Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gizo wato www.rahamalls.com,bakin gado ya koma sannan ya rubuta sunan makarantar *RAHA COMPUTER INSTITUTE* ,cikin qaramin lokaci ya samu dukkan bayanai,kuma tsarin ya gamsar dashi,ya dauki number dake cikin bayanan ya kira.

Cikin sanin daraja da mutuntaka tadan adam ya sake samun bayanan da yake buqata,cikin abinda bai gaza awa guda ba yayi register dasu da komai da komai,ajiyar zuciya ya sauke sanda komai ya kammala,ya duba agogo yaga lokacin daya kwashe,ya miqe a hankali yana fidda kayan jikinsa,ya sauya wasu marasa nauyi,wando iya gwiwa sai jallabiyya daya fitar ganin lokacin sallah ya kusa,ya shiga bandaki ya daura alwala,sanda ya fito wayarshi na ruri,gab da zai isa gareta ta katse,saiya duba mai kiran,nafisa ce,miscal na shida kenan daga sanda ta fara kiransa zuwa yanzu,sai a sannan ma zancan ya dawo masa,ya duba saqon data tura masa wanda na godiya ne da kuma ya yaje gida,aje wayar yayi ya isa inda magungunansa suke ya cira yasha,sannan ya fesa turare ya qarasa bakin gado ya dauki jallabiyyarsa ya saka,hakanan yakejin kaman wani nauyi ya ragu daga zuciyarsa.

Cikin mamaki ta dubi table din sanda ta fito daga dakinta,taji kaman ya shigo amma bataga alamun hakan ba,kaman zata share sai kuma taba hakan bai dace ba,kodon jikinsa takega ya kamata ta duba,idan lafiya lau shikenan babu buqatar sake damuwa ko saka ido.

Zai fita ita kuma zata shigo,kusan lokaci daya suka murda handle din,baya tadanja kadan bayan ta dubeshi ta dauke idanunta,sai taga kaman ya fada kadan daga jiya zuwa yau da kuma fitar daya sakeyi da dawowarsa,ganin alamun fita zaiyi sallah saita juya ta soma sauka tana cewa
"Sannu da zuwa"
"Yauwa" ya amsa yana tsaye cak yana dubanta sanda take sauka din,yanajin kaman ya rintse ido ya bude yaga duk abinda ya farun da wanda ke faruwa a mafarkine,bai taba kwana ya kwatanta a ranshi ko sau daya rayuwar zata iya zuwa musu da wannan salon ba,dai gashi lokaci daya komai ya canza,komai ya tabarbare,komai yazo da cikin wani bahagon yanayi.

Karon farko tun bayan rabuwarsu dayaji wani abu mai kama da tausayi tausayi akanta saboda tuna cewa nan gaba kadan nafisa xata shigo gidan a matsayin kishiya a wajenya,ya tuna yadda mata ke komawa duk sanda zance makamancin haka ya shiga kunnensu yatuna yadda nafisa ta birkice a sanda labarin wanzuwarta qarqashin inuwa guda ya shiga kunnenta,a sannanma bata zama qarqashin ikonsa na,basu taba kwana qasan rufi guda ba,inaga ita?,duk da bashi da tabbacin cewa zataji wani abu ko zata damu,saboda dukkan dalilin dake sawa mace tayi hakan babushi tattare da ita.

"Kidan samu kifi ki dafaminshi idan ba damuwa,zanje sallah na dawo" ya fada cikin laushin murya wanda har hakan yaso bata mamaki,saita juyo tana kallonshi,suka hada idanu ta sake dauke kai ganin yadda ya kafa mata idanu,taji kallon nata har cikin jikinta,sai taba baiken kanta data sanya kaya irin wannan ta zauna haka ko mayafi babu bare hijabi,amsa masa tayi da to tana ci gaba da sauka daga benan,har sai dayaga bacewarta sannan ya sauko shima yawuce masallacin.

Sai data soma shiga daki ta samu dan qaramin hijabi ta saka sannnan ta wuce kitchen din har yanzu tana mamakin irin salon da yayi mata magana dashi,ta ciro kifi ta gyarashi,ta kauda wancan tunanin na farko ta fada tunanin yadda zata sarrafashi ta yadda zai dace da yanayinsa,wani gashi ta tuno mai kama da romo romo da takanga anty xubaida bayi,ba bata lokaci ta soma hadashi,wanda cikin mintuna qalilan ta kammala,qamshi kuwa ya cika gidan ko ina,ta gyara komai a kitchen din ta gogeshi sosai yadda ta saba sannan ta fito don barin kitchen din.

Tunda ya dawo yana falon a zaune yana shaqar qamshin kifin har cikin zuciyarsa,da mamaki tadan dubi sashen da yake din,don iya zamanta a gidan batace ga sanda ta ganshi zaune haka sosao cikin falon ba,kamar yasan da tsaiwarta shima ya waiwaya yana dubanta,yabi hijabin jikinta da kallo,shima hakan yayi masa don tamkar gata tayi masa,baisan me yasa takeson ta zame masa tamkar wani maganadisu ba ko mayen qarfe aduk sanda ya ganta?,baisan me yakeson sauyashi haka ba,bayan a baya yasan bai damu da dukka shigarta ba,amma cikin abinda bai gaza sati biyu ba yanason sauyawa gaba daya?.*Alqawarin Allah*
44



Komawa tayi da baya kitchen din ta shirya komai ta dauko kan tray sannan ta sake fitowa
"A'ina za'a aje maka?" Nuni yayi kata da gabanshi,ta qaraso nan ta aje ta shirya komai ta dauko sauran na wajen dining shima ta shirya masa,tayi sarving dinsa sannan ta yunqura zata miqe saiya dakatar da ita yace ta zauna,ba musu ta koma ta zauna din,saidai duka bata jinta dai dai,baiyi magana ba harya qare cin abincin sannan ya soma da cewa
"Da can kafin aurenki ina tare da wata yarinya nafisa wadda har an saka mana rana lokacin biki ya rage saura sati uku,to wasu abubuwa suka biyo baya wanda ya zama silar fasa auren namu a wancan lokacin,a yanzu maganar ta dawo wanda ina tunanin duka ba za'a wuce sati uku ba nan gaba" bata taba tunanin zataji irin abinda taji a zuciyarta ba'a yanzu,tunda ya ambaci sunan zuciyarta da idanunta suka haska mata ita,saita dinga binsa da kallo kawai sanda yake bayanansa,gaba daya saita daina fahimtarsa,duka bayanan da yake kawai tana ganin yana yine saboda radin kanshi,yarinyar daya aiko mata da hotunanta sanda take tsaka da radadin rashin mahaifinta?,yarinyar daya turo mata da fuskarta sanda take tsaka da jimami da alhinin rabuwa dashi?,yarinyar daya kawo mata hotonta ta gani cewa ya samu wadda ta fita?,ya sauya wata a madadinta,a yanzu ita zai aura ya kawo gidan?,shine yake wani rufa rufa dason yiwa zancan kwaskwarima?,tana ganin abu mafi sauqi kawai ya fito ya gaya mata zai cika muradi da burinsa ne,yanzune manufar da yasa ya aureta zai bayyan muraran baro baro,me yayi saura?,me xata xauna taji daga bakinsa,ai komai ya qare hakanan komai ya fito fili,sai kawai ta miqe sanda yake tsaka da bayanin nashi,binta yayi da kallo ganin ta soma tafiya zuwa hanyar dakinta ba tare data ko waiwayeshi ba,kiran sunanta ya soma yi abinda ya jima rabonshi dayin hakan,saidai ko daya bata saurareshi ba bare taji me yake fada,da hanzari ya miqe ya bi baya,taji takun tafiyarsa,saboda haka tana shiga dakin ta saka key,ta samu gefan gadonta ta xauna ba tare datasan me zata tuna ba,wani kuka ne mai sautu ya qwace mata wanda ta kasa tsaidashi,hannunsa saman kanshi yana yamutsawa jin sautin kukanta dake ratso har inda yake tsaye
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta yana kallon qofar dakin da yayi juyin duniya ta bude taqi,bai taba xato ko tunanin xata damu ba ko sau daya,me yasa ta damu?,me yasa ranta yw baci?,bayan ta gaya mishi cewa bata qaunarshi ko kadan?.

"Me yasa kike kuka shahida?,kukan me kike?,kins kukane saboda mutumin da kika dainaso xai qara aure?,ko kina kuka ne saboda mutumin daya daina sonki xai auro wadda yakeso?,muradin zuciyarsa?,haske rayuwarshi?,meye abun damuwa a ciki shahida?,har yanzu anwar na cikin zuciyarki ko kuwa?" Tambayoyin da zuciyarta ta dinga mata kenan wanda yasa ta soma tuhumar kanta da kanta.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Duban nafisan mima takeyi sosai da wani irin banzan kallo,cikin ranta ji take kaman ta tashi ta shaqe nafisan,cikin ranta tana ala wadai da sakacin da tayi har ta bari tunanin nafisa yakai gata nemi anwar karo na biyu,tabbas da tasan da irin wannan ranar da tunu ta saka almakashi ta datse alaqar da tayi saura tsakanin anwar din da nafisan,koda yake a yanzu ma bata baci ba,saidai kuma ba haka taso ba,dole ya saka taka tsantsan da nutsuwa dinta wargaza tsakaninsu,don a yanzu bata da burin daya wuce ta ganta itama gidan anwar din a matsayin matarsa,sake duban nafisan tayi a karo na biyu yadda taketa faman fara'a,bakinta kamar zai hade da kunnenta,irin kallon da miman ke mata yasanya jikinta yadan soma sanyi
"Ko bayi dai dai bane hajjaju?,bafa zan iya haqura da anwar ba matuqar ina raye shima yana raye" baki miman ta tabe tana ci gaba da dubanta
"Dama aida kin jira ni nidin xan miki wannan aikin,abinda yasa kika ji shuru ba'a kai gabar bane,naso mu gasashine harsai ya kawo kanshi da kanshi ta yadda koda kin shiga saikinfi daraja da qima a idanunsa,amma a yanzun yadda kikayi wallahi qimarki ta zube qasa warwas,kuma haki da wata fuffuka da xakiyi idan kin shiga gidan,hasalima ba baiyi matsuwar shigowarki gidan ba kinga baki da abun cewa sawa ko hanawa koda kin shiga gidan" sai jikinta ya danyi sanyi,taji maganar mima tabbas tana kan hanya,shigen maganar da mummynta ta gaya mata kenan,ita kuwa a rayuwa yanzu burinta na gaba shine ta shiga gidan anwar ta zama ita ke fada aji,ita zata sa ayi ta hana kuma a hanu,wanda daga qarshe take fatan shahidan ta fita tabar mata gidan gaba daya taci gaba dayin yadda takeso.
"Gaskiyar magana mima banason nayi rayuwar da bani zance ayi ba cikin wannan gida,saboda har yau ina tsoro kuma ina shakkar soyayyar dake tsakanin anwar da wannan mayyar yarinyar" abun nema ya samu wajen mima,hanyar da zata wargaza rayuwar auren nafisan cikin sauqi,duk da haka saita sake tsuke fuska ta kuma gum da bakinta harsai da nafisan ta sake magantuwa cikin mitar tayi mata shuru,fuska ta yatsina
"In sake shiga sabgarki ki watsamin qasa a ido?,ina qoqarin fiddo miki da daraja da martabarki amma ke baki gani,gwara kawao na qyaleki kici gaba da samawa kanki mafita" harara ta watsawa miman
"Banason wulaqanci wallahi mima,haba don Allah,sau daya dai don nayi amfani da shawarar kaina saiya zama matsala?" Sai data gama shan qamshinta sannan tace
"Shikenan,zaki samu yadda kikeso,zaki mulka anwar ki kuma juyashi shida waccar yadda kikeso matuqar zaki jure ki kuma bi doka da qa'ida,zan dawo next week randa kikacemin zaki fara rabon IV zakiji sauran qarin bayani" kamar ta goya mima haka nafisa taji,kudade masu yawa ta baiwa miman sannan ta rakata.

Dariya mima ta saki bayan ta gama irga kudaden,mota takeson sauyawa,kuma ba shakka lokacin da zata sauya motar da takeso din yayi,a jikin nafisan zata hada kudinta tsaf,daga qarshe kuma ta tashi a tutar babu,ba anwar din ba kuma kudinta,daga haka ta tada motarta taci gaba da tafiya tanabin waqar dake tashi cikin motar cikin nishadi gami da tsara yadda zata mallaki anwar ita kadai bayan ta fitar da shahida da nafisan ma daga gidan dukkansu.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Kaman a mafarki take jiyo sallamar anty xubaida cikin falon nasu,da sauri ta sauko daga gadon wanda ta maidashi wajen rayuwarta,idan kaga ta fito tota tabbatar anwar ya fita baya gidan sannan zata fito tayi aikace aikacenta a gaggauce ta koma,sam bata qaunar haduwa dashi ko daya,Suna shirin yiwa kansu mazauni ta fito fuskarta a washe
"Anty yau a gida na?,ashe xakixo?"
"Kamawa ai take,gashi ta kama shahida naxo" cikin walwala da farinciki ta tarbesu.

,sun jima sosai ranar,sunata hira dasu huda,duk sai yaji kewar gida ta sake kamata,kaman ta koma gidan haka takeji.

Saida suka dan kebe sannan anty zubaidan ta gaya mata abinda ya kawota,zancan auren anwar,kebe fuska shahidan tayi cikin nuna halin ko in kula,saidai can qasan ranta wani abu ke tsinkulinta,maganganu sosai anty zubaidan tayi mata,gami da jan hankalinta,suna gama cin abincin rana tace zasu koma,kaman shahidan tayi kuka amma hakan ta haqura,taso sosai antyn tabar mata hudan amma qememe taqi,haka suka tattara tanaji tana gani suka tafi.

Zuwan antyn yasa tadan sake ranta,ta koma sabgoginta kamar baya,saidai ta sake janye sosai daga anwar din,sati biyu da faruwar hakan anwar ya shigoda set din manyan akwatina guda hudu,da farko tayi burus amma daga bisani tayi tunani kada ya tsammaci kishinsa take saita karba ta masa godiya,yayin daya bita da kallon mamaki,da gaske bata jin kishinsa? Hakan na nufin bata sonshi?.

Cikin kwanakin ka'in da na'in ya maida hankalinsa ga koyon abinda yasa gaba daga raha computer instute,ya ware lokaci har gida yake iskeshi malamin,baisan me yasa abun ya tsaya masa a rai ba,bai san me yasa ya maida hankali fiye da yadda ya xata ba,wanda yake da tabbacin cewa cikin wata uku ya cimma abinda yakeso ya cimma din,ta bangare guda guda kuwa yayi qoqarin kawo sauyi ko yaya yake tsakaninsa da shahidan,don ko kusa baida burin nafisa taxo ta fuskanci komai dangane da zamansu,duk da qoqarin nasa sau da yawa yakan cimma tasgaro,saboda rashin samun cikakken hadin kai daga shahidan.

Ta bangaren amarya nafisa kuwa shirye shirye sun kankama ka'in da na'in,dukkan wani abu da aka sani na bidi'ar biki ba wanda bata tsara xatayi ba,harda ma wanda ba' saba gani ba,ko sauraren abinda anwar din zai bayar batayi,sha'aninta kawai take.

Qarfe shida saura malamin da suke karatu tare ya tafi,yarage saura shi kadai a dakin,ya shiga cumputer din sosai yayi shige da fice wanda ya tabbatar masa lallai ya soma nisa,hakanan yana cimma abinda ya nufa din,saiya kasheta yana sakin murmushi wanda yayi dai dai da shigowar kira a wayarshi,duban wayar yayi sai yaga nafisa ce,ya manta shaf cikin satin zasuxo jeran kaya,bai daga ba harta katse,saiya janyo wayar yana laluba inda ya aje numberta,cikin sauyin da aka fara samu wanda ada bashi da ita.

Har tayi ringing sau biyu tana katsewa ba amsa,sai ana ukun sannan ta daga,shuru tayi tana sauraren muryarsa wadda ko mutuwa tayi ta dawo ba zata kasa gane muryar waye ba
"Bakisan ina cikin gidan bane?" Ya tambayeta ganin tsahon zamansu baiji motsinta ko gilmawarta ba,shuru babu amsa saboda haka ya kautar da wancan zancan
"Ki sameni a dakin karatuna....am yana nan daga baya kaman zaki shiga qofar kitchen ta baya" ya sake mata bayani don ya sani bata sani ba,tunda bata taba zuwa ba.

Wayar ta sauke tana jin wani haushinsa na kamata,tome zaiyi mata,kiran me kuma yake mata?.

Har sai daya zaci ba zata zo ba yaci gaba da aikinsa sannan yaji an murda murfin qofar,ya daga kai yana kallon bakin qofar,itace cikin jar doguwar riga wadda ta yane kanta da qaramin mayafinta,idonsa ya dauke wani abu na tsirga masa,ba kwalliya a fuskarta amma tayi masifar amsarta rigar wanda ya kasa kubuta daga qyasata da zuciyarsa tayi.

Daga sallama bata sake cewa komai ba,ta samu gefansa ta zauna,saiya kashe wayar tashi da yake dannawa,ya juyo gaba daya suna fuskantar juna sosai yatsunshi sarqafe da juna idanunshi cikin nata,fuskarsa na nuna zancan da zaiyi mai muhimmanci ne,sai taji kallon da yamata nauyi,ta kauda kanta gefe guda
"Gobe jibi gata masu jeren amarya zasu zo...."
"Me zanyi musu to?,meye amfanin gayamin din?,Allah ya kawosu lafiya" ta fada cikin zafi zafi wanda ita kanta batasan ta aikata hakan ba,idanu ya zuba mata har takai aya sannan yace
"Babu abunda xaki musu,kawai inason ki kwashe kayanki xaki koma dakunan sama" waiwayowa tayi tana dubanshi,me zataje samanshi tayi masa,dai kawai ta miqe ta soma takawa tana cewa
"Na barwa amarya,inda nake nan ya isheni na qarasa kwanakin da suka ragemin" bai fuskanci me kalmarta ta qarshe ke nufi ba,amma ganin zata fice sai yace da ita
"Umarni na baki ai ba shawara bace bare ki gayamin naki ra'ayin" daga haka shima ya juya abinda shida kujerarsa,saita waiwayo tadan dubeshi kadan sannan taci gaba da takawai ta fita daga dakin.

Tana shiga nata dakin taji kuka ya qwace mata,duk yadda taso hana kanta abun yaci tura,batasan me yasa takejin bacin rai da damuwa ba,kuka tayi sosai kafin taji zuciyarta tayi sanyi.

*BAYAN KWANA UKU*


Tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata doguwar riga na wani yadi me sulbi wanda yake kama da yadin satin,hakan yasa yabi jikinta ya lafe,gajeran hannu ne dashi gami da wuyan half shoulder wanda ya fitar da wuyanta da wani sashi na qirjinta sosai,kanta babu dankwali kana a tsefe yake,hakan yasanya gashinta da bata kamashi da ribbom ba ya biyota shima ya kwanta saman filon da take kai,gama wayarta kenan da ummanta tana nazarin maganganun data gaya mata taji an murda qofar dakin,wanda hakan yaja hankalinta zuwa kallon qofar,yana shigowa idanunshi cikin nata,mamaki ya sanyata miqewa ta zauna sosai saman gadon,tama mance da irin dinkin da yake jikinta,idanunta fal da alamun tambaya,jingina yayi daura da qofar ya goye hannayensa a qirji yana qare mata kallo,sai a sannan ta tuna da rigar jikinta,tabi kanta da kanta da kallo saita daga kai tana hade fuskarta tsaf,miqewa tayi ta nufi wardrobe dinta ta soma lalubar mayafi,yana tsaye still yana kallonta har yanzu baice komai ba,harta gama yafa mayafin ta dawo gefan gadonta ta zauna
"Ki shirya gobe qarfe tara na safe xamu fita tare xan saukeki gida" fuska a tattare ta bishi fa kallo har ya fice,saita ja qaramin tsaki ta koma ta kwanta tana tunanin ina zai kaita?,kuma me zata fita tayi.

Tara saura tana tsaka da shirinta wayarta ta shiga ruri,ta qarasa inda take aje ta daga tana duba mai kiran,anty usaina ta gani,a ladabce ta daga suka gaisa sannan tace
"Na kasa samun layin anwar,inata kira busy,taimaka don Allah ki gaya masa idan zai fito ya fito da wadan nan takardun"
"Toh anty" ta amsa mata a ladabce tana aje wayar,qarasa shiryawa tayi sannan ta fito ta haura saman nashi,tana shiga yana aje wayar gami da miqewa ya tura qofar toilet ya shige,bata masa magana ba don qyashin hakan takeji,saita barshi ta samu saman kujerar mudubi inda ya tashi ta zauna tana dakon fitowarsa.

Wayar daya aje saman mudubi wanda take dab da ita ta dauki ruri,idanunta kai kan me kiran,nafisa ta gani,ta riga data haddace sunan,saita dauke kai saidai hankalinta ya kasa daukuwa daga kai,tana jin sautin ringing din har cikin kanta harta katse,aka sake kira ta sake katsewa,ba jima wani kira yasake shigowa,batasan sanda taja wani mugun tsaki ba ta finciko wayar ta kasheta gaba daya ta dangwarar da ita awajen,tana tuna sanda ta shigo waya taga ya gama,wala'alla ma shi yasa anty usaina ta gaza samunshi wayama yake kenan
"Ina ruwana da wayarshi" ta gayawa kanta tana sake tsuke fuska ita kadai,daidai lokacin daya fito daga bandakin jikinsa jiqe da lema,da alama wanka yayi,fuskarta a dinke tsaf cikin kaushi tace dashi tana miqewa
"Anty tace karka manta ka fito da takardun nan" daga haka tayi gaba,binta yayi da kallo,tana gab da ficewa yasha gabanta,ya murza key ya rufe qofar,saita danja da baya tana dubanshi,kuka takeson tayi amma batasonyi a gabansa,don tasha alwashin ta daina yi din yana gani yana jin dadi
"Ka budemin na fita na qarasa shiryawa" ta fada cikin sanyi,wanda ba haka taso,taso tayi maganar ne cikin kaushi da zafi,saiya kada kai yana duban idanunta wansa hakan yaso mata tasiri,saita zare nata idon gami da kauda kanta wani sashen daban.


_Dadai zakuyi haquri harmu cimma manufar labarin,don kowanne labari yana da manufar da akeso a cimma,idan kuma kunason shortcut shikenan_🤷🏽‍♀️

Mai yiwuwa gobe kujini shuru,idan kuma Allah ya bada dama to.



*karku manta kuyi wekend dinku da tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,ku saurari littafanmu ba tare da kunsha wahalar karatu ba kuna daga kwance*💃🏻

*Asha weekend lafiya*🤝🏽*Alqawarin Allah*
45


"Zuwa yanzu ya kamata ki fara koyan wasu abubuwan,saboda karta shigo ta rainaki" ya fada yana son dawo da salon tsokanarshi.

Wani kallo ta watsa masa da idanunta sanda yake komawa zuwa bakin mudubi,wani abu ya tokare mata wuya
"Wace zata shigo din?,bani ya kamata ka gayawa wannan maganar ba,don ni ba kallon mijina nake maka ba" saiya waiwayo yana zare idanu
"Da gaske?,lallai kinci tuwo da yawa,wait....waima kallon me kike min?" Harara ta sake watsa masa ganin yanason maida abun shirme kamar yadda ya saba,baisan yadda ranta ke tafasa ba
"Oho,koma meye ba damuwarka bane,ka budemin qofa kawai na wuce,abu daya na sani shine,daga kai har ita kada wanda ya sake yashiga hurumina" baki ya kama yana kallonta,sau tari yakanso yaga tana rashin kunya,sai dan qaramin bakinta yayita burgeshi,don a tsahon xamansu na baya bai taba ganin tana tsiwa ba sai yanzu
"Idan kuma akaqi fa?"
"Raine zai baci" ta amsashi kai tsaye,qaramar dariya ya bushe da ita
"Kinga...kawai ki fito kice kishi ne yake damunki ko?,to kiyi haquri,na miki laifi" sake hararshi tayi,tanajin kaman ta makeshi ko zataji sauqi
"Ni na gaya maka duka wannan na damuwata bace,bama kallon miji nake maka ba bare nayi kishinka,ka budemin na fice kawai"
"Aiko kin makaro,dakin yadda kawai da hakan yanzu zan bude miki qofar salin alin,amma tunda kika musa to sai na gama shiryawa tsaf sannan zan bude ki mu sauka tare" tanaji tana gani yayi funfurus yahau shiryawa a gabanta ko kunya baiji,haka ta zauna ta kallo bango harya gama ya budeta.

Har daki yabita ta gama daukar abinda zata dauka kaman wani body guard,tana kumburi tana komai amma bai kula ba ta fito suka fita.

Gidansu ya soma kaita,ta cika da mamaki sanda suka isa taga ya sake cikinsu sosai kaman yadda suka saba a baya,sai taga kamar ma sunfi zumudin zuwanshi akan nata,hira suke abinsu da umma kamar danta,baqinciki yasa ta kasa sakewa ma bare tayi hira,basu bar gidan ba sai qarfe daya da rabi na rana bayan yaje masallacin layinsu yayi sallah sannan yace ta taso,kaman ba zata tashin ba,don ita sam lokacin bai isheta ba,amma yadda umma ke jifanta da harara yasa dole ta miqe tabi bayanshi.

Daga nan gidan anty zubaida sukayi,can dinma haka suka gaisa da antyn cike da sabo,sannan ya yiwa anty zubaidan sallama kan zaije anjima zai dawo ya dauki shahidan.

Kusan fiye da rabin hirarsu ya ranar jirwaye me kama da wanka anty zubaidan ta dinga mata da gugar zana,ta kuma fahimceta sarai saidai tayi kaman bata gane ba,duka dai kan zamantakewarsu ne da nafisa dake shirin shigowa gidan,wanda duka ita tana ganin wannan ba matsalarta bace,dubanta anty zubaidan tayi sanda suke tsaye cikin kitchen tana tayata yanka cabbage zata hada coleslow
"Ranar yaushe zaki yinin naki ne banji kince komai ba,yaufa alhamis,lahadi kuma daurin aure" baki ta tabe bayan ta dubi anty zubaidan
"Ko nawa bikinma ban tsaya wani tsara wuni ba bare bikin wasu" ta fadi cikin qunquni,murmushi ya subucewa anty zubaida saita kada kai,lallai yaro yaro ne,ga zallar kishi na bayyana kan fuskarta da kalamanta amma taqi yarda da cewa kishi take
"Wancan daban wannan daban,bakyace ba zakiyi ba kodon idon mutane,kuma kema zaki buqaci wadanda zasu tayaki karbar amarya"
"Waini zan karbeta ma?" Ta fada tana nuna kanta da wuqar hannunta
"Eh mana,haka akeyi ai" saita jijjiga kai tana ci gaba da yankanta
"Lalllai kam" anty zubaida ta fuskanci zancan ciwo yake mata ba tare datasan da hakan ba,sai kawai ta shareta suka shiga wata maganar daban.

Bayan sunyi sallar la'asar anty zubaidan tace tazo ta rakata kitso,ba musu ya dauki mayafinta suka fita a motarta,huda tace zata bisu antyn yace sam tayi zamanta,suna tafe a motar antyn na nuwa shahidan wasu robobi masu dauke da gumba ta kwakwa da dabino,wanda idan kanaci zaka xaci an hada kayan qwalamane kawai sai aiki a jiki,wadda takan jima jikin mace bata bar jikinta ba,ta dinga mata dabara kanta dandana mata taji,haka ta dinga ci suna hira,antyn tana tuqi a hankali har sai dataci da yawa,ta sake nuna mata wata roba wadda ke cike da tsumi tace
"Sha kiji wannan fa"dan bata fuska shahidan tayi
"Wainikam anty wadan nan ba irin kayan nan naku bane na matan aure?" Harara ta jefa mata
"Ke matar shika ce?" Sai zancan ya bawa shahidan dariya,ta bude robar ta ta soma sha,zaqinsa da dadinsa yasa sai data sha rabi,abun har ya baiwa anty zubaida dariya tace
"Ya haka?"
"Wannan kam yayi dadi sosai shima"
"Tsumin maman farida ne,jiya aka aikomin shi daga zariya"tana rufe robar tace
"Amma yayi dadi wlh ya tsumu" dariya ta sake baiwa antyn.

Bata gane inda sukazo ba saida

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment