Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Anwar ya samu ya kammala karatunsa cikin wahala da dagiya da kuma taimakom anty husaina wadda ta sadaukar da dukkan wani abu nata don ci gabanshi,yayin da shahida ta zamo mutum na biyu data sadaukar da dukkan wani abu da take ganin ta mallaka saboda anwar din.

Bayan fitowar sakamakonsa wani yayan abokinsa ya kirasu yayi musu tallar aikin d'an sanda da za'a soma dauka,rimi rimi sukayi komai da karime karime da qarfafawar gwiwar shahida data dage kan sai yaje,sai kuma batun tafiya training ya taso,a nan ne ya sare saboda lissafen lissafen abubuwan da za'a buqata daga garesu,wanda kusan duka harka ce ta kudi,koda wasa bazai doshi anty husaina da wannan batun ba saboda yasan cewa wahala ce da nauyi kawai zai dora mata,saiya shiga neman kudi babu ji babu gani,sai lokacin da tafiyar ta matso sannan ya shaidawa anty usaina,ta masa addu'a sosai,ranar da zaiyi sallama da shahida ta dauko baqar ledar viva ta dire masa.

Sai daya gama kalla sannan ya dago yana dubanta,baisan ma da wanne baki zai mata magana ba,da wanne harshe zai gaya mata yadda take a wajensa?,kaya ne da tasan cewa zai iya buqata a ciki,wanda ko bata fada ba yasan a qalla zata kashe dubu biyar,Da hannu ta masa nuni dole yayi shuru,tamkar ba zasu rabu ba ranar,ji yake kaman idan yaje zaiyi shekara ne bai dawo ba.

Kwanansa uku acan shida wasu mutum biyar suna cin wuya saboda ance sam babu sunansu cikin list din,bawai kuma babu dinba,yanayin qasarmu ne kawai,an suba wadanda sukafi kowa rashin galihu an cire sunayensu daga list din an maida gurbinsu dana wasu,hakanan suka tattara suka dawo gida.

Randa shahida ta ganshi ya dawo ba qaramin jin takaici tayi ba,har kuka ta kusa yi,shi ya dinga lallabata yana bata haquri
"Duk randa Allah ya horemin abu na farko da zan fara ginawa shahida shine makaranta,zanyi irin makarantar da yaran masu kudi suke zuwa,irin makarantar da suke karatuna zuba yaran masu qaramin qarfi,su samu irin ilimin da yaran masu hannu da shuni suke samu,su samu gata da kulawa irin na yaran masu dashi"shuru shahida tayi tana karantarsa,har cikin zuciyarsa maganar take fitowa saboda yadda hakan ya bayyana saman fuskarsa
"Yaran marasa shi suna shan wahala,suna shan wahala matuqa wajen neman ilimi,bayan sun samu karatun da qyar ya zamana karatun ya kusa zama na banza,sakamakon yadda aiki ke musu wahala,wanda wasunsu daga qarshe sakamakon karatun nasu kusan dai dai yake da takardar tsire" nan ma dan shuru yayi yana hadiyar yawu,sosai lamarin ke sukar zuciyarshi,sun jima suna tattaunawa game da halin rayuwa sannan daga bisani sukayi sallama.

Anwar bai gajiya ba bai kuma sare ba yaci gaba da neman aiki baji ba gani,burikansa din nan guda biyu su yake fafutukar ganin ya cimmawa,yana tsoron shahida ta kammala secondry ba tare daya samu aiki ba,babban burinsa a duniya suyi aure sanda zata kammala makaranta,ya kuma tsaya mata tayi karatu kaman yadda takeso harsai tace ya isheta,yana da burin yi mata halacci kwatankwaci koma fiye da yadda tayi masa.


*BAYAN WATA HUDU*

Kallonshi take tamkar ta zabga masa mari haka takeji,saidai hakan ba maiyuwuwa bane tunda ba tarbiyyarta bace,dawowarta kenan daga gidan anty amina ya tsaidata,sam batasan yana biye da ita tun daga qofar gidan anty amina ba cikin motarsa saida ta iso layin nasu,ta shiga gida da niyyar ba zata saurareshi ba yadda yaketa zabga aike yasa umma tace ta fita ta saurareshi.

Hakanan cikin jikinta takeji kamar akwai wanda yake kallonta,kamar anwar na wajen tare dasu,a hankali ta kalli damanta,shine kuwa sanye cikin jibgegiyar rigar sanyi da wandon jeans,kasancewar ana cikin yanayin sanyi,yayi kyau matuqa,kai kace wani ne ko dan gidan wani,kyansa ya sake fitowa,fitilun motar daya bari a kunne sun haskeshi sosai kaman yadda suka haskesu,idanunta cikin nashi saiya ja da baya ya juya ya soma barin wajen.

Wani tashin hankali ya ziyarceta,da wanne baki zata yi masa bayani?,ganin yadda hankalinta ya wajen ya sanya saurayin shima juyawa yana kallon wajen saidai baiga komai ba,bata sake bi ta kanshi ba ta shige gida da hanzari,wayarta ta laluba ta soma kiran layin anwar din,saidai harta qaraci ringing dinta ta gama bai daga ba,hakan ba qaramin daga mata hankali yayi ba,ba zata manta ba shekaran jiya suna hira yake ce mata
"Shahida tsoro nakeji,gani nake kaman zan rasaki,kaman kinfi qarfina" cikin mamaki tace
"Me kake fada anwar?" Murmushi yayi saidai ya taba har zuciyarsa
"Shahida...kina kallon kanki a mudubi kuwa?,irinki ba qananun mutane ke aurenki ba....ina tsoron kada wani mai motar yasha gaba na" sosai taji haushi harma ta shige gida ta barshi ko sallama basuyi ba,da qyar yasha kanta ya waya,to jiya bai samu zuwa ba kasancewar ya samu dan wani aiki yana kulawa wani da provision dinsa cikin anguwarsu,ladan da yake bashi ba wani mai yawa bane kasancewar kanti ba wani girma gareshi ba,amma ya karba yana yi saboda ba mutum ne shi mai raina sana'a ba komai qanqantarta.

Kusan ranar kwana tayi tana kiran layin nashi amma ko sau daya bai daga ba,daga nashi bangaren hankalinsa a tashe yake,hakanan zuciyarsa ke wani irin tafasa,kishi ne ki cinsa sosai,fargaba ta lullubeshi,fargabar kada ace zancansa ne zai tabbata zai rasa shahidansa,duk sanda ta kirashin bai daga ba sai yaji wani qunci na sake ziyartar zuciyarsa,bai iya daurewa yana jin kiranta na shigowa amma ya kasa dagawa,daga bisani tilas ya kashe wayar duka yana fatar ta haqura tayi bacci.

Kwana biyu ba anwar din ba dalilinsa,hakan ya daga hankalinta don har wajen kai sadaka bata ganinsa,da yammacin kwana na ukun bayan ta dawo daga kai abinci wanda yanzu ajewa kawai take wajen baba ado dake wajen ya raba a aiko da botikin don fir anwar yace ta daina kaiwa,shiryawa tayi ta tadda ummanta zaune tana jan carbi bayan ta idar sallar la'asar
"Umma....zanje gidan anty amina"kai ta daga ta dubeta sannan ta shafa addu'arta
"gidan amina kuma?,makarantar fa?"kanta tadan sunkuyar tana wasa da farcenta
"hadda ake karba,kuma ni na bada tawa tun jiya" dan jim tayi sannan tace
"Shikenan,ki gaisheta....yauwa....kice mata yaushe za'a fitar da ankon umaiman,ki gaya mata lokaci yana qurewa fa"
"Tohm umma....saina dawo"
"Zan rakaki yayaa" cewar mubina wada ke shirin islamiyya ta fada bayan ta watsar da hijabinta wajen
"Babu inda zaki,makaranta zakije" cewar ummanta,tana jiyo ihunta ta saka kai zata fice tana dariyar rikici irin na mubinan,dai dai lokacin abbanta ya shigo,saita koma da baya tana masa sannu da zuwa yayin da yake tambayar abinda aka yiwa mubinan
"Wai gidan anty amina tace zata bini,kuma islamiyya zata"
"Ke ina taki islamiyyar?"
"Hadda ake amsa abba kuma na bada tawa tuni..."
"To ma sha Allahu,dama inason ganinki"
"To abba gani" ta dawo tana dawowa saman kujera 'yar tsuguno ta zauna,
"Shahida....ina fatan ba wani abune ya shiga tsakaninki da yaron nan ba anwar?"
"Abba meka gani?" Ta tambaya a sanyaye
"Kwana biyu bana ganinsa yana zuwa" shuru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,dukkaninsu ummanta da abbanta wani irinso sukewa anwar din,halayen anwar abun sone,nagarta gareshi wadda ta zama tilas ko waye kai ya burgeka
"Uhmmm...bakice komai ba"
"Abba in gaya maka?" Mubina dake goge hawayenta ta fada,harararta shahida tayi amma hakan baisa ta fasa magana ba
"Wanine mai mota yazo...umma tace taje ta sallameshi,shine yaya anwar ya ganshi ya tafi"
"Ubanki mai shegiyar magana" umman ta fada tana kai mata duka
"A'ah hadiza barta ta fada....kice kawai kin soma shanshano wani ne....ke shahida tashi ki tafi,kema zamu gamu dake"
"Duk abinda kaga dama ka fada,tunda dai ba zuciyata ka shiga ka hangi haka ba shikenan na gode Allah" tun kan ta fice daga soron nasu ranta ya soma baci,saboda taji suna gab da kaurewa da halayyar tasu da suka saba,saitayi maza maza ta ficema don kada ta jiyo abinda wunin yau zai sa ta kasa walwala,sam bata iya daurewa duk sanda wani sabani ya hasu tafi kowa jin zafin abun,tqfi kowa shiga qunci,ta rasa me yasa dukkansu basu haquri da juna,kowa kaman jiran kowa yake,kamar wadanda aka sakawa hannu cikin mu'amalarsu.

Ba dadewa ta isa gidan anty amina,ta taddata tana wanki ta saka mata hannu suka gama tare,tanata tambayarta anwar kwana biyu bai leqo ba batace komai ba,har sai da suka gama suka zauna dakinta suna ninke wasu kayan da suka soma bushewa
"Anty....nifa zuwa nayi ki mana sasanci da anwar"
"Sasanci kuma,me ya hadaku kenan?,yau kwana uku kuwa da zuwanshi ya gaidani"ana ya gobe abun zai faru kenan?,shahida ta raya a ranta,batasan ma yazo din ba,jininsu ya hadu da anty amina,gashi kuma ba wani nisa sosai tsakanin gidanta dana anty usaina,don har zumunci ma suke yanzu ta sanadinsu,tsaf ta kwashe komai ta gayawa anty aminan,a take tasa shahidan ta kirashi,saidai harta gama ringing bai daga ba
"kin gani ko anty?"shahidan ta fada idanunta na cikowa da qwalla
"Bari na kirashi da wayata" anty amina ta fada tana daukan wayarta,ringin biyu ya daga cikin girmamawa
"Anty amina...da kanki?" Ya fara fada cikin girmamawa
"To ya zanyi?,diyata ta dagamin hankali?"dariya ya danyi
"Shahida ko?"
"Ita mana"
"Karki qona katinki anty bari nazo"
"Da kuwa ka taimakeni karta fashemin gata nan ta cika fam" da haka sukayi sallama tana duban shahidan
"Shima a muryarshi kadai ya isa kasan cewa yana cikin damuwa da kewarki,wanne irin so kukewa juna shahida?" Kunyace ta kamata saita soma sinne kai.

Ba'ayi minti talatin ba cikakke d'aya daga cikin yaran anty amina suka shigo suna cewa ga uncle da yake haka suke kiranshi,anty amina ta saka hijabinta tace suce mishi ya shigo.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGπŸ™πŸ½*
πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*Alqawarin Allah*
1️⃣0️⃣


A nutse cikin sallama ya shigo ta daga kai a hankali ta kalleshi saboda ita kadai tasan yadda tayi missing dinshi,shi dinma idanunshi na bisa kanta ji yake kamar ya shekara dari bai ganta ba,amma duk da haka saiya gintse saboda tuno ganinta da yayi da wani,daya daga kujerun falon ya samu ya zauna suka gaisa da anty amina sannan ta soma tambayarsa
"Wai me ya hadaka da shahida?,duk ka firgitamin diya?"
"Ta firgitani dai anty...bakiga har rama nayi ba?" Murmushi anty aminan ta saki,yadda sukeson junan nasu na bata sha'awa,bai boye komai ba ya gaya mata sannan ya dora da cewa
"Wallahi anty wani irin kishine dani,ina da matuqar kishi kan abinda nakeso,ranar dana ganta wallahi anty ban iya bacci ba"
"To kayi haquri mr kishi....bari kaji me ya faru" ta shaida masa kamar yadda shahidan ta gaya mata,nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana jin kaman an sauke masa qaton dutse daga zuciyarsa,sai a sannan ya sami salama
"A rude nake anty,shahida ba ruwanmu bace mu talakawa,hankalina a tashe yake kada wani ya qwace min ita"dariya ya baiwa anty amina sosai har sai data dara
"karka damu anwar,shahida taka ce in sha Allah,yo shahida muka bata wani bakaiba ai inajin fiya fiya zata sha ta mutum" sosai anty amina ta baiwa shahidan kunya,har sai data diba a guje ta shige dakin anty aminan,shima ya miqe ya fice yana dariya.

A dakin ta taddata ta dubeta
"To laila majnun,saikije ku sameshi tunda na kashe case din,saiki kula a gaba"
"Na gode anty amina ta"
"Eh kyace haka mana tunda na dawo miki da hasken rayuwarki ko?" Dariya ta tuntsire dashi sannan ta miqe ta zura hijabinta ta fice.

Yana tsaye a soron gidan amma qofar fita yake kallo,tadan tsaya kadan a bayanshi,a jikinsa yaji tana wajen saiya juyo a hankali idanunsa zube fes a kanta,takowa yayi har sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sannan ya tsaya,a hankali cikin wata murya dake cike da mayen so yace
"Nayi kewar wannan kyakkyawar fuskar,wannan ruhin ya hana ruhina samun barci bare ya samu salama,na cika da fargabar cewa na rasa hasken idaniyata,ashe abun duka ba haka bane" sosai kalamanshi suka sanyaya mata rai cikin daqiqu kadan,tayi qas da kanta tana fidda murmushi
"A'ah dago kanki sosai don na samu qwarin gwiwar fada miki albishir din danaso yi miki tun rannan mai mota ya korani"
"Don Allah ka daina zancan mai motar nan honey haba"
"Na daina" ya fada yana murmushi
"Na samu aikin kamfani Allah ya taimakeki...wani maqocinmu ne ya sama min,kwana goma sha biyar zan dinga aikin kwana,kwana goma sha biyar aikin wuni,zasu dinga biyana albashi duk wata dubu sha biyar" sosai fuskarta ta washe da fara'a tana jin farinciki na ratsata,tana jin burinsu ya soma daukar hanyar cika,rasa inda tsoma ranta zatayi har sai daya tsaya yana kallonta cikin mamaki,sun jima a soron gidan anty aminan kafin ya sanyata ta tattaro kayanta tazo su wuce gida,napep ya tsaida musu har qofar gida,sanda suka sauka ta zaro kudi zata biya ya harareta ya ciro daga aljihunsa ya biya,dariya kawai tayi,ko yaya idan yana da kudi ko iyakarsu kenan jikinsa baya yarda tayi masa hidima da kudinta,nan ma sun dan jima kafin suyi sallama ta wuce gida shima ya wuce.

Cikin taimakon Allah ya soma zuwa aikinsa,saidai babban qalubalen daya soma fuskanta shine na rashin kudin mota,tafiya ce mai nisa tsakanin unguwarsu zuwa kamfanin haka yake niqar gari ya tafi,duk da cewa ya saba tun sanda yana makaranta amma tafiyar bata kai ta makaranta nisa ba,sai kuma abincin da zaici shima saiya dawo zai jiqa kwakinsa yasha musamman idan aikin dare yayi zai dawo da safe,duka wannan bai dameshi ba tunda yasan cewa komao lokacine,hakanan bai yarda shahida ko anty usaina sun sani ba saboda baiga dalilin da yana namiji zai dinga daura nauyi wa mata ba,a haka ya cinye watanshi guda,saidai kafin cikar watan ya fada yayi baqi,hakan ya sanya shahida ta sanya ayar tambaya a kanshi.

Ranar daya amso albashinsa yazo da daddare,duka ya zube mata albashin nasa yana dubanta
"Me zanyi dashi honey?" Ta fada bayan ta gama saka musu albarka
"Inason ki dauki iya abinda ranki yayi miki,a matsayin albashin mijinki na farko" kai ta girgiza tasan ko tace masa a'ah cewa zaiyi bata isa ba saiya dauka,saboda haka tasan maganinsa.

Da fari ta ware wasu kudaden tace wannan kudin kayan abinci da zai siyo ya dinga dafawa yana tafiya dashi kamfani,ta sake ware wasu tace ya sake dinka kaya kala guda duk wata zai dinka kala daya,ta sake ware wasu tace ya riqe ya kashewa ne,sannan ta cire wani abu a ciki tace wannan ya kaiwa anty usaina ita yafi cancanta ta sanya albarka,next month kuma idan ya sake amsa to ya fara ajiya saboda lalurorin yau da kullum,duk sai data gama kasafin ya cakude kudaden waje daya sannan yace
"Qurun qus kin gama tatsuniyar taki?,toni ba haka nakeso ayi ba,da safe me mike ci idan zaki makaranta?"baki tadan cuno
"Kome meye ya samu"
"Good" ya fada yana cire wasu kudi ya aje
"Indomie da qwai nakeson ki koma ci" idanu ta zaro tana kallonshi baki bude
"Honey...me kake fada ne?"
"Abunda kunnuwanki suka jiyr miki.....wannan kuma kudin kashewarki na wata gud....."
"Kaga...don Allah ka tsaya ka daina wannan lissafin mana" nan sa'insa ta kaure tsakaninsu,da qyar ya yadda da nata lissafin bayan ta masa alqawarin wata na gaba ta yadda za'a sata cikin kasafin,saidai duk da haka yayi cancel kudin kashewarsa ya bata dole ta amsa saboda ya kafa mata sharadi.

Koda ya kaiwa anty usaina ma itama cewa tayi ba zata soma amsa yanzu ba,ya aje wajensa zata masa magana idan lokacin daya dace yayi,haka ya dawo dasu ya miqawa shahida
"Shikenan...zan saya banki na dinga tara maka,duk sanda kake da buqata saika amsa" washegari kuwa ta sayi bankin ta zuba masa harda kudin daya bata,ta nuna masa sannan ta roqeshi
"Don qaunar da kakemin kada kace a'ah,za'a tara ne ka siya abun hawa ko keke ne,ko baka fadimin ba nasan tafiyar qafa kake" da qyar ya amince da shawararta,donshi a son ranta tayi hidimar gabanta kawai dasu.

Wata hudu cif da fara aikinsa komai ya soma tafiya babu laifi,ta wanni fannin abubuwa da dama sun soma sauqi,cikin godiyar Allah da yadda da cewa komai lokaci ne.

Cikin haka aka fitar da ankon bikin umaima,wadda take cousin ce a wajenta,ranar data kawo musu ankon wuni tayi a gidansu,har dare tana nan,sanda ta tashi tafiya anwar yazo shahidan na wajensa,mubina ce ta rakota tana nanata mata idan ta tashi dawowa ta kawo mata alawarta,qarasawa tayi wajensu shahidan tana mata sallama daga bisani tace
"Ina zuba ido saikinzo siyan ankon,kuma wlh baki isa ba ba wani daya da zaki duka biyun zakiyi"
"To ummata" ta fada tana hararta,don batason ta tada zancan a gaban anwar din,sun riga da sun gama maganar su tun cikin gida,da haka sukayi sallama umaima ta wuce.

"Wai ina bankin nan kuwa?"
"Yana cikin gida"
"Idan yana kusa daukomin shi idan yana kusa" bata ce komai ba ta shige gidan ta fito dashi,bankin qasa ne ya amsa saiya sakeshi ya fadi take ya fashe kudin ciki ya bayyana,baki ta bude tana zaton itace bata bashi dai dai ba ya riqe ya fadi haka,sai taji yace
"Yauwa yayi dai dai,tayani qirgawa" cikin mamaki ta duqa ta soma tayashi hada kudin,bayan sun gama hadawa ya miqa mata yace ta irga,cikin murna da mamaki tace
"Da gaske ne kudi wawayene....ban zaci zasu kai haka ba wallahi" murmushi shima ya saki,walwalar da take kawai ta isheshi farinciki
"Kije ki sayi ankon ko kala nawa ne,saura kiyi dinki,idan ba zasu isa ba kiyimin magana" ranta ta ba'ta sannan tace
"Me kake fada ne?,kudin keken naka zaka bani kace nayi anko bayan sunkai kudin keke sabo harda canji?,kuma ma tuni umma tace zatamin daya abba guda daya"
"Duk bansan wannan ba....abinda kawai na sani shahidana zata saka kaya kamar yadda kowacce mace zata saka...kada kice zakimin musu indai baso kike raina ya baci" kaita duqar
"Allah ya baka haquri" dole ta fidda kudin ta sayi ankon kala biyu mayafi da abun daurawa,cikin sati uku suka shiga hidimar biki amma hakan bai hanata ganin anwar ba,shima hakan ya masa dama tunaninsa rashin ganinta.

Ranar da za'ayi dinner tun safe suna gidan kwalliya,qarfe biyar da rabi na yammaci ya kirata yazo ganinta tana ina,itama yana ranta don jiya basu samu ganin juna ba basa unguwar kwata kwata suna can aikin snacks,ta kwatanta masa gidan kwalliyar,ya gane gidan saboda cikin anguwarsu ne.

Sanda ya iso tuni an gama mata tata,zata wuce kuma gidan bikin ta saka kayanta kafin a soma dibansu zuwa wajen da za'a gudanar da shagalin.

Dan kwalinta a hannu ta fito soron gidan don kada ya bata mata kwalliyarta,dubansa tayi yadda yayi mata kyau cikin wani sabon yadi blue black,wanda aka yiwa dinki irin na matasan zamani,bata mancewa da ita yayi shawara kafin ya sayi yadin ta kuma zabar masa dinkin qarshen wata sanda aka biya salary ya cira a ciki yayi,anwar nada wata baiwa ta daban,idan yayi dressing kai kace shi din wani ne,daga kai yayi daga danna wayarsa da yake yana dubanta,subhanallah ya fada a sarari,wani azababben kyau yaga ta qara masa,kai kace ba shahidarsa bace,sai yayi sak yana ci gaba da dubanta,abun ba qaramin dariya ya baiwa shahida ba har sai data d'an dara
"Yaya anwar wucewa zanyi fa ana jirana.....tun daxun kake kallona sannan kuma kai baka ce komai ba" ta fada a shagwabe tana langabe wuya,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dubeta
"Ba inda zan barki ki fita a haka shahida....gaskiya zuciyata ba zata iya jurewa wasu su kalleki a haka ba a filin Allah wajen bikin dake cakude da maza da mata"
"To a yaya kakeso na fita?" Ta fada tana cuno baki wanda hakan ya sake tafiya da imaninsa,dan qaramin bakinta mai dauke da pink din labba yasha maroon din jambaki
"Mafita kawai ki wanke fuskarki" idanu ta zaro tana dubanshi
"Haba yaa anwar....haba don Allah" ta fada kaman zatayi kuka tana dan buga qafarta,fuskarsa ya hade sosai,harga Allah yana da wani irin kishi akan shahidan,yana jin kaman zai mutu idan wani ya zuba mata idanu bare akai ga batun furta yana sonta
"Ashe kuwa zaki shekara a soron nan,don na rantse ba zaki matsa ko inaba indai fuskarki da wannan kwalliyar" tasan cewa da gaske yake saita rasa ya zata masa,hakan yasa ta juya ciki ta yiwa amarya umaima magana,ita tazo ta roqa mata alfarma wanda daga qarshe yace saidai ta cire eye lashes din da aka qara mata don nata ma ya isheta,sannan kuma a goge wasu abubuwan da aka sa mata a fuska,saida akayi hakan sannan ya qyaleta,duk da haka a gaba ya sakata tana gaba yana bayanta,sai faman sakin ajiyar zuciya yake,duk da an rage kwalliyar gani yake kowa ma kallonta yake,adaidaita ya tare mata bai barta ba sai daya rakata har qofar gidan bikin,yana mata sallama zai juya itama ta tubure kan dole yaje wajen bikin,yasan da biyu tayi hakan don bai fiya zuwa wajen fate fate ba,to amma abinda bata sani ba gata tayi masa,don har yanzu hankalinsa bai aminta ba da zuwanta wajen ita kadai,gani yake tafi kowacce mace kyau,hakanan idanun kowanne namiji yana akanta
"Zanje na dawo,idan kun gama shiryawa kimin magana" tana masa dariyar cin galaba ta shige ciki.

Qarfe shida aka soma daukan 'yammatan,a sannan tuni ta yiwa anwar waya,shida da rabi ya kirata yace ta fito yazo,su biyu ne ita da 'yar anty umma yayar ummanta,ga mamakinta yana jingine jikin wata qaramar mota mai kyau qirar kia,ya sauya shigar jikinsa,wannan dinma yadine wanda tare ya siyesu da wancan,saidai wannan ruwan madara ne lallausa,shima bamai tsada bane amma sai taga kaf mazan wajen ba wanda ya kamoshi a kyau duk dacewa jayan jikinsu yafi nashi tsada nesa ba kusa ba.

Shi dinma gaba daya saiya daina ganin 'yammatan dake kai kawo a wajen,ita kadai take gani cikin dinkin ankon da ya amshi fatarta fiye da zato,kowa idonsa cikin na dan uwanshi a haka ta qaraso,baice mata komai na sai gaban motar daya bude mata ta shige,shima ya bude sit din driver ya zauna bayan kubra 'yar anty umma ta shiga gidan baya ya tada motar.

Saitake jinsu yau kaman rana ta musamman ce a wajensu,wani farinciki taji yana ratsata,ta samu kanta da addu'ar Allah ya shiga lamarinsu ya buda ma anwar din,motar tayi masa kyau qwarai da gaske kaman tashi
"Wani abokina ne ya dage lallai lallai yau sai na amsheta na dana,tun tana sabuwa yamin tayi ban taba danawa ba,kinga kuma bai kamata naqi ba karya dauka wani abun ne na daban kuma" kai ta gyada yayin daya dinga satar kallonta lokaci zuwa lokaci,har bintu ta fahimta ta d'an masa tsiya,kunya ta sanya shahida daukan wani plate data gani ta saka jikin redion motar,tadan qaro volume sanda taji batajin me yake fita daga cd din,waqa ce ta hamisu breaker waqar jarumar mata,sautin waqar ya ratsa motar,kidanta ya fita sosai ta speakers din motar ya karade ko ina,har ta saka hannu zata kashe anwar ya daga mata hannu alamar ta barshi,shuru ya ratsa motar saidai gaba dayansu waqar na ratsasu ne,ji suke kaman su suke rerawa junansu,shurun yaci gaba da yi musu jagora har zuwa inda za'a gabatar da bikin.

Sai daya rakata har ciki yayi mata mazauni,ya kuma gaya mata bai yadda da shiga rawa ba sannan ya fito ya dawo cikin motar ya zauna,wanda ya faka ne a bakin titi,sai yabar murfin motar a bude iska na shigowa qafarsa daya a waje.

Awa guda da fara gabatar da bikin yana zaune yasa sauraren redio
"Yauwa ga wani can....salamu alaikum" yaji an ambata,kanshi ya dago yana dubanta sannan ya amsa,matashiyar budurwa ce wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da d'aya,sanye cikin doguwar riga da siririn mayafi,fuskarta saye da tafkeken glass,gabanta ne yayi mummunar faduwa saboda cika mata idanu da kwarjini da yayi mata,uwa uba kyau data jima bata ganshi tattare da wani d'a namiji ba,da qyar ta tattaro miyan bakinta tace
"Don Allah bawan Allah ko zaka taimaka ka duba mana motarmu?" Tayi maganar

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment