Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itama Fulani da take hannun ka ba lallai ka koma ka sameta a raye domin sun shirya maka yadda baka yi tsammani ba."

Daga haka ya mik'e tsaye, sannan yace mata.
"Ni zan tafi!"
"Nagode ranka shi dad'e, kayi ƙoƙarin gano waye ki bibiyar ka!"
"Insha Allah!" Ya furta a hankali.

----
Washi gari.

Ya samu ganin Baba Galadima. Sun tattauna sosai, har ya mike zai bar gidan Baba Galadima yace mishi.
"Ka shirya niman wanda baka sani ba?" Juyawa Jay yayi sannan yace mishi.
"Yallabai tsaf na shirya niman shi, na shirya cin kaniyar shi, sai na gyara mishi zama, idan na kama shi sai na haramtawa Zuri'ar shi mulki baki daya, sai na fitina kome na shi muje zuwa."

Daga haka ya fice daga gidan..
Kai tsaye daura ya wuce abun shi.

----
Tun da ya isa, ya shiga yiwa manyan masarautan, lokaci guda ya shiga amsar duk wani abun da aka yi ba bisa ka'ida ba. Wasu abubuwan ma kawai jin su ake amma Jay ya Bankad'o su.

Ana cikin haka Allah yayi wa Ajiya rasu, take aka mai da mutuwar kan Jay, inda suka ce da hannun shi. Sai dai bai ce musu kome ba.

Yana sane amma yaki magana abin da ya kuma basu haushi yadda yasa aka kwashe kayan fadar aka kuma saka wasu, abin ya basu haushi domin a garin cire wasu abubuwan aka yi zaro layyu, da wasu abubuwan murmushi yayi sannan ya bada aka kaiwa Baba Magaji. Gefe gudakuwa Ba komai ke damun shi ba sai kewar Yar guzumar matar shi, ta tsaya mishi a rai.

Ban da yana matuƙar kunyar Mamah Raihanah ba, da yake ya dauko matar shi, amma cike yake da kewarta. Nutsuwar da ya samu da ita, ba na wasa bane shi yasa yake kuma jin lallai zai koma Abujan.

..... "Jay jiya na sami wannan takardun a hannun Baba Hashim, ya bani kuma abun mamaki sunan Galadima ne ya fito a cikin. Meye alaƙar shi da mutuwar Ajiya dan Abba ya gaya min cewa akwai matsala a tsakanin su. Kafin wannan abun ya fito." Karb'an takardan yayi sannan ya duba kana ya dube Najim yace mishi.
"A bisa binciken da nake, Galadima yana cikin magadan masarautan nan! Domin shi kakan shi na uku shine Zulum, Ziryana itace kakar Ammih na uku.

Abun da na kasa anan wancan lokacin da lokacin Ammina akan ta akayi rigimar! Wannan lokacin kuma akan wacece za ayi rigimar?"

"Eh amma, ina ganin babu mace a wannan karnin da za ayi rigimar akanta shine ya koma akan karagar mulkin ka." Inji Najim,

"Nima na fahimci haka,"

Shiru yayi sannan ya cigaba da dube dube, har zuwa lokacin da suka bar fadar.

.....
"Fulani! Dama ina son muyi tsayayyar magana. Waye ya.."
.
"Jalal ban san kome ba!" Ta gaya mishi haka tare da kauda kanta, dan dole ya hakura ya fita, yana shiga gidan shi, ana kiran shi a waya yazo ga shi an shigo an kashe fulani.

Wannan tashin hankali yayi matukar tasiri akan shi, yasan suna fakon mutanen da yake zargi ne, shi yasa.

Haka ya isa yaga irin kisan da aka mata, sawa yayi a kama masu kula da kofar ta, yayi ta azabtar dasu, har sai sunyi magana.

.... Kusan mutane goma, aka yi ta basu wahala, kuma sun kafe basu bane.

---
Tun ranar da ya dawo dani, nake yawan mafarkin gani cikin jajjayen kaya, hannuna da kafana cikin jini ysna zuba. Kaina kuwa wani irin kambun jan zinariya ce, me katon tagulla a gaban kambu.

Yau kam ina zaune naga suna jan wani mutum, duba shi nayi naga Jay ne, anje an saka kan shi a saman katako, wani kato ya d'aga adda zai sare shi na fasa kara na farka.

Cikin tsoro na duba naga karfe biyu na dare ne, a hankali na sauka naje nayi fitsari na dawo na kwanta, a sannu barci yayi gaba dani.

---
Washi gari ina fitowa Mamah Raihanah take gaya min abin dake faruwa. Yaki sauraron kowa . Dan haka ina son nace mata ko zamu tafi can ne ina tsoron kar ta ce na cika damuwa da shi. Juyawa nayi zan fita tace min.

"Fatimah! Jay yana bukatar me taimako, barcin da kike yaci ace kin farka, ki taimake mu mana."
.kallonta nayi sannan nace mata.
"Insha Allah, zan tsaya mishi."
Daga haka nasa kai zan fita tace min.
"Ki shirya muje."

Kaina a sunkuye na gyad'a mata kai, sannan na koma d'akina nayi wanka na shirya, bamu bar Abuja ba sai karfe hudu, koda muka iso yana can gidan horo yaki fitowa. Matsawa Najim nayi ya kai ni har bakin kofar shiga cikin gidan.

Da sauri na shiga, na same shi a tsaye ya juya musu baya, ana ta zane mutanen.
"Ku dakata!" Na faɗa musu.
"Ranka shi dad'e! Meye amfanin haka?" A fusace ya juyo min. Tare da zuba min ido, tattare alkyabar jikina nayi na isa gaban shi, cikin damuwa nace mishi..
"Kazo muje kaci abinci."

"Taya? Ya kike son nayi? Ya zanyi da jinin da ake zubdawa ba bisa ka'ida ba?" Ya faɗa min a tsawace.
"Amma bayyana fushin ka, kasawa ce! Taya zaka biyewa mutane kana aikata kuskure talakawan kane fa! Kuma mutanen ka da ka yarda dasu don Allah kazo muje, taya za'a ce babu wanda zai dakatar da Kai."

Rigima sosai muka yi kafin ya riko hannuna a fusace, ya nufi cikin gidan sarautar bai zame ko ina ba sai a fadar shi, ya juyar dani yana faɗin.
"Kalli kujeran da ake zubda jini sabida dashi, ki duba ki gani sabida wannan ake kashe masu yunkurin gaya min meke faruwa, ya kike so nayi?" Naushi ya kaiwa bango Ya fita hayacin sa, sai illata kan shi yake.

A tsorace na shiga ƙoƙarin rike shi, kamar mara hankali haka yayi ta jima kan shi ciwo, yana yi yana faɗin.

"Sun meye ke damun su? Meye nayi musu, da basu son a fadi gaskiya, yau sati Uku da dawowa daga gurin ki, kin san yadda nake rayuwa kuwa, abu daya ya gaggara, sun Kashe Ajiya. Sunce ni ne, jiya na shiga gurin Fulani Hasiyah sun bi sahu sun kasheta meye nayi musu da zafi?"

Ya faɗa da karfi, cikin wani irin tausayi shi, na mike a hankali na isa gurin da yake ta dukar bangon na riko hannun shi, zan hana shi, juyawar da zai yi ya ture ni, Allah ya takaita ban fadi akan kome ba sai akan karagar mulkin masarautan. Mik'ewa zanyi naji kamar an mai dani, cikin kujeran da karfin tsiya.

Wani abu da bazan iya cewa gashi ba, yana bin jikina da mugun gudu, wanda yafi na fitar numfashi.

A hankali mafarkan da nake yi, ya shiga dawo min. Ji wani abu nayi yana haura min saman kaina, a hankali nake jin kamar ba dai-dai nake ba, ihun mutane da Hayaniyar dawakai suna kara kusanto ni. A sannu nake jin duniyar tana juya min, kome yana zuwa min daki da daki. Tun daga wasu karni har zuwa karnin goma sha tara, izuwa yanzun da kome yake faruwa.(wato tun daga karnin Ziryana zuwa karnin kwarkwarah)

Karan bushe bushen algaitu, nake ji. Tare da ganguna, a hankali na bude idanuna da suka rine zuwa jini, wani irin dakiyar zuciya nake ji, bana jin kome akan kowa musamman da na bude idanu naga wasu irin mutane sunyi sahu a gabana. Sannan suka dunkule hannun su, suka saka a gefen kirjin su na dama.

Sannan suka zube a gabana alamun girmamawa.
"Muna maraba da Sarauniya Aanih Fatimah Khatoon! Sarauniya ta hudu daga cikin al'ummar bani Adam! Kuma Matar korarren Sarkin mu, Jalaludeen Jamaluddin! Muna jiran cewar ki, domin isar da umarnin ki! Ranki shi dad'e shekaru dari uku da ashirin muna jiranki."

Kallon su nayi, sannan na kalli yadda kayan jikina yayi ja, hannuna da kafana sun yi ja kamar an kwara min jini. A hankali aka kawo wani tire da wani abu lullube da jan mayafi, suna kawowa suka janye kambun jan zinariya ce, sannan wani dattijo ya dauki kambun da wata sandar tsafi ya daura min a kaina, a hankali kome na jikina yake komawa ja. Juyawar da zan yi naga Jay yana kallona da sauri ya tawo gani na a tsaye ya tun karo inda nake, cillar dashi suka yi zasu far mishi nace.
"Ku dakata!" Da sauri ya kuma dawowa ya rungume ni, tare da kallona yana fadin.
"Aanih lafiya kuwa?"

D'ago kaina nayi zan mishi magana naga kamar abin da ya faru ya b'ace min daga idanuna. A hankali jikina ya sake tare da zuɓewa a jikin shi ina mai da idanuna na rufe, da sauri ya dauke ni, dakyar muka bar fadan.

Gida ya kai ni, falon Mamah Sarah, ina sume. Nan suka shiga ƙoƙarin ganin na farka, koda na farkan ma da ciwon ciki tare da yunkurin amai, basu kawo kome a ransu ba, sai ma komawa da nayi ina Barci, shida Mamah Raihanah suka kaini daki.

Daga nan ya zauna a bakin gadon yana rike da hannuna.

Magayen mafarkan da nake ya hani barci, karshe wanda yafi munin shine wanda nayi ana kashe mutane, sannan Jay shine wanda ake bi zasu kashe shi, haka sukayi ta bin shi garin gudu ya isa gaban wani katon rami, sake biyo shi suka yi na fada ramin, shine suka juyo kaina. Zasu sare ni. Wasu irin halittu, suka far musu. Gurnanin halittun ne ya sani farkawa da mugun kara tare da rike kunne na, ina niman inda zan b'oya. Rungumo ni yayi cikin nutsuwa yana cewa.
"Fatimah ni ne, ki nutsu!" Ina ganin shine na kifa kaina a kirjin shi zuciya ta tana wani irin bugawa.

"Jay na gaji kullum sai nayi wasu irin mafarkai masu mugun ban tsoro, wallahi na cigaba da haka haukacewa zanyi na gaji!" Shafa bayana yayi sannan ya shiga rarrashina, yana gaya min nayi addu'o'in Insha Allah bazan kuma ba.
Alola ya raka ni nayi, sannan muka yi sallar dare, barci ne ya sa stfffffgtfgni dole na tashi, har asuba n .. Fitan

Da ya tafi masalaci, bayan an idar da sallah ne ya samu ne Baba Magaji da sauri.

"Ranka shi dad'e! Lafiya?"
Numfashi yaja sannan yace mishi.
"Wallahi Baba Fatima ce take wasu irin abubuwan masu ban mamaki, sannan tana yawan mafarkai masu firgitarwa jiya take ce min ta kusan haukacewa, sabida abinda idanunta suke gani cikin barcinta."

Shiru Baba Magaji yayi yana jinjina al'amarin, idan ya kintatta dai dai, Tabbas abin da bai faru a baya bane ya faru jiya da Aanih toh taya?

"Kaje kuzo da ita bayan sallar isha....
10/23/20, 10:05 AM - Ummi Tandama: *Birnin kura Akuya bata dilanci*

"Me kike nufi? Me zan yi musu!" Na tambayeta muryana yana rawa, had'iye yawu tayi sannan tace min.
"Sun san cewa makarin bame wahala bace, shi yasa suka zabi bashi yaci, sunyi haka ne dan ki kalubalence su, kuma haka shine suke bukata! Idan kika yi magana ban san me zai faru ba amma tabbas abin ba zai miki dad'i ba"

  Wani shiru ne ya gifta a tsakanin mu, haka yayi matukar tasiri sosai dan ya sanya zuciyar mu cikin damuwa da nazari, d'ago kai nayi na kalleta, sannan na mike.
"Meye kuke ganin ya dace nayi?"
Na tambayeta,
Murmushi tayi sannan tace min.
"Karki damu, ba zan iya saka ki ba ke da kanki zaki aikata hakan."
Shiru tayi sannan tace min, "ranki shi dad'e. Zan tafi masarauta.". Gyada mata kai nayi, kaina a sunkuye. Kwalla na kuma cika min ido, toh meye na kuka? Lokaci ne da zan kwaci mijina, daga halin da yake ciki. Lumshe idanun nayi sannan na bude shi. A hankali na fito daga dakin ina zaga ko ina, daga nesa na hango Mamah Nana.

    Ita da Husnah, banyi mamaki ba. Amma kuma meye suke a bayan gidan, a hankali na sauko daga sama na fita. Tare da bin hanyar da ba zai hada mu dasu ba, na d'an rabe da bango ina kallon su,kamar abu suke tsara wa.
                "Mamah ni fa na gaji wallahi Aanih fa kamar ba mutum ba, wani lokaci sai kiga kwarya idanunta yayi jajjur."
Murmushi tayi sannan tace mata.
"Karki damu! Baba Galadima yana shiri akanta, fatana dai yaci abincin yau."

    Ta mika mata wani kumshe idanuna yana kansu, murmushi nayi sanan na juya tare da barin gurin, bayan wani lokaci ina zaune a falo ta shigo, kamar ba zan mata magana ba, nace mata..
"Barka dai!"
Yake tayi min sannan tayi maza ta wuce, yar karamar dariya nayi.
            ---
Ina fakon ta da zaran tayi girki zata ajiye mishi sai na san dalilin da na zub da abincin, tun tana daukar haka a matsayin tsautsayi har ta fara zargin na fahimci shirin su, ganin haka ni kuma sai na kauda kai akanta.

               A hankali fitinar Jay yayi kamari, dan abu kadan za ayi mishi ya hau fada ko yayi zuciya, gabaki daya ya kwayance mana, yau yana zaune shi da ita Munih ta je sunyi fada da shi, tazo tana kuka. Take gaya min halin da take ciki, ga rashin mutunci da ya tsiro mana, sauka nayi na zuba mishi ido ina kallon yadda yake wasa da Maryam wacce ake kiranta Saddiqah.

    Kawo mishi abincin Husnah tayi, na zubda mata ido. Tana ajiyewa nace mishi.
"Baka kyauta mana! Kuma ka hana mu. Muyi Magana wallahi mu da kake cin mutuncin mu, mune bazamu tab'a cutar da kai ba.

        Idan nayi karya ka ce Husnah taci abincin da ta kawo, wani irin B'oyayyen firgici tayi wanda yayi masifar tasiri a idanun ta, sabida na gani sosai a idanunta.
"Me yasa kika ce haka?"
"Sabida na fahimci cewa laifin mu kake so gani a koda yaushe!"

      Kallon Husnah yayi cikin nutsuwa yana jiran me zata ce.
"Hamma! Ban tab'a jin a raina na cutar da kai ba, sai dai ban sani ba ko da nake girkin ta turo Zabba'u ta zuba min wani abu.

    Dan sau uku ina kamata tana yunkurin zuba min wani abu. Ban gaya maka bane, sabida gudun tozarci daga jinin sarauta, masu ƙarfin iko." Ya karshe maganar tana me kallon cikin idanuna.

Lumshe idanunshi yayi sannan ya zuba shi a kaina. Ban yi mamakin abin da tace ba.

     Domin fadar da suke ban ga hujjar yin shi ba, amma a haka suke yaki domin kare kansu.

"Baki ce kome ba?kin kura mana ido, ki kira Zabba'u." Sunkuyar da kai nayi sannan na juya na koma sama, na kira Zabba'u, tare muka sauko, Jay ya bukaci Husnah ta mai-maita abinda ya faɗa.

    Tana faɗa tana Zabba'u ta fashe da kuka, zata rantse na dakatar da ita, sannan nace mishi.
" Jalaludeen! Ana ciyar da kai guba! Kuma nayi magana ta juya laifin kan Zabba'u."

              "Hamma! Wallahi ka tambayi Munih, ita kanta Aanih tasha bata abu ta zuba min cikin abincin da nake dafa maka." Kallon mu yayi daga Ni har Zabba'u tare da Munih da take saukowa daga sama, rike da baƙinta.
         Rashin Maganar Munih shi ya sanya Jay ya amince da abin da Husnah ta fada.
"Daga yau kar na kuma ganin kafarki a kasa! Kuma kar na kuma ganin Munih taje gurinki, sannan bayin da aka kawo miki a  maida su bana son ganin su,  na kashe wannan maganar daga nan kar na kuma jin wani ya zo da batun."

            Juyawa nayi zan bar falon, yace min.
"Nace ki sallami mutanenki"
"Naji ranka shi dad'e!"

            Kwalla ne ya cika min ido, sannan na juya na bar gurin, ina jin. Kamar na shake Husnah da Munih , banzaye kawai. Na faɗa a raina, haka nayi ta sintiri daga d'akina zuwa falo..kaina ya kulle.

"Karki damu! Amma maganar bata mutu ba, domin haka gobe zata kuma kamawa da wuta."

       "Akan me? Ba yace a bar maganar ba.!"
"Tuba nake sarauniya ta."
Tsaki nayi na kwanta, har washi gari naki cewa kome, ina jin bakin cikin abin da suka min, kawai sai ga sako daga cikin gidan wai nazo.

    Dama kuma ina kallon yadda kowa yake sunkuyar da kan shi, ina shiga na sami Jay a kwance, ana mishi karin ruwa, a hankali na zauna, tare da gaishe da manyan fadan. Kallona suka yi sannan suka yi shiru, dake a falon bana sarki suke.

            "Fatimah! Meye amfanin gubar da kika saka mishi?" Inji Baba Galadima, zaro ido nayi akan shi, kafin na rike bakina, sannan na kalli bakin shi yayi fari. Girgiza kai nayi sannan nace mishi.
"Kaji tsoron Allah!"
"Ku fito min da Ita!" Fito da Zabba'u aka yi! Jikina ya dauki rawa, domin kuwa sun mata duka na fitar hankali, ta zube a gabana.
"Uwar d'akina! Kiyi hakuri sani aka yi." Lumshe idanun nayi sannan na mai da tambayar da Baban Fahad yayi min.
"Ke baki haihu ba, sannan baki bar shi ya rayu cikin salama da aminci ba,.meye ribarki."

           "Kuyi hakuri! Nayi Kuskure. Ba kuma zan kara ba," cike da mamaki Galadima ya kalle ni, sannan yayi kwafa domin yaso nayi musu, ya sami hujjar da zasu kafa a kaina.

       Kuma na san cewa hakan dole ce zata faru.
"Zamu haramta miki shiga cikin mutane, sannan bamu yarda ki yi mu'amala da kowa ba, sabida karki kara sa mana shi."

"Toh da aljanu zanyi rayuwa, kawai ku janye sharadin ku na farko, shine gaskiyar magana, amma ba makawa wallahi zan yi mu'amala da mutane, idan ta kama nayi da irinka ma zanyi ."

         "Kee mara kunya, ki iya da bakin ki,".juyawa nayi na kalli bafaden, da kan shi ya fasa ihu..sannan na nuna Galadima ina kallon Bafaden, nace mishi.
"Me kace ma?"
"Ranki shi dad'e! Kina da damar kiyi yadda kike so."
"Tashi kabar nan!"
Da sauri ya mike zai fita aka taɗe shi ya fadi, sai da kashin kafar yayi kara, sannan na kalli Baban Fahad, nace mishi.
"Me kace?"
"A'a! Ban ce kome ba, kawai abun ya bani mamaki yadda kika iya cutar da mutumin da kike so?"

"Ka yarda kenan?"na jefa mishi tambayar, girgiza min kai yayi sannan. Yace min
"Bani da zab'i da ya wuce na amsa!"
"Haka yayi kyau, shi yasa Galadima zai bawa Fahad Shkurah! Bayan anyi maganar shi da Jannart?"
"Wannan tsakanin mu ne! Bata shafe ki ba,"

Gyada mishi kai nayi, sannan nace mishi.
" Zaka iya tafi."
Jikin shi a sanyayye, ya fita tare da rike hannu Galadima suka fita daga gidan, zuciyar su na kara ruruwa. Kallon sauran nayi wanda dama su kansu a haɗe yake, jini ne ya digo min a hancina,nace musu.

"Kuyi hakuri! Ba zan tab'a cutar da karen Jay ba, balle shi.na amsa ne sabida. Bana son a cigaba da wulakanta wannan baiwar Allah, don Allah kuyi min afuwa zan kula dashi."

"Babu damuwa zaki iya kula dashi, amma sarki Kazeem ya nemi da akai shi borno suyi jinyar shi a can."

"Don Allah ku barni na bishi."
"Zaki iya shiryawa ku tafi tare!"
Dan haka na fito daga cikin falon, ina fita suka yi shiru, Abban Jay ya kalli Jay da ya bude idanun shi taree ya zauna, yace musu.
"Don Allah wai meye Galadima yake nima dani?"

"Kai zamu tambaya tunda kai ne ka shirya ka kuma bamu damar mu zama kananun mutane."
Shafa kan shi yayi sannan ya janyo laptop din shi, ya tura musu suna gani, shigowar Najim, ya kara musu bayanin abinda yake ganin ya kamata ayi.
"Munih ta zauna a gurin Mamah, ita kuma Husnah zata cigaba da amsar shirin Kakanta ba tare da tasan mun sani ba, sai dai akwai matsala"

"Wacce irin Matsala?" Suka tambaye shi.
"Dole zan raba Aanih da abin da suke damunta, ku duba na'ura zaku ga tana magana, har tana kuma nuna dagaske akwai wani a kusa da ita. Sannan kadan idan kuka isa zaku ga wani abin mamaki."

Aikuwa sunyi mamakin ganin abinda yake son gaya musu, kallon shi, Baba Magaji yayi sannan yace mishi.
"Dole idan za a raba ta dasu, zai zama tashin hankali, domin tana faffutikar ganin ka samu kome naka, ita kuma suna kokarin ganin ta koma musu, matukar aka bar ganuwar nan dole zata bisu, idan kuma aka rushe zata rayuwa sai dai zata nakasa, dan ba lallai bane tayi lafiya kamar da."

"A'a bana son ko daya, kawai ta zauna dani yafiye min Alkhairin akan ta tafi tabarni don Allah karku raba mu." Ya fada a sanyayye.

"Jalaludeen! Kuje ku dawo, amma kai da kanka zaka bukaci haka, domin tayi nisa a mu'amala dasu, tunda tana iya sawa ayi hukunci a can fadar Ziryana."

"Taya haka ya faru?" Ya faɗa bakin shi yana rawa.
"Ta sakacin ku da ambaton Allah! Gidanku ya zama kango, kowa yana rayuwa a inda yake, babu kome. Har gwara ita, tana mai da hankali akan ibada, shi yasa wancan mutanen basu yi tasirin juya tunanin ta ba, amma da sunyi nasarar tafiya da tunanin ta zuwa ga duniya, zai yi wuya ta iya fahimtar kome akan su.

... Kana tare da ita sai da na gaya maka, karka bari wani alamun ciki ya bayyana a tare da ita, shine kayi wannan kuskuren, har kake tuninanin dakatar dasu, ba zai yiwu ba, sabida ta rigada ta amshi kambun su, kuma abu me wuya kenan, rabata da wannan kambun, cikin ruwan sanyi. Kuje da ita Maiduguri idan kun dawo kazo mu san me zamu yi, karka manta ka dawo nan da wasu kwanaki uku, karka yarda ka wuce haka, sannan itama sayare ka dawo da ita, cikin gidan ku. Kun dai ji....kuyi hakuri don Allah har yanzun sai a hankali 🤦🏽‍♀?
10/23/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: *_Daminan bana ba irin ta Bara bace._*

"Da yafi maka!" Har ya juya zai tafi ya dawo da baya, cikin jin haushi riko hannuna zai yi nayi maza na dakatar da shi.
"Karka tab'a ni!"

"Kee wai meye nayi miki ne da zafi? Na lura haushina kike ji!" Juya mishi baya nayi na cigaba da abin da nake, haka ya karaci tsayuwar shi ya bar dakin.

A hankali kome ke tafiya, Jay kuwa, idan zai fita nakan ce mishi, ka dai dage da addu'a, kawai. Idan na fadi haka mamaki yake ji, sai ya tafi zai kuma turo min sako ga abin da yake faruwa a cikin fada Habu da kan shi ya gaya musu shi ya kashe

Please Login or Register in order to submit comment