Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaja qwafa tana maida kallonta saman benan,tanajin kamar tahau ta jawo shahidan ta sauko da ita tama fiddata daga gidan gaba daya,gashi kwata kwata bata kulata,babu fuska ma tattare da ita bare ko fadi in fada suyi ta samu caccaba mata maganan da zata tsaya mata a ranta,don taci alwashin saita sa mata baqinciki da takaici a ranta tabbas kuwa,koba dade ko bajima.

Qarfe uku na rana ba zato saiga mima ta kawo mata ziyara,ta dinga kallon inda suke zaunen bayan ta gama zagaya gidan tana qissima ranar shigowarta,tanajin ba zata iya haqura takai har lokacin datake hasashe din ba,gwara tashigo kota yayane itama a dama da ita,mai rabo ka dauka,ya kamata tasoma yiwa nafisan jirwaye da kamar wanka,ta maida kanta kan nafisan dake aje mata kayan qwalam
"Kuwai komai da kanku kuke ko irin mai aikin nan baki da ita?" Baki ta tabe tana neman wurin zama
"Shifa mutumin nan duk inda na zaceshi ya zarce nan,ra'ayinsa komai nashi daban yake da sauran maza,baya ra'ayin me aiki idan ba iyali matarsa ta tara suka mata yawa ba,anan dinma yace saiya zabo dattijuwar daya yarda da ita mai asali da mutunci" kai ta jinjina cikin zuciyarta tana cewa bari dai tashigo saita gyara zaman kowa.

"Gidankun nan yayi min kyau" miman ta fada tan kurbar lemo idanunta akan nafisa tanason taga yanayinta,saitayi murmushi
"Donma qaraminne bakiga babban ba" idanu tadan fiddo
"Oh,yana da wanda yafi wannan ne?" Kai ta jinjina
"Sosaima,ainishi naso ya sakani yace a'ah dukka anan xamu zauna"
"Allah yasamu a danshinku"
"Ameen" ta fada cikin alfahari,haushi ya kama mima ganin nafisan bata shinshino komai ba,saita rabe baki,badon tanason dorata akeken bera kada tagano da wuri ba ai dayau kam zata fada mata abinda ke ranta
"Nifa mima,matar nan ta soma shigemin hanci qwarai,kawai so nake na fatota"
"Kaman yaya fa?,banace miki kibar mata shiba nadan lokacine aiko?,kinga nafisa ki rufawa kanki asiri karki xo kiyi abinda zai dameki ki bata rawarki da tsalle,wannan banzan kishin fa dole ki taka masa burki zuwa na wani dan lokaci" nan mima ta fitittike mata saida ta tabbatar nafisan tahau ta zauna daram sannan tasamu sukuni,zuwa sanda komai zai qare zatasan yadda zatayi dasu gaba daya.

Daya fita gidan anty usaina yaje wanda yayi wajen kwana biyar bai samun zuwa,tunda yaje kowa zancan shahidan yake masa,ita kanta antyn ita take tambaya,a hanyar dawowa ne ya tsaya ya kira wani yaronshi marwan,ya masa bayanin binciken da yakeso ayi masa,ya dauki hoton fiddausi,suna da unguwarsu,sannan yadauki fuskar matashin duka ya tura masa,sai daya tsaya ya yayi musu takeaway na abinci duka su ukun sannan yakoma,a lokacin biyar da rabi na yamma.

Sanda yashiga baisamu nafisan ba tana bandaki,ya aje mata ledar nan cikin dakinta sannan yawuce saman,sanda yamurda qofar shahidan sai yajita akulle,yasan dai saboda shine,murmushi yasaki ya sauka qasa dakin karatunsa,inda yake aje muqullan gidan duka ya laluba yaciro spare ya dawo ya zira ya bude,a hankali ya tura qofar,duka dakin yayi duhu sakamakon qwan lantarki da aka kashe sannan kuma dukka labulayen dakin a sauke kuma a zuge,duk da haka yana iya hangota kwance tsakiyar gadon tana baccinta hankali kwance da tunanin babu wanda zai shigo mata daki,murmushi yasake saki cikin zuciyarshi yana cewa
"Wannan fa shine bonono din rufin qofa da barawo" aje mata ledar itama yayi ya rufe mata qofar yadda yaganta yajuya ya fice.

Wanka yasake sannan yazauna sosai ya soma cin nashi abincin ,yanaci yana nazari gamida shirya yadda abubuwan zasu kasance,wayarsa ya dauko dake gefe ya lalubo number muhsin yakira,bata wani jima tana ruri ba yadaga,suka gaisa kana suka dan taba hira,irin hirar da suka saba sannan ya jeho masa tambayar
"Amm da Allah nace zaka iya tuna fuska ko wanda ya baka envalope din nan daka kawomin shekara shida baya?"
"Wace envalope fa?" Kwatanta masa lokacin yayi,muhsin yasaki dariya
"Kai mutumina,da alama an baka alawa irin tada shine ka tuno da lokacin ko?"murmushi ya kubce masa,saidai bai bari muhsin ya fahimta ba
"am seriouse inason nasani ne muhsin"
"Gaskiya ban sashi ba,infact ma ban taba ganinsa ba,har yauma ban sake ganin fuskar ba"
"Oh god,try to recall mana muhsin"
"I can't recall anything....da gaske nake maka namanta anwar,shekarunfa da yawa"
"Alright,shikenan,amma inason indan rage ayyukan office dina zuwa naka,saboda akwai muhimmin abinda zanyi,wanda maybe ya dinga jamin lokaci ya hanani aiwatar da duka ayyukana"
"Baka da case,aikai yanzu sai an maka uzuri,ka zama mai gida biyu" murmushi kawai yayi masa,sannan ya masa godiya katse kiran.


*10:30 pm*


A tsorace ta daga kai ta dubi bakin qofar,dama tun daxu data farka taga abinci jikinta yabata anwar ne ya bude qofar,to amma ta ina yasamu key dinta?,tambayar data dinga yiwa kanta kenan,idan tace bata tsorata da anwar ajiya ba ba shakka tayiwa kanta qarya,hakan yasa yau din gaba daya ta kasa sakewa cikin dakin nata,dukda ta gama shirin kwanciya amma tana zaune daga gefan gadon.

Yakaranci abinda ke idanunta amma saiya basar ya isa saman gadon ya aje butar shayi da cup din dayashigo dashi gamida wayoyinsa da qaramin littafin addu'o'insa,saita sauya wajen zama kan kujerar dake kallon gadon,bai tanka mata ba kaman yadda itama haka har ya gama komai ya haye saman gadon,yazauna sosai ya jingina da fuskar gadon yamiqe qafafunsa bayan ya rufe qafafunsa zuwa qugunsa da duvet,idanunsa cikin nata yace
"Taho ki kwanta" saita maqale kafada,idanunta na shirin raina fata
"Bakiji ba?" Ya tambayeta yana daga girarsa,saitayi shuru ba tare data amsa masa ba
"Ba abinda zan miki ki taho ki kwanta" ya fada yana daga hannunsa sama kaman wanda yayi surrender
"Mema ya kawoka dakina?" Ta tambayeshi cikin tsoron da takeson boyewa,ya danne dariyarsa ya amsa mata
"Abinda ya kawoni jiya" yankewa gabanta yayi yafadi,idanunta suka hada qwalla tanason shanyesu don kada yagani,ya zuba mata ido yana karantarta dariya tana cinsa
"Duk jarumtarki da iya maida magana?....tsokanarki nake to taso ki kwanta,idan kika musamin kuma zanyi abinda bakiso" hakanan ta taso cikin mutuwar jiki da tsoron da bata taba zaton zatayiwa anwar din shi ba.

Yana kashe wutar dakin taji caraf ya rungumota ta baya,a tsorace tace
"Kayi alqaw...."
"Ban manta ba..." Yayi saurin tararta gami da bata amsa,sosai ya sanya shahidan cikin jikinsa yanajin duminta,lumshe idanunsa yayi yanajin wani madaukakin farinciki na yawo dashi,yanajin kamar duk duniya babu wata halitta data kaishi farinciki a irin wannan lokacin,tun suna sauraren bugun zuciyar juna har bacci yayi awon gaba da kowannensu.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Cikin kwanakin duk yadda taso kauce masa yaqiya,duk yadda taso nesanta kanta dashi kamar yadda suka saba yaqi bata wannan damar,ya shanye yacinye ya kuma jure duk wani qalubale daga gareta,ta sashe guda kuma lokaci zuwa lokaci tana mamaki dason sanin meye ya sauya dukkan wani tsauri nashi zuwa laushi sanyi taushi da zallar qauna?,ta kasa samo amsa ko fahimtar komai,haka ta kasance cikin wannan tunanin na tsahon lokaci.

Gefe guda nafisa nata lissafin kwanakin da suke gabanta,saidai kowacce rana cike take da shahida,bata ishi shahidan kallon ba bare ta tanka ta kota samu abun fada,sautari koda hanya ta hadasu da shahidan kallo daya shahidan take mata ta kauda kanta kamar batasanma Allah yayi tsiron nafisan ba,duk yadda ta tsammaci shahidan saita taddata ta wuce nan,wani irin aji ne da ita,kamun kai da jan mutunci,qasanma takan iya jera kwana biyu batako leqo shiba bare tasauko.

Hakan yana yiwa nafisan ciwo,ba haka takeso ba,duk da haka tayi lamfo tanason ko sau daya ne ta tanka ta amma bata kula ba.

Ranar data soma janta shahidan ta sauko qasa a backyard dinsu ta wanke undies dinta ta shanyasu anan saboda bandakinta rana bata shigowa,ita kuma tafiso rana ta dakesu su bushe saboda.zafin ranar yakan kashe qwayoyin cuta idan akwaisu a jikin undies.

Da yammaci ta sauko zata debe,tunda ta sauko daga sama ta tadda nafisan zaune cikin falon,bata ko kalli gefanya ba amma taji a jikinta irin kallon da take mata,ta wuce abinta zuwa inda tayi shanyar,saidai abin mamaki babuko abu daya a shanye,data duba wajen dakyau saita gansu cikin wani kwando da ake zuba sharar flowers da ake yayyankewa na gidan,tayi mamakin meya kaisu ciki?,saidai bata kawo kowa a ranta ba ta juya don komawa ciki,tana shiga falon ta soma jin dariyar nafisan,bata sani ba waya take koba waya takeba oho don bata dubi sashen ba,amma ta tsinto muryarta tana cewa
"Wallahi kadanma mutum yagani,ba abinda mutum ya aje sai shegen jin kan bayan ba kowan kowa bane,da bamusan asalin balbela ba da sai muce daga masar tazo saboda tsabar fari" ta gane ta kuma fahimci sarai cewa da ita take,ranta yabaci sosai ta haura sama abinta ba tare data nuna mata ma taji abinda take cewar ba,tasamu gefan gadonta tazauna tana hadiye bacin ranta,ta shanye wannan bata gayawa anwar ba,again ta sake aike a siyo mata naman kan rago xata dafa,hakanan ta tashi tana mugun sha'awa cinsa,shi kuma anwar din bai wani damu dashi ba shi yasa bai fiya siyoshi ba,ganin shuru shuru dan aiken bai dawo ba yasanyata zura hijabinta ta saka slippers dinta ta sauko qasan,da mamaki take kallon falon yadda yadan hautsine,don ita kwana biyu kenan bata sauko ba,indai ba randa zata amshi girki ba dama ba saukowan takeba,ta maida mamakinta donba abinda yashafeta bane tawuce zuwa harabar gidan,saita samu yaron data aika zaune dame gadin suna hirarsu,tasowa yayi da sauri sanda ta daga mishi hannu,ya qaraso cikin girmamawa ya rusuna
"Ina aiken jamilu naji shuru?"
"Ai na kawo hajiya tun dazu,amarya ce ta karba tace zata aje miki cikin kitchen" cikin mamaki ta dubeshi sai kuma ta basar
"Ohkey,ba damuwa bari na duba" ya amsa sanda take juyawa tawuce cikin gidan.

Kai tsaye kitchen din tanufa,saita hango nafisan tsaye gaban tukunya da alama girki take,tayi sallama kamar yadda tasaba qamshin naman kan yacika mata hanci,saita qarasa gefan nafisan kamar zata dauki wani abu ba tare data mata magana ba,naman kanne acikin tukunyar har yayi nisa a dahuwa,hada ido sukayi da nafisan,ta yiwa shahidan wani kallo sannan ta maida murfin tukunyar ta rufe,kanzil batace mata ba,saidai wani abu daya tokare mata wuyanta,wani bacin rai da bata tabajin irinsa ba ya taso mata,ta juya a hankali bayan ga dauki fresh milk cikin fridge tafice daga kitchen.

Tana zaune gefan falon saman,ga fresh milk din a hannunta amma bacin rai yasa ta kasa sha,tariga ta saka rai dayawa akan zataci naman,iskancin nafisan ya isheta,tana jin ya kamata ta taka mata burki haka,amma ita ba sa'arta bace bare tashiga sabgarta,wanka takesonyi amma ta gagara tashi daga wajen,a haka anwar din yashigo gidan ya sameta.

Cikin mamaki qwarai yake dubanta,don zai iya irga sau nawa yazo yasameta zaune a falon,ta masa kyau sosai cikin wata doguwar riga ya wani cotton yadi mara nauyi me gajeran hannu,kanya babu dankwali,yadan lumshe ido yanajin wani yanayi yana ratsashi,tayi masa dandani haukaci,tun daga wancan lokacin bata sake bari ya kuma rabarta ba,ta kasa masa zuma a baki wanda kullum cikin tuna dadi da gardin zumar yake,tare da burin da fatan ya sake dandana,saidai dole ya lallaba a yanzu har zuwa lokacin da komai zai bayyana,bincikensa ya kammala ya sanar mata da komai,ciki ciki ta masa sannu da zuwa ya amsata yana jin dadin ganinta yauta fito
"Ina da magana dakai" ta fada cikin dakiya shariya da shan qamshi
"Uhmmm,inajinki,ya akayi?,meya faru?" Aje madarar tayi wadda ta kusa awa riqe ahannunta,ta kalleshi sosai,sai data kama kunnenta da hannu daya sannan tace
"Ka jawa matarka kunne,ka jawara matarka kunne,ka sanar mata idanma bata sani ba ni shahida ba sa'arta bace,tako ina na tsere mata na mata fintikau,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,idan ma tana ganin don zama ya hadamu ta hanyar kai shine zata ringa min abinda takemin din ta kiyayi kanta" daga haka ta miqe zata bar falon,yabita hanzari don bai gama qoshi da kallonta ba,yadda lebbanta ke motsawa kawai ya isa ya sanyashi a wani hali,uwa uba kuma yanason jin meye don kada wata sabuwar matsalar kuma ta kunno cikin vidan bai gama kashe wata ba,ya sani sarai tunda can shahidan bata da tsokana ko rashin gaskiya,a tsaye take kome zaka mata ta yadda ta rungumi gaskiyarta.

Hannayenta yasamu nasarar cafkowa ya riqesu gaba daya a nashi hannu,ya soma murzasu a hankali laushi da taushinsu na rasa nashi hannun yana aika saqo har qwaqwalwarsa,qwayar idanunta ya lalubo ya saka tashi a ciki,zallar bacin rai yagani qarara
"Meya faru?,gayamin karki boyemin zanwa tufkar hanci" kaman ta shareshi sai kuma taji ta kasa,ta hadiye wani abu daya tokare mata wuya sannan tace
"Tanason dole saita shiga rayuwata bayan niban shiga tata ba...." Ta gaya masa duk abinda je faruwa wannan da wadancan na baya,kai ya girgiza ranshi yana baci,bawai don yafison shahida a'a,koda shahidan ce kewa nafisan haka ba shakka zaiji babu dadi,ita gaskiya daya ce,daga qinta sai fada
"Koma ki zauna,jirani minti biyu" ya fada yana sakar mata hannun,jim tadanyi sai kuma ta koma tazauna din,sauka yayi qasan,cikin minti uku sai gashi sun dawo da nafisar,tunda ta daga kai sau daya taganta ta kauda kanta,anwar yasoma mata tambayoyi saidai suka ta kasa bada qwaqwqwarar amsa,tabbacin bata da gaskiya kenan,ya karanto mata duk abinda ke faruwa sai tayi shuru yana raba ido
"Ni bazan lamunci haka daga wajen koma wacece daga cikinku ba,banason tashin hankali banason neman fitina,daga yau babu abinda ya shafeki da sabgarta ko wani abu nata,ki sauka ki daukomin naman gaba daya ki kawominshi yanzu yanzu" kamar zata fashe haka takeji,wata tsanar shahida na ninkuwa cikin ranta,saita miqe ta sauka daga saman.

Hada ido sukayi da shahidan ta sakeyin wani kicin kicin itadinma kamar zata fashe
"Tayimin lefin shine zakace ba zaka lamunci haka daga kowaccenmu ba?,ni harkarta nake shiga?" Ta qarashe maganar kamar kuka zai qwace maga,saiya dafe goshinsa yana kiran sunan Allah dariya nason qwace masa,ya gama karantar cikin kwanakin nan wani rigima take bala'in ji dashi,to a haka ma kenan ya kuma daa ace ya gaya mata komai,ko kafin yabude idanun nasa tuni ta miqe tawuce dakinta hawaye na layi kan kuncinta,hawayen da taketa son ta riqesu amma sunqi riquwa,dai dai sannan nafisa tashigo da warmer me dauke da naman,ya tsaya ya amsa ya sallameta kan yana nan saukowa yanufi dakin shahidan dashi.

Yaga hawayen nata amma ya shareta,ya isa gabanta ya aje yana dubanta
"Ga abinki nan gaba daya ba'a taba miki ba" hararar kwanon tayi
"Idan naci Allah ya tsinemin,nace ta dafa min?,ni danye nakeso a dawomin da abuna" tashin hankali ya furta a hankali saiya zauna a qasa dirshan yana kallon agogo
"Ki rufamin asiri kiyi haquri,a yanzu dai kinga dare yayi bansan inda za'a samo danyan naman kai ba,amma kizabi wani abun komeye zan nemo mikishi" murmushi tasaki cikin ranta,ko banza zata rama iskancin nafisa cikin ruwan sanyi,saita qunsa mata itama,amma afili saita sake hade rai ta dage ga abinda takeso,yaci gaba da lallasarta,saida tagama sarautarta sannan tace
"Ka daukeni muje,awara nakeso da miyan cabbage" haba ya kama
"Tirqashi!" Idanu ta zaro
"Au hakama kace?,na fasa aje a samomin nama na danye" miqewa yayi yana dariya,shi gaba daya ma rigimarta dariya take bashi
"Ni bance ba,kinga yanzu an kusa sallar magariba,bari idan anfito daga sallah sai muje" saita kauda kanta tana qissima yadda zata kaya,har yaje bakin qofa ya dawo,ya durqusa saitinta har tana juyo hucin fitar numfashinsa
"Anya ko my anshad,wannan abun naki babu walakin goro a miya?" Fito da dukkan idanunta tayi tana kallonshi,don bata gane me yake cewa ba
"Me kake cewa?" Bata ankata ba taji hannunshi saman mararta,ya sake qasa da muryarsa wanda hakan yasa ya sake wani sanyi da taushi
"Banyi ajiyataba a nan kuwa ranar nan?" Buge hannunsa tayi da sauri sannan tamiqe tsaye
"Allah ya kiyaye,bakinka yasari danyan kashi" yana tsaye yana dariya harta shige bandaki kana ya juya yafice,yana qissimawa ranshi dama hakan ta kasance,da shikenan fargabarsa kan boren dazai fuskanta wajen shahidan yaragu matuwa,da zuriyyarsu da suke kadan sun qara yawa kenan,saiya tsinci kansa da cewa
"Allah amin", amma kai kam wanne irin qwararren dan qwallo ne haka idan haka ta tabbata,ace bugu daya ka jefa qwallonka a raga?", shi da kanshi ya baiwa kanshi dariya,ya tura qofar dakinsa yashiga.

Tsuru tayi a bandakin,hakanan maganar anwar din ta tsaye mata a rai,saita shiga lissafin kwanakin al'adarta,kwananta dai biyar da gama al'ada wancan al'amarin yafaru tsakaninta dashi,sai gaba daya lissafin nata ya rikice inda daga qarshe ta tattara ta ajeshi waje daya tana cewa
"Bari na saka idon zuwan next periode,kai haba daga abu sau dayama sai ace wani abu ya afku,gashinan wasuma sai suyi shekara sunayi amma ba cikin ba dalilinsa" sai kuma kunya ta kamata da lafazin data fada din,hankalinta kuma ya kwanta da wannan tunanin,tashiga yin wankanta abinta.


_gobe zakujini shuru zanje weekend in sha Allah don na samu damar typing sosai,na gaji da qananun pages din nan nima,ku huta lpy_🥰🥰*Alqawarin Allah*
50

Kwalliya ta dauka sosai,tane sani taqi sauka saidaya fito daga nashi dakin,baki ya saka kawai yana kallonta,yanajin kamar dabiyu tayi wannan adon,ta masa wani irin kyau na daban,saiyaji kaman ya boyeta yayi ta kallonta shi kadai.

Tana gaba yana bayanta suka sauko,daidai lokacin da nafisan ke zaune a falon hannunta riqe da remote tana dakon fitowar anwar din,kanta ta daga ta dubesu sanda suka sauko din,wani malolon kishi ya tsaya mata a wuya,kaman yadda shahidan ta saba bata dubeta ba tayi gaba abinta tabarshi dayi mata bayani.

Minti wajen uku sannan yafito yanayin fuskarshi yadan sauya,da alama ba maganar dadi sukayi ba,ta tabe baki cikin ranta don tasan ko banza iya yanzu kawai burinta yacika,hakanne kuwa,don sanda yafice din bayan ya gama mata iya bayanin daxai matan dora hannu aka tayi xata runtuma ihu,sai kuma ta tuna tunda basu fita ba zasu iya jiyota,nadamar taba mata naman datayi ya kamata,don bataso farincikin data tanada ayau shahidan ta wargaza mata shi ba,so tayi yau ta lallaba ko yaya anwar din ya rage mata zafi gashi da alama shahida ta bata komai,haka ta dinga zarya tsakanin waccan bango zuwan wancan tana tunanin matakin daya dace ta dauka,don tasan shahidan tana sane,ramuwar gayyace taso yi mata wanda hausawa sukace tafi ta gayya zafi.

Saida suka hau kwalta sosai sannan ya dubeta
"A wanne guri yanzu zamu samu awarar" baki ta tabe ta yatsina fuska
"Na fasa,kaini gidan anty usaina kawai" baice komai ba ya sauya akalar motar zuwa kan titin da zai sadashi da gidan anty n.

Ba qaramin murnar ganinsu anty usainan tayi ba,ta amshi shahidan hannu bibbiyu,a rayuwa Allah yasa mata qaunar shahidan,suka sha hira sosai har anwar din yaso yazama dan kallo,saidai ko banza ranar ya mori kallonta,don duk wani motsi nata tana idanunshu,anty usainan taganshi yafi sau nawa saiya shafa qeya kawai ya waske,daga baya ya dora daga inda ya tsaya,tayi musu tayin tuwo anwar din yace
"Nidai a qoshe nake,itama kuma tunda bata damu dashi ba bana tunanin zataci" harara ta saci idon anty usaina watsa masa gami da murguda mishi baki sannan ta dubi anty usainan
"Qyleshi anty,zanci a zubomin" sa'ida ce ta zuba mata ta kawo mata,taci kuwa sosai ta qoshi abinta,sai tajima bata sha'awar naman koda za'a kawo mata shi yanzu
"Ya kamata ka samu lokaci kaje ka dubo inna,jikinta ya tashi fa batajin dadj,nima dazu na dawo daga katsinan ana sallar magaribar nan"
"Wallahi kawu ya gayamin,amma cikin satin nan sha Allah zan samu muje mu dubata"
"Yadai kamata" sai wajen qarfe tara suka mata sallama suka fito.

Suna shiga motar caraf ya kama hannunta,yadan matsa yadda taji zafi kadan sannan yace
"Wa kika murgudawa baki?,waikin manta mijinki ne ni?" Zame hannunta zatayi amma ta kasa ya riqeta qam,bai qyaleta ba duk yadda faje turjewa sai daya jawota jikinsa yadan rage xafi sannan ya tada motar yana sauke numfashi yace
"Awarar taki fa?"
"Na fasa banaso" ta fada tana gyara yafenta hadi dayin kicin kicin,har sukaje gida bata sake tankashi ba.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


A cikin satin ana ya gobe zata fita girki tana kitchen tana hada abincin dare a gaggauce saboda wani dogon bacci daya dauketa,bata farka da wuri ba sai wajen qarfe shida saura,shima wayar zunnurah ce ta tadata,haka ta shiga kitchen din ta saka wayar handsfree tana girkin suna hirarsu.

Ta dade dacin wannan burin,Taci alwashin saita bata mata ranarta kamar yadda itama tayi mata,sanda nafisan tashigo kitchen din sam shahidan ma bata lura da ita ba,ta juya baya taba gyara salad,kusa da ita ta tsaya tana qoqarin kunna gas gamida waqe waqe,sau daya ta kalleta taci gaba da aikinta,abinda yafi bata mata rai yadda sam nafisan bata iya sallama ba,idan zata taddaka sau nawa ba zata tabayi maka sallama ba,tukunya ya dauko ta isa bakin fanfo ta cikata da ruwa,saitin bayan shahidan tasaki tukunyar take ruwan cikin ya zube ya fantsama har bayan shahidan wanda hakan yadan razanata saboda yadda ruwan ya fantsamo mata ba tare data tsammata ba
"Subhanallah" ta ambata da sauri tana waiwayowa,kallon banza nafisa tayi mata ta duqa tadauki tukunyarta kamar bata aikata komai ba,abun yayi masifar bata ran shahidan,saita waiwaya ta katse wayar da sukeyi da zunnurah ta waiwayo ga nafisa cikin kaushin murya
"Bakiga abunda kikayi bane?" Dadi yacikata dama haka takesk,saita juyo ta jefa mata harara
"Ai bani da ido,au baki sani ba" sosai ran shahidan yasake baci,cikin zafi tace
"Haka kikace?"
"Eh,na fada,ko za'a hadani da mijine?,aikin banza mutum yawani dinga nuna koda yaushe shi dan gaban goshin mijine,bayan munsan komai,an gama tsotse tsotsen syrup da bin maza,an zubda ciki anzo an liqema mutum,bayan yace bayayi bayayi,an rabu dakai tsahon shekaru amma baka haqura ba sai daka bi diddigin mutum ka nemoshi ka aura,wallahi tur da irin wannan zuciyar,halin 'yan....." Wata gigitacciyar tsawa ta ratso kitchen din ana ambaton sunan nafisa!!!!.

Wata mummunar faduwar gaba tasamu nafisa sanda ta waiwaya suka hada idanu da anwar yana shigowa cikin kitchen din,fuskarsa a dinke murtuk,bacin rai ya nuna baro baro kan fuskarsa,cikinta yawani murda,take fitsari yacika mata mara,wani tashin hankali ya rufto mata gumi yasoma wanketa,tashiga uku!,yanzu duka anwar yaji wannan maganar?!,me zatace masa?.
"Nafisa?,me kike fada?,kinsan me kike cewa?!" Ya qarashe managar tasigar tambaya kuma cikin tsawa

Dauke idanunta da suka cika tafff da qwalla shahida tayi daga kan anwar sanda ya qaraso ta rabeshi tafice daga kitchen din,kuka takesonyi,kuma batason yi a gaban nafisan,duka suka bita da idanu harta fice,maida dubansa yayi ga nafisan yamatso inda take tsaye kamar wanda zai shaqeta
"Nafisa!,matata kikewa wannan cin fuskar?,ita kikewa wannan zagin?" Cikin qarfin hali dason kare kai ta turo baki
"To basai ka tsaya ka tambaya ba tukunna kafin kayi hukunci....."
"Keep quite....a ina kika san dukkan abinda naji kina fada?!" Tofa anzo wajen,take taji wata hadaddiyar gudawa ta taru a cikinta kamar xata saketa,take idanunta suka raina fata,qwaqwalwarta tahau aikin harhada mata amsar da zata bashi ba tare data samu matsala ba,tsawa yasake daka mata cikin tashin hankali,qwaqwalwarsa nason masa wani hasashe da baya fatan tabbatuwarsa,ta yaya nafisan tasan shahida ta taba shaye shaye?,ta yaya tasan wani abu dayayi kama dabin maza daya taba faruwa a rayuwar shahida?
"Bincike nayi maka.....a dakinka" tayi saurin fada tana ja baya saboda yadda yake huci,shuru yayi yazuba mata idanu yana kallonta yana fitar da numfashi daga hancinsa da qarfi
"Me yasa kikayimin bincike?,me yasa kika shiga hurumin daba naki ba?,bakisan cewa wannan shine babban kuskuren da zaki aikatawa rayuwarki ba?,to bari kiji,shahida ba shaye shaye ba,ko kamfanin magunguna na duniya duka ta shanye tana da qima da mutunci a idanuna,shekarun da mukayi ba tare da juna ba hakan yafaru ne saboda duk duniya babu halittar da nake kishi kamarta,babu halittar data taba yimin abu daya tsayamin arai saboda qaunar da nake mata kamar shahida,shahida rayuwata ce wanda hakan yasa nakasa haquri da ita sai dana mallaketa,shahida duniyata ce,shahida itace anwar gaba daya,banda shahida da baki ganni kamar yadda kake kallonaba a yanzu,da tuni wani anwar din

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment