Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasan cewa ba zata yarda komai ya wakana ba,to ba shakka zatayi iya bakin qoqarinta ta ragewa kanta zafi ta wannan hanyar,uwa uba a nata tunanin gwara ta rikita anwar din,ta yadda ko wata shida tayi bata barshi yayi ba bazai iya haqura ba bazata fita daga ranshi ba,zaita bibiya ta yadda duk randa akace komai zai wakana zai zamto tamkar salla a wajensa a ranar.

Mamaki qwarai yakama anwar din,yadda take tafi da lamuran nata ba kunya ciki,amma bashi da wata hujja dazai hanata,tunda haqqinta ne ta kuma nema,ko a wajen Allah idan ya hanata yayi laifi,saboda haka ya bude mata nashi salon wanda yakusa tafiya da ita har taso mance sharadin maganinta,saidaga baya data ankata ta tattakura ta tureshi gaba daya,wanda yatafi luu saboda dukka qarfin jikinsa babu,gaba daya hankalinsa yana gab da tafiya shima,da farko ya zaci tsoro takeji yabi hanyar da zai amintar da ita amma furrr taqi,dole daga qarshe ya miqe dukka jikinsa rawa yake,yakai wani stage da shine na qarshe,yakai matakin da yakejin ya kamata ace shima ya wuce sahun samartaka,shi yasa yadda tazo mishin ya tabashi sosai,amma bazai sake taba koda yatsarta ba ayau tunda bata da muradi,saiya bude toilet din dakin ya shiga ya budewa kansa shower tun daga saman kanshi,sanyin ruwan na ratsashi yana qoqarin controlling kanshi,ya jima ahaka kafin ya samu yanayinsa ya daidaita sannan yayi wanka ya fito,a sannan ya sameta zaune,ba alamun tsoro ko kunya a fuskarta,ta maida rigar baccinta tana shirin kwanciya,gefen gadon ya samu shima ya kwanta yana sakin numfashi,ta matso da niyyar rungumeshi ya kada mata yatsa,don ba shakka idan ta sake ta tabashi a yanzun komai zai iya wakana,shi kuwa baijin zai yiwa nafisan dole,don badon tun farko ta nuna aniyarta bama ba abinda yayi niyyar nema daga gareta,har sai lokacin da zuciyarsa ta gama gamsuwa da aminta da ita,haka takoma can qarshe tana kallonshi,baisan me take ji bane,tanajin ta fishi buqatuwa zuwa gareshi,amma dole tabi sharadi saboda tacika muradin zuciyarta.

Qarfe goma da rabi na safe ya tura qofar dakinsa ya fito,dai dai lokacin da shahida ke haurowa saman bayan ta gama kintsa inda zata kintsa din ta dafa abubda zataci dai dai cikinta,don batajin zata iya musu wani abinci suci daga nafisan har anwar din,hada idanu sukayi,ita tana dubanshi ne cikin mamakin me yake a dakin,yayin dashi kuma yake kallonta saboda yadda tayi masa kyau matuqa gaya cikin wasu riga da skert,kanta babu dankwali saboda saurin da take ta gama komai tahige dakinta,don batason ganin kowa cikinsu,take abun jiya ya taso masa,har sai daya rintse ido gami da dunqule hannunsa yana dan cije lips kadan
"Ina kwana" ta gaidashi tana niyyar wucewa,qamshin nan nata mai sanyi ya cika wajen gaba daya
"Lafiya lau" ya amsa da wata irin muryar datayi laushi,yadda tamasa maganar bai masa ba,yana buqatar fiye da hakan,don haka yabi bayanta tana shiga shima yana saka qafarshi.*Alqawarin Allah*
47



Ja tadanyi da baya tana kallonshi,sai kuma ta juya taci gaba da takawa har zuwa gaban mudubi,ta aje tray din hannunta,kafin ta waiwayo yana tsaye dab da bayanta,dubanshi take idanunsu cikin na juna,fuskarta a dinke tsaf saiyace
"Koki tambayenima yana tashi saboda baki damu dani ba?" Kamar ta maida masa mai zafi sai kuma taga lokaci yayi daya kamata ta dinga gyara harshenta kodon nafisan,idanunta ta janye tana zamewa daga ritsatan da yayi tana cewa
"Na tambayeka ina kwana,kuma me kakeso bayan haka?,zancan ban damu dakai ba kaima kasan a zaune take" saiya zaro ido yana dubanta,kallonta na masa dadi gamida kashe masa jiki
"Shikenan,na gode,na samu wadda ta damu dani din ai yanzu....me aka dafa mana?" Ya tambayeta yana dage girarshi,maganarsa hakanan taji ta taba ranta,tana zama bakin gado tace
"Ka tashi wadda ta damu dakai din ta hada maka" bai tanka mata ba ya soma takawa zuwa inda taajje nata abincin,sai gani tayi kawai ya soma hadawa,ya zauna sosai saman kujerar ya soma ci,yana ci yana kallon idanunta ko zatace wani abu,amma saita shareshi kaman bata gani ba,saita ciro wayartama dake chargy gefan gadonta tahau danne dannenta,ba haka yaso ba amma saiya qyaleta,harya kammala ya miqe yadan matsa gabanta
"Nina qoshi,xaki hada mata itama?"ya kaita maqura saita daha fararen idanunta ta zube mishi su,dama abinda yakeso kenan ganin qwayar idanun nata
"Da aka mata auren bata iya girki ba dama?" Dariya taso qwace masa,amma baiso ya tsawaita tsayuwarsa a wajen saboda idanunta nason rudashi,irin feelings din da yakeji a tattare da ita shekarun baya da suka shude,saiya saki murmushi wanda ya qarwa fuskarsa kyau ya soma ficewa daga dakin yana cewa
"Na gode".

Qaramin tsaki taja tana aje wayar hannun nata wanda dama danne dannen dole take,takalli kwanukan abincin daya gama ci,ba wani mai yawa ma ashe yaci ba,saita jawo ta cinye sauran,sannan ta maida kwanukan kitchen ta dawo ta rufe dakinta abinta.

Ranar sur wani tayi abinta a daki,ko anwar din bata sake bari ya ganta ba bare nafisan,gwara shi da alama ba wunin gidan yayi ba,duk hayaniyar da ake da baqi data ringa yi tana jinsu,kallo tasha sosai a laptop dinta,series series masu kyau,idan ta gaji ta kashe ta huta.

Ba ita ta fito ba saida akayi sallar magariba,bayan yayi wanka ta shirya cikin wani dan banzan material me kyau da daukar ido,qasa ta sauko donta shiga kitchen,gaba daya falon qasan ba'a saitinsa yake ba,kana gani kasan cewa ansha baqi,baki ta tabe ta wuce kitchen,canma dai kamar falon yake,saita hauyin abinda ya shigo da ita,ta hada sanwar jallop dai dai cikinta ta samu waje ta tsaya tana jiran ta dahu ta juye abarta ta tafi da ita,wayarta na hannunta tana duba saqonni ta watsapp,ta samu zunnurah online suka shiga hira tana tsokanarta ita kuma ta biye mata.

Shigowar da akayi kitchen din ya sanyata daga kai,hada idanu sukayi da nafisa wadda ta shigo neman abinda zata ci,don duk abincin baqin ne suka dafa sannan kuma ya qare babu wani abinci da yayi saura,idanunsu suka hadu dana juna,ta xubawa shahida ido,kallo daya shahidan tayi mata ta janye idanunta ta maida kan wayarta suka dora hirarsu da zunnurah wadda ke tambayarta ina amarya,ta maida mata amsa
"gata yanzu ta shigo kitchen"
"Kitchen kuma shahida,bake ke giki ba?"
"Girki ni?,Allah ya sawwaqe,nizanmusu ma girkin jakar gidansu ce ni?"
"Baqonka fa annabinka"
"Karki sake fada,niba annabina bace wallahi,ina ruwan biri da gada,uban gayyarma bai dameni ba bare ita dorin dosano"
Emoji na zaro ido da dariya zunnurah ta turo mata sannan ta sake aiko mata da
"Shikenan kice ina gaisheta"ta maida mata amsa
"Bata isa ba wallahi,sanda tashigo bata yimin sallama ba nafarko kenan,nabiyu a qa'idar musulunci ita zata soma min magana tunda ita tazo ta taddani"dariya sosai zunnurah ta dinga yi,tana ganin kishin anwar qarara tattare da shahidan amma tana qaryata kanta da kanta,yanzu da zata fada cewa zatayi fur ba haka bane,saboda haka saita gwada tabotan
"Wai....muhammad anwar dan baiwane wlh,irin wannan kishi nashi haka da ake?" Emojin duka ta tura mata sannan tace
"Allah ya tsari gatari da saran shuka,nifa jiran zaman wa'adi nake,zunnurah anwar yajima da fita daga kaina gaba daya,shi yasa ko sha'awar ma zaman tuna me yafaru banayi game dashi,bana tunanin akwai wata qauna tashi da tayi saura a raina bare akai ga maganar kishi,kawai rainin hankaline banaso daga wajenshi ko wajenta,shi yasama ba wanda zan sakewa fuska bare ya rainani" saqon yana zuwa ya kashe data din ta aje wayar don duba girkinta,sai a sannan ta lura da nafisa ta fita,wadda ta qaraci satar kallon shahidan ta juya ta fita batare data iya daukan komai ba,duk randa zata ga shahidan sai taga ganin data mata yau yafi na jiya qawatuwa,ta rasa wanne irin abune haka?.

Dakinta ta kuma komawa ta bar abincin a gabanta donya huce taci gaba da amsa saqon zunnurah data dage tana son tuburata,turo qofar da akayi yasata daga kai tana duban me shigowar,anwar ne da alama bai jima da shigowa ba gidan,dagani wanka kawai yayi da sallah,jallabiya ce baqa a jikinsa data haskashi qwarai,maida kanta tayi kan wayarta taci gaba da abinda take har sai daya qaraso
"Sannu da zuwa" ta fada cikin shariya ba tare data dubeshi ba,bai amsa ba sai kujerar mudubi daya jawo ya zauna suka sanya plate din abincin a tsakiya,ya dauki cokalin da yake ciki ya soma kaiwa bakinsa,tsayawa tayi yana kallonshi cikin jin haushi,me yasa yake mata haka ne?,yanaci yana kallon idonta,ganin da gaske yana da niyyar cinyewa saita dafe hannunsa da tafin hannunta wanda batasan ma tafi haka ba,lumshe ido yayi tsigar jikinsa na tashi,saiya zame nashi hannun,kafin takai ga cewa wani abu ya miqe ya dauki gorar ruwan data aje ya balle yasoma sha,sai daya shanye tas sannan yace
"Indai zakici gaba da sonkai kina girkinki ke kadai bazan gaji da cinye miki abinci ba.....qarfe takwas da rabi inason ganinku"
"Karta shigomin wuri zan sauko qasan" ta fadi masa sanda yake gab da fita,bai waiwayo ba hakanan bai amsata ba yafita.

Takwas da minti arba'in ta miqe don amsa kiran,saita samu kanta da fesa turare hadi da sake gyara fuskarta,qaramin mayafi ta yafa ba tare data daura dankwali ba ta dauki wayarta ta sauko.

Sanda take saukowa nafisa na fitowa daga kitchen dauke da gorar ruwa da kofi,yayin da anwar ke zaune yana kallon VOA africa,idanunsa yakai kanta sanda take zama nafisa na miqa masa ruwan,saita waiwaya taga me yake kallo,shahida ce wadda ta samu waje ta tsume qafa daya kan daya,saita maida idanunta kan anwar da yake kurbar ruwan qaramin murmushi na fita daga fuskarshi,yayin da yake duban shahidan ta saman kofin,yasanta tun lokacin da da kadan ta dara qwaila,ya gama fuskantarta,babu shakka akwai tsiwa kenan yau a iya zaman datayi ya fuskanci haka,sosai nafisa ta qulu iyaka ta kawo wuya,ko ita data zauna ta tsara masa kwalliya cikin qananun kaya riga da wando bai kalleta haka ba,yadai yaba wanda yanayin yadda ya yaba din bai mata ba,zata zauna ya miqa mata kofin yace takai kitchen,haka ta amsa ta nufi hanyar kitchen din ta cika tayi taf.

"Kinyi kyaufa" ya furta cikin qaramar murya wadda tasa dole ta daga idanunta ta kalleshi,mugun dan rainin wayone mutumin,yayi magana da ita amma ba ita yake kalla ba,sai dayaga ta daga kai tana dubanshi sannan shima ya dubeta,ya mata wani kallo daya sanyata saurin janye qwayar idanunta.

Shahidan na kujerar dake fuskantarsa,yayin da nafisan ke zaune daura dashi,shuru ya ratsa na 'yan mintina sannan anwar yayi bismillah
"Shahida ga nafisa,nafisa ga shahida" kallon kallon akai na wani lokaci,shahida na sake qarewa nafisa kallo,fuskar data kusa tarwatsa tunaninta,fuskar data janye mata abun sonta,fuskar da saqonta yazama baqin aike a dukka tsahon rayuwarta,yayin da nafisa ke kallon shahida tana qissima irin cin zarafi da wulaqancin da zata sanya anwar yayi mata aduk sanda haqarta yacimma ruwa,irin wulaqanci da tozarcin dako uwarta data kawota duniya zata tsine mata ba zata yarda ta sake gama wajen zama da anwar din ba.

Jawabi yayi musu irin wanda akasarin mazan kanyi xuwa ga matayensu sannan yadora
"Zaku raba kwanaki bibbiyu kaman yadda akasari akafiyi,sannan idan akwai mai qorafi gyara ko shawara bismillah" shuru ne ya ratsa tsakani,nafisan ta kasa kunne taji ko shahida zata fito da wata tsirfar,ko zatayi wata magana da bata gamsheta ba,saidai taji bata tanka komai ba,ganin haka yasa tace
"Kamar yadda naga take taken gidan,da kuma abinda nakega zaifi shine kawai kowa ya dinga girkinsa,ba batun hade girki" sai a sannan shahida ta daga kai ta kalleta,da tana tsammanin zasu wani hada girki ne?,ko ta zaci itadin zata iya wani cin girkinta?,baki ta tabe tamaida kanta kan wayarta ba tare data tanka ba,tanaji anwar yana bata amsa da
"Idan hakan yayi muku nibanda matsala dashi" shuru ya sake ratsa tsakaninsu,sai qarar sautin tv kadan kadan,har yanzu dai shahidan bata tofa tata ba tunda tazo wajen,idonta na bisa screen din wayarta,yayin da gaba daya hankalin nafisa ya karkata kan shahidan,tana qare mata kallo cikin dabara,saidata sake bada minti kaman uku sannan ta rufe wayar ta miqe tadan dubi anwar
"Ni bacci nakeji,muje ka rakani" cikin mamakin dayayi qoqarin hadiyewa ya dubeta,saiya miqe din yawuce gaba,ta waiwaya ta watsawa nafisa kallon banza sannan tabi bayanshi,tana sane cikin gayya ta soma sakin masa shagwaba tun kafin ta soma taka step din
"Nifa na gaji,anya zan iya hawa da kaina,haka kawai zan kwanta ta tasoni,bayan duka maganarma ba wata babba bace a wajena" taja ta toge cikin shagwaba tana maqale kafada,suman wucin gadi kawai yayi yana kallonta,tayi wani bala'in tafiya dashi,salon saiyajishi kamar a mafarki
"Nifa saidai kadaukeni" ta sake fada tana narke masa sosai hadi da sake maqale wuya
"Kiyi haquri ki hau,bazan sake tasoki ba"
"Kayi alqawari?" Ta tambayeshi cikin dai shagwabar,kai kawai ya iya daga mata,ta gabanshi tazo ta gifta,taba sane ta sauya yanayin takunta,tana hawa step na gaba yana biye da ita a baya har suka gama haurawa,ta tabbatar nafisa bata iya ganinsu sannan ta qara wuta,kaman tasan akwai abinda ya qudurta wuf tashige bedroom dinta ta saka key,qarasowa yayi bakin qofar yana murdawa ya tabbatar ta rufe,tana jinsa,dariyar mugunta ta dinga cinta,dariyar da zata iya cewa tunda tazo gidan batayi kamarta ba,ko banza ta rama yadda yake mata,tace dashi
"Kaje kaji da waccar akwalar matar taka,wadda shekara da shekaru bayan ka auri wata saidata aureka,yauwa...sannan,ka gaya mata donni bata isa inyi magana da ita ba, wallahi niba sa'arta bace,naga kanta yana rawa,ta kama kanta da kyau,ka bata labari kaima baka isheni komai ba bare ita" duk maganar tanayinta ne cikin dariyar mugunta,kawai sai yaji murmushi ya subuce masa,dama yasani da biyu tayi,saiya kada kai kawai yabude dakinsa yadauki abinda zai dauka ya sauko.

Aikuwa!,nafisa ta shaqa iya shaqa,ta cika tayi fam,idanunta kawai zaka kalla su gaya maka,dan tsaiwar da yayi yashiga dakinsa yasa mintunan da yayi a saman suka dadu,sai kawai tabayar suna tare ne
"Ko bakayi hakan ba ai dama nasani basona kake ba,ka aureni ne bisa babu yadda zakayi" ta fada sanda suke shirin kwanciya taga yaqi tanka fushin daya gani kan fuskarta,kanshi ya daga ya dubeta
"Duka me ya kawo wannan zancan kuma?"
"Au baka sani ba?,bakaga wulaqancin da matarka tayimin ba kai kuma ka biye mata?" Murmushi ya saki yana son fahimtar da ita amma fir taqi,ganin haka sai shima ya shareta yaci gaba da shirin baccinsa.

Da taga haka ta tabbatar cewa ita zata yiwa kanta,donko babu komai tana da buqatar dan romance din nan,wanda taji dadinsa matuqa,saita tura baki
"Shikenan,amma gaskiya zamanta a sama kamar cin fuska ne a gareni,ina buqatar kwana nima dakin mijina,ina buqatar privacy" dubanta yayi
"Wannan maganar an riga da an gamata ai,banason ki sake tado da ita" wani abu ya shaqeta,tsanar shahida ta linku a ranta,wai wane irin wuri tasamu har haka a zuciyarsa dahar yanzu ta kasa fita?,taya zata fitar da shahidan?,ganin babu wata mafita adai yanzu saita tattara komai ta watsar gefe,ta shiga shirin morar daren yauma kamar jiya,duk da tanajin komai ragagge ne a wajenta.

To yadda yafaru jiyamadai haka yau aka kwatanta,yauma ya qyaleta yayi kwanta,sai ya zamana kwanaki uku kenan hakan na faruwa,tun yana mata uzuri har ya fuskanci kamar iskanci ne abun,hakan ya sanya a kwana na uku data durfafeshi yayi kunnen uwar shegu da ita,harta gaji ta sama masa lafiya takwanta,ranar ta huduma haka haka ata biyar baiko kalleta ba,saita saka mishi kuka kan me yasa zai qwararta da tauyeta,baiko bi ta kanta ba yayi baccinsa,ana ya gobe kwananta zai qare ne yake tunanin ya horata ba zata sake masa wannan iya shegen ba.

*SIXS DAYS*


Bakinta yadinga bi da kallo sanda take tauna qwan a hankali,tunba yau ba lebbanta yake burgeshi,ada sautari idan tana magana yakan yi shuru yabarta tayita magana saboda yakalli bakinta sosai,a haka harta gama sannan tamiqe,sai a sannan suka hada idanu
"Ina kwanata" ta gaidashi tana shigewa kitchen,bai amsa ba,saiya miqe ya biyo bayanta,zata juyo ta fada jikinsa,saita janye da sauri shima yadanja baya gamida sauke ajiyar zuciya yana kallonta,kamar tadan fada kadan
"Me yasa baki fitowa kwana uku?"
"Ba komai" ta fada tana kauda idonta,hannu yaza zai kama hannunta saiya kuma janye dasauri yana murza hannun nashi
"Lafiya kike?"
"Eh" ta amsashi a taqaice,saiya juya ahankali yafice daga kitchen din.

*10:50 pm*


Kaman gaske yau dinma ta sake neman abinda ta saba,a tsammaninsa ya horata,wanda wannan tunanin ya jagoranceshi zuwa qyaleta ta cimma galaba akanshi,saidai ga tarin mamakinsa saida tafiya tayi nisa kaman koyaushe tazame,wannnan karon bayan haske ya gauraye dakin idanu ya zuba mata yana kallonta cike da mamaki da bacin ran yadda takeson raina masa wayau,akoda yaushe ita ke soma haddasa komai kuma ita take soma bijirewa,ranshi yau yakai qololuwar baci fiye da kullum,tana tattare waje daya cikin bargo.

Bacin ranshi yafito xalla qarara ya bayyana saman fuskarshi,ya hadiye wani abu mai daci yana dubanta
"Wannan itace rana ta qarshe da haka zata kasance tsakanina dake" daga haka yasauka daga kan gadon cikin bacin rai,yadauki jallabiyyarsa ya zura kana ya dauki wayoyinshi dake gefan bedside ya taka da hanzari yafice daga dakin,tabbacin fushinsa nayau yafi na kullum kenan,tunda kwanakin da suka shude yakan shiga bandakin cikin dakinne yayi wanka,saigashi yau yafice,da alama ma yafita kenan,bargonta taja ta sake rufa,har cikin zuciyarta da jikinta tana jin babu dadi,saidai babu yadda ta iya don cikar burin nata shine jin dadinta har qarshen rayuwa.

Yana fita baikai ko inaba mararshi tayi wani masifar daurewa,da qyar yasamu ya haura saman,saiya zube anan falon saman daya daga cikin kujerun,ya kwanta rigingine yana fidda numfashi dai dai,tare dajin irin azabar da mararsa ke masa,yasan cewa dama a rina,kwanakin da yayi xaman lafiyar jikinsa na tashi yasan cewa matuqar abinda ke damun nashi bai fitaba komai na iya faruwa,sosai marar ke masa azaba,haka ya dinga sauke numfashi me nauyi yana jujjuya kanshi dama da hagu.

Toshewar da hancinta yakeso yayi yasa ta kasa bacci,tilas ta sauko tashiga kitcheb ta hada ruwan shayi wanda tacika masa kayan qamshi da tafarnuwa ta matsa lemon tsami tajuye a cup guda,tafe take tana kurba tana takowa saman a hankali saboda yadda yayi mata dadi,sam bata ankare dashi ba harta qare hawa tashigo ainihin falon tashige dakinta.

Gefan gadon take yunqurin zama ta gama sha daga nan tahau ta kwanta kofin ya sube daga hannunta ruwan zafin ya zube mata a qafa,radadi yasanyata sakin qara wadda ta sanya anwar dake kwance a falo tashi yazauna yana kallon qofar dakin nata,yaso yamiqe da hanzari saidai yadda mararsa ta daure yasanyashi rage saurin,yasoma takawa a hankali har ya isa qofar dakin.*ALQAWARIN ALLAH*
47



Cikin mutuwar jiki yamurda ya tura sannan yashiga,daidai lokacin da take duqe tana duba qafartata tana yamutsa fuska saboda radadin da take mata,numfashinsa ne yakusa daukewa saboda yadda take duqen yabaiwa rigar baccin jikinta damar zamewa,wuyanta zuwa qirjinta yafito gaba daya,ranar ko bra bata sanya ba saboda zazzabi,saita daga kai tana dubansa sanda yaqaraso cikin dakin,idanunsa sun sake janyewa sun rage girma qwarai,kamar wanda yasha wani abun maye
"Lafiya?" Yace da ita yana duban qwayar idanunta
"Qafata,ruwan zafi ne yazuba" ta fada da wata murya me sanyi dake tafe da sautin shagwabar da batasan ta fita ba
"Subhnallah" ya furta a kasalance yana duqawa gaban nata yasa hannu yakama qafar yana kalla bawai don yana gane komai ba,don tuni qamshin jikinta da rigar baccin jikinta yasake birkita masa dan sauran lissafin daya shigo dashi gaba daya,numfashinsa da bugun zuciyarsa suka qaru,saiya soma karanta mata fatiha yana tofa mata don hana wajen tashi.

Saidai daqyar ya iya qafa biyar karatun ya gagara,saiya miqe tsaye ya kamata ya tsaidata suna fuskantar juna,sosai tazuba masa idanu karon farko da tunda yashigo ta fuskanci kaman ba dai dai yake ba,fuskarshi ta hada jaa,ya cije lebanshi sosai,hakanan numfashinsa ajejjere yake,saita tsaya kawai tana kallonshi tare dason fahimtar abinda yake damunsa,tana tsammanin baida lafiya,jawota yayi zuwa jikinsa cikin wani irin zafi ya rungumeta tsam kamar zai tsagata gida biyu,mararsa ta sake murdawa,ya sauke mata wata qatuwar ajiyar zuciya a kunnenta sanda yacusa fuskarshi cikin wuyanta wadda ta sanyata rintse ido tsigar jikinta na tashi,dumin numfashinsa da sautin ajiyar zuciyarsa nabin kowacce kafa ta jikinta
"Bani da lafiya?,zaki taimakeni?" Taji ya ambata a birkice,wanda hakan yasake tsoratata gamida rudata
"Please...help me" ya sake fada da sauri,hannunta yakama ya dora saman marartashi,idanunta ta fiddo gaba daya waje,bugun zuciyarta na qaruwa da wani irin bugu,saita janye hannun nata dasauri tasoma yunqurin raba jikinta danashi,gam ya riqeta yana qoqarin hanta,ta hada dukkan hannunta ta turashi baya amma yaqi bada damar faruwar hakan,saima yasake mannata da jikinsa ya soma mata magana cikin kunne
"Ki taimakeni,minti biyar zaki baki don Allah,bazan iya miki fin qarfi ba,karkice a'ah.....mutuwa zanyi" yafadi qwalla na taruwa cikin idanunsa saboda wani irin abu da yakeji yana masa yawo cikin jiki wanda bai taba jin kamarsa ba,kalmar mutuwar ita ta sanyaya mata jikinta qwarai,saita daburce ta rasa abunyi,ya qarasa toshe mata dukkan wani tunani nata sanda yashiga aika mata da wasu saqonni,saita kasa tuna kome,ta kasa yanke kowacce shawara,ta tasa makama,a haka yasamu nasarar danganata da gadonta.

Duk yadda yaso ya daure amma ya kasa lokacin da muradinsa yasoma cika,kaman yadda take kuka haiqan shidinma kukan yake,abubuwa da yawa suka tarar masa sukayi masa yawa,yasha wuya kafin ya fitar da abinda ya tattarar masa ya hanashi sukuni,kaman qaramin yaro haka yaci gaba da fidda hawayenshi,kama hannunta yayi ya qanqame cikin nashi sannan ya hade fuskokinsu waje guda,idanunsu duka a lumshe saidai kowannensu qwalla ce ke fita daga nashi idanun,yayin da fuskar kowa tajiqe da hawayen dan uwanshi.

Har yanzu bugun zuciyarsa bai daidaita ba,ji yake kaman numfashinsa zai dauke,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yake furtawa qasa qasa,yayin da wani sanyi da farinciki yake ratsa zuciyarsa,wata iriyar qatotuwar BAZATA ya tadda tattare da shahidan MEKE FARUWA?,ya jefawa kanshi da kanshi tambayar daya tabbatar baida amsa face sanyashi cikin rudu data sakeyi,ya jima zuciya dagangar jikinsa na gaya masa,ya jima yanajin cewa kamar hakan ba zata kasance ba,ya dade yana kokwanto,ya dauki lokaci yana shakka,saidai ya kasa samun tabbaci saboda rashin gamsashishiyar hujjar da zata sanyashi ya yarda yakuma nutsu kamar yadda ya samu cikakkiyar hujjar data jefashi a wancan ko kwanto.

Gaba daya ya sanyata cikin jikinsa yana matseta gam,yanajin yadda take sakin wani marayan kuka mara cikakkiken sauti me hade da sheshsheqa,ya sani koda bata fada ba ta wahala,habarshi saman kanta yana shafawa a hankali yana hadiye wani abu mai tauri,ya kasa cewa komai illa
"Amsorry" da yaketa maimaitawa,tunani barkatai suka addabi qwaqwalwarsa kamar zai zauce haka yakeji a sannan,sauqinta daya wata iriyar nutsuwa da sanyin zuciya daya samu,uwa uba yanayin kaman an dauke wani qaton dutse ne daya danne zuciyarshi
"La'ilaha ilallalah" yaci gaba da fada hadi da fitar da numfashi,ya rasa wanne tunani zaiyi?,da wanne zai fara?.

A hankali ya dagata daga jikinsa yana kallon fuskarta wadda hawaye ya jiqeta,idanunta suka dan tasa kadan,bai ankara ba yaji wasu hawaye masu dumi sun kubce daga idanunsa,randa aka cillota gabanshi cikin jini da sunan zubda ciki shine abu na farko daya fado masa,saiyaji kuka yakesonyi,dada hali irin kukan nan me sauti ma,ko zai daina jin wani murdadden ciwo da radadi daya riqe masa wuya,whose behind this???,ya furta cikin murya dake nuna zafi fushi da tashin hankali.

Fuskar saurayin ta dawo masa tarrr a fuskarshi kamar yanzun yake tsaye a gabanshi,hotunan da aka aiko masa suka dawo masa
"Shiri ne?" Ya tambayi kansa qwaqwalwarsa nason shirya masa dukkan yadda abun yake
Kada dai ace plan ne?"baisan sanda ya diro daga saman gadon,ya nufi safe dinshi gadan gadan ya duqa a gabansa ya saka pin din da yake amfani dashi,saboda rawar jiki da tsabar sauri har yayi mistake,ya sake sakawa ya bude,ya

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment