Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wowa tareda karban sandar hannun bappa Na agiye,
yace Sannu Da gida nace yauwa,

tareda kawo masa ruwa atulo mai sanyi, ya karba yana cewa "an gaisheki' yace Ina ita lnnar tatu take bangan taba? nace tana daki, muna cikin magana saigata tafita tanayi masu Sannu, ya amsa tasamu guri ta zauna sai suka fara fira har aka kira sallar magriba,
bappa yai alwala shida mado suka tafi mallaci, nikuma mukai tama nida Inna,

*********
Bayan sati biyu da misalin karfe biyar Na yammacin ran alhamis, lokaci har mungama girkin dare nida inna bayan naci abinci sai nafita waje, Dan nisada bukkar mu kadan ta gefen wata bishiya na daura lilo,

Tunani ruggar mu kawai nakeyi Da Kuma kawayena, gaskiya a lokacin Na matsu mukoma ruggar mu,

Can nahango mado yana daga mani hannun yana dariya, nima nayi dariya tareda saukowa daga kan lilon,

A hanya muka hadu muka Kuma yiwa juna dariya, na ce har kundawo kiwon? yace tundazu muka dawo bappa yana Kiranki, nace lafiya dai KO"? yace lafiya lau,

Muka jera muna tafiya muna fira sai Mado ya kalleni yace Adda Albishiri ki?, (kasan cewar haka yake kirana wato yaya kenan da fullanci), nayi murmushi tareda cewa goro madona Kuma fari tas- tas,

Yace kinsan abokina nan Na bappa dayake bamu labarin raban dasuga juna tun suna kana nan?

Nace "eh bansan shiba Amma Kuma ban manta DA labarin sa ba,
Mado yace toh" yau mungan shi agurin kiwo, Kuma bappa yace masa" yadubi hanyar mu yau din nan zamu kawo masa ziyara,

Nace ahaba dai? yace aradun, a dai- dai lokacin da muka karasa bukkar mu, muka isko bappa yana yiwa Inna bayani harnaji yana fadin sunan ruggar wato yolde kohe,

bayan na gaida bappa sai Na kalli Inna nace, nace Inna wata rugace yolde kohe Amma dai bamu taba zuwa can bako?
batare da takalle niba tace nima ban saniba, amma idan ki kayi hakuri "ai can zamu tafi yanzu KO?

Dajin haka Sai naja bakina natsuke munshirya tsaf, muka fito zamu tafi sai bappa yace yana zuwa mujirasa kadan,

can sa gashi' yadawo yana cewa nafada wa "Malam jauro zamuje ruggar yolde kohe, yajimani motsin shanu tunda bazamu dawo yauba sai gobe,

"Malam jauro magocin mune, tunda muka sauka agurin sa" mike daukar karatun kasan cewar sa Malamin makaranta kallo,

haka muka Kama hanya da yamma nan, domin kuwa a lokacin rana tayija ta tafi yamma zatafadi, kunsan Fulani basuda tsoron dare, haka nan muka cigaba da tafiya, su bappa" suna gaba mu Kuma muna binsu abaya
munyi tafiya sosai,

Ta! ta!! ta!!! haka naji karan abu da sauri Na waiga bayana "aiko nai arangama dawani katon Mutum", bakikirin dashi' hannun shi yana rikeda wani abu, Wanda koba afada maniba nasan bindiga ce"

gabana yafadi tsoro yakamani domin kuwa ban taba ganin Mutum irin shiba, "azato nama KO" aljani ne

Sai naji yai magana Cikin kakkausar murya, yana cewa duk Wanda ya motsi koyai yankurin gudu saina harbemashi Kai, Cikin firgici muka cukuikuye juna nida Mado, bappa Kuma yayi tsaye yayinda Inna ta boye bayan bappa, daga bayan mu Kuma mukaji wata murya mai Kama da irin wancan yace komotsai Mutum yai ka harbeshi,

Muka Kuma rike juna nida mado, ashe su biyu ne
Kuma kowan'ne hannun sa da bindiga, gudan yace kudi zaku bamu KO" muka she ku' yanzun nan,
bamusu bappa yafito da kudi Cikin aljihunsa ya mika masu da sauri gudan ya warce kudin yasa aljihun wandon,

Sannan ya kalli Inna yace ke Kuma fa? bamu kudi, Da sauri bappa yace "aisune duk Na baku' tsawa mutumin' ya bugawa bappa yace yimana shuru makaryaci

keh! bamu kudi ? Jikinta yanarawa tace handin boni bani da kudi, yadaka mata tsawa tareda cewa karya kikeyi kina dasu, Cikin tsoro tace "aradu banidas,

Bai bari "taka rasaba yana karanta harbi agoshi, aikon take tafada kasa,
Cikin matsananci firgici muka saki juna nida Mado, muka nufi inda take kwance da sauri gudan yarike Mado,

ni' kuma na karasa inda Inna take bappa Na kiran ta nima Ina kiran sunan ta'amma bata amsa kiranan kowa daga Cikin muba', da'alama ta amsa kiran Ubangijinmu,

Kuka nasaki domin kuwa tuni jini ya wanke mata' fuska, da sauri bappa ya dauki sandarsa yarafkawa dayan, ya Kuma rafka masa take yafadi sumamme,

Da gudan yaga haka saiya harbi bappa akafa, tuni bappa yafadi hannun sa rike da kafarsa dake zubar jini,

wani sabon kuka Na Kuma Saki, domin kuwa naga wayan nan mutanan suna kikarin nakasa mana rayuwa, shiko Mado yanata ihu mutumin nan yasake shi amma yaki yasake shi,
don haka sai Mado ya Kama hannun mutumin ya gantsara masa cizo, da sauri yasake shi da gudu "yataho muka hadu muka rungume Inna muna kuka hada bappa,

Domin kuwa mungane cewa Inna tarigamu gida gaskiya, da sauri mutumin yabiyo Mado zai Kuma rikesa Ciki zafin nama bappa ya dauki sandarsa ya rafka masa akafa,
yafadi tareda rike sandar da hannun suka fara komawa da bappa, Ciki fullanci bappa yace mu tashi mugudu
da sauri na kalleshi nace bappa Ina zamu tafi? tsawa yadaka mani yace nace kutafi KO?

Zumbur Na mike nafinciki hannun Mado nukanufi Cikin duhun daji da gudu,
gudu muke ba tsayawa munyi gudu sosai sannan muka tsaya agefen wata bishiya mai yawan ganye,

muka hada Kai nida Mado muna kuka sosai ba me lallashin wani, saida mukai mai isarmu tukun sannan mukai
shuru, can sainaji tsoro yaka mani tunani nafara yi kar wani Abu yasame mu Cikin dajin nan,

Don haka sai Na Kuma Jan hannun Mado" muka koma gurin su bappa, atunanina zamu iskosu koda muka isa gurin bamu iske kowaba , "aiko basan lokacin da Na Dora hannu akai Na kurma ihu kiran sunan "bappa da "Inna, shima Mado' kukan yakeyi haka mukayi tsaye agurin muna tafan kuka, ga garin sai duhu yake karayi don haka sai Na Kuma fincikar hannun Mado,

Muka nausa Cikin dajin dagudu, gudu mukeyi batare da mun San ida muka dosaba Cikin ikon Allah sai gamu abaki titi,
nakali gabas da yamma kudu da arewa ba alamar mota KO" mashi balls keke,
Mukai tsaye Ciki jiran tsammani domin kuwa bamu Santa Ina mota KO mashin zaya bullo ba,

Can sai muka hango hasken fitilla mota daga gabas tanufo Inda muke tsaye, sai Kuma muka ga ta tsaya sai hasken fitillar ya dauke alamar ankashe,
sai Kuma mukaji shuru Na tsawan lokaci ba "akaraso inda muke ba, ni Kuma ganin haka sai naja a hannun Mado muka nufi gurin motar dagudu,

saida mukai gudu sosai sannan muka iske motar ashe ma akori kurace, bamu tsaya bata lokaci ba muka hau motar daba musan ida tadosa ba, mudai burin mu mubar wannan dajin, saida muka shiga muka zauna sannan ne muka fahimci ashe rake tadauko,

can sai mukaji anfisgi motar da karfi da sauri muka rike juna, Cikin tsoro domin kuwa ba mutaba shiga mota ba sai a wannan lokaci,
Bansan KO" awa Nawa muka dauka muna tafiya ba, saidai kam mun dauki lokaci mai tsawo muna tafiya,

Can saigamu aciki birni muna tabaza idanu muna kalle- kalle, ahaka yashiga wata anguwa ya tsaya DA alama salla zayayi tunda munga mutane natayin alwala,

Sai bayan daya shiga masallaci ne sannan muka sauko daga motar, naja hannun Mado muka Fara tafiya ba tareda munsan inda zamu ba,

Tafiya mukeyi batareda mun hadu dako dabba ba balle ba bil'adamu, tsit gurin bakajin motsin komai sai Na tafiyar mu, sai KO"bukun zuciyoyin mu domin kuwa tsoro yafara kama mu'

Ko"Kuma nace yakama mu' har,madai ni domin kuwa Allah yayini Da matsananci tsoro,

Saboda haka sai nakara sauri tareda Kuma damke hannun Mado, muka cigaba da tafiya har muka isa wata anguwa wanda tafi inda muka baro kyau,

Domin kuwa manya- manyan gidajene masu dauke da manyan kofofi, sai Kuma manya- manyan fitilu dasuka haske anguwar, saika rantse DA Allah badare bane rana ce,

A kofar wasu gidaje masu kamada tagwaye kuma tsaya, domin kuwa komai nasu irin guda ne, hatta da fantin kofar irin guda ne wato kore, kowani kofar da karami da babba,

abakin karamar kofar muka zauna, kuka ne ya kwace wa Mama saida tayi mai isarta sannan taci gaba da cewa...?



๐Ÿ’žLufhat ce๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page96-100

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

Slm don Allah kuyi hakuri da rashin ganin posting din Na akan lokaci, banida Lafiya ne kwana biyu shiyasa, Amma yanzu Alhamdullah nagode,



Wannan page nakane kai *DAYA*wato *ZAINUDDEEN JIBRIN ZAIN* Ina tayaka murna zagayowar ranan haihuwar ka, *ALLAH* yakara maka tsawon rai mai *ALBARKA*
*Happy* *Birthday* once again Dan ๐Ÿ•บ๐Ÿป *Zainunu*๐Ÿ˜œ *ALLAH* yakara shekara masu yawa muga diyanka da jikoki harda tattaba kunne, Ameee, Yeeeeee ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐ŸผDan *YARO*
Cut the *CAKE* ๐Ÿ”ช๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐Ÿ˜€


----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------

only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers.


โœ๐Ÿพ


"Mado yace Adda inajin bacci, kallon sa nai Cikin tsananin mamaki na kalle sa wato shi har yaga gurin bacci,?

Arai na kuwa fadi nake Hodijam lallai yaro yarone "inbanda abin Madon toh" mu har wani bacci zamuti yanzu, "wayanda suke Cikin wannan tashin hankali, narashin iyaye da rashin sanin takamai man inda zamu mado sa,

Mado ne ya katse Mani zancen zucin danake, da yasake mai-mai tamani abinda yafada,

Kallon sa nai duk sainaji yabani tausayi, domin KO" dani dashi duk munyi wurjan-wurjan, ahankali Na mike kafa-funa nace ya kwana yayi bacci, nikuma sai najingina Da kofar sai Kuma nafara tunanin, tayaya rayuwar mu zata kasance? taya kuma zamu fara rayuwar ba tareda "Inna da bappa ba?

Can Kuma saina tuna " ashefa "Inna tarigamu gidan gaskiya, bansan lokacin da Na fashe Da kuka ba da sauri Na toshe bakina saboda kadana tayar da Mado daga bacci, domin naga yana jin dadin baccin,

Hakana cigaba da kukana ina tunanin kila shima bappa" sun kashe sa, can wata zuciya tace toh" insun kashe sa ina gawarsu" take shida Inna"? can Kuma naji wata zuciya tace kura sun cinye,

Da karfi Na Kuma sakin wani sabon kuka, nace shikenan munrasa Inna" da bappa" bamu da kowa" sai Allah, ni kadai nake ta faman surutu sai kace wata tababbiya,
Shi KO" Mado yanata bacci sa ba bu abinda ya damesa',

************
Bansan rana tayiba sannan Kuma banji karar bude kofa ba, hakalizika banji karar fitowar mota ba,domin kuwa nayi matukar nisa a tunani Wanda yahana Mani rintsawa,
Saidai naji da karfi ance "ku Lafiya me kukeyi anan gurin?

Nasan zakai mamakin yadda "akai mukejin hausa, tunda mu fulani ne kuma "arugga muke zama, sanna kuma bamu taba zuwa birniba maka toh" ba abin mamaki ba,

Domin kuwa min koyi Hausa ne abakin wani Mutum mai suna mlm Mudi" da matarsa hassu," adalilin zaman daya kawosu ruggar mu toh" saboda haka agurin su muka koyi Hausa,

Na daga Kai don naga me wannan maganar,
"aiko nai aranga da wani kyakkawan "Mutum acikin wata, zukekiyar mota baka wulik har sheki takeyi Saboda tsananin bakinta,

Da sauri Na duki Mado Ina cewa tashi Kai ga aljaninan yazo yakama mu, domin KO" azatona ba Mutum bane Saboda kyawunsa ya muce tunanina,

wani tunani ne yafado Mani inda Malamin mu Na makarantan allo, yataba fada mana cewa mutanan boye sunada matukar kyau, don haka saina Kama hannun Mado narike tareda yin duk wata Addu'a datazo bakina,

Mado KO" dama tuni ya watseke daga baccin dayakeyi, sai mukayi tsaye tareda tsurama wannan Mutum idanu,

Sai yafito daga Cikin motar yanufo inda muke tsaye, da saurin muka jada baya sai yayi tsaye Cikin murya sa mai dadi, yace nace Lafiya me kuke nema anan gurin? da sauri nace bakomai , toh" wakuke nema acikin gidan, nan na Kuma cewa bakowa,

Jinai yace Peter sai gawani Mutum yafito yana KO" karin rufe kofa, sai bayan da yarufe kofar ne sannan yanufo inda muke tsaye, saiji suna wani irin yare shi ba fullanci ba shi Kuma ba Hausa ba,

Domin KO" su kadai muka iya, Saboda haka sai kawai muka tsura masu idanu, tunda bamajin abinda sunke fadi, kallon mu yasake yi yace wai kudaga Ina ku" kafito? da sauri nace daga ruggar husiri bombe,

Yace' "Ina kika ce? Na Kuma mai-mai tawa, sai naga yai shuru can Kuma yace toh" Ina iyayan Ku! sai nasaki kuka mai karfin gaske tareda cewa "ankashe su, da karfi yace suwane ne suka kashe su? Cikin kuka nace wasu mutane ne suka kwace kudin bappan" mu, suka harbeshi akafa sannan Kuma suka harbi Inna"

Da sauri naji yace innalillahi sannan yace kubiyoni, bamu tsaya bata lokaci ba muka bisa domin KO" mungane Mutum ne ba aljaniba, Cikin wannan gidan muka shiga gidan kato ne sosai gawasu shuke- shuke Na bishiyoyi, da Kuma fulawoyi masu kamshi farfajiyar gidan Kuma, wayansu duwatsune kanana-kanana masu ban sha'awa,

Munata kalle-kalle can sai idanun mu suka kallo mana, wayan su mutane manya-manya masu bakaken kaya, dakuma dogayen bindigogi a hannun su sunkai kimanin "Mutum goma sha biyar koma fiyeda haka,

Gashin duk sunyi saranda fuskokin nan babu annuri ko" kadan, da alama jirasuke abasu dama sukashe mutanan gari gaba daya,

Wani irin ihu nasaki mai karfi tareda rungume Mado, da sauri ya waigo inda muke yace Lafiya,? Nace mu baza mu shiga wannan gidan ba yace Saboda me? nace masu irin wannan abin'ne suka kashi mana Inna" Da bappa" Na nuna mashi, mutanan nan,

Yace "aisu wayan nan bamasu kashin mutane ba ne, masu tsaron Lafiya Mutum ne, nace a ah mudai bazamu shiga ba, yayi yayi damu mu shiga nace a ah, dadai yagada gaske bazau shiga ba sainaga ya kallesu tareda irin wannan yaren nadazu, duk sai naga sunjuya baya "a lokacin guda,

Sai yakalle mu yace toh" kuzo mu shiga babu abinda zasuyi maku, sai muka bishi munata waigen wayan mutanan har muka shiga ba tareda sunjuyo ba,

Wani guri muka shiga mai girman sosai da kujeru manya, sannan Kuma ga wasu irin abuda aka manna ajikin bango mai dauke da sunan Allah, kasan Kuma wani abune mai taushi domin kuwa jimukai kamar kafaunmu zasunutse aciki,

ga Kuma wani katon hoto "aman'ne "ajikin bango, kallo guda zakaima mutanan Cikin hoton ka tabbatar tagwayene, badon komai ba sai don tsananin kamar da sukai da juna,

Ya juyo ya kallemu yace kujirani anan inazuwa,ga guri nan kuzauna mukace toh", sai yabita wata kofa yashiga cikin,

Saida muka gama kalle kallon mu sannan muka nufi kujera Dani yar zama, "aimuna zama sai muka mike zumbur kamar
wayanda suka zauna akan "allura,
Nida Mado sai muka tsurama juna idanu domin KO" munga "aniyar hadiyemu,

Mado yace Adda "aradun Allah idan muka zauna zata hadiye mune,
Nace eh toh" kadamu zauna,
Don haka sai mukai tsaye cirko-cieko sai kace zakarun dasuka shafada suka gaji,

Can sai gashi yafito shida wata mata kyakkyawa mai cikar kamala, tana sanye da doguwar Riga baka ta Kuma lullube kanta tada mayafi baki, kasan cewar farace sai kayan sukai mata kyau, Dana kalleta' sainaga suna Kama da wannan mutumin daya shigoda mu gidan,

Cikin sakin fuska ta kalle mu tace toh" baku zauna ba? Mado yace aradu "in muka zauna nan gurin yana hasiyemu, sainaga sun kalli juna sunyi murmushi, tace bazai hadiye kuba nace "a ah tayi dariya tareda cewa toh" shikenan ku zauna anan tanu banana kasa,

Muka zauna sannan suma suka zauna,muna kallo bai hadiye Suba kamar yadda muka zato, araina nace kila Dan sun saba ne, ahankali tafara tambaya ta "Ina bata amsa kamar yadda naba wannan mutumin, Wanda nake kyauta ta zaton danta ne,

Sai naga ta kallesa tace kasan ruggar dasuka fadi yace baisani ba,
tace yanzu idan akasaku amota zaku iyagane ruggar taku?

Nace "aiba amota muje zuwaba akafa muke zuwa, KO" yanzu ma wani" mai motar rake mukabiyo yakawomu nan cikin birni Amma muba mutaba zuwaba sai yau,

Sai ta girgiza kai tace ya sunan ki' nace lndo shi Kumaz Mado, tace indo A'isha kenan KO" nace "eh toh" shi kuma Mado fa? Nace Mahamud,

Tace masa kaje ka Kira Mani lya Asabe yace toh", can saiga shi yadawo tareda wata yar dattijiyar mata sai matar tace Haj baki mukai, tace "eh wannan sunan ta A'isha shi Kuma sunan sa Mahamud,

Don Allah Inna Asabe akaita dakin anan nakusa danawa, tayi wanka akwai kaya wadurof abata tasa sannan abaya abinci tayi karin kumallo,
ta kalli mutumin nan tace Kai Kuma kai Mahamud dakin nan Na hanyar boy's quarter, shima yai wanka akwai kaya a cikin wadurof kabashi yasa sannan yazo yai Karin kumallo,

Tamike tana cewa Bari "inje nasami general kila bazaya rasa sanin ruggar tasu ba, suka amsa da toh" dukkan su" Nina bi wannan mata Da akakira Inna Asabe, shi Kuma Mado yabi wannan mutumin da bansan sunan sa ba,

Gaskiya dakin ya kayatu matukar kayatuwa, "ainan nasaki baki Ina kallo dama gani yardaji Dan haka sai nakara zama yardaji sosai,

Tanuna Mani bayi nashiga nai wanka nafito tabani mai nashafa, sannan tabani kaya nasaka sannan muka koma falo, anan muka isko Mado shima haryana shirya, aka bamu abinci banyan mun gama sai ga,

Hajiya tafito bayanta wani mutum yana biyeda ita kyakkyawa dashi managarci, mai cikar kwarjini yasamu guri ya zauna adaya daga Cikin kujerin falon, tace
Hajiya general kaga yaran nan Kai ya girgiza Cikin tausayi mu,

Sai yace gaskiya doctor bansan ruggar nan ba Amma insha'Allahu zansa abincika Mani,
dajin haka sai kawai nasaki kuka "Ina fadin shikenan mun banu, ahankaki ta karaso gurin na tace haba A'isha yace maki kunbanu,?

Insha'Allahu za'a gane ruggar kinji " aiyace zaya sa "abinci ka ki ba?
Nace "eh tace toh" kidaina kuka haka nace toh" tare da share hawayan,

Wasa-wasa saida mukayi satin uku agidan nan batare da angane ruggar mu ba, a lokacin Kuma idan kaganmu saika rantse da Allah bamu bane fulanin nan yan daji, mun goge munyi kyau abinbu,
Sai ranan damuka cika sati hudu sannan aka samu Wanda yadan ruggar mu,

"aikam dadi kamar ya kashemu don murya, munsan dai KO" bakomai idan aka kaimu husiri bombe ruggar mu, akwai kannan bappa" da Kuma Na Inna"

Don haka sai mukayi ta murna muna hada kayan mu,Wanda mu kasan anbamu Hajiya natayi mana dariya,

Saida muka gama shiryawa tsaf sannan muka fito afalo muka isko Hajiya,

Sai muka ajiye kayan mu muka zauna tareda tsurama Hajiya idanu, ta kallemu sai tayi dariya,

tace karfe Tara darabi na dare zamubi hanyar ruggar husiri bombe? Nace "eh toh" aimu da daddare muke tafiya, sai tace...?




๐Ÿ’žLufha ce๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page96-100

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

Slm don Allah kuyi hakuri da rashin ganin posting din Na akan lokaci, banida Lafiya ne kwana biyu shiyasa, Amma yanzu Alhamdullah nagode,



Wannan page nakane kai *DAYA*wato *ZAINUDDEEN JIBRIN ZAIN* Ina tayaka murna zagayowar ranan haihuwar ka, *ALLAH* yakara maka tsawon rai mai *ALBARKA*
*Happy* *Birthday* once again Dan ๐Ÿ•บ๐Ÿป *Zainunu*๐Ÿ˜œ *ALLAH* yakara shekara masu yawa muga diyanka da jikoki harda tattaba kunne, Ameee, Yeeeeee ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐ŸผDan *YARO*
Cut the *CAKE* ๐Ÿ”ช๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐Ÿ˜€


----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------

only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers.


โœ๐Ÿพ


"Mado yace Adda inajin bacci, kallon sa nai Cikin tsananin mamaki na kalle sa wato shi har yaga gurin bacci,?

Arai na kuwa fadi nake Hodijam lallai yaro yarone "inbanda abin Madon toh" mu har wani bacci zamuti yanzu, "wayanda suke Cikin wannan tashin hankali, narashin iyaye da rashin sanin takamai man inda zamu mado sa,

Mado ne ya katse Mani zancen zucin danake, da yasake mai-mai tamani abinda yafada,

Kallon sa nai duk sainaji yabani tausayi, domin KO" dani dashi duk munyi wurjan-wurjan, ahankali Na mike kafa-funa nace ya kwana yayi bacci, nikuma sai najingina Da kofar sai Kuma nafara tunanin, tayaya rayuwar mu zata kasance? taya kuma zamu fara rayuwar ba tareda "Inna da bappa ba?

Can Kuma saina tuna " ashefa "Inna tarigamu gidan gaskiya, bansan lokacin da Na fashe Da kuka ba da sauri Na toshe bakina saboda kadana tayar da Mado daga bacci, domin naga yana jin dadin baccin,

Hakana cigaba da kukana ina tunanin kila shima bappa" sun kashe sa, can wata zuciya tace toh" insun kashe sa ina gawarsu" take shida Inna"? can Kuma naji wata zuciya tace kura sun cinye,

Da karfi Na Kuma sakin wani sabon kuka, nace shikenan munrasa Inna" da bappa" bamu da kowa" sai Allah, ni kadai nake ta faman surutu sai kace wata tababbiya,
Shi KO" Mado yanata bacci sa ba bu abinda ya damesa',

************
Bansan rana tayiba sannan Kuma banji karar bude kofa ba, hakalizika banji karar fitowar mota ba,domin kuwa nayi matukar nisa a tunani Wanda yahana Mani rintsawa,
Saidai naji da karfi ance "ku Lafiya me kukeyi anan gurin?

Nasan zakai mamakin yadda "akai mukejin hausa, tunda mu fulani ne kuma "arugga muke zama, sanna kuma bamu taba zuwa birniba maka toh" ba abin mamaki ba,

Domin kuwa min koyi Hausa ne abakin wani Mutum mai suna mlm Mudi" da matarsa hassu," adalilin zaman daya kawosu ruggar mu toh" saboda haka agurin su muka koyi Hausa,

Na daga Kai don naga me wannan maganar,
"aiko nai aranga da wani kyakkawan "Mutum acikin wata, zukekiyar mota baka wulik har sheki takeyi Saboda tsananin bakinta,

Da sauri Na duki Mado Ina cewa tashi Kai ga aljaninan yazo yakama mu, domin KO" azatona ba Mutum bane Saboda kyawunsa ya muce tunanina,

wani tunani ne yafado Mani inda Malamin mu Na makarantan allo, yataba fada mana cewa mutanan boye sunada matukar kyau, don haka saina Kama hannun Mado narike tareda yin duk wata Addu'a datazo bakina,

Mado KO" dama tuni ya watseke daga baccin dayakeyi, sai mukayi tsaye tareda tsurama wannan Mutum idanu,

Sai yafito daga Cikin motar yanufo inda muke tsaye, da saurin muka jada baya sai yayi tsaye Cikin murya sa mai dadi, yace nace Lafiya me kuke nema anan gurin? da sauri nace bakomai , toh" wakuke nema acikin gidan, nan na Kuma cewa bakowa,

Jinai yace Peter sai gawani Mutum yafito yana KO" karin rufe kofa, sai bayan da yarufe kofar ne sannan yanufo inda muke tsaye, saiji suna wani irin yare shi ba fullanci ba shi Kuma ba Hausa ba,

Domin KO" su kadai muka iya, Saboda haka sai kawai muka tsura masu idanu, tunda bamajin abinda sunke fadi, kallon mu yasake yi yace wai kudaga Ina ku" kafito? da sauri nace daga ruggar husiri bombe,

Yace' "Ina kika ce? Na Kuma mai-mai tawa, sai naga yai shuru can Kuma yace toh" Ina iyayan Ku! sai nasaki kuka mai karfin gaske tareda cewa "ankashe su, da karfi yace suwane ne suka kashe su? Cikin kuka nace wasu mutane ne suka kwace kudin bappan" mu, suka harbeshi akafa sannan Kuma suka harbi Inna"

Da sauri naji yace innalillahi sannan yace kubiyoni, bamu tsaya bata lokaci ba muka bisa domin KO" mungane Mutum ne ba aljaniba, Cikin wannan gidan muka shiga gidan kato ne sosai gawasu shuke- shuke Na bishiyoyi, da Kuma fulawoyi masu kamshi farfajiyar gidan Kuma, wayansu duwatsune kanana-kanana masu ban sha'awa,

Munata kalle-kalle can sai idanun mu suka kallo mana, wayan su mutane manya-manya masu bakaken kaya, dakuma dogayen bindigogi a hannun su sunkai kimanin "Mutum goma sha biyar koma fiyeda haka,

Gashin duk sunyi saranda fuskokin nan babu annuri ko" kadan, da alama jirasuke abasu dama sukashe mutanan gari gaba daya,

Wani irin ihu nasaki mai karfi tareda rungume Mado, da sauri ya waigo inda muke yace Lafiya,? Nace mu baza mu shiga wannan gidan ba yace Saboda me? nace masu irin wannan abin'ne suka kashi mana Inna" Da bappa" Na nuna mashi, mutanan nan,

Yace "aisu wayan nan bamasu kashin mutane ba ne, masu tsaron Lafiya Mutum ne, nace a ah mudai bazamu shiga ba, yayi yayi damu mu shiga nace a ah, dadai yagada gaske bazau shiga ba sainaga ya kallesu tareda irin wannan yaren nadazu, duk sai naga sunjuya baya "a lokacin guda,

Sai yakalle mu yace toh" kuzo mu shiga babu abinda zasuyi maku, sai muka bishi munata waigen wayan mutanan har muka shiga ba tareda sunjuyo ba,

Wani guri muka shiga mai girman sosai da kujeru manya, sannan Kuma ga wasu irin abuda aka manna ajikin bango mai dauke da sunan Allah, kasan Kuma wani abune mai taushi domin kuwa jimukai kamar kafaunmu zasunutse aciki,

ga Kuma wani katon hoto "aman'ne "ajikin

Please Login or Register in order to submit comment