Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta kuma sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta kafeta da idanu shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta
"Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina wayonki ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa anty zubaida qwarin gwiwa
"Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki sanshi ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce ke wadda batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki muhimmanci,kin rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda yayi silar kawoki duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga taitayinki!" A hankali ta soma girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma motsawa,mikin dake danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin dake tsakar gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce mata komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake fita,ta sani duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin radadin dake danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan ta dinga shafawa a hankali a hankali tana tayata jin radadin.

Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma rage sauti ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen ya sake raguwa
"Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba kanta na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da niyyar rage baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da anwar sannan ta dora da cewa
"Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu dashi zan mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin kukanta,kai anty zubaida take girgizawa
"Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani babban abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali irin kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki farinciki da walwala irin karatun qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa bashi da wani tasiri a gareshi,baya haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin damuwar,baya yaye damuwa ta har abada face ya sake sanyaka cikin wasu sabbin matsalolin,ya haifar maka da ciwuka masu kai d'an adam ga kushewa,Daga kai tayi ta dubi anty zubaidan maimakon yadda ta saba yi mata a baya duk sanda ta ganta,takan tashu cikin farinciki tana mata sannu da zuwa dama tambayarta yaushe ta iso,hadi da tambayarta su faruqu,a nutse anty zubaida itama take qare mata kallo bayan ta zauna dab da ita,cikin mintina qalilan ta gama karantarta
"Shahida" ta soma kiran sunanta a sanyaye,sake tada kai tayi ta dubeta saita sake saukewa,shawarar da zuciyarta ta bata tabbas itace mafita,dole ne saita fara tayar mata da mikin dake zuciyarta don da ala zuciyarta ta riga data daskare,dab take da rasa feelings,dole ta sata tayi kuka ta rage radadin da yake damun zuciyarta wannan shine hanya daya na farkar da zuciyar tata,dole ta sakata da kan kanta ta nuna akwai ciwo a zuciyarta wanda ta wannan hanyar ne kawai zata dawo da feelings da emotion dinta na fushi,sannan asan yadda gyara zai iya yiwuwa,tana son maida zuciyarta ne matacciya idan ba'ayi gaggawar gyarawa al'amarin ba
"Shahida!" Ta kirata wannan karon da mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta kuma sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta kafeta da idanu shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta
"Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina wayonki ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa anty zubaida qwarin gwiwa
"Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki sanshi ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce ke wadda batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki muhimmanci,kin rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda yayi silar kawoki duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga taitayinki!" A hankali ta soma girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma motsawa,mikin dake danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin dake tsakar gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce mata komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake fita,ta sani duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin radadin dake danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan ta dinga shafawa a hankali a hankali tana tayata jin radadin.

Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma rage sauti ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen ya sake raguwa
"Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba kanta na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da niyyar rage baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da anwar sannan ta dora da cewa
"Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu dashi zan mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin kukanta,kai anty zubaida take girgizawa
"Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani babban abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali irin kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki farinciki da walwala irin karatun qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa bashi da wani tasiri a gareshi,baya haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin damuwar,baya yaye damuwa ta har abada face ya sake sanyaka cikin wasu sabbin matsalolin,ya haifar maka da ciwuka masu kai d'an adam ga kushewa,Kana daukan cuta ne kana laftawa kanka,kana kashe kanka da kanka,Allah S W T da kansa yace kada ku kashe kawunanku,shan abun maye ba komai bane face kashe kai,don baka da maraba da mutumin daya dauki makami ya dabawa kansa,domin kuwa shaye shaye ba cutar da baya haifarwa,lalacewar qoda,lalacewar hanta,ciwon cancer,ciwon zuciya,yana nakasta hunhu,yana kuma lalata qwaqwalwa wanda hakan yake jagoranci zuwa ga haukacewa,dukka daya daga cikin wannan cututtuka idan aka bar mutum dasu sun isheshi azabar nan duniya,sun ishi mai hankali gujewa abun maye"ajiyar zuciya anty zubaida ta saki sannan ta dora
"A duniyance shaye shaye bai haifar maka da komai sai zubewar qima da mutunci,mummunar dabi'a ce dako wanda yake yinta yake boyewa,kuma baiso a sani,dabi'ace dakan gusar da imani da hasken fuska,dabi'ace dake barin tabo cikin rayuwar wanda ya taba aikatata,sannan ba'a sanyaka cikin sahun managarta mutane ko mutane masu dattako har abada,saboda kowa kallon mahaukaci yake maka,sannan a addinance manzan rahama yace dukkan wani abu da zai saka maye haramunne,musulunci yafimu sanin cewa kayan maye abubuwane masu cutarwa ga lafiyarmu,shi kuma ko yaushe tattalin lafiyarmu yake,sannan addini ne dake kare mutunci da martabar dan adam,bambancin mutum da dabba hankali,kinsha abinda zai gusar da hankalin me sunanki kenan a wannan lokacin?,dalili kenan daya sanya aka haramta mana su,duk sanda kake cikin maye babu kunya tattare dakai,hakan na nufin ba alkhairi a tare dakai kenan,saboda ma'aiki ya gaya mana duk inda kaga kunya akwai alkhairi a wajen,sanda kuma babu kunya tare dakai zaka iya aikata dukkan komai ciki kuwa harda kisan kai!,tunda kike sha din damuwarki ta taba tafiya gaba daya?" Kai shahida ta girgaza,don da zarar ta farka dukkan wata damuwa take dawo mata sabuwa fil,harma tafi ta dazun
"Zaki iya tuna sau nawa kikayi loosing sallah saboda tazo ta riskeki kina cikin bacci sanadin abinda kika sha?"shuru shahidan tayi tana tunani hawaye masu dumi nabin fuskarta har cikin kunnenta,kome take komai runtsi sallah bata taba wuceta ba sai a wannan karon,sai data shiga wannan mugunyar dabi'ar
"Kina tunanin hujjace da zaki gayawa Allah ranar gobe qiyama na dalilin jinkirta sallahrki?" Ta jefo mata tambayar data sanya shahida fidda sabuwar qwalla,dana sani da nadama mara misaltuwa na sake shigarta,kaico da rayuwarta da haduwarta da fiddausi
"Kina da yaqinin sanda kika farka kika ramata Allah zai amsa ya saka miki a mizanin ayyukanki wajen sallahrki na lokacin bazai tashi blank ba?,bayan kina baccin sabo ne bana ibada ba?" Sabon kuka shahidan ta sake saki,tsoron Allah na sake kamata,tana jin kaman yanzu Allah zai amshi rayuwarta,me ta tanada?,wacce amsa zata bayar?.
"Allah yana karban tuban bayinsa ne matuqar ran bawa baizo gargara ba,sannan kuma rana bata fito daga mafadarta ba,bai halatta bawa ya jinkirta tuba kan wani aikin sabo da yake ba,yace har sai Allah ya shiryeshi,don haka yana daga cikin alamar 'yanwuta,kuma alamace dake nuna bawa ya tabe,sannan alamace ta toshewar basira,anaso koda yaushe bawa ya dinga gaggauta tuba saboda baisan randa ajalinsa zai riskeshi ba"
"Astagfirullah...astagfirullah" shahida ta dinga maimaitawa a fili har na tsahon wani lokaci,sai data fuskanci ta samu nutsuwa sannnan ta dagota suna kallon juna
"Shahida...maganar anwar....." wani abu mai ciwo taji ya tokareta,abinda yayi mata ya dinga yawo cikin idanunta kamar tariyar film,da sauri ta katsi antyn
"Anty...don Allah ki daina kiramin sunanshi....don Allah anty ki dainamin maganarsa,yanzu bashi a gabana,yadda ya buqaci na barshi na barshi har abada...yadda ya nuna bai buqatata saboda wani kuskure dana aikata nima bana buqatarsa har abada" murmushi anty zubaida tayi tana karantar yanayinta da yadda maganar ke fita daga zuciyarta zuwa harshenta,kai ta girgiza tasan cewa wani bacin raine dake qonata tun daga cikin jiki zuwa zuciyarta,kowa ya shaida irin qauna da soyayya dake tsakanin shahida da anwar,koda baka sansu ba labarinsu ba shakka ya iskeka,bata da tabbaci ko yaqinin kan abunda shahidan ke furtawa saboda ta riga ta sani cewa soyayya ba qarya bace,ba qaramin dalili ne yake da qarfi da isar da zai karyata ba,karyawa ta har abada,karayar da ba zata doru ba
"Duk wannan lafazin shahida ban buqatar jinsa daga bakinki,ba'a ciwa soyayya alwashi kuma ba'a cika mata baki....kiyi addu'a kawai a yanzun,ki tattara hankalinki waje guda,ki karbi qaddararki,kiyi moving forward,stop worrying about what u have to loose,and start focusing on what u have to gain,har yanzu yarinyace ke,shekarunki nawa?,me kika soma gani cikin rayuwa?,akwai abubuwa daya kamata ace kinyi achieving a rayuwarki,karki bari wani abu guda daya ya tsaidaki waje guda,ya ruguza dukkan wani kyakkyawan tanadi daya kamata kiwa rayuwarki,wannan abun daya faru ba komai bane cikin rayuwarki,daya daga cikin challanges kenan na rayuwa,ki godewa Allah kina da chance,kina da dama,kamar ya baki wata dama ne naci gaba da gina sabuwar duka rayuwar da kikaso kikaga dama,just choose tobe strong rather than letting it drown you" wadan nan sune ire iren kalaman da anty zubaida ta dinga amfani dasu tsahon shekara biyar don dawo da rayuwar shahida cikin nutsuwarta.

Cikin qaramin lokaci taji anwar din ya wanke mata a rai tas,ya sire mata,ya fice mata daga ruhinta,taji zata iya rayuwa babu shi,taji abune mai sauqi hakan,saidai baizo mata da sauqi ba yadda ta tsammata,ta share darare da yawa bata samu bacci ba,ta ga wuninnika da darare masu tsaho da tsauri cikin rayuwarta a wannan lokaci,ta cika bangon dakinta da shafukan littafanta ta kalaman qarfafa kai da qarfafa gwiwa akaran kanta,ta siya littafi tayi rubutu mai tsaho da yawa kan rayuwarta har kawo bigiren da yau take kai,ta tattara duk wani abu da zai iya tuna mata da anwar ta ajesu waje daya,ta shiga tsara yadda rayuwarta zata kasance nan gaba,tun saga lokacin ko masoya ta gani sai taji tana tausayinsu,musamman mace idan taga ta zura jiki da yawa.

Bayan umma ta fita takaba uncle hisham shi ya karbi ragamar daidaita musu duka al'amuran gidan,sannan suka yanke shawara dashi shahida zata koma hannun anty zubaidan,tunda har yanzu bata gama daidaita ba,saidai cikin kaso dari an samu sauyi na kaso shida,rabata da unguwar da duk wani tsohon memory dinta zai sake taimakawa wajen saita tunaninta,da wannan suka dauke shahidan ta koma wajensu.

Makarantu daban daban anty zubaida ta sakata wanda zata qaru ta fanni da dama,wasu na koyon harshen larabci wani na koyon turanci bawai don bata iya ba,a'ah saidon ta maidata busy sosai wanda hakan zai sanya bata da lokacin zama ma ta tuna wani abu mara dadi daya faru da ita a baya,tayi hakanne kuma kafin wata shekarar ta zagayo su nema nata admission saboda wannan shekarar ta qwace mata.

Rayuwarta ta soma samun sauye sauye,kullum kwanan duniya saitayi kukan dabi'ar shaye shaye data ta taba tsintar kanta a ciki,kullum sai tayi nadamar sanin fiddausi a rayuwarta,sai tayi nadamar sakin jiki ga duk qawar data kutso rayuwarki sama taka,abune mak wahala da idan ka sake ka jefa kanka da wuya ya fice daga rayuwarka salin alin ba tare daya haifar maka da nadama da danasani ba,bai kuma bar maka qatoton tabo ko baqin fenti a rayuwarka ba,ta godewa Allah da yayi gaggawar fiddata tun batayi nisan da ba zata ji kira ba kamat yadda tagani ta kuma ji labari da yawa akan wasu,wanda ta shiga bincike ne akai bayan ita Allah ya tsamota,gefe daya kuwa yaqi take tuquru da kanta game da lamarin anwar,wata irin tsana da bata taba tunanin tanawa wani dan adam ba ita ke taso mata,duk wani abu da yayi mata da yadda ya dubu qwayar idanunta ya gaya mata magana,fiddota daga gidanshi da sauransu,uwa uba hotunan yarinyar da yake gaya mata ya sake ya sauyata a madadinta,kullum qoqarin goge duk wani tabo ko abun tunawa daya barwa rayuwarta take,tanason ta nuna masa ta kuma nunawa duniya she can survive without him,tana son watan watarana yaga cewa shi din ba komai bane da ba zata iya rayuwa babushi ba.



*Cikin rashin kunya murjewar ido dajin wannan karon dai dai take da kowa,zata iya karawa da kowa,a shirya take ta rabu da kowa saboda shi,bata jin akwai abinda ya isa yayi mata hijabi tsakaninta dashi,koda waye,koda mahaifiyarta data haifeta,koda mahaifinta da yayi silar zuwanta duniya*

*"Allah ya isa ban yafe ba duk wanda yayi silar rabani da Zamab,ko wayeshi bazan taba yafe masa ba wallahi, dan an haifeka ai ba halittarka akayi ba, kai ma babu wanda yayi maka auren dole, haka a addinance babu inda Allah yace ayiwa mace auren dole"*

*kalaman da suka fito kenan kai tsaye daga bakin Basmah zuwa ga mahaifinta Ya Mu'allim tana dubanshi kai tsaye ba kunya ko rusunawa*

_SAKI RESHE KENAN littafin da zaizo muku daga jarumarku haziqar marubuciya HAUWA A USMAN JIDDERH_

*WANNAN WACCE IRIYAR DIYACE HAKA?,ME YAKE FARUWA ME KUMA YA FARU?,DON JIN CI GABAN WANNAN LABARI DAKE QUNSHE DA BADAQALA,SAKIN RESHE DA SAGEGEDUWA ZAKA BIYA NAIRA 300 KACAL TA WANNAN HANYA,BA TARE DA BATA LOKACI BA ZA'A SADAKA DA WAJEN DA ZAKA SAMU NAKA*

Hauwa Auwal Usman
GT bank
015325259310

*saiki tura shaidar biya zuwa ga wannan number*
07020489340

*katin waya kuma xaku tura 300 ta watsapp ta wannan number*
07020489340


_kar ayi babu ke,maza garzaya ki nemi naki_🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos



*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899


*Alqawarin Allah*
1️⃣7️⃣



Daga gefan anwar kuwa yaso barin garin ne gaba daya,saboda yadda garin yayi kishi zafi,yaji ya tsani komai,bashi buqatar duk wani abu daya sani,yana buqatar baqon muhalli,anty husaina ce ta kafe kai da fata kan bata yarda ba,ganin yadda ya dage kan son tafiya din ta sakar masa kuka,wanda ya sanya dole ya haqura shima yaci gaba da zaman.

A wannan lokacin da nafisa taga dama tazo mata,taso ta gabatarwa da anwar kanta ne gaba gadi,taso anwar ya dawo cikin gidansu da zama qarqashin abbanta,ya bashi gida mota da kuma jari suyi aurensu,saidai yadda labari da halayyar anwar tazo mata ta tabbatar da cewa aikata hakan babban kuskure ne da zai janyo kwabarta tayi ruwa,wanda daga qarshe suka gama shawara da mima kan yadda zasuyi.

Alhaji abba kabara mahaifin nafisa mutum ne mai yawan taimako da samawa matasa ayyukan yi,yana da kamfanoni hakanan yana da shagunan da yake sanya matasa a ciki,duk matashin da yayu shekara guda riqe da amanar shagon ba tare da an taba kuka dashi ba alhj abba yakanyi masa kyakkyawar sallama ta hanyar bashi jari mai tsoka,wani lokaci ma bai duba da abunda aka samu a shekarar,zamanka a shagon iya karantarshi da amanarka kawai ya nuna idan ya baka jarin ba zasu salwanta ba,wasunsu kuma yakan daukesu ne ya kaisu kamfaninshi,musamman masu takardun makaranta,dalili kenan sanya sanya ta samu abban nata
"Uhmm...ya akayi nafi?" Cikin nuna yanayi najin kunya tadan sadda kanta
"Abba dama...dama" sai tayi shuru
"Dama me?" Ya tambayeta yana sauke medical glass dinsa
"Akwai wani marayan matashi ne,abba yana da amana da duk halayen qwarai,ya kammala karatunsa baida aiki,abba yana shan wuyar rayuwa sanadiyyar haka,idan na masa magana abba da kaina bazai karbi duk wani abu ba,amma idan kaine da kanka abba zaifi amsar duk wani taimako" shuru ya danyi yana nazarinta
"A ina ke kika sanshi?"
"Abba...a unguwarsu qawata yake,ita take bani labarinsa,na tabbatar zaka yaba da halayenshi hakanan zaka tabbatar daya cancanci taimako" kai yake gyadawa sannan yace
"Ba damuwa,ki turamin adress dinshi,zamu fidda sanarwar daukan ma'aikata a kamfanina zansa a duba takardunshi sosai"
"To Abba Allah ya qara budi" amin ya fadi yana daukar jaridarsa yaci gaba da dubawa,yayin da nafisan ta fita cikin farinciki da walwala.

Randa aka kira anwar aka shaida masa sunan kamfanin da sukeso duba takardunsa yayi mamaki qwarai,don iya yawon neman aikinsa bai taba bi koda ta titin da kamfanin yake ba,don bai taba sama ranshi cewa zasu daukeshi aiki ba.

Qarfe taran safe na ranar da zaije kamfanin ya gama shirinsa ya fito yana kulle gidan yaga mota tsaye a qofar gidan,horn aka danna mishi kana aka jawo motar zuwa gabanshi
"Daga kamfanin alhj abba ne akace muzo mu daukeka" ya kalli motar sosai yaga tambarin kamfani jiki,hakan ya sanya ba musu ya bishi suka shiga.

Sam bai kula da itaba ashe tana zaune a bayan,sai daya waiwaya suka hada idanu ta sakar masa murmushi,sam bai ganeta ba,ita ta soma gaidashi sannan ta gabatar mishi da kanta a matsayin diyar alhj abba,mamaki day ayayi na wanne matsayine dashi da har za'azo har qofar gida a daukeshi cikin motar kamfani shi da za'a yiwa alfarmar bashi aiki,bashi da amsar wannan saboda haka shuru shi yafi masa,yana jin nafisan na bashi labarin abubuwan da suka shafi kamfanin kamar ma an daukeshi aikin ne,shidai nashi kunne ne,don yanzu baya ga anty husaina baya jin dadin hira da kowacce diya mace,hasalima bayaso su rabeshi.

Bisa jagoranci da shigewar gaban nafisa ya gama komai cikin kamfanin,aka kuma bashi babban gurbi wanda ko a mafarki bai taba tsammata ba,koda wasa bata nuna ita ta roqa masa wannan alfarmar ba saboda tasan ba wani abu bane cikin aikinsa yaqi amsar aikin gaba daya.

Lokaci kadan da fara aikinsa alhj abba ya tabbatar da duk maganar da nafisa ta fadi a kansa,yana da gaskiya yana da amana,hakanan yana da aiki tuquru,baya taba saba lokacin zuwa kamfani hakanan lokacin tashi,gwara ma lokacin tashin idan akwai wani aikin da kamfani zaici gaba yakan sarayar da lokacin nashi ya gabatar dashi,dalilin kenan daya sanya alhj abba da kanshi ya danqawa anwar qaramar motar hawa mai azabar kyau da tsada irin wadda bai kawo zai mallaketa ba nan kusa,sannan ya nemi daya dawo cikin gidanshi da zama,wanna ne kuma ya bawa alhjin haquri,saboda yadda nafisa ke shishshige masa sam baya masa dadi,yana karanta mata ne da daga mata qafa kawai saboda girma da darajar mahaifinta,motat ta sauqaqa masa sauran ayyuka da zuwanshi ma kamfani gaba daya,hakanan ya dinga barin motar a wani garage dake farkon layinsu wanda masu abun hawan da basu da muhallin ajesu suke ajewa a nan su biya wani abu ladan ajiyan.

A sannan rayuwa ta soma mishi kyau,koma ya soma canzawa,kama daga sutura cima da sauransu,anty husaina ma kanta canji ya soma zuwa mata,a wannan lokacinne nafisa ta kasa shanye halin ko in kula da anwar ke nuna mata,duk wata alama da ake nunawa mutum ya gane ana sonshi ta nuna mishi amma a banza wai an mintsini kakkausa,hakan ya sanya tayi qundunbala taci alwashin sanar mishi wata rana da abbanta ya gayyatoshi cin abincin dare gidan.

Abban da mamanta sun kammala sun bar wajen saura nafisan da tunda taji labarin zuwanshi ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta tsara kwalliya ta a mutu,sannan ta aro duk wani salo da tasan zai iya tafiya da d'a namiji,saidai kuma har ya kusa gamawa bataga ya nuna wani abu game da ita ya burgeshi ba,hakan ya sanya tayi gyaran murya
"Anwar....idan ba zaka damu ba don Allah...ina da magana dakai"
"Uhmm...babu damuwa ina jinki" shuru tayi na wasu mintuna sannan ta daga kanta tana dubanshi sosai
"Tun ranar da Allah yasa na soma ganinka anwar Allah ya dasa min qaunarka...na rasa ta yadda zan furta maka bansa ya zan gaya maka ka gane ba,wani irin soyayyarka nakejin har cikin jinina,anwar ina fata da roqon ka soni koda rabin yadda nake sonka ne" tunda ta soma maganar ya zuba mata idanu yana jin wani abu da baisan meye ba yana taso masa,ko kusa ko alama baison yaji wannan kalmar daga bakin kowacce diya mace gani yake duk yaudara ce,ba gaskiya bane qarya ce,yatsunsa ya dinga bugawa a saman teburin kadan kadan har ita sai data tsargu da kallon da yake matan ta soma kame kamen abunyi,da qyar ya iya hada abun fada
"Nafisa" ya kira sunanta a kausashe,daga kanta tayi ta dubeshi sosai jin yadda sunan nata ya fito bilhaqqi daga zuciyarsa
"Inason daga yau wannan tunanin yabar qwaqwalwarki,wannan kalmar ta fita daga bakinki,ina ganin qimarki data mahaifanki,kada ki jawo abinda bazai mana kyau da dadi ba ni dake gaba daya"daga haka ya miqe ya dauki maqullan motarshi ya wuce ya barta a wajen,kuka ta saki sosai,bata taba tunanin lamarin zaizo da haka ba,tayi tsammanin yadda yake nuna kulawa a gareta kaman qanwarshi zata samu soyayyarshi ta sauqi,haka ta miqe ta shiga bedroom dinta cikin tashin hankali ta dauki wayarta ta kira mima ta zayyane mata komai
"Nafisa kenan,dama ke kina tunanin samun kanshi da wuri ne,to kinyi kuskure idan ma zaki zage damtse kiyi kaman kinayi to" ta jima tana juya zantukan miman a kwanyarta,inda daga qarshe ta zage damtsen kaman yadda ta bata shawara,saidai gogan ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,yadda ya saba mu'amala da ita haka yake babu abinda ya canza,naci kuwa babu kalar wanda batayi masa ba,inda daga qarshe ma ta matsawa dadynta ya bata gurbin aiki a kamfanin,ya bata din saidai tace matsayin secretary din anwar takeso,babu musu ya bata kasancewarta diya mace diya tilo dake gareshi,anwar din bashi da bakin cewa don me?,haka ya amsheta saidai kusan ba wani aikin kirki take ba,cikin qaramin lokaci kowa ya fahimci yadda nafisan ke bala'in so da qaunar anwar din,wannan labarin shi yakai har kunnen umminta,take ta saka abban nafisan ya karbe gurbin aikin daya bata aka maida shi da wani,fada ta dinga ma nafisan kan wautar da take nunawa na nunawa namiji irin wannan zallar son bayan shi baisan tana yi ba,kuka ta dinga duk da ta bata tausayi amma sam bata nuna ba,don tana sone idan anwar zasiso nafisan ya sota don karan kanshi,ya kuma sota da datajarta ba tare data zubda qimartata ba wajen neman soyayyarshi ba a matsayinta

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment