Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine sarkin da zai jagoranci al'ummar alkarya guda biyu, soyayya da sadaukarwa itace zata kuma dakatar da wannan matsayi biyun da zai taka.

Da a ce uwar shi ta sami damar kusantar kujeran mulkin kasar dafur, toh da babu hatsabibiya irinta, shi kuma zai kwantatta wani kuskuren da ba kowa ya tab'a aikatawa ba.

Tabbas zai aikata! Kaunar da aka yi shi domin Ziryana da Fairo zai tabbata! Zai bar mata kambun wanda haka shine abu mafi daraja a duniyar aljanun! Kuma kuskuren ga rayuwarta, idan ta saka kambun zata iya karban sadaukarwa! Kuma zata iya bin sahun Ziryana da Fairo! Matukar ya fahimci hannunki a illatar mishi da ahalin shi.

Azzabar zata rub'anya, ina jin kamshin tozarci, ina jin kamshin mutuwar ki! Dan sai kin gwammace, mutuwar sau dari sama da rayuwa sau daya!

Amma ba zaki fahimci haka ba, sabida baki ga zahiri ba, baki ga abinda yake tunkaro ki ba, Magajin Izzah yana tafe nan da wani lokaci, zaki fahimci haka ne lokacin da kika tsinci kanki a gaban shi."

Wani irin zufa ke karyo mata kamar an watsa mata ruwan zafi, tsoro da tashin hankali, sun kamata. Bata san meye mafita ba. Amma dake zuciyar ta, ta gama kangarewa daga aikata laifukan son zuciya ya sata mikewa.

"Da baƙo da tukura, duk umbutawa ne. dan haka bazan sare daga cikin tafiya ta ba, na Barka lafiya " tana fadar hakan ta bar dakin baki daya.

Dukar kasar shi yayi tare da fashewa da dariya.
"Hasiyah! Kinyi gaggawar buɗewa makiyarki dama..."

---
Daura..
"Jaamal! Insha Allah yaron zai dawo! Amma shima kaddarar shi, akwai ban tausayi, dan ba lallai bane. Ya sami soyayyar shi, koda ya samu akwai yuwar ya iya rasa kome na shi.

Jalal! Sarki ne da wasu suke jiran shi, kuma muma nan muke kiran shi, ban san yadda zan maka bayani ka Fahimta ba, amma an sami gamiyyar halittar shi.

Yaro karami amma ya taso tare da kadarorin Mahaifiyarshi, kayi hakuri zai dawo da kanshi amma kafin nan ka nime Najim ya tafi niman shi, ka kuma tabbatar da ya janyo hankalin shi gida.

Mahaifiyarsa tayi iyaka kokarinta na dakatar da wasu abubuwan, daga ciki kuwa har da aikin da ba nata ba, da ta rayu da duk wannan fitinar bai wanzu ba, da tun shekaru ashirin da bakwai kome ya zama tarihi, sau uku tana zuwa nan domin ta dakatar da matsalar da take bibiyar mijinta da kuma masarautar baki daya.

Sai dai abinda na gani ya sani kin gaya mata gaskiya. Domin na fahimci bazata iya kawo karshen rikicin masarautan ba, amma Insha Allah itace zata haifi wanda zai dakatar da abubuwan da yake faruwa.

Yarinyar tayi nisa, gurin son dakatar da kome, amma Allah bai nufa ba, sannan kayi ƙoƙarin shiryawa Najim tafiyar dan haka ne zai samar maka bayanin da kake bukata."

Shiru Kawu yayi tare da goge kwallar idanu shi, sannan yace.
"Baba, shima Jalal din rasa shi zanyi ? Kamar yadda na rasa Mahaifiyarshi"

Girgiza kai yayi, cikin damuwa yace..
"Bana tunanin haka! Amma tabbas shima zai rasa nasaba da yadda ka a rasa rayukan wasu! Idan ta kama abinda yake so ne tilas zai iya rasata.

Amma muna namu, Allah yana nashi, kuma nashi ne gaskiya. Amma tabbas zanen kaddarar ku, kusan guda ce....
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:54 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

   *HAZAKA WRITER'S ASSO*
     (HWA)

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

SHA TAKWAS.

"Karka damu, kome zai zo mana da sauki Insha Allah zamu tsaya da addu'a Allah yana sane da kome."

     Magana masu dad'i da ma'ana Baba Magaji yayi mishi, tare da nuna mishi kar ya takura kan shi akan lallai sai Jay ya dawo.

           ----
Calgary....

Yau ya cika kwana bakwai da dawowa, doguwar magana bai hada shi da kowa ba, asalima zai fita da sassafe zai kuma dawo sunyi barci. Duk suna lura da shi.

       Karfe sha biyu na dare, ya tura kofar falon ya shigo a hankali, tare da rufe kofar. Sannan ya cire takalmin shi, ya fara takawa a hankali kamar mara gaskiya.

      "Bamu san laifin mu ba? ranka shi dad'e! Shi yasa muka tsaya jiranka ko zaka dawo da wuri ka gaya mana me muka yi maka da zafi haka?"

         Cak ya tsaya bai kuma juya ba, kawai tsoro ne ya dabaibaye zuciyar shi, idanun shi suna cika da kwalla.

              "Mujaheed me muka maka da zafi?"  Mamah ta tambaye shi, a sanyayye ya juya tare da zuba mata ido, kafin ya sunkuyar da kan shi.

       "Na kasa fahimtar kome, na gaza gane waye ni? Taya zan iya fuskarta ku na tambaye ku wanene Ni? Ba zan iya tuna kome na rayuwa ta ba, amma Mamah ina jin waɗancan mutanen sune Ahalina!" Ya faɗa a sanyayye kamar zai fashe da kuka.

....cikin tsananin mamaki tare da kallon Juna miji da mata suka yi tare da isa gaban shi, suka rike hannun shi, suna cewa.
"Mujaheed! Gaya mana waye ya faɗa maka ba mune muka haife ka ba? Waye ya gaya maka?"

      Zama yayi cikin tashin hankali, sannan ya fara basu labarin abinda ya faru! Har zuwan shi nigeria.

Shiru suka yi kafin suka mike tare da ce mishi.
"Kaje ka kwanta, zamu duba Alamarin nan da wani lokaci."

  Girgiza kai yayi tare da zama a bakin matakalar benen yace.
"Hmmm! 'Yar bori, ba ta kallon bori. Ku fidda Ni cikin duhun damina mana"

         
     Takawa baban shi yayi sannan yace.
"Ba a hana ma bada rago, fata. Dan haka kaje kamar yadda muka ce! Domin gudu da wai-waiye shi ke kawo zargi"

              Mik'ewa yayi cikin nutsuwa bai kuma magana ba, amma tabbas ya fahimci abinda Baba yake nufi ba lallai bane yaji abinda yake bukata ba.

      .... Koda ya shiga cikin dakin shi, wanka yayi tare da alola, yana fitowa ya gabatar da sallar isha tare da nafilla, sannan ya kuma jima yana addu'a.

     Allah ya kawo mishi dauki cikin duhun da yake ciki. Sannan ya kwanta. Yana ta sake sake, har barci yayi gaba da shi.

         --- 3:38am.
"Jalal! Jalal!! Jalal!!!" Yaji ana kwala mishi kira, buɗe ido yayi a hankali yaga wannan matar ce da baya ganin fuskarta.

      Riko hannun shi tayi suka fita, a hankali tare da barin d'akin.
"Jayyyyy! Jayyyyy!!! Yaji ana kiran shi a wani daki can da kofar shi yake rufe da katon kubba(wato katon kwad'o)

          Kallon matar yayi cikin son yin magana kafin yace wani abu ta buɗe kofar me cike da haske, da sauri ya kare fuskar shi. 

Da gudu ya koma dakin da yake jin ana ihu ya buɗe, ganinta yayi cikin jini, a kwance. Cikin tashin ya shiga ƙoƙarin daukar ta sai ji yayi an rufe kofar d'akin, duk yadda yaso ya fita ya kasa.

                   Girgiza kanta yai tare dakyar ta bude ido tana ganin shi ta sake murmushi.
"A sauran abinda ya rage min, har yanzun baka sona!"

      Cikin wani irin tausayi ya d'agota,  ganin hannunta yayi sun yi baya, alamun ta rasu.
"Fatimah!!!" Ya kwala mata kira, kallon dakin yayi tare kallon Muniba da ta makale shi kamar zata shige jikin shi.

Yakince ta yayi da karfin tsiya, tare da kifa mata mari, sauka tayi da sauri, tana kallon shi.
"Fita!"
Babu shiri ta kwashe kayanta tayi waje.
 
Tashi yayi tare da yin alola, sannan ya gabatar da sallar nafilla, sannan ya zauna har zuwa lokacin sallar asuba.

    ---
Daura...
"Zaka iya, toh gashi ka Fatimah amma bari na kira mahaifinta naji."
Wayar shi ya ciro a cikin aljuhun rigar shi, ya danna Number Aaryaan sun jima suna magana sannan ya kalli Najim ya gaya mishi kome akan Jay.

      Da inda zai sake shi.
..... Sallama Najim yayi mishi sannan ya bar gidan.

                  ---
Yau ki manin sati biyu, rabona da sokoto, kallon yadda kome ke tafiya cikin wani irin yanayi ya sani jin kewar Jay!

   Ruwa ake tsugawa, kamar da bakin kwarya. Na nutse cikin bargo ina kuma tuna kwanakin da muka yi dashi a Damagaram, wani irin son shi da kuma kaunar shi suka kamani.

        Abubuwan da suka shiga tsakanin mu, ya fara dawo min. A hankali, kafin zuwa wani lokaci kasala da bukatar abokin rayuwa ya taso min, lumshe idanuna nayi cikin jin haushin abinda ya faru. Da ya saurari abinda yake raina ince da haka bai faru ba.

           ... Shi kallon wacce maza suka gama hawa da sauka akaina yake bayan ni nasan ba haka bane hatta iyayena kallon bazawarar da tasan mu'amala da namiji suke min.

      Shi yasa ma nake kokarin b'oye yanayin da nakan tsinci kai na, sabida gudun kar su min wata irin fahimta na daban.

   Lumshe idanuna nayi lokacin da wani irin sanyi yake ratsa tafin kafana, tare da wani uban dad'i, a hankali barci ya fara dauka na, tare da saukar min da wata kasala me mugun cin rai,  idanuna nake son budewa amma na kasa, sabida jin wani karsashi kamar ina tare da D'a namiji.

    Kafin wani lokaci, na sauke wasu ta tagwayen ajiyar zuciya, tare da rike zanin gadon da karfi.  Ba zan iya cewa kome ba.

Amma na farka naga na ɓata jikina, wani irin kunya ce ta kama ni lokaci daya na hango zanin gadon a can kasa.

    Rigar jikina kuwa ban san ya akayi na cireta ba, wani mugun tsoro ne ya kamani, yaushe na aikata wannan tashin hankalin?

     Kamar mafarki nayi? Na tambayi kaina, kafin na kuma mik'ewa zuwa ban daki nayi wanka  na fito. Kallon agogon dakin nayi tare da karfe huɗu da wani abu.

       Shiryawa nayi cikin doguwar rigar, na yafa mayafin shi na gyara fuskana sannan na tako a hankali.

           Na nufi falon kasa, inda nake jin muryan ana hira, tun daga matakalar nake kallon mutane.

             Kamar na juya sai kuma na daure na sauko, ina jin ba dad'i a raina. Kallo daya nayi musu ban kuma marmarin kallon su ba, na wuce inda aka jera abinci. Kofi na dauka na zuba kunun tsamiya dan ban karya ba, har huɗu na yamma.

          Sai farfesun kayan cikin da na zuba, na wuce abuna ban kuma kallon inda suke ba, dan son magana.

      "Yarinyah baki ga mutane bane?!" Inji Aunty Aina'uh, idanuna ne suka cika da kwalla nace.
"Ina wuni ku?!" Daga haka ban kuma na wuce sama.

      "Amma kamar yar Fareedah?"
Matar ta faɗa dan su uku ne da wasu yan mata.
"Wasilah ita ce, Aanih Fatimah Khatoon." Aunty Aina'uh tai maganar cike da takaici.

"Ba naji anyi mata aure ba? Kamar an sami matsala ranar auren?"

Numfashi Aina'uh ta sauke sannan tace.
"Sace ta wani yaro karami yayi, shine dalilin da aka fasa auren, amma mahaifinta ya ajiye sarautar sabida ita, amma dake bata da mafadi shine har take kukan tana son wancan yaron da ya sace ta, shi kuma baya sonta"

          "A'ah yana Sonta, kawai bai san meye ake kira da soyayya bane, kawai yaƙi amsawa ne sabida ba zai iya daukar laifi biyu bane." Inji matar.

        "A gaban Jama'a yace baya kaunar ta, ya kuma ce ba zai tab'a auren bazawara ba, toh meye yafi haka muni? Don Allah ki bar wannan maganar" inji Aina'uh,

             Gyara zama matar tayi sannan ta kalli Aina'uh kafin tace.
"Ba dan tayi girma ba, da na nimawa Asood auren ta, sabida ina Son ya nutsu. Macen da tafi shi hankali ta dace dashi ba wacce ya fita wayo ba, don Allah ko zan sami wannan kyautar daga gare ku?"

         Shiru Aina'uh tayi sannan ta kuma kallon Hajiya wasilah, sannan ta sauke numfashi kafin tace.
"Mai ido daya ba ya gode Allah ba, sai ya ga makaho. Me yafi haka dad'i? Wasu na gudun ta ke kuma kin daukawa d'an mijinki. Gaskiya mun gode sosai. Kuma ita ma zata amshi tayin da amfani."

        " Alkama bissa dutse, Allah shi kan bashi ruwa. Karki manta d'an tsakon da uwar shi ta kasa Allah ke ci da shi ba mutum ba, ni a gurina babban alfarma ce kuka min, na bawa Asood ita ko babu kome zata zame mishi garkuwa."

      Sun jima suna tattaunawa akan abinda ban sani, dan haka bayan tafiyar Hajiya Wasilah,Aunty Aina'uh ta shigo min ina cin abinci, wanda kusan na saka tunanin akan abincin.

        Zama tayi bayan tayi sallama, sau daya na kalleta gabana ya fad'i, sannan na cigaba da cin abincin.
"Yarinyah, ina son muyi magana dake, wanda zai taimaka miki."

     "Uhm!" Nace mata ba tare da na kalle ta ba, ta tsani yadda nake mata wannan uhhm da hmm, Ni kuma dabi'ata ce nayi hakan.

"Hajiya Wasilah ce take son ko zaki amince da d'anta da yake karatu a Canada?"

                Furza da namar bakina nayi tare da juyawa na zuba mata ido, sannan na kuma mai da hankali na, kan abinda nake ci.

          Cigaba tayi da magana tana faɗin.
"Amma nayi tunanin kafin nayi miki magana na Fadawa Ya Aaryaan."

      Cikin bakin ciki na zuba mata ido, kafin nace mata.
"Hmm!"
     "Kamar ya hmm? Ki buɗe bakinki kiyi min magana, bawai kice min hmm.

        Kamar yadda taso nayi magana fir naki kula ta, kuma nayi nasarar kular da ita, karshe ta fita a dakin tana banbami na rena ta, bayan ba reni bane iya gaskiyar kenan.

  ........
         Ta kira Baabina ta gaya mishi abinda nayi mata, kai tsaye ya gaya mata gaskiya babu ruwan shi, tunda bana son haka ta barni. Ai kuwa ta cika ta batse.

      ---
Ƙarfe sha biyu na rana ya sauka a garin Calgary,  Kawun Muddam shi yazo ya dauke shi, cikin girmamawa ya gaishe shi tare da gabatar da kan shi.

  Murmushi suka yi lokaci guda sannan Muddam yace mishi.
"Kar ka damu, tunda Aaryaan ya gaya min kana zuwa, na sanya aka shiga niman inda zaku haɗu, wannan takardan shine inda yake yawan zuwa shan coffee, nan kuma gurin da yake zuwa motsa jiki. Da sauran su dai zaka gani."

      "Amma bai da abokai ne?"
Shiru Muddam yayi na wani lokaci, kafin ya ce.
"Akwai wani abokin karatun Aanih Me suna Hikmi, ina ga zan duba maka shi."

             "Haka yayi min!" Daga nan suka wuce gida.

           ---
Zaune yake a gaban ruwa, yayi nisa sosai cikin damuwa, shi kan shi bai san lokacin da ya b'ata a gurin ba.

         D'aura kanta tayi a kafad'arshi.
"Ya Jay! Ina sonka. Kuma ina,"

            Juyawa yayi tare da zuba mata ido, kawai yana jin wani irin zafi akan ta.
"Fatimah!"
        Da sauri ta d'ago kanta idanun ta cike da kwalla.
"Ya Jaheed, sabida bana gabanka shine kake min kallon wacce karuwa....."

                  Kallonta yayi na wasu lokuta, kafin ya mike tsaye tare da riko hannun ta, ta mike tsaye tana kallon shi, jan iska yayi cikin nutsuwa sannan ya riko hannunta suka nufi cikin gidan, ba tare da wani damuwa ba ya nufi dakin shi da ita.

      Cillata yayi saman gadon shi, sannan yabi kanta. Idanun shi rufe kamar yadda yake tunani.

  Kuka tasaka tare da rike hannun shi, tana me cewa.
"Don Allah karka min haka, bana so"
       Jan rigar ta yayi wanda yayi dai-dai da shigowar Mamah,  a tsora ce ta sake kara tare da, isa gadon da karfin ta.
"Mujaheed! Sakamakon da zaka mana kenan? Haba Jaheed meye laifinta? Zaka iya tafiya ka bar mu, amma bamu ne muka haife ka ba. Kaje ka nime...
#Mai_Dambu...
10/23/20, 9:54 AM - Ummi Tandama: SHA TARA.
Cak ya tsaya kamar wanda aka watsa mishi ruwan zafi, haka ya sauka daga kan Munih ya kalli Mama hawaye na zuba daga idanun shi.

              bude baki yayi zai magana. Ta d'aga mishi hannu.
    Shekaru Ashirin da daya Baya.
(Mu koma kwarkwarah 🤣)

.....
Shekarun mu bakwai da aure, Allah bai bamu Haihuwa ba, dake Harisou yana aiki a Saudiyya a matsayin malamin Faransaci a wata jami'a, haka ya samu Bama zuwa ziyara akan lokaci sai bayan shekara daya.

Muke zuwa, haka yayi matukar tasiri a rayuwar auren mu, ga kuma Innar shi da take takura mana akan haihuwa, shi yasa ya dauke ni muka daina zuwa.

A shekarar ne Allah ya dube mu da rahama, mun zo hutu Damagaram..har mun gama zamu koma amma dole sai mun je gida gurin dangina, koda muka zo sai da muka yi kwana uku, a ranar da zamu koma ne Allah ya bamu kai, tun daga nesa nake gano tsuntsaye suna ta shawagi, kawai sai naji ina son na isa inda kake duk da a mota muke.

Har zamu wuce nacewa Harisou.
"Kalli can kamar wani abu ne don Allah kar mu wuce mu duba."

"Bana son damuwa! Yanzun sai ki ga ba kome bane kawai dai shirme ne."

"Don Allah kaji" dakyar ya amince min. Tsayar da motar, da sauri na fita, koda na isa saman sahara kawai me zan gani, bugu har na juya zan bar gurin kawai sai naji ina da shakku akan buhun da na gani.

Dan haka na dauka tare da bude bakin buhun, abin mamaki. Kawai ido biyu muka yi da kai, kana jan numfashi. Kafin ka suma.

Sabida zafin sahara, dan haka cikin tashin hankali na dauke ka, tare da nufar cikin motar da kai, daga nan muka nufi garin Damagaram da kai, inda muka sami likita ya duba ka tare da sanya maka ruwa. Koda ka farka kaki magana duk abinda zamu ce maka shiru kake mana.

Kwanaka biyu aka sallame mu, ba tare da damuwa ba muka kai ka gidan iyayen Harisou, duk da sunyi maraba da kai, amma mahaifiyar shi taki magana akan ka, dan dole muka tafi da kai Saudiyya.

Sai a lokacin ka fara magana, shima sunanka ka fada mana daga kace Saraki, sai kace Magajin Izzah, sai kuma Jay. Da zaran mun matsa maka da tambaya sai ka fita daga cikin gidan.

Tunda muka fahimci haka sai muka daina, damun ka. A hankali ka taso cikin kulawa har kasami shekaru goma sha daya, kafin muka sami haihuwar Munih.

Tunda na haifeta ka rage shiga cikin mu, kawai dai kana taimaka mana da renonta, har zuwa lokacin da ta fara tafiya, Jay sai da ka shekara sha shida kafin muka san cewa kana magana kawai baka cika surutu bane, ka taso baka da kiriniya baka shiga hidimar yara, ko a makarantar ku. Malamai suna fada cewa kaina rayuwa ne kamar Basarake.

Baka son reni, kuma baka rena kowa, a shekaru sha bakwai, ka kammala sakandare. Lokacin an dawo damu nan Canada. Baban Munih yaso kayi soja kace kai likita zaka yi.

Dan haka ya kyale ka, shekara ashirin da hudu cik ka gama matakin farko na digirin ka, daga nan kuma, muka so gaya maka waye kai sai muka fahimci kana farin ciki da yadda kake rayuwarka, dan haka muka bar maganar bamu ne muka haife ka ba.

Abun da muka so shi kake mana, dan haka muka sanya ka koma mataki na biyu na digirin ka, tunda a bangaren da ka karanta, duk wannan abin da muka yi shine zaka saka mana da lalata mana Yar mu? Mun gode amma zaka iya tafiya tunda mun gaya maka waye kai zaka iya tafiya don Allah ka bar mu karka lalata mana rayuwar ta."

Ta karshen maganar cikin Kuka, da ban tausayi.
"Bani da inda yafi nan! Amma dole zan tafi naji me yasa aka min haka, nagode kuma ina baku hakuri da abinda nayi muku."

Daga haka ya fice daga gidan baki d'aya, tafiya yake da kafa. Idanun shi jajjur. A wani ƙwana suka haɗu da Najim!

Inda suke ta tafiya a tare.
"Saraki!"
Juyawa yayi tare da kallon Najim, mai da hankalin shi yayi gaban shi, har zuwa wani shagon coffee. Zama suka yi Jay yace a bashi coffee me zafi, Najim yace a'a me sanyi dai.

"Saraki! A yadda kake a tafashen nan idan ka sha ruwan sanyi, yafi na zafin da zaka sha. Ai sai ka iya tadda gari guda."

Bai ce kala ba, haka ya cigaba da shan shayi me sanyi, har suka gama Ya mike zai tafi.
Najim yace.
"Ranka shi dad'e! Idan aka cigaba da haka wallahi muna cikin wani yanayi, ka taimaka min na samu gurin fakewa."

Iska yaja sannan ya zuba mata ido, yace.
"Ina cikin damuwa!"
"Na sani, amma al'ummar daura da Mahaifinka tare da kakanni ka, suna zuba ido tare da saka tsammanin Magajin Izzah!

Ban san me yasa kowa yake dauki da son ganin ka ba, amma Shehun Borno da wasu daga cikin dangi suna maraba dakai, Sunana Brrst Najim Aswad Magaji, ni ne lauyan masarauta.

Da fatan zaka Duba alamarina. Ga takardan jirginka bazan iya zama na wasu lokuta ba, idan ka shirya jibi zamu sauka a Lagos."

Cikin hasala ya kalli Najim,
"Umarni kake bani?"
"A'ah Saraki! Abinda ya dace nake, Saraki tun ranar da ka b'ata nake tare da Abba Jaamal, dan bana son ya duba gurbin ka, ya ga baka nan, idan kayi ra'ayin tafiya shi kenan, amma zukatar mutane suna dayawa akan ka. Sa ran su yayi matukar tasiri akan zukatar su.

Ya zaka ji labarin Jarumar Uwar da ta tabbatar da kaine zaka kawo karshen rikicin masarautan da Insha Allah, faffutika tayi tare da sadaukarwa. Ko kasan ciwon da miji yake ji a lokacin da ya rasa matar da yake matukar kauna! Sannan abin da tabar mishi aka wayi gari ya b'ace, ka san nauyin da zuciyar Wannan uban yake dauke da shi.


Ka duba yadda duniya take, ka dubi yadda kowa yake tattalin abin da yake na shine.

Zaka iya rasa yau a rayuwar ka,

Please Login or Register in order to submit comment