Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka kawo ni gidan ban tab'a lekowa waje ba, kallon kaina nayi a madubin daya daga cikin motar shi, na kalli fuskana.

            Murmushi nayi naga uban kumatan da na tara, a hankali na gyara zaman mayafina, sannan na nufi kofar da zata kai ni cikin gidan, tsabar na kwana biyu ban fita ba sai nake ganin gidan yayi min nisa, da sauri sauri na isa cikin gidan. Duk inda na gifta sai an zube an gaishe ni har na isa. Da sallama na shiga falon. Naga sun juya a firgice.

    Tare da zuba min ido. Murmushi nayi na karasa a hankali na durkusa tare da gaishe su. Yadda suke amsa min gaisuwar yaci ace na fahimci rashin nutsuwa a muryan su, sai kawai na nime guri na zauna a kunyace.

                Kowa sai kallona yake, karshe Mamah ta jani zuwa shashinta, na zauna sannan ta kuma fita ta barni can naga Raihanah karama, ta shigo fuskarta yayi jajjur, murmushi na mata tare da tambayar ta.
"Lafiyanki naga fuskarki tayi haka."

Cikin tausayi da damuwa ta kalle ni sannan tace min.
"Babu komai mura ke damuna."
"Allah ya sauwaka, kuma kisha magani zaki ji dad'in jikinki."

Daga nan tafita, sai bayin da suka shiga kawo min abin tab'awa har zuwa wani lokaci, naga babu wanda ya kuma shigowa, zuwa wani lokaci.

      Na jima a dakin kafin Karama ta shigo, muka zauna muna yan hira dan itama bata jima da dawowa daga cikin gidan ba, muna zaune na duba yar qaramar jakar hannun da na fito da ita, na shiga duba wayata, kafin na turawa da Jay sakon.

*Da fatan ka isa lafiya?"
Babu amsa, ne kuma tura mishi bai dawo min da amsar ba, kawai sai na shiga kiran shi.

Bai dauka ba, har zuwa wani lokaci bai dauka ba, mik'ewa nayi na fito zuwa babban falon inda naji abin da  ya kusan tarwatsa min kunne na.
"Eh toh! Har yanzun bamu ji labarin halin da yake ciki ba, amma munfi zargin cewa sun wuce dashi katsina tunda dama can zai je, yanzun na bar Fahad da Najim a gurin dayan su zai wuce Katsina daya kuma zai duba mana nan asibitin daura dan munje mun sami motar shi."

           Zubawa Baba Aswad idanu nayi cikin tashin hankali na karaso tare da zuba gwiwata a kasa, na fashe da kuka. Na kasa cewa kome. Kuka nake har da shasheka, domin tabbas abin da na gani, ne yake faruwa.

Kiran layin Abban shi aka yi, ya saka a kunne, kawai ya furta.
"Alhamdulillahi! Toh gamu nan zuwa."

              Kallon Mamah Sarah tayi sannan yace.
"Maryam, ko zaki zauna da Fatimah."
"Don Allah, Abba kuje dani.. Don Allah karku bar ni a gida zan je na gan shi."

            Babu yadda suka iya dole suka tafi da ni, a wani asibitin kudi aka kai shi.
Koda muka isa zuciyata kamar zata fado kasa, har bakin dakin da aka shiga dashi.

      Idanuna sai zubda kwalla yake tare da niman hanyar da zasu fito dashi, can bayan awa daya suka fito dashi kamar yadda na gani, hakan suka fito dashi rike bakina nayi wani irin kuka ya kwace min.

    Mutumin da ya kawo shi yake bada labarin yadda akai hatsari, wai wata motar diban kasa ce, da wata motar itace, suka saka shi a tsakiyar su, suka yi ta make shi,karshe dai suka juye mishi kayan su akan shi, sannan wata mota yazo ya kuma buge shi ya faɗa a rami, Allah ya nufa zai yi nisan kwana. Kan shi kuwa yasha wata uban bandaje.

            Abin tausayi, haka nake kuka duk yadda aka so na dawo gida naki, na kasa hakuri da halin da yake ciki, dan gani nake da zaran na dawo gida wani irin labari zan ji mara daɗi.

     Ina zaune har aka kawo su Munih da Husnah, sun gama tsora ta, da halin da yake ciki. Muniba tace.
"Dama ai an gaya mana ke matar mutuwa ce, duk namijin da ya aure ki, sunan shi gawa, wallahi wani abu ya same shi kema mutuwa zaki yi."

          Ban tab'a yarda da maganar ba sai yau, domin daga auren mu, har ya faɗa cikin wannan hatsarin.

Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, a gigice na zuba mata ido, na mik'e tare da fita daga dakin, na nufi Ofishin likitan da yake da ya duba shi. Ina shiga na fashe mishi da kuka tare da cewa.
"Don Allah a wani hali mara lafiyan nan yake ciki? Don Allah karku bar shi ya mutu, don Allah ka taimake ni kar ya mutu."

    Zare madubin shi yayi cikin nutsuwa, sannan ya kura min ido. Duk yaga yadda na birkice da kuka yace min.
"Ranki shi dad'e, babu abin da ya dame shi, kawai dai muna zargin ya bugu ne a kan shi. Wanda bamu tabbata ba, sai zuwa nan da wani lokaci."

        A rikice na zuba mishi ido, kamar yadda yake kallona, sanan na sake kukan da nake ta hadiyewa nace.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Na zama annoba. A cikin al'umma, idan Jay ya mutu me zancewa mutane, da wani ido zan kalli iyayen shi, wato nice dai damuwa." Mik'ewa nayi na fito daga ofishin sa, na tsaya daga jikin tagar dakin da yake ina kallon yadda yake cikin halin rai kwai-kwai mutu kwai-kwai.

      "Kin shigo rayuwar shi, dan ki kashe shi, meye ribarki?....

          07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: _Kowa yaci ladan kuturu! Dole ya biya da yatsu_

Tafiya nake amma zuciyata cike da wani mugun tsoro, koda na shiga ji nake kamar zai fado kasa, haka na rike kirjina numfashina yana kaiwa da komowa, najima ina kiran sunan Allah kafin na samu sukuni, kasa kuka nayi, na zauna kwayam a dakin ina zare idanuna. Ina ji ina gani aka fara kome babu sanina.

      ... A hankali kome ya sauya, Jay bai damu dani ba, koda kuwa zamu hadu da juna kamar zamu buge juna matsawa yake ya bani hanya, wani lokaci haka zai ta kallona kamar yaga bakuwar fuska.

        .... Can fada kuwa, abin da basu tsammani ba, shine ya fara faruwa. Domin cikin iya taku tare da Najim suka shiga gwara kan mutane, musamman ajiyar da Sa'i,  yayinda suka hade kan su da Sa'i, haka ya bawa Ajiyar haushi, har ta kai sun fara rigima a tsakanin su, rigimar da ta kai har a cikin fadar suna iya yi a gaban kowa.

           Idan suka yi fadawa ke musu magana tsawa su bari, sosai abin ya fara tab'a ahalin  gidajen guda biyu. Yau ma Juma'a sun gama abin kunyar su a gabab Jay, yabi Sa'i har gida bayan sallar esha, bayan ya samu shiga Sa'i yace mishi.
"Jalal kai ne a gidana? ban kawo zaka zo ba, kai Nagode sosai."  Cikin murmushi Jay yace.
"Haba Ranka shi dad'e gani nan, kawai nazo ne mu d'an zanta, na kuma baka hakuri da Abinda Ajiya yake maka ina ga zan dakatar da shi ma baki daya."

      Nan Jay ya shiga tona mishi magana a bakin shi, tare da nuna mishi yadda yake jin haushin rigimar da suke da Ajiya, sannan dole ya dakatar da Ajiya, ai wannan bayi bane. Sosai ya zage yana fada.  Fir Sa'i yaki magana, sai da Jay yace mishi.
"Karka gayawa Ajiya nazo gurinka, dan wallahi zai iya jin haushinka, domin shi yaso na zama yaron shi naki yarda dashi na sabida ina Son zama da manyan masu hikima da hangen nesa."  Nan ya shiga yabon yadda Sa'i yake, take kan shi ya fara kato yana jin shi wani ne.

"Wato idan kana niman munafuki ka sami Ajiya ka samu." Mik'ewa Jay yayi sannan yace mishi.
"Kayi hakuri zan wuce gida! Idan na sami lokaci zan kuma kawo maka ziyara." Daga haka ya fice ko dogon sallama bayi ba.

           Har ya fito daga cikin gidan, yazo gurin Najim ya ciro yar wayar shi, ya mikawa Najim sannan ya  suka bar gidan. Shiru suka yi kafin Najim yace mishi.
"Kar muje gidan Ajiya! Ni na jima ina zargin su, amma dole sai ka shiga jikin su dukkan su biyun, dole ka hade kan ka dasu. Ana zaka kuma sanin abinda yake faruwa."

Sun jima suna tattaunawa, kafin suna iso gida, daga nan kowa ya kama gaban shi, dake dare yayi dan haka na yanke shawarar zama na jira shi ya gaya min meye nayi mishi ne?

Ina zaune har Allah ya kawo min shi, mik'ewa nayi tare da zuba mishi ido, murmushi nayi a raina nace.
"Abinda kake so yafi kome baka wahala." Da sauri yazo zai wuce nasha gaban shi, ina kallon shi kauda kan shi yayi sannan yace min.
"Malama bani hanya don Allah." Ya faɗa a uzurance!
"Jay meye nayi maka?"
"Baki min kome ba, kawai bana son ganinki ne kusa dani!" Ya faɗa min kwalla ne suka zubo min, nace mishi.
"Haka kawai kace min baka son gani na! Jay ko na maka wani laifin ne ban sani ba?" Saka kai yayi zai wuce na rike hannun rigar shi.
"Ka rufa min asiri kar duniya tayi min dariya! Ka gaya min meye laifina da Kuskure na!"

  Gyara tsayuwar shi yayi sannan ya zuba min ido, kafin yace min..
"Baki da matsalar kome! Sai dai kina w...!" Shiru yayi zai wuce..
"Me nake yi Jay?" Na tambaye shi a sanyayye.
"Wari kike min! Kuma wallahi bana son ganin ki dan kamar wata dodaniya nake ganinki, don Allah ki rabu dani!" Maganar shi kamar ruwan zafi ya watsa min, kallon shi nayi, a hankali na sake Mishi hannun rigar shi.

         Kasa gayawa kowa nayi, na shiga gayawa Allah kuka na, ina yin ibada ina azumi, a hankali. Na fara lalacewa, ina addu'o'in sosai.

     Amma karshe sai na fahimci, gabaki daya ne bana cikin duniyar shi, bana cikin tunanin shi bai damu dani ba.

Baya tunani na, sai na goben shi ga cikin Husnah da ya taso Sosai, nan rikicin da Munih take dani ya koma kan Husnah, tunda nice na tsare mata mijinta...

   Ban tab'a yunkurin gayawa wani ba, haka ya sa nake cikin damuwa, domin yadda na koma ko fita nayi cikin gidan sai Mamah Sarah ta tambaye ni ko ciki ne dani.

            ---
A wannan karon bayan sati biyu, Jay ya nufi gidan Ajiya domin kuwa ya shiga jikin tsofin sun a tunanin su yana bin su ne, sabida sun fi shi,basu san cewa wannan din bom ne da kan sa...

Haka ya gama shigewa jikin su, ana haka. Gwamna ya kawo wani abun cigaba, daura dan haka da aka zo kaddamar da abun ne Jay yace ba zai samu zuwa ba ya. Wakiltasu, na, yana sane ya hadu da aikin fidda wanda zai je taron . Aikuwa Sa'i yace shi yafi dacewa da zuwa. Ajiya yace bai iya ji ba. Karshe sai gashi suna shirin komawa yara ƙanana zasu daku da juna. Budar bakin Sa'i yacewa Ajiya.

"Munafuki me fuska biyu, ince kai ne kasaka a buge shi ranar! Kace kar a kashe shi?"
Cikin fusata Ajiya yace.
"Naji amma kai ne ya dauke shi shekara ashirin d'aya da suka wuce?"

"Eh naji ai Fulani Hasiyah ce ta sani tare da cewar wani wanda bamu sani ba, ashe bani kadai bane fitinanne.". Shiru Jay yayi yana kallon su, ba iya shi ba hatta sauran mutanen da suke fadar, sai da suka gama sannan suka fahimci abinda suka aikata.

     Take kunya ta kama su, tare da mik'ewa zasu bar fadar Jay yace musu.

"Ku kama su?" Mik'ewa yayi bai tsaya ba, sai cikin gidan. Inda ya sami Umma Rumanah kakar shi, zama yayi tare da zuba mata ido.
"Wacece Fulani Hasiyah?"

Kallon shi tayi sannan ta zuba mishi abinci ya fara ci, a hankali ya fara ci tana bashi labarin abinda ya faru, da kuma yadda Zuwan Jannart kome ya zama tarihi.

      Murmushi yake yana cin abincin sannan yace mata.
"Ai kuwa za a dawo da ita! In dai har tana can tana iya shirya yadda kome zai tafi mata dai-dai toh Tabbas ina bukatar ta a raye yazo ta koya min muna kisa.".

Duk yadda taso fahimtar dashi yakasa fahimtar ta, shi kawai zai dauko Fulani Hasiyah ne. Daga nan gidan su ya wuce, yaje ya sami Mamah Sarah, sun jima suna hira har ta kawo mishi batuna.
"Jay meke Damun Aanih? Naga ta lalace ne!" Shiru yayi sannan ya mai da kan shi inda yake kallo ya tabe baki yace mata.
"Tana da mugun hali, bata son zama a waje sai zaman daki kamar daddawa, ba dole mutum yayi wari ba."
Nan ya shiga yayi ta mita, wai din nayi mishi laifi." Hakuri ta bashi dan bata zata abun ya kai inta haka ba.

       Bayan ya gama hira ya koma cikin gidan shi. Yana zuwa ya sami tashin hankali, domin kuwa  Husnah ya samu suna Fada da Munih, saura kadan su kaure da dambe.

Gata dama da cikin shi, kallon su yayi yaga da gaske fadan zasu yi sai ya wuce su bai kuma bin takan su ba, har ya kusan kulewa yace musu.
"Wallahi kuka barni na sako na same ku! Sai na lahira yafiku jin dad'i, kuyi kokarin tab'a min cikina ku gani sai na lalata musu rayuwa". Daga haka yayi wucewar shi bai kuma jin ko tarin su ba.

....yana isowa bakin kofa na ya kurwa kofar ido, cikin sanyin jiki, kafin ya saka kai ya wuce abun shi, dan ji yaƙe wani irin wari yana tasowa dole ya kauce dan zai iya kwara amai.

----
Yau da gobe bai bar kome ba, an dakatar da Sa'i da Ajiya, kuma Jay ya tura da sako Masarautan kwantagora a turo mishi da Fulani Hasiyah.


Duk da taso kin zuwa, amma ya kuma tura mata da sakon shi kamar haka.
ان كركا كذ ثكطا امد كككسك نذ طكن تبس ابمب ذمكقب فتم ألكرن
سرك جللدن
_Ina kiranki da kizo da kafarki cikin da'a idan kika sake nazo da kaina tabbas abin ba zai miki kyau ba! Sarki Jalaludeen_
(Wannan karon ma na kuma amma ga na asalin harshen Hausan da muka sani)
Shiru tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya, Tabbas Jinin Sarautar ke huda jikin shi, babu tsoro a cikin kalaman shi, sai tsantsar Izzah! Idan kuma tace ba zata ba, tayi imani da Allah zai zo da kafar shi
Hmm ance mai laya ya kiyayyi me zamani, da badan haka ba ba zata je ba. Kuma toh amma kuma ai korau ya gaya mata.! Da sauri ta mike tare da saka alkyabar ta ta nufi inda ake ajiye mota ta kira a kaita can inda korau yake.

Tafiyar awa daya da wani abu ya kaita garin, tun da ta shiga, yake dariya sannan yace.
"Da na gaya miki zai nime ki, ai ƙaryata ni kika yi! Babu inda zaki iya kaucewa tarkon yaron, domin zai ji dake fiye da yadda baki zata ba, Yaro ne da ya tsaya da kafarshi yaki tallafin kowa balle a sauya mishi akala.

Yaron ba zai tab'a sarewa akan mulkin shi na, dole idan kin isa kiyi muba'yi a, dole idan kin isa ki saukar da kanki, sai kin amince da muradin shi sannan zaki fahimci meye tsoron shi! Meye amfanin shi, meye raunin shi idan ba haka ba, ba zaki tab'a tsira daga dukka uƙubar shi ba.

Kamar yadda Uwar shi take, haka shima yake, kuma yana dab da kara samun karfin Sarauniya ZIRYA! Domin tana faffutikar ganin ta kuma shiga tarihin shi, dan haka kiyi kokarin dakatar da shi, idan halin haka ya samu. Karfin mulkin shi zai kuma bunƙasa ne daga ranar da yayi wata yunkurin da babu Sarkin da yayi sai shi a karnin shi.


Kayi ƙoƙarin kare kanki da kuma gano meye burin shi ta haka ne zaki iya samun damar juya hankalin shi."

Daga nan ya bata abun da zai iya bata, sannan ta bar gidan shi.

.........
Daura.
"Kasan tayi imani da bokaye! Kuma abin da naji a bakin Baba Magaji yace min zai yi wuya bata nemi wanda zai bata Sa'a ba, dan haka meye ka shirya mata?" Inji Najim.

Juya kujeran shi yayi cikin nutsuwa, yana wasa da wata abin wasa, na lissafi sai juyata yake. Yana kuma kallon Najim. Sannan ya cilla mishi ya mike! Ya zaga kujeran. Tare da zama a kusa da Najim!


"Kai lissafin ka Fulani Hasiyah ce! Ni kuma lissafina kujeran da na taso a kai. Misali zan maka sai ka fahimci wani abu wanda tun daga ranar da na shigo cikin masarautan nan na gama gabatar da kome.
Wannan shine kujeran da ake kawo min farmaki a kai! Sa'i shine wannan! Wannan Ajiya. Ga Fulani Hasiyah! Nan Jakadiya Sahurah bata nan! Sai mutum na ƙarshe."

Dariya ya saka, sannan ya cigaba da cewa.
"Akwai mutanen da bakin su yake shiru a masarautan nan! Kuma suna sane da wasu abubuwan! Misali Baba waziri na yanzun wato Baba Hashim! Baba Shamaki! Wato Baba Umar. Basu san kome ba.

Har zuwa kan san madami dan baram, kan magatakardan masarautan, Akwai fitinannen a cikin gidan nan, matsalar yaki bayyana kan shi ne. Amma idan Hasiyah ta shigo ya tabbatar tana cikin masarautan zai b'ata kamar masarar da taji wuta! Zai magantu makara wanda yaji dukar bayyanan shi daga bakin Fulani Hasiyah."


Shiru Najim yayi sannan yace.
"Wa kake zargi?"
"A'a ban isa can ba! Amma ina da yakinin cewa yana sane da ni, Yardan shi da yayi a kaina ya sashi sake min wani shashinsa..

.yana tsaye a kaina ba dare ba rana."
"Amma naga ba wani"
"Ina sane da ba wani jimawa nayi da tashi daga jinya ba ko?"
10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: *_Tabur man kunya... A nad'e shi da hauka._*

"Ba jimawa nayi da dawowa daga jinya ba ko? Toh amma ka sani dole ce Kanwar naki. Ta sani fahimtar haka." Daga haka bai kuma magana ba ya cigaba da juya kujeran shi can ya mike zai tafi Najim yace mishi.

"Ina ganin mu fara bin su Baba Hashim mana!" 
Juyawa Jay yayi sannan yace mishi.
"Na yarda da shawarar ka! Amma taya? Ba lallai bane ya fahimce mu!"

"Fahad! Zai iya mana kome! Zai iya taimaka mana! Shima zai iya tsayawa sabida kakan shi yayi ƙoƙarin inganta gaskiya a masarautan nan!" Inji Najim.

"Baka tunanin ya iya cewa ba zai iya shiga matsalar ba, domin bai da wannan zuciyar! Kasan me yasa su Abba suka nace maka ka zama lauya?"

"Sabida na kasance, me kare masarautan idan bukata haka ta taso!" Ya faɗa yana kallon Jay.

Jan kujeran yayi ya zauna sannan yace mishi.
"Ko daya ba haka bane! Sabida ka zame min garkuwa ne, sabida ka tsaya min a koda yaushe! Domin taya Ni yaƙi da abokan gaba na, dan haka bana gayyatar kowa, kai ɗaya na yarda da kai, kuma bana tunanin zan iya yarda da wani bayan kai. Duk faffutikar da nake sabida masarautan ta kafune da kafarta, kafin ma shiga cikin alamarinta."

          "Haka yayi amma kuma kasan akwai abinda baka tabbatar ba shine matan ka ka zabi Fatimah. Kome ya dalili?" Inji Najim.  

  Lashe bushashen lebban shi yayi sannan ya tattaro duk nutsuwar shi ya zubawa Najim ido kafin yace mishi.
"Zan rabu da ita! Bana sha'awar zama da ita.!

"Akan me? Kuma meye laifinta? Kasan girman kasadar da ta dauka akanka kuwa? Haba Jalaludeen, wannan ba adalci bane!"
"Toh ya zanyi bana jin ta ne a raina, kuma zan cigaba da zama da abinda bana ra'ayin shine? Kaga ai haka ba zai ma taɓa yiwa ba."

   Sosai Najim ya tsorata da abin da Jay yake fada akan Aanih dan tsakanin shi da Allah yake fadar zai rabu da ita.

......... Kwana goma tsakani sai ga Fulani Hasiyah, duk abinda take bukata Jay sai da yasa aka ajiye mata, sannan yasa Fadawa suka tsare shashin da take, sosai ya tara shiri akanta, tana zuwa kuwa ya kaita nan, kallon shi tayi iyaka kokarinta da ta gano wani abu daga gare shi.

Zama yayi ya daura daya akan daya! Yana murmushi sannan yace mata.
"Barka da zuwa,!"

"Yaro man kaza!" Kafin ta rufe bakinta ya amsa da cewa.
"Idan yaji rana zai narke! Ci abinci, dan ina karb'an bakina da soyayya ne!" Yace mata.
"Gashi nan ga wannan soyayyar ba! Naga wutar fansa a idanun d'an kwarkwarah!" Ta gaya mishi,

"Na jima da jin sunan, sannan ina alfahari da sunan, sabida mu din na musamman ne! Ranki shi dad'e kici abinci." Ya gaya mata bayan ya tura mata kwanon gabanta.

"Bana cin abin da ya fito daga hannun mutumin da ban yarda da shi ba!" Ta faɗa kai tsaye, gyad'a mata kai yayi sannan ya janyo kwanon miyar ya zuba a cikin wata faranti, sannan ya zuba tuwon shinkafa wanda aka kwashe da man shanu, a hankali ya saka cokali ya fara cin abincin yana gyada kan shi tare da kallonta.
"Wannan girkin Mamah Sarah ne! Uwata kenan" ya faɗa a hankali.
"Kuma itace sanadin mahaifiyarka!" Sake cokalin yayi cikin mamaki, kura mata ido yayi cikin fusata yace.
"Ki iya da harshen ki, bani da wata uwar da tafi Mamah Sarah."

Ture abincin yayi tare da mik'ewa, jikin shi na rawa. Ya saka kai zai fita.
"Zaki! Irin wannan fusatar! Toh idan kaji da saka hannun mahaifinka yayi sanadin mahaifiyarka me zaka yi? Ka zata kowa sha-sha-sha ne, toh kaje ka nime tarihin masarautar zaka ji abinda suka mata."

Fita yayi bayan ya gama jin abinda tace.
Murmushi yayi, sannan ya murda hannun shi tare da barin gurin a nutse.

---
A hankali Fulani take gayawa Jay magana tare da son hada shi da kusantar shi, har aka ta samu ya fara biye mata.

.... Alamarina da shi kara gaba yake domin kuwa Jay ya manta dani, ko zamu hadu sau dari Wallahi kallon bakuwa yake min, na rasa wanda zan gayawa, sau da dama za a kawo kayan abinci ni bana zuwa sai dai bayina su kwaso min, dan me gidan baya yina.

.... Ana haka kwatsam Munih ta fara laulayi, cikin wata biyu. Amma zo kiga yadda gidan mu ya koma kamar Husnah bata da cikin, tun ina share su har na daina fitowa falon, sabida habaicin da suke min yasani daina shiga harkan kowa.

.ta Gurin miji ban huta ba, ta gurin kishiyoyi ban huta ba, kafin wani lokaci magana ya fara fitowa wai ni juya ce, Mamah Sarah bata san meke faruwa ba, ta sani a gaba muka je har Asibiti aka shiga min gwaje-gwaje, sun tabbatar musu da lafiyata lau, koda muka dawo cewa aka yi dan tana kare ni yasa ta shirya karya dan ka rufa min asiri.

.........bayan wata takwas,
Babu abinda ya canza, ga rigimar da ta Kunno Kai a masarautan, domin Jay ya hana kowa sukuni, kuma ya hana kan shi shima sukuni, take aka fara korafin a tsige shi. Wasu suka yi na'am da batun wasu kuma suka koma bayan shi, kasuwar masarautan gida biyu ya kuma d'aga musu hankali.

Ana cikin wannan yanayin Husnah ta haihu, ga Munih da tsohon ciki. Nice hidima idan na gama su fashe da dariya, yan uwan ta suna faɗin.
"Ba dole ba, ta sami Yaro sabon

Please Login or Register in order to submit comment