Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito,aikata hakan kuwa dai dai yake da tafka babban kuskure Da zata tafka,bata da wata abokiyar shawara ko qawa shaqiqiya kamar mima,ita kuma ga abinda ya hadasu wanda take tunanin ya rabasu kenan,amma daga bisani taga me miman tafi buqata?,kudi,ta baiwa kanta amsa,tana iya lallabo miman ga sakar mata bakin aljihu,taji shawararta kan lamarin,idan yaso ta toshe mata baki da kudi,suyi yarjejeniyar idan komai ya fada duk abinda tasamu za'a dinga rabawa gida uku,ita tadauki biyu,miman ta dauki daya,da wannan shawarar tata ta soma kiran layin miman,saidai duk layin data kira nata sai a gaya mata a kashe yake,kwana biyu kenan tana kiran layin amma yaqi shiga,daga bisani takoma kiran duk wanda tasan yana alaqa da miman,amma kowa sai yace mata baisan inda miman ta shiga ba,shima kwana kaza yana nemanta,abun duniya haka ya sake taruwa yayi mata yawa,lallai idan batayi da gaske ba wankin hula yana neman kaita dare,gwagwarmayarta ta shekara da shekaru tana neman tashi a banza.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Sam gaba daya bacci yayi qaura a duniyarra cikin wannan daren daya cika da sanyi da kuma nutsuwa,duk yadda taso tunkude tunaninsa abun yaci tura,da gaske tunaninsa so yake ya hargitsa zaman lafiyarta,anya ko lafiya yake?,lafiyarsa qalau kuwa,yace idan tace yatafi zai tafi kada dai ace da gaske tafiyar yayi?,gabanta yayi mummunan faduwa da wannan tunanin ya fado mata,ta miqa hannu ta dauki wayarta ta kunnata haske yakawo,saita zuba mata idanu kamar me tunanin amfanin da wayar take a rayuwar mutum,kwanaki da yawa da suka shude haka ta tsinci kanta da saurare da kuma tsammatar ganin gilmawar waya da lambarsa tacikin wayarta saidai shuru maqatau,ta kwatanta ta kirashi yafi sau nawa amma saita kasa,kamar yanzun data nemo lambarsa ta tsaya tana kallonta,saita maida wayar kuma ta ajiye,ta sake maida kanta saman filo,tana jin wani rauni yana ratsa zuciyarta,tana jinta kamar wata marainiya data rasa uwa da uba,tanajin tamkar ta rasa wani muhimmin sashe daga cikin rayuwarta,sanyin jiki da kasala suka sake qaruwar mata,da qyar tasamu bacci ya sureta cike da mafarkansa barkatai.

**** **** ***** ****


Tana idar da sallar asuba ta sake kifewa idanunta cike da wani azababben bacci wanda rashin samun isasheshen baccin da batayi ba daren jiya ya zamto sila,tun daada bata leqota har nauyin baccin yasa tadinga leqota don ta gani ko lafiya,saidai ta leqo ta koma haka ta dinga sata zirga zirga,inda daga bisani data gaji ita kadai tasoma mita
"Wannan yarinyar bata gama sanin ciwon kanta ba,ya zama dole taje asibiti,don naga alama idan na qyaleta ba zuwa zatayi ba,haka zatayi zama da abu a jikinta bata sani ba,taje tayi wani gangancin ma ya zame mata matsala"

Cikin nutsuwa yayi sallama a tsakar gidan,sanye da shadda gezna dinkin tazarce ruwan toka mai kyan kala,qafarsa saye da rufaffen takalmi na maza,kansa babu hula,idanunsa cikin farin glass,sumar kansa tayi kyau sai qyalli take,hakanan sajensa da shima yasha gyara yayi kyau yana sake fidda kyau da kwarjininsa,qamshi kawai ke tashi a jikinsa mai sanyi,sai wata 'yar rama daya danyi,wanda duk wanda yasanshi idan ya kalleshi xaiga hakan.

Baki daada ta kame sanda yake shigowa gidan yana kallonshi fuskarta fadade da fara'a,murya qasa qasa tace
"Idonka kenan?" Saiya saki wani murmushi mai sanyi yana zama kan kujera 'yar tsugona da daada ta tura mishi
"To ya zanyi daada,tunda kema kinqi cetata akan kari"
"In sha Allahu yau za'a yita ta qare,ai ta nuna yadda akeso,sauran aikin kwa qarasashi a gida,nasan tayi laushin da bazaka wani wahala ba" ji yayi kamar an masa rahama,wani qayataccen murmushi ya subuce masa
"Allah ya tsundumaki a aljanna daadata,bansan wacce irin qauna kikemin ba"
"Dukkan mutumin qwarai ai abin so ne a wajen kowa,abu daya zaka yimin,don Allah kodan gaba ka zama mutum mai bincike kan dukkan lamari kafin ka yankeshi,idan yayi maka tsauri na baka dama ka nemeni,sannan kuma....abinda yafaru tsakaninka da ita,duk da bakasan waye ya kitsashi ba ya kamata ka bincika saboda kore wasu wasi a nan gaba"
"In sha Allah daada,matsalarmu ma na gama bincike,sai gabar daukar mataki da nake kai"
Miqewa tayi ta yafa mayafinta tana cewa
"Ina zuwa,shiga tana ciki,zan shiga maqota yanzu zan dawo"
"Toh" ya amsa bakinsa har kunne yanajin wani farinciki da nishadi na yawo dashi,yana tsaye har daada tafita daga gidan,sannan ya waiwaya yasoma takawa cikin nishadi xuwa cikin dakin.

Ba kowa a falon,hakan ya tabbatar masa kenan tana uwar dakan,baiko tsaya na sai daya dangane,yayi tsaye kawai a kanta yana kallonta wani farinciki na ratsashi,cike da mamaki yake kallonta,ta sake haske gami da wata 'yar qiba kadan,kumatunta sun sake cikowa,fatarta kamar ka latsa jin yafito,tsigar jikinsa ta zuba sanda yakalli labbanta da suke qyalli kaman wadda ta shaf musu man lebe,saiya kasa daurewa,ya tsugunna a gabanta a hankali ya miqa hannunsa da niyyar shafasu yaji yadda suke.

Cikin baccin nata tadinga jinta kamar a wani baqon waje,ta dinga jin kamar anwar na wajen,kamar kuma ana cewa tashi gashinan,a hankali tasoma bude idanun nata,kamar a mafarki kamar almara taganshi tsugunne a gaban nata,ya miqa hannu zai taba lebanta,zumbur ta miqe ta zauna sannan taja baya,idanunta qur bisa kanshi tana kallonsa,tashi daya ta gano ramar da yayi,duk da cewa yayi mata kyau ainun,sai taji kaman wani abu daya tokare mata a qirji yana sauka a hankali,miqewa tsaye yayi ya goya hannayensa yana ci gaba da kallonta
"Iyeeee,yarinyar nan keda alama ma hankalinki a kwance yake,wallahi banga wata alama na kinyi missing dina ba,jifa kumatunki kamar kin boye fanke" ya miqa hannu sa zummar ja mata kumatun,tayi saurin bige masa hannu tana ja baya
"Ta yaya zaka shigo mata daki haka kai tsaye" saiya dage gira yana komawa gefan gadon yaxauna abinsa hankali kwance
"To meye a ciki?,nima ai kakata ce kokamar yadda take kakarki"
"Ka tashi kafita tun kafin tashigo tasamemu tayi mana kwaroroto ko?"
"Ai nafisan hakan ma,kinga shine dai dai,zata kuma gane ina buqatar matata" soma yunqurin sauka take ita tabashi waje,ya qyaleta saida ta gama sauka din tsaf sannan yayi caraf da ita ya rungumeta tsama jikinsa yana sauke numfashi
"Wallahi na kusa mutuwa,sati ukun nan daqyar na iya kaishi,ke bakima tambayeni ina na shiga ba sai fada sai qorafi?,haba my anshad?" Kiciniyar qwacewa kawai take,saboda ita kadai tasan me yake haifarwa jiki da zuciyarta,zuciyartata tayi raunin da takejin ci gaba da tauraratan kamar zai iya zame mata matsala,bataso tayi giving up,yayi hurting dinta alort,she have to teach him a lesson saboda gaba.

Daidai sannan daada ta sako kai,bata qarasa dakin ba saboda tasan yana ciki,saita tsaya a falo tahau rabka salati kamar tagansu
"Oh ya ilahi ka kawomin agaji,ke rahama kina ciki?,sake gayyatoshi kenan kikayi ko?,oh jama'a ni naga abinda yafi qarfina yau" sosai ran shahidan yabaci,ta qwace daga jikinsa tana cewa cikin fushi
"Ka jawomin magana kaji dadi,saika fita ka tafi ko?"cikin daga muryar daada tace
"Au ina magana kun qule kun barni kamar mahaukaciya,ke rahama?wannan zunubi har ina?,ana shirin raba aure amma kuna nanuqe?" Batasan sanda tace
"Haba daada,koda kwarto kika kamani wallahi iya abinda zakimin kenan,nice ma na gayyatoshi,gashinan saiki tambayeshi"
"Au laaaahaaaa'ila haaa'ilallaaaaaahhh,to wallahi zamanki ya qare,yau sai kinbi mijinki,na gaji daji bare gani" kawai saita banka dakin,ta rufe ido ta fitittike tadinga hadawa shahidan kayanta,tun shahidan na ganin abunda wasa ne harta gane da gaske fa daada take,tilas tasoma bata haquri tana qananun hawaye,shima anwar yashiga da nashi guntun wayon da salon iya taku
"Kiyi haquri daada,don Allah karki koreta,duka nina jawo mata,don Allah kiyi haquri ki barta tazaun,idanma don ta takarda ne,bari na rubuta kawai yanzu" ya fadi yana ciro takarda da biro daga aljihunsa,cak kukan shahidan yatsaya,ta zubawa anwar din idanu,gabanta yasoma dukan uku uku sanda taga rubutu yake bilhaqqi daada kuma taqi tsaidadhi,ta bude baki zatayi magana ta qware da yawu tahau tari,ya wurgar da takardar yayo kanta yana mata sannu,daqyar tarin ya lafa
"Kaga bar takadarka kada tazo tana tsinemin daga baya,baka ga har shaqewa tayiba saboda taga saki muraran,algunguma ashe kinaso kikazo kina min 'yar muryar na rabaku almura,kai anwar,daukar mata kayanta kubarmin gidana" hakanan ta kasa musawa daadan,saidai ta gefe daya tana jin haushi haushin anwar,sannan gashi uwa uba tashinta ma a bacci kenan ko wanka batayi ba,kamar wadda ba'aso daadan zata wani tattara masa ita?.

Tamkar wadda aka aikowa saqon mutuwa haka tayi kicin kicin cikin motar,kosau daya bata dubi sashen dayake ba bareshidin kansa,yasan zai fuskanci tarzoma da turjiya,amma adaren yau yakeson sauke kaso tamanin cikin dari na fushi da bacin ranta,saboda haka shima yaja bakinsa yakulle bai kulata ba.

Kai tsaye hanyar kano ya nufa,don baiga sauran abinda zai tsaya yi a katsina ba tunda sun bashi matarsa,kusan shuru shiya ci gaba da yi musu jagora a tafiyar tasu,ganin shurun yayi yawa ya sanyashi janyo plate din waqoqi ya saka,waqar dako yaushe take tuna masa abubuwa da dama,waqar da idan tana tashi sai yaji kaman mawaqin ya raci bakinsa yaci masa albasa,kamar mawaqin yasan abinda yake zuciyarsa ne kan shahida yake rera waqar,ji yake kamar shi yakewa shahida baitukan,waqar jarumar mata,wada ta sake sakashi a shauqi ba kadan ba,tun shahida na saurare har wani mayen bacci da taketa tunkudeshi ya lallabo ya saceta,murmushi anwar yasaki ya shafi gefan fuskarta yana furta
"Shahida rigima,shahida fada,yi a hankali,zan sake maidaki yadda kike a baya,asalin shahida na" ganin tadan motsa ya sanyashi saurin dauke hannu yaci gaba da tuqinsa.

Lokaci lokaci yakan waiwaya ya kalleta har zuwa sanda suka shigo kano,suna gab da dawanau ta farka,ta ware idanunta da suka san sauya kala saboda bacci tana kallon garin,wanda a qalla ta doshi wata daya bata cikinsa.

Bai tsaya ako ina ba sai gidanshi da yayi hijira yadawo,ya kutsa kai cikin gidan bayan mai gadi ya bude masa,cikin mamaki take kallon gidan tana tambayar kanta nan kuma ina ne?,ita dai tana biye dashi yana dauke da akwatinta don ya hana yaran gidan dauka masa ganin tare da shahidan suke karsu kalle masa mata har cikin gidan.

A falo taja tunga tana ta kumbure kumbure,cikin ranshi yace
"Ko fashewa zakiyi babu damuwa,na tattare kayata a haka" bai tanka ta ba sai daya shiga bedroom dinsa ya hada mata ruwan wanka mai zafi don yana ganin kayan jikinta yasan bata samu yin wanka ba
"Allah ya taimakeki,ga ruwan wanka can na hada miki ki shiga kiyi wanka,me za'a siyo miki kona dafa miki da kaina?,wanne kikeso?" Taso ta jefa masa harara amma yau sai taji nauyin haka,abu daya zatayi ta rama kawai ta bashi wahala itama
"Dan wake nakeso da manja da yaji,da salad sa qwai da yaji,kuma da kanka nakeso kayimin,har yajin banason na siyarwa
"Done!" Ga mamakinta taji yace,sannan yamiqe ya fice,taja qwafa a ranta
"Yadda ka wahal da zuciyata,ka wahal dani daga tashina daga bacci aka sani tafiya tun daga kano har katsina kaima sai kasha wahala yau,kakawo dan waken kaga yadda zamu kwashe" daga haka ta miqe tayi hanyar bedroom din,tanabin gidan da kallo,ya birgeta komai a tsare.

Ruwa kuwa ya hada mata me dumi sosai wanda yakusan sata gyangyadi,ta jima sosai cikin ruwan tana jin dadinsa kafin tayi wankan tafito,koda tafito din ta tadda wata sabuwar doguwar riga aje a gefan gadon wadda bata santa ba cikin kayanta,ta dauka ta farke ta saka,ta mata kyau hakanan ta mata cas a jiki,saita dawo gefan gadon tazauna donta shafa mai,hakanan laushinsa yayi mata,saita samu kanta da zamewa tayi kwanciyarta,kafin kace meye wannan bacci ya dauketa.

Da wata iriyar gigitacciyar yunwa ta tashi,ta sauko saga saman gadon da sauri dai dai lokacin shi kuma yashigo sanye da apron dauke da kayan abinci yana sauke waya daga kunnenshi,wanda yagama waya ne da wani abokinsa immagration daya sanya amasa passport urgently.

"Ki dauraye bakinki kizo kici,naga alama gadon nawa ya miki dadi,daga baki aron daki kiyi wanka saiki bige da bacci?" Bata tankashi ba donta cikinta take,ga wani zazzabi da taji yanason saukar mata tacikin qashi,kafin tadawo.ya zuba mata,taso cewa bataci ya kwashe amma yadda taga ya jera komai ya zubashi yadda yadace sai kawai yawunta yatsinke,sanda tasoma ci duk da tana yatsina fuska amma mamaki ya kamata,shi ya zauna ya tsara wannan dan waken?,komai yayi perfect?,yajin kawai take cikawa a danwaken saboda yadda yayi masifar yi mata dadi,hannayensa kawai ya hade waje guda yana binta da kallo gami da karantarta a nutse,ta daga kai suka hada idanu ta tsuke gira
"Meye haka zaka sani na qware"
"Ai wallahi saidai kiyi haquri,yadda nayi missing cute face dinki,na dade ban qare mita kallo ba over years dole yanzu na fanshe,kinga idan kinji ma zaki qware ga ruwa nan ki magana nayi sauri na baki" ya fada yana balle murfin robar ruwan yasoma tsiyayawa a cup,saita shareshi taci gaba da cin abinta.

Sai data tabbatar ta qoshi ta dinga yatsina fuska tana kushewa waidon yaji haushi,amma sai taga ko a jikinsa sheqa dariyarsa ma yake,abun ya sake quleta,ta sake jijjigo masa alale,haka ya hada waken yayi matashi tsaf ya kawo yana cewa
"Kin manta cewa nidin riqaqqen gauro ne kuma cikakken maraya da yayi rayuwa shi daya a gida ba uwa ba uba,ba dangi ba qanne,rashin iyaye bashi da dadi ko daya shahida,da mahaifiyata tana raye zan gaya mata ta tayani addu'a ne Allah ya dawomin da hankalinki kaina kamar yadda muke a baya,don addu'ar mahaifiya karbabbiya ce akan 'ya'yanta" take jikinta yayi sanyi sosai,wani tausayinsa mai qarfi ya kamata,gaskiya ya fada,ita data rasa mahaifi ma kawai banda babban jigon wato mahaifiya amma duk sanda ta tuna sai tayi kuka mai yawa,ina gashi wanda ba wansa zai kalla nan doron duniya duk girma da fadinta yace shine wanda ya kawoshi duniya?.

Tana zaune tanaci yashiga yayi wanka,ya fito a shirye tsaf yana qamshi ya dubeta
"Zanje gida na dawo,dame dame kikeson a dauko miki?" Kamar ta tambayeshi bacan zasu tafi ba sai kuma ta share
"Komai ma" ta amsa masa a taqaice,sai kawai yayi murmushi yayi gaba yana cewa
"Ba wani abun kuma da kike buqatar ci?,don naga alama kin zama acici,daada tabude miki cikinki,nidai adan ragemin nima nasamu naci" da haka ya fice yabarta cikin tunani,a yanzu tana ganin anwar dinta zam yana dawowa,anwar dinta dake rakata sadakar wake da shinkafa,anwar dinta dake iya fasa kudin albashinsa daya tara da wuya yasiya mata abinda ranta yakeso,anwar dinta dabai iya wuni ko kwana ba tare daya ganta ba,anwar dinta dake boye mata duk wani abu da zai sata shiga damuwa,anwar dinta dake sonta kamar ranshi,anwar dinta dake tunkude mata dukkan wani abun cutarwa dayaga zai tunkarota,anwar dinta dake lullube asirinta wanda har yau yana kan wannan qadamin,tayi mamakin sanda yaga hotunan,ya ganta cikin maye babu daya cikin wani nata daya taba gayawa har yanzun nan datake zaune,tannan kam ta sara mishi babu shakka anwar dinta keson dawowa rayuwarta,amma saidai har yanzu zuciyarta taqi amsar lamarin gaba daya,tanason tasan waye ya hada mata dukka wannan sharrin,waye ya musu wannan bita da qullin indai harda gaskene hadin ne?sharrin ne?,bayan fiddausi saiwa?.54

*Sadaukarwar wannan page din ga*

🌻MAMAN HAJIYA🌻
_shahida da anwar na gaisuwa_πŸ˜‚πŸ˜‚



Kwance take saman doguwar kujera dake falon qasan ta miqe sosai rigingine tana kallon sama,wasu siraran hawaye ke fitowa daga idanun ta,tanajin gaba daya duniyar bata mata dadi ta mata daurin huhun goro,takira anwar har batasan sau nawa ba amma ko sau daya number bata shiga,bai bata izinin zuwa ko ina ba bare tasiyo wani,hakanan cikin yan uwanta ba wanda taga qeyarsa bare ya debe mata kewa duk da bawani shiga dangi take ba,ita kadai ke rayuwa cikin gidan kamar mujiya,son anwar da kewarsa kamar zasu kasheta,tana tsaka da wannan halin taji sallamarshi yana turo qofar falon yashigo.

Zumbur tayi tamiqe tsaye tana dubanshi sanda yake takowa cikin falon,ya mata wani bala'in kwarjini sosai,hakanan ya mata kyau,fuskarshi saika rantse bai taba sanin wani abu mai suna dariya ba,ko gefan da take tsaye bai kalla ba yadoshi kitchen,sak ta tsaya tana bin bayansa da kallo harya wuce,da gaske mutumin nan wai yake?,ya gama gane komai ya gama fuskantar komai?.

Store din gidan yashiga,ya dudduba ya tabbatar akwai duka kayan abinci,saiya juya yafito daga kitchen din,kasa haqura tayi ta kirashi da hanzari tabi bayanshi,cikin karyar da murya tamkar zata saki kuka tace
"Haba ya anwar haba don Allah,wanne irin laifi na maka dana cancan ci wannan hukuncin?,koma meye nayi maka aika tsaya mu fahimci juna in baka uzurina ko?,kayi haquri don Allah" cikin mamaki da maganganunta na rainin hankali yake kallonta,shi zata gayawa wadan nan maganganun banzan?,tana nufin har yanzu kenan batasan meta aikata ba,shi zata yiwa pritending,lallai ba shakka tacika yar rainin wayo,zaici gaba da gasata da ruwan jikinta harsai tafito ta bayyanawa duniya da bakinta abinda ta aikata
"Baki aikata komai ba,kawai bani da muradin zama dakene" yafurta sanda ya soma hawa zuwa sama,saita soma mara masa baya ya waiwayo da hanzari
"Karki sake ki takomin nan" qwalla tacika idanunta taf,saita karkatar dakai
"Duka dai wannan akan shahida neko?,kaji meye na aikata mata,eh nina aikata anwar,amma kome kaji na aikata din nayine saboda kai,nayine saboda qaunarka,kuma nayine saboda soyayyarka"
"Bakya qaunata nafisa!" Ya dakatar da ita cikin tsawa da wani irin bacin rai dake cinsa
"Da kina qaunata da bazaki cutar da zuciyata da rayuwata ta hanyar rabasu da muradinsu,shahida itace rayuwata,itace zuciyata,bakiyi don kina sona ba,kinyine saboda son kanki dason zuciyarki,kina tsammanin saikin rabamu sannan zaki cimma naki burin?,kin manta cewa ALKAWARIN ALLAH BAYA TASHI,idan Allah yayi alqawari saiya cikashi,babu wani abu daya isa ya kankare koya dakatar....gaskiyane nafisa,kinyi nasara kinsameni,amma ki sani,ba zaki taba farincikin kasancewa tare dani ba,muradinki bazai taba qarasa cika a kaina ba,ga gida nan na anwar shahida,ga kayan buqatar rayuwa nan daga anwar amma bazaki samu anwar ba,laifinki ba irin lefin da zukata suke mantawa bane,dake watace ba diyar alhj abba da mummy ba da tuni kina prison a qulle,amma kinci daraja da martabar mutanen guda biyu,hukuncinki yazo a yadda yake yanzu,kici gaba da zama a haka har zuwa sanda kika yankewa makomarki hukunci" daga haka yaci gaba da takawa da ssassarfa ya haye saman,a nan ta durqushe waje daya ta cure tana sakin kuka,dana sani da nadama na baibayeta,shikenan koma meye ya tashi a banza?,shikenan ba zata taba yin rayuwar datasha nafarkin sunayiba dashi?.

Dakin shahidan yabude yashiga,ya diba duk abinda yasan takan iya buqata,kayane masu yawa yasauko dasu harda nashi daya sake qarawa,yazo yawuceta nan tana kuka,ya aje mata wasu kudaden ya kama gabanshi yasake bar mata gidan.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Tana tsaka da baccinta taji kaman ana taba filon da take kai,tabude idanunta da sukayi mata nauyi saboda tsabar barcin dake kanta
"Ga ruwa can ki tashi ki wanka ki samu abu kici xaki rakani unguwa" anwar dake tsaye kanta daure da towel wani a saman kanshi yake gayamata,saita maida idanunta ta lumshesu,tanajin yadda baccin ke zagayata,baccin kawai take da buqatar yi.

Ruwa taji ya yarfa mata kadan a fukskarta,tabude ido zata masa masifa yarigata cewa
"Gurine me muhimmanci,yi haquri ki tashi ki shiya muje,idan mun dawo saikita bacci babu me tashinki" sake maida idanun nata tayi ta lumshe,ta motsa labbanta can qasa tace
"Babu inda zani" bata gama fada ba taji ansureta,bata gama bude idanunta ba saicikin ruwan me dumi sosai,haka ya zundumata ita da kayan jikinta yajuya yafito yana cewa
"Ina jiranki" shuru tayi dumin ruwan na ratsata,ta gwada komawa baccin a haka amma saita kasa,dariya ta kubce mata sanda tabude idanun nata taganta zundum cikin ruwa,dole tafito ta kwabe kayanta tasoma wankan.

Sosai mamaki ya kamata sanda yatsaida motarsa qofar gidan birsin dake qofar kudu,cikin mutuntawa yagaisa dasu tun daga kan maigadin zuwa gandurobobin,daya daga cikinsu ya masa jagora suka shiga ciki bayan sun cika dukka qa'idojin ziyara,dakin da ake ganawa da wanda kazo gurinsa aka kaisu,saita kasa shuru ta daga kai tana dubanshi
"Me mukazoyi nan ne?" Shuru yayi yadan xuba mata ido yana kallon yadda tayi kyai cikin doguwar riga,saiyake ganin idanunta sun qara girma da kyau,hakanan hancinta yasake fitowa,idanunsa ya lumshe kana yabudesu tarrrrr a kanta yana cewa
"Na kawoki ne inda zuciyarki zata wanke daga dukkan wani zargi da sauran tambayoyin dake ranki wadanda baki furta min ba...." Bai kai qarshe ba aka shigo dasu mutum biyu,mima sa kammaninta suka soma yin qaura zuwa wata kama ta daban,sai kuma wani saurayi,suka zauna bencin dake fuska tarsa,gaisheshi suka soma saidai bai kula ba,ya waiwaya ya dubi shahida
"Kin gane wadan nan?" Idanunta tasoma saukewa kan saurayin,ko daya bata ganeshi ba,hasalima ita bata taba ganinsa ba,ta dauke idonta daga kanshi ta maida kan mima.

Itama bata ganeta ba,amma taso qwarai ta shaida fuskarta sosai,kamar tasan fuskar,kamar ta taba ganinta a wasu gurare,jiki a sanyaye kan ganin mace cikin gidan kurkuku tace
"Ban sansu ba" wani tausayinta ya tsirga masa matuqa,har sai daya kasa daurewa ya saka hannunta cikin tafin hannunshi,sunyi kutse cikin rayuwarta,sun kafa mata baqin tarihi,sun dasa mata bacin rai da baqinciki banda Allah ya nuna buwayarsa da isarsa,sun hanata sukuni na tsahon wasu shekaru alhalin ita ko fuskokinsu ba zata iya shaidawa ba,wannan wanne irin zalunci ne,mima yasoma nunawa
"Wannan,ita da nafisa sune ummul aba'isin na rabuwarmu dake da dukkan wani abu daya biyo baya,wannan kuma...." Ya fada yana hadiyar wani abu me daci,kishi da bacin rai na taso masa,musamman idan ya tuna yadda yariqo shahidan a jikinsa,ya taba pant dinta harya cillo mata,banda shari'a da zatayi aikinta ba shakka shi kadai yasan wanne hukunci zai masa da zai sanyashi ya huce
"Wannan,dashi aka hada bako aka bako abinda kika bugu,ya kawoki qofar gidanku ya zubda ke da sunan ciki kika zubar" idanunta dukka tafito ta qura masa idanu tana kallonsa,wani irin suya qirjinta yake,gumi ya karyo mata,abinda yafarun a baya ya soma dawowa qwaqwalwarta
"Kuyi mata bayani da bakunanku azzalumai macuta!" Ya fada cikin tsawa,cikin rawar jiki mima tasoma bayyana dukkan wani abu daya faru,tundaga ganin da suka yiwa anwar din na farko a qofar hall din biki har ranar da anwar yaji meya faru,bayan ta dire shima saurayin yadora da bayanin dukka abunda yasani.

Ko kafin su kammala kuka shahida take shabe shabe da hawaye,sun zalunceta da yawa sun kuma zalunci anwar,babu shakka anwar yacika masoyin qwarai daya rufe wannan mugun sharrin ba tare daya barshi yayadu a bakunan al'ummaba,idan yana da laifi ma cikin kashi dari laifinsa kaso biyarne na rashin bincike,tabbas koda ita taga anwar a wannan yanayin da wadan nan hujjojin,a yadda take mace mai qaramin tunani da gajeran tsinkaye qasa da wanda da namiji yake dashi Allahne kawai yasan me zata aikata,anwar yayi qoqari matuqa gaya daya iya rayuwa da irin wannan bacin ran da baqincikin,da qazaman hotunan dako maqiyiyarka ka ganta cikin wannan yanayin zaka dade kana ta'ajjubi,zaka jima cikin mamaki da nema mata shiriya.

Kasa zama tayi sai kawai tamiqe da hanzaei tafice daga wajen,anwar yatashi shima cikin wani sabon bacin ran ya rufamata baya,ba tare daya damu hurwa da nema gafararsu da suke ba.

Tuni harta isa bakin mota,kuka take haiqan,haqiqa ta jahilci kanta kenan data tsani anwar,tazurfafa kan laifin dayayi mata,ba tare data bashi dogon uzuri ba,ta kuma zurafafa bincike kan dalilin daya sanya tashi guda yajuya mata baya,anwar din data sani cewa ranshine kawai bazai bata ba,harda fiddausi cikin wadanda aka hada baki dasu?,ta tsammaci fiddausin ta aikata ne cikin rashin sani ashe harda ita cikin shirin maqiya?,amma idan tasan fiddausi yaushe tasan nafisa?,me ta yiwa nafisan?,kawai donta ganta da anwar,hadin data tabbatar Allah ne kawai yayishi?,shine zata nemi jafata cikin wannan ramin mai wahalar fitowa banda Allah ya dubeta?.

Shiya bude mata qofar tashiga ya mayar yarufe,ya zagaya yashiga shima ya tashi motar,yadda yaga tana kuka ya tabbatar tana buqatar tafitar da abinda ke damun ranta ne,shi kansa a sanda abun ya bayyana a gareshi yaso ace yayi kukan kozai samu saasauci.

Suna shiga harabar aje motoci na gidan yayi parking din motar

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment