Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali tace tambayar ka" nake sanyi Kuma inasan don Allah "kafada Mani gaskiya banasan ka" boye Mani komai,

Murmushi yayi har saida taji sautin sa akun'nanta ta rintsa ido, yace my cool ki tambaye ni KO" mene shi indai nasani zanfada miki gaskiya kinji?

tace OK Abdul-jabbar kanada MATA? Jiyayi kirjinsa" yabuga zaune yake Amma saboda tsabar razana dajin tambayan datai masa" saida "yamike tsaye,
tace ina nufin kataba AURE NE?
gaba daya Abdul-jabbar ya daburce Cikin Karfi hali yace.....?



๐Ÿ’Lufhat ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page81-85

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

edited by Zainuddeen zain

----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------

only exquisite and whizkid writers are oppw to be pen writers.


โœ๐Ÿพ


Ah! Eh! Da sauri Humeeh ta katsesa da cewa just amsa my question yes or no? Saida ya tattara natsuwar sannan yace "eh nataba aure Amma!

da sauri ta katse sa dacewa OK nagode kwarai DA abinda Kai Mani sai anjim, Da sauri Abdul-jabbar ya katse ta da cewa my cool ki saurareni, tace no I don't want to hearing anything from you, da sauri ta katse wayar,

tabarsa yanata fadin Hello! hello!! hello!!! gaba daya Abdul-jabbar ya birkice sai fadin yake pls my cool ki saurare ni mana sai faman neman line din "ta yake Amma switch off,

itakam Humaira tana katse wayar sai ta tsugun'na tareda sakin wani irin kuka Mara sauti fadi take meyasa zakai" Mani haka Kasan yadda nake sonka" kuwa? "my special Ina sonka dayawa shiyasa nake matsananci KISHIN Ka" har Ina tunanin babu wata ya mace dazata rabeka sai ni" Ashe bansani ba tuni wata mace tadade da rabarka?

Wani kuka tasake Saki mai ban tausayi, daga can Umma ta kwala mata kira, da sauri ta amsa tareda mikewa tsaye tana goge hawaye,

tace Umma gani' kallon ta Umma tayi tace meki keyi awaje? Ciki rawar murya tace bakomai da sauri Umma tace kuka kikeyi? tace a ah, tace hmmm yaro man kaza yanzu saboda Da namiji kike kuka? tun yanzu Zaki farasa damuwa da namiji a zuciyar ki? lallai kinada "aiki dalla wuce kitafi ki kwanta, sum-sum tawuce ta kwanta.

A bangaren Abdul-jabbar kuwa abun ba'acewa komai, domin kuwa gaba daya ya birkice yatada hankalin sa" yatada Na Dalter boy" yakira Waya har yagaji Amma amsar dai guda ce wato switch off, kusan kwana yai yana abu daya, dayaga abun yanason birkita masa kwakwalwa sai kawai yaje ya dauro alwala, yafar gabatar da lafila tareda rokon All akan duk abinda yaza faru tsakanin sa da my Cool dinsa toh" Allah yasa yazo cikin sauki, yanda yaga Rana haka yaga dare,

Itama Humeee hanne Ya kasance agareta yadda taga Rana haka taga dare ko kadain bata runtsa ba,don haka kids gariyawa sai ta tashi da matsananci Zazzabi mai zafi da kyar ta'iyayin sallar asuba sannan takoma ta kwanta

Tunda Umma taga takoma ta" kwanta tasan cewa yau ba Lafiya tunda bata saba komawa bacci ba idan tayi sallah,

Su Lariya kam sunzo da safe suka kwashi kayansu Amma fa "an rabu kare jini biri jini, itakam Baba Lami sai basu Hakuri takeyi,

inda Haj Jumma tace Haj A'i "ai zamu hadune wlh, da suri Mama tace insha'Allahu Allah baya sake hadani dake ba daga nan duniya har lahira muguwar Aminiya kawai,

Yayinda Baba Lami take fadin "ai duk abida ba'ayisa domin Allah ba toh" dama karshen sa kenan Allah dai Ya kyauta, nima nace Amin
Haka dai aka rabu bada dadi.

A yau jumma@
Wanda yayi dai-dai da kwana biyu kenan da zazzabi ya kwantar da Humeeh, hankalin Umma yatashi sosai Ana cikin haka sai gaya Yah Himu yazo weekend kamar yadda yasaba,

Hankalin sa yatashi sosai da yadda ya ga Humeeh, Umma ke fada masa dalili zazzabin Nata "aikam yanata fada ya Kuma ce karta sake kiransa awaya dama shi bawai ya yarda da wannan Abdul-jabbar din bane,

Ana cikin wanna hali Kuma saiga notis anbasu sutashi gidan tunda wai basu biyan kudin haya, hankalisu yatashi sosai basuda gurin zuwa dole suka tattara suka koma gidan Malam mahaifin Umma,

wanda bai sannan halin dasuke cikiba saida yagansu, aikam yayi fada kamar ya ari baki, musamman dayaga halin da Humeeh take ciki nadai, Umma tayi ta ba shi Hakuri har ya Hakuri amma yace tarege wanna zurfin cikin Nata,

Wasa wasa saida Humeeh ta kwanta gadon Asibiti ahakadai akai tafama" har tasamu Lafiya taci gabada harko kinta" Amma fa son "Abdul-jabbar yana nan makale acikin zuciyarta,tawani bangane Kuma jin haushi sa take sosai akan abunda yai mata,

Abdul-jabbar kuwa kullum yana cikin Neman line "Humeeh Amma shuru baya samu, Dalter boy yayi magana akan yayi hakuri harsu koma gida Amma yaki sauraren sa" saboda haka sai ya kyale sa,

wanna shine abinda ya faru da Abdul-jabbar Da Humeeh, toh" wai Soyayyar Humaira ce ke faman wujujuwa da Abdul-jabbar kodai akwai wani abun ne? toh bari mugani,


CIGAGAN LABARIN
------------------------------
Wurjan-jan yashi ga parlor tareda yin sallama,
Alh ya'u nakaka Dattijon kirki mai cikar kamala, ya amsa Sallama tareda kallon Dan nasa"

Dayake ta faman zuba gumi kamar yahadiyi Karin kuna ma, sai duk yabashi tausayi gashi duk yarame yayi duhu, alamar dai tare suke yin jiya Da abokin'nasa,

Yasamu gurin ya zauna tareda cewa sannu, Baba,"

Batare daya amsa ba yace "any-anya nadabo ciwon nan Na "abokinka Ana samun cigaba kuwa?

yau kimanin sati hudu kenan fa Amma ace har yanzu "Mutum baisan duniyar dayake ba, balle yasan Wanda ke kanshi ,

Nifa 'ni abin'nan yaki toh" fa Zan fita da "yaron, Germany tunda suna da kwararru likitoci,

domin nidai tausayi mahaifiyar sa" yakaini makura gaskiya,
DA sauri Y Y K yace...?


๐Ÿ’Lufhat ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page86-90

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

edited by Zainuddeen zain

----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------

only exquisite and whizkid writers are oppw to be pen writers.


โœ๐Ÿพ


"Ansamu cigaba'

Alh ya'u yace ta ina aka samu cigaba? "Mutum kashiga har kafito Amma bai sani ba,

Y Y k yace daga asibiti nake yanzu shine nazo nafada maka cewa "Abdul-jabbar din ya farfado, saidai haryanzu baiyi magana ba,

Sai "yanata wasu surutai alamar baya cikin hayyacinsa,
Sannan Kuma yanata kiran Mama,

Shine nace toh" bari inzo nafada maka, abinda ke faruwa,
Alh yace toh" masha'allah Allah mun gode maka,

Yanzu abida nakeso dakai" shine Kai" maza- maza,
Kaje kataho Mani da "Haj A'isha,
Sai Ku iskemu can asibitin kaji KO"?
Yamike tareda cewa toh" yafita dasauri,


Asibiti Abdul-jabbar yana zauna ya jingina da filo, Alh ya'u yashiga dakin da sallama sa ya kalli Abdul-jabbar,

Yace sannu Abdul-jabbar yaya jikin naka,Ina fata kasamu Lafiya?

Bai amsa ba saidai ya zubawa Alh ya'u idanu, kamar bai taba ganin shi ba,
Ya sake tambayar sa still shuru ba amsa,

Sai ga Doctor I S G yashio dakin, yace sannu Alh kaga Abdul-jabbar ya farfado ko?

Alh yace kwarai nagansa", ya farfado saidai Kuma banji dadin ganinsa" hakaba gaskiya,

Doctor shiyasa nace kabari nafita dashi Germany, amma kace nabarsa ,

Yanzu haka zaya zauna babu magana, hakanan zayayu kuwa doctor?

Doctor I S G yace a ah Alh insha'Allahu dazaran ya" warware zakaji yai magana,
sannan Kuma yana bukatar ganin "mahaifiyar sa"

yace "eh natura nadabo ya daukota" docto yace OK shikenan,

Alh yayi shuru yana tunanin, abinda Doctor ya fada masa tun kwankin baya dasuka wuce,

Aransa yake fadin shiko "Abdul-jabbar meya keso haka, wanda yasaka shi acikin rai haryana baraza nan salwantar masa"da rayuwa?

Ahankali aka turo kofa aka shigo,
Y Y K yana gaba Mama tabiya dashi abaya,

Wannan shine Karo nafarko Da Mama tazo asibitin, domin KO" da'akace tazo taga jikin Abdul-jabbar din sai tace "aibasai tazoba,

Tunda ga abokanan" sa nan suna zuwa, sannan Kuma ga "
Haj karima ga kuma "Baba lami kullun idan taje da safe sai dare take komawa gida,

Don haka ba dole sai tajeba, saboda haka bata taba zuwaba sai yau,

Mama ta tsurama dan tilon dan'nata idanu tana kallon sa,
ta firgita kwarai daganin yadda ya koma,

A ranta take fadin ashe haka "yaron nan ya koma? tabbas duk abinda
yasa meshi nice sila,

Domin kuwa naki fada masa" ko wane mahaifinsa", sannan nasa shi ya auri "yarinyar da bayaso,

Alh ya'u nakaka' neya katse mata tunanin da takeyi", dacewa Haj A'isha matsa kusa da dan'ki,

Yana bukatar ki kusa dashi, sannan Kuma "akwai abinda yakeso" Wanda muba musani ba, Amma babu mamaki ke kinsanshi,

Tunda kinzo don haka matsa gareshi KO" yaji sanyi aranshi,

Batayi musu ba ahankali ta matsa kusada gadon dayake, sai kallon ta yake kamar bai taba ganin taba,
ita din'ma shita ke kallon,

A hankali ta zauna a gefen gadon tace sannu ya jinkin ka?,
Haryanzu kallon ta yake batare Da yace komai ba,

Ta Kuma cewa meka keso yanzu? nan'ma babu amsa saidai hawaye daya wanke masa fuska,

Jitayi ga banta yafadi aranta Kuma fadin take tabdijam, lallai abu yayi abu tunda harya keyin kuka, domin ba karamin abu ne kesashi" kuka ba,

A hankali ya matso kusada ita ya kwantar da kansa akan ciyarta, hakanan taji ta tsinci kanta da Dora hannun ta saman kamshi, ahankali tafara shafa masa" cukur kudeddan sumanshi irin Na fulanin asali,

Tace Na tambaye ka' meka keso? baka bani amsa ba,
Koda yake nasan abinda ka keso, tana' maganar ne Amma idanun ta Na zubar da hawaye,

ta cigaba da cewa nasan kana" san kasan wanene mahaifinka KO?

Sannan kana san kasa dalilin da ya rabu dashi KO?
toh" zanfada maka komai,

Amma kafin nan inasan kayafe abinda nai maka,nasaka' dole ka aurin "Lariya wanda nidai basan ya akai haka tafaru Dani ba,

Nasan Na kunta tamaka' a rayuwa saboda kayi hakuri, Na Kuma gode da biyayyar da Kai mun,
Ina rokon Allah kaima yabaka mai yi maka biyayya fiye da yadda Kai Mani

A yau zanfada maka KO" wanene mahaifinka' sannan Kuma zanfada maka dalilin daya rabani dashi,
A hankali tace....?




don Allah kuyi hakuri DA wannan


๐Ÿ’Lufhat ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page91-95

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)


edited by Zainuddeen zain



*Assalamu'alaikum, friends dan Allah kuyi hakuri narashin gani post din Na akan lokacin abubuwan ne sai Ahankali nagode*




----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------

only exquisite and whizkid writers are oppw to be pen writers.


โœ๐Ÿพ


Asalinmu mutanan" Adamawa ne kamar yadda kasani sunana A'ishatu, Amma ana kirana lndo, mahaifina Kuma sunan sa Ibrahim amma ana kiransa Malam lro,
mukuma bappa muke kiranshi,
ita Kuma mahaifiya ta sunan ta Hajara Amma hajjo ake kiranta mukuma Inna muke kiranta,

Mu biyu iyayan mu suka haifa nida kanina Mahmud amma mado muke kiransa,

Mu fulanine gaba da baya masu zama a wannan ruggar zuwa waccan ruggar, a takai ce dai mu fulanin tashine,

Amma dai asalin ruggar mu idan muke zaune shine Husirin bombe,
nakance yar fari a gurin Inna ta' don haka take nuna Mani kunya Da kawaici irin tamu ta Fulani, saboda haka ban faye sakin jikina da ita ba domin bata bani damar yin haka ba,

Idan ma kaga "tasaki jiki Dani toh" sai idan bappa" da Mado basanan, kamar wata rana basanan su tafi kiwo kasan cewar bappa" baya barina, natafi kiwo,
saidai yace Na zauna Na taya Inna "aikin gida kamar su tatsar nonon shanu, da Kuma dafa madara, da dai sauran aika-aikacen gida Wanda baza'a rasaba sai shi' kuma bappa da Mado su tafi kiwo,


A wannan lokacin kuwa munkai kimanin wata goma, rabanmu da ruggar mu, muna zaune nida Inna' Ina tankadan Karin tuwo ita Kuma tana kada zaren kadi (audiga),

Saina kalleta tareda jefa mata tambaya kamar haka, Inna meyasa bamu zama a ruggar mu saidai muje mudawo?
sai tace "aidaga bappan' kune yafi gaye ma haka shiyasa,
saina Kuma cewa Inna kice ma bappan" idan muka koma kawai muyi Zan,mu a ruggar mu, karmu Kuma zuwa KO" wacce rugga,

Harara Na tayi tareda cewa toh" Sannu uwata sai kisani dole nafada masa", tunda duk maganar Dana kemasa' bata isaba sataki daki ka kawo yanzu kam "ai zaiji sosai KO"?
Kin wani tasani agaba da tambaya sai kace wata tsarar ki KO"? da sauri Na kalleta sai naga ta tsuke fuska tareda harara ta,

toh" daganan nafahimci cewa firata tafara isarta, dama baka safai take zama Dani muke firar ba,
wani lokaci sai su bappa"da mado" basan nan KO" Kuma idan naganta cikin nishadi,

toh" inda muke batawa da ita shine gurin tambaya, domin kuwa haka nake da dankaran tambaya kamar yar jarida, toh" ita kuma bata san yawan tambaya don haka dagan nan firar ke tsayawa domin kuwa tashi taka tabarni agurin, kamar lokacin danai mata wannan tambayar tashi tayi ta barni agurin,

Bin bayanta da kallo nai har saida tashiga daki sannan nayi ajiyar zuciya, domin kuwa mamakin Inna' take bani araina nace oni indo, wai Danna kasance yar' fari shikenan Kuma banida yanci daza "azauna Dani ayi fira?

Ina Cikin wanna tunani sai ga bappa shida mado sun dawo kiwo, nayi musu sannu da wowa tareda karban sandar hannun bappa Na agiye,
yace Sannu Da gida nace yauwa,

tareda kawo masa ruwa atulo mai sanyi, ya karba yana cewa "an gaisheki' yace Ina ita lnnar tatu take bangan taba? nace tana daki, muna cikin magana saigata tafita tanayi masu Sannu, ya amsa tasamu guri ta zauna sai suka fara fira har aka kira sallar magriba,
bappa yai alwala shida mado suka tafi mallaci, nikuma mukai tama nida Inna,

*********
Bayan sati biyu da misalin karfe biyar Na yammacin ran alhamis, lokaci har mungama girkin dare nida inna bayan naci abinci sai nafita waje, Dan nisada bukkar mu kadan ta gefen wata bishiya na daura lilo,

Tunani ruggar mu kawai nakeyi Da Kuma kawayena, gaskiya a lokacin Na matsu mukoma ruggar mu,

Can nahango mado yana daga mani hannun yana dariya, nima nayi dariya tareda saukowa daga kan lilon,

A hanya muka hadu muka Kuma yiwa juna dariya, na ce har kundawo kiwon? yace tundazu muka dawo bappa yana Kiranki, nace lafiya dai KO"? yace lafiya lau,

Muka jera muna tafiya muna fira sai Mado ya kalleni yace Adda Albishiri ki?, (kasan cewar haka yake kirana wato yaya kenan da fullanci), nayi murmushi tareda cewa goro madona Kuma fari tas- tas,

Yace kinsan abokina nan Na bappa dayake bamu labarin raban dasuga juna tun suna kana nan?

Nace "eh bansan shiba Amma Kuma ban manta DA labarin sa ba,
Mado yace toh" yau mungan shi agurin kiwo, Kuma bappa yace masa" yadubi hanyar mu yau din nan zamu kawo masa ziyara,

Nace ahaba dai? yace aradun, a dai- dai lokacin da muka karasa bukkar mu, muka isko bappa yana yiwa Inna bayani harnaji yana fadin sunan ruggar wato yolde kohe,

bayan na gaida bappa sai Na kalli Inna nace, nace Inna wata rugace yolde kohe Amma dai bamu taba zuwa can bako?
batare da takalle niba tace nima ban saniba, amma idan ki kayi hakuri "ai can zamu tafi yanzu KO?

Dajin haka Sai naja bakina natsuke munshirya tsaf, muka fito zamu tafi sai bappa yace yana zuwa mujirasa kadan,

can sa gashi' yadawo yana cewa nafada wa "Malam jauro zamuje ruggar yolde kohe, yajimani motsin shanu tunda bazamu dawo yauba sai gobe,

"Malam jauro magocin mune, tunda muka sauka agurin sa" mike daukar karatun kasan cewar sa Malamin makaranta kallo,

haka muka Kama hanya da yamma nan, domin kuwa a lokacin rana tayija ta tafi yamma zatafadi, kunsan Fulani basuda tsoron dare, haka nan muka cigaba da tafiya, su bappa" suna gaba mu Kuma muna binsu abaya
munyi tafiya sosai,

Ta! ta!! ta!!! haka naji karan abu da sauri Na waiga bayana "aiko nai arangama dawani katon Mutum", bakikirin dashi' hannun shi yana rikeda wani abu, Wanda koba afada maniba nasan bindiga ce"

gabana yafadi tsoro yakamani domin kuwa ban taba ganin Mutum irin shiba, "azato nama KO" aljani ne

Sai naji yai magana Cikin kakkausar murya, yana cewa duk Wanda ya motsi koyai yankurin gudu saina harbemashi Kai, Cikin firgici muka cukuikuye juna nida Mado, bappa Kuma yayi tsaye yayinda Inna ta boye bayan bappa, daga bayan mu Kuma mukaji wata murya mai Kama da irin wancan yace komotsai Mutum yai ka harbeshi,

Muka Kuma rike juna nida mado, ashe su biyu ne
Kuma kowan'ne hannun sa da bindiga, gudan yace kudi zaku bamu KO" muka she ku' yanzun nan,
bamusu bappa yafito da kudi Cikin aljihunsa ya mika masu da sauri gudan ya warce kudin yasa aljihun wandon,

Sannan ya kalli Inna yace ke Kuma fa? bamu kudi, Da sauri bappa yace "aisune duk Na baku' tsawa mutumin' ya bugawa bappa yace yimana shuru makaryaci

keh! bamu kudi ? Jikinta yanarawa tace handin boni bani da kudi, yadaka mata tsawa tareda cewa karya kikeyi kina dasu, Cikin tsoro tace "aradu banidas,

Bai bari "taka rasaba yana karanta harbi agoshi, aikon take tafada kasa,
Cikin matsananci firgici muka saki juna nida Mado, muka nufi inda take kwance da sauri gudan yarike Mado,

ni' kuma na karasa inda Inna take bappa Na kiran ta nima Ina kiran sunan ta'amma bata amsa kiranan kowa daga Cikin muba', da'alama ta amsa kiran Ubangijinmu,

Kuka nasaki domin kuwa tuni jini ya wanke mata' fuska, da sauri bappa ya dauki sandarsa yarafkawa dayan, ya Kuma rafka masa take yafadi sumamme,

Da gudan yaga haka saiya harbi bappa akafa, tuni bappa yafadi hannun sa rike da kafarsa dake zubar jini,

wani sabon kuka Na Kuma Saki, domin kuwa naga wayan nan mutanan suna kikarin nakasa mana rayuwa, shiko Mado yanata ihu mutumin nan yasake shi amma yaki yasake shi,
don haka sai Mado ya Kama hannun mutumin ya gantsara masa cizo, da sauri yasake shi da gudu "yataho muka hadu muka rungume Inna muna kuka hada bappa,

Domin kuwa mungane cewa Inna tarigamu gida gaskiya, da sauri mutumin yabiyo Mado zai Kuma rikesa Ciki zafin nama bappa ya dauki sandarsa ya rafka masa akafa,
yafadi tareda rike sandar da hannun suka fara komawa da bappa, Ciki fullanci bappa yace mu tashi mugudu
da sauri na kalleshi nace bappa Ina zamu tafi? tsawa yadaka mani yace nace kutafi KO?

Zumbur Na mike nafinciki hannun Mado nukanufi Cikin duhun daji da gudu,
gudu muke ba tsayawa munyi gudu sosai sannan muka tsaya agefen wata bishiya mai yawan ganye,

muka hada Kai nida Mado muna kuka sosai ba me lallashin wani, saida mukai mai isarmu tukun sannan mukai
shuru, can sainaji tsoro yaka mani tunani nafara yi kar wani Abu yasame mu Cikin dajin nan,

Don haka sai Na Kuma Jan hannun Mado" muka koma gurin su bappa, atunanina zamu iskosu koda muka isa gurin bamu iske kowaba , "aiko basan lokacin da Na Dora hannu akai Na kurma ihu kiran sunan "bappa da "Inna, shima Mado' kukan yakeyi haka mukayi tsaye agurin muna tafan kuka, ga garin sai duhu yake karayi don haka sai Na Kuma fincikar hannun Mado,

Muka nausa Cikin dajin dagudu, gudu mukeyi batare da mun San ida muka dosaba Cikin ikon Allah sai gamu abaki titi,
nakali gabas da yamma kudu da arewa ba alamar mota KO" mashi balls keke,
Mukai tsaye Ciki jiran tsammani domin kuwa bamu Santa Ina mota KO mashin zaya bullo ba,

Can sai muka hango hasken fitilla mota daga gabas tanufo Inda muke tsaye, sai Kuma muka ga ta tsaya sai hasken fitillar ya dauke alamar ankashe,
sai Kuma mukaji shuru Na tsawan lokaci ba "akaraso inda muke ba, ni Kuma ganin haka sai naja a hannun Mado muka nufi gurin motar dagudu,

saida mukai gudu sosai sannan muka iske motar ashe ma akori kurace, bamu tsaya bata lokaci ba muka hau motar daba musan ida tadosa ba, mudai burin mu mubar wannan dajin, saida muka shiga muka zauna sannan ne muka fahimci ashe rake tadauko,

can sai mukaji anfisgi motar da karfi da sauri muka rike juna, Cikin tsoro domin kuwa ba mutaba shiga mota ba sai a wannan lokaci,
Bansan KO" awa Nawa muka dauka muna tafiya ba, saidai kam mun dauki lokaci mai tsawo muna tafiya,

Can saigamu aciki birni muna tabaza idanu muna kalle- kalle, ahaka yashiga wata anguwa ya tsaya DA alama salla zayayi tunda munga mutane natayin alwala,

Sai bayan daya shiga masallaci ne sannan muka sauko daga motar, naja hannun Mado muka Fara tafiya ba tareda munsan inda zamu ba,

Tafiya mukeyi batareda mun hadu dako dabba ba balle ba bil'adamu, tsit gurin bakajin motsin komai sai Na tafiyar mu, sai KO"bukun zuciyoyin mu domin kuwa tsoro yafara kama mu'

Ko"Kuma nace yakama mu' har,madai ni domin kuwa Allah yayini Da matsananci tsoro,

Saboda haka sai nakara sauri tareda Kuma damke hannun Mado, muka cigaba da tafiya har muka isa wata anguwa wanda tafi inda muka baro kyau,

Domin kuwa manya- manyan gidajene masu dauke da manyan kofofi, sai Kuma manya- manyan fitilu dasuka haske anguwar, saika rantse DA Allah badare bane rana ce,

A kofar wasu gidaje masu kamada tagwaye kuma tsaya, domin kuwa komai nasu irin guda ne, hatta da fantin kofar irin guda ne wato kore, kowani kofar da karami da babba,

abakin karamar kofar muka zauna, kuka ne ya kwace wa Mama saida tayi mai isarta sannan taci gaba da cewa...?



๐Ÿ’žLufhat ce๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page91-95

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)


edited by Zainuddeen zain



*Assalamu'alaikum, friends dan Allah kuyi hakuri narashin gani post din Na akan lokacin abubuwan ne sai Ahankali nagode*




----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------

only exquisite and whizkid writers are oppw to be pen writers.


โœ๐Ÿพ


Asalinmu mutanan" Adamawa ne kamar yadda kasani sunana A'ishatu, Amma ana kirana lndo, mahaifina Kuma sunan sa Ibrahim amma ana kiransa Malam lro,
mukuma bappa muke kiranshi,
ita Kuma mahaifiya ta sunan ta Hajara Amma hajjo ake kiranta mukuma Inna muke kiranta,

Mu biyu iyayan mu suka haifa nida kanina Mahmud amma mado muke kiransa,

Mu fulanine gaba da baya masu zama a wannan ruggar zuwa waccan ruggar, a takai ce dai mu fulanin tashine,

Amma dai asalin ruggar mu idan muke zaune shine Husirin bombe,
nakance yar fari a gurin Inna ta' don haka take nuna Mani kunya Da kawaici irin tamu ta Fulani, saboda haka ban faye sakin jikina da ita ba domin bata bani damar yin haka ba,

Idan ma kaga "tasaki jiki Dani toh" sai idan bappa" da Mado basanan, kamar wata rana basanan su tafi kiwo kasan cewar bappa" baya barina, natafi kiwo,
saidai yace Na zauna Na taya Inna "aikin gida kamar su tatsar nonon shanu, da Kuma dafa madara, da dai sauran aika-aikacen gida Wanda baza'a rasaba sai shi' kuma bappa da Mado su tafi kiwo,


A wannan lokacin kuwa munkai kimanin wata goma, rabanmu da ruggar mu, muna zaune nida Inna' Ina tankadan Karin tuwo ita Kuma tana kada zaren kadi (audiga),

Saina kalleta tareda jefa mata tambaya kamar haka, Inna meyasa bamu zama a ruggar mu saidai muje mudawo?
sai tace "aidaga bappan' kune yafi gaye ma haka shiyasa,
saina Kuma cewa Inna kice ma bappan" idan muka koma kawai muyi Zan,mu a ruggar mu, karmu Kuma zuwa KO" wacce rugga,

Harara Na tayi tareda cewa toh" Sannu uwata sai kisani dole nafada masa", tunda duk maganar Dana kemasa' bata isaba sataki daki ka kawo yanzu kam "ai zaiji sosai KO"?
Kin wani tasani agaba da tambaya sai kace wata tsarar ki KO"? da sauri Na kalleta sai naga ta tsuke fuska tareda harara ta,

toh" daganan nafahimci cewa firata tafara isarta, dama baka safai take zama Dani muke firar ba,
wani lokaci sai su bappa"da mado" basan nan KO" Kuma idan naganta cikin nishadi,

toh" inda muke batawa da ita shine gurin tambaya, domin kuwa haka nake da dankaran tambaya kamar yar jarida, toh" ita kuma bata san yawan tambaya don haka dagan nan firar ke tsayawa domin kuwa tashi taka tabarni agurin, kamar lokacin danai mata wannan tambayar tashi tayi ta barni agurin,

Bin bayanta da kallo nai har saida tashiga daki sannan nayi ajiyar zuciya, domin kuwa mamakin Inna' take bani araina nace oni indo, wai Danna kasance yar' fari shikenan Kuma banida yanci daza "azauna Dani ayi fira?

Ina Cikin wanna tunani sai ga bappa shida mado sun dawo kiwo, nayi musu sannu da

Please Login or Register in order to submit comment