Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata iya komai ba kaman yadda na lura,saboda bangani a qasa ba" ya fada yana takowa zuwa inda take tsaye,yanajin bazai iya barinta yadda ta rikitashi taci bulus ba ba tare da shima yau yadan taba koda fatarta ba yaji yadda akeji,baya ta soma ja tana kallonshi,bata fahimci me yake shirin aikatawa ba saida ya kusa qureta jikin madubin dakin,idanunta cike fal da tsoron da takeson boyewa tace
"Meye haka kakeyi?"
"Abinda kika gani" ya bata amsa bai fasa nufota ba,cikin dan tsoro tace
"Karka tabani" cak ya tsaya yana kallonta
"Tunda kwartone ni?" Ya amsa mata ta sigar tambaya,bai kuma bi ta kanta ba yaci gaba da nufarta,don baijin zai iya haqura din shima bai d'aana ba,ko ina ta kalla ya riga daya kangeta,a haka ya hade gap din dake tsakaninsu,ya zagaya hannunsa ta qugunta ya janyota sosai cikin jikinsa,fuskarsa ya sauko da ita dokin wuyanta yana kai hancinsa,ta soma juye juye tana son ta qwace daga hannunshi
"Banaso,meye haka,ka sakeni"
"Ni kuma inaso" ya fada yana fidda numfashi saboda yadda abun ya soma masa dadi,wayarsa dake saman mudubin ta dauki haske da qara,wanda hakan yaja hankalinsu gaba dayansu,a tare idanunsu ya sauka a tare kan screen din wayar,sunan NAFISA ya bayyana saman screen din,dauke idanunshi yayi yaci gaba da abinda yake,hakanan taji wani abu yadan sosa mata rai kadan,amma saita dauka yadda ya tarfata ne yake yadda yaso da ita,sosai yake shinshinar kowanne lungu da saqo na jikinta yana fitar da numfashi,ko ina jikin shahidan rawa yake itama,karon farko da irin hakan ya soma faruwa da ita a rayuwarta,tsoro da haushin anwar din ya cikata ganin da gaske yake yau ba wasa bane,kaman wanda aka tsikara ya saketa da sauri gami da turata baya shima yaja baya da hanzari yana zama gefan gado ya dafe kanshi dayaji ya sara masa lokaci daya
"Ya Allah" ya furta yana ci gaba da dafe kan nashi,hanqota kawai yayi sanda take rungume jikin wani,bayaso ire iren wadan nan tunanukan su dinga dawo masa kwanya,saboda haka saiya dinga maimaita
"Hasbunallahu wani'imal wakil" tana zuge zif din rigarta tana mamakin yadda lokaci guda yasaketa haka,yanayin da taga ya shiga din,saidai itama ba'a nutse take ba saboda haka tana gama jan zip din nata ta soma tattaki cikin hanzari zata fice
"Dawo nan!" Ya fada cikin kakkausar murya,ba musu tadawo din ta tsaya cak saidai bata dubeshi ba,fuskarshi a dinke take tsaf babu fara'a ta sisin kwabo
"Shiga ki hadamin ruwan wanka" jikinta a mace take takawa zuwa bandakin,ta hada mishin ta fito ta shaida masa,saiya miqe kawai ya zari towel
"Karki tafi saina fito" ya fada yana shigewa cikin bandakin,tsayawa tayi cak,ta jingina da madubi tanajin yadda qafafunta suka mutu,jikinta babu qwari sam,ta soma tuna yadda taji daxun da yadda abun ya kasance,saita lumshe idanunta tana tuns komai,qamshin jikinsa daya goga mata yana zarya cikin hancinta har zuwa qwaqwalwarta,kasala na sake saukar mata,qarar da wayar tashi ta sakeyi ita ta katse mata duk tunaninta ta sanyata bude ido,bata tabata ba sai dubanta data kai kan wayar,sunan nafisa ne dai again,saita ci gaba da kallon wayar harta katse,tana shirin dauke idanun nata wani kiran ya sake shigowa.

Ci gaba tayi da kallon wayar har kiran ya sake katsewa,duk kiran daya shigo din kan idanunta ya dinga shigowa yana katsewa,wanda a qalla kafin ya fito din an kira yakai sau goma sha biyar,kuma ba'a fasa kiran ba,bata dauke idonta ba itama saida taji ya soma qoqarin bude qofar bandakin sannan ta kauda kai tana tunanin wace wannan haka?,meye ya faru take jero kira haka ba qaqqautawa?,bakin mudubin ya tako saita matsa gefe tana sake dauke kanta wani sashen,towel ne daure a jikinsa iya qugu,sai wani daya ratayo wanda duka duka bai gama rufe jikinsa ba gaba daya,wani nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,gabanta ya dunga faduwa sosai,ta sake dauke kanta yadda ko inuwarsa ba zata gani ba,baice mata komai ba ya daga wayar ya duba mai kiran,duka nafisan ce,cikin zuciyarsa yaja tsaki yana tambayar kanshi me zata masa?,ya aje wayar yana cewa
"Kije ki shirya,zamuje duba anty usaina batajin dadi" waiwayowa tayi cikin faduwar gaba da fargaba,bala'in kunya da nauyin anty usainan takeji,yanzu kuma zai kaita gidanta?,saidai a kamatance ma bai kamata ta musa masa ba kodon karamci irin na anty usainan da qaunar da take gwada mata.

Tana shiryawa amma kiran wayar ya tsaya mata arai,ta rasa dalili,kiran sai takega kamar yayi yawa,a haka ta gama shiryawa tsaf cikin wani lace,ta yane kanta da yalwataccen mayafin daya dace da shigar tata,saidata dubawa anty usainan abinda zata kai mata ta saka cikin jakar hannunta sannan ta fito,a falon qasa suka hadu,saita tsinci kanta da satar kallonsa duk da bata shiryawa hakan ba,anwar badai wanka ba,tunda can tun lokacin da bashi da komai mutum ne mai tsafta da kwalliya ma gaba daya,yayi kyau cikin yadin kufta na maza,dubanta yayi sosai wannan karon kanshi tsaye babu boye boye
"Wannan qamshin yayi yawa" yana takowa zuwa gabanta,tuna abin daxu daya mata tayi saitayi hanzarin jaa da baya kada ya maimaita,don har yanzu jikinta a mace yake,tsayawa yayi cak saiyayi murmushi cikin ranshi,ya gane me take gujewa,itakam ba wani turare ta saka ba bayan na jikinta,juyawa yayi ya fice ta mara masa baya.

Zata shiga baya kamar yadda ta saba masa taji qofar taqi buduwa,haka tayita qoqarinta na budewar amma taqi da alama lock ya saka,dole ta dawo gaba ta bude ta shiga.

Horn biyu maigadin ya dage masa gate din ya saka motar,ya qaraso suka gaisa da anwar din sanda yake fitowa daga motar,suka soma takawa zuwa cikin gidan,suna gab da valcony din da zata sadasu da qofar falon tana fitowa cikin doguwar riga da yalolon mayafi,hada idanu sukayi da anwar,saita kasa dauke idanunta daga kanshi,gabanta na faduwa qaunarshi na sake ratsa zuciyarta fiye dada,sai taga kaman an qara masa kyau da haske,ga wani kwarjini na musamman da gake fitarwa,shi ya soma janye nashi idanun ya soma yin gaba,suka hada idanu da shahida dake bayanshi,kowacce nata idon cikin na 'yar uwarta,sake kallon shahidan nafisa take sama da qasa,kishinta na ratsata,ta sake kyau da aji fiye da daa,duk da cewa ba zata taba mance fuskarba,duk da cewa ta ganeta amma saita janye idonta daga kanta ta rufawa anwar baya,tana jin wani abu na sukar zuciyarta,da kallo tabi bayan shahidan har suka wuce,sannan taja qwafa ta wuce,tanajin a zuciyarta wannan karan kam ba zatabi shawarar mima ba,zuciyarta takai maqurar da bazata iya jurewa ba.

Yana gaba tana binsa a baya cike da kunya har cikin babban falon anty usaina,gaba daya yaran suke miqe suna musu sannu da zuwa,sa'ida ta soma tare shahida ta rungumeta
"Oyoyo anty,uncle,amma bakacemin zakuzo da anty ba yau"
"To ai gata kin ganmu" ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun,yayin da maibin sa'idan ta haura sama donta shaidawa anty usainan zuwan sun tana cewa
"Yanxu ma tahau saman,anty nafisa ce tazo dubata" cikin shi da shahidan ba wanda yace komai ba,itakam nunawa ma tayi kaman bata santa ba bare ta ganeta,sunata taba hira da sa'idan,yayin da shi kuma ya shiga tunanin me nafisan tazoyi gidan anty usainan?.

Dawowa tayi ta shaida musu tace su hau saman,shine dai a gaba tana binsa a baya har suka bayyana wani falon dake daman,anty usainan na zaune qasan carfet suka shiga da sallama,fuskar anty usaina wadace da fara'a takewa shahidan lale kota anwar ma bata biba,a kunyace ta zauna gefan anty usainan tana jin anwar na tambayar antyn fitilun harabar gidan da wasu suka mutu
"Ka qyalesu hakanan tunda dai gidan da haske ai shikenan" saita sake maida kanta ga shahida wanda kanta ke sunkuye a qasa,gaidata tayi a kunyace anty usainan ta amsa cikin kulawa,Shahidan ta mata sannu da jiki ta amsata
"Aina warware alhmdlh,shine sai daya tattagoki" qaramin murmushi ta saki kanta a qasa cike da jin kunya da nauyinta,daidai lokacin sa'ida ta shigo dauke da tray wanda ta cikashi da kayan ciye ciye,kai tsaye ta aje gaban shahidan,ta durqusa tana zuba mata duk abinda ke cikin farantin,qasa qasa shahidan ke kallonta tana dariya idanu a waje yadda su anty usaina bazasujiba tace
"Sa'idah,wannan duka?,aisai cikin antyn taki ya fashe"
"A'ah anty kici wallahi,yauke baquwarmuce ta musamman"
"Mu kuma aisai a koramu ko?,yauni aka yiwa danwaken zagaye saboda kin ganta ko?" Tana dariya sa'idan ta daga kai daga shiryawa shahida cake da take cikin plate ta kalleshi cikin dariya
"Ba haka bane uncle nina isa?,kawaidai nasan ka gayamin cewa kaida anty abu guda ne,kaga idan na bata kamar kai na baiwa" murmushi yayi yana daga mata hannu yana satar kallon shahidan,shi sam ya mance daya gaya mata hakan,ya fada ne a gaban anty usaina don sake kwantar mata da hankali da amintar mata tunaninta,saidai ya manta sa'idan bata mantuwa,ta kammala zubawa shahida komai ta miqe tana duban anty usaina
"Na gama ummi"
"Shikenan,idan kin sauka ki shiga kitchen ki tafasa min maganin nan,ki samu botiki mai murfi ki xuba a ciki kidan sabashi yasha iska kafin na sauko shi xansha"
"Tohm" tajuya ta dubi shahida
"Anty kici sosai don Allah ki cinye duka" murmushi kawai tayi tana dubanta,sosai yarinyar take sonta da burgeta.

Inda shahidan ke zaune ya sauko,ya zauna sosai a gabanta,farantin dake tsakiyarsu ne kawai ya raba tsakaninsu,idanunsu suka shiga cikin na jina,kowanne ya zare nashi idon daga cikin na dan uwanshi yana jin yarrr cikin jikinsa saboda kusancin da sukayi da juna yayi yawa,saiya sanya hannu ya dauki kofin gabanta yana cewa
"Tunda niba wanda yayimin tayi bari nayiwa kaina"
"A'ah..ban yarda da wannan juyin mallakar ba,aje mata,kaidin baqo ne da bazaka dauka da kanka ba?" Murmushi ya saki yana tsaida kofin da yayi nufin kaiwa bakinsa
"To ai anty itama ba zata sha ba idan bansha ba" ya qarshe maganar yana waiwayawa ya dubi shahidan yana kashe mata ido,sadda kanta qasa tayi saboda wani abu dataji ya saukar mata saman zuciyarta mau nauyi,yakai bakinsa ya kurba lemon ya miqa mata suna magana da anty usaina,qin amsa tayi har ya gama maganar ya juyo yana dubanta
"Karbi mana,kosai na baki da kaina?" Harara ta cilla masa a fakaice ta saka hannu takarba ganin yana kai kofin bakinta,ya xuba mata ido sanda takai kofin nata bakin,tana sane ta juya daga wajen daya sha ta sauya gurbi,murmushin mugunta ya saki ya waiwaya wajen anty usaina yana tambayarta
"Me yarinyarnan tazoyi gidan nan?,na ganta sanda muke shigowa"
"Nafisa?....waitaji banji dadiba shine tazo dubani,amma tazomin da wata magana da nace saikazo naji ta bakinka tukunna" ta fada tana dan dubam shahida,batason yin maganar a gabanta,amma kuma tana ganin yin maganar a gabantan kamar xai bada wani alfanu game da kawo gyara kan yanayin mu'amalarsu da anwar,don har yanzu bata gamsu da yanayin zaman nasu ba,tana ganin yadda suke abu kaman baqin juna
"Tace na baka haquri akan kuskuren datayi a baya,tana son idan da hali ka dawo ka....." Daga kai anty usaina tayi tana duban shahida wadda ta miqe tsaye
"A'ah,ki zamanki shahida mana?"murmushi tadan saki,don tunda aka ambaci sunan nafisa zuciyarta ta gaya mata ba kowa bace illa wannan wadda suka gani dai sanda zasu fita,fuskar da anwar ya aiko mata da ita cikin envalope din data baiwa suna da baqin saqo,hotunan da har yau ta kasa rabuwa dasu dukda yadda suke qona ruhi da zuciyarta duk sanda ta tuna dasu,ko kuma duk lokacin data kallo gefan da suke aje
"Zan saukane wajensu sa'ida"
"To shikenan,nima ganinan zuwa,ai bamu gama hirar ba"
"Toh anty" ta fada ta juya tana fice daga dakin,anty usaina ta bita da kallo farinciki na ratsa zuciyarta,tanason karanto wani abu game da shahidan,saita maida dubanta ga anwar,wannan karon shiya soma magana
"Don Allah anty karki shiga maganar nan,an riga da an wuce wajen tuni,na godewa Allah da bani na soma gudunta ba bare aga butulcina,ta ruga data gayamin manufarta tun rannan,kuma kullum kwanan duniya saita aikomin da saqo kan hakan" ajiyar zuciya anty usaina ta saki,itakam a duniya yanzu ba abinda ya rage mata illa taga kan shahida da anwar din ya hadu kawai,ta tabbatar idan hakan ta faru babu kuma sauran wata matsala
"Shikenan Allah ya zaba abinda yafi alkhairi,nikam yanzu bani da burin daya wuce naga kanku ya hadu yadda ya kamata kaida shahida,yarinyar tana da nagarta anwar,kayi qoqarin gyara zamanku,gashi kuna qoqarin cinye wata na biyu amma a karatuna banga hadin kan da nake buqata ba,ajiyar zuciya ya saki yana dan kashingida kadan,cikin zuciyarsa yana fadin antyn ba zata gane ba,shi kadai yasan me yakeji kullum kwanan duniya,a raye yake amma zuciyarsa matatta ce,ya gaza gano dalilin daya sanya shahidan aikata dukkan abinda ta aikata a rayuwarta,meye sila?,meya janyo haka?.

Shahida na qasa suna hirarsu dasu sa'ida anty usaina ta koro anwar qasan takuma ce ya turo mata shahidan,sanda taje kusan karatun xama da miji tayi mata sosai ba kunya ko nauyi tsakaninsu
"Shahida...kiyi haquri da yadda rayuwar aurenku taxo muku ahagunce kuma a kaikace,farinciki gamida walwalar gida a hannun matar gida take,tana da ikon maida gidanta aljannar duniya ko kuma akasin haka,duk yadda namiji keda taurin kai,taurin zuciya da kuma kafiya abune mai sauqi matarsa ta canzashi matuqar tayi karatu mai yawa akanshi da halayyarshi,kiyi haquri kiyi qoqarin canza gidanki,ki zama mace sosai,kiyi amfani da hikima da basirarki,kaf dinmu makusantanki dana anwar ba wanda yake fata ko burin rabuwarki dashi,kinga kenan babu ranar da zaku rabun,tome zayasa abinda babu ranar yankewarsa maimakon ka gyarashi kaji dadinsa ka amfaneshi saika zabi dawwama cikin karkatacciyar rayuwa maras dadi?,duk lokacin da rayuwar auratayya ta kacame ta lalace babu wanda yafi cutuwa a ciki,yafi quntata,yafi zama cikin wahala baqinciki da bacin rai irin MACE,namiji nada tarin hanyoyin da zai debewa kansa kewa ya ragewa kansa baqinciki da bacin rai,ba kamar ke mace ba da taki damar qwaya dayace wannan mijin da kike aure,kome anwar ya miki,duk da bansan girman cutarwar da yayi miki ba abaya,ina mai qasaqantar da kaina da roqa masa alfarmar ki yafe masa,ki tashi tsaye ki gyara gidanki,ki masa kyautatawar da girmanta zaisa yayi nadama yayi danasani,ya kuma ji kunyar aikata miki dukkan abinda ya aikata mikin,ita mace tana da wannan power,zuciyar namiji a wajenta ba komai bace horewa ce ta ubangiji,nasan zaki iya din ina kyautata miki wannan zaton,ina roqar alfarma zakiyimin shahida?"cikin jin kunya da nauyi gamida gasgata kalaman anty usaina ta gyada kai
"Xan miki anty,zanyi in sha Allahu" ajiyar zuciya ta saki tana lumshe idanu
"Na gode qwarai,amma kafin sannan,ki nutsu ki mu'amalanceshi ta yanayi da sigar da yake mu'amalantarki gudun kadda kisha wahala,ina fatan kin fahimceni?" Kai ta gyada mata alamun ta gane,hakan ya yiwa anty usaina dadi sosai,da kanta ta bude cupboard dinta ta ciro mata wasu rigunan bacci masu shegen kyau da sulbi guda shida,ta hada mata da turarukan bedroom suma guda hudu masu kyau da tsada,ta amsa tayi mata godiya sosai,saita danyi jim,anty usainam ta fuskanci akwai maganar da takesonyi,saboda haka tace da ita ta fada kada taji nauyi ko kunya
"Anty aron sa'ida zaki bani don Allah tayimin ko sati guda ne" baki anty usaina ta bude
"Keda zaki shiga yaqarmin tunanin dan uwa na hadaki da sa'ida ta hana ruwa gudu?" Kunya ta sata sadda kai tana dariya
"Shikenan,amma ba zata wuce kwana uku ba"
"Don Allah anty ki barta tayi sati" daqyar ta yadda da hakan,sa'ida murna kaman me ta hada kayanta ta bisu.


*11:30 pm*


Doguwar rigar bacci ce a jikinta mai sulbi wadda takai har qasa da dogon hannu,sai baby hijab data sanya wanda iyakarsa saman kafadunta,duk motsin datayi qamshi ne yake tashi harta iso matatattakalar qarshe wadda daga ita sai qaramar baranda da zata sadaka da falon samanshi,cak ta tsaya tana ajiyar numfashi,shida kanshi ya mata magana kafin su shigo gidan kanta taho samanshi saboda sa'ida kada ta karanci yanayin zamansu,baiso anty usaina ta fahimci komai,baisan yayi sara bane kan gaba,ta riga data gama shirinta dukda ciwo da takeji a qirjinta da nauyin alqawarin data dauka,anya zata iya saukewa?,takewa kanta wannan tambayar,duk sanda fuskar nafisa ta gilma mata a idanu,yadda ya cillota da girman kalaman daya sossoka mata saitaga gaba daya yayi mata baqi a ido,koren shaidan tayi sannan tayi bismillah taci gaba da takawa ta tura qofar falon ta shiga.[8/20, 2:39 AM] Nadady: *afwa,gutsirewa yayi ban sani ba ga full nan*

*Alqawarin Allah*
42

https://youtu.be/-tPtW9YtNpU

Yana zaune saman kujera ya miqe qafafunsa gaba daya,sanye yake da gajeran wando iya gwiwa da vest,hannunta riqe da wayarshi yayin da rabin hankalinsa ya tafi ga kallon labaran da ake a VOA,bude qofar yaja hankalinsa,ya daga idonsa ya dubi qofar,hada ido sukayi da ita,ta janye nata idon saboda nauyin ganinsa da take a haka,yayin dashi kuma yaci gaba da kallonta har zuwa sanda ta iso inda yake,ga mamakinsa sai yaga tayi wucewarta bedroom dinshi rungume da kaya a hannunta ta tura qofar ta shige,sai a sannan ya janye idanunsa yana lumshesu gamida budesu duka lokaci guda hadi da zuqar qamshin turaren data wuce tabar masa,saiya sake miqe bayansa saman kujerar,ya aje wayarshi saboda kasalar data saukar masa,ya tattara hankalinsa duka kan tvn yaci gaba da bibiyar labaran.

Idanunta ta waro tana sarawa kanta abinda tayi na farko na wuceshin da tayi kaman dakinta,ta kalli gadon nashi,fes dashi kaman gadon mace,ta tabbatar shike gyara abinsa,ta bude ma'ajiyar kayan sawarshi ta aje kayan data shigo dasu a hannunta,bata kwanciya saida ruwa,saboda haka dole ta fita ta samu ruwa,ta zare hijabin jikinta ta gyara dankwalin kanta ta rufe gashinta sosai sannan ta soma takawa ta fito daga bedroom din.

Baiji fitowarta ba sai gilmawarta ya gani zuwa saqon da fridge dinsa ke ajiye,yaso yiwa idonsa shamaki amma ya gaz,yana kallonta qasa qasa wanda ahaka saika tsammaci bacci yake ta ciro ruwan gora daya ta juya ta koma zuwa ciki.

Duka addu'o'inta tayi,ta shafe jikinta da su sannan ta dauki remote ta qaro gudun acn,sannan ta kashe qwan wutan ta koma ta kwanta.

Sha biyu saura yaji zaman ya isheshi,duk da yawancin lokutan yakan wuce haka azaune ya riga daya saba,saiya kashe duka kayan wutar ya tattare komai ya tura qofar dakin ya shiga,duhu ne ya masa maraba,ya laluba ya kunna wutar,can ya hangota saman gadon nashi a kwance abinta,ta tattara dukkan filallukan,wani ta dora kanta wani qafafunta,wani ta takore bayanta kamar mai ciki,duvet din nashi ma hannunta ta dora akai don ba rufe tayi ba,hakanan ta raba gadon biyu ita bata gefe guda kuma bata tsakiya gaba daya,saiya tattare hannayensa kawai ya tsaya yana kallonta,yana tunanin ta ina zai kwanta?.

Qarar wayarshi ta katse masa tunani,ya cirota daga aljihunsa ya duba,tsaki yaja ganin wadda take kiran,saiya maida wayar aljihu,ya qarasa side bed ya dauki remote na ac ya rage sannan ya nufi bandaki ya daura alwala,sallah yayi raka'a biyu yana saman abun sallah yana addu'a wayartashi ta sake ruri,tsakin dataji yaja tuni zuciyarta ta gaya mata wacece,gyara kwanciyarta tayi ta soma gunguni qasa qasa yadda tasan zai iyaji
"Haka kawai a takurawa mutane da waya,sannan a kashewa mutane iska bayan zafi sukeji" daga kai yayi daga tasbihin da yake qirgawa da yatsun hannayenshi yana kallonta,saidai bai samu nasarar kallon fuskarta ba,sai bayanta daya hanga wanda rigar baccinta mai sulbi tabi ta lafe,sake maida kanshi yayi yaci gaba da tasbihinta ba tare daya sake daga kanshi ba,saida ya kammala komai,ya sanya kayan baccinsa sannan ya tsaya yana tunanin ta inda zai kwanta,ya jima yana kallonta ta rigar baccin dake jikinta wata kasala na saukar masa,saiya zauna gefan gadon qafafunsa a qasa,hannu ya sanya ya dan daki gefan filon da take kai,shuru ta masa kaman batajiba,saida ya sake sannan ta juyo gaba daya a fusace,cikin rashin saniiii wuyan rigarta yadan zame,saman qirjinta ya fito bata sani ba,idanunsa suka soma kaiwa nan,yayi hanzarin janye idanunsa,saiya tsuke fuska
"Bafa wai zaki dinga zuwa min da duk shigar da kikaga dama bane,saboda haka ki tashi ki saka hijabinki" saidata koma arub da cikinta ta juya masa baya sannan tace
"Ina cewa dai duka gidan nan gidana ne ko?,ko bayaga haka ma ni ban saba kwana da hijabi ba,ban iya ba saidai kayi haquri kam" daga haka bata sake waiwayoshi ko cewa komai ba,hakanan ya qaraci zamanshi,dole ya kashe wutar ya dawo daga gefe daya kaman wanda ya roqa ya kwanta,gamida hade hannayenshi yayi matashin mai dasu karon farko tsahon shekarun da suka wuce dabazai iya tunawa ba.

Qamshinta shine abu na biyu daya ringa takurashi,ya juya baya a banza,yayi kai da qafa amma banza,saida bacci yayi masa mugun kamu sannan ya samu salama.

Sanda ta bude idonta ta fuskanci bacci yayi awon gaba dashi,saita miqe ta sauka daga gadon ta koma saman kujera tayi kwanciyarta,abinda bata sani ba shine tunda ta motsa ya tashi,kusan ya saba kwana shi kadai,ya jima rabonshi daya kwana da wani,hakan ya sanya tunda suka kwanta yakejin banbarakwai baccin bai sama dai dai yadda ya saba ba.

Cikin duhun taji an sureta gaba daya,ihu take shirin saki taji bakinsa cikin nata,bai ajeta ko inaba sai saman gadon,qarfinsa ya aza mata,qasa qasa yace da ita
"Tunda kika fara saikin sauke,anan zaki kwana kamar yadda kika tattare min filo da abun rufa"
"Ce maka akai tsoro nikeji?,kawai banda muradin hada gado dakaine"
"Nasan da hakan,kuma saboda sanin baki da muradin yasa na dora mikishi a matsayin wajibinki" ya fada sanda yake komawa inda ya tashi,saita yunqura zata sake sauka
"Idan kika sauka ban yafe ba" a hankali ta dawo ta kwanta inda ta tashi,jikinta yayi sanyi da kalmarsa,tasan tabbas idan ta sauka din ba ruwan Allah sai Allah ya isanshi ta bita.

Washegari data sauko tuni har sa'ida ta kusa kammala kintsa gidan,rainon anty usaina na wasa na,dama ko a gidan duk yalwar gidan nasu babu mai aiki,ita da yaranta suke kula da gidan,sai masu share can harabar gidan,saita tsaya ta hada breakfast, sunayi suna hirarsu harta kammala,cikin dakinta ta shiga tayi wanka,ta shirya cikin atamfa riga da skert.

Sama ta sake komawa da zimmar dauko wayarta,ta turo qofar bedroom din ta shiga,saita sameshi xaune gefan gado tana latsa wayarshi,kai ya daga suka hada idanu,saiya kasa dauke idanunshi
"Ya salam" ya furta can qasan ranshi,sosai kayan suka fidda kamarta,ta dauke kenta zata gotashi tana gaidashi,baisan ya akayi ba ya tsinci kansa dakai hannunshi ya fincikota,bata zata ba saboda haka jikinsa tayo gaba daya cikin tsoro,saiya riqrta gam,ta dinga yunqurin qwatar kanta amma qoqarinta ya gaza,wani irin abu yakeji yana zagaya jikinsa,idanunsa ya saka cikin nata cikin qanqanin lokaci ya kashe mata jiki gaba daya,saidai duk da haka bata bari hakan ya nuna ba,hade ranshi yayi sannan yace
"Bana gaya miki cewa ba kowacce shiga nakeso ba?" Ranta a hade tana sake son qwace kanta tace
"Nifa gidana ne,kuma sai an kafamin dokar yin dressing?" Girarsa duka ya dage
"Au haka kika ce?,bari na koya miki hankali,gobe idan na hanaki kya sakeyi" daga haka ya juyata qasanshi ya aza mata dukka qarfinsa,yanayin yadda yake matan saiya soma bata tsoro,jikinta ya dauki rawa gaba daya ta zaro ido tana kiran sunanshi,harga Allah yasone kawai ya razanata saboda zuciyarshi da jikinsa ba zasu jure ci gaba da ganinta a haka ba,zaifison taci gaba da kaikawonta cikin hijabi,don bayason dukka abinda zai dinga daga masa hankali yana zaman zamanshi,amma sai gashi yana niyyar wuce gona da iri.

Cikin second daya bacin rai ya rufto mishi,saiya mirgina gefe sannan ya tashi ya zauna yana dafe da kanshi daya sara masa,zuciyarsa ta cunkushe bacin rai ya mamayeshi,fuskar saurayin ta bayyana muraran,zayaso ya sake ganinsa a rayuwarsa,ba shakka duk randa ya sake katarin ganinsa baiga abinda zai hanashi daureshi ba,me yasa ya shiga rayuwar shahida?,me yasa ya haifar da gibi a rayuwarsu da har yau ya kasa cikewa?,saiya miqe kawai ya nufi bandaki ba tare daya sake waiwayarta ba,cikin tsoro ta tashi ta gyara gashinta ta dauki dankwalinta da sauri ta fice daga dakin.


🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Cikin kwanakin duk wata hanya da tasan zatabi ta raunana zuciyar iyayen nata sai data bi,ta kwantar dakai

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment