Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ake magana ba wannan ba,kinyi kuskuren da nake miki gargadi da babban murya da dagayau karki sake maimaita makamancinsa,dukkan abinda idanunki kuma suka gani ki tabbatar ya tsaya daga qirjinki ne zuwa zuciyarki,idan ba haka ba....ki shirya tarbar dukkan sakamakon da zai biyo baya" yana kaiwa aya yajuya cikin gaggawa yabi bayan shahidan,wanda ina tuni ya shige dakinta ta kuma kulle kanta,jin kanta take yana juya mata wanda yarage saura kadan jiri ya kada ita,ta samu gefan gado tazauna,kukane ya qwace mata,wannan wacce irin masifa ce?,haka aikin sabo yake dama?,yayita bibiyar bawa,yau kishiyarta ke goranta mata abinda tamanta datayishi cikin babin rayuwarta,ta yaya tasani?,ba shakka idan ba anwar ne ya shaida mata ba babu tayadda za'ayi tasani,kuka sosai take tana fatan ta rage koda kadanne daga zugin da takeji a zuciya da qirjinta,tana tsaka da wannan tajishi yana knocking tare da bata umarnin tabude,saidai bata da buqatar ganinsa ko kadan,don haka ta kwanta rub da ciki ta tura kanta qasan filo.

Ta fannin nafisa kuwa jingina tayi da cabet din kitchen din,maganganun anwar na girmama cikin kanta da qwaqwalwarta,yadda yake jefa mata maganganun tabbas kamar yadda yafada ne babu abinda bazai iya aikatawa ba akan shahidan,wannan wanne irin mayen so ne da aka gaza cisgeshi a wurgar daga zukatansu gaba daya,a daddafe ta fice daga kitchen din itama zuwa nata dakin cikin firgici.

Gaba daya ranar wani irin kwana akayi a gidan,kowa ranshi babu dadi,gaba daya bacci ya gagari idanun anwar din,nafisan nason sake saka kwabarsa ta sake ruwa shakaf,abinda yake tsoron tuni ya afku na kada shahidan tayi zargin shiya gayawa nafisan sirrin rayuwarta,a haka asuba ta sameshi,sam bai bude mata dakin ba don yanason yabata lokaci ta sauka ko yayane,uwa ubama yafison tabude masa da kanta,saidai har aka idar da salla gari ya waye ya soma haske rana ta hudo aka doshi goma harda rabi na rana taqi budewa,ya gagara haquri hakan yasa yadoshi dakin wannan karon kota bude koya bude da kanshi.

Dai dai lokacin tana saman abun sallah ta gama sallar walaha,idanunta qur yana kallon waje daya,duk sanda ta tuno kalaman nafisa suna qona mata zuciya,knocking dinsa nafarko kaman idanunta ya buga,ta hango brown din envalope rabi qasa gadonta rabi ta fito,ta miqa hannu ta janyota tana tunanin ko cikin takardunta ne ta zubada bata sani ba,ta bude envalope din tana qwaqulo abinda yake ciki saman cinyarta.

Ilahirin jikinta ne yadauki rawa gaba daya,idanunta ta zarosu duka a waje kaman wadda ke shirin zazzagowa dasu,so take tagani abinda idanunta ke ganin gaskiyane ko kuwa?,cikin rawar jiki tadinga bude hotunan tana kalla,itace jikin wani saurayi haihuwar mahaifiyarta,saurayin da zata iya tuna fuskarshi,kamar saurayin nan daya ajeta a qofar gida,kamar shi,wannan ba ita bace,ba ita bace sam ta fada tana girgiza kanta sanda hawaye yasoma sintiri a fuskarta,saita tsaya cak tana tuna wancan satin anwar yashigo yana neman wata envalope,kada dai ace wannan cw envalope din da yake nema?,daga idanunta tayi da hanzari sanda yagama bude qofar dakin yashigo suka hada idanu,idanunshi suka sauka kan cinyarta da hotunan ke watse,da sauri yasoma takowa daniyyar yakwashesu
"Dakata!" Ta fada cikin sauri da wata irin kakkausar murya
"Wadan nan ne hotunan dakake nema kobasu bane?" Bai amsata ba sai kallonta da yake,murmushi ta saki mai ciwo ta miqe hotunan suna watsewa a qasa
"Koda matarka bata fada ba ya tabbata daga bakinka komai yafito,wadannan hotunan daga ina aka samesu?"
"Sune hotunan da suka tarwatsa duk wata alaqa dake tsakaninmu tsahon shekara shida" idanunta taware duka tana duban anwar din,yana nufin tsayin shekarun zarginta yake dama da fasiqanci mai muni irin wannan?,wannan ce hujjar daya riqa data tarwatsasu ta tarwatsa farincikinsu?,saita lumshe idanunta hawaye mai zafi na fitowa daga idanunta,ya sake takowa inda take
"Zauna muyi magana" ya fada cikin wata murya daya kasa banbance inda ta dosa,saiya koma saman mudubi ya zauna yayin data koma ita kuma tazauna inda ta tashi,ta bude idanunta fes a kanshi tana kallonsa,kafin yace komai tarigashi
"Koma meye yafaru nasan cewa ina karbar hukuncine wanda ke bibiyata bisa kuskure ko ince gangancin dana tafka na sakin Allah da nayi na kama wani abu da sunan maganin da zai maganta min dukkan wata damuwata,na manta da qur'ani,na manta da addu'a,na manta da sallar dare,na manta da azumi,na manta da nafila,na manta da sadaka,na tattara dukkan samun salamata bisa wani magani dake sanya maye ba tare da nasan cewa inashan abinda zai tarwatsa rayuwata bane,zai kawo baqinciki da bacin rai da zai dinga bibiyata,na yadda da aminiyar data zalinceni,taci amanata,ta tarwatsa rayuwata,saidai abun mamakin" ta fada tana dan dakatawa
"Ka gujeni a lokacin daya kamata ka kusanceni,ka tattarani ka watsar dani daga rayuwarka,na tsammaci ko mutum nakashe kaimai rufamin asirine anwar ashe na tafka babban kuskure!" Ta qarasa fada cikin tsawa da daga murya gami da sake bude idanunta,tanajin bacin rai da maganganun data jima suna qunshe a bakinta da zuciyarta yau sunata rige rigen fitowa daga bakinta kamar sunason sufi qarfin qwaqwalwarta,saita miqe tsaye ta soma takawa zuwa wani sashe na dakin
"Kasa hannu ta tunkudeni ka tunkude rayuwata,kaqi sauraron kalaman bakina.....baka qyaleni haka ba!,saida ka aikomin hotunan wadda kayi iqirarin ka musanyata dani,tafiye maka ni,ka dasawa zuciyata da rayuwata guba,ka hana idanuna bacci na tsahon lokaci,ka gigita rayuwata tsahon wani zamani ba tare data samu daidaito ba!" Ta qarashe maganar tana zazzage masa hotunan da aka aiko mata cikin envalope saman cinyarsa
"Ka tirsasani ka aureni,sannan ka aurota don ka tozartani ka nunan iyakata,duka wannan bai maka ba,saida ka kwashe dukkan wani sirrina ka gaya mata wanda a yanzu tasamu bakin gorantamin?" Ta dasa masa ayar tambaya,sai zuciyarta tayi wani irin karyewa ta sulale ta durqushe awajen tana sakin kuka mai tsuma zuciya.

Cikin tsananin mamaki yakebin hotunan da kallo,hotunan dako cikin mafarki yasan bai taba daukarsu ba,hasalima shi tunda yake bai tana daukar hoto da nafisa ba,koda kuwa na bikinsu,yaushe kayi wadan nan hotunan?,waye ya aika mata dasu?,waye yayi hotunan?
"Waye ya aika miki da wadan nan hotunan?"ya tambayeta cikin kaduwa yana kallonta,miqewa tayi tana hada hanya ba tare data bashi amsa ba ta nufi cupboard dinta tabude yasha gabanta
"shahida ki tsaya muyi magana mana"
"Ba wata magana tsakaninmu,komai yariga daya qare,kaiba masoyin qwarai bane,bana sha'awar zama dakai anwar kwata kwata,saki kawai yanzu nake buqata daga wajenka,waishin mema yayimin saura bayan duka abinda yafaru ka kwancen zanina a kasuwa?,yanzu kace zaka biyoni ka dauramin?"
"Idan akwai wanda zan gayama sirrinki tsahon shekarun to yabiyo bayan anty usaina,bayaga zuciyata dana barwa duk duniya ba wanda yataba ganin hoton ko yasan dalilin rabuwarmu,koda na rabu dake shahida ina kare qimarki da martabarki a bayan idanunki,dalili kenan daya sanya ban yarda wani yasan komai kan rugujajjiyar alaqarmuba ta baya" Sam bata saurareshi ba sai kayanta data soma zubowa dasu qasa,wani irin jiri da amai yana taso mata,duk yadda anwar yaso ta tsaya ta fuskanci taqiya,hada kayanta kawai take,ga wani kuka da take wanda yakejin kamar ana yankar zuciyarsa,yadda ta birkice haka ta birkitashi,ya rasa ta ina zai soma,ganin ta gama hada kayanta tsaf,hakanan tana yunqurin sanya hijabinta yaga bashi da wani sauran dabara illa ya rufeta,haka kuwa akayi wanda hakan yasake tunzurata,ta zauna ta dinga kuka sosai tare da gaya masa yabudeta,yana zaune a falon dafe da kanshi,yanajinta tana amai amma babu damar yabudeta,yasan hakan da zaiyi shine hanya daya tak da zai bata damar subuce masa,gaba daya kaman ba shahidanshi ba,ta birkice fiye da baya.

Haka sukaci gaba da xama har aka kira azahar,dole ya miqe yashiga dakinsa yadaura alwala ya sauko zuwa masallaci,falon shuru babu kowa wala'alla itama nafisan na dakinta tana jinyar zuciyarta,abinda yafaru dazun duka yadinga dawo masa akai,wansa taabar tension din shahida yasa yama kasa yin tunanin dakyau,sabida haka ya watsar dashi yana tunanin hanya mafi sauqi dazai hana shahida tafiya.

Da sauri tamiqe sanda ta tuna da ragowar muqullin dakin guda daya data cire ta ajjiye,ta jawo locker din ta duba yana nan inda ta ajeshi kuwa,hijabinta da slippers dinta ta sanya ta dauki jakar kayan nata ta bude tafice.

Bata jima tana takawa ba tasamu taxi,wanda saida tashiga ya tambayeta inda zata,a sannan ta soma canki canki,daga qarshe ta yanke tafiya katsina,wannan karon gwara kome daada zatayi tayidin amma aurenta da anwar tasan yadda zatayi ta rabashi
"Ka taba zuwa katsina malam" murmushi yadanyi
"Gaskiya hajiya nafi jigilata a cikin gari tsakanin unguwannai"
"Ida nacema yanzu ka kaini katsina shata ni kadai,zan biya kudin duka sit din motar na qara maka akai xaka?" Cikin farinciki yace
"Ah hajiya me zai hana?,dondai katsina kawai,Allah yakaimu lpy" daga haka ya sauya akalar motar tashi,a maimakon tasha da zai kaita saiya dauki hanyar titin katsina.

Qarfe daya na rana tadira gidan daada,ko kafin suje tuni ta galabaita,don babu komai a cikinta,tana sallama tsakar gidan tanufi bakin famfo tasoma kwara amai,daada na daga falonta zaune,labulen falon a dage yake saboda haka tana iya hangota,daga sanda ta amsa mata sallama kafin tace komai saijin kakarin aman tayi,ganin abun bana qare bane saita miqe ta qaraso inda shahidan ke duqe cikin galabaita
"Kee,lafiya kuwa?" Bata iya bata amsa ba saita dafeta yadda taketa yunquri saidai babu komai a cikin da zata futar,saidaya lafa yunqurin sannan daadan ta zuba mata ruwa ta wanke fuskarta da bakinta,ta taimaka mata suka shiga rumfarta,saman kujera tasamu takwanta rigingine tana maida numfashi,tsahon minti goma sai kuma tafashe da kuka,daada ta tsaya daga hada lagwanin da take baki sake tana dubanta
"A'ah?,ke kuma meye?,waime yake faruwa ne?,inama anwarun koke kadai kika taho?" Baya ta juyawa daadan ba tare data amsa mata ba taci gaba da kukanta,me yasa anwar yayi mata haka?,me yasa ya azabtar dasu tsayin shekaru akan wannan dalilin?,me yasa bai tuntubeta yaqi ta bakinta ba,ashe bai yarda da ita ba?,ashe yana da shakka akanta?,dukda ta wani fannin yana da 'yar gaskiyarsa,saboda hausawa sunce gani yakori ji,ya ganta a gabansa aka sauketa cikin maye,kuma aka jefata da mummunar kalma bin maxa wanda harta hada da zuba ciki,d worst part ma shine yadda akayi yabar nafisa tasan komai,ta tsammaci zai rufa mata asirine kamar yadda xai rufawa kanshi?,idan duk duniya zaya gayawa ba zata damu ba amma kishiya fa?,ta sani cewa duk wani abu datake gani sakamakone da kuma daya daga cikin illoli na sabawa dokar Allah tashan wani abun maye,saita koma rub da ciki ta sake fashewa da kuka,idanu daada ta zuba mata kafin ta tabe baki kana ta miqe tana tattara kayanta don barin falon tana cewa
"Kinga nikam bazaki kashemin dodon kunne a banza a wofi ba,bayan na tambayeki kinqi gayan komai,saikace wadda uwarta tamutu" da haka tafice takoma sararin tsakar gidan tabarta a falon.

Ba qaramin tashi hankalinsa yayi ba sanda yazo ya tadda batanan din,yaduba ko ina cikin gidan amma ba ita ba alamarta,gurbin kayanta da akwatunta da yaga ba wasu ya tabbatar masa tatafi din kamar yadda ta niyyata,zama yayi gefan gadonta jikinsa a sanyaye,yasan tabbas dama za'a rina,amma bai zaci har haka ba,yajima zaune ya rasa abun kamawa,baisan ina tayi ba,baison kuma yakira kowa ya tambayeshi bare ya daga masa hankali,amma daga qarshe tilas yasoma kiran anty zubaida umma sannan anty usaina saidai duka bata nan,komawa yayi ya kwanta rigingine saman gadon nasu yana kiran sunan Allah,daada ta fado masa a rai,ya tashi yazauna sosai yana lalubar wayarshi.

Mintina kusan talatin daadan tana zaune tana saqe saqe ita daya a ranta kan meye faru da jikartata,qarar wayarta dake soke cikin qarafunan window ta katseta,don anan take ajjiyeta tace batason abu yayita qara shi kadai yana damunta,ta daukota tadaga ta kara akunnenta ba tare datasan me kiran ba,don ba ganewa takeba saidai idan ka kira ka gaya mata waye,yana sallama tagane waye,ya gaidata kana cikin hanzari yace
"Daada,don Allah shahida ta iso nan?"
"Au dama bakasan da tahowar tata ba?"
"Alhmdlh,indai tana nan din shikenan,ina tahowa nima inakan hanya"
"Karkazo yau,kabari sai gobe idan Allah ya kaimu" dan jim yayi,don ason ransa ayau din yakeson yataho din,donko ya zauna din bashi da kwanciyar hankali,amma yasan dole akwai dalilin daya sanya daadar ta fada haka,a sanyaye yace
"To Allah yakaimu"
"Ameen" ta fada tana katse kiran,dakin tasake komawa,wannan karon kukan nata yayi sauqi,gefanta tasamu tazauna ta kira sunanta
"Tashi ki xauna na tambayeki" daqyar taja jiki tazauna daadan ta dubeta yadda lokaci daya tafada
"Meya hadaki da anwar har kika baro kano zuwa katsina ba tare da saninsa ba"
"Na gama aurensa ne daada,ki gaya masa yasakeni kawai" tafada kanta tsaye,baki daadan ta kama
"Wannan tsiyar kuma kika tsiro da ita aure ya doshi rabin shekara?"
"Wannan karon dagaske nake daada,bazan koma gidanshi ba,kunso na aureshi tona aureshi yanzu kuma sai a barni na huta" kai kawai ta gyada tana nazarinta,saita miqe ba tare datace mata komai ba tafice daga dakin.

Ganin alamun bataci abinci ba yasaka daadan dora wani abu,sannan ta dama kunu don ita bason tea take ba,sanda tagama ta tadda shahidan wannan karon zaune jingine da kujera,ta aje mata tace ta dauki wani abu taci,kunun kawai ta iya sha daadan na ankare da ita,sabida haka tana fita tayi kiran kawu ummaru da kawu shehu a waya tace suzo tana son ganinsu nan da qarfe biyar na yammaci.

Kuka kawai take a tsakiyar kawun nan nata da daada,juyin duniya tafadi abinda ke faruwa taqi bude baki tace komai,abunda yasake tunzura daada kenan,takaici yacikata,ji take kaman takai mata mangara,banda taga alamun bata da isashshiyar lafiya,daga qarshe daadan tace
"Ummaru,ku tashi ku tafi kubarni da ita,ai gobe anwarun xaizo xanji komai daga bakinsa,kuma wallahi ki kuka da kanki indai harya tabbata iskancine da iya shege yakawoki" daga haka taron ya watse,yayin dataci gaba da kukanta,duk da daada najin tausayinta a qasan zuciyarta saboda yadda taqi cikin isashshen abinci amma saita watsar da ita,sai daga bisani tadauki abinci takai mata
"Idan kinga dama kici,don kuka babu abinda zai qara miki koya rage miki"


*kin karanta littafin DANGANTAKAR ZUCI?,NA RAYYAN SHUGABAN KAMFANIN TRIPLE R GEM WANDA NAFISA SUKAJE SIYAYYA KAMFANINSA?😊IDAN BAKI KARANTA BA MAZA GARZAYA TASHAR SAUTIN HKIMA DAKE YOUTUBE KI SAURARI LITTAFIN CIKIN SAUQI,TASHAR SAUTIN HIKIMA TAKUCE!*51

Qarfe tara na safiya cikin garin katsina tayi masa a qofar gidan daada,yana isa sukayi kacibus da sulaiman,don haka tare sukra rankaya gaba dayansu zuwa cikin gidan.

Tunda gari ya waye tayi wanka da sassafe take kwance,cikin doguwar riga da hijabi kamar matar mamaci,tana nade saman gadon daadan ta soma jiyo muryarshi sama sama,saita rintse idaninta tana jin bugun zuciyarta na daduwa,haushinsa na kamata,hakanan takejin wani mugun haushinsa,duk wata wahala ko qunci dasuka fuskanta suke kan fuskanta ma shine sila,saita sake lafewa,tana kallo sanda daadan ta daga labule saita runtse idanu kamar maiyin bacci,harta sake labulen tasake fita tana kallonta.

Sosao daada ta tsareshi da idanunta da suka masa nauyi da kwarjini,irin kallon da tunda yake da ita bata tabayi masa irinsa ba
"Anwaru,ka dubeni da kyau,banason wani sauran boye boye,mun gaji da boye boyenku da ninkemu baibai da kuke kai da ita,kafito ka gayamin asalin rigumarku da abinda ya raba tsakaninku wanda har kawo yanzun nan da ake magana kanku bai hadu ba kai da ita" tofa tashin hankali,hankalin anwar din ya tashi qwarai,idan har ya gayawa daada cewa ya zargi raihana da fasiqanci ne kuma bayan ba haka bane,toba shakka zancan ta taba shaye shaye zai fito,hakan kuwa dai dai yake daya dauki wuqa ya dabawa cikinsa ne,cikin sanyin murya da nutsuwa yace
"Kiyi haquri daada,bashi da amfani ayita bada labarin abinda yariga daya wuce,amma abunda zan gaya miki kawai shine,mun samu babban sabani ne nida shahida shekarun baya,wanda hakan yayi silar rabuwarmu,na zaci wata halayya daga gareta ashe kuma ba haka bane,na aureta akan hakan,nayita bata mata rai duk abisa hujjar abinda nake ganin da idanuna nagani ashe akwai wani daurin boye da bansan dashi ba,duka gaskiyar hakan bayyanar min ba sai a satittikan da suka gabata,na gane cewar abinnan da nake zato ba gaskiya bane kuma ba haka bane,to ban sanar mata ba,ina tsaka da bincike sai sabani ya hadata da abokiyar xamanta,ta goranta mata kan wannan abun da nake zato akanta,kunnuwa sukaji kuma na tsawatar,don wallahi wallahi ban taba maganar shahida da ita ba bare na gaya mata wani abu daya shafeta,donko yayata da take makwafin uwa a gareni haryau har kwanan gobe batasan meye sila ba,batasan dalili ba,dana ritsata da tambaya ta gayamin buncike tayi cikin dakina ta gano hakan,saboda akwai wasu abubuwa dana aje da suka shafi matsalar,amma kafin na tadda shahida nayi mata bayani taga wadan nan abubuwan da naketa boyewa,ta tubure kan nina gayawa nafisa,saboda itama an taba kai mata hotunana nida ita a sannan azuwan nina aiko dasu,sannan nafisan itace zabina,wanda kaf rayuwata ban taba tsayawa munyi hoto da nafisa makamancin wannan ba,bansan waya kai mata ba,bansan waya hadasu ba,duk yadda naso mata bayani ta gaza fahimtata,ta kuma qalubalanci bana sonta bana qaunarta,tunda na hukuntata kan wannan abun,nakuma barta na tsahon shekarun baya,saboda haka saki take nema daga gareni"
"Ashsha,ashsha,saki?,a'uzubillahi" dada ta fada ranta na baci,tayi shuru tana nazari,babu shakka akwai soyayya mai qarfi da girman gaske dake dawainiya da wadannan zukata da kowanne yakasa bude baki tsahin shekarun ya gayawa makusancinsa abinda ya hadashi da dan uwansa,wuya da dadi,bacin rai da farinciki har yanzu babu wanda yasamu nasarar jin abinda ya hadasun,itadinma ba zata matsanta ba,indai ba shahidace tayi ra'ayin kanta tabude bakinta ta gaya mata ba,iya bayanin da anwar din yayi mata ya isheta madafa da makamin dafawa,kallo daya tayi masa ta karanci tsantsar nadama da tashin hankali tattare dashi,wannan kawai ya isa hujjar shahida tayi haquri,ana raba aurene idan ya bayyana akwai cutuwa mabayyaniya cikin tarayyar ma'auratan,irin cutuwar da abokin zama ya gaza gyara halayyarsa,cikin biyu babu ko daya a zamantakewarsu,kuskure ne kuma ya gane yayi ya kuma soma gyarawa ma tun kafin aje ko ina,amma hakan baxai hana ta sake masa fada ba saboda gaba
"Dukkaninku kunyi kuskure,wanda abu nafarko da Allah ya umarcemu dashi cikin qur'aninsa me ya mana bayani yana cewa(yaku wadanda kukayi imani idan fasiqi yazo muku da labari kuyi bincike ku nemi shaida,kada kuje ku afkawa wasu mutane cikin rashin sani,saiku wayi gari kuna nadama kan abinda kuka aikata),kaga wannan aya gaba daya ta ishemu a rayuwa,da kuna zamuyi aiki da ita da yawan yawan matsalolin da muke fama dasu da basu samemu ba,da bamu afka cikin mutuncin junanmu ba,da bamuyi gaba ba,da bamuqi junanmu ba,babban kuskuren daka tafka anwar shine rashin bincike da biyewa wata shaida wadda kaga daga qarshe ka fahimci shaidar bogi ce,q rayuwa koba a wannan bigiren ba inamai horarka daka kasance me bincike aduk wani labari ko lamari dayaxo gabanka,koda kana da shaida idan akwai yiwuwar samun wata shaidar ta hanyar bincike to kayi,mu kuma idan muyum ya fahimci kuskurensa,to cikar mutum shine yayi yafiya ga wanda ya masa laifin,a yanzu bazan tilasta shahida ta yafe maka ba,don idan na tilastata din bansan gaba me zata haifar ba,zata iya komawa gidanka amma kuma zama yaqi dadi,saboda haka,kaje kawai,zanyi iyakar iyawata inga komai ya daidaita tsakaninku" take gumi ya karyo masa,ya kuma sare saboda dadan ita kadaice hope dinsa na qarshe,baya fatan zancen yaje kunnen innarshi don yasan halinta sarai ba zata masa uzuri ba,zafi gareta hakanan ta tsani miji ya cutar da matarsa ko qaqa,don tace ita nata mijin bai cutar da ita ba,zamowa yayi yazauna dirshan gaban daada bayan yacire hular kanshi kozai rage jin zufar dake damunsa,muryarsa tayi laushi sarai kamar yadda jikinsa yayi
"Ki taimakeni dada,qaunar shahida cikin jinina take,koda na rabu da shahida zuciyata bata fasa wahala akanta ba,raina da jikina bai daina buqatarta ba,kullum kwanan duniya cikin tuhumar kaina da kaina nake yare da kwadayin son ganinta kojin muryarta,amma kishinta da nake duka yadanne wannan,don Allah daada ki rufamin asiri,ki taimakeni,koda wannan shine taimako na qarshe da zakiyiwa rayuwata" sosai taji wani sanyi cikin zuciyarta,ko iya haka aka tsaya ta tabbatar da cewa anwar din ba qaramin soyayya yakewa shahidan ba,hakanan bazai sake kwatanta abu makamancin haka ba,tausayinsa da dariya suka taso mata amma saita danne,sabida tana son ko yaya ne ya dandana shima,zatayi kuma hakanne badon shahida tata bace kodon mugunta,A'ah,zatayinne saboda gujewa barakar da zaya faru anan gaba,sannan tasan duk inda akaje aka dawo hukuncin da zata yiwa shahida to na anwarfa mai sauqi ne akan nata
"Kaje anwar kaci gaba da addu'a,zanyi iyayina in sha Allahu" kamar bazai tafi ba hakanan yayi mata sallama yamiqe yana raba idanunshi wurare daban daban ko zaiga gilmawar shahidan amma harya fice ba ita ba dalilinta,gaba daya ji yake kaman ya rasa shahidan kenan,maganar da suka gama yanzu da daada,binda ya sake kashe masa duk wani qwarin gwiwa kenan,gidan inna yaso ya qarasa amma saiya kasa saboda kanshi dake sarawa,ya sauya akalar motarsa sashen da zai samu hotel donya kama daki yahuta,yana fatan ba hawan jininsa ne zai tashi ba,don bashi da buqatarsa wannan lokacin,lafiya yake da buqata cikakkiya da zai samu damaryin binciken dayake gabanshi,ya lashi tokobin duk wanda keda saka hannu kan wannan lamarin bazai qyaleshi ba,saiya biya farashin duk wani tashin hankali da suka fuskanta da baqinciki.

A bazata daadan tasake shigowa wannan karon don haka bata samu damar rufe idanun nata ba tashigo dakin
"Karki kuskure,na ganki,tashi muyi magana" kuka keson qwace mata amma ta danneshi,tasan cewa tunda yazo bata da wani sauran goyon baya cewa daadan zatayi ta tashi ta bishi,amma ga mamakinta saitaga ta zauna gab da ita cikin taushi tana cewa
"Muyi magana ta hankali dake mana shahida" sai hankalinta yadan dawo jikinya,nutsuwa kadan ta saukar mata
"Me anwar yayi miki ne?" Sai kuma ta sake dirircewa,daadan tasaki murmushi
"Ki kwantar da hankalinki ki gayamin,wannan karon ina bayanki,don na gaji da ganin wannan kukan naki ace watanni da shekaru masu yawa amma har yanzu basu qare ba?" Ajiyar zuciya tafitar sannan cikin rawar murya tace
"Wallahi daada anwar ba masoyin gaske bane,ya rabu dani tsahon shekaru masu yawa ashe saboda zargin da yakemin da hujja guda daya daya gani da idanunsa wadda hujjar tasa cakude take da qarya da makirci,bayan mun sake haduwa yacigaba da cutar dani da kalamansa,xamana dashi a gidansa duk sanda ta raya masa zai gayamin baqar magana da zata qonamin zuciya,daga qarshe ya auro wadda ya wulqantani ya maida gurbina da ita,ya kwashe abinda bata sani ba ya gaya mata har tana goranta min,alhalin ya gano gaskiya kuma bai gayamin ba saboda sonkai irin nashi,ta yaya zanci gaba da zama dashi daada?" Haba ta kama tana kallonta,itadinma dai bata fadi ko daya daga cikin abinda ya hadasun ba,sai bayani take tana rurrufewa kamar shidin,da sauri daadan tace
"Kai kai kai,amma anwar bai kyauta min ba,yaci amana,ashe azabtar dake yadinga yi bayan nayi ruwa nayi tsaki na aura masa ke?" Da sauri ta dubi daadan,don sai taji kalmar tayi girma da yawa datace azabtarwa,saboda haka tace
"Ni gaba daya banason zama dashi,don Allah daada"
"Kwatar da hankalinki,saki kikeso kenan yanzu?" Gabanta yafadi,amma eh shine amsar da zuciyarta ke bata,saboda haka cikin sanyi ta kada kai sannan tace eh,kanta ta shafa
"Sha kuruminki idan dai wannan ne kin nema kin samu,tashi maza kiyi wanka kici abincinki ki qoshi ki shiga harkokinki,na sake ganin qafarsa cikin gidan nan" mamaki ya kama shahida,baki bude take kallon daada,meya sauyata haka lokaci daya?
"Ko baki yarda bane kika kafeni da ido?,ai dama ko abaya don idanuna sun rufene ina masa kallon na Allah ashe ba haka babe,yanzu kuwa zai gane kurensa,zaisan inasonki,tashi maza kije ga ruwa can mai dumi" murmushi ya subuce shahidan
"Na gode daada,dama nasan shiga yayi kawai tsakaninmu"
"Qwarai kuwa,yanzu kuwa na fiddashi fit" haka ta miqe cikin qwarara jikinta tafice donta sake wanka takuma gasa jikinta,don kwanciyar jiya dayau duka jikinta ciwo yake mata,da kallo daada ta bita sannan tamiqe tabi bayanta.

Har yayi sallar magariba yana dakin hotel din daya kama,bacci da hutawar dayaso yi duka basu samu ba,lokaci daya yaji hankalinsa kuma yayi gida,ya kamata yaje yaji me ake ciki kam bincikensa,don lokaci yayi daya kamata ace ya matsa lamba,saiya tattare dukkan wani dake mallakinsa a hotel din yafito.

Tunda safen ta

2 Comments On ALKAWARIN ALLAH
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls cmplt ????

Please Login or Register in order to submit comment