Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jini ga aiki kamar me, dole ta hakura da wulakancin sa dan haka Husnah mike kafa kiyi ta haihu, ita kuma tana muku bauta miji na wulakantata"

Murmushi nayi daga ranar ban kuma saukowa nayi musu aiki ba, Yau na sami saukowa ne sabida zuwan su Rumah da Karama, tunda gobe suna sai naga Zabba'u tana ta aiki ana mata tsawa, ba ita ba hatta su Larai.

"Zabba'u!" Ajiye aikin tayi. Ban tab'a jin zafin lusarancina ba sai yau, dan haka nace mata.
"Ajiye aikin!"
"Ke Aanih ina ruwanki da aikin da take mana ba bayin...."

"Inji wani d'an iskan? Bayi na ne, daga masarautan mu aka kawo min su. Ni jinin Sarauta ke bin jikina, ba daurin dausono kunun bayan ludayi ba, duk wata yar iska ina dai-dai da ita kuma kar na dawo daga rakiyar bakina ba same ku kuna aikin nan in ba haka ba zan sa akawo min Barde ya hukunta min kowacce ku."

Daga haka nayi wuccewa ta na raka su Qarama, tun da na juya da sauri suka bar aikin kowacce tabi Zabba'u zuwa Shashina. Nan suka shiga zagina wai na kwashe bayina dama basu da bayi ne, karshe dai maganar aka yi ta ririta alamarin har washi gari suna. Mamah Nanah ta shigo da safe tayi min cin mutuncin na fitan hankalin, har da min gorin haka zan zauna ban haihu ba.

"Ai Nagodewa Allah, dan ban samu ba amma ai bayi barci ba, kuma ban makara ba. Yana sane dani, kuma ina ganin girmanki dan haka ki fita kafin na kasa sarrafa fushina." Na gaya mata sannan na wuce d'akina, can sai ga su tare da Jay da Husnah, Mamah Nanah tana kuka take gaya mishi naci mutuncinta.

Ina cikin daki ina cire kayan da zan saka kawai naji ya fincikoni zai mare ni, na rike hannun shi.
"Tsakani na da kai shekaru shida zuwa bakwai! Ashe kuwa baka isa ka d'aga hannu ka dake nie ba, wallahi baka isa ba. Na kuma gaya maka baka isa ba, kana tab'a ni zan rama." Na sake hannu shi na cigaba da abin da nake. Nan ya shiga gaya min magana. Har da ce min dan ya rufa min asiri yana zaune dani duk da ina matsawa rayuwar shi da wari bai tab'a jin ya rabu dani ba. Kai abubuwa marasa dad'i haka ya gaya min. Tun ina iya jurewa har na kasa na shiga mayar mishi, abin da ya haifar mana da zazzafar sa'in'sa, kamar zai dake ni kuma kuma na kafe bai isa ba. Kawai muna cikin haka Mamah Raihanah da Mamah Sarah suka iso, ban san waye ya gaya musu ba.

"Wawuya sakarya wacce ta rasa mijin aure ta makale min." Juyawa nayi ina kallon shi, murmushi nayi domin su Mamah sun shigo, kawai sai ji nayi an kifa mishi marin da ya sashi tsorata, ba kowa bane sai Abban shi.

Domin yana tare dasu Mamah aka gaya musu muna fada, ban ce kome ba, kawai na shiga hada kayana, kallon Abban shi yayi idanun shi jajjur, sannan yace.
"Ni dama na jima da saketa, domin wari take min!"

Sake kwalbar turaren hannuna nayi ya fadi a kasa sai da ya tarwatse, wani irin hawaye ne ya zubo min, na shiga ta cikin kwalbar na wuce na ka rasa kwashe kayana na cikin ma'ajiyar kayana, ina kwashewa ina zubawa a cikin kwatinae.

Waya tace ta kawo wuta, na dauka tare da sakawa a kunne na.
"Na'am Baabina!"
Shiru nayi hawaye na zuba min cikin karfin hali nace mishi.
"Laa babu komai, wallahi kawai muna magana ne akan sha'anin sunan da za ayi ya fara fada, amma wallahi babu kome dan har ya fita ma!"

Sake jadadda min yayi idan akwai matsala na gaya mishi.
"Wallahi na rantse maka babu kome, yanzun ya fita da na bashi wayar." Addu'a yayi min tare da saka min albarka, suna tsaye na kwashe kayana, na zuba a cikin jakkuna na, sannan na dauki babban hijab dina na saka, na shiga ban daki na wanke fuskana na fito, kallona suka yi na sunkuyar da kaina kasa.
"Fatimah! Zaki wuce sokoto yau Insha Allah. Sannan kiyi hakuri Nagode da rufa min asirin da kika yi dan bashi kika rufawa ba wani ne."

Tunda Abban shi ya mare shi yafita, har zan fice Mamah Sarah tace.
"Dawo nan! Mamah ki tafi da ita, Amma wallahi ku duba Alamarin Jay ba haka kawai bane yayi wannan aikin, bamu san me aka gaya mishi ba, kuma kunji yace tana wari akwai matsala fa!"

Juyawa Mamah Raihanah tayi ta sauko, tare da kiran matan shi ta zauna tare da daura daya akan daya tace musu.

"Zan tafi kuma Fatimah zata bar muku gidan ku! Na baku sati Uku! Wallahi tallahi billahil azim, na koma dawowa gidan nan, Jay bai zo Abuja niman Fatimah ba,
Na rantse da Sarkin sarauta. Wallahi sai kun bar gidan nan, kuma sai na baku mamaki," daga haka tayi kiran mu,

Har zata fita tace.
"Ku ajiye magana ta, kar na riga shi zuwa gidan nan, domin kuwa zuwana babu Alkhairi a cikin ta " daga haka ta haura zama muka sauko, tana rike da hannuna, a ranar muka bar garin, su a tunanin su Sokoto na wuce nan kuwa wucewa tayi dani Abuja.

Bayina kuwa cikin gidan suka koma.
Nayi kuka tun kafin na isa, har ina jan zuwa, ai kuwa muna shiga gidan ta fara min balbalin Bala'i.
"Sha-sha-sha, kin zauna hanjin cikin ki, suna saki kuka kekan baki yi kama da jinin sarauta ba, share hawayenki zai zo nan kuma ina nan ina jiran mara kunya."

Tayi min fadar yadda na bari ya rena ni, sannan kuma ta kuma kara min da nasiha, tun daga ranar take yawan jana hira.

--- a can daura kuwa, daga Husnah har Munih kowacce zargin yar uwarta take dan gani suke kowacce tana da wata mummunan manufa, dan haka suka shiga nuna junar su...

Bayan anyi suna, aka watse saura Munih ba, Jay kan Abban shi fushi ya dauka dashi, abin da ya shafi rayuwar shi na yau da kullum, har kowa ya fara fahimtar haka, kuma ya kira Rahil ya gaya mata, itace ta kira babanta ta gaya mishi nan suka dukufa da addu'a da sadaka, ba dare ba rana, kullum yi ake..cikin niman Yardan Ubangiji. Nan ma Daura ba abar su ba, haka ma Sokoto Ummin itama ta maida hankalinta sosai gurin sauka da sadaka.

... Abin da ya matukar d'aga musu hankali, shine yadda wasu abubuwan suke bayyana daga cikin masarautan....
10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: *_Ana zaton wuta a makera... Sai a kasame shi a masaka_*

Abin da ya faru ba kome bai ne shine fitowar Hashim baban Fahad yana kalubalantar Jay da rashin adalci, takanas yaje ya sami Jaamal da Aswad da zance bayan sun gaisa. Nan suka shiga hirar duniya. Daga nan ya kawo batun Jay.
"Jaamal da zaka bashi shawara akan ya daina zurfaffa bincike akan iyayen mu, da kome yazo da.."
Ruwan dake gaban Aswad ya sauka ya watsawa Hashim a fuska, tare da mik'ewa ya d'ago kwalar rigar Hashim zai mishi magana Jaamal yace.
"Kyale shi! Manta dashi, kaje ka gaya musu nace bazan iya dakatar dashi ba, duk wanda ya isa namiji ne ya dakatar da shi."

Kallon su Hashim yayi sannan ya juya zai fita. Jaamal yace mishi.
"Albasa bata yi halin ruwa ba, amma mun maka Uzuri." Haka ya fita ran shi a b'ace, yana komaws gidan shi ya sami Fahad yana waya da Qarama, bayan ya gama ya sami Hashim a falo yana gayawa mahaifiyar Fahad abin da Jaamal da Aswad suka mishi,

Shiru tayi kafin tace.
"Amma sun fika gaskiya, taya zaka ce a dakatar da yaron daga aikin da yaƙe? Bayan kai da kanka kake cewa, Yaron yana abin da ya dace, don Allah karka bari haka ya shafi zumunta dake tsakanin mu, domin ko babu kome, mun zama daya ga kuma Fahad da Jannart, don Allah domin yaran mu kar mu girmama abin ya zama babba."

Jikin Fahad yayi mugun sanyi, dan haka ya fita daga gidan baki daya ya koma kofar gidan su ya zauna yana nazarin abin da ya faru da Mahaifinshi. Kuma yayi imani haka kawai mahaifin shi bazai tab'a juya halin shi ba. Dan haka Ya turawa Jay sako.. dake kan shi a sunkuye yake yana d'agowa yaga wasu kartin maza akan shi, kafin yayi wani yunkuri har sun rufe mishi bakin shi. Tare da wurga shi cikin mota, haka suka tafi dashi. Babu wanda ya sani. Cikin abin da bai fi minti arba'in ba sun bar unguwar baki daya.

---
Jay yana zaune yaga sakon Fahad, koda yayi kokarin kiran Fahad din wayar taki shiga sabida rashin yanayi me kyau, dole ya hakura, sai bayan awa biyu ya samu wani sako daga Fahad din da ya turo mishi.

*_Wasu mutane da ban san su ba sun dauke ni. Amma ina da yakinin zaka iya kub'utar dani, idan kuma haka bai samu ba! Jay ina maka fatan Alkhairi sannan ka gayawa Firdausih Qarama ina son ta_*

Turawa Najim sakon yayi, sannan aka shiga bibiyar sakon, abin mamaki a cikin masarautan yaƙe domin har yanzun lokacin Wayar bata daina aiki ba. Dan haka Najim ya turowa Jay sakon.

Allah ya taimaka bai fita fada ba,dan haka ya badda sawu tafi cikin masarautan yana bibiyar bayyanin da ake mishi..

......
Bayan awa daya Allah ya taimaka ya sami Fahad a can a yashe, sannan aka kira shi da wayar Fahad din yana dauka aka ce mishi.
"Ta yaro kyau take bata karko, gashi mun shirya maka gadar zare! Kuma ka fada ka wanke kanka idan ka isa."

"Tsoho me ran karfe na same ka! Ka jira zuwa na katsina."
Daga haka ya kashe wayar, yana mik'ewa Najim suna isowa. Aka ɗauki Fahad zuwa asibitin masarautan.


. A nan aka kwantar dashi, dake an kunsan gama wasu shashi na asibitin, dan ma ana wasan kwaikwayo da Jay dan yace babu abinda zai hana shi aikin shi na likitanci, shi yasa yake gayyatar, su Hikmi Abeel su zo suyi aiki a cikin asibitin shi.

Lokacin da ya dawo, zai haura sama yaga wuccewa mutum, bai kawo kome ba, ya nufi dakin Munih me fama da dan karamin ciki, tana zaune sai waya take tana gayawa Mamanta irin kayan da za a saya mata, zama yayi yana kallonta, kashe kiran yayi ya zuba mata ido cikin takaici, domin wallahi bai tab'a jin sha'awar Munih a matsayin matar shi ba.

Amma kaddara ta riga fata, tunda shi har da cikin shi a jikinta, *Khatoon* sunan da zuciyar shi ta ambata kenan, ya mike da sauri, ya nufi sama, yau sati Daya kenan, baya ganin wuccewarta. Bude kofar ta yayi ya shiga yaga yadda kome na ciki yayi kura, sannan kamar ance ya kalli dakin yaga alamar an shigo an fita.
Share batun yayi ya koma dakin shi ya zauna, yana nazarin wasu abubuwa, kamar wanda aka tuna mishi ya mike da sauri ya koma d'akinta Littattafan shi ya gani a kasar matashin ta, Janyowa yayi yaga wata farar takarda..ajiyar zuciya yayi sannan ya shiga karantawa.

---
_A yanzun na san nayi nisa da kai! Amma zan tuna maka wani abu da baka sani ba, Jay Ina sonka! Amma zan tafi na Barka! Masarautan ku cike yake da abubuwan damuwa, koda yake bashi bane damuwar rubuta maka wannan sakon tun ranar da ka kawo min Littafan nan nake ta yawan nazarin yadda zan buɗe nayi nayi amma na kasa, abin mamaki juya na zauna na gwada sa'ata kayi hakuri zan kira sunan Ammih! Jannart+ Jamal! Ka gajerce sunayen mu gani, idan aka Cire Janjamal_

Jikin shi na rawa ya gwada yaki, shiru yayi, tare da sake duba wasikar! Dariya tayi mishi da
_Hahaha! Nima haka na gwada, akwai wani sunan da su Mamah suke kiran Ammih dashi, wato Janny, muma haka muke kiran Autan Ummi, idan aka gajarce Jan! Aka kawo harafin i aka saka zai bada Jani! Kaga kenan sunan Ammih yafito saura sunan Abba wanda su kuma zasu kasance harafin uku ka na karshen sunan shi Jay Ina matuƙar sanka da wannan nayi lissafin bude Littafin labarin Amminka, amma ban karanta ba. Nagode daga Sakakkiyar matar ka Wacce kayiwa gorin aure._

Wani irin kunya ce ta kama shi, a hankali ya tuna abin da wata tsohuwa ta tab'a gaya mishi a lokacin da zai bar Nijar....
*karike kalmar Janimal zata amfane ka wata rana*

Bude Littafin yayi na farko, ya bude shafin hoton Abban shi lokacin yana matashin sa, hoton baki da fari, a kasar hoton ta rubuta.
*Kawu kenan! Mutumin farko da naso shi a rayuwata ya kuma ce baya sona!*

Bude shafi na biyu yayi hotonta, ya gani, sanye da kayan makarantar ta Rubutu..
*Jannart Jamal Jalaludeen J³ wasu suna kirana da Janny amma nafi son Firdausih dan Kalmar daga bakin Kawuna, Kawun JANNART*

Shafi na gaba ya bude sai ga hoton Sarah, *Aminiyata ce ita Kawata ce ita Dole abin da na haifa yayi biyayya da da'a a gareta. Dan yar uwata ce*

Shafi na hudu hoton Aaryaan ne, ta rubuta a kasar tace. *Yaso ni! Ya kuma kaunace ni, ina umartan abinda na haifa ya girmama al'amarin Aryaan, dan mutum ne da bazan manta dashi ba..

Ita al'amarin kaddarar a cunkushe take da soyayya sadaukarwa, farin ciki bakin ciki, kuka dariya, mugunta hassada kyashi. Rikid'ewa zuwa wata siffa ta cutuwa. Laifina da Kawu babba ne, da yau na fito na gayawa Sara ina son Kawu da bata shiga rayuwar mu ba.

Amma na boye mata bayan so shi bai iya boye kan shi, babu ruwan shi da babba ko yaro, so dangin mutuwa ce, da zaran ta zo maka babu makawa sai. Ta same ka. Daga nan zaka ji yadda kome ya kasance mana, da kuma yadda zaka kawo karshen rikicin masarautan...

A hankali yake bin shafi zuwa shafi. Har zuwa shafin karshe ajiye Littafin yayi, dan tun daga farawa har ya gama, idanun shi basu daina zubda kwalla ba, wani irin yanayi ne haka? Me yasa zuciyarsu take rufewa daga matar da suka dace dasu? Dake labarin bai kare ba, ya bude daya Littafin ya fara karantawa, a wannan ranar Jay yayi kukan da na kasa dainawa ji yaƙe mutuwar Mahaifiyarshi kamar yanzun aka mishi daga karshe inda zata tsaya tace.
_Ban sani ba ko mace ko namiji zan haifa, koma waye don Allah karki / karka wulakanta duk wanda zai ce yana sonki ko yana sonka, Ni nasan ciwon da mutum yake ji idan aka ce ba a son shi, duk wanda zai soka ya gama maka kome a duniya._ tayi nasiha sosai har da misali da rayuwarta, tayi fatan da tana raye taga me ta bari, tayiwa abin da ta bari addu'o'in, sannan ta roke shi da ya nemi ilimi Addinin domin da ita zai yake abin dake faruwa a cikin masarautan, daga haka ta rubuta zan koma mahaifata Maiduguri.

Kifa kan shi yayi a jikin Littafin ya fashe da wani irin kuka, sabida tausayin Mahaifiyarshi, da Aanih, anan ya fahimci zubda jinin da Aanih take yi da, sabida shigar ta rayuwar shine tun farko.

.mik'ewa yayi lokacin da ya fahimci, bata ga gidan. Da sauri ta sauka kasa.

"Kee ina Aanih Fatimah Khatoon take?" Cikin gangancin tace mishi.
"Taje koyar sallama,!"
"Ni zaki gayawa maganar banza!" Ya daka mata tsawa,
"Jay nifa bana son fitina, kaje ka nimo Matarka inda take karka dame ni don Allah."

Da sauri ya fita, zuwa cikin gidan su. Kamar wanda aka wurgo shi ya zuba musu ido, kafin ya wurga musu tambaya.
"Ina Aanih Fatimah Khatoon?" Shiru suka yi suna kallon shi, kafin ya kuma tambayar su.. cikin rashin damuwa Abban shi yace mishi.
"Ba ka saketa ba? Ai tayi komawar ta sokoto!"

A kidime ya zuba musu ido, yana kallon su, bakin shi na rawa yace.
"Yaushe? Ni da hankali na zan sake abin da nake s... Abba Wallahi ban saketa ba!"

"Amma kafara shaye shaye ko?" Inji Abban shi,

"Wallahi ban tab'a sha!" Ya fada musu a raunane, share shi suka yi karamin hauka ne bai yi ba a masarautan, sannan ya nufi gurin Baba Sarki, shi kuma ya mishi fata fata, tare da koran kare.

Haka ya isa cikin gidan gurin kakar shi Umma itace tayi ta rarrashin sa.
.......
Washi gari ko asibiti bai leka ba, ya jajjibi Najim, sai Sokoto. Kasa hakuri yayi ya gayawa Najim abun da aka mishi, aikuwa Najim yace.
"Yau kenan! Ba kai kace zaka sake ta ka huta ba ka tsane ta, tana maka wari ba!"

Sake baki yayi, cikin bakin ciki yace.
"Mara mutunci ashe dama kana sane da abin da aka shirya min algungunmin lauya kawai, kai baka dace da mataimakin shugaban lauyoyi na kasa ba, kafin dacewa da shugaba algunguman Daura baki daya.. mai Najim zai yi ban da dariya. Sabida Baban shi ya tab'a bashi labarin yadda Jamal yake kiran shi da Shugaban munafukai daura. Yau kuma Jay ya kira shi da shugaban algungunman daura. Haka suka isa sokoto Najim yana kara kular da Jay, dan yake bashi labarin wanda zai auri Aanih karshe yaji haushi yace mishi.

"Kai dan ubanka a wani birnin jahilan ake aurar da mace bata yi idda ba? Dan haka babu wanda zai aure..."
"Bayan da kanka ka gaya min babu abinda ya haɗa ku! Idan ka samu damar samun ta, baka cire kazamin kishin da ke cinka ba, har abada ba zaka iya amfanan kanka ba balle kuma wanin ka."

Jikin shi ne yayi sanyi, ya kalli Najim sannan yace.
"Hala na gaya maka wasu abubuwan ma ko?"

"A'ah aminin Arziki! Iya k'iyayyar Aanih ce baka iya boye min ba, shima ba k'iyayya bace lalura ce, amma kayi hakuri ɗan ba zasu baka ita ka cigaba da mata gori ba" juyawa yayi ya zubawa Najim ido sannan ya sauke ajiyar zuciya yace mishi.
"Na gaya mata magana marasa dad'i ko?"

Domin ya kuma kambama al'amarin yace mishi.
"Ina dad'i ai ta kare maka wallahi.." gaban Jay ne ya fadi cikin tashin hankali yace.
"Kuma Wallahi ina sonta"

"Son banza dai da kaga zaka rasa ba! Ai duk me sonka bazaka wulankata shi ba, balle kuma fatima shi yasa baba sarki yace yayi mata miji!" Inji najim.

"Wallahi zanci Ubanka dan 'iska, a gidan wata uwar za a mata miji wallahi zan kafta maka rashin mutunci, matar yawa shugaban algungunman daura kawai! Idan na gama da su Fulani dan ubanka kai ma sai na maka rashin mutunci, sauke ni na tafi da kafana, mara mutunci na fasa bink"
10/23/20, 10:04 AM - Ummi Tandama: *_Kura da shan bugu! Gardi da amsar kuɗi_*

"Toh Yallabai! Zan sauke ka amma kasan dole sai ka biya ni kudin tuka ka da nayi, dan wallahi bani aikin banza!" Inji Najim wanda yake cike da jin daɗin ya kular da Jay.

"Sauke Ni nace!" Yadda yayi maganar sai ya baka dariya, haka suka yi ta faɗa har suka isa cikin Masarautar Sakkwato, kallon Jay yayi sannan ya kunshe dariyar shi yace mishi.
"Me zaka gayawa Ummin da Baabina?" Shafa kan shi yayi cikin nutsuwa sannan ya juya yana kallon Najim yace.
"Wallahi Malam Lauya ban sani ba! Ga baki daya kome ya tsaya min cak, ji nake kamar nayi ta fasa ihu ko zaku ji yadda nake ji. Ina sonta! Wallahi bazan iya rayuwa babu ita ba, don Allah ka taimaka min kar na rasata." D'aga mishi gira yayi sannan yace mishi.
"Tunda ka iya tafiya babu masu tsaron lafiyar ka, sannan ka tawo niman abin da zuciyarka keso ai ka shiryawa yaki akan ta."

Shiru yayi bai bar Najim Amsa ba, sabida zasu shiga cikin gidan, bayan sun shiga cikin gidan, aka gaisa sai raba idanu yake ko zai ganta, amma babu ita babu labarin ta, nan yayi ta kame kame, yana wasa da Jannart din Ummin shi, dan ta kure shi tace mishi.
"Ina Khatoon? Da fatan tana lafiya"
Dakyar ya iya amsawa da cewa,
"Tana lafiya! Tace a gaishe ku!" Yana fadar haka ya mike tare da cewa zasu wuce dama sun zo wani abu ne suka ratso nan, suka shiga shashin Baabi suka gaida shi sannan suka fita, a waje ya hadu da Muhammad kanin Aanih nan Jay ya ja shi da hira dan yana sane da Muhammad yacewa Noorie yana son irin ipad ɗinta, har take gayawa Jay, yace idan ya samu lokaci zai saya mishi irin nata, aikuwa Mutumin Najim na kallon shi ya dauki Muhammad suka nufi cikin gari, acan yayi ta latsa Muhammad bayan ya saya mishi ipad din ya gaya mishi inda Addah take, nan kuwa yaron ya sake baki ya bashi labarin abinda yake ji abakin su Ummi, amma yacewa Jay.
"Hamma don Allah karka bari a san na gaya maka domin Ammihnmu hannunta zafi idan tana zaneka wallahi."

"Babu ma wanda zai ji sirrin mu." Haka ya dawo da yaron sannan Najim ya shiga motar Jay na tuka su, sai wani gudun gangancin yake musu, tunda Najim yaga haka ya fashe da dariya yana faɗin..
"Hala baka san wacece Mamah Raihanah ba ko? Allah ya bada sa'a!"
"Yayar Abbana ce ita! Sai dai nima muka baka san waye ni ba, Jini Insha Allah zan dawo maka, nan da karshen wata naje na kuma dauko Matana." Ya fada yana wani jin nishadi.

"Baka ce kome ba akan Fulani?" Najim ya tambaye shi.
"Bata da wani amfani sosai, nima ina jin ba dad'i akan riketa da nayi, amma wanda nake son ya fito yaki fitowa, shi yasa na ajiye ta, kuma naji wasu bayanai na ban mamaki, ashe kafin a haife ni Ammina tasha wahala a hannun Wani wai Shamaki tare da Dan shi Abdul, shi yasa nake son datse wanda yake saka su aiki." Shiru yayi..Najim yace mishi.
"Kasan wanda yake sasu kenan?" inji Najim.
"A'ah ban ce na san shi ba, kawai ina kintatta muryan wanda ya kirani da wayar Fahad."

"Jay! Anya baka aiki da mutanen boye!?" Inji Najim,
. Dariya yayi sannan ya isa tashan jirgin saman, ya fita da komin shi, sannan suka yi musabaha da Najim, kafin suka yi sallama.

...... Jirgin Abuja ya nima kuma Allah yasa aka samu, dan haka yana shiga ya a sauke ajiyar Zuciya, tare da fadin.
"Yan matan Saraki ga sarakinki nan zuwa gare ki." Ya sake wani kad'aitaccen murmushi, yana hango yadda zai yi wasan kura da yar tsohuwar matan shi.

.......
Sosai na sake amma bawai dan Jay baya raina bane, kawai ina jinjina yadda ya iya furtawa ya sake ni ne! Sai naji abin yayi min girma, a hankali na gama abin da

Please Login or Register in order to submit comment