Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ya dauki takarda da biro,ya zauna ya rubuta takardan murabus din shi sannan ya koma ya zauna a kujeran hutawa, yana jijjiga kan shi.

     Yayi imanin duk inda take, tana cikin kariyar Ubangiji, bai lalata na kowa ba, yayi Imani Allah bazai tab'a barin a lalata mishi na shi ba.

    Sake bude ido yayi sakamakon, jin muryan Hanisah tana kuka,. Kallonta yayi tare da mika mata hannu, a hankali ta karaso ta daura kanta a bisa cinyar shi, tana wani irin kuka.
"Baabi kayi hakuri! Insha Allah Didih zata dawo muna da yakinin sace ta aka yi."

     Shafa kanta yayi, sannan ya fara magana yace.
"Me yasa kika canza abinda ya faru! Bayan kin tabbatar itace ta gudu da kafarta?!"

    "Baabi! Kimar kace na kare! Taya zan yarda a zubda maka ita! Sannan kuma zai iya shafar masarautar? Nasan idan nace musu nasan da kanta ta nime a sace ta, aure zai mata wahala, amma idan na nuna ban san kome ba akan haka, duk ranar da ta dawo.

  Ba zata  rasa mijin aure ba, Baabi, yaranka maza bi, mu hudu kuma mata,. Baabi dole mu koyi boye sirrin gidan mu, dole mu rufawa kan mu asiri."

"Allah yayi miki albarka! Amma idan ta dawo me kika ga ya dace nayi mata? A matsayin ki na uwa mace!"
    D'ago kai tayi cikin damuwa da tashin hankali, tace.
"Baabi! Sabida a wanke ta daga zargi za a iya kaita asibiti ko likitan yazo ya dubata a cikin gidan, a tabbatar da lafiyarta! Shi kenan."

.  "Toh madalla da shawarar ki. Jeki zan huta!"

    Ya sallame ta, sannan ya cigaba da zurfaffa tunanin shi, da kuma Halin da Babbar Yar shi take ciki.

       ---
Daura...

"Kawu! Ka rage tunanin nan haka! Don Allah, Insha Allah nima ina ji a jikina abubuwa suna dab da faruwa!"

Juyawa yayi cikin nutsuwa ya kuma dawowa gabanta ya zauna yana kallon ta.
"Sarah! Yaron da na gani ya sace Aanih! Ƙwayar idanun shi sak Na Janny! Kuma babu abinda ya bari, da yanayin idanunta.

   Cikin idanun shi, sun kasance irin nata zaiba, sai girman su sak nawa, Ina tsoron kar."

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, don Allah ka daina fadar haka, domin wallahi bana jin kome akan haka, Ni dai karka sa a fara zargin Yaron da bai san kome ba da aikata wani abu."

        "Ba haka bane! Abinda nake son."

Mik'ewa tayi ta bar Mishi dakin, haka kawai kullum sai ya nanata abun daya, sai kace akan shi aka fara ganin abu me kama daya, tana fama da ciwon zuciya akan sace Mata Yaronta tsowon shekaru ashirin, amma dare daya ya wurgata da wata damuwa, duk ya diririce ya koma wani irin mutum.

    Dan abu kadan sai ya mai da shi kamar wani yaro karami..
     

    Har yau bincike take, tsawon shekaru tana nan tana bin rayuwar Jakadiya Sahurah, wacce ta samu labarin tana macina taje aka ce mata bata garin, kwanaki aka ce mata tana jibiya, bata fasa tura yan aike ba, kullum abu daya take yi ko Allah zai sanyata ta sami inda take.

    Sannan waye mutum na uku nan, dan kwanaki da Baba waziri ya rasu, ta dauka shine sai daga baya aka kuma turo ma ta da wani sakon, haka ya tabbatar mata da cewa. Tabbas me don ganin bayan su yana tare da su, toh waye ne shi? Wannan tambayar takewa kanta har yau bata ga alamar zata ga wanda yake wasa da rayuwarta.

      Sannan bata da ikon ta tuhumi Ajiya da Kuma Sa'i, tunda basu fadi kome ba.

                 ---
Damagaram..

Zufa nake karyawa, sakamakon zafin da ake, sannan na farka daga barci, kallon shi nayi yana barci cikin nutsuwa kamar baya tare da wata damuwa, sai ma kara fad'adda farar da ban tab'a gani ba sai yau.

            Tari nayi ya sanya shi bude ido da suka yi ja. Tashi yayi ya tawo har inda nake, ya cire min abin karin ruwan dake hannuna, sannan ya koma ban dakin shi ya dibo ruwa a wani abu ya dawo dakin, zama yayi a gabana da yar karamar tsuma, ya durkusa a gaba na.

. Hannun shi ya kai zai tab'a ni na make hannun, tare da b'ata fuska.

   Hannun shi ya kai baya ya zuge min rigar, ta baya.
Kare kirjina nayi, cikin jin haushi nace.
"Ni ka rabu dani bani ciki da iskanci, ka bar ni nace d'an iska kawai! Ban da rashin hankali da yarinta meye zai saka ka same ni a b'agas kana wulakantani, jikina da zaka tab'a."
     
Bai damu ba, sai ma kokarin ganin ya cire min rigar yake, na saka mishi kuka, buge min hannun yayi tare da saka yar tsuman a ruwa ya shiga goge min jikina, Allah ya taimaka bai cire min yar shimin ciki ba, da na shiga uku.

Kallon fuskana yayi na wasu lokuta, kafin ya kai hannun shi bakina yana shafawa, buge hannun nayi cikin jin haushi, zan bude bakin ya kai hannun shi kirjina, buge hannun na kuma, fincikoni yayi tare da manna ni da kirjin shi, ya saka hannun shi ya cire min shimin jikina k'amk'ame shi nayi tare da fasa mishi kuka.

         "Don Allah ka rufa min asiri! Karka min abinda bazan iya fuskantar dangina dashi ba."

          Hannun shi ya kai wuya na tare da d'ago kai na.
"D'an iska kika ce!"
Rufe idanu nayi wasu irin kwalla na zuba min, tare da d'igar jinin daga hancina, tattausar bakin shi ya d'aura akan lebbena, na bude idanuna tare da sake wani irin kuka, sakamakon jin hannun shi a kirjina.

          A hankali ya zare tare da ɗaukar tsumar ya shiga
       goge min ina kare kirjina, karshe na bashi haushi, saka hannu. Shi yayi tare da yaga rigar,. Dauke kan shi yayi kamar  bai ga kome ba.
"Mtseew, dube su kamar lemun tsami! Dalla cire hannun nan!"
Ya daka min tsawa,kuka ne ya kwace min, ina son zanyi magana na kasa tsabar tsoron dan wani b'ata rai yayi sosai.
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

SHA UKU.
"Don Allah Jay! Ka barni na saka kayan," na fada a rauna ne.

     Banza yayi min, kamar ba dashi nake magana ba, gyara min kwanciya yayi sannan.

  Wani b'ata rai yayi, kamar bashi ba, kawai ya shiga kokuwar cire kayan shi.

Wani irin tsoro ne ya kamani, lokacin da ya cire rigar naga haikan ni zai hakewa.

"Jay! Karka min haka! Dan girman Allah karka min abinda kake shirin aikatawa, wallahi tallahi ban."
   Rumfa yayi min da kirjin shi, ina kasar shi, da gaske Jay. Kuka na sake Mishi da mugun karfi.

      ...ga baki daya na birkice,  zan iya cewa ban tab'a rud'ewa irin na yau ba, mara mutunci ashe zolaya ce kawai. Ganin yadda na birkice yasa sake murmushin mugunta.

"Na zata ko dan kin saba da maza."

        Janyo bargo yayi ya rufa min, sannan ya bar d'akin yana me jin haushin abinda yayi min.

     Shi ba dan iska bane, amma lokaci guda halittar shi tana niman birkice daga tozali da surar jikina.

......
Ban san wacce irin kulawa zan gaya muku yake bani ba, amma tun da ya fahimci bani wani damuwa da namiji a keb'ence, sai ya mai da hankali gurin bani kulawa.

       Wanda ta kai, wani lokaci idan jikina ya d'an tashi, yakan kwana a d'akin, wani lokaci kuma idan yaga jikin yayi zafi haurawa gadon yake, ya shiga jikina sosai yadda har zan daina jin zafin, tun ina tsoron kar wani abu ya faru a tsakanin mu, har Allah ya taimaka bai kuma yunkurin min wani abu ba.

Amma bani  da lafiya! Kawai ina ƙoƙarin b'oyewa ne, sabida kar yace bazai mai da ni gida bane, amma duk wanda ya kalle ni, sai ya kuma kallo na, bani da haske sosai, amma ina da duhun fata, wannan zubda jinin ya sani nayi wani irin fayau.

          .... Kwana biyar nayi a d'akin shi a cikin wannan kwanakin, na gama mutuwa akan shi kamar ji nake a duniya bazan iya rayuwa babu shi ba, duk da na fahimci shi mutum ne me tsananin kamun kai, kuma bai da tunanin wani abu a kaina,

              Sau biyu, ina ba shi damar, ko zai far min amma wani ikon Allah, idan yazo yaga nayi wata banzan kwanciya, zai gyara min kwanciya, sannan yayi ficewar shi, idan ba jikina bane bai tab'a kallona a matsayin mace.

Shi mutum ne dai bai cika magana ba, sam baya son hayaniya, sai dai haduwar mu tasa shi magana. Sam baya da hayaniya. A cikin kwanakin da nayi dashi zai yi wuya idan ya shigo yace min ya jiki na amsa mishi toh zai iya shafe awa biyu bai ce min cikanki ba, sabida tsabar miskilanci.

           Nice ma Innaih take cewa, na sashi magana, kasancewar ita ce tayi renon shi,  dan tace har ya shekara sha shida, baya magana,.
      Ina kwancen, wanda ya zame min jiki, sai gashi nan yazo min kayan daga Ashasha sai  bougaje, ya kawo min tare da riga da wandon Pakistan har da mayafin su.

              Tare da wasu kaya, ya ajiye min.
Kallon agogon hannun shi yayi, sannan ya juya zai fita, ya kalle ni.
"Idan kina bukatar zuwa gida, ki shirya nan da minti goma, idan kuma na sake shigowa na samu baki shirya ba, zanyi tafiyata dan jibi zan koma Canada!"

      Kallon shi nayi cikin wani irin yanayi, zuciyata tana wata irin bugawa. Ji nake kamar kirjina zata fashe kallon shi ne tsaya yi kamar naga sabuwar halitta.

Takowa yayi gabana, tare da cewa.
"Baki ji bane?!"

Hawayen da nake rikewa ne suka zubo min nace mishi.
"Ni bazan koma ba!"
Zaro idanu waje yayi, tare da cewa.
"Baki da hankali ne? Mahaukaciya ina ce ke?!"

        "Wallahi bani dashi! Mahaukaciyar kace ni! Don Allah karka mai dani, kaje dani ko ina ma!" Na faɗa cikin kuka.

Mik'ewa y hannun shi cikin aljuhun wandon shi yace.
"Baki da lafiya! Kina b'oyewa ne, shi yasa nake son mai dake gaban iyayenki!  Sannan zama na dake akwai shaidan, dan haka bazan iya aikata zina ba.

       Shi yasa nake ganin ki tafi gaban iyayen ki kawai."

    Rarrafawa nayi dakyar na mike, tare da isa gaban shi.
"Don Allah karka rabu dani! Ko na koma bazan iya zama dasu ba? Jay don Allah kaje dani ko ina ma, a shirye nake na bada rayuwata akan ka don Allah."

               Zaunar dani yayi cikin nutsuwa, yana kallon fuskana, jikin shi yayi mugun sanyi.
"Kinga ni wani abu nazo yi,"

                  Shiru yayi yana kallon yadda nake kuka, sosai. Zuba gwiwar shi yayi a kasa sosai sannan ya kalle yadda nake ta kukan.
                    "Toh naji idan muka je zan roki gafarar Baabi sai na tafi dake!" Ya faɗa min.

        Cak kukan ya tsaya ina kallon shi, a hankali nace.
"Da gaske kake ko kuma kana rarrashina ne, kake?!"

B'ata rai yayi tare da cewa.
"Na tab'a miki karya ne?"

   Daga haka ya bar d'akin, shiryawa nayi tsaf na fito sanye da riga da wando, sai mayafin da na rufe kaina.

             A hankali na shiga cikin gidan gurin Innaih na mata sallama, ta ɗauki da wo. Da madarar rakumi hadi da cukwai ta bani, nayi ta godiya. Jay Mugu ne.

  Farkon zuwa na gidan, sawa yayi tayi ta bani dawo da nonon raƙumi, ba suga. Ina sha ina amai daga baya da na iya sha kuwa ko ya sayo abincin Innaih ta girka bana ci sai da wo.

            Goge kwalla nayi sannan na fita da sauri ganin yana ta danna mana korototo, a hankali na shiga motar ina d'agawa Innaih hannu, a hankali yake jan motar har ya fita daga garin, dan sai yanzun na fahimci a kauye muke.

     Bai kalle ni ba, muka nufi  gidan su da yake cikin Damagaram, bari na yayi a cikin motar ya shiga cikin gidan. Take yan matan dangin su tare da yan uwansa suka mishi caaa.

     Murmushi yayi sannan ya kalli kakar su yace.
"Annah! Zan koma inda na fito!"

        Tab'e baki tayi, sannan tace.
"Da fatan dai ba wani abun ka rakato ba."

Mik'ewa yayi zai fita ya ajiye mata kuɗi me mugun yawa, sam bai san lokacin da zai burgeta ba,da ace tare da Munih suka zo da tuni ta shiga rawan jiki dasu.

       "Ya Jay! Don Allah ka tsaya muyi hoto mana!" Inji wata yar kyakyawar budurwa.

         Tsayawa yayi suka dauki hoto, sannan ya shiga cikin gidan ya gaida matan baffanin shi, kafin ya fito.

  Motar shi ya shiga, gani na ina wasa da awarwaron hannuna, yasa shi tab'e baki, yaja motar da mugun gudu.

                  Sanyin motar wanda yake hade da turare, yasa ni lumshe idanuna, gudu yake sosai, tare da kallona lokaci zuwa lokaci, sai da mukayi tafiyar awa biyu sannan ya tsaya tare da saya min abinci, kugun tsamiya tare da gashashen nama, tunda na sha, sai ga zufa na karyo min.

       Murmushi yayi tare da share abinda yayi niyyar fada, yasan shi ba mutum me yawan magana bane, amma haduwar mu tasan yashi zama me yawan magana tare da dogon magana abinda yakewa da kallon damuwa ko ciwon kai, sai gashi yakan iya tsawaita magana kamar bashi ba.

         "Shaidaniya!"
Kallon shi nayi tare da b'ata fuska,
"Ba dai ni ba?!" Na faɗa a hasale.
"Toh cire min kayana!"
Ya fada fuskarshi babu wasa.

Sunkuyar da kaina nayi, cikin tashin hankali.
"Kayi hakuri!"
Share ni yayi kamar bazai kuma magana ba, ya cigaba da tukin shi... 

       Kallon shi na tsaya ina yi, kamar wata mara hankali..
"Don Allah kalli gabanki"
 
Ajiyar zuciya na sauke sannan nace.
"Jay ince baka manta alqawarin mu ba?!"
                 "Don Allah kayi min magana mana!" Janyo asusun jikin motar shi yayi tare da dauko wata yar kamar kwalba, da abin allura, yaja ruwan cikin shi.

          Sai da ya gama durawa,sannan ya rufe yana tukin gangancin, sai da yaga hankalina yayi nisa, kawai ya cakka min a damtsen hannuna, sannan ya zare ya cigaba da tafiyar shi, a hankali barci yayi gaba dani, sauke min kujeran yayi sannan ya cigaba da tafiyar shi.

    Tafiya muka yi wanda ni kaina ban san awowin da muka yi ba, sai dai naji yana shafa min ruwan sanyi, a fuskana. A hankali na bude idanuna ina kallon shi. Ganin har karfe biyar na yammaci ake nima, na kalle shi tare da cewa.
"Ban yi sallah ba."

        Fita yayi a hankali yace min.
"Muna boda! Kiyi sallah ina jiranki"

      Sauka nayi  na tafi wani gidan wanka nayo tsarki da alola, sannan na dawo na yadda sallah, ina idarwa yana mika min, abinci  a cikin kwalin tafi da gidanka wato (take away)

       Tunda na sami guri na zauna na fara ci, shakuwa na fara ya mika min ruwa nasha, sannan ya koma ma zauna shi. Har muka isa inda ake duba kayan mu, sannan muka wuce.

                     Kallona yayi, cikin ko in kula yace.
"Barka da zagayowar ranar haihuwarki, ga cake can a bayan mota, ki dauka. Amma kiyi hakuri ban cika miki sauran burinki ba."

   A hankali na juya naga wata ƙatuwar kwali.
"Taya aka yi kasan da haka?!"

            "Duk wanda ya shigo rayuwata! Ina bindidigin shi!" Ya fada min,
"Kamar Y'a?!" Tun daga lokacin da kika fara fada dani! Na shiga bin dukkan tsarin ki!"

   Shiru nayi dan Jay ya fara bani tsoro, ban ce mishi kala ba, sai ɗaukar cake din da nayi..
Naga an rubuta Barka da zagayowar Haihuwar ki 34, kwalla ce ta sauka akan cake ɗin.
."taya kasan ina son chocolat cake?! Naga ban tab'a gaya maka ba, sannan."
."na gaji bani son Damuwa!".
    Shiru nayi ina kallon shi,"kalli gabanki" yace min.

              Taya zai fahimci ainihin abinda yake damuna! Taya zan fahimtar dashi yadda nake jin shi. Da Jay zai fahimci halin da nake ciki da ya sassauta min.

        Goge kwalla nayi tare da yanka cake din na sanya mishi a gefen bakin shi.

Kallon yadda nayi da fuska ya sashi bude bakin shi, sai da ya ciza da hannuna, da sauri na cire hannun tare da zabga mishi harara.

     Kallon madubin motar shi yayi yaga ana bin mu motar yan sanda tare da na sojoji.

      Karawa motar shi gudu, yayi dan yana son yau idan ya ajiye ni ya koma nijar, gudu yake sosai kamar zai tashi sama.

   Har ya b'acewa ganin su,. Ajiye min agogona yayi akan gwiwata.
"Kin tuna shi?!"

         Kallon shi nayi sake da baki, a hankali ya kuma fisgar motar kaman zai tashi sama,  karfe tara yayi mana a garin sokoto, kallona yayi sannan yace.
"Ban tab'a sab'a alqawari ba, amma bazan iya cika miki naki ba, kiyi hakuri da abinda nayi yanzun haka ana jiranki a cikin gidan ku, suna bukatar ki."

          Dai-dai ya cusa hancin motar shi cikin gidan mu,kamar yadda ya dauko ni. Cincirindon yan sanda da sojoji ne..
   
"Akan me zaka yaudare ni da."
      A hankali ya sauko daga motar, sannan yazo ya bude min kofar,  ya riko hannuna. A hankali muke takawa, tare da rakiyar jami'an tsaro, juyawa yayi cikin damuwa yace.
"Ku bar bina! Idan ba haka ba, zan iya mata wani abu."

Jin haka yasa su, suka dakata da bin mu, a nutse ya nufi cikin gidan dani, Baabi na zaune da  casbi a hannun shi.

      Ganin yadda yan uwan shi, suka zuba mana ido,  nayi maza na koma bayan Jay cike da tsoron abinda zai faru.
             
        Hannuna rike da rigar shi.
"Toh Fatimah babu wanda ya isa ya dake ki, matukar ina tsaye da kafaffuna!"

"Kai d'an ta'adda! Waye ya tsaya maka?! Ka sace yarinyar mutane kaje kayi abinda yayi maka sannan kazo zakawa mutane rashin mutunci, kai gaka mara kunya tsagera! !"

     "A.s.p! Kaga laifin shi! Da ita ƙaruwar bata bishi ba,  zai samu damar tsageranci ne?!"inji Yayar Baabi,

      Dariyar Da A.s.p yayi shi ya fusata Jay yaja hannun rigar shi sama, sannnan ya juya a fusace ya kaiwa Dan sandar wani mugun naushi, sai da haƙora biyu suka zubo, ya kuma d'ago shi yana nuna mishi yatsa!

         "Ban da kana sanye da rigar hukuma! Sai na karya kashin mukamikin ka, Idan kuma wani yayi subul da baka, ya ambaci yarinya mai daraja irin Fatimah da sunan karuwanci, sai na mishi abinda bazai manta dani ba. Ficce min da gani. An san yan sanda suna kare al'umma ce akan gaskiyar su, ba dan a ci zarafin su ba. Fita nace."

      Juyawa yayi ganin yadda nake shashekar kuka, riko hannuna yayi har gaban Baabi, ya tsaya sannan ya kalli yan uwan Baabi,  zama yayi saman d'aya daga cikin kujerun falon, ya daura daya akan daya.

             Sannan ya ciro wasu takardun a cikin yar jakar da take rataye a gefen shi.

            Shiru yayi, tare da nazarta mutanen da suke falon, ina tsaye har zuwa lokacin.
"Wannan takardun na shaidan lafiyarta ce! Nayi iya bincike na ban gado dalilin da yasa take zubda jini ba. Ranka shi dad'e! Ni ban yi niyyar cutar da Yarka ba, kawai na gwada mata ne idan na saka abu a gaba na, duk duniya banda iyayena bana d'agawa kome kafa.

       Kafin yau ni ban iya magana ba, amma zuwan wancan mahaukaciyar ta mai dani magananne, ban san wani irin goyan naci kayiwa yar ka, ba amma dai duk mijin da ya aureta.

      Zai sha bakar azaba da nacin Bala'i, domin bata iya dogon magana bata ambaci Baabi ba, abin dariya da tace min shekarunta  amma kullum tana nan kamar jinjira, tsabar kaunar da ka gina mata a zuciyarta.

               Yallabai nasan nayi maka laifi da na sace Yarka, sai da babu sauki Gaye irina a samu mace ta kwantsama mishi mari, ai kuwa kasan haka bazai ma sabu ba, shi yasa na dauketa ranar aurenta.  Domin nima na rama tijarar da tayi min.
          Kayi hakuri! Sunana Dr Mujaheed Harisou Agla! Don haka ga Yarka nan zaka iya kaita asibiti a kara bincika maka ita!"
. Yana gama fadar haka ya mike abinshi.
                     "Jay! Don Allah karka tafi"
"Ke manta dani! Zan tafi can nayi rayuwa ta, ki zauna kiyi aurenki amma ina son don Allah idan kin haifi mace! Ki ajiye min ita zan dawo na dauketa kuma ta faɗa soyayya ta."
."Jayyyyy!" Na kira sunan shi.
"Don Allah ka tafi dani! Wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba, don Allah ka taimake ni, ban san lokacin da haka ya faru dani ba!"

        Juyawa yayi gaban jama'a yana kuma kallona, ya tako gabana.
"Ke zaki iya rayuwa mana, Insha Allah mijin ki zai zama mutum mai kamala."
.rufe mishi baki nayi cikin wani irin kuka, jini na zuba ta hancina ..
"Jay Ina sonka!"
Cike da mamaki yake kallona, sabida shi duk abinda nake bai fahimci cewa soyayya bace....
#Mai_Dambu....
10/23/20, 9:53 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

SHA HUDU
"Da gaske! Ina sonka ne? Don Allah karka ka min shiru."

   Dariyar da ban tab'a ganin yayi ba, ita ce yaƙe yi tare da nuna ni da yatsar shi.

"Meye amfanin cin fuska?! Idan baka sonta a bayyane yake tayi hakuri! Amma mu a halin babban gida mun san dajarar kanmu Yace da Mahaifinta ya zab'e ta sama da mutanen shi, zaka iya sadaukarwa haka, don Allah ka tafi Allah zai bata wanda take so." Inji Ummi Rahil,

     Daga haka ta riko hannuna tayi zata ja ni.
"Jay!"

      Na faɗa cikin kuka, bata dube shi ba, ta ja hannuna.

  Cire hannunta nayi, da sauri na sha gaban shi.
"Kace wani abu! Don Allah kayi wani abu! Karka tafi ka barni. Kai kace bazaka tafi ka barni ba. Me yasa zaka karya alqawarin da kayi min!

           Don Allah kayi hakuri kaso ne!"

      "Kinga ni bana jin kome akanki! Asalima Ni bana kaunarki! Wallahi bana sonki! Kinga ne kiyi hakuri ki...."

Kifa mishi mari nayi, kuma sai tsoro ya kamani, naja da baya.
"Kayi hakuri! Bazan kuma ba kawai ina ganin abinda idanun ka suke faɗa ne! Jay karka manta ina sonka! Ka fahimci sakon da zuciyata tazo maka dashi."

       "Yayi kyau! Amma bari na gaya miki! Ni bazan tab'a auren yar ashirin da biyar ba, balle ke da kika kusan haihuwa na,  talatin da hudu fa, ji min cutar kai! Ke bani hanya. Tsabar rashin tsoron Allah ina zan kai ki bazawara."

   . girgiza mishi kai nayi tare da riko hannun shi.
"Wallahi ba yadda kake tsammani bane, Jay"

    "Ke bani hanya na wuce, na kawo ki gidan ku ga iyayenki da danginki, kiyi zaman ki."

          "Babu inda ka! Ka dawo! Idan kuma kana ganin karya ne kafi daga gidan nan Mu gani! Jalaludeen D'an Jannart! Baka isa ka fita daga cikin zanen kaddarar

Please Login or Register in order to submit comment