Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana qare masa kallo ta cikin glass dinta,sai daya kashe redion sannan yace
"Me ya sameta?"yarfar da hannu tayi cikin yauqi
"toh wlh ban sani ba,ina cikin driving ta soma slow sai kuma ta tsaya gaba daya" dan jim yayi kafin ya jinjina kai ya fito daga motar ya rufeta sannan yayi gaba zuwa inda motar tata take.

Tsahon wani lokaci yana qoqarin ganin ya gyara saita tashi saita sake mutuwa,saboda haka ya dago yana goge hannunsa da tsumma
"Gaskiya dole sai bakanike yazo"ya fadiwa nafisa dake gefe tsaye suna qare masa kallo ita da qawarta mima
"Ya salam...bari na kirashi Allah yasa yana kusa" ta ciro tsadaddar wayarta ta soma nemanshi,cikin sa'a yace yana kusa ta bashi adress din inda motar take
"Idan ba damuwa ko zamu dan zauna cikin motarka kafin ya iso saboda zama a wajen ba dadi" nafisa ta fada sanda anwar ke komawa zuwa cikin tashi motar,tsayawa yayi ya waiwayo,kaman yace a'ah sai yaga mata ne bai kamata ya barsu tsaye ba,tunda motar tasu ba zasu iya zama cikinta ba,shi kuwa diya mace ako ina take yana da kishi da qoqarin kare mutunci da martabarta bakin gwargwado koda bai santa ba
"Ba damuwa" ya fada yana sake yin gaba,idanu suka hada da mima ta kashe mata ido gami da sakin murmushi suka bi bayansa.

Ya tsammaci duka baya zasu shiga,sai yaga mima ce kawai ta shiga bayan,nafisa ta shiga kujera mai zaman banza,sai data zauna sosai sannan ta waiwayo ta dubeshi tana murmushi
"Suna na nafisa....kaifa?"
"Muhammad anwar" ya bata amsa a taqaice,idanu ta lumshe
"Nice name...sunan ya dace da maishi" saiya waiwayo ya dubeta kafin ya dauke kai,murmushi ta sake saki
"Dan wanne anguwa ne kai?,Allah yasa ban matsanta maka ba da tambaya" kai ya jinjina sannan ya gaya mata unguwar da yake
"Kai ai bamu da nisa sosai" itama tasu unguwar ta fada masa,kusan duk unguwannin nasu maqotan juna ne,shuru ne ya sake ratsa tsakani yayin data lula duniyar tunanin yadda zata sha kan anwar,don ba zata cuci kanta ba kallon farko taji anwar yayi mata,infact ma zata iya cewa ta kamu da sonshi ne kai tsaye.

Isowar mechanic din shi ya katse duk wani tunaninta,hanya daya ta rage mata saboda haka ta miqa mishi wayarta
"Idan ba zaka damu ba ka sakamin numberka mana,saboda nayi maka godiya" kai ya girgiza
"Basai kinmin godiyar komai ba" kai ta langabe
"Ya zama dole na gode maka,saboda alkhairi kayi min" baison jan zancan saboda ya gaji da surutunta,saboda haka ya amshi wayar daidai sanda shahida ke takowa zuwa inda motar take,tana iya hango komai saboda akwai haske cikin motar,mummunar faduwar gaba ta samu,saidai ta kasa hana kanta qarasawa wajen,saitaci gaba da takawa harta isa bakin motar,daidai sanda ya gama saka mata number din ta amsa tana murmushi tace
"Na gode,sai gani na gaba" ja baya shahida tayi a hankali sanda nafisa ke fitowa daga gaban motar,idanunsu suka hadu dana juna,kallon kallon suka yiwa juna kafin nafisan tayi gaba mima ta rufa mata baya,binsu shahida tayi da kallo har suka bacewa ganinta cikin duhuwar wajen sannan ta dawo da dubanta ga anwar wanda sai sannan ya lura da tsaiwarta a wajen.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽


https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos




*Alqawarin Allah*
1️⃣1️⃣


"Wacece?,me takeyi a nan wajen?" Ta tambaya tana daga tsaye ba tare data shigo cikin motar ba
"Motarsu ce ta lalace nayi qoqarin gyara musu,bata ma gyarun ba sai data kira bakinikensu"
"Shine tazo kusa da kai ta zauna?,har kana amsar wayarta tana jifanka da murmushi?"
"Shigo tukunna sai muyi maganar" ya fadi yana bude mata murfin motar sosai,kaita girgixa sai kawai ta juya tabar wajen idanunta cike fal da qwalla,cikin hanzari ya fito don ya cimmata saidai ina tuni ta kutsa cikin mutane ta bace masa bat,haka ya qaraci nemanta bai ganta ba,dole ya dawo gaban motar ya dinga jera mata kira amma bata daga ba.

A hankali wajen ya soma yoyewa,ya sake shiga ya dubata amma kome kama da ita bai gani ba bare ita
"Ya salam shahida....ya salam" ya dinga furtawa a jejjere sanda yake tuqa motar zuwa hanyar gidansu amaryan,ba qaramin tashi hankalinsa yayi ba,bai samu 'yar nutsuwa ba sai daya isa gidan yasa aka shiga aka binciko masa aka tabbatar masa ta dawo gidan nan sannan ya saki ajiyar zuciya,nan kuma ya shiga jera aiken kiranta,saidai mirsis taqi zuwa,ganin dare ya soma yi ya sanyashi haqura kan tilas yaja motar yabar unguwar,bai je gida ba sai daya soma kaiwa abokinsa matar,yace daya barta ma sai sun gama bikin don tafiya ma zaiyi ta sati guda,murmushi ya saki wanda kusan na yaqe ne,donshi kusan sam baiji dadin hawa motar ba,yana ganin kaman itace silar faruwar komai,inda ace a motar haya suka tafi shikenan nafisa ba zata ganshi ba,da amotar haya suka tafi nafisa ba zata rabi wurinsa ba saidai wajen wani,don bashi da gurin da zata roqi alfarmar zama har shahida ta gansu tare,da a motar haya ne da tuni tare zasu dawo da shahidanshi su rabu cikin farinciki sa walwala.

Ta gefan shahida kuwa hankalinta a tashe,gani take kaman za'ayi mata qwacen anwar din,duk kwanan duniya idan ta kalli anwar din sai taji fargaba ta cikata,anwar nada kyau kwarjini da cikar zatin da zai zama abun kwadayin mallakar kowacce mace,kallo daya ta yiwa nafisa ta tabbatar 'yar masu dashi ce,idan hakan yayi nasarar janye hankalin anwar fa tayi yaya?,da sauri ta kori wannan tunanin daga ranta,don fatan dorewar hakan,a ranar da qyar ta sami bacci duk da wayarta na silent tana da yaqinin ta tara miscal na anwar din.

Itama kusan tubure masa tayi yadda ya mata kwanaki,qarshe dai saida suka dangana da anty amina tayi sasanci kamar yadda ta saba,zuwa lokacin ba qaramin jigata yayi ba,wanda hakan ya faranta ran shahida ta wani gefe,tunda ko babu komai ta sake sanin mizanin da zata dora soyayyar da yake matan.

A haka rayuwar wannan masoya take ta kuma ci gaba da gudana,kowanne cike yake da tsananin so qauna da kuma kishin dan uwanshi,kowannensu cike yake da buri da fatan farantawa dan uwanshi,har zuwa sanda shahida suka soma shirye shiryen yin candy,a boye ba tare da saninta ba don yasan zata iya hanashi anwar yasa akayi mata jaka da memo,yace bazaiyi calender ba bare wani qato ya rataye a dakinsa ya dinga kalle masa mata,ko memo dinma babu hoto a jiki,yayi mata key walder hakanan ya soya kayan da zata saka ran walima complete,dukka yayi hakanne bada saninta ba don yanason mata suprise ne.

_*TAURARUWA MAI WUTSIYA*_



Tsaye take a hamshaqin falonta gaban window,wanda yaji komai da komai na kayan alatun more ruwa,falone dan qarami saidai ya wadatu da dukkan wani abun buqata domin hutawa da nutsuwar ruhi,tana sanye da riga da skert wanda iyakar skert din qaurinta
"Ina jinki mema....na zaqu naji daga gareki,wallahi tun ranar dana soma ganinshi har yau ban sake samun nutsuwa cikin rayuwata ba....duk iya qoqarina na ganin na samu zuciyarsa abun yaci tura,yana da wata izza kaman d'an wani,kwarjininsa shike sake dakusar dani,inajin sonshi ya kaimin ko ina cikin jiki da ruhina" tayi maganar duka tana tsaye jikin window din ba tare data juyo ba,idanunta na farfajiyar gidan data wadata da korayen tsirrai.

Tabe baki mima tayi,ita duka mamaki ya cikata,ta yadda feena ta fada qaunar talaka matsiyaci kaman anwar din,ta kuma fita hayyacinta lokaci guda,haka kawai tana tsaka da more rayuwarta,to amma ita nata yi mata aiki ta kuma biyata,indai zata biyata din ai shikenan
"Ba haka kawai kika kasa samo kanshi ba ai feena" meman wadda ke zaune kan daya daga cikin kujerun falon qafarta daya kan daya tana karkada takardar hannunta ta fada,da hanzari nafisa ta baro inda take ta qataso gaban feena sannan ta yiwa kanta mazauni kan wata kujerar daban tana duban feena idanu bude
"Kaman yaya?,meye dalili?" Wani shu'umin murmushi ta saka tana qiyasta kudin da zata tatsa wajen feena a yau sanadin wannan zazzafar jaridar da zata saida mata
"Zaki iya tuna yarinyar da kukayi kallon kallon da ita ranar da muka zauna motarshi" yatsanta manuni ta daga sama da sauri kaman maishirin bada amsa cikin aji
"Exactly....na tunata,tun ranar yarinyar na tsaye cikin raina...na rasa wacece mai shegen kyau da izza haka,da farko nayi tunanin qanwarsa ce saikima naga basuyi kama ba tako ina"
"Right....budurwarsa ce" gaban feena ya fadi ta zaro idanu
"Wait....da saura fa" mima ta fada tana dariya qasa qasa sannan ta gyara zamanta
"Idan kin taba karanta labarin soyayyar romio da Juliet wannan sun wuce haka,qauna ce irin wadda zata bawa bahaushen mutum mamaki,son junansu suke kaman tare aka haliccesu,daya baya komai saida shawarar daya,daya baya iya tafiyat da komai saida daya,bari dai na baki a taqaice a dunqule,sun narke sun zama abu daya...."
"Dole su rabu su zama abu biyu kuwa...na fahimta,wato saboda itane na kasa cimma burina kenan?" Ta tambayi mima kai tsaye,kai ta jinjina tana lumshe idanu sannan ta bude
"Qwarai kuwa....amma saidai karki damu akwai mafita" ta ambata tana warware takardar hannunta,daki daki ta soma karanta mata abinda shahida tafiso da wanda bataso har sai da nafisa ta gaji daji ta daga hannu tana dakatar da ita
"Jin wannan abun dame zai qare ni?,qara qonamin rai kikeson yi mima"
"Kina da gajen haquri inda matsalarki take kenan....amma tunda kina ganin haka shikenan bari na wuce" ta fada tana ninke takardarta,caraf ta kama hannunta
"Mtsweeww,banason ko jin sunanta ne wlh,zauna mu qarasa" bata wani jaa ba ta zauna din don tana lissafin abinda zata samu ne,taci gaba da karanto mata inda gabar qarshe take dauke da
"Ta tsani cin amana,ta tsani munafurci,ta tsani ta zauna dakai zuciya daya kai kuma ashe da zuciya biyu kake tare da ita" tana kaiwa nan ta daga kai tana duban shahida sannan taci gaba da karatunta,fagen anwar ta shiga,abinda yakeso da wanda bayaso inda shima tashi gabar qarshe ta zama
"Ya tsani mace mara kamun kai,ya tsani macen dake bin maza,sannan yayi masifar tsanar mace 'yar shaye shaye" ta sake yin shuru tana duban feena,dan jim tayi sannan ta gyada kai tana sakin murmushi sosai tana nuna mema
"Shegiya mima,sai yanzu na gane...ko shahidan yana tsoron kaidinki qarashe bayaninki" sosai taji dadin yadda take sake samun karbuwa wajen feena koda yaushe,ta ninke takardar sannan ta sake tattara nutsuwarta
"Yarinyar tana da ciwo tana da matsala cikin rayuwarta,duk da har yanzu ba'a gano wace damuwa gareta ba,amma zamuyi amfani da wannan damar mu sanyata ta zama 'yar maye,kinga mun samu matakin farko na rabasu,zai zama matakin farko ne saboda wanna kadai bai isa ya rabasu ba bayan bai kamata da wani laifi ba bayan wannan,itama bata kamashi ba,bayan ta zaba tantiriyar mashayiya zamu qara mata da sharrin bin maza...wannan kuma aikin wadanda suka san kan na'ura mai qwaqwalwa ne,zamu saka mata cewa baya sonta ita kuma yana tare da wata,duk zan kula da yadda komai zai kasance,naki kawai ki saki kudi ki zuba idanu" murmushin nasara ya subucewa feena,ji take kaman ta samu anwar ta gama,dukka kudin da yayi saura a jakarta ta zazzagewa mima,ta kuma yi mata alqawarin wasu
"Ya...zaki dinner dinsu mu'az dinne" idanu ta fiddo
"Me zai hana?,ai har na shirya qaryar da zanwa momy ta barni na fita,kedai jirani na shirya" cikin mintina qalilan ta fito cikin wasu matsiyatan riga da wando,hannunta riqe da burmemen hijab da take qoqarin sakawa mima na zaune na sheqa dariya,ta zuba duk kayan makeup dinta cikin haka ta maqaleta cikin hijabin sannan ta dubi mima
"Mu hadu a bakin gate,don da mun shiga tare ta ganki zata saka ayar tambaya" haka kuwa akayi,ta isa wajen momy ta shirya mata qarya ta yadda ba yadda za'ayi ta ganota sannan ta fice suka hadu da mima,tun a cikin motar ta cillar da hijabinta tahau tsara kwalliyarta yayin da mima ke driving.

Cikin nasara da taimakon ubangiji ta kammala rubuta jarabawarta kaf,wanda a ranar sukayi bankwana da dalibai da sauran malamai 'yan uwansu,a daren ranar anwar yayi shiga ta musamman yazo don tayata murna,ya kuma bata duk wani gift daya tanada saboda ita,sai data shiga dakinta tana dubawa abun ya sake burgeta,duk da anwar ba wani mai hali bane amma Allah ya hore masa tsari da iya siyayya,komai daya bata ya burgeta,ta jima tana kallon wani zobe,duk dana azurfane amma an qawatashi qwarai dole ya burgeka,zanen heart ne a jiki amma heart din rabi ne,murmushi ta saki tana sakashi cikin yatsunta,yayi masifar yi mata kyau,saita tattara kayan ta kaiwa ummanta wanda ita kanta ta yaba da qoqarinsa kaman yadda abbanta ya yaba,hakan ya mata dadi qwarai,ya kuma bata tabbacin kenan bata da matsala bata da wani shamaki da zai hanata mallakar anwar,tuna haka cikin jin dadi ya sanyata qanqame filon da take kai tana hango kanta da anwar dinta a matsayin ango da amarya qarqashin inuwa guda.

Cikin farinciki da walwala ta gabatar da walimarta,komai ya tafi lpy ya kuna qayatar sai jiran sakamako,a sannan komai na tafiyar mata lpy,rayuwar tana hangen nan gaba kadan zata yi mata kyau,komai zai qarasa dai daita musu,anwar ma an masa qarin albashi wanda hakan dukka su biyun ya musu dadi.


*SANADIYYA*

Ana tsaka da haka gagarumin tashin hankali da yayi sanadiyyar lalacewa komai,ya zama silar tabuwar rayuwar mutane da dama,yayi sanadin wargajewar wannan iyali,ya kuma silar tarwatsa rayuwar shahidan...ya zama wani sanadi na dasa baqinciki mai tarin daci da zafi a rayuwarta ta faru.

Rayuwa tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta rayuwa ce ta rashin haquri,dauke kai yafiya da juriya da akasan dukkan ma'aurata da yiwa junansu,fada gaban yaransu wannan ba wani sabon abu bane tun tasowar shahidan,wanda hakan ya sanya bayan girmanta abun ya zame mata wani ciwo da duk sanda ya taso mata yake mata zafi da quna a zuciya,dukkan wani mataki da take ganin ya dace ta dauka a matsayinta na diya mai qarancin iko da abun fada ta dauka harma wanda ya zarta huruminta amma babu abinda ya sauya,duk da alqawari da qoqarin sauyawar da suke.

Kwatsam dare guda mahaifinta ya jijjigo maganar qarin aure suna tsaka da rayuwarsu cikin rufin asirin Allah,wanda hakan ya sanya mahaifiyarta tayi tsalle ta dire tace batasan wannan zance ba,dalilin daya janyo tashin tashina da fadan da bata taba gani ya wanzu tsakaninsu ba,hakan ya sanya walwalarta da duk wani kuzari nata ya ragu,anwar ne mutum na farko dayafu kusanci da ita a sannan shiya soma gane tana cikin damuww,amma baisan dalili ba,taqi kuma sanar masa,ta yaya zata gaya masa wannan murdaddeb zance?,tun baya baisan halin da gidan nasu ke ciki ba saboda kare martaba da qimar iyayenta,duk sanda ta fuskanci akwai rashin jituwa tsakanin iyayen nata bata taba yin zance a gidansu,a gidan anty amina take zancanta,toko yanzu ma da lamarin gidan nasu ya lalace can take tafiya ya sameta anan,don ba zataso wataran wani mummunan abun ya faru a gabansa ba duk da yana musu kallon iyayensa amma asirin ciki sai hanji.



*MAFARI*


Cikin tashin hankalin da bata taba tsintar kanta a ciki ba ta fito daga gidan nasu tana hawaye,yau a gidansu a gaban idanunta ake doki in doka tsakanin ummanta da abbanta?,wanne irin iyaye gareta?,ya ilahi ji take kaman zuciyarta zata fashe,ji takae bugawa zuciyarta zatayi,ita kadai tasan yadda takeji tana jin kaman zuciyarta ta kumbura ne ta cika qirjinta,zataso ace zunnurah na nan saidai ina,gidan anty amina takeson zuwa amma babu ko nutsuwar daukan kudin mota a wajenta,ba tare da tuna nisa da tazarar dake tsakaninsu ba ta hau tafiya cikin fitar hayyaci da tashin hanakali bacin rai da baqinciki.

Dawowarta kenan daga inda taje ta sauka a abun hawa,tana yunqurjn shigowa layin nasu ta hangi kaman shahidan,tayi mamaki don shahidan bata taba zuwa gidansu ba,hakanan bata yowa layinsu don asalan ita bamai yawo bace,sauri ta qara donta cimmata,sai taga itace dince kuwa,amma a binda ya bata mamaki hawayen data gani shabe shabe a i fuskarta,hannu tasa ta kamota tana cewa
"Shahida,meye haka kuka kike fa akan hanya" sai a sannan ta kula da fiddausin,sake fashewa da kukan tayi,ita koma waye ta gani zata iya fada masa abinda ke damunta ko zataji sassauci a zuciyarta,abun ya mata yawa,wannan damuwar bata shekara daya bace ko biyu,ganin haka sai fiddausin ta janye shahidan zuwa gidansu,ta tura gate din gidan suka shige sannan suka nufi dakinta ta qofar baya,sau tari takan iya shigowa ba tare da an sani ba saboda gidan nada girma babu laifi.

Kuka take sosai tana cewa
"Na gaji fiddausi....na gaji da wannan bacin ran,ina zanje naji dadi,me zanyi na samu sassauci?" Murmushi fiddausin ta saki,duk da shahidan bata gaya mata damuwarta ba amma tana ganin sara ne yazo kan gaba
"Ina da maganin damuwa shahida,maganin da zai dauke duk wata damuwa da kike ciki komai qarfi da girmanta,zaki jiki fresh kaman yau aka haifeki,nauyi da zuciyarki keji ya sauka kaman bai taba faruwa ba" idanunta dake jiqe da hawaye ta daga tana kallon fiddausi
"Don girman Allah ki bani kona daina jin suyar da qirjina yakemin"
"Kwantar da hankalinki basai kin hadani da girman Allah ba" ta fada tana zuge jakar data shigo da ita,kwalabe ta fito dasu ta hada abubuwan ciki ta gauraya sannan ta miqawa shahida
"Daga kanki ki shanye nina daga wajen likita nake shi ya rubutamin shi yace maganin damuwa ne" ba tare da kowanne tunani yazo kanta ba,ba tare da tayi lissafin komai ba,ba tare da ta jinkirta ba ta daga kai ta shanye duka din kamar yadda fiddausin tace mata,cikin wasu qananun mintina ta soma jin dummm,ta soma ji kamar ana sauyata daga tata duniyar zuwa wata daban,ta soma daina gane komai,take a nan ta zube saman gadon fiddausin,lokaci qanqani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita,dariya fiddausin ta saki tana rufe kwalabenta tare da maidasu haka tana cewa
"WASA FARIN GIRKI YARINYA".


*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videoshttps://youtu.be/T9a10h1Apqs
👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽

*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899


*Alqawarin Allah*
1️⃣2️⃣


A hankali ta farka tana mutstsuka idanunta da taji sun mata nauyi,sam ta mance inda take saida tayi dan tunani sannan ta tuna,da hanzari ta tashi ta zauna ganin gari yayi duhu sabanin sanda suka shigo gidan akwai hasken rana,agogon bango ta kalla sai taga qarfe takwas,hakan yana nuna kenan ta rasa sallar la'asar magariba dama isha'i.

Da hanzari tayi nufin tashi saidai gaba daya jikinta a mace yake babu qwari,daidai lokacin da fiddausi ta shigo dakin dauke da plate din abinci,cikin murmushi take duban shahida
"Sannu kin tashi?,ya kike jin kanki yanzu fresh ko?" Eh to,lokacin da tayi baccin ta mance komai,saidai yanzu bayan ta farka komai ya sake dawo mata,saidai baccin da tayi din ya rage mata bacin rai kadan,amma duka ba wannan ba,sallolin data rasa lokacin da take bacci su sukafi damunta,saboda haka tace
"Banyi sallah uku ba fiddausi,nunan bandaki na daura alwala"ta fada tana jin babu dadi har cikin ranta,wannan wanne irin bacci ne?,bata taba irinsa ba,hakanan koda bata da lafiya bata taba hada salloli ba.

Qofa ta nuna mata wadda take cikin dakin gadon nata,nan shahida ta shiga ta daura alwala,ta fito sannu sannu saboda yadda takejin jikinta sam.babu qwari,gagara yin sallar tayi a tsaye saboda yadda takejin qafafunta kamar lagwani tilas ta zauna ta yita a zaune.

Tana gamawa ta miqe don hankalinta yayi gida kuma,don bata taba tsayawa a waje har wannan lokacin ba bata koma gidan ba
"Ki tsaya kici abinci saiki sake samun qarfin jikinki"
"A'ah fiddausi gwara na wuce gidan,ba wanda yasan inda naje"
"Shikenan....bari na baki wannan duk sanda kike cikin bacin rai kina sha zaki baccinki ki manta da kowa" sam a cikin ranta batajin zata sake sha,saboda bata taba bacci irin haka ba,bugu da qari ita babu wani raguwar bacin rai data ji,don kada ta gwasaleta kawai ta amsa
"Maganin damuwa ne,zaki samu relief,kin ganni nan,ko bacci ne yaqi daukata saboda wani bacin rai dana sha zanyi baccina hankali kwance" kai kawa i ta gyada,fiddausi ta rakota har qofar gida ta wuce ita kuma ta koma cikin saurin don ta labartawa mima komai da yadda abubuwa suka gudaba,sannan ra fara da turo mata kudin data alqawarta mata,don syrup dinta dama ya qare tana buqatar siyan wasu ta aje.

Tsakar gidan nasu babu wadatar hasje sosai kasancewar babu wutar nepa,bata nemi kowa ba don bacin rai ke sake taso mata na yadda tabar gidan nasu dazu,uwa uba kuma wani sabon baccin take ji,gqba daya jikibta jibsa take kaman an tsoma lagwani a ruwa.

Kan katifarra ta fada rub da ciki tana lumshe idanu tanajin yadda gabobinta sukayi rauni,idanun nata na arufe taji wayarta na ruri,sam baki daya ta mance da ita,ta miqe cikin kasala ta daukota daga saman akwatin kayanta,anwar ne yake kira,take ta dannan ta kara a kunneta
"Ina kika shiga haka shahida?,nazo gida ana nemanki sama da qasa ba'a ganki ba?,na kira wayarki ya kusa sau hamsin ba'a daga ba" sai data lumshe ido sannan tace
"Babu inda naje fa,ina gidansu fiddausi,wayar kuma na manta ta ne cikin akwatin kayana,koka kira babu lallai aji sautinta" ajiyar zuciya ya sauke yana jin tashun hankalin da yaji dazu na sauka
"Karki sake irin wannan fitar,hankalin umma ya tashi sosai"
"In sha Allahu" ta fada amma cikin zuciyarta tana fadin koma meye sune suka ja
"Ya naji muryarki haka?,lafiya kike?" Saidata gyara kwanciyarta saboda baccin dake fisgarta tace
"Lafiya qalau....kawai...bacci ne yakeson saceni"
"Bacci yau kuma?" Ya tambaya cikin mamaki,sabida yasan a qalla suna kaiwa sha daya suna waya,a hakama shike datsewa yace tayi bacci,sam bata iya baccin wuri ba
"Wallahi" ta fada a gajarce,saiya raya a ransa jiki da jinine kawai don haka yace
"Alright,asuba ta gari to,tunda yau anmin ruwa gani da jin muryarki" murmushi ta saki a kasalance tace masa na gode ta datse wayar ta cillar gefe tana maida kanta saman filo hadi da sake lumshe idanunta.

Mubina ce ta dago labulen dakin ta shigo
"Yaya kizo inji umma...ashe kin dawo tun dazu ake nemanki" juyar da kanta tayi daya side din cikin muryar jin bacci tace
"Saida safe...kice mata nayi bacci" yau ba 'yan maganar bane akan mubinan don haka ta fita ta shaidawa umman tasu saqon shahida,sai gata ra taso da kanta
"Ke shahida....ina kika je tun dazu?"
"Gidansu fiddausi" ta bata amsa ba tare data juyo fuskarta inda umman tata ke tsaye ba
"Tashi ki dauko abincinki a kitchen kici"
"Ba qoshi" ta sake fada cikin muryar bacci,sam umman tata bata lura da sauyin dake tattare da ita ba,ga tunaninta fushi tayi kaman yadda ra saba a duk sanda wani abu ya gilma tsakaninta da mahaifinta,saboda haka ta tabe baki
"Indai ba zaki sawa ranki haquru da kauda da kai ba zakita ganin bacin rai,kije ki hadu da hawan jini a banza,babanku baida haquri kuma baida adalci,ni kuwa bazan tsaya ya tauyen haqqina ba atoh" tana gama fada ta juya ta fice,sama sama take jin abinda umman ke cewa,ga mamakin kanta da kanta,maimakon ta sake jin haushi yadda ta saba sai taji sam maganganun basu d'a d'ata da qasa ba,baccinta ya fiye mata komai,idanu ta sake rintsewa ba jimawa kuwa wani nannuyan bacci ya kwasheta.

Kwana biyu tsakani suka ci gaba daga inda suka tsaya,a lokacin tana daki zaune tana turawa anwar tex,tun tana daure zuciyarta harta kasa,ta toshe kunneta duk a banza,takai ta kawo cikin dakin ita kadai saita fita,haquri ta soma basu tana kuka kowa idanunshi ya rufe ba wanda ya saurareta bare yayi shuru ya ragawa dan uwanshi,dare yaui ba damar ta fice daga gidan ta huta,sai kawai maganin da fiddausi ta

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment