Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na shafa gashin kan shi ina murmushi, zama nayi muna cin abinci muna d'an tab'a hira, har muka gama. Sannan yaci sosai. Daga nan ya mike zai fita na dauko gyalena, tare da amsar jakar kayan da zai fita da ita.
"Saraki! Ko zaka d'an kira min Jannart!" Juyawa yayi tare da zuba min ido,  ran shi a b'ace, a rude na shiga tambayar shi.
"Wa kika ce na kira miki?"
Take sunan da na kira ya fado min a raina. Sunkuyar da kaina nayi sannan nace.
"Ka kira min Ummul khair." Takowa yayi gabana, sannan ya riko hannuna yana faɗin.
"Sunan Mahaifiyata ce da ita! Don Allah ko a wani gurin karki kuma kiran sunan nan haka"
."Insha Allah!" Nace mishi, har kasa na rako shi, ina kallon Munih ta tare shi na mika mishi jakar shi zan dawo daki ya riko hannuna.
"Jay! Ka dai sannan ban iya girki ba, kuma naga alamar zaka kashe ni a gidan ka, dan haka ka nima min abinda zan ci ko kuma wannan guzumar tayi girkin da nayi."
"Wuce ki koma, zan turo miki da Noorie din."
.yana gama gaya min haka, na juya da sauri shi kuma ya riko hannun Munih, ban san ya suka kare ba, sai dai Karamah tazo ta amshi kayan abincin ta kai cikin gida.

   Can ina zaune sai ga Mamah Sarah da Mamah Raihanah, sun shigo,  ina kwance Husnah tazo ta kirani, har na canza kayana zuwa doguwar rigar material.

            Babban mayafi na yafa, sannan na  fito, na same shi a falon shi na kasa, ashe har dashi.
...
   Cikin jin kunyar su na gaishe su, sannan suka amsa suma cikin fara'a, sannan suka yi shiru. Kafin suka hada mu suka mana nasiha sosai. Sannan suka kuma tambayi Munih abinda ke faruwa. Kai yarinyar nan bata da kunya, dan a cikin abinda bai fi minti goma ba. Ta fadawa su Mamah wai bai tab'a kusantar ta ba.
. Sannan ya kusanci dukkan mu, amma ban da ita.
"Kuma yasan ban iya girki ba,sai wancar guzumar ta girka mishi ya cinye ya hanani, wallahi ba zan yarda ba. Tunda Husnah ba bani nata zata yi ba. Ina laifi ita wancan babbar banzan ta girka dani."

"Ai kin san zamanki nake da zan girka abinci na baki, toh bani Husnah Umar ba."

         Kai na a sunkuye suka shiga rashin mutunci a gaban surukan su.
     Zai magana Mamah Raihanah ta dakatar da shi.
"Aanih ko Husnah ba bayinki bane? Suna iyaye ne suka haife su, dan haka ki mike ki shiga kicin ko koyi abinda zaki dafawa cikin ki, kuma idan kin san kin auri Jalal dan ki d'aga mishi hankali ne, ki gaya min yanzun na saka shi ya sake shi tunda ke baki san yadda zaki zauna dashi ba.mara kunyar banza da na wofi.

   Ke gaki me baki, kin zagi Aanih a gaban mu, kin san yadda muke da Ubanta, sannan Husnah da kike gani Ubanta kanina ne, dan haka ko shiga hankalin ki, ko a tura ki inda kika fi wayo. Sakarya kawai. Wallahi koda wasa naji wata ta kuma cutar da dayan ku, sai ba baku mamaki. Aanih kiyi hakuri. Kece babba a cikin su dole zaki yi hakuri da halin kanenki, sannan ki rike su da zuciya daya."

Nasiha bayin Allah nan sun mana shi, sannan zasu mike Mamah Sarah tace min.
"Sai ga abin karyawa, muna shirin kawo miki."

   Murmushi nayi, tare da wasa da hannuna nace mata.
"La babu komai."

"Allah yayi muku albarka!" Daga haka suka fita har dashi, Ni kuma na koma d'akina ina me shigewa kitchen na shiga ƙoƙarin daura na rana, ashe wai kai karar shi Munih tayi ya make ta, ina wanke  tukunyar da zanyi amfani da shi, naji ya rungume ni ta baya, yana lasar wuyana zuwa kunne na, da sauri na ture shi ya sake murmushi yana cewa.
"Nazo da cefene, sauko ki raba muku!"

   Zuba mishi ido nayi kamar zance a'ah yadda ya narke min sai naji babu dad'i.
"Toh ina zuwa."
"Don Allah muje!" Haka na bi bayan shi tare da samun kayan abincin a shirge a gefen falo, ina gani ya wuce kowani bangare ya fito da su, akan idanun su na raba kome Dai-daiton yadda zai musu.

           Amma uwar marasa kunya tace min..
"Kwai da kika ajiyewa kowa kiret uku, ai raba shi zaki yi a kirge." Buge mata baki yayi sannan yace min.
"Kaji ba sai kin raba ba, kowa ya dauki haka daya. Haka kwalin kifin da namar ma kowacce ta dauki ledar gabanta,kayar miyan ma haka, tunda Aanih bata iya rabo ba..
Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga 300? katin mtn 300 normal posting 21/October Insha Allah
Zahrahn Addah Ramlat domin nuna shaidar biya! ita za a turawa....
07035133148/ +22784506476 yan Nijar zasu iya samun A'isha Indo Nijar....
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:59 AM - Ummi Tandama: *Baya bata zani*

"Daga yau babu wacce zata kuma muku rabo, wallahi Munubiya. Idan kika kure ni."

   Daga haka ya juya ya fice abin shi, ina kallon yarinyar nan tasaka kafa zata taka min kwai, Allah ya taimaka sai ga Jay, ai kuwa ran shi ya b'aci, sosai dan tun daga bakin kofar yake falla mata mari, nima da naje kwatar ta, sai da ya ture ni na fadi, na buge gwiwata.

     Ran shi ya b'aci, sosai. Ganin yana shirin illata musu yar mutane, Husnah ta fita da sauri. Zata cikin gida ya daka mata tsawa, tare da cewa.
"Wallahi kika bar Bakin kofar nan kin tafi kenan."

Bai da hankali, akan haka zai iya sake mace, mari kawai yayita mata, sai da fuskar ta ya kumbura sumtun, sannan ya fita ya bar mana gidan, kowacce taja tsimar kafarta tayi shashin ta.

               Karshe bata dauki kayan abincinta ba, ta bar mishi a gurin. Da ta dawo yagan su a gurin bai mata magana.

      Dan haka ya kwashe kayan baki daya ya raba mana, ya kuma buga mana kashedin kar mu bata abincin, haka bai min ba, dan haka nace mishi.
"Ba zai yiwu ba, sabida hakkinta ne da yake kanka, kuma dole ka sauke, kai kana jin cewa zaka zauna ne cikin farinciki babu tashin hankali, ai kasan haka ma ba zai faru ba."

       Bayan mun gama magana, bai ce min kome ba ya ficce. Can sai ga Fulani Balkisu tazo. Ganin yadda fuskar Munih ya koma ta sakata a gaba suka nufi cikin gidan.

    ......
Har falon Abba suka nufa, ta zauna a kujeran dake kallon Abba, Fulani Nanah da Yahanasu suna zaune.
"Yallabai! Kaga abinda Jalal yayiwa Munubiya! Don Allah kalli fuskarta! Idan baya sonta babu dole, meye na duka kuma?!"

     Shiru yayi sannan ya kira, Jay yace.
"Kazo nan!"

    Bai jima ba, ya isa falon ya nemi guri ya zauna. Tare da sunkuyar da kanshi.

   Shiru yayi yana sauraron abin da Abban shi kece mishi.
"Babana! Yanzun a matsayin ka na me hankali meye Munih tayi maka haka."

  Kasa magana yayi, sabida bai taɓa tsammanin zasu iya kawo karar shi ba.

"Afwa Abba"
Nan Fulani balkisu, ta shiga faɗa  kamar me, Abban shi ya zuba mata ido, shima jay din bai magana ba, har ta gama masifar ta tayi shiru dan kanta.
"Toh kaji abin da kai mata don Allah ka zauna da matan ka lafiya mana."

  Duk laifin na shine, sannan Abban shi ya sa shi ya mai da mata abincinta da ya raba, bai ce mishi kome ba, da zai bar falon ya bawa Abban shi hakuri sannan ya bar musu falon. Nan itama suka bar falon da Munih, inda tayi mata alkawarin sai ta samo mata kan Jay duk bala'in taurin kan shi. Sannan ta kuma ce mata karta ragawa kowa har shi.

  ........
Ina kwance ya shigo min yana huci, tashi nayi na zauna. Sannan na mika mishi hannu, ya tawo a sanyayye ya zauna goran ruwan da ke kan Yar teburin kwalbar falon na dauka na mika mishi sai da ya rabi, sannan ya sauke a bakin shi, amsar kwalbar nayi na ajiye kuma.

           Sannan na rike hannun shi ina murzawa, kallon yadda fuskar shi ta sauya.
"Kayi hakuri! Yanzun nauyin mu da duk wani abu ya haura kanka, dole kayi hakuri da halin mu, sannan ka san yadda zaka iya biyar da kowaccen mu, ba sai lallai ka d'aga hannu akan mace ba.

   .... Na san dukiyar ka zata ɓannatar kai kuma ka hukuntata, amma kuma hanyar da kabi ba zai kare ka da kome ba sai zuɓewar kima!"
.d'aga kai yayi tare da tsare ni da ido.
      Gyad'a mishi kai nayi cikin nuna mishi, gaskiya ne nake gaya mishi..
"Me yasa kike ce haka?"
  Hannuna na saka a cikin gashin kanshi, tare da hautsina shi, nace.
"Yau ka dake ta! Gobe kuma Ni zaka daka, jibi kuma Husnah. Kafin mu ankara, mijin mu ya zama maduki, kaga kenan mutum daya ya koya maka mugun aiki."

         Shiru yayi yana kallon yadda nake kokarin fahimtar da shi abin da ya sani.

     "Toh nagode tunda kin san da haka toh bari na.."

Da sauri na kalle shi, kamar zan yi kuka. Tare da ture hannun shi da yake kokarin cusawa a cikin rigana.

        "Ni don Allah bana son haka, kai ba halin kaga mutum sai ka nemi tab'a mishi jiki."  Na faɗa ina mik'ewa, dawo dani yayi sannan yace.
"Waye yace ki makale min?"

         Dan renin hankali, kawai shige min yayi tun ina ture shi da jin haushin abin da yake min har dai na zuba mishi ido, dan ban san lokacin da nabi jirgin shi ba, sai da aka bankad'e kofar da mugun karfi, tare da wani irin iska, muka mike daga ni har shi, gyara zaman rigana nayi cik'e da kunya, zan bar falon.

    Shi kuma ya zubawa kofar ido babu kowa daga ni sai shi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo gare ni har na shige d'akina.

       Bai shigo ba, kawai ya fice daga gidan.
         

              ....
Kwatarkwashi.

   A kauyen garin, kwance Jakadiya Sahurah take, idan ka ganta tsufa ya cimma ta, amma har yanzu tana nan a tsayen ta.

         Abu daya take fama dashi shine makanta, wanda tayi rashin lafiya ta sanadin haka idanunta suke daina gani.

          Mik'ewa tayi tare da kallon kofar d'akin ta kamar tana gani, kafin ta lallubi sandarta, tace.
"Har ila yau, bai zo ba. Koda ba a haife shi bane? Ina tsohon shekaru ashirin da takwas, sai dai ko mace. Ina indai ita ce, tsuguno bata kare ba.

              Idan kuma na miji ne! Karshen zamanin yazo, waye zai isa Daura."

   Gyada kai tayi tare da mik'ewa ta fito bakin kofar ta, tana surutunta, mutanen gidan da take kallon hauka suke mata, yayinda ita take ganin kamar basu san meke damunta ba shi yasa suke kiranta da Mahaukaciya.

      ---
"Saurin me kike? Bayan shi zai zo! Karki damu kanki tabbas zai zo nimanki, kuma har ya saka a tafi mishi dake, da dai kinyi hakuri ne dole zaki fuskanci kalubale daga gare shi." Inji wani algungunmin tsohon wanda yake sanye da fatar ɓauna.

            "Hmm! Kawai ka kife shi! Yadda ba zai iya zama a karagar mulkin, ka haukata mishi Ƙwaƙwalwar shi, yadda." Ta faɗa.
"Dakata!" Ya d'aga mata hannu..
"Ba Jaamal bane! Jalaludeen ne, karfin tsarin da yake nima zai iya kashe min aljanuna da suke min aiki. Daf yake da zama me cikakken iko da nasara, karki yarda ya kasa wannan damar zuwa gida biyu.

           A sannan ne babu wanda zai dakatar dashi ko ya hana shi, sai dai har yanzun muna da damar niman Sahurah, domin itace take da masaniyar akan yadda zai dakatar da kome, kuma naga baku son dakatar da abin da yake faruwa a masarautan.

      Dan haka dukkan ku, ku bazama niman Sahurah yadda zaku iya dakatar da ita, idan shi ya same ta. Tabbas zai nimo ki, nake ba hatta sauran wanda yake boye a bayan idanun jama'a. Amma kafin nan ku fara mishi bayani Yaren da zai fahimta  haka zai sanya a fara wani tunani na daban."

      Ajiye mishi jakar hannunta tayi tare da barin d'akin. Da sauri.

  Tana isa gurin motar ta shiga, tare da zama ta dauki alkalami ta fara rubutu, da ajami.

    اسلام الاكة
بي غيثو إرت الدنم مسلث، دفتن سشقن ييث غزك. كمر يدد كدقك عن كو في ابين د يدث. كغرغطس يدد ءٱخ سير تاكررم غب. كركگشيس كبر شي يري ثكد شيرم، دغن دمطر دغ إدمكثي
دغ
فلن طثي....
Daga haka ta nade takardan sannan, mikawa driven tace mishi.
"Idan mun isa ka kai daura."

Amsa yayi sannan yajata suka nufi cikin garin kwantagora.

***
Kwana biyu da rikicin Jay tare da Munih ya sauka a d'akinta, Allah sarki, yau munga feleke. Shiga da ficce, shan kamshi habaici da rawan kai.
Dake ina sama, ina jinta ban ma leko ba balle tace an zo saka mata ido..

         Har dare, ana girki can da ta gama zagayenta ta gama ihu da zage zage, babu wanda ya kulata.

                    Har ya shigo, ina zaune akan kafet, hankali na yayi kan na'ura me ƙwaƙwalwa, ji nayi an tab'a ni, na d'ago kaina daga shi sai yar gajeren wando tare da farar riga, ya gyara fuskar shi da kasumbar shi, mika mishi hannu nayi.

Ina murmushi, buge hannuna yayi da sauri na mai da hankali na kan shi, tare da zuba mishi ido.
"Zo d'an kanina!" Kamar na zage shi, ya buge hannuna.

"Toh meye nayi kuma?"  A sannu ya mike zai bar d'akin nace mishi.
"Don Allah, kayi hakuri ba san laifina ba."

       Mik'ewa nayi na isa gare shi, ya riko hannuna, cikin na shi, yana me kaiwa fuskar shi. Kashe mishi ido nayi sannan nace mishi.
"Au! Yallabai aski kasha haka, shi yasa naga kana kyalkyale amarci."

     Saka hannun shi dukka biyu yayi ya rungume ni, yana murmushi sannan yace min.
"Yau wuni guda, ina kallon wayana ko dan sakon nan babu, sam baki damu dani ba."

          Hada goshina yayi da nayi, ina yar karamar dariya nace.
"Ina zan iya da shariyar ka, idan miskilancin ka ya motsa baka ji baka gani, shi yasa naki kula wayar ma, ai fita kayi kana fushi dan nace zan shiga cikin gidan gaida su Mamah."

     Daura bakin shi yayi saman nawa, a lokaci guda muka kalli cikin idanun juna.  Nice na fara kasa da kaina, kafin na janye bakina baya nace.
"Jay! Kana sha'awan jikina ne fa! Sam baka tunani na, jikina shine muradinka, tunda da bakin ka kace baka sona."

"Eh shi yasa lokacin da kika turo min Hanisah ta gaya min kina son kayan fitar liyafa, baki yi tunanin bana sonki ba!"

Da sauri na kalle shi, murmushi yayi sannan ya d'aga min gira daya.
"Ni ban tura ta ba! Taji dai muna magana da Saif.."

Cizon bakina yayi, tare da b'ata fuska.
"Karki kuma kira min sunan wani kato a cikin gidan nan!"

"Toh Naji, amma."

"Baki tambayi taya aka yi na kasa wancan tuzurin saurayin baki ba?" Ya faɗa min.
"Toh ni nuna ruwa na"
"Zaki ga baki da ruwa."

        Ƙoƙarin kwace kaina nake yi, yaki sake ni, "tun daga ranar da kika shiga rayuwata nake jin duk yadda aka yi, ina da nasaba dake.

            Na rasa fahimtar haka, sai ma rigimar da kika ta takalowa,  haka bai ishe ki ba, sai da kika kwafta min mari, sannan kika yi sanadin haɗuwa na da iyayena.

                 Ana saura sati daya bikinki, Baba Sarki yake gaya min shekaru Ashirin da daya, da suka wuce, sun daura mana aure. Bayan b'atar da nayi da shekara daya aka raba auren, iyayen mu basu sani ba, daga kakanin mu, babu wanda ya sani.

           Sai gashi kin nimo mijinki, ko kunya baki ji, Baba Sarki da yake gaya min, nayi mamaki dan haka nazo har sokoto, na sami Dattijo, muka yi magana. Na kuma ce ko bana sonki a bani matana ko kuma a tashi Sokoto a tsaye da kafarta.

    Ranar da na sauke ki, ai sabida kar wancan banzan ya kare miki kallo ne, dan haka ki ji a ranki ni har yau ina kan bakana, bazan tab'a sonki ba. Dan bana jin kome akan ki, sai yan uwanta ka."
Wani irin abu naji a raina, ban san lokacin da na ture shi ba, nayi juyawa na kwashi kayana, yana min magana tuni na isa d'akina na rufe kofar, na zauna a jikin kofar, tare da cusa kaina cikin cinyoyina. Wani irin abu nake ji a raina, me mugun ciwo, tare da jin tsanar Jay a zuciyata.

  Bai bi takaina ba yayi ficcewar shi, kasa. Haka na kwana da b'acin rai da asuba nayi mafarkin wai an kawo min shi cikin jini baya numfashi. A firgice na farka na shiga nayi alola nazo na gabatar da sallar nafilla, da sauri na shafa addu'o'in na fito kasa, na tsaya a bakin matakalar benen, ina jin ya fito daga dakin Munih na sauke ajiyar zuciya. Sannan na juya abuna, ya hango Ni, amma ya share ni kamar bai ganin ba.

              Bai dawo gidan ba sai da gari yayi haske, ina kwance a saman...
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 9:59 AM - Ummi Tandama: *Zuma, ga zaƙi ga harbi*

Ina kwance ya shigo, dake Allah ya daura mishi niman rigima, idanuna na lumshe ya shiga ja min babban yatsar kafana, bude ido nayi tare da lumshe su, dan bana son damuwa. Da sauri na kuma buɗewa tare da b'ata fuska kamar zan yi kuka.

         "Dan nace bana sonki shine kike fushi?" Ya faɗa min,

"Toh ina ruwana da kai, karka so ni mana, idan baka soni ba, dubunka sun so ni, dan haka ka kyale ni naji da abinda yake damuna." Fadar haka da nayi ya bashi haushi amma jin na fadi ya barni naji da damuwa ta, ya sashi zama kusada dani. Yana kallon fuskana.

    "Batul!" Tsigar jikina ne suka mike sosai, a hankali na tashi zaune.
" Matso kusa dani naji meke damunki!" Ya fada min tare da mika min hannu, kamar zan yi kuka nace mishi.
"Babu kawai bana son magana ne!"
"Zo ki gaya min meke damunki!"
Ya mika min hannun, babu yadda zan yi haka na isa jikin shi. Kawai naji zuciya ta tayi mugun rauni, kuka ne ya kwace min.
"Ya ilahi! Dan nace bana sonki?"

"A'ah, ba haka bane kawai ina jin wani irin yanayi ne, da ban saba jin shi ba, sai da rasa wani abu daga jikina nake ji shi."
.zuba min ido yayi sannan yace min.
"Kamar Ya? Kawai naji kamar zan rasa wani na jikina ne"

     Murmushi yayi sannan yace.
"Har yanzun akwai masu yarda da canfe kenan? Toh babu abin da zai faru sai Ikon Allah, dan haka karki kuma zubda wannan hawayen masu mugun tsada, kin san nawa darajar su take, da kike zubda min su?"

     Girgiza mishi kai nayi, a hankali ya janyo hannuna yana fadin "yau ban yi sallama da."
Buge hannun shi nayi tare da dariya nace..
"Kai angon Munih ce, dan haka me zaka dauka a jikin yar tsohuwar da zata haife ka, kawai jeka gurin yan matanka."

"Lallai kin gaya min magana, Insha Allah zan nuna miki abin da zai baki mamaki."

    Rufe idanuna nayi cikin jin kunya da dariya nace.
"Kai kan inda kunya tabi ina da yakinin baka bishi ba, kawai sai ka sake magana kamar yadda yake babu sakewa."

"Hmm! Da bance a bani wannan abin na tab'a ba." Ya faɗa yana nuna min kirjina, wani irin kunya ce ta kama ni, da gudu na bar mishi falon, Jay bai ga inda kunya ba, ina ga kunya na gabas shi yana yamma, biyo ni d'akina.

Haurowa gadon yayi, ya janye bargon, ya shiga min chakulkuli. Wayyo Allah na, kamar zan yi hauka, sabida tsabar dariya da wani irin farin ciki.

Tsabar ya addabi rayuwata da chakulkuli, karshe zuɓewa nayi a jikin shi, tare da k'amk'ame shi..ina sauke wata irin ajiyar zuciya.
   
Bakin shi a kunne na, ya sauke min wata irin numfashi, wanda ya saukar min da kasala, na kuma narkewa a jikin shi, d'ago kai na yayi tare da kallon fuskana, tare da zaro harshen shi yana lasar bakina, a hankali na bude idanuna akan shi. Ina jin hannun shi yana yawo a jikina,

Ji nake kamar a cikin Ƙwaƙwalwata yake min yawo dashi, kare narkewa nayi a jikin shi,.kirjina na wani irin bugawa, kallon fuskana yayi cikin nutsuwa yace min.
"Ina son kasancewa dake, amma ina ganin yin haka kamar cutar wa ce."

.... Kifa kaina nayi a kirjin shi, na rasa me zance mishi, duk yadda nake ji akan shi bazan iya sakewa na bashi kaina da jikina sabida yayi farin ciki ba, indai da gaske yana yina toh dole sai ya yarda da hakan tare da gayawa mutanen da yace musu shi yana yina. Hmmm lallai kuwa, ba dai wannan Jalal din ba domin baya jin zai iya ƙaryata kan shi....

    D'ago kaina yayi tare da sumbatar goshina, yace min.
"Zanyi tafiya Katsina! Insha Allah yau zan dawo, d'azun na ganki ne shi yasa na zo duba lafiyar ki."

          Mai da kaina kirjin shi nayi, wani irin tsoro na kuma kamani, mafarkin da nayi akan shi ya shiga dawo min,  rintsa idanuna nayi cikin tashin hankali na bude baki zan yi mishi magana ya rufe min da nashi.

          Tare da kashe min ido, dole nabi shi ba dan naso ba, ya gama cinye min bakina, kafin Allah ya kwace ni sakamakon bugun kofar da matar shi take kamar zata fasa mana dodon kunne.

          ----
Bayan ya janye daga jikina, ya fice da sauri, shi nan yana ƙoƙarin ƙaryata zuciyar shi, har ya isa bakin kofar ya same ta, da kayan barcin da ya barta, ko sallah bata yi ba, daure fuska yayi kamar bai tab'a dariya ba, sannan ya sauka kasa, taso shigowa ta zage ni, bai bata damar haka ba, dan haka ta sauko ta biyo bayan shi, lokacin ya wuce dakin Husnah, itama tana barci a cikin bargo yaga alamar tayi sallah.

  Dan haka ya fita bai gaya mata zai yi tafiya ba, har ya nufi dakin Munih tana kallon shi ya shiga yayi wanka tare da gyara zaman tawol  ya fita daga dakin ya nufi dakin shi.

Ya saka kayan shi tsaf ya shirya, sannan ya kuma dawowa d'akina, Tabbas da kayan na gan shi a tsorace nake kallon shi jikina kamar wacce aka tsoma cikin kankara, kayan cikina sun cure guri guda. Ga wani sanyin da yake damun jikina kamar ana kusanta ni da kankara.

Bakina yana rawa nace mishi.
"Karka je ka hakura da zuwa katsinar nan yau!"

Wata uwar harara ya watsa min tare da kauda kan shi yana min wani,. gargad'i sannan ya ficce daga d'akin, ko sallama bamu yi ba.

Yayi ficewar shi, ina kwance a gurin har wani barci ya rufe ni, kamar yadda nake cikin tashin hankali haka nake barcin cike da tashin hankali sabida miyagun mafarkin da nake wanda ya sani farkawa ina kwala mishi kira, zaune na tashi naga kamar giftawar mutum ta tsakanin baranda na, na sama mik'ewa nake son yi naji kamar ana wasa da ruwa a ban d'akina, wani tsoro ya kamani, dan dole na mike tare da lek'awa ban dakin babu kowa.

.ina juyowa naga wucewar mutum da sauri, a firgice na kuma juyawa. Kai karshe da tsoro ya gama kamani da gudu na dauki mayafina, na sauko daga sama, kasa ina sauke ajiyar zuciya.

  Tsabar tsoron bala'i. Da sauri na yafa mayafin zan fita, naga Munih ta fito tana waya tare da yatsina fuska kamar yaga mugun abu, bata gabana dan haka na saka kai zan fita ta kalle ni.

"Gidan Uban wa zaki?" Murmushi nayi tare da saka kai zan fita ta riko min mayafina dina, da sauri na juya muka kalli juna, sake min da sauri.

            Saka kai nayi zan fita, tare da fita filin gidan, tunda

Please Login or Register in order to submit comment