gidansu da gaida
abokanan arziki
Haka nan sun soma sabawa, wani lokacin
yazo sati daya, wani lokacin sati biyu.Duk
komawa idan zaya yi sai ta masa miyar kaji ko
danbum nama. Ashura sai ta ringa yi mishi
tsiya dacewa Mman shi naji dashi, sai kac wani
dan makaranta, sam bata san yana da mata
ba. Dinkunan Ashura suna burge shi, ya sata
taraka shi kasuwa ya sayi yadika masu kyau,
ya kuma kai ma telanta it ace jagora, Aka tsala
wa Ikilima dinkuna, a zatonta kanwarshi ce,
don haka taji yana fadi.
Amma koda ya kaiwa ikilima tayi godiya amma
bata yaba dinkunan ba don ita tafi son zani
maimakon siket . Nata ganin asarar kaya ne,
tun daga nan sai dai ya siyo mata ya kawo
mata takai dinkin tad a kanta.Zamansu zama
ne na so da kyauata wa juna tare da ganin
kimar juna. Cikinta kuwa ya kusan zuwa dunya,
wannan karon dai Ahura c eta raka shi ya darzo
kayan haihuwa, yace mata kanwarshi ce zata
haihu.Kaya kuwa na iyayan kudi,ikilia tayi ta
mishi godiya tare da mamakin yanda yasan
kayan haihuwa,haka sai kace mace.Ko kusa
bai taba bata labarin Ashura ba saboda kada
zuciyarta ta zargi wani abu. Tace masa in Allah
ya sauke ta lafia tana son zata shiga SS 3 don
ta zana jarabawarta tare da masu fita ko zata
samu takardarta ta shaidar gama secondary
school. Yace to. Nafisa ta samu sauki
sakamakon maganin masu kanjamau da take
sha, in ba wanda ya sani ba babu mai cewa
tana dauke da ciwon kuma Ikilima ta bata
shawaran cewa ta shiga Islamiyya.
Hakan kuwa ta faru, sai dai kun san ma Ikilimar
c eta sata. Su yaya danlami yanzun an koma
harkar dinkuna tamkar da.Aminu mara kunya
gurin baban nasu day a raina ma wayo ya
koma. Ikilima ta sauka lafia,ranar wata laraba
ta samu yarta mace.Tun kafin Mahmood ya
diro Minna yake fadin ya samu uwarshi.Ranar
ce Ashura tasan Mahmood kanwarshin da yake
fada matarsa ce. Nan suka shiga yi masa
barka. Ashura dai bata so haka ba,don tun
ranar da ta soma saka mahmood a idonta ta
fara son shi.Duk yanda yaso a cashe suna
Ikilima ta ce a闂傚倸鍊搁崐鎼佸磹閻戣姤鍤勯柛顐f礀绾惧鏌曟繛鐐珔缁炬儳娼¢弻锛勪沪鐠囨彃濮曢梺绋款儐閿曘垽寮婚妸鈺傚亞闁稿本绋戦锟� babu taron suna kai dama
baka nan ?
Yace 闂傚倸鍊搁崐鎼佸磹閻戣姤鍤勯柛顐f礀绾惧鏌曟繛鐐珔缁炬儳娼¢弻銈囧枈閸楃偛顫紒鎯у⒔閸嬫捇骞堥妸銉㈡斀闁圭偓娼欓锟� khalil dan ba mu dashi ne wannan ko
ba laifi 闂傚倸鍊搁崐鎼佸磹閻戣姤鍤勯柛顐f礀绾惧鏌曟繛鐐珔缁炬儳娼¢弻銈囧枈閸楃偛顫紓浣插亾闁告洦鍘剧壕鍏笺亜閹伴潧澧悗姘炬嫹 ce A闂傚倸鍊搁崐鎼佸磹閻戣姤鍤勯柛顐f礀绾惧鏌曟繛鐐珔缁炬儳娼¢弻锛勪沪鐠囨彃濮曢梺绋款儐閿曘垽寮婚妸鈺傚亞闁稿本绋戦锟� batun tamkar zzaya sasu
rigima, har ya hada tad a Hajiya Uwa.Hajiya
tace tunda bata so kyale ta, mum ayi namu a
nanK
MABUDIN WAHALA 3**6
Y ace 顏� Manyan raguna biyu ya sai
mata ya kuma dire mata duk wani abu da zata
nema, sannan ya bata ishashhen kudi, Tun day
a koma sai dai suyi waya har take mishi korafi
wato yanzun bata da amfani tunda tana jego
shi ne yasa yaki zuwa ko? Yak an ce bah aka
bane kanwata. Muna nesa nesa ban damuwa
in ko ina ganinki ban damuwa in ko ina aninki
kema kin san zan sa rai amma duk ranar da
kika cika arbain, to ki shirya zaki biyan bashi
mai yawa.
Ashura tana burge Mahmood, don yana son
mace ta gaban mota, ta fita unguwa, mai tsarin
ado yanga kwarkwasa da kisisina. Son shi ace
Ikilima tana irin wannan abubuwan gare shi,
amma ita inaaa! Yana zaune gaban laptop din
sh yana duba facebook, sai yaga wani hoton
Ashura data dauka tana mishi albishir da tayi
sabon hoto, nan ya yaba. Ashe itama tana
kusa, sai suka ci gaba da hira.Daga nan sai ya
zamar musu jiki, duk dare sai sunn hadu a
facebook ko 2go. Dagan an sai suka soma
musayar kalaman soyayya, ta 2go don yafi
sirri. Basa nuna ma kowa cewa suna soyayya.
Saboda basa son bankinsu su sani, domin
doka ce bankin ba zasu bari ma顓絘ta suyi
musu soyayya ba.
Haka nan koda Ikilima tayi arba'in da ya je bai
nuna mata komai ba sai ma wani so da tattali
da yake nuna mata ita da ya'yanta. Ya sayi
wani fili sakamakon shawar da yayi da ikilima
kan cewa zaya sayi mota. Tace ,"yaya kasai fili
in Allah ya hore sai ka gina, sannan a sa sai
motar "ya ce to ban da abinki nan ma ae ba
haya bane" Ta ce duk da haka dai na gado ba
naka bane, ka lura kana da kannai da yawa ko
su Musa in sunyi aure gidan nan zasu
hara,lokacin kai ka matsa gaa."YACE "Haka
ne" Ya sayi filin har an soma gini, haan yayi wa
Alhaji Ibrahim yaji dadi, har ma ya kasa
daurewa sai da ya sanar da dansa nasa cewa
"Mahmood yanzun na amince ka soma yin
hankali, kuma ina sa ran zaka rike kannanka"
Da ya natsu cikin tunani sai ya ce "Kenan
Ikilima ta fishi tunani har ta hango abin da shi
nai hango ba? Lallai ya daina yarda da batun
nan da ake cewa mata ba abokan shawara ba
ne"
Yarsu Hauwa'u suna kiranta Ummita, tayi wayo
kuma har sunje kwantagora don kai ta gurin
takwararta. Nafisa tana cikin bin layin karbar
magani sai taji an dafa ta, tare da cewa "Nafisa
ko ba ita bace? Ta dubi mai maganar, ta rufe
fuskarta cikin niqabi. Tace wacece ke? Faty ta
daga niqabinta duk da rama da kurajen da
suka munanata bai sa Nafisa ta gane Faty ba,
wadda gurin bikinta suka hadu da Alhaji Jamili
Dukku. Tace "Faty kema kin hadu da alakakai
dinne? Faty tace "Ga shaida" Nafisa ta jinjina
kai, sannan tace "Layi ya kusa zuwa kanmu
bari mu amsa sai muyi labarin bayan rabuwa.
Sai da suka fita wajen asibiti , sannan suka
samu wani benchi suka zauna .Faty t ace
Nafisa ai ke naga kamar bai kamaki sosai ba.顏�
Nafissa tace tace ya kamani mana ani nasha
kema in kina sha zaki samu sauki. Dubi jikina
ga tababon kurajen nan , kin san tabon su
baya mutuwa Faty ta cire niqabin tasa cikin
jaka tare da cewa, Duk lokacin dana saka
niqabin nan sai na ringa tunanin cewa ina
cutar da masu sakawa, tunda su don Allah
suke sawa闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏� Nafisa tace 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌ょ喊鍗炲闁绘粏宕甸埀顒傚仯閸婃鈻嶉ˇ锟� ne , da muna
kallon masu shiga irin ta addinin mususlunci
bas u waye bay au gashi irin halin da muke ciki
mu wayyayu. Fati tace, kinsan Allah lokacin
da kuka kai ni gidan mijina ranar ya soma ludi
dani nayi nay inki abin ya gagara, iyayenan
sunga kudi sun makace lokacin da nazo gida
don in shaida musu halin da ake ciki,
maimakon su tsorata su raba mu sai suka ce
sharri ne na mishi. Suka ce in ban zauna ba
zasu tsine min, na hakura , sam na mata babu
biyyaya ga abokin halitta dan saba ma
Mahalicci, ya mutumin da ciwon bayan ya
likamin gadon shi da aka raba aka bani nawa
duk sun tafi gurin magani.Yanu dai gani ba
komai sai ciwo ya ya kwace mata.
Nafiisa ma cikin kuka take bata hakuri sannan
tace gara ke tusasa ki akayi, ni kuwa fa? Nice
ma da kaina gashi yanzun na tsira da
ciwo suka jero tafe suna ganin laifin
kawunansu. Ashura da mahmood a nata
soyayya, sai dai yana jin tsoron Ikilima ta sani,
haka nan kullum kara lura da ita yake yi , ita
day an yaranta. Tuni kuma ya biya mata kudi
tayi jarabawa tare da masu zana SSCE a wata
makarantar kudi , karatuta na islamiyya kuwa
ae shi tasa gaba, don har sunyi nisa
Sanawiyya .Ya so ta dainakoyarwa tace a
ladan take yimawa, sannan in kana karantar da
dalibai karatunka yana karuwa e Shikenan
Gininshi yayi nisa, a hankali yake tafiyar dashi.
Ikilima ta farka daga bacci sakamakon hannu
data kai makwancinsa bata jishi ba, ta tashi
zaune a zatonta toilet ya shiga. Amma sai a
jiyo Magana kasa-kasa, a zatonta wani ne ba
lafia a gidan. Dn haa sai ta nufi falon da
hanzari ta kama labule kenan zata buda taji
yana cewa., my Dear ba ina nufin ban
damu dake ba ne, ki fahimta . In nazo gida
lokacin iyalina ne b azan iya free call ba. Amma
zamu hadu da safe a facebook ko a 2go., kin
san ina sonki kada ki damu Ikilima ta toshe
kunnuwanta , tare da komawa ta zauna baking
ado ta sma tambayar kanta dawa mijinta ke
waya.azubillahi minasshaidanir rajim顏� Ta
lura shedan yana son yasa tayi zato. Ta sulale
ta kwanta cike da nadamar farkawara.kunnu
wanta na amsa kuwwar Kalmar da mijinta yake
furtawa wata kin san ina sankiTo wacece?
A hankali ta furta cewa Matsala顏� ta sani tana
da kishi mai tsanani shigowar shi taji, don haka
ta lumshe ido kirjinta na bugawa a hankali ya
kamata ya gyara mata kwanciya don kada ya
tashe ta, ga mamakinshi sai yaji ta sharkaf da
zufa ga kuma fanka.
Ya janyo singiltin shi dake gefen gado yana
share mata tayi mika tare da hade idanu a
hankali tamkar yanzun ta farka, ta dube shi
lafia? YA CE zufa naga kina yi, ina ne yake miki
ciwo? Ta maida kanta a hankali ta kwanta
sannan tace ba ko. Shima ya kwanta tare
da jawo ta jikishi Bayan ya kara fanka duk da
cewa shi fankar ta dame shi bai jima ba yayi
baccy, ita kuwa zamewa tayi ta rage fankan ta
zuba mishi ido Tana kishinsa amma bat a iya
ja da hukuncin Allah, fatanta in dai ba yaa
ce ya gamu da ita ba tazo su zauna.
Sam batayi baccy ba har asubahi, haka ta
tashi sukuku jiki ba karfi , ama bata nuna mishi
komai ba sai dai shi ne yaga duk ba yanda ya
saba ganin ta ba. Yana zaune ka kujera ta
gama goge goge kallonta kawae yake don ko
karyawa bata yi ba ta dibo kayan su khalil da
ummita zata goge. Ta soma kenan yace "kawo
n taya ki" Ta dube shi ka barshi zan goge" Ya
amshi dutsen "kawo ki karya, tun safe kike aiki
kin ki karyawa, ina zaton ma baki da lafia, zufar
da kika dinga yi jiya ta ban tsoro" Fuskata ba
yabo ba fallasa tace lafia ta lau" jiya anyi zufa
ne? Ya ce "to je ki karya" Ta girgiza kai. Yau
haka kawae bana jin cin komai , kuma ba inda
ke min ciwo. Yace shikenan" yaci gaba da guga
ita kuma ta saka kaset ba kira'ar Abdullahi
Abba tac gaba da bi a hankali.
Shi kuwa yana ta guga tare dayi mata hiraraki
yana so dole sai ya sata saki jikinta" Ta mike ta
nufi kitchen ta dibi kayan miya ta markada,, ta
shigo falon ta same shi "Baban Khalil me za'a
dafa? Ya dube ta cikin mamaki Dama ni ne
nake fadin abin da za'a dafa? Koyaushe zabar
mana kike yi ban taba kin ci ba"
Ta sunkuyar da kai kasa, daga yau in har kana
gari abinda ranka yake so shi zamu yi. Ya tashi
yazo har inda take ya kama hannunta suka
zauna yace Ikilima kale ni闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌ょ喊鍗炲妞ゎ偅娲樻穱濠囧箻閸涱喖顏� dube shi 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌$仦璇插姕閻庣數濞€閺屾洟宕奸悢绋跨ar
dani meke damunki闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏�
Ta kakro murmushi Ba komai闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏� Yace 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌ょ喊鍗炲缂佲偓閸曨厾纾兼い鎰靛墯鐎氾拷 me ya
kawo kice ina nan ni zan dinga zabar abinda
za闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌$仦璇插姕闁稿锕㈤弻銊╂偆閸屾稑顏� dafa, ko kin taba gani nace abincin ki baiyi
ba ? Tayi yar dariya 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌$仦璇插姕閻庣數濞€閺屻劑鎮ら崒娑橆伓 kawae nake na kara
faranta maka, in tabbatar baka cutuwa da nit a
kowane fanni , ma闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌$仦璇插姕闁稿锕㈤幃妤呭捶椤撶噥妫� ina son in dinga fita
hakkinka. Ya rike hannunta gam 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌涘▎蹇fШ闁绘繂鐖奸弻锟犲炊閵夈儳浠奸梺缁樺笒閻忔岸濡甸崟顖氱鐎广儱娴傚Σ顕€姊烘潪鎵妽缂佹宕縜 fita
hakkina Ikilima , ni dai nasan in sanadin miji ne
ake shiga Aljanna zaki shige tab a haufi 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌ょ喊鍗炲缂佲偓閸曨厾纾兼い鎰靛墯鐎氾拷 ce
Bababn Khalil don Allah zabi abinda kake so 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌涘▎蹇fЧ濞存嚎鍊濋弻銊╂偆閸屾稑顏�
ace To yi manatuwon shinkafa miyan alayahu闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏�
Tayi murmushi 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌$仦璇插姎闁兼瓕顫夐妵鍕晜閸忕厧顏� gani nida doya zan dafa sai
yace Yauwa1 Dafa kawae闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏� Tai dariya 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌ょ喊鍗炲闁活厽鑹捐灃闁挎繂鎳庨弳鐐烘煟閹惧啿鏆i柡灞炬礃瀵板嫬鈽夊鍡樺枠闁诲氦顫夊ú鈺呭箯閿燂拷
tuwon zamuyi ni nasan na jima ina kwararka,
don Allah ka yafe min. Ya daure fuska tamkar
bai taba dariya ba 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌$仦璇插姕闁搞倖鍨块弻娑橆吋鎼淬垺鍣� bata miki rai in kina
min irin wannan maganan Ni ne nace kin taba
cutar dani? Ta mike tare da cewa Allah ya baka
hakuri
Da yamma sai gashi kim kim da kwalin AC tare
da me sakawa, tayo sororo yasan zata yi
korafi, don haka sai ya daure fuska Aka gama
saka AC a bedroom. Takaici ya ishe ta
mutumin dake gini me ya hada shi da siyan
AC ? Tasan AC din a banza za ya kai 40k, kafin
kace haka tuni daki ya guraye da snayi ya
hadu da kamshin turaren da tasa na dakin ya
saka yanayi mai dadi. Tana zaune a palo ya
shigo gurin Abokanshi ta mishi sannu shima ba
tare day a amsa ba Ta dago sai suka hada ido.
Ya zauna gefenta. 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌涘▎蹇fЧ缂傚秴娲弻娑樜旈埀顒勫绩閿燂拷 shin Ikilima mee
damunki ne?daga lokacin dana shigo da AC
duk kika sake yin kicin kicin da ranki?闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏� Baban
Khalil kai dake aikin gini me zamuyi da AC
yanzun? Dab a sai ka bari ba in ka gama ginin
sai ka saka ko nawa ka ke so ba ?闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏�
Yayi aksa da murya 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌ょ喊鍗炲闁绘粏顕ч埞鎴炲緞瀹€濠勫悅 kef a nasa, kinga
zufar da kika dinga yi jiya ? Nasan in nace zan
tsaya yin shawararki ba zaki bari ba Tace Allah
ya saka da alkhairi闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏� Y ace Fuskarki babu ko
fara闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌$仦璇插姕闁稿锕㈤弻銊╂偆閸屾稑顏�?闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧灝鈹戦悩瀹犲缂佺媭鍨堕弻銊╂偆閸屾稑顏� Ta dube shi sannan ta danyi yake.
Yayi dan murmushi 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌ょ喊鍗炲闁绘粎绮幈銊モ攽閸ャ劌绀媤ata kenan 闂傚倸鍊搁崐鐑芥嚄閸洖纾婚柕濞炬櫅绾惧潡鏌涘▎蹇fЧ濞存嚎鍊濋弻锟犲焵椤掑嫭鏅搁柨鐕傛嫹 jawo
wayarshi ya shiga danne danne tasan facebook
din ne na fama
Ta mike ta nufi daki don yin baccy
Ranar da zai tafi har ya kai Kaduna yana
mamaki canzawar da Ikiima tayi sai wata
Magana da ta fada mishi da ta

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment