Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai da kuka da magiya kansu yafe mata,to hausawa sunce tsakanin daa da iyayensa sai Allah,hakance kuwa ta kasance,suka yafe matan tare da sake jan kunnenta kanta sake aikata sakarci makamancin wannan,ta kuma nuna musu ta tuba,farinciki sosai ya cikata ganin ta cimma nasara a matakin farko,saita bijiro musu da magana ta biyu bayan 'yan kwanaki.

Anan ne kowa yacoge a cikinsu,abban yace sam da kunya a idanunsa bazai nemi anwar ya dawo ya aureta ba,,ganin abba yaqi saita waiwaya tana hawaye ta dubi mummy
"Mummy don Allah" kaita girgiza
"Wa?,ni?,toba dani ba sa lallen karya,idan anwar ya dawo yau yace zai aureki sai nafi kowa farinciki saboda sanin nagartarsa,amma a yanzu dai ina bayan mahaifinki,keda kika bata ke zaki gyara abinki" sosai hankalinta ya sake tashi ganin ga qoshi amma tana neman tayi kwanan yunwa,anwar kam tun kafin ta tunkari kowa shita soma tunkara amma babu wani abu dake nuna mata cewa zaya saurareta,kai ta jinjina gamida sakin murmushi lokacin da wani tunani ya fado mata a rai,lallai hanyar da akabi da farko wannan karonma ita za'abi.

Cikin kwanakin ta dinga fakon wayar abbanta,tasa ido sosai ko Allah zaisa ta samu damar dauka.

Kwanakin sa'ida a gidan kwanakine da suka sake kawo kusanci qwarai tsakanin shahida da anwar din ba tare da sun ankara ba,dukkansu kowa na qoqarin yin abinda zai wanku a idon sa'ida koda zata baiwa anty usaina labari,takanyi kwalliyarta kamar kowacce mace kafin ya dawo daga aiki,tayi abincinta ta kammaleshi waje guda,idan ya dawo daga aiki takan bishi sama koda idan tahau din xata shareshi ne,kota takali fada kaman yadda yake mata shima,zata hada masa ruwan wanka koda ba zata kalleshi ba,zasu sauko tare,suci abincin tare sannan suyi hira tare,daganan zasu tafi saman su mata saida safe,tsaf ta dauke yadda yake mata kaman yadda anty usaina ta bata dama,shirinta sosai take tayi kwanciyarta bacci,wani lokaci ta kwashe masa dukan filo da abun rufa,wani lokacima idan taso gadon gake rabawa inda bashi da wajen kwanciya sai qarshen gado.

Takanyi mamaki sau tari idan taji yaqi yace mata uffan bare ya kulata saidai ido kawai,abinda bata sani ba shine shi daya yasan me yakeji cikin jikinsa da zuciyarsa,qiri qiri ya birkice kan ta daina saka kayan da take sawa din saboda yadda yake azabtuwa amma saiya fakaice mata da cewa basu kamata bane,abinda ya fuskanta shine duk sanda ya mata wannan fadan toya takalota ne ma,shigar da zatayi gobe tafi ta jiya xafi,yakai maqura qwarai wajen kauda kai da dakiya gamida aro jarumta da juriya ya azawa zuciyarsa,baiyi mamakin kasancewar hakan ba duk da yadda abunda ta aikata ke yawan fado masa,don a iya shekarunsa abinda yake da buqata kenan,babu wata baiwa da Allah baiyi masa ba,idan ya kasancema baijin hakan abun ya tuhumi kansa da lafiyarsa ne.

Sa'ida da zatayi sati daya sai gata sun riqeta har sati uku,don kowannensu zuwanta yasa gidan yana masa dadi,ita babu zaman kadaitaka da rana,yayin dashi kuma ya samu abokiyar firar dare,sai data cika sati ukun anty usaina ta matsanta su dawo da ita hakanan,haka suka tattara suka maidata ba tare da duk sunaso ba.

Daga gidan anty usaina sai taga ya wuce da ita gidan anty xubaida,duk yadda taji farinciki amma haka ta dake ba tare data nuna ba,suna zuwa qofar gidan ya waiwaya ya dubeta sanda take shirin fita
"Nace ki fita ne?waike irin ma bakiji dadi ba dana kawoki ko?" Yana sane ya fadi haka,don tunda suka aje sa'ida suka dawo bakinta ya kulle gam bai sake jin tace komai ba,saita juyo ta kalleshi
"Ni nace ka kawoni dama?"
"Au haka kika ce?" Kafin ta ankara ya saka hannunshi ya rufe murfin motar,kafin tace komai yaja motar sunbar qofar gidan,wani qululu ya tsaya mata sanda taga da gaske fita zasuyi daga unguwar,ga qoshi ga kwanan yunwa,haka ta zuba masa idanu tana dacin rai,bakin wani qaramin store taga ya tsaya ya kashe motar ya fice,baqinciki ya sanyata kifa kai kan cinyoyinta,har sanda ya dawo ya tada motar bata daga kai ba.

"Bude ki shiga ku gaisa,saura ki zauna" ta tsinci muryarsa yana fada,ta daga kanta a hankali saita sake ganinsu qofar gidan anty zubaidan,dadi ya sake kamata batasan sanda ta balla mishi harara ba sannan ta fice da sauri,tana jinsa yana cewa
"Ni kika harara?" Tayi shigewarta da sauri gudun kafa ma yace ta dawo.

Kaman anty su huda zasu goyata amma ta hada rai tsaf tace tayi fushi,zuwansu daya ba wanda ya sake dawowa,da qyar ta sakar musu fuska suka shiga hira,faruq ne ya futa suka gaisa da anwar wanda anty zubaida tayi tayi ya shigo su gaisa amma yaqi wai mai gidan bayanan bazai shigo masa gida ba,saiga faruq da leda niqi niqi yace inji anwar din.

Sun kusa a qalla minti talatin suna hira kaman ba zata tafi ba,aiken da anwar din yayita yi yasanyata dole tayi musu sallama ta fito.

Aje wayarshi yayi sanda ta bude motar ta shigo daidai lokacin daya gama karanta saqon alhj abba cewa gobe misali bakwai na dare yanason ganinsa,akwai muhimmin abu da zasu tattauna,suka hada idanu saita basar,ya gyada kai yana sakin qwafa,shi kadai yasan hukuncinta yau.

Yana fitowa daga wanka tana shigowa dakin sanye da kayan baccinta masu kauri da qaramin hijabi,taso tayi kwanciyarta a dakinta amma saita kasa,haka kawai taji tanajin tsoro,ta riga ta saba yanzu da kwana da mutum a cikin daki,kanta ta dauke ganinsa daure da towel tana gunguni can qasan rai kamar yadda ta saba duk lokacin data ganshi haka,ta tsani ganinsa da towel saboda wani irin kwarjini da yake mata,hakanan gabanta ya dinga faduwa kenan harsai ya sanya sutura,yana jinta ya qyaleta baice mata uffan ba har ya kammala,ya saka nashi kayan baccin,ya dubeta a sannan tuni tayi abinda ta saba,ta tattare masa duka filallukansa harda abun rufarshi,yadan jima taaye yana qare mata kallo gamida tuna meye bataso?,murmushi ya saka
"Ko banza na rage zafi" ya fada qasan ranshi,sai kuma yadan bata rai shi daya yana qaryata kanshi kan cewa ba zafin da zai rage.

Bata zata ba tajishi dab da ita,kafin tayi kowanne motsi ya sanya hannu ya birkitota gaba daya ya aza mata nauyinsa,numfashinta na fita daqyar take qoqarin tureshi rai bace
"Ka dagani,meye hakan?"
"Bani kikewa tsaki ba?,yau zako banbance tsakanin aya da tsakuwa"
"Wace tsakuwa wace ayar,ba abinda zan banbance" ta fada tana ci gaba da yunqurin tureshi duk dako gezau baiyi ba,idanunsa ya saka sosao cikin nata yana mata wani kallo dashi kansa baisan yana mata shiba,cikin sakannin da basu wuce goma ba ya kashe mata jiki gaba daya,saidai qwarin gwiwar da take baiwa kanta yasa taqi yarda da mutuwar jikinta,sai daya gama zuba mata dukkan wani dafi sannan ya hade bakinsu waje daya.

Baisan abinda yake aikatawa ba ya wuce plan dinsa ba,baisan abun yaso ya wuce yadda ya tanada ba saidaya lula wata duniya,wadda daf take daya shiga duniyar ma'aurata sannan tunaninsa ya dawo,kaman wanda aka tuna masa shahida ce saiya samu kanshi da miqewa da hanzari ya mirgina gefe daya sannan ya tashi ya zauna gami da zuro qafafunsa qasa ya dafe kanshi da dukka hannayenshi saboda yadda yake sara masa yana ambaton sunan Allah.

Itama cikin hanzari ta miqa hannu ta janyo rigar baccinta ta zura,ta miqe da gudu ta fice daga dakin ta sauka qasa,bai iya dago kanshi ba bare ya kalleta,gudu gudu sauri sauri ta qarasa sauka,ta bude bakinta ta shige,kai tsaye ta fada saman gado rub da ciki tana sakin wani irin kuka,kukan da batasan na meye ba,hakanan takejin rauni da wani irin abu mai qarfi da nauyi yana tasowa kaman zai fasa zuciyarta.

Ta jima a haka kafin ta sasauta kukan,zuwa sannan fuskarta ta hada jaa sosai,idanunta sun tasa sunyi rumfa,bandaki ta shiga ta hada ruwa tayi wanka sannan ta fito ta sauya kaya ta koma saman gadonta ta kwanta,zuciyarta na jero mata tunanuka barkatai,harta rasa wanne ne na dauka a ciki?,me yasa anwar ya zabi rusa rayuwarsu da ruguza farincikinsu ne?,me yasa anwar baiwa rayuwarsu su duka adalci ba?,shin ya isa iya abinda ya gani kawai ace ya ruguza soyayya qauna tausayi da kulawa da suke baiwa junansu tun zamanin quruciya danya sharaf?.

Daga bangarensa shima ya dade a zaune ahaka kafin daga bisani ya samu shiga bandaki yayi wanka duk da matsanancin ciwon kan da yakejin kamar yana barazanar raba kanshi gida biyu ne,ko tantama bayayi jininsa ya hau,duk da haka sai daya daura alwala sannan ya fito ya sauya kaya ya kafu saman abun salla ya soma nafilfilu,yana roqar Allah ya cire masa abun daga zuciyarsa,koda sassaucima kadai ya samu yana maraba da hakan.

Raka'a hudu yayi abun ya gagara sakamakon riqewa da mararsa tayi,take ta shiga ciwo gadan gadan,anan ya duqe saman abun sallar yana kiran sunan Allah gamida fidda nishin ciwo.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Sama sama ta dinga jinta washegari kamar ledar da iska ke yawo da ita,amma duk da haka bata gaza tashi tayi dukka ayyukanta ba,sauri sauri ta dinga don batason su hadu dashi,haushinsa da kuma wani abu mai kama da kunya takejin yana taso mata,abun haushin shine yadda duk sadda zata gifta sai idanunta sun kalli samanshi,tunda asuba taje saka kunnen jiyo motsinsa amma ko alamar motsinsa ma bataji ba,a haka ta gama ta koma daki ta sake saka ruwa mai dumi sosai tayi wanka ko zataji ta warware,tadan gasa idanunta dabai baje ba da ruwan dumi sannan ta zira doguwar rigar wani yadi mai taushi ta koma saman gadonta ta kwanta,ko marmarin abincinma bataji bare tasa a bakinta.

Tara ta wuce,goma tazo tawuce hakama sha daya,ga sha biyu na rana tana neman yi,hakanan taji hankalinta ya kasa kwanciya,duk da yadda zuciyarta ke gargadinta ta kasa kauda tunanin,zumbur ta miqe saboda tunawa datayi yadda tabarshi jiya dafe da kanshi,saita daura dankwalinta ta zira takalminta ta bude qofarta ta fito.

Sai data leqa harabar gidan taga dukka motocinsa na nan alamun bai fita ba kenan,sannan ta soma hawa saman,ta qofa ta leqa saitaga falon wayam ba kowa,da alamu ko fitowa baiyi ba,saboda haka ta tura qofar falon ta shiga,ta zarce dakin gadonshi,nan ma data leqa sai taga babu kowa ciki,mamaki ya cikata to ina yayi?,hakan ya sanya ta tura qofar ta shiga nan ma,wanda hakan yayi daidai da bude qofar toilet ya fito daga ciki jikinsa na digar ruwa da alamu wanka yayi.
[8/21, 12:42 PM] Nadady: *Alqawarin Allah*
43

Wani irin murdawa mararshi tayi wanda hakan ya sanyashi duqawa riqe da cikinsa,ya tako a haka a hankali zuwa gefan gadon,idanu ta zaro jikinta ya dauki rawa,ta tako ta tsaya daga bayanshi amma ta kasa cewa komai,da qyar cikin rawar murya tace
"Sannu,baka da lafiya" kallonta kawai da yayi da qwayar idanunsa da suka kada zuwa launin jaa ya tabbatar mata da bashi da lafiyar kenan,ta juya zata futa da niyyar ta kira anty usaina ta shaida mata,saiya dakatar da ita
"Jirani na shirya,zanje naga likita".

Hannu likitan ya saka ya cire abun abun awon jini daya sanya a dantsen anwar din yana kallonshi
"kamar yadda na tsammata ne,jininka yahau sosai,kamarma yahau fiye da kowanne lokaci,gaskiya anwar bazan boye maka ba,wani lokaci sai naga kamar kana wasa da lafiyarka ne,bansan meya hanaka kwantar da hankalinka ba ka samu jinin nan ya sauka gaba daya,sai yayi kaman ya sauka saiya sake hawa,bansan daga inda matsalar take ba" murmushin qarfin hali yasaki,ya lumshe idanunsa kana ya bude
"Share kawai khalid" likitan mai sunan khalid ya waiwaya ya dubi shahida wadda ke zaune wata kujerar daban,hannayenta rungume a qirjinta,ta zubawa anwar ido ba tare da yasani ba,kallon mamaki take masa na bayanan da taji daga bakin dr khalid,wanne irin hawan jini?,yaushe anwar din yasamu hawan jini?,iya saninta dashi kaf tarayyarsu anwar baida hawan jinin,yaushe ya gamu da wannan matsalar?
"Madam" ya kirata wanda hakan yaja hankalinta zuwa kanshi
"Bayan hawan jini gaskiya abokina na buqatar kulawa,don Allah ki kulamana dashi,nasan kinfi kowa sanin mutumin kirki ne,lalurarshi ba zata yiwa mutane da yawa dadi ba" kai ta gyada likitan ya miqe yana cewa
"Ruwa naso indan saka maka,amma nasan hali ba zaka taba yarda ka zauna ba,bari na rubuta maka wasu magungunan na bayar a karbo maka,madam sai a kula da bashi akan lokaci" kai ta sake gyadawa tana duban anwar din,saita kauda kai sanda taga ya waiwayo suna shirin hada idanu.

Suna tafe a hanya motar ta dauki shuru,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,tambayar ta yiwa shahida tsaye a rai na hawan jinin anwar,yayin data gefan anwar din maganganun dr khalil suka dinga kai kawo a qwaqwalwarsa,tabbas ba shakka shine mutum na farko da zaifi kowa son rabuwa da cutar,zaifi kowa son ganin ya cire kome cikin ransa,zaiso ace ya goge kome dake damunsa,amma saidai shi kansa yasan hakan bame yiwuwa bane,shahida ce,idan da wata macen ce daban ha tabbatar da tuni ya cireta daga rayuwarshi irin fitar da mai rai kanyi daga duniya wanda har abadan bazai dawo cikinta ba,amma akan shahidam hakan ya gaza,ya sani cewa koda zai fada a baki koda zai nuna a aikace shahidan bata dameshi ba yayiwa kanshi qarya,karon farko dayakejin inama inama,inama ace bai kalli hotunan ba,inama ace ranar baije gidansu zance ba bare yaga abinda ya gani,inama ace shahidan bata fada halin data fada ba a baya,da wannan tunanin suka isa gida,da kanshi wannan karon yasha maganin sannan ya shiga bedroom dinsa ya kwanta kozai samu relief.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


A kasalance yake shiryawa cikin farar shadda,riga iya gwiwa mai gajeran hannu da dogon wando,kana ganin yadda yake shiryawar kasan cewa ba wani dadin jikinsa yake ji sosai ba,yana daura agogon hannunshi ta turo qofar dakin da sallama,hannunta riqe wata butar shayi me kyau,da mamaki take dan dubanshi saidai bata tanka ba ta aje butar
"Ya jikin?" Ta tambaya a taqaice,daga kai yayi ya dubeta yadda ta juya baya ya maida kansa yaci gaba da daura agogonsa sannan yace
"Alhamdulillah" tadanyi taku biyu sannan ta sake tsaiwa,ya fuskanci akwai magana a bakinta saiya amsa
"Tun jiya akwai alqawari. Haduwarmu dashi,jiya banjin dadi,so yau nakeson nacika" yana gama fadi ta taka ta sauka daga saman,dama tanson jin fitar zaiyi amma tanajin nauyin tambaya.

Tun jiya take zuba idanun ganinsa,ta kasa zaune ta kasa tsaye,tun bakwai na dare take zirya tsakanin harabar gidan,falon abbansu zuwa nasu falon da dakinta ma gaba daya,ganin goma na dare tayi hankalinta yayi mummunan tashi,Allah yasa abba bai gane ba,Allah yasa anwar bai kira abba ba ya sanar masa yaji yana nemansa ba abba kuma yace bashi bane,daga daren zuwa safiyar ranar ji tayi kaman ta zare,duk motsin shiga da fitar mota a gidan yana kan idanunta,saida dare yayi ta tabbatar babu wani sauran wanda ka iya zuwa a wannan lokacin sannan ta haqura.

Da safema haka ta dasa abun zama cike da fata da kuma buri,qarfe goma da rabi da minti takwas aka saki horn mai gadi ya doshi qofar don ya bude,gabanta wani mugun faduwa yake haka tamiqe tsaye tana duban qofar gidan,kusan shidewa tayi sanda taga fitowarsa daga motar,idanunta qur akanshi yana sake burgeta duk wani motsi da yayi,tana kallon aka masa iso cikin falon daddyn,cikin wani mugun hanzari ta diba tayi cikin gida kai tsaye ta wuce dakinta,hijabi ta lalubo ta zira saman kanta sannanta sake fitowa da hanzari don kada lokaci ya qwace mata.

Sanda ta shiga mummynta na tare da daddyn,hakan yayi masifar yi mata dadi,sait tayi qoqarin daidaita nutsuwarta ta taka zuwa cikin falon da sallama.

Dukkaninsu suka amsa mata,ta isa gefan daddyn inda anwar ke zaune qasan carfet saboda girmamawa suna gaisawa,nan ta duqa kan duka gwiwoyinta,ta saki kuka sosai wanda ya karade ilahirin falon,duka sakin baki sukayi suna kallonta,mummy ce cikin hade rai tace
"Kewai meye haka?,wanne irin shashancine wannan kawai zaki shigo kisa mutane a gaba da kuka?" Cikin muryar kuka tace
"Don girman Allah mummy ku yafemin,ku yafemin,ku roqamin ya anwar shima ya yafemin"
"Me ya dawo da wannan maganar data riga tawuce kuma nafi?"
"Gafarar ya anwar nake nema" gaba daya kanshi ya kunce,shi sam.bai dauki abunda tayi a matsayin wata matsala ko abun bacin rai ba,tuni ya riga daya wuce wajen,tun a lokacin da abun ya faru shiya tattara komai daya shafi wannan fannin ya ajeshi a gefe,baison zancan yayi tsaho saboda haka yace
"Ya riga ya wuce har abada" ranta taji yayi,wani mugun sanyi,alamun nasara na tabbata kenan a gareta,saita sake sunkuyar da kanta qasa sosai sannan tace
"Bansan cewa nayi wauta ba kuma nayi kwaba saida na rabu dakai,nakai kukana ga abba da mummy amma kowannensu yaqi mara min baya ka dawo cikin rayuwata,sunce idan ka amince suna murna da hakan,saboda sunsan cewa idan sukayi maka magana ko bakaso zakace eh,gani a gabanka anwar don girman Allah inason ka sake dawowa rayuwata karo na biyu,ka yiwa iyayena dake shauqin son ganin haka alfarma wanda alkunya da kawaici yasa suka kasa gaya maka"
"Ke nafi!" Abbanta ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsaw,a,bataji komai ba don idanunta da zuciyarta sunyi nisa wajen son ganin cikar muradi da burinta,saita daga kai ta dubi abban sannan ta sake sunkuyarwa
"Abba na fadi masa gaskiyar abinda yake faruwa ne,na tabbatar da zaka iya da kaine xaka nemi ya aureni karo na biyu....anwar,ka duba wannan alkunya da kara ta iyayena gami da girman soyayyar da nake maka" baqinciki ya kama mummy na yadda sam halayen nafisan suke wadansu irin mabanbanta daban,ta kawo mata duka anwar ya dakatar da mummyn cikin sauri
"Rabu dani na mata duka,baki da kunya nafisa ko kadan?,a gabanmu kice kin fasa aurensa,sannan ki dawo a gaban namu dai kice ya aureki?,wace iriyar yarinya ce ke?" Cikin kuka sosai nafisan tace
"Kuskure ne mummy yanzu kuma na gane kuskuren da nayi,wallahi idan babu anwar rayuwata ba zata taba dai daita ba,mummy ku tayani bashi baki"
"Ce miki akayi baida zuciya da zaki gujeshi yanzu ki dawo masa saboda rashin ta ido?,kema kinsan bazai taba yiwuwa ba" mummy ta amsa mata tana jifanta da harara,so take kawai ta samu dama ta daki bakin nafisan ya fashe ko zata samu sassauci takaicin dake cikata
"Na amince zan aureta" anwar ya furta,lafazin daya girgizasu dukka su ukun,basu taba zata ba sam ko a mafarki,sunyi tsammanin bazai taba yarda ba,cikin hikima yake karantar yanayin fuskar alhj abba da munny bilkisu,ko basu fada masa ba ya gama karantar yanayin da zukatansu suka shiga,alhj abba da mummyn suna da daraja a idanunshi,ya sani cewa tsantsar kara kawaici da alkunya ne dasu,amma da qauna kowa ya sani suna matuqar qaunar nafisa,me yasa shi bazai iya musu kara ba ya auri diyar su wanda yasan shine cikon muradinsu,ba shakka da nafisan diyar wani ce da ya barta kenan har abada,amma ko a lahirama wani yana cin albarkacin wani bare nan gidan duniya.

"Bazaiyiwu ba anwar,ka tashi kawai kayi tafiyarka" cewar alhj abba,don harga Allah bayason su xama sila na yiwa anwar din dole,wani tashin hankali ya saukowa nafisan,ya ga qoshi ga kuma kwanan yunwa tana shirin yi?,me yasa abban nata zaiyi mata haka?,girgixa kai anwar yayi cikin qarfin hali
"A'ah abba,ba za'ayi haka ba,nafisa qanwa take a gurina idan da kara da kawaici,abinda ya wuce ya riga daya wuce tunda ta gane kuskurenta,Allah ya yafe mana gaba daya ya kuma kiyaye gaba" murna farinciki kaman ta taka rawa a gabansu,saidai yanzu ba lokacin hakan bane,sake kwantar dakai tayi sosai ta sake neman afuwa gamida nuna tsantsar nadamarta,itakam hajiya bilkisu miqewa tayi ta fice tabar falon,tana jin ciwo cikin zuciyarta sosai duk lokacin da nafisan ke roqar soyayya,ta rasa wacce irin diya Allah ya bata?,zataso ace nafisan ta auri wanda shi yake mutuwar sonta ba ita take mutuwar sonshi ba,ta rasa meye matsalarta meye damuwarta?,ba kalar saurayin da bata dashi wanda kowa neman yardarta kan ya aureta yake amma sam ita ta qwallafa rayuwarta kan anwar,eh anwar ya isa mutumin da za'aso a zama mata a gareshi,amma duka hakan a ganin mummyn xaifi kyau idan har shine yazo da kanshi ya nemi hakan.

Tunaninsa ne ya dinga kasuwa kashi kashi,abinda ya faru yanxu cikin gidan alhj abban,tabbas shi shaidane kan irin son da nafisan ke masa wanda sautari hakan yakan bashi mamaki qwarai,karbar aurenta da yayi yasani shi kadaine abunda zaiwa alhj abba ya saka masa dimbin alkhairin da yayi masa da kyautatawa a rayuwa,da yadda yake kallonshi tamkar danshi,saidai ko daya zuciyarsa babu nutsuwa ko jin dadin karbar da yayi,bayajin wani daidaito ko daya kan batun nafisan,duk da agefe guda ya sani yana da buqatar kulawar mace,amma,ta yaya wata zata sanyo kai cikin rayuwar gidan alhali ga yadda take?,ta yaya zai kawo gyara?,tuninsa ya sake tafiya kan hotunan dake aje har yanzu suna yankawa gami da qona zuciyarsa duk daqiqa ko sa'a daya da zata shude,duk lokacin da idanunsa suka kai kai,yaha shahidan tsirara tare da wani sai yaji kaman mai shirin haukacewa,duk sanda ya kallo hoton yaga shahidan rungume qirjin daya daga cikin masu saida kayan maye sai yaji dama makaho ne shi,Allah ne kadai da qarfin addu'a suka sashi ya rayu har yakai bigiren da yake kai a yanzu.

Sassanyar ajiyar zuciya ya saki sanda yake kashe motar shi,ya daga hannunsa ya kira maigadin,cikin girmamawa ya qaraso
"Baqi indai ba 'yan uwa bane na jiki duk wanda yazo kace musa bama nan"ya qarashe maganar cikin muryar dake nuna jiki da zuciyarsa duka babu qwari
"To ranka ya dade" ya wuce ya koma bakin qofa yayin da shi kuma ya fito,ya dinga takawa a hankali zuwa cikin falon.

Shuru yake kaman koda yaushe,saidai ya hangi abinci a shirye saman dining,hakanan yayi sha'awar xama a falon,idonsa kan wata tasha da suke nuno fasahar zamani da qere qere,suna wani shirin kan na'ura mai qwaqwalwa,tsohon mintuna idanunsa nakan allon talabijin din,wani bayani da baqon nasu yakeyi ya dauki hankalinsa matuqa,yadda ci gaban xamani yazo da sauye sauye,yadda za'a qirqiri abu a idanunka kaga haka yake,amma da za'a sanyashi a na'ura sai kaga abun ba haka yake ba,tsahon minti ashirin yana bayanin wanda yayi matuqar daukan hankalinsa.

A hankali tunaninsa ya karkata ga abunda zuciyarsa keson tuna masa tun daxun,saiya miqe da hanzari ya soma haurawa saman cikin sassarfa,bai tsaya ko inaba sai bakin safe din nashi,cikin sauri ya tsugunna,ya soma saka lambobin sirrin ya budeshi,envalope din ya ciro kaman ko yaushe ya zazzage hotunan ciki duka suka fado
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta kaman yadda ya saba sanda yake binsu da kallo daya bayan daya,duk sanda zai gansu yakanji kaman duniyarshi sama ta kona qasa ne,kullum yanajin kamar ranar ya soma ganinsu,saiya zauna sosai zuciyarsa na fata da kuma burin samun mafita,xuciyarsa ta cika da fatan dama ace ba haka bane,dama ace ba ita bace,dama ace ba shahida bace a jiki shine bai ganin dai dai duk sanda zai kalla,saiya sake gyara zamanshi sosai,ta ina zai fara?,bashi da wani qarfin sani ta wannan fannin,idan kuma yi masa za'ayi duk duniya bayajin akwao wani mahaluki da zai iya bari yaga hotunan,koda mahaifiyarshi data haifeshi ce inda tana raye.

Sake miqewa yayi da sauri saboda tunawa da yayi da makarantar computer da sa'ida ta mishi xancan ummi ta musu register xasu fara zuwa,idan bai manta ba ta gaya mishi akwai online classes da special classes da za'azo har gida a koya maka,system yayi nufin kunnawa,sai yaga kamar ba zata masa sauri ba,ya ciro wayarshi daga aljihunsa ya kunna data sannan ha fada google ya soma rubuta sunan makarantar,bai manta sunanta ba saboda kusan ma'abocin siyayya ne a shagonsu na yanar

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment