Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duba ni.

   Har  na cika kwana sha biyar, da dauri, shi yazo ya kawo ni aka warware min suka duba ya had'e kashin.  Daga nan na tako har ajin mu, Barka yan ajin suka min, nayi godiya dake duk zaman da nayi, a gidan nan shi a banza ba.

Muna karatu musamman Ni da bana makarantar, ta online Class.

             ......  Hango d'an iskan yaron nan nayi, yana ajiye motar shi, addu'a nake Allah yasa nazo da wani abu me tsini, duba jakar nayi naga babu wani abu me tsine, har zan rufe sai naga ashe akwai yar roban kayan karafunan lissafi, budewa nayi na dauki Abinda zan dauka ina murna, ina maida jakar agogona yana faduwa kasa, dauka nayi dai-dai fitar malamin na fita da sauri ina gyara zaman agogona, ashe bai zauna ba, da sauri nake sauka, na shiga ts tsakanin motocin da suke gurin, ina zuwa gurin motar shi, na kace tayar gaba.

      Take yayi wani fitar da iska, na kuma komawa gefe na cake tayar gefen, ina gamawa na juya zan tafi, muka yi tawo mu gama dashi, karfen da agogona suka zube na juya da sauri na bar gurin, zuciyata na wata irin bugawa, na tsoro. Bai fahimci abinda nayi mishi ba, sai dai ya dauke karfen da agogona yana juyawa, cike da mamaki.

                       Ganin motar ya sauka kasa ce yasa shi fahimtar, abinda na aikata mishi daukar agogon yayi ya saka a cikin aljuhun shi, tare da dukar motar da hannun shi, ran shi na kara b'aci.

Idan dalibai suka san abinda ya faru da shi, tabbas zasu mishi dariya, dan haka. A fusace ya nufi ajin mu.

     Tunda ya shigo naga yadda idanun shi, suka kad'a jajjur har jini na kwantawa akai ya sani kauda kaina cikin tsoro. Ina shiga ajin naga babu agogona, kafin nayi wani yunkuri na hango shi yana tawowa.

  A hankali yake takowa har zuwa inda nake, ya dafa hannun shi akan tabirin da nake yace.
"Kin shirya?!"
Banza nayi da shi, kawai yasa kai zai fita, kawai yace.
"Toh bismillah!"
          Daga haka ya fita, ban damu ba, kawai dai naji a raina bai da mutunci kuma zai iya kuma min abinda yayi ranar, shi yasa da aka tashi nazo fita na kiyayye fita da sauri.

     Duk yadda nasaka rai zai min abu bayi ba, sai ma shirin da muke da Hikmi, take rashin ya kuma b'aci, dan haka ya shiga hada mana abinda zai rabamu.

      ..... Bayan sati biyu.
Na fito da sauri zan, isa inda muke haduwa da Hikmi domin yaron yana da ilimi sosai, sai naga baya gurin, dan haka na juya zan koma aji. Kawai naji yan mata suna ta min dariya ban damu ba, sai da wata tace min.
"Amma gaskiya kina da jiki me kyau."

Kallonta nayi, dariya suka saka sannan ta mika min wayar hannunta, tare da sanya min magudanar kallon, a hankali ya fara tafiya, Hotona ne gani a gaban wani Bature yana shafa jikina, a tsorace na sake wayar ya fadi kasa.

       Ji nayi kamar bazan iya daukar kaina ba, na zube kamar danyen nama a kan ciyawar da take gurin, kuka yaki zuwa min, kawai na mike ban tsaya ba, sai a filin da suke buga kwallon kwando, basa gurin suna cikin makaranta dake guda biyu ne, ina shiga gurin na same su da Hikmi, sai fada suke shida Abeel babban shaidanun yana zaune. Asood da Bilal suna raba su, ina zuwa na same shi yana fadin.
"Idan yar uwanka aka tozarta zaku ji dadi? Insha Allah sai kunyi dana sanin abinda kuka aikata, haba don Allah."

     "Muje Hikmi! Na Barsu da Allah."

          Juyawar da zanyi naga abu ya fado daga aljuhun wandon shi, kallon abin nayi da ido, naga an rubuta,(Golder ring condom) wani irin kuka ne ya kwace min, lokacin da na fahimci, sun rufe kofar da na biyo, shi kuma sun saka shi a tsakiyar su suna mishi dariya.
"Ai mun gode maka, gashi nan ta yarda da kai, kai kuma kayi sanadin kawo mana ita. Jay gaya mana ya zamu yi da ita?;"

        "Ku barsu su tafi!"

Saukowa yayi sannan ya tako zuwa gabana, yana kallon yadda nake kuka me mugun ciwo, ya amshi jakata ya ciro wayata, ya mika min yana murmushi yace.
"Ya kika ga wasan? Hmm" daga haka ya juya ya fita, raina ya b'aci dan haka na fita da sauri,  ina isa inda ya ajiye motar shi na dauki wata sandar da naga ni na buga a jikin gilashin motar sai da ta fashe.

          Bai kalle ni ba, na tsaya a gaban shi, ina mishi kallon kaskanci.
"Idan ka fasa daukata tsirara ka rena Iyayen ka, banza wanda bai san darajar mutane ba, wawan Yaro kawai kai har ka isa ka tozartani? Wallahi baka isa ba, kuma ni da kai shege ka fasa."

     Daga nan na wuce abuna, tun daga ranar bamu kuma, yin wata rigima ba, dan hoton ya zaga makarantar mu.

   Har takai malamai sun min caaa, aka kirani zuwa ofishin shugaban makarantar, koda na shiga na same su. Kallona suka yi na sanan suka shiga tambayana, abinda ya faru.

Ban boye musu ba, Jay da abokan shi suka min haka, sannan Ni ba jikina bane fuskata aka dauka, dan haka suka kira Jay, ai kuwa yana zuwa, ya tsaya suna tambayar shi, yace shi yayi kuma bashi bane Abeel ne, kallon shi Mahaifin shi yayi cikin damuwa dan yasan zasu dakatar dashi na kwanaki ne.
. Aikuwa haka ce ta faru aka bani hakuri na fita, bayan na tafiya suka mishi fada sosai.

     ...... Wata guda suka dakatar dashi, amma yana karatun shi, a (online) haka da ya faru ya dawo min da kimata, dan haka na fita hanyar kowa, shima kuma Hikmi na rabu dashi dama shige min yayi muke karatu tare.

            ......
Na mai da hankalina sosai kai karatu, dan haka koda ya dawo, bana shiga harkan kowa, sai dai wannan karon ya dawo da zafi ne.

    Abinda ya fara min, shine sanyawa malamai suna hanani shiga ajin su, karshe na kuma zuwa gaban mahaifin shi, aka shiga tsakanin mu, amma bai hakura ba.
..... Haka zasu saka hotona, suyi b'atanci akaina, ban kuma magana ba, sai ma kauda kan da nayi, abin yana damuwa.

         Watanni uku muka fara jarabawar zango na farko, aikuwa zance Alhamdulillah. Sai dai ranar da zamu gama jarabawa aka wurgo min, da takardan satan amsa, kawai akan idanun me kula da jarabawar.

    Duk yadda naso dakatar da kar a soke min jarabWata, sai da aka yi, nayi kuka kamar idanuna zai fita. Shi kan sa da yaga yadda na rikice ina basu hakuri sai da jikin shi yayi mugun sanyi, zuwa gaban shi nayi nace mishi.

"Hankalinka ya kwanta? Ka rama abinda nayi maka, toh nagode sosai, amma ka sani wallahi sai na rama."

          Daga haka nayi wuccewa ta, zan koma gida, Hikmi ya biyo ni.
"Khatoon! Insha Allah bazasu soke miki jarabawarki ba, kiyi hakuri na dame su, kuma anyi abinda ya dace. Ga abubuwan ki da suka kwace, don Allah karki lukace Jay wallahi sanya shi suke"

    "Ai shi ba mahaukaci bane! Yasan me yake yi, dan haka yaje yà cigaba da cewa yake yi."

Raina ya sosu, shi yasa amshi kayana, na nufi gida. Koda za ayi hutun kin zuwa nayi, suka gama shirya min mugunta suka ga banzo ba.

     ....... Hutun sati Uku aka bamu, koda muka koma, naja girma na, sosai. Na kuma kin shiga harkokin kowa sai na karatuna.

           Lokacin da muka dawo mun kuma maida hankali sosai gurin karatu kasancewar, wannan lokacin akwai abubuwa da yawa, shi yasa muka mai da hankali sosai, ranar mun fita dakin gwajin kimiyya, muka hadu dasu Hikmi tare zamu yi dasu.

     Ban san ya akayi ba, dai ji nayi an tab'a bayana, ga kuma Jay a gefena fuskar shi a hade, kawai ina juyawa na kifa mishi mari.....
#MI
#HWA
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

TAKWAS

Daukar marin dakin yayi, shi kan shi a firgice ya kalle ni, cikin mamaki da al'ajabi, na mare shi, yadda kowa ya juya ana jiran aji abinda zai ce ko zance na bude baki zanyi magana yace.
"Dalla ki min shiru, na gaya miki dole ne?

Ki rabu dani kinki? Toh ya zan baki mamaki."

...sake baki nayi ina kallon shi, ya fincikoni muka fita, can inda ake ajiye aladun da ake gwajin kimiyya dasu ya kai ni cikin turb'ayan su ya jefa ni cikin su, wani irin tashin hankalin na tsinci kaina a ciki.
Ya kasa magana sai huci yake, sannan ya juya ya barni a gurin,  da sauri Hikmi yazo ya rasa me zai min, inda ake ajiye mesan makaranta na gudun karta Kwana ya dauko tare da bude ruwan, da yazo da karfi yana watsa min.

      Sunkuyar da kaina nayi, cikin bakin ciki da damuwa, wannan shine karo na biyu da aka watsa ni cikin kazamtar dabbobi. Dole na dakatar da haka kar a kuma yin na uku.

            Kayana ya jike jagab, a hankali nake takawa, duk inda na gifta sai an bini da ido, sabida kyan surar jikina, tare da zubin halittar da Allah yayi min, dayawan mutane da suke ganin na cikin dogayen riguna, sun sauka rigar ce take rufa min asiri, basu san nice nake son boye baiwar da Allah yayi min ba,

            Mika min Wata babban rigar sanyi Hikmi yayi na amsa, hawaye na zubo min, na rufe jikina saboda irin kallon da kowa ke min.

      Karshe shi ya kawo ni gida, har zan sauka yace min.
"Khatoon! Don Allah kiyi hakuri! Wallahi bashit bane, Asood ne yayi miki hak5ra, amma ko Alkur'ani aka bani zan dafa! Jay bai da dabi'un tab'a  mata. Mace bata cikin rayuwar shi,

       Kuma da zaki bi, duk abinda yake miki zaki samu ba wai dan ke dashi bane, abokan shi yake tsayawa,

             Kiyi hakuri! Abin da zance domin nasan waye Jay meye dabi'ar shi, Allah ya baki hakuri."

Share kwalla da suke tsiyaya a idanuna nayi, sannan na juya na kalle kofar fita nace mishi.

"Ni ba yarinya bace! Ƙaddarar rayuwa ya kawo ni nan, badan na rasa mazajena ba, babu abinda zai kawo ni, kuma na fahimci yarinta yana samun shi. Shi yasa yake min abinda ya gadama, amma ba damuwa na barshi ya cigaba da abinda yake min."

   "Kayi hakuri mana, a duniya Jay ya tsani a tozarta shi a cikin mutane! Kinga kenan ba laifin shi bane, dan ya wurgaki cikin datti, ki fahimci wani abu daya, shi kimar shi yake karewa. Da ki tab'a mishi kimar shi a gaban mutane gwara ki mishi kome a bayan idanun mutane."

                 Sauka nayi a motar kawai, sabida raina zai cigaba da ɓaci ne a banzan.

..... Karshe haka Hikmi ya tafi tunda baki fahimtar kome.

          A makarantar ma, karshe d'aga abin da zamu yi aka yi sannan aka raba mana kwanakin da zamu yi.

                 ----
A hankali rayuwa take tafiya ban kuma shiga harkokin yaran ba. Na zuba musu ido, ina kallon futsarar da suke aikatawa. Kuma ba a tab'a taka musu birki ba.

       A dan rigimar da muka yi da shi na fahimci yana da mugun naci,karku ce nacin da zaka kyale abu a'a na shi kamar halitta ce.

          Sai dai samun lafiyata shine rabuwa da nayi da rigima dashi, ita ta sama min nutsuwa na mai da hankali akan abin da, yake hada mu.

     ......
Ban san me ya faru ba, ranar na shigo makarantar, kawai d'aya daga cikin abokan shi ya tare ni, tare da kewaya ni, da keken shi. Shi kuma yana can  ajin su, daga can yake kallon mu, zan wuce yaron yasha gabana.

    "Bana son fitina! Ka bani hanya na wuce!"

          Wuce shi nayi, tare da barin shi a gurin dan yana amsa Waya ce.
          Ban kuma haduwa da irin haka ba, sai dai tsakanina da Jay, rigimar mu ta zafaffa, domin sun bani haushi na kai ƙarar su gurin shugaban makarantar, haka yayi masifar b'ata mishi rai, da zan koma gida yabi motar da na hau, ya tsayar damu, tare da bude kofar ya fidda ni, da karfin tsiya.

    Ya mai dani cikin motar shi, sannan yaja da gudu muka bar titin.

"Dalla malam ka sauke ni! Wallahi idan baka rabu dani ba, sai na maka abinda baka zata ba."

       Bai kula ni ba, sai dai ya kai ni,can wata tsohuwar makabarta, ya fito tare da fincikoni waje, ya wurga a can gefe.

Kasa magana yayi yana motar shi ya barni a gurin, mik'ewa nayi na bar gurin dakyar na sami abin hawan da zai  mai dani gida.

      ---
Washi gari!
Ina shiga makarantar, na fasa mishi tayar motar shi na bar gurin, yana zuwa ya gani ina zaune ya shigo zai min hauka Malamin da yake ajin ya kore shi, har zai fita muka kalli juna gwalo nayi mishi,  juyawa yayi tare da dukar Kofar sai da na razana.

      Murmushin ban haushi na mishi, tun daga ranar malamin ya saka aka shiga tsakanin mu, domin na gaya mishi irin abinda yake min, aikuwa malamai da dama sunki bada goyan baya sai daga baya, ni kuma nayi amfani da wannan damar, nayi ta mishi tsiya iri iri, wanda ya sashi kasa hakuri ya fito da halin shi yana hauka a makarantar.

     Sau biyu ana dakatar dashi a kaina, na uku ne suka ce mishi Tabbas koran shi zasu yi, abinda ya masifar d'aga mishi hankali kenan, kawai ya zubda hawayen bakin ciki.

     ----
Shekara daya muna wannan yanayin, kawai ina cikin makarantar su Baabi suka zo, kai murna kaman zanyi kuka.

    Tunda na fito nake fad'adda murmushina, suna zaune nazo na wuce su. Ina zuwa na rungume Baabi tare da kanena, ina murmushi.
" Addah Aanih! Kinga yadda kika koma kuwa! Su Ummi na gida kizo muje."

    "Kai Hanisah yanzun zan dawo, muna karatu ne! Baabina ina kewarki, kuje zan dawo yanzun nan!"

     Shigowar sako a wayata ya sani, duba wayar.
   
          *_Ya zaki ji idan na sakewa wannan tsohon vedion nan ki duba na turo miki ta Whatsp_*

     A tsorace na duba vedion bayan na koma gefe, hoton b'atanci be suka yi min, d'ago kai na nayi, tare da kafe shi da ido.

      Sako ne ya kuma shigowa,
*_Karki damu zan zo na rungume ki a gaban shi haka zai fi sauki_*

    A birkice na tura mishi.
*_Toh me zan maka?!_*

      _Dukkan mu abu daya muke son karewa kimar mu! Dan haka kika sake yau kika zauna a cikin mutane zan baki mamaki ki tawo inda nake ajiye motana._

     _Me zaka min da zanzo_

_Abin da mace da namiji suke idan sun hadu mana_

      _Tir_
Raka su Baabi nayi, sannan na dawo aji.
   Bayan mun gama darasi ya kuma turo min sakon.
_Idan baki zo ba!_

_Ka kashe ni!"
Ko a gidan Uban waye ya sami Number ta, hankalina yana gida, tunda na shiga na manta da kome na kashe wayar baki daya.

    Tunda muka fita da kanena muke yawo, muyi ciye ciye. Da wasu abubuwan dan washi gari zasu koma.

        Wata Mall muka shiga muna sayayya, naji kamar ana kallona, juyawa nayi kawai idanuna ya sauka akan nashi, tsaki nayi tare da cigaba da abinda nake yi.

    Har zai tafi kawai ya tako har gefena, tare da ɗaukar wani, kwalin pant, ya bude sannan ya zazzage shi.
"Ina kallon mace kamar yadda nake!"
    Barin gurin shi nayi da sauri, haka ya zame min kamar karfen.

     Cigaba da abinda ya kawo mu, shagon nayi har Hanisah tana min tsiya wai kamar ban waye ba, gani cikin turawa amma ina gidadancin irinta mutanen da.

Murmushi nayi, tare da kai hannuna zan dauki kwalbar turare naji hannun shi akan nawa, a razane na cire tare da yarfe hannun, kamar na tab'a wuta.
Kafin na juya har ya bar gurin mu, sako ya turo min.
_Kamar yadda kika shirya fada dani haka nima sai shirya yadda zan lalata miki suna da hujjar ki!_

    Na rasa yadda zanyi da Jay, domin ya dauki marin da nayi mishi da girma, dan haka a cikin satin kamar nayi hauka, domin burin shi ya haɗa ni da iyayena, Ni kuma nak'i biye mishi har suka tafi.

               Sau uku yana hada min rikici, a makarantar Allah yana fidda Ni, na karshe ne ya hada min rikicin da aka kusan korana a makarantar, domin sai da Abban Ablah yaje makarantar. naji mugun tsoro.

   ...sannan ya kuma sanya aka sani na bashi hakuri a gaban kowa da kowa, na yarda Jay fitinanne ne,.tun daga ranar Allah ya zuba min shakkar shi bawai dan yafi karfina ko yafi karfin Ubangiji ba, sai dai gaba ki daya, takardana nake tsoron kar yaja min sanadiyyar da zasu kore ni.

       Babu ranar da zan shiga makarantar, ban dawo da bakin cikin Jay ba. Sai da ta kai ina tanka mishi muna fada sosai, mutumin da baya magana sai gashi sosai yake iya jin haushin idan na gaya mishi magana, musamman da nake ce mishi Gata tayi kishi yawa, shi yasa yake abinda ya gadama, kuma bai yi dace iyaye na gari ba.

       Gashi ni da na dace da iyayen kwarai, burina na gama dasu lafiya. Wannan lokacin kamar yayi hauka, karshe aka gayawa Kanwar shi, ban san tana cikin makarantar.ba, sai ranar ina, karatu a kasar bishiya tazo.

   "Ke! Naji ance kece kike bibiyar dan uwana toh ahir dinki, wallahi na kuma ganin ki dashi, sai na ɓatar dake."

..."ina da abinyi idan kin gama zan wuce! Idan kuma baki gama ba, zan tsaya ko gama."

      ---- Bayan shekara daya
Abin haushi haka zan ga Jay suna tsokanata bani da ikon ramawa, kawai muna cikin wannan yanayin ne, wasu da ba san suwaye ba, ba suka yiwa wata yarinya fyade. Tashin hankali garin bincike tace har dashi.

              Abin ya faru bayan mun tashi mun fita,. ita kuma tana matakin degree, an fita an barta a cikin aji, tana wasu abubuwan ta, tana d'agowa tagansu..shine suka afka mata abin tausayi suka lalata rayuwarta baki daya, sakamakon kiran sunan Jay aka dakatar dashi, inda aka shiga bincike.

     Muna tsaka da karatu, aka mishi wannan abin bai bani tausayi ba, sai ma murmushi da nayi dan haka yayi min kyau da dad'i, kamar zai yi hauka..dan haka ya sa aka kira mishi Abeel, aka shiga tambayar shi, dakyar ya bude baki yayi magana tare da gaya musu gaskiya,, shi da Asood ne, suka yi haka tare da wasu abokan shi.

         Dan haka yan sanda suka tafi da shi,ba tare da sun kuma jin ta bakin shi ba.
#MI
#HWA
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:50 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

TARA.

   Wannan abin da ya faru ya sanya shi,. shiga hankalin shi da mutane, karshe dai ya rasa inda zai huce fushinsa sai a kaina, ban damu ba. Sabida Ni nasan abin da nake shirya mishi.

.......... Muniba ta kan zo har gabana ta fessa min rashin mutunci,bata gabana balle ya dame ni, sabida kusan sa'ar kanina Abdul ne.

.... Dan ko ina tsammani Hanisah ta girmeta. Muna gab kammala karatun, muka hadu da Dr Hanash Maisara, kamar da wasa muka fara gaisawa,

     Dukda shi din dan kasar Pakistan ne, amma yana da matukar mutuncin, da sani ya kamata.

    .. sosai muke dasawa dashi, a hankali d'asawar ya koma soyayya,.tun daga ranar da ya rufta yana sona.

...na shiga mugun mafarki akan shi, abinda ya sani. Amma a hakan ban fasa jin shi a raina ba.

....."Fatimah Khatoon! Har yanzun baki bani damar nayi magana da iyayen ki ba."

      Ya kafe ni da idanun shi, manyan nan, kasa nayi da kaina, sannan na d'ago zan yi mishi magana sako ya shigo min.
      _Lallai! Toh kin zata fadar mu ya kare ne? Bari nazo na kori wannan farin fatar da yake rud'arki_

....a hankali na d'ago kaina na sauke shi a kan shi, yana shan coffee. Takaicin shi ne ya kamani, ina kallon shi ya mike ya bar gurin,

         Bayan tafiyar shi, muka cigaba da hirar mu, dan ni wallahi na manta da shi.

      ....
Shakuwar da muka yi, tayi Yawwa, domin ba karamin burge kowa muke ba, kwatsam muka fara karatun yamma, idan na shigo makarantar sai dare nake fita.

         Bani daya ba, hatta sauran daliban haka muke, yau mun taso ana ruwa, dan haka na fito da sauri. Dan lungun da ban san dashi ba, kawai naji an fincikoni tare da toshe min bakina, ya saka hannun shi a bakin shi.
"Shiii!"

         A tsorace ya zuba mishi ido, kawai sai ga su Asood, da gudu suna nima na, kamar zasu yi hauka, ashe sun zauna sun tsara yadda zasu min rashin mutunci ne, shi kuma yazo ya tare ni.

      Matse ni yayi ko nace, mun matsu a lungun gashi ruwa hana jika mu, kuma zan iya cewa jikina da nashi yayi matukar haɗuwa a guri guda, a hankali na janye daga jikin shi na koma gefe, bayan tafiyar su muka fito.

   Motar shi ya kaini, na mishi wani mugun kallo na nufi bakin hanya.

Ina fita cikin makarantar na tsaya ina jiran motar haya, zuwa yayi ya tare da tsayawa a gaba na.

    Sauke gilashin motar yayi,  tare da bude motar na kauda kaina tare da tare wani motar, shi kan shi, ya sha mamaki na, yadda naki shiga motar shi. Bayan taimakona yake son yayi.

    Daga Ni har shi babu wanda yake jin a ran shi zai iyawa wani magana. Sabida kowa ji da kan shi yake.

        Rufe kofar yayi tare da cilla kan motar shi zuwa gida.

          ---
Da sauri na fito, zan wuce Muniba ta tsare ni, Yarinyar Bata da kunya, ko nace bata jin magana, gata masifaffiya ce, kowa yasan halin ta, ashe ta bakin fita makarantar, Jay na murnan zagayowar shekarar Haihuwar shine shima, ina zuwa hango Cake din da aka yi shi da wasu abubuwan masu kyau an rubuta 27. Murmushi nayi, dan na fahimci da yarinta akan shi muka yi ta abin kunya.

  Wuce su nayi, har na kusan fita wata yarinya kawar Munih tace.
"Kee! Zo mu Baki cake Dan yay murna muke."

Ban bi ta kansu ba, na cigaba da abinda yake gabana

           ----
Tun daga wannan ranar, ya daina shiga hidima ta, nima kuma ban damu dashi ba.

         Yawan mafarkan da nake da Dr Hanash ya sani rabuwa dashi babu shiri.

Na mai da hankali na, kan karatun da ya kawo ni, tare da taimakon Hikmi na samu damar sanin abinda Jay baya so.

    A shekara na biyu, Baabi ya kawo min magani daga gida, yace na fara amfani dashi anyi min miji, sam Banji daɗin haka ba, amma kuma babu abinda zan iya mishi.

  Bayan tafiyar shi nayi amfani da maganin kuma naji dadin shi. Bayan wata shida da tafiyar shi.

     Sai ga Ikrama, tunda

Please Login or Register in order to submit comment