Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata wani kyakkyawan ruqo,karon farko shida ita a rayuwarsu,ihu ta saki kaman wadda taga abun tsoro tana qoqarin qwacewa,daukarta yayi cak kamar yadda ya saba mata,abinda tafi tsana kenan,saboda idan yayi hakan gani take kaman ya raina mata wayo,bai sauketa ko ina ba bandaki,ya ajeta saman toilet sit,ta bude baki zatayi magana yasa yatsa ya dalle mata bakin gami da cewa
"Shshshs,karki sake ki mana surutu a bandaki" yana maganar yana zaro ido kaman wanda yakewa qaramin yaro,bacin rai ya hanata magana,saita qyaleshi tana kallonsa ya daura mata alwalar,zai sake sungumota ya fito da ita ta zille,ta tashi tana dingisawa ta fito,fafur taqi zama a bedroom dinsa sai a falo,a nan tayi sallarta.

Daidai sanda ta idar wayarta tayi tsuwwa,lokaci daya idanunsu suka sauka kan jakar,ya rigata saka hannu ya dauki jakar ya zuge ya ciro wayar,zai daga ta dubeshi
"Karka daga min waya,bani abata" fuska a tsuke ya daga kai daga daga wayar da yayi niyya yi
"Saboda baki da gaskiya?" Saita ware ido tana kallonshi
"Eh bani da gaskiyar,duk abinda zakace kace,ka fadima abinda yafi hakan idan kaso,bakinka rayuwarka kuma zuciyarka ba tawa ba" ta qarashe cikin hasala,yana tsaye cak yana kallonta saiya saki murmushi ya dauke idanunsa daga kanta
"Ko baki fada ba dama ai haka yake,dama ai zuciyata ce ba taki ba,haka rayuwata vata taba zama taki ba ki rubuta ki aje" daga haka ya daga wayar ya kara a kunnesa,hakanan taji kalaman sun samata ciwo,saita jefa masa harara ta dauke kanta wani sashe daban
"Lpy qalau....eh,to" kawai taji ya fada ya latse wayar,yana shirin maidata wayar jakar aka sake kira
"Triple R company" ya furta a fili,ta waiwayo da sauri ta dubeshi,da alama kira ne daga kamfaninsu,saita samu kanta tana addu'ar Allah yasa ba daga cikin maza abokan aikinta bane,bata gama wannan tunanin ba tajishi yana bada amsa
"Maigidanta zaishigo ya samu boss dinku,zamuyi magana dashi" daga haka itama ya yanke wayar,tana kallo ya juya wajen da layi yake ya ciroshi,ya fidda layin saiya soma lanqwasashi
"Karka karyamin layina" ta fada cikin hanzari,saidai ina tuni ya karyashin ya watsashi cikin dan qaramin abun sharar dake kusa dasu sannan ya dubeta
"Namiji ne ya kiraki yana tambayar ba'asin rashin zuwanki aiki yau,baisan kina da aure ba?,ko baya ga haka dole ki rabu da wannan layin,bazan lamunci kici gaba da amfani dashi ba" ya qureta matuqa ta kasa daure bacin ranta ya bayyana muraran
"Wai me ya dameka da rayuwata ne?,ina ruwanka dani?,me yasa kakeson shishshigema rayuwata bayan ni bayan ni gana shigewa taka?,bayan ni ban damu da taka rayuwar ba?,me na tsare maka?,ohk....alwashinka kakeson ka cimma ko na quntatawa rayuwata shine kake aiwatarwa yanzu?" Tsaf ya xuba ido yana kallonta ba tare daya motsa ko yace wani abu ba,mamaki take bashi idan tana masifa wanda ko iyawa ma batayi ba,batasan me yake ji cikin zuciyarsa bane,batasan wanne hali yaje ciki ba,da yana da ikon maida bara bana daya dawo da ita ya goge dukkan wani tabo da aibu,ba zata fahimci komai ba,ba zata gane komai ba,tanata amfani da zahiri ne ba tare data binciki me badinin ta haifar ba,saiya saki hannuwansa kawai gami da fidda qaramin murmushi,indai ba tunzurata yayi ba bazai taba jin muryarta ba,idan bai tunzurata ba yasan halinta sarai ba zata taba yin magana dashi ba ko zasu shekare a haka,yasan halinta tsaf,baijin baya ga mahaifanta akwai wanda yasan halinta sama dashi
"Donke baki damu da rayuwata ba saime?,akwai dubbai da suka damu da ita,don na taimakeki ma na rabi rayuwar taki shine kike wani zaqalqalewa kina zaton ke watace a wajena?" Ido da baki duka ta saka tana son tantance me yake cewa,daidai lokacin da qararrwar dake nuna akwai baqi can falon qasa ta soma kadawa,saiya miqe kawai yana tabe mata baki ya fice ya sauka qasa.

Daada ce ita da mubina da khadija,su sukayi waya dazu kan zasu rakota,tun bikin daada bata koma ba umma tace saitayi sati uku,sai yanzu ta soma shirin komawa,zuwanshi gidan wajen daada hira babu adadi,ta fuskanci abubuwa da dama game da zamansu ba tare daya gaya mata ba,da batayi niyyar zuwa gidan ba sam,amma taga ya kamata ta danyi gyara ko yaya ne kafin ta wuce karta tafi tabar baya da qura,don tasan umman shahidan koda wasa ba zata taba taka gidan shahida a yanzu ba,donko hira ake bata sanya baki,yaji qishin qishin din zata zo din yau dalili kenan dayasa ya tsare shahidan a sama don kar daada ta ramfo komai,don hausawa sunce babba babba ne,abinda zai gano ko kahau bishiyar rimi ba zaka hangoshi ba.

Shi ya tarbesu daada tahau baza ido
"Ina ita waccar ja'irar,kaine kake tarar baqin ita kuma tana me?" Murmushi ya saki
"A'ah a'ah,kawai yaune na karbata,tana sama batajin dadi ne,ta samu targade a qafarta"
"To ce mata ta sauko,don tayi targade saboda tsabar son jiki shine zata hau sama ta nade?,oh ni habiba,yaran yanzu saidai abarsu,kamar wadda ta karye"
"Yi haquri daada karki rudamin mata,kin manta ke mai laifi ce dama?" Ya fada cikin tsokana,da ido ta bishi baki sake
"Iyeeee....au wato harka soma bin bayan matarka?" Murmushi ya saki sosai sannan yace
"Yi haquri daadarmu,so so ne amma aisonkai yafi ko?" Kasa amsashi tayi,cikin zuciyarta tanajin sanyi da dadi na yadda ta fuskanci.yana kulawa da jikarta,ta cika da fata da addu'ar Allah yasa itama haka take masa kada ta basu kunya,kada kuma ta watsa musu qasa a ido,mubina yasa ta shiga kitchen ta hada musu abin motsa baki,sai dayaga ta shirya musu komai sannan ya zqri muqulli don zuwa ya sama musu abinci
"Ku hau saman daada ku sameta kafin na dawo"
"Kaga nifa ba zama zanyi ba,mai motar daya kawomu ma yana qofar gida yana jira in fito ya maidani,don yau ni kam kwanan garinmu zanyi" qememe taqi barinshi ya fita,tace saidai yahau sama ya sauko mata da shahida
"Kiyi haquri daada ki hau,ba zata iya saukowa ba"
"Ita sabon qashima taqi saukowa bare ni tsohon qashi za'ace nayi tattaki nahau,tunda goya mata baya kake tayita narkewa kaga tafiyarmu" daqyar ya lallaba daadan tahau saman,inda mubina da khadija sukayi xamansu nan falon suna kallo.

Har yanzu tana zaune saman abun sallah a haka daada ta shigo,sai taji dadin zuwan daadan,tana ganin tazo a daidai,ita ta qulla komai saboda haka dole ta yiwa anwar magana ya barta ta koma bakin aikinta,ba yabi ba fallasa ta gaidata,ta amsa tana qare mata kallo,bawani sauyi data gani tattare da shahidan na mace me aure,saita tabe baki,zata fara magana shahidan ta rigata cikin sautin wanda keson fashewa da kuka
"Daada ki masa magana ya barni na koma aikina,kinga tun asali da aikina ya ganni,sannan kuma baice min bazanyi ba sai jiya da nake gaya masa zan koma yace waina gama aiki,daxun nan kan ku shigo ya dauki wayata ya ballamin layina waina daina amfani dashi" rashin sani yafi dare duhu,wani kallo daadan ke mata akaikaice,sai data gama tsaf sannan tace
"Yo ai ni banga wani abun azo a gani dakika tabuka ba daxai nuna kinsan ma kina da aure,daga ke harshi banga wani sauyi tattare daku ba"
"Kai anwaru" ta kira sunanshi tana zare ido,ya amsa mata ta masa nuni da kusa da shahida
"Xauna nan" ba musu ya zauna yana qunshe dariya,daada sarkin rigimammu,da alama akwai magana a bakinta
"Tunda kuka tare ta taba maka kwanan turaka?" Ta jeho masa tambayar kanta tsaye,take qwaqwalwarsa ta gaya masa abinda take nufi,kunya ta rugo ta rarumeshi,bai taba tunanin tambayar da zata masa kenan ba,cikin hanzari yace
"Daada ai...."
"Aime?,idan baka da amsa to bari na amsa maka,bata taba ba,kalli qafafunta da wuyanta,idan tace ma eh to qarya take,oh la'ilaha illallahu muhammadarasulillahi sallallahu alaihi wasallam" ta debo salati tana tafa hannuwa

_afwa masu karatu,kunsan yadda sabgogi ke kutso kai cikin rayuwa_🙏🏽*Alqawarin Allah*
40


"Ni habiba naga abinda ya isheni.....rahama?!" Tayi kiranta da sunanta na ainihi,daga ita har anwar din sai sukayi tsuru tsuru suna kallon daada yadda ta dauki abun,kunya da daurewar kai duk suka cikasu
"Kinason ki gama lafiya kuwa?,kinsan tsinuwar mala'iku kuwa akanki?,so kike ki shiga wuta da qafafunki?,to wallahi kishiga taitayinki karki jawowa kanki masifa ki jawo mana,rahama!" Ta sake kiran nata cikin kambama abun,yadda daadan ke magana da yadda shahida ta soma turo baki fuska a hade cikin bacin rai saiya so baiwa anwar dariya,shi tuni a nasa shekarun ya fahimci tayine tana sane donta tsorata shahidan,ta kuma sake kawo gyara a zamansun gaba daya
"Yanzu daada fisabilillahi waya gaya miki wannan maganar?,shi yace miki haka?ko kuwa ni?" Daquwa ta watsa mata
"Kinci gidanku,don gyatumarki a tsufana ni akwai abinda za'a boyemin?,to wallahi wallahi tun muna shaida juna ni dake ki gyara duk abinda na gane da wanda ma ban gane ba,duka kin fini sani ai basai nayi filla filla ba,kin ganni nan bana daukar sakarci,ba abu bane me wahala na miki dukan tsiya cikin gidan nan kibar ganin kina da igiya a kanki,girma kuwa ban ganshi ba bare ya hanani dakarki,aiki kuma ba zakiyishi ba haihata haihata...."
"A'ah daada....ba'ace haihata haihata ba" anwar ya dakatar da daada yana boye dariyarsa wadda shahidan ta fuskanci hakan,ta sake qulewa sosai,wato ita tako ina bata da nasara,bata da rinjaye kenan?
"Zatayi aiki idan tanaso....amma ba bisa qarqashin kowa ba sai qarqashina,zatayi aiki a nawa companyn kuma a office dina" ya qarashe zancan yana duban daada ba tare daya dubi shahida ba,don yasan kai tsaye cewa zatayi ba zatayi ba,amma ga mamakinsa sai yaji ta amsa da
"Na amince zanyi" ta amsa masa idanunta qyar a kansa,tasan yayine don ya qureta yayi da manufa,ita kuwa tacu damarar takura masa itama tunda har ya bullo ta wannan hanyar,sai daya gama karantarta ta qwayar idanunta sannan ya girgixa kai
"Well,hakan yayi,daga yau daga yanzu ma na daukeki aiki,za'a dinga kuma baki salary kamar na kowanne ma'aikaci dai dai da matsayinka,salary dinki shine salary na farko dayafi na kowanne ma'aikaci yawa duba da matakin aikin dana baki" kaita juyar tana hadiyar bacin ranta,cikin ranta ba haka taso ba
"Shikenan ma,shine daidai,kaga kuna tare ko yaushe,tuwona maina,yamafi tsari" daada ta fada tana ware hannaye,daga haka daadan ta miqe bayan ta sake kwakkwafar shahidan,ba yadda anwar baiyi ta zauna ba tace sam,daqyar shahida ta iyayi mata a sauka lafiya,ya fita rakata.

Cikin kwanakin hakanan shahidan naji na gani ta zauna saman nashi,saidai kwana uku rak tayi wanda ta jita kaman akan wuta take,a falo duka tayi xamanta,sai shima ya shareta kawai ya shiga sabgarsa,randa taji dama dama a qafarta ranar ta sake tarkatawa ta koma dakinta.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


A hankali take takowa zuwa bakin dining din donta samu tadan dumama cikinta,bayan ta gama shirinta tsaf kamar yadda ta saba duk lokacin da zata je office,madaidaiciyar kwalliya tayi wadda ta qawatar da ita matuqa,ta sake fidda kyawunta,kallo daya xaka mata kasan macace mai aji tako ina,wannan itace ranar farko da zata soma zuwa office din anwar da sunan ma'aikaciya.

Shi dinma yana tsaye daura da teburin yana kurbar tea gami da jefa soyayyen chips a bakinsa,kacokam idanunsa nakan wata takarda dake saman teburin kusa da farantin chips dinsa,wanda ke dauke da zanen taswirar wani gini da gwamnati ta basu kwangilarsa da xasu soma yinsa cikin satin.

Takun daya soma ji shi yaja hankalinsa,har yakai kofin bakinsa ya janye ba tare daya kurbi tea din ba,daga sama zuwa qasa ya qarewa kwalliyar tata kallo cikin taqaitattun daqiqa ya kauda kanshi yaci gaba da shan tea dinsa.

Qarasowa tayi itama ta fara hada nata ba tare data dubeshi ba tace
"Gd mrng" fuska a tsuke
"Mrng" ya amsa mata a taqaice shima yana juya fasalin takardarsa ba tare daya dubeta ba,wani abu ke tsunkulin zuciyarsa,shigarta sai yaga ta bayyana ado da yawa,duk da ko ina a jikinta rufe yakr ruf ba wani abu nata daya bayyana,amma sai yake ganin kamar kallonta za'a yita yi idan suka je,dana sanin cewa tayi aiki a kamfaninsa ya kamashi,inama ace cewa kawai yayi ba zatayi aikin ba gaba daya,gashi ya ruga ya furta babu damar ya canza,yin hakan zai nuna qarantarsa ne kawai.

Sai daya gama tas ya dire cup din yana cewa
"Wannan shigar batayi ba,kije ki canza wata ki sameni a mota,idan kuma kika makara to cikin albashinki" daga haka ya juya ya soma takawa,ya dauki handkherchief dinsa da muqullin mota dake aje saman daya daga cikin kujerun falon,ta bishi da kallo galala baki sake harya fice,sai daya bacewa ganinta sannan ta dauke idanunta tana lumshe ido,takaici nason kamata amma tana daurewa.

Yana daga xaune cikin motar,ta baqaqen gilasan da batasan yana kallonta ba ya xuba mata ido,karo na biyu kenan daya sake maidata ta sauya shiga amma shi har yau baiga wani abu na kyanta daya buya ba,bayyananniyar ajiyar zuciya ya sauke,tunda can yasan cewa haka take halittarta ce,duk kayan da zata saka suna mata kyau gami da dacewa da ita komai rashin kyau ko tsadarsa,agogon dake daura a hannunsa ya kalla,dole ya haqura ya qyaleta su tafi hakanan,zuwa yanxu ya cinye sauran lokacin da suke dashi.

Tana zuwa gidan baya ta shiga,baice mata komai ba yaja motar suka fice daga gidan,suna dab da ginin kamfanin ya tsaida motar,ba tare daya juyo ya dubeta ba yace
"Dawo gaba" jim tayi sai kuma ta fito don batason ma ta yawaita magana dashi.

Tun daga harabar kamfanin ta karanci yadda suke ganin qima daraja da mutuncinsa,wannan karon baiyi parking inda kowa yake ba,sai dayaje gaban ginin sosai sannan ya tsaida motar suka fito,basu shiga ta gaban ginin ba saita bayanshi.

Kallon office din babu abinda ya tuna mata dashi face nata office din,kusan tsari yanayi da kuma zubinsa kamar nata office din,take kewarsa ta kamata,ta lumshe idanunta sanda take zaune kan cushion din office din tana jira ya kaita nata ofishin.

Abinda ya bata haushi da mamaki shine bai wuce yadda taga yayi zamansa kan tashi kujerar ba ya shiga ayyukan daya taras kan teburinsa ba,yayin da take zaune shuru bata wani aiki.

Ganin sun cinye awanni biyu cur a haka ya sanyata gyara zama sannan ta dubeshi
"Ban gane manufar ajeni cikin office dinka ba,ka mantane aiki nazo yi?" Sai sannan ya daga kai ya dubeta,saiya maida kan cumputer dinsa yana cewa
"Na fiki sanin ai aiki kikazo yi,gaggawar me kike?,zakiga aikin naki ai" daga haka ba wanda ya sake tankawa wani,saidai sau uku tana daga kai sai taga kaman kallonta yake,daga kanta yasa ya kauda nashi kan,saidai har yanxu bata kamashi dumu dumu ba shi yasa bata tabbatarwa da ranta hakanne ba.

Minti talatin bayan nan yace
"Hadamin coffee,ki bude can ki ciromin cake guda uku" duk yayi maganar ne ba tare daya dubeta ba,karon farko daya fara bata umarni irin haka tunda sukayi aure,saita miqe din tayi yadda yace ta dawo ta zauna.

Ba'a jima ba sosai ya sake cewa ta dauko mishi ruwa,ta dauko ta aje masa saman table din,saiya daga kansa ya kalleta sannan ya maida kan computer dinsa yaci gaba da aikinsa,awa biyu tsakani yace ta dauko mishi lemo a fridge,idanunta ta juya cikin nuna qosawa,ta sauke numfashi sannan taje ta bude ta dauko masa ta aje
"Ba wannan kalar nakeso ba,ki duba akwai wani daban shi zaki dauko min" hadiyewa tayi ta juya din ta maida ta dauko masa ta aje,saiya dubeta ya kauda kai
"Waishin haka ake bawa mutum abu,a dire masa kaman dutse,baza'a bude masa ba bare a zuba masa?" Hannayenta ta goya a qirjinta ta zuba masa ido
"Wai na tambayeka?,aiki nazo yiwa kamfani ko kai nazo yiwa aiki?" A nutse ya dubeta sannan ya ture cumputer din gefe kadan ya hada yatsunsa cikin na juna
"Bakisan cewa nine kamfanin ba gaba daya?" Ido ta fiddo alamun bata gane ba,girarsa ya daga mata
"Eh,aikin kamfani xakiyi,kuma nine kamfanin gaba daya,babu aikin dayafi nawa aikin,wannan aikin shine aikinki a office dina,zan biyaki albashi kamar kowa albashinma daya fi na kowanne ma'aikaci,ba shikenan ba?" Idanu kawai ta zuba masa tana kallonshi yana fidda qaramin murmushi,tsantsar raina mata wayon da yayi kawai ya isheta bacin rai,saita juya kawai ba tare data tanka masa ba ta nufi qofar fita.

Gabanta yasha ya tsate hanya
"Ina zaki?,lokacin tashi baiyi ba madam"
"Aikinne na fasa bazanyi ba gaba daya" duka kafadunsa ya daga,hakan ya masa shima,don baisan ta yaya zai dinga barin mutane na shiga masa office ba alhali tana ciki
"Fine and good....saiki jira sai lokacin tashi yayi saimu wuce gida" daga haka ya juya zuwa wajen wayarsa da tunda suka fara taqaddamar ta soma ringing,daga wayar yayi yana dubawa,wannan shine kira na dari da biyu daya samu da lambar daga farkon satin xuwa yau,tunda ya daga yaji muryar nafisa bai sake daga wayar ba,don baisan me kuma zata ce masa ba,me yayi saura tsakaninsu?.

Wayar ta wurgar a gefanta ta fada saman kujera tana yamutsa gashinta,sam ta kasa jurewa da rashin anwar kamar yadda mima ta shawarceta ta jira sai zuwa wani lokaci da ita miman ke shirya mata,ta rasa ta yaya zata iya jurewa,daga qarshe dole tabi zabin ranta ta soma neman khalipha baji babu gani,tana neman hanyar da zata gyara kurenta,kullum ranta soyuwa take ta gaza sukuni idan ta tuna yanzu haka fa yana can suna rayuwarsu shida shahidan?,me yasa kishi ya rufe mata ido haka ta tauyi rayuwarta?,ta yaudari kanta akan ba zata iya aurenshi ba?,bayan tasan cewa ka ta kawai ta yiwa qarya,ta ina zata soma gyara wannan babban kuskuren data tagka,tasan cewa abune ba mai sauqi ba musamman idan ta tuna da yadda ta samu soyayyarshi a baya,saidai koma meye tanajin zata jure harsai haqarta ta cimma ruwa,sai taga abinda ya turewa buzu nadi,zata aje mima a gefe wannan karon,zatayi yaqi ta samawa zuciyarta abinda takeso kota yayane ma,idan yaso ta nemi miman daga baya su dora daga inda suka tsaya.

Dirowa tayi daga saman gadonta ta shiga bandaki ta dauraye fuskarta sannan ta yafa qaramin mayafi saman kanta ta fito.

Dakin mahaifiyarta ta wuce,ta sameta zaune tana waya,saita samu waje tana jiranta garta kammala,kusan tunda abun ya faru ta sake dauke mata wuta,a baya ta sani amma ta nuna kamar abin bai dameta ba,tunda tana tsammanin abinda ta aikata shine dai dai
"Mommy,zuwa nayi na baki haquri" dubanta tayi sannan tace
"Akanme?" Shuru tadanyi sannan daga bisani kanta a qasa tace
"Nasan na bata muku kan qin auren anwar da nayi,amma a sannan idanuna ya rufe,don Allah momy kuyi haquri,ki tayani baiwa daddy haquri" tabe baki mommyn tayi tana miqewa
"Aike za'a baiwa haquri,name zaki bamu haquri tunda kin aikata dai dai,rayuwarkice fa kuma kika zaba mata abinda kike ganin yafi davewa da ita" daga haka mummyn ta bude qofar dakin nata ta fice,da kallo ta bita kafin daga bisani ta janye idanunta tana sauke ajiyar zuciya,lallai aikine ba qaramiba a gananta kafin ta soma shan kan iyayenta,wanda sune tsaninta na nasararta Wajen anwar,saita miqe kawai tabi bayan mummyn,sai inda qarfinta ya qare kam.

Lokacin sallar azahar taga ya sanya rigarshi ya fita,hakanan ta miqe itama ta shiga bandakinsa dake nan cikin office din ta shiga tayi alwala tazo ta tada sallah kan abun sallarsa dake cikin office din.

Bai wani jima ba da yawa ya dawo dauke da takeaway,ya aje mata nata ya bude nashi ya wanke hannunsa ya soma ci,ta gefan ido take satar kallonsa,wato har yau halinshi nacin abinci da hannu dai yana nan.

Ranar haka suka wuni har lokacin tashi,yana aikinsa tana zaune waje daya,saidai sam taqi zama saitin da zata ga fuskarshi koshi yaga tata,tayi danasanin karbar tayin aikinsa da biyoshi kamfanin datayi yafi sau shurin masaki,kome za'ayi kam ba zata taba iya aiki dashi ba,ta gwammace tayita zaman gidan akan zamansu qarqashin inuwa daya,suna musayar numfashi daya kusa da juna sosai har kamar haka,ta saurari muryarsa data wulaqantata wulaqancin da har yau yaqi gushewa yabar zuciyarta,duk sanda ta nutsa duniyar tunani saita tuna kalamansa da har yau bataji kalaman da suka yiwa kunnuwanta muni kamarsu ba.


🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Qarfe shida da minti ashirin da biyar na yammaci ya shigo gidan.

,yana zaune a falon yana sauke gajiyar daya tarawa kansa yau,ji yake kaman bazai iya hawa samanshi ba,da ido yake bin kowanne sashe na falon da kallo,ko ina fes yake ba alamun datti ko qura,hakanan yana fitar da sassanyan qamshi mai ratsa zuciya,amma saika rantse ba wani dan adam cikin gidan,sai qarar na'urori kawai dake fita kadan kadan,ya janye idanunshi kenan yana shirin miqewa yaganta tana fitowa,sanye take da doguwar rigar atamfa mai gajeran hannu,wadda tafitar da shape dinta sosai,kama dafa damammen cikinta,qirjinta da yake das cikakku,zuwa mazaunanta da suka dace da qirar jikinta,kanta babu kallabi sai gashinta dake daure waje daya,tayi kyau kamar wata 'yar tsana,fatarta ta sake fresh na zama waje daya,da alama ta fito daukan wani abune,suna hada idanu tayi turus kamar zata juya,sai kuma ta maze taci gaba da takowa,dab da zata giftashi tace
"Sannu da zuwa" ciki ciki kamar wadda aka turawa tsumma a baki,wanda banda kunnuwansa dake dukka wajen ba bazai iya jin me tace ba,hakanan yaji yana da sha'awar ya takaleta,kwana biyu da bai ganta ba saiyaga kaman ya jima bai ganta din ba,saboda haka ya hade rai qyam sannan yace
"Zonan" yadda ya kirata cikin gadara da bata haushi,amma saita tuna koma meye itace a qasanshi,saboda haka ta sassauta ranta ta tako inda yake zaune ta tsaya gefanshi,saiya daga kai yana kallonta
"Me haka?,zaki samin ciwon kai rage tsahonki" dubansa tayi sosai kaman zata tanka saita shareshi,ta zauna hannun kujerar da take daura dashi,samun kanshi yayi da qare mata kallo,idanunsa suka tsaya kan qirjinta kamar wani mayen qarfe ke janshi,idanu ta zaro data fuskanci inda yake kalla,saita goye hannayenta a wajen abinda ya fargar dashi cewa kallonshi ya zarme da yawa,saiya maze yana sake hada rai
"Haka kike zama dama idan bana nan?" Ya jeho mata tambayar,mamaki ya kamata,ta kasa gane me yake cewa?
"Kamar yaya?,ban gane ba?" Ta tambayeshi itama tana kallonshi bayan ta kalli kanta
"Wannan shigar gaskiya bata dace ba" mamaki ya sake kamata
"Waini da waye cikin gidan?"ya gane sam maganarsa bata da makama saboda haka yace
"tunda haka kika zaba shikenan,bani ruwa nasha tunda baki iyaba har sai mutum ya roqa" ta gane sarai neman abun fada yake,saboda haka ta miqe kawai ba tare datace masa komai ba ta wuce kitchen din,saiya waiwaya ya bita da kallo,karon farko da yaji wani abu yana ratsashi tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafafunsa,ya lumshe ido yana ambaton sunan Allah,baqon feelings yakeji sosai wanda har yaso danne gajiyar da yakeji.

Idanunsa ya bude sanda take aje masa ruwan,idanunsa kuwa sukayi kyakkyawan gani,saiyaji kaman yakai hannunsa kamar ana janshi ne,ya samu da qyar yayi controlling kansa sanda qamshin turarenta ya soma rarraba mishi hankali,yana kallon tasoma takawa don barin wajen ya kasa magana sai binta da idanu,da qyar yasamu cewa
"Nace ki tafi ne?" Waiwayowa tayi tana kallonshi fuska a turbune
"Zo nan" ya sake fada,ba yadda ta iya don batason ta saba da dabi'ar musu da gardama data soma masa ya zame mata jiki
"Zubamin" ya fada yana nuna mata ruwan,haka ta sake duqawa tana zuba masa,ta gama ya amsa yana nuna mata wata leda daya shigo da ita
"Kaimin dakina" ya dora qafarsa daya kan daya ya soma shan ruwan,baki take turowa ciki ciki,ya soma kaita bango,ta dauki jakar ta soma hawa saman,nan ma da kallo ya bita yadda mazaunanta ke juyawa kai kace tana sane takeyin hakan,ajiyar zuciya ya sauke bayan ta bacewa ganinsa,ya dire cup din da hanzari ya miqe ya rufa mata baya.*Alqawarin Allah*
41

_ku ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsofaffi dama sabbabin littafanmu,da sababbin ma da bakusan dasu ba wadanda zasu fara zuwa muku ta tashar nan gaba kadan da ixinin ubangiji_

https://youtu.be/-tPtW9YtNpU


Tana shirin fita yana shirin shigowa sukayi kacibus,tadanja da baya tana neman hanyar wucewa
"Waye ya miki karatun yadda ake zama da mijine?" Yayi tambayar yana dubanta,dagowa tayi cikin mamaki ta kalleshi,saiya dage mata gira guda daya
"Eh,gaskiya

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment