Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anty zubaida tayi parking,wajen da aka mata gyaran jiki ne na aure,saida suka shiga ta gane wai ita antyn ta kawo ayiwa,narke mata tayi don ita sam bata sha'awa,hasalima tasan cewa asarar kudi kawai za'ayi
"Don Allah anty,iya qunshinma kawai ya isa" daga qarshe dai da qunshi kawai aka tsira ja da baqi,itama antyn aka mata jaa sannan sukayo gida,zuwa lokacin har anyi sallar magariba,saboda haka tana shiga salla kawai tayi,ko abinci bata ciba ya iso suka wuce.

Tun daga falon qasa taga gidan gaba daya kamar ba nata ba
"Sama zaki wuce" ya furta mata yana zama saman daya daga cikin kujerun,bata kulashiba ta shige,saidai tayi tayi qofar dakin nata ya budu amma sam yaqi,haka ta dawo falon tana raba ido zuciyarta fal qunci,da gaske kenan ya maidata saman ya saka nafisan a nata dakin?,zuwa yanzu baya falon,haka ta gaji da zama a falon bacin rai na sake cikata,tilas ta haura saman.

Dakin da yake kallo nashi ta tura,komai na dakin sabo ne kaman yadda kayan falon saman ma suke sabo dai dai dana qasan,abu daya yasa ta gane dakinta ne takacen kayan makeup dake jere saman mudubinta gasunan jere saman sabon mudubinta,ta jima tana qarewa dakin kallo yadda yatsaru yayi wani kyau,dukka colours din ciki masu kyau da kwantar da hankaline,sai data gaji don kanta sannan ta cire kayanta tafada wanka,tana wankan tana kallon lallenta wanda yayi kyau sosai ita kanta ya burgeta.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Kallo daya zaka yiwa fuskarta ka tabbatar da cewa yau din rana ce ta musamman a wajenta,hakanan farincikin da take ciki ayau din shima farinciki ne na musamman.

Ta kasa boye duk wani jin dadi da walwalarta,duk da cewa yadda taso ba duka haka anwar yayi mata ba,dinner daya yaje mata a gaggauce,hatta yau da yake daurin aurensu tana da labarin a makare ya iso wajen,bai kuma jima ba ya koma,saidai duka wannan ba damuwarta bane,da taimakon mima tasan cewa komai zai daidaita,zata kuma samu yadda takeso.

"Qawata jimana" mima dake tsaye dankwali gaban goshi ta fada bayan ta gama yiwa duk yarinyar dake madaidaicin falon nafisan kallon tara saura
"Kowa zaici uwasa" ta fadi a ranta,shigowarta kenan ita dinma batazo da wuri ba,ta jima tsaye daga waje tana kallon yafda nafisa ke wani rawar kai kamar zata taka kan shege
"Gani,ta samu ne?"
"Eh kusan hakanne,amma qawata,bayan sauran event da ango baizo daurin aurenma ance a makare yazo ko?" Tabe baki nafisa tayi da alama tadanji haushin abun
"Hmmmm,wallahi in gaya miki mima,ban sani ba ko waccar matar tashice ta tsaidashi Allahu a'alamu"
Sake tabe baki mima tayi
"Waxai hanashin idan ba ita ba?,kinga abinda nake gaya miki aiko?" Sanyin jikin nafisa yayi,saita zubawa mima ido kawai tana kallonta,da alamun neman mafita take,hakan yayi dai dai da tsarin miman,saboda haka tasa hannu cikin jikirta ta fito da wani qullin baqar leda ta soma warwareta,layune tafka tafka guda biyu wanda jikinsu yake wani iri babu kyan gani ta nuna mata
"Wannan,ki tabbatar ayau ko gobe idan an kaiki kin maqalata gefan gadonki" ta ajeta ta dauko wasu baqaqen garin magunguna da wani mai kama da man shafawa saidai kore sharr yake
"Wadan nan kuma kin gansu?" Tafada tana duban nafisan sosai,alamun maganar da zata gaya mata babba ce
"Kin gansu dakyau ko?"ta sake jaddada mata,gyada kai nafisan tayi tana kallonsu tana kallon mima
"qananu ne amma amfaninsu yawa ne dashi,wadan nan da kike gani idan kikabi doka da tsarinsu to rayuwar gidan aurenki zata inganta ta tafi yadda kike fata,idan kika tsallake doka daya ko sharadinsu to kuwa babu shakka kjn wargaza komai,kuma komai zai iya biyo baya" cikin nuna zaquwa da qaguwa ta gyara tsaiwarta tana cewa
"In sha Allahu ba abinda zai faru,gayamin ya amfaninsu yake" sai data daure ta miqa mata sannan tace
"Daga randa za'a kaiki gidanki zaki jiqa kowanne kiyi tsarki dashi,mai kama da man shine na shafawa,zakiyita amfani dasu har tsahon watanni uku cif cif,sharadinsu sune,idan kika soma amfani dasu babu maganar kwanciyar aure harsai kin kammala,kinga kenan daga randa xaki shiga gidanki harki kammala amfani dasu ba zaki bawa anwar kanki ba harsaikin gama amfani dasu,ammafa daga randa kika gama amfani dasu yasanki a 'ya mace ko?" Sai tayi shuru tana juya idanunta sannan tace
"Uhmmm.....abun ba'a magana kawai" ta furta murmushi na qwacewa fuskarta,shuru nafisa tayi tana nazari,da alamu ta shiga damuwa,cikin zuciyarta tana jin babu dadi,ba qaramin buri ta cuwa first night dinta ba,tayi alqawarin saita hana shahida bacci a ranar saboda tayi tayi anwar ya kaita gidansa na alfarma data sani wanda da yake zaune a ciki amma yaqj,gidan da xai kaitan sam yayi mata qanqanta
"Yanzu har watanni uku kenan ba wani mu'amala tsakaninmu?"
"Eh...indai kinanson samun yadda kikeso,idan kuma ba haka ba,kina iya bani maganina na juya dashi,saiki shirya fuskantar duk wata rayuwa da zaki gani" da sauri ta janye maganin ganin mima ta miqo hannu tana cewa
"A'ah,Allah na tuba don dai wata uku kawai?"
"Ah to nima shi na gani,kuma gidan nan bake kadai bace bare kice akwai matsala,idan ya matsu ya tafi wajen dayar" harara nafisa ta watsa mata cike da kishi
"Tabdi,lallai ma,to bari kiji,nijin kaina nake ni kadai nake wallahi" dariya mima ta kwashe da ita harda tafa hannu tana duban nafisan,yayin da nafisan ta taka tayi gaba ta koma cikin mutane yana yiwa miman godiya,juyawa tayi mima ta fice daga gidan tana sakin murmushi don tace mata ba zata zauna ba akwai inda zata,amma anjima da ita za'a kai amarya.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Sake dawowa yayi jikin qofar karo na babu adadi,tun kafin ya fita daurin aure take cikin dakin kuma taqi fitowa,yayi juyin duniya amma taqi tabude mishi,ko bata fada ba koda bai sani ba jikinsa ya bashi kuka take,dalilin daya sanyashi makara baije akan kariba kenan,bayan yaje ya dawo kuma nanma ko reception din da aka shirya bai tsaya ba yayo gida saidai jiya iyau,daga qarshe badon yaso ba ya yanke tilas ya kira anty xubaida ya gaya mata.

Sakin ajiyar zuciya tayi tana aje wayar bayan gama doguwar waya da sukayi da anty zubaida da kuma zunnurah,ita kanta tanason tayi controlling kanta amma ta kasa,wani irin bacin rai da baqin ciki ke taso mata,tadan dauki wasu mintuna a zaune a wajen sannan ta miqe ta shiga bandaki,ta hada ruwan wanka mai dumi sosai tayi wanka,already ta riga data sauko ta gyare gidan tun sanda taji fitarsa,shi kadai dinne kawai batason gani,amma dole ta haqura ta dauki maganar anty zubaida da zunnurarta,donta wuce komai a wajenta.

'Yar madaidaiciyar kwalliya tayi cikin wani sabon coffe lace me adon silver pink da golden,sosai ta dinkin ya tsaya mata,hakanan lace din yahau fatarta qwarai,ta saka awarwaro dan kunne da sarqa duka silver ta wadata jikinta da turare.

Dai dai nan taji ana sake knocking,ta kalli qofar ta dauke kanta,sannan ta soma takowa ta bude ba tare data tambayi waye ba,anwar dinne yana tsaye qofar dakin sanye da rigar da wando na shadda blue ruwan sararin samaniya,fuskarsa sam babu walwala,hannunsa goye a qirji ya zubawa qofar ido,wanda tana bude qofar idanunshi suka sauka a kanta,rabon daya sanyata a idanunsa tun ranar dinner din nafisa data matsanta mishi sai yazo,sanda ya shirya zai fita tana falon qasa tana kallo,abinda kusan ba dabi'arta bace,zai mata magana bata tsaya saurarenshi ba ta tattare wayoyinta da kayanta ta haura saman ko waiwayoshi batayi ba,sai yaji sam baiji dadi ba,tunda ba dabi'arta bane zaman falo mai yiwuwa yau tayi sha'awa ne gashi ya bata mata yanayi,koda yaje a gurguje ya dawo,amma saiya tadda ta garqame kanta,tun ranar rabonshi da ganinta sai yau.

Bata ankara ba har ya iso gabanta,saiki tayi ta riqe dukka hannayenta cikin lallausan tafin hannunshi,runtse ido tayi tana son zamewa amma ya riqe gam,saita soma qoqarin ganin ta qwace din,gaba daya ya janyota sai gata cikin jikinsa,saura kadan numfashinta ya dauke,ta dinga qoqarin zuqoshi hadi da shaqar qamshin daddadan turarenshi
"Babu dadi ko?,kiyi haquri" ya gaya mata muryasa qasa qasa,tsigar jikinta ta zuba sosai,saita soma kokawar cire jikinta tana tureshi da dukka hannayenta
"Ina ruwana?,meya dameni?,ka sakeni don Allah bana son irin haka"
"Ko baki taba sona ba shahida dole kiji haushi,dole kiji kishi,nasan halin mata fa" yayi maganar yana sakinta daga jikin nashi,saiyadan jaa baya kadan
"Kije qasa kina da baqi" daga haka ya juya ya nufi dakinsa,yayin data gyara daurin dankwalinta sannan ta sauka zuwa qasan.

Mubina ce khadija da huda sai sa'ida da qanwarta ,fuskarta a sake ta karbesu,nan suka sake sosai abinsu cikin gidan,sa'ida ta gaya mata anty usaina na gaidata,can gidan anty usainan dole ta hada wuni saboda 'yan katsina da sukazo duk da basu da yawa,amma wannan karon harda inna kakar anwar,wanda ta manta rabonta da kano,shi yasa wannan karon anwar din ya matsa sai tazo,tunda ta fuskanci shahidan bata da ra'ayi hada wani taro sai ita ta hada a gidanta,saidai sa'idan ta gaya mata anjima zasuzo karban amarya.

Kaman babu abinda yake damunta haka suka dinga sabgoginsu da yaran,anwar din yana daga sama,wani lokaci ya leqo yayita kallonsu bata sani ba,wani lokaci kuma yana daga daki yakejin motsinsu,shi ya aika akaje aka dauko yaran yasa aka kawo mata,yasan koba komai zasu hanata zaman dakin daya tsira,ta kuwa ji dadin zuwan nasu,duk wata damuwa da take jinta liqe da ranta sai takejin ta ragu.

Ko data gama abinci iya ita da yaran suka zauna sukaci,bayan sun gama tasa suka kwashe suka kai mata kitchen zata wanke,tana tsaye a kitchen din ta soma dauraye kwanukan ya shigo,ta waiwaya ta dubeshi ta dubeshi sai kuma ta dauke kai tana ci gaba da wanke wankenta
"Ni ban taba ganin ango irin wannan ba,ba abokai ba komai,ka dawo gida ka samu waje ka zauna?" Take tadin ita da zuciyarta,wanda harya iso bayanta dab da ita bata sani ba,kallonta yake hakanan qirarta da shape dinta yake daukan hankalinsa fiye da qima,saiya dinga tuna baya can da bai taba ganin komai nata ba,saboda a sannan ma'abociyar sanya hijabi ce,a lokacin da yake cike da buri da fatan Allah ya bashi kudin da zai aureta ya mallaketa a matsayin matarsa,yanzu gata a matsayin matarsa,amma wani abu ya ma rayuwarsu karan tsaye,saiya kauda wannan tunanin yace
"Ni ba za'a bani abincin ba?" Gocewa tayi gefe jin maganarsa dab da ita,da alama tsaye yake kenan a bayanta
"Ban dafa dakai ba" ta amsa masa tana ci gaba da wanke farantan ba tare data juyo ta dubeshi ba,shuru yayi yana dubanta,bata taba hanashi abinci ba sai yau,sai baice komai ba ya matsa gefe kusa da inda tukwane suke,ya dauki daya ya dauraye ya ya tari ruwa a fanfon dake kusa da ita,ya hada kayan qamshi ya dora ruwan shayi,ya jingina da jikin kwabar kitchen din yana kallon ruwan yana jiran ya tafasa,duk abinda yake tana kallonshi ta gefen ido,ta rugashi gamawa don haka ta fita tabar masa kitchen din,suna falon yazo ya wucesu da ruwan shayin,harya soma hawa saman saiya waiwayo yana dubanta,hankalin yaran duka nakan arewa24 yace
"Banfa ji haushi ba,wanda ma aka dinga bani a baya Allah ya amfana ko?" Ya qarashe maganar yana daga mata gira,kauda kai tayi yadda ta saba kaman bata ganshi ba,yayin dashi kuma yaci gaba da hawa saman.

Da yammaci suka sake gyare gidan tsaf suka cikashi da qamshi tako ina,har turarukan da bata taba amfani dasu ba sai ranar,kama daga na labule carfet da wanda kebin iska,sun gama kenan sai gashi ya sauko cikin shadda brown sabuwar qarr,kyau uya kyau yayishi,sai taga kamar wannan shigar ta musammance,duk da dama shidin koda yaushe cikin saka sabbin sutura yake,hakanan taji wani abu ya tokareta sanda suka hada ido ya dage mata gira guda,saita aje pillow din hannunta ba tare data bari ya iso inda suke ba ta shige kitchen,tana jinshi da yaran suna uncle kayi kyau,ya gama dan hirarsu dasu ya fice daga gidan bayan ya dauki daya daga cikin motocinsa.*Alqawarin Allah*
46


Sanda takoma dakinta da niyyar shiga wanka taga wayarta na haske,ta jawo ta bude sannan ta duba,saqone daya shigo minti biyar baya
"Haka kike kishina?,ki rage kishina wallahi" kalmar da aka rubuta kenan,tsaki tadan ja tana ture wayar,tasan ba kowa bane sai anwar,batasan me yasa yake wasu abun kamar da gayya ba,sautari yana hakanne kawai donta biyeshi ko yaji tabakinta musamman idan yafuskanci batason magana ko batason kulashi.

Bayan ta fito ta shirya kanta cikin wani lace mai azabar kyau da tsada,qirar qasan switherland,wanda anty zubaida tun a sannan taso ta sakashi ranar da za'a kawota nan gidan amma taqiya sam,blueblack ne me yarfin adon peach a jiki da green dan kadan kadan,gaba daya baki yaran suka saki suna kallonta sanda ta fito kafin daga bisani kowa yahau sharhi,saida suka saka ta koma ta sake kallon kanta a mudubi,ba qarya sukayi ba,kamar amaryar haka ta koma,ga uban qunshi dama hannu da qafa,saita kalli kanta ta sake juyawa ta kalla,har batasan sanda murmushi ya qwace mata ba.

Tana daga dakin ta jiyo 'yar hayaniya,mubina ta shigo ta gaya mata su anty usaina ne suka zo,saita laluba mayafin da zai dace da kayan ta saka sannan ta fita.

Cikin girmamawa suka soma gaidawa,kanta a qasa don harda inna a ciki,karon farko data soma ganin innar a ido,har qasa ta tsugunba ta gaidata,innar ta amsa cikin walwala saboda yadda suka samun shahidan wanda basu tsammaci zasu ganta haka ba,ta gabatar musu da abinci amma sukace a qoshe suke,ganin magariba ta gabato suka soma yin alwala,wanda a sannan anty usaina ta samu ta kebe da shahida,maganganu ta mata masu kwantar da hankali da saka nutsuwa,wanda hakan ya qara mata nutsuwa qwarai.

Suna idar da sallar ayarin amarya suka qaraso,saboda yawansu yawanci a qofar gida wasu motocin suka tsaya,a sannan idarwarta kenan da salla tana saman abun sallarta,wani matsananciyar faduwar gaba taji saidai bata bari ta dirirce kota rude ba,saita dinga ambatar la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla,bata miqe ba hakanan bata yi magana ba tana zaune a wajen tana sauraren hayaniyar mutane.

Mubina ce ta shigo ta sameta
"Yaya wai ki fito,ga baqin nan sun iso" amsa mata tayi tana miqewa mubina tafice ta barta,sai tayi tsai gaban mudubi kawai tana duban kanta,faduwar gaba da fargabarta na qaruwa,powder ta dauka ta sake shafawa,ta fesa turare sannan ta gyara daukin dankwalinta,ta dauki mayafinta daya dace da kayan ta saka ta zira plate din takalmi sha daya shiga da kayan,tanayi tana addu'a sannan ta fito.

Kusa da ita anty usaina ta matsa mata tace ta zauna,basu da wani yawa mutanen cikin falon,sai tayi shuru kawai tana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa,wanda ita kanta batasan dalili ba.

Gudar data karade gidan yasanya suka gane motar amarya ta iso,sai anty zubaida dake zaune a daya barin na shahidan ta kalleta
"Kina addu'a dai ko?" Kai kawai ra gyada mata saboda yadda taji jikinta yayi sanyi kamar an zare mata laka,dukkansu hankulansu nakan qofar har aka shigo da nafisa.

Kanta na lullube kaman kowacce amarya,tana riqe hannun qanwar mummy suka qaraso da ita inda su inna ke zaune,aka gaisa sannan suka damqata a hannun shahidan kamar yadda al'ada tanada,anty zubaida ita tayi musu addu'a sannan suka qarasa da ita gefanta.


*10:30 pm*


Ruwa mai azabar dumi ta hada tayi wanka dashi wanda hakan ya taimaka wajen saukar gajiyar jikinta,ta dawo gaban mudubi ta zauna,sannan ta bude manta ta soma shafawa,tanayi tana sauraren yadda gidan yake shuru,kusan kowa yatafi,daga ita sai nafisa sai wasu daga cikin qawayenta da suka kafe kai da fata kan ba zasu ko ina ba sai ango ya shigo an siyi baki,kusan kafin ya haura samanta tana jiyosu sunata shaqiyancinsu da iya shege,nan ta tattara ta wuce tabar musu qasan,duk abinda take ba cikin kasala da mutuwar jiki takeyinsa,haka kawai takejin zuciya da ruhinta babu dadi.

Cikin mintina qalilan tagama komai,ta mulke jikinta da cream perfume,ta cire sabuwar rigar baccinta cikin kayanta mai santsi da kwantawa a jiki ta zirata ba tare data buqaci bra ba,don jin qirjinta take kaman yana mata ciwo kadan kadan,ta kashe qwan wutar dakin nata tabi lafiyar gadonta,saidai fafur bacci yaqi zuwa,haka ta dinga raba ido cikin duhu tare da tunani barkatai cikin zuciya da qwaqwalwarta,harta gaji da ruf da ciki ta koma rigingine.

Sha daya saura na daren taji shigowar motarsa,ba jimawa taji shigowarsa cikin gidan da fitar 'yammatan amaryar suna mita,ta runtse idanunta sanda taji qarar rufe gate din gidan gaba daya,saitaqi bude idanunta tabarsu a rufen tana fata da addu'ar zuwan bacci.

Ta cikin rufaffun idanunta taga haske ya gauraye dakin,cikin mamaki ta bude idanunta da sauri,saita waiwaya tana duban bakin qofa,sam batasan sa'adda daya bude dakin ba.

Yana tsaye qyam goye da hannunshi,sanye da kayan daya fita dasu dazun,idanunshi zube fes a kanta yana qare mata kallo daga sama har qasa,surarta cikakkiya ta gama bayyana cikin rigar baccin data lafe a jikinta ba tare data sani ba,wani abu yaji yana tsirga masa daga kanshi har qafa,sai ya kasa dauke idanunsa daga kanta,kauda idonta tayi da sauri sannan ta soma lalubar mayafi donta lullube jikinta,bata ankara ba ta jita cikin jikinsa gaba daya ya rungumota ta baya,zuciyarta tahau bugawa da sauri da sauri,kafin tace komai ya rigata
"Wai me yasa kikemin haka ne?,ko don kinga na qyaleki?" Ya fada da muryarsa wadda tayi laushi,saita kasa aiwatar da komai maimakon daa da tayi niyyar qwace kanta,a qalla minti uku sukayi a haka sannan ya janye jikinsa yayi baya ganin idan baiyi da gaske ba zai saki layi,baison hakan kuma ta kasance a lokacin dabai dace ba,ledar daya aje a baya ya dauko ya aje mata a gabanta sanda ta sulale ta zauna a gefan gadon tana tattare jikinta waje daya,don bata da kuzarin dauko mayafin nata,dubanta yake cikin tsakiyar idanunta sannan yace
"Kika samu waje kika zauna,waye zai kaini dakin amaryar?" Ya fada can qasa,so take tace masa kada Allah yasa yaje din indai itace zata rakashi,amma saita kasa fada,tayi banza dashi kawai,harya gaji da kallonta da kuma jiran amsarta,saiya saki ajiyar zuciya yana qoqarin yaqi da abinda yakeji a kanta
"Shikenan,saida safe" ya furta yana takawa zai fice daga dakin,har yakai bakin qofa sannan ta bude bakinta tace
"Karka sake shigomin daki bada izinina ba" fasa bude qofar da yake shirin yi yayi,saiya sake takowa yadawo cikin dakin,sai dayazo gab da ita sannan yace
"Maimaita abinda kikace,banji ba" banza tayi dashi tana kauda kai,saboda yadda ya tsareta da ido,uwa uba kuma kusancinsu da bataso wanda ke haifar mata da wani yanayi wanda yake saka wani abu dake kama da kishi yana taso mata daga ranta,wanda itasam batason hakan,ya tsaya gab da ita da yawa,idan kuma ta biyeshi tasan zai jima bai fita mata a daki bane,wala'alla ma daga qarshe saiya jangwalo abinda xaisa ta bige da kuka
"Ashe ana tsoron iya inji dan mayya,zanyi maganin bakinkin nan" ya fada yana kai yatsanshi lebanta,saitayi saurin kauda kai tana balla masa harara,ya gani sarai wanda har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba
"Yaushe wai shahida ta zama mara kunya me tsiwa ne?,shahidan dana sani mai kunya,idan naje zance bata iya......" Kasa qarasawa kuma yayi,sam ya mance baisan yana sakin layi ba sai dayaga ta tattara dukkan hankalinta kanshi ta zuba mishi ido,dukkaninsu kowa yaji cikin jiki da zuciyarshi,ya tuna musu wani abu ya kuma famawa kowannensu tabo da miki,har ya futa daga dakin yaja mata qofar bai iya sake cewa komai ba.

Dakinsa ya tura yashiga,ya zube bakin gadonshi yana fitar da iska daga bakinsa,bayajin karsashi ko wata walwala ko kadan tattare dashi,yabi dakin da kallo kamar yau ya soma ganinsa,sannan ya miqe ya soma cire kayan jikinsa,ya hada ruwan wanka mai zafi ya dauki towel yashige.

Dai dai lokacin ta hauro saman,tsam ta tsaya tana qarewa falon saman kallo,ya qawatashi matuqa wane falon qasa?,wani kishu bacin rai baqin ciki da tsanar shahida suka cikata,takalli sashen da akace mata dakin shahidan na nan ta zuba mishi harara kamar shahidance a tsaye,sannan taja wata doguwar qwafa kana tayi gaba,tura qofar dakin nashi tayi ta shiga,ko ba'a gaya mata ba tasan wanka yake don ta jiyo qarar ruwa,ta qarasa bakin gado inda ya tube kayanshi ta dauka tana shinshinawa,qamshin kayan ya ratsata kamar ba kayan daya cire ba,ta lumshe ido tana sakin murmushi,ba shakka zata morewa rayuwarta da miji dan gayu,inama ace mima batazo yau da wannan maganin ba,yau da sai tayi ihu iya ihu,ihun da zai hana shahida bacci,idan banda tsabar wulaqanci ta ina amarya na qasa uwar gida na sama?,ita zata yiwa bariki,baridai magani ya kammala abubuwa su fara daidaita yadda ta tsara,kowa zaizo hannu ne,da wannan tunanin tasaki kayan,ta isa bakin mudubin dakin tadan jaye yalolon mayafin data yafawa kanta,tana kallon kanta da kanta ta mudubi cikin rigar baccin data saka,juyawa tayi baya ta tabbatar ko ina yafito,taso ace ma ta tadda shahidane a falo tazo ta wuceta tana kallo kuma babu yadda ta iya,amma babu komai ajuri zuwa rafi da tulu
"Toke daba kwanciya zakuyi ba inake ina wannan shigar?" Ta tambayi kanta da kanta tana riqe haba,saita saki murmushi tana baiwa kanta amsa
"Ko babu me gaba daya ai ba'a hanamu romance ba ko?" Tuna hakan yasake faranta mata ranta,lallai yau zata morewa jikin anwar,saita kai maqura a romancing dinsa.

Tana tsaka da karanta wannan wasiqar jakin yaturo qofar bandakin yafito,sak yayi cikin mamaki yana dubanta,murmushi ta sakar masa tana dan sadda kanta alamun kunya tana tsaye a wajen,sai daya gama qare mata kallo da suturar dake jikinta cikin sanyin jiki sannan yajuya ya rufo qofar bandakin ya soma takowa zuwa cikin dakin,ita tasoma magana
"Na jika shuru ne inata jiran kuma naji ban sake jin motsinka ba" yana shafa mai sanda take qarewa qirarsa kallo tana hadiyar yawu,ta qagu ya qaraso kodan rungumeta ne yayi amma saiya zauna shafa mai,sai yabata amsa dacewa
"Da kinyi zamanki ma,zan qaraso nan din ai" bayanshi ta tako ta tsaya,ta miqa hannu ta dauki man shafawar ta soma shafa masa a baya,wanda hakan yasa wutar jikinsa ta dauke gaba daya,yaci gaba dayi masa magana cikin shagwaba
"Na kasa jira ne,so nake naganka,yau sau daya fa na ganka" sam kasa amsa mata yayi saboda gaba daya jikinsa yadauki wuta,saiya ture hannuwan nata ya miqe don baiso ta sakashi abinda baida niyyar yinsa ayau,ya isa ma'ajiyar kayan sawarshi yacire wasu kayan bacci yakoma bandaki yasanya.

Tana tsaye har yanzu,ya karanceta a nutse,ya fahimci yanayinta,amma ta yaya zaiyuwu su zauna saman shahidan na nan?,hakan saiyake ganin kamar anci fuskarta ne,saboda haka ya dauki ledojin yace da ita
"Muje" saita narke
"Nan fa?,ni nafison wannan dakin" kaiya girgiza yana kewayeta yayi gaba,dole ta biyoshi,amma taso su zauna nan din ko motsin qarya tayi duk da babu wani abu da zata yadda yafaru tsakaninsu tasan zata matuqar baqanta nata rai tare da barinta cikin tunanin ko komai ya wakana?.

Ta fannin shahida kuwa qur'ani ta saka a wayarta qira'ar shaik shuraim wadda ta karade dakin gaba daya ta ratso har falon,hakan yasanya mata nutsuwa qwarai,har taji bacci yasoma fisgarta,sanda zai gifta dakin karatun yaratsa kunnuwansa,a karon farko tun bayan wasu shekaru yaji tausayinta ya ratsashi,a haka suka sauka shida nafisan zuwa qasa.

Amaryar zamani ta yadda da wannan sunan ta kuma yiwa kanta laqabi dashi,saboda haka bata yiwa kanta qauro ko cutar kanta ba taci kazarta sosai,hakanan da suka kammala shirin kwanciya ma,abubuwa suka soma tafiya ta zage sosai tana aika da nata wasannin,tunda

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment