Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya
nuna baya so me yasa ta amso? In ma Baban
ta ya ji wannan batun ranta zai matukar baci.
Nafsa suka yi sallama suka shigo,ta dubi dakin
ko ta ina sannan ta zauna a kujera. Iklima ta
nata yi musu sannu da zuwa,Nafsa sai ya
mutsa fuska take yi tare da toshe toshen
hanci,wai warin me take ji? Iklma tace "ba
komai,kin ji wari ne? Tace "naji ki shiru ban
ganku ba shi ne na biyo.
Ita kuwa nafisa jinsu shiru basuzo ba sai tasa
aminu ya kawo ta gidan byan magariba. Ikilima
ta idarda sallah kenan ta zabga tagumi tana
tunanin yadda zata shawo kan mijin nata. Sai
yanzu taga wautarta, tun acan daya nuna
bayaso meyasa ta amso? Inma babanta yaji
wannan batun ranta zai matukar baci
Nafisa sukayi sallama suka shigo, ta dubi
dakin koina sannan ta zauna a kujera. Ikilima
tanata yi musu sannu da zuwa, nafisa sai
yamutsa fuska take yi tareda toshe toshen
hanci, wai warin me takeji? Ikilima tace
bakomai, kinji warin ne? Tce najiki shiru ban
anku ba shine na biyo.
Iklma ta tashi taje gurin Maman Ummi tace
yauwa bani kudin nan dama na Mamana ne ta
bani ajiya,ga shi nan ta aiko. Ta zi ta danka
ma Nafsa tare da cewa "gashi yaya,nayi2
amma ya ki karba".Nafsa ta amsa tasa a jaka
"shi kenan yayi ma kansa. Kice masa duk
lkacin da ya canza ra'ayi ina jira. Iklima tace
"to zan fada mishi Allah Allah take yi su tafi
kafin ya shigo.
Haka yayi mata yajin kwana3, kai gsky fada da
miji babu dadi hardai irinsu mhmud, don cikin
kwanakin ikilima tayi baki ta kuma rame.
Hakuri kam ta bashi hartagaji amma bai
saurareta ba, damuwaa da rashin cin abinci su
suka haifar matada ciwoncikin tamkr mai
nakuda cikin dare yana falo inda yayi mata yaji,
yajiyo nishinta da sauri ya shigo ya riketa an
mata sannu sai 4 saura cikin yadan lafa
matada ciwo. Shine barci ya kwshesu har suka
makaara.
Toh dukda bai saki duka ba ana kulada ita, nan
tasamu dama ta bashi hkr sosai yace ya hkra
amm kadata sake I mashi makamancin wanan
tace insha Allahu bazata kumaba. Sun dawo
zamansu daidai saidai rashi domin na cefane
babu sai dai yan daabaaru.
Ita kuwa nafisa ta koma da takaicin ama tasha
alwashin cimma burinta. Taana mamakin
wacca irin tsanace wannan harya ki karban
kudin hannunta? Dubu goma ta biya aka sa
mashi wuta a shago don tayi amfani da wanan
damar ta jawoshi da kudi. Sunansa kawai zata
kaiwa boka, hakan kuwa tayi lokacin data ama
zayyanama boka komai. Saiyace bari yayi
bincike, daya gama yace maganin dazan baki
sai ya had shimfida dake zaiyi tasiri, zai bar
kow nashi bama matarsa ba in har kikayi
amfani da maganin saiya zama kina korarsa
ma. Wa'iyazubillah!
Tace toh abu mai wuyar shine yadda zamu
hada shimfida dashi don ba mazinaci bane.
Boka yace wanan kuma aikinkine, koki kawo
mana hotansa mu turo maki shi har gida, tace
to zanga me zanyi. Suka barshi akan zata
kawo hoton.
Shikuwa mahmud ya maida lamuransa ga Allah
kamar yadda ikilima kulum take tausar sa.
Yanxun sun rage barci kowane dare suna
rabasa wajen kai kukansu wajen Allah, duk da
irin sonda mahmud keyima kayan wutansu
musaman fridge dole ya fitar dasu suka sayar
don babu abinci.
Cikinta ya shiga watan haihuwa amma ko pant
basu saya ba tunda ba kudi. Asibiti ma
xuwanta 1 haryau bata koma ba don sun bata
scaning ko nuna masa takardan batayi ba sbd
zai damu. Makaranta ma ta daina xuwa tunda
ba kudin biya, towa keta batun makaranta?
Omo na wanki ma ya gagara, Allah kayi mana
da sauki.
Duk da wanan halinda suke ciki baisa ikilima
daga hankalin mijinta ba. Su maman ummi da
matan gidansu hakan yayi masu dadi. Bansan
meyasa mata kowane lokaci suke da irin
wanan dabi'ar ba wasu matan ko yaushe
burinsu suganki kina shan wahala gurin miji ko
suga kuna fada ko kuma suga bakuda cin yau
balle na gobe.
Nan zasu nuna suna son taimakwa idn anyi
kwantan abinci a baki dakin juya ayita
zundenki inkin fita unguwa a kasa gulmar ki, in
ko anga mijinki na sonki yana maki komai shi
kenan sai a dauki gaba dake ace kin cika iyayi
sai inga wanan ba halin kwarai bane domin
malamai suna aya mana;
MABUDIN WAHALA 2**7
Manzon Allah (S.A.W) yace; mu sowa yanuwan
mu abinda muka sowa kanmu, duk kuma
wanda ya rufama dan uwansa asiri Allah zai
rufa masa.
Ikilima dai ko sun bata abinci bata karba kuma
bata taba nuna masu gazawar mijinta ba. Yau
sun wayi gari ba suda komai sai shinkafa
gwangwani 5, gashi basu dakomai sai gishiri. A
hita ta jona ta dafa masu ta ajiye dan shi bai
taso bama. Ta zuba cikin kula ta zauna tasa ta
gaba tana kallo
Wani ciwo take ji can kasan mararta amma ta
danne. Ta sameshi zaune akan gado tace
ruwan wankanka ya huce. Ya dubeta cikin
tausayawa dama baki dafaba yau da zafi sai
nayi a shower. Ya shiga yayo basuda sabulu
ma da guntun omo ta aijiye mashi turare
sannan tace ga abincin sai dai yau abincin
namu shine asalin garau garau.
Ya bude kular, da miya ne? Tayi murmushi
batace komaiba ya gane. Don haka ya rufe bari
in fita in samo ko mai ne a saya. Ta rike masa
hannu kada ka ciyo bashi fa muyi hkr da
wanda ya samu Allah yana sane damu. Yayi
shiru sanan yace wanan baxai ciwuba ikilima
tace zauna ka dandana zai ciwu mana. Wlh na
neman kamar wanan bai samuba zauna ina
zuwa, ta nufi kicin ta daga galan din man
gyadan ta dina zazzagowa cikin roba ta gama
ya dan taru tasan ya isheshi taxo ta xuba
masa shinkafar cikin plte ta juye masa man
yace kefa? Tace da wani a kicin din yaci harya
koshi tanayi masa yar hira cikin dauriya don
mararta tana dan ciwo.
Tana kai kawon aikin gyaran dakinta ciwon na
karuwa daga karshe saita koma daki har bayan
laasar sai wani ruwa ke zuban mata. Tana cikin
haka ya shigo. Ta zauna cikin dariya yace
bakijin dadi ko? Ta kirkiro murmushi meka
gani? Yace kinyi wani iri ne tace na gajine.
Ya miko mata ledar hannunsa tareda cewa fura
da nono aka bani shine nace barina kawo maki
nasan kina so. Ta yatsina fuskarta sbd ciwon
dayake taso mata tace baxan shaba kasha
yanxun ina shan fura kwanarfi take sakani

Ameena Baba Suleiman
Ta yunkura barina dauko maka kofi ka juye.
Yace yi zamanki ya tashi ya fita. Yana shan
furar suna yar hira daga baya ya fahimci cewa
batajin dadi yace ikeelee baki da lfy? Tace ni
nace maka lfy lau ya tashi kona nemo kudi
muje asibiti ne?
Tace aa ina da kudina in haihuwa ce ai zan
fada maka ciwon kaine, yace ba wani kudin
dakike dashi don dai kada na ciwo bashine.
Tace zauna ni dai muci gaba da lbr kacemin
zaka fara binsu hamza aiki? Yace eh, nayiwa
su hamzan magana zan dinga binsu aikin gini
in sun samu su fada min
Cikin tausayawa tace zaka iya yayana? Yace
mezai hana? Namijine fani zama bazai minba
wlh, yanda nake ji ko dako ne zanyi. Injin nauyi
ace ni da zan ba mahifana abu saisune zasu
bani. Nine babba agidanmu ya dace ace zuwa
yanzun na ragewa babana nauyin wasu daga
cikin kannena duk cikin yayansa nine na samu
gatan makaranta
Tace Allah yasa ka koma cikin saa yace amin.
Har bashir dake buga tayals nace musu zan
bisu aiki. Cikin dare fa haihuwa gadan gadan ta
kuma hanashi kiran kowa wai ya bari saida
safe itadai ya riketa. Lokacin haihuwar yaxo
gadan gadan kankame shi tayi tana nishi
gamida salati iyaka firgicewa mahamud ya
firgice ga zatonsa mutuwa zatayi itama hakan
ta zata sai fadi take ka yafemin kace dasu
baba su yafemin
Hawaye sharkaf idanunsa baima san suna
zuwa ba. Wani yunkuri guda 1 tayi saiko ga da
ya fado ya canyare da kuka take uwa ma ta
fado sai taji tamkar an zare mata ciwon. Suka
shiga yiwa Allah godiya sai kuma ya tuna ba
kaya yace innalillahi wa ina ilaihir rajiun gashi
ba kayan baby, tce ka kira minsu hajiya kosu
maman ummi yace toh.
Ya fada tareda mikewa tace k aya masu saika
wuce idansu hajiyan. Maman ummi dukka
suka dauki sankacecen yaron mai kamada
ubansa sak suka nade shi cikin zani bayan sun
yanke cibi sai sannu suke mata. Sai gashi su
hajiya uwa da haj rabi nan aka jona ruwaa aka
wanke yaro itama tayo sunata cewa tanada
juriya, sunyi kokari su kadai basu kira kowaba
saida akace ina kaya? Yana jinta daga falo
tana cewa basusan lokacin haihuwar yayiba
harya bata kudin tace ya bari sai watan gobe
Haj uwa taace ina kikaga ana haka? Wanan ai
kuruciya ce, to ashi kin haihu babu ko wandon
da za'a sama yaron. Nan suka nade yaro cikin
zani suka gyara gurin suki nufi gida don yin
sallah. Bayan su mahmud sun dawo daga
masallaci yazo ya zauna kusada ita ya dauki
yaron yana kallonshi
Tausayin yaron ya kamashi hawaye suka zubo
masa dan shine babu kayan sawa. Ya share
hawayen ya kwantar dashi ya fita waje sukaci
karo da babansa ya dawo ya fito masada yaron
daga aljihu ya bashi ga wann nasan bakada
kudi kuma su haj sunce ka bata kudin siyayyar
bata yo ba bata zaci haihuwa ba, ai wanan
shirmene.
Mahmud ya dubi babansa yace baba wlh ta
fadi hakane donta rufan asiri amma wlh ban
taba bata ko sisi ba. Alhajin yace Allah sarki
matar rufin asiri kenan. To ayi kokari a nemo
mashi tufafi. Yace to Allah ya saka. Ya shigo
ya samu ta farka yace baba na gaisheki ya
nuna mata kudindaya kawo tace to kadan siyo
mana kayan tea daga nan dan Allah kada kaci
bashi. Yayi murmushi ya fita
Ya tsinto masa kaya yan masu sauki, ya kuma
ciyo bashin kaan shayi gurin da yake sari da.
Yaje gidansu ya fada kuma babansu ya shaida
ma haule. Shima baban yaxo dubata sanan ya
kawo dubu 1 yace ta rike don kowa yasan
halinda suke ciki
Su hamxa sun sami aiki kuma yabisu harya
somo dubu1 ya dan sayo shinkafa. Killum haj
uwa na zuwa mata wanka tayima yaro ,
kannensa na gidan aure suzo suyi mata girki.
Ranar kauri duk ya damu don sun saba kan
akuyoyin nan kowa yasan ana dafawa da kunu
Ita kuwa tace ta yafe kada ya damu. Makwabta
da dangi kowa yazo cewa take ita batason
bidi'a taron suna ma dasu maman ummi
sukazo sukace ta kawo cingam za'a raba tace
ba za'ayi taroba nan suka koma daki suna ta
dariya dama tunda akayi haihuwar suke cewa
zasuci dariya zasuga yanda zaayi hidima bata
daure masa gindi ba ita mai tausayin miji sai
su wuni a daki ai gashinan. Mhm mutane
kenan Allah yasa mufi karfin zuciyarmu Allah
ya tsaremu daga sharrin masu sharri da
mahaassada
Ko daya zo mata da shawarar cewa yana son
yasa sunan mahaifinsa ibrahim, tace Allah ya
albrkace shi. Ana gobe suna yace ya za'ayi?
Tace ba fa za ayi wani taro ba, dama wannan
dk ba sunna bane bazamu ci bashi ba. Tnda
Allah yasa lfyta lau mun gode ma Allah. Ido ya
zura mata bai san me zai ce mata ba. Ya
rungumeta tare da cewa, na gode ikilima ynda
kike rufa min asiri Allah ya rufa miki kema.
Mahaifiyar shi taxo ana gobe suna, acan gidan
taji wai ba taron suna, sai dare taxo gidan
mejego. Sukayi hira, tace yan nan naji ance
baza ayi taron suna ba? Tace mama dk
wannan bidi'a ce, ku dai in zakuyi kuyi a can
gidn alhji. Tace shikenan, amma kina samun
dan nama kina ci ko? Tace yana siyo min.
Alhalin tnda ta haihu ko kifi bata gani ba. Byn
tfyrta da yan mintuna ne sai ga haule da nafi'u,
murna gurin ikilima, haule ta kalli ko ina,
sannan tace dubi dakin yarinyar nan sai kace
dakin tsohuwa. Ikilima Batayi magana ba, ta
tashi ta miko mata yaron ta amshe shi tana
kallanshi tana tabe baki, baku da tawul din
daukan jariri? Tace muna dasu, an wanke ne
basu bushe ba. Ta kalli ko ina, ina kayan jariri
fa, ina nufin durowar yaro? Tace, muna da
akwati shiyasa nace ya brshi. Haule tace
wancan mitsiyaciyar akwatin guda 1 jal, kai
Allah ya raba mu da tsiya, dubi dk ynda kika
kare kika dashe sai kace wnda kika kwnta
ciwo. To me zaku girka goben?
Ikilima tace, mama nace bana son taron suna,
kin san dk bidi'a ne. Haule tace, matsiyaciya,
nasan dama ke ai ba wnda ke kan tafarki
madaidaici se ke. To kin hutar damu, dama
nafisa tace ita baxata zo ba, dn hk muma
masha zamanmu. Ita dai bata ce komai ba, ta
bada yaro ta mike tare da cewa, kudin mu ya
huta dn wlhy tnda kince bb taron suna sile
biyar bazan kashe miki ba. Ikilima tace ba
komai mama, haka ma na gode Allah. Tace
oho miki dai.
A masallaci aka sa suna. Mejego tai kyau cikin
atamfar akwatinta daya data rage, ta bada aka
dinko mata ta saka abinta. Yaro ma cikin
kayanshi sabo. Ibrahim amma khalil zasu
dinga kiranshi. Ya sameta zaune tana shayar
da yaron shima dk ya rame ya dube su da kyau
yai murmushi. Maman khalil kunyi kyau
dayawa. Tace mun gode baban khalil. Ya ciro
dubu goma sha uku da dari 5 ya miko mata
tare da cewa kirga ta kirga ta bashi yace su
mama ne dasu hajia wai suka bani
gudunmawa dubu takwas dari 5, dubu 5 km bb
ya bani wai in cika in sai rago. Ta zuba mishi
ido ynxun ragon zaka siya? Yace Eh, tace ni ko
nawa ganin da an hkra da rage ka sai mana
kayan abinci mu dan kwana 2 muna ci. Yai
shiru yana tuna matan gidan su wato su
maman ummi, jia ya shigo da dare gulma tayi
dadi ko sallamar shi basuji ba, suna cewa kai
wannan mata da son mijin tsiya take, dn kar ya
wahala ne tace kada ayi taron suna da ta bude
wuta ko rance ne ba dolen shi yai ba, to bari
mu gani za ayi hakika ko shima zata ce ta
yafe? Maman ummi tace tnda fa ta haihu ko kifi
bata taba ci ba, kina ganin abincin ma da kyar
ake samu, wake ta wani kifi? Dk yana jinsu.
Ikilima ta dube shi tana cewa, shawara ce, in
km kana ganin gara ragon to bb matsala. Ya
sauke ajiyar zucia ikilima ynda kika ce din yafi
sai dai surutun mutane ne yan sa ido, kai baka
damu da mu2m ba shi ya damu da kai. Tace
ina ruwanmu da mutane? Mu dai muyi harkar
gabanmu. Bama cire rai dg rahamar Allah, yace
shi knan haka za ayi, Allah ya kara mana kauna
da son juna tace amin.
Itama matar baban su ikilima ta dako yaji, su
manja, gishiri, magi, daddawa har da albasa.
Shi km baban karamin buhun shinkafa da
turmin zani da rigar yaro suka kawo. Danlami
da haule tace kada su mata komai ya sai mata
turmin zani a boye ya ba nafi'u ya kai mata.
Kannan mahmud da mamanshi dasu hajia sun
hada ma mejego kaya da zannuwa 3 da riguna
sun kai mata. Albrkacin haihuwa sun sami
alkairi. Haka nan bayan suna makota wasu sun
aiko mata, me sabulu, me dari, me hamsin. Su
maman ummi kam dk inda aka zauna sai ance
matar gidan mu danta ba a mishi hakika ba,
itama aisha haka, dk inda taje sai ta tsegunta.
Ita kuwa mejego ko a jikinta, abinci ya wadata
shima ya samu nutsuwa ganin suna da abinci.
Sannan abokanshi masu aikin hannu dk wnda
ya samu aiki yana bin su dan samun na
batarwa. Itama tuni ta nemi koyarwa a
islamiyyar da take xuwa, km sun dauke ta
amma sai tayi arba'in. Shi da kanshi mahmud
din ne ya shawarce ta yin koyarwar. Sunyi
arba'in khalil yai bul-bul gwanin sha'awa lkcin
mahmud ya saba da aikin gini. Sun zaga dangi
har kwantagora suka je suka kwan 2, da zasu
dawo cikin tsarba har da tsumi da sauran
tarkace lkcin ne ta gane ko maganin me mama
ke bata, domin har gjy take da message din
baban khalil. Zamansu gwanin sha'awa ta
soma koyarwa ta hkra da boko, da safe taje
islamiyarta da yamma taje koyarwa.
Nafisa na xaune gaban boka tace boka ina
mamaki ace duk aikin dkkeyi yanci mma wann
ya gagara. Yace ban taba tura tsafi ya dawo b
si wnan karon, ban san dame suka dogara ba.
Tayi shiru tna tunanin cewa duk yaanda akayi
ikilimace ke bata mata aiki da yawan adduo'I
tasanta ko lokacin da suke gida duk dare saita
tofe jikinta da aduo'I sanan itama ta tofa mata.
Wata rana har fada sukeyi da nafisa in tana
shafa mata tace kada ki kara shafan yawunki
kazamar banxa
Nafisa ta sauke ajiyaar zuciya tace ikilima ce ta
kalli bokan tacigaba; matarsa tanada yawan
adua kodai itace ke bata aikin? Boka yace
yanxu naji maana, na tura tsafi da safe ya
dawo, na tura da yamma ya dawo, na turda
dare ma ya dawo, toh bnsan yanda zanyiba.
Saidai ki binciko lokacin da basa yin aduar
Nafisa tace to zan kokarta. Way ta dinga yiwa
haule wai in ikilima tayi 40 tazo mata yawo.
Lokacin da ikilimar taje idan haulen sai take ce
mata nafisa tace kije bari na kirata kuyi
magana. Nan kuwa suka gaisa tayi mata barka
tareda cewa kiyi hkr banzoba banajin dadi ne.
Ikilima tace bakomai Allh ya sawwake tace
amin, zakizo min din insa direba yaxo dauko
ku?
Ikilima tace zanxo amma zan fada masa idan
ya yarda zamuxo nafisa tace idaan bai yarda
bafa? Kindai san halinsa tsaf, saiya ki yarda.
Ikilima tace zai iya kam. To in yaki shikenan kin
raba zumunci dani? Kindaiyi kratu kune dai
malam kinsan makomr mai ynke zumunci
Tace na sani zan lallaba shi. Nafis tace in ma
yaki kice masa jalingo zaki. Ikilima tace insha
Allahu ma zai yarda. Tunda ta dawo take tufka
tana warwarewa, ta rasa ta ina zata soma
tambayar. Dadare ta gama yiwa khalil shirin
bacci ta kwantar dashi ta juye ma babansa
ruwn wanka yaana zaune yana cin abinci yace
ki sirka min shi da dan dumi jikinaa da ajiya ina
anin ma wankan ke zakiyi min.
Tace toh. Tana cudashi suka fito da alwala
sunyi shafa'I da wutiri sanan suka kwanta tana
matsa masa jiki tace yauwa baban khalil! Ya
dan bude ido naam maman khalil! Tace inason
ziyarar ya nafisa. Ya mike zumburda cewa;
wace? Taji shaakkar mimaitawa don tasan yaji.
Yace kinyi shiru? Tace cewa nayi zan ziyarci ya
nafisa, yayi tsaki ya kwaanta tareda cewa sai
kin dawo amm in zaki tafi ki tabbata kin aje min
yarona a gida......
Tayi sororo tana kallon shi, ranta ya baci tace
shi kenan, ynxun zaka yanke mana zumunci
don Allah? Yace na isa? In dai zaki tafi ynxun
ma ga hanyar nan, yaro nane nace bana so aje
min wani guri dashi. Ke yaruwarki ce, shi fa me
suka hada? Ranta ya sake baci, ai ko shima
uwarshi ce domin in aka tsaga jinina za aga na
yaya nafisa, to haka za aga nashi. Dn hk ni sai
naje dashi. Ya tashi zaune yana kallonta, ta
daure fuska irin ynda bai taba gani ba shima
ya daure tashi fuskar, to sai kije dashi din in
gani, ina me tbbtar miki zaki sha mamaki in har
kika je dashi. Ya juya yayi kwanciyar shi tace ai
wannan raba zumunci ne wlhy manzon Allah
S.A.W yace mai yanke zumunta be zai shiga
aljanna ba. Allah ya sani naso zuwa, shi kenan
ace mutum abu ba zai wuce a gurinshi ba? Ya
dai yi bnza da ita.
Haushi ya sake cikata, tace ni dai bb mai raba
ni da yaruwata tnda tare aka ganmu, km in
mutum yace in tafi dole gurin su zani, namiji
bashi da tbbs! Jin zantukan sunyi yawa gashi
masu kona rai sai ya dauki filo ya fita falo. Ya
cika da mamaki, ikilima yarinya me hnkli ita ce
ke gaggaya mishi irin wannan zantukan?
Ranshi ya kai matuka gurin baci, ranar hk suka
kwana suna jin haushin juna, abnda basu taba
yi ba. Da safe dk suka share juna ko gaida shi
batayi ba, shi kuwa ko karyawa be yi ba ya fice
abnda ya sama kuwa gidansu ya wuce ya turo
kaninshi ya kawo mata. Sai da ya tbbtr sunyi
bcci sannan ya shigo dakin, dg sallar asubahi
be dawo ba, ranta ya sake zafi. Shedan ya
dinga zugata wai ta tafi gidan mamansu tace a
kira mata nafisa ta turo direba ya dauketa.
Amma wata zuciar tace mata a'a. Tana
makaranta ya dawo yai wanka dn suna bikin
sulaiman abokinshi, ya aje mata kudi ya fita.
Sun kusan sati idon shi be hadu da nata ba.
Haule tazo ranar ta sameta zata dora taliya,
suna gaisawa tace ke km sai inji shiru?
Yaruwarki dk ta dameni kije kije. Ikilima ta debo
ma haule ruwa tace ki sha. Ta zauna tana ba
khalil nono tare da cewa, mama wlh yaki yarda.
Haule ta zabga mata harara. Kin dai ji haushi,
bn san meyake tsinana miki ba duk kika nace
mishi, dole ne auran? Dubi dakinki, dubi abinda
zaki dafa, taliyar hausa. Dube ki, da haka kike?
Dk kin kara baki kin tsofe, wa zai ce shekarunki
18 ynxun? Tnda ya hana kin hanu shi kenan,
zance mata ta hkra kowa ya zauna
mazauninshi. In bnda shashancinki ku kenan
mata ku hada kanku ya gagara. In ma kun
hada ai kece zaki fi cin moriyarta dn kin san ita
abin hannunta be rufe mata ido ba. Ikilima
ranta a bace tace ki bata hkri mama, zanje
ynxu hk rigima muke kan haka. Tace A to gara
dai ki matsa mishi. Shi fa namiji in ka sake
mishi yaga gadon bccnka shikenan, ka zama ta
bakin ku yan boko kuka ce sori. Ta kada knta
tai gaba. Daren ranan ta zauna sai ya dawo
suyi wadda zasuyi.
Sha biyu ya dawo, hakan ya kara kona mata
rai. Wato sai ynxu ma zai dawo. Ciki-ciki ta
amsa sallamar shi, bayi ya nufa ya watsa ruwa
sannan yai shafa'i da wuturi yazo kan kujera
ya kwanta tace kai fa nake jira muyi magana. A
zaton shi hkri zata bashi sai kawai yaji tace
kan maganar tafiar ne. Cikin mamaki ya dube
ta fuska daure. Irin daurewar da bata taba gani
ba. Gabanta ya fadi sai km tai shiru. Yace ina
jinki. Tace dama hkri zan baka sannan ince
inje? Ya ce Eh kije mana ba tntuni n2e kije ba?
Yaro ne kawai be ze je ba sannan ki daina min
zancan nan bana son ji. Zatayi magana ya
daka mata tsawa har ta firgita yace ki kiyayeni
tnda na lura ke baki san zuru ba. Ya mike ya
fita abin shi, ita km ta nufi uwar daki rai na zafi.
Kai-kawo ya dinga yi gani yake tmkr ba ikilimar
shi bace wadda daya ce kaza zata ce to in yai
fushi ta lallashe shi, ta kwntr masa da hnkl
dama haka halin mata yake? Su zuma ne ga
zaki ga harbi? Ynxun ya ze mata? Ita kuwa
rigingine tai kan gado nata ganin be mata
adalci ba, shi kansu na hade da danginshi ita
ze rabata da nata kenan tnda yana fushi har
ynxu be daina son nafisan ba?
Sunyi kwana uku suna 'yar shariya,gashi
kwana biyun babu aiki ba ya kawo komai,duk
ya damu. Ita kuma yanzu hankalinta ya dawo
ta gane bata kyauta mishi ba,amma ba sa
haduwa bare ta ba shi hakuri. Sammakon fita
yake yi sai sun yi barci yake dawowa,in kudi ya
dan samu zata tashi ta ga ya aje mata,kuma
bai cin abincin ta. Hankalin ta bai sake tashi
ba sai ranar da wani yaro ya shigo yace wai
ana kiran mahmud inji wata.
Ta dafa kirji tare da kwantar da yaronta a kasa
"kai kace wata?" yace eh ta suri hijab "muje in
ganta" sai gashi ya shigo ya aje mata kudin
hannunshi ya canza kaya zai fita tace cikin
kidima "ance wata na nemanka" yace na
ganta,ba tare da ya kalli gurin da take ba ya
fita.
Kishi kumallon mata nan ta soma tunanin
cewa budurwar shi ce? Kasa cin abinci tayi ta
zauna zaman jiranshi,sai da ya tabbatar tayi
barci yanzu sannan ya nufo gidan. Zaune take
kan kujera ta zabga tagumi ya dube ta sai ya
wuce da kudurin in ta dame shi zai tura ta gida
don mahaifinta yayi mata fada.
Wanka yayi ya fiti ya kwanta ta matso "baban
khalik dn Allah idan baza ka damu ba ina son
muyi magan ta fahimta. Yace ina jin ki."ba tare
da ya dube ta ba tace ni ban ki kayi aure ba ko
ka nemi budurwa ba amma ka bari mu dan
warware. Ya dube ta ban gane ba? Tace
"budurwarka da ta zo dazun".
Bai san sanda ya saki murmushi ba don ya
tuna Sa'Ida ce budurwar muktar ta zo neman
shi sun dan samu sabani ne da muktar din ya
share ta shi ne take so yayi musu sulhu. Ya
sake daure face "ai ba yanzun bane auran
dama sai mun dan warware din. Ya yi nufin
zolayarta.
MABUDIN WAHALA 2***8
Ta matso "me yasa kake son yin aure yanzu
alhalin ba kullum bane muke dora tukunya?
Kuma ma ba kayi min alkawarin cewa ba za ja
kara aure ba? Yace "to ai naga kin canza ne
yanzu kin fi son tashin hankalina" tace to in
don ta ni ce kayi hakuri nina fa daina don Allah.
Ya kauda kai don kada yayi daria "to ya ya zan
yi da ita? Ta hau jikinsa "taje can ta nemi
mijinta wannan nawa ne". Yace,shine kike gaya
man magana son ranki?
Tace to ni na zata akan gaskiyata nake.
Yace,haka ki ke gani? Tace,to ni ai ina ganin
kamar ya kamata komai ya wuce tsakaninta da
kai. Yace,to ni raina ne bai kwanta ba da
tafiyar. Tace,to shi kenan,maganar tafiya an
wuce gurin,da dai ka min bayanin haka ne tuni
da ba'a kai ga haka ba. Yace,ni ko in na kalle
ki ne sai na ringa tuno yanda ki ke iya gaya min
magana gashi kina da ilimi. Tace,ai ba wanda
ya wuce kuskure,ka yafe min. Yace to na yafe
miki,duk da raina bai so abubuwan da ki ka
min ba,amma da na tuno halayan kirkinki sai
naji na miki uzuri. Suka yi dariya,ranar dai sun
tabbatar sunyi missing din juna don msgs ba
sauki.
Nafisa ta matsa ma haule da waya,haule
tace,dama kin daina damun kanki,ta ce mijinta
ya hanata. Nafisa ta ciji yatsa ta koma gurin
boka ta shaida masa,yace to tunda haka ba ta
samu ba ki bari zamu yi ta gwada sa'a in an
samu sabani ko mantawa ba suyi adduar ba
zamu dace. Sun manta Allah ne mai kare
bawa,matsawar yana addu'a. Allah ka kare mu
daga sharrin masu sharri. Duk kwanakin a gida
take ganin Alh jamilu ya rage yin tafiye-tafiye,y
au ma tana bacci wayar shi

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment