Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ranta taji zafin kalaman Haj jumma musamman Na San shegan ta mata DA datake shirin yi saidai babu yadda zatai da'ita,
ita dai yanzu burinta kawai shine Haj Jumma ta amince yarta ta auri danta,

Ahankali tace Haj Jumma wallahi dukkan abunda kike fada ba haka bane,
ni banyi abun kunyaba
kuma bana tunanin "aikata sa a rayuwa ta,

kuma kamar yanda nafada miki abaya cewa shi ba shege bane toh"ba shege bane yanada uba,
Saboda haka mu daina wannan maganar,

Mufuskanci wannan maganar danazo muyin, nidan Don Allah Haj Jumma ki yarda da maganar auren yaran nan,

Wallahi idan ba auran nan akayi ba hankali Na bazai taba kwanciya ba,

Haj Jumma tace Hmmm Haj A'i manya toh shikenan,
Amma dai kije tukun Na sainayi shawara

Mama haba Haj jumma wani irin shawara kuma?

Tace "eh idan mukai shawara da ita Laririn tawa kinga koda nan da kwana biyu ne ke" dawo kiji abunda kenan,

Itakam Mama ba haka nan taso ba toh" Amma ya ta'iya dole ta tafi gida har zuwa bayan kwanan biyun,

ta mike tsaye tareda cewa
Toh"shikenan nagode Haj jumma nizan tafi toh" ki gaida gida toh" tafita,
yayin da Haj Jumma tabi bayanta
da harara a ranta tace Zaki gane naje gidanki" kinyi Mani walakanci saboda haka sai narama abunda kikai mani domin nibana yafiya",

taja wani dogon tsaki mtswwwww sannan ta mike tashiga daki.


Washa gari da misali karfe 10:15 Am,
Zaune suke su uku suna break fast suna Dan fira kadan- kadan kamar yanda suka saba, Amma kuma sai sukaga yau Humeeh tayi shuru,

Humeeh kam tunanin halin dataga special dinta jiya takeyi, itakam tunda take dashi bata taba ganin sa Cikin wani yanayi irin najiya ba
Ahankali tayi ajiyar zuciya,

Haleeh ce tadan taba Hannah tareda yimata nuni da Humeeh, tambayan ta tayi da ido alamar meyasa mi Humeeh din? amsa tabata alamar itama bata sani ba,

Hannah ce tace Hey Miss special what is happen?
Haleeh tace yes tell us" meyasa meki ?

Murmushi tayi tace nothing, baki suka hada sukace Ahhhh!
Shine mukaga kinyi shuru?

Dataga sun dameta saita fada masu abunda yasa tai shuru
Suma shurun sukai,

can sai Haleeh tace kila kansa ke ciwon kamar yadda yafada maki,
Hakan nan sukaci gabada fira har lokacin komawa class yayi suka tashi sukanufi class.

*******************
Kwana biyu nan Mama tayishi ne Cikin matsananci wahala domin kuwa hankalin ta atashe yake natsuwarta ta gushe, hada wata yar ramewa tai tunanin ta yatsaya a guri daya shine Abdul-jabbar ya auri "Lariya yar gidan "Haj Jumma,

shikasan Abdul-jabbar baya cikin nutsuwa badama yashiga cikin gida sai Mama tace masa kaje gidan su "Lariya kuwa? wani lokaci yace mata "eh wani lokaci kuma yace mata "a ah dayagane idan yace mata "a ah sai tayi tafada, saboda haka saiya daina ce mata " a ah idan ta tambaye sa sai yace mata "eh kawai.

Kamar yanzu ma yashiga Cikin gida Don yafada mata zai fita,yana sanye Cikin kananan kaya sai kamshi yake zubawa,

Bayan ya gaida ita kafin duk yace wani abu, sai tace zakaje gidansu "Lariya ne? yace "eh tace toh" nima Ina nan zuwa saboda yaune mukai da ita zanje sai mutsara yadda auren zaya kasance,

Jiyai kirjinsa" ya buga ya kalleta" cikin tausayin kansa yace Mama Dan Allah kiyi Hakuri da maganar auren na da "yarinya nan Wallahi bana Santa,

Nafada miki Mama
Inada wacce nake So itama tana sona" kuma wallahi yar gidan mutunci ce, kinga yau saura sati biyu mutafi kinga Dana dawo sai "ai maganar aurenmu da Humai

Katse shi tai da cewa dalla rufe mani baki, ni"basan wata "Humaira ba "Lariya nasani, maganar aure kuwa idan kaga na barshi toh" bana numfashi ne "aini idan ba auren nan akai ba toh" hankalina bazaya taba kwantawa ba, saboda haka kawai katashi katafi nima gani nan zuwa
Haka yatashi jiki ba kwari yafita.

Shikam Abdul-jabbar daya fita
Bai tsaya ko'ina ba sai gidan "Alh ya'u Na kaka, domin yasanar dashi abunda ke faruwa, saboda yasan "Alh ya'u Na kaka ne kadai mutumin da "Mama take jin maganar sa",

Ya yinda ita kuma tafito tanufi gidan Haj Jumma,

Da sallamar ta tashiga gidan yayinda Haj jumma ke zune a tsakar gida taji sallaman Amma bata amsa mata ba, toh" itama Mama bata damu darashin amsa matan ba,

Kujera ta dauka ta zauna bayan sun gai sai sannan Mama tace Haj Jumma nazo ne akan maganar auren yaran nan,

"aikam nanta ke sai Haj Jumma ta daure fuskarta tafara surfa masifa tana cewa "aidama nace sai narama walakanci daki Kai Mani lokacin da naje gidanki,

kuma maganar aure tsakani danki da yata babu saboda ta tace bazata auri Abdul-jabbar din ba tunda kince batada tarbiyya

saboda haka sai kije kisamo masa mai tarbiyya ki aura masa,

Itakam Mama jikinta sai rawa yake saboda tsanani tashin hakali,

tace Don Haj Jumma kitai makeni kirufa Mani aisiri wallahi idan ba auran nan akai ba hankalin bazaya taba kwanta waba, Oh Allah sarki Mama baiwai Allah,

(Kai jama'a Allah Kai mana tsari da Aminai irin su Haj Jumma Amin)

Saida Haj jumma ta tabbatar dacewa Mama ta galabaita sannan, tunda harda guntun hawayen tareda zube guywuyunta akasa tana rokon ta akan ta aminci da auren yaran nan sannan,

Da karfi Haj Jumma tace Na amince Amma da sharadin?

Da sauri Mama tace na amince da KO" wani irin sharadi ne

Tace inason da daurin aure da komai karya wuce sati daya, Don wallahi idan ya wuce sati daya toh" saidai afasa,

Mama tace na amince, Haj Jumma ta mike tanufi daki tareda yima Mama dariyar mugunta, tace Oho nadai fada maki" dai dai lokacin da tashiga daki,


Mama ta mike tana cewa nagode sosai sai anjima.

Koda Mama tafita batai tunanin zuwa ko'ina ba sai gida "Alh ya'u Na kaka,

domin tasan shine kadai ne mutumin" da zaya tsaya mata akan maganar aure nan Don haka direct cen tanufa.


Da sallamar ta tashiga parlor zaune suke su uku, Alh ya'u Na kaka Y Y k Da Kuma Abdul-jabbar domin tun-tuni ya isa gidan,

Suka amsa sallaman tareda daga Kai suka kalleta, Alh ya'u Na kaka Dattijon kirki mai cikar kamala,

Yace ah Haj A'isha ne sannu da zuwa, tace yauwa sannu Alh adai-dai lokacin data zauna a daya daga Cikin kushin din parlor,

Bayan sun gaisa ne sai Alh ya'u yace Haj A'isha dama KO" yanzu nake cewa Na Dabo" yaje ya daukoki"saboda Ina San magana dake",

Tayi murmushi tare da cewa Allah sarki nima dama nazone naiman wata alfarma,

Alh yace toh" Haj A'isha wani irin alfarma kenan fa?
Nan tafada masa abunda yake tafeda ita,

Shuru Alh ya'u yayi yana nazarin maganar ta, cen yanisa yace Naji abunda ketafe dake Amma Haj A'isha meyasa like San Abdul-jabbar ya auri "yarinyar nan? Shin meyasa bazaki bari ya nemi yar gidan mutunci me tarbiyya yaura ba?

Tayi dariya tace Alh wannan ma "ai yar gidan mutunci ce "Lariya ce fa yar gurin Aminiyata ce "Haj Jumma,


Yace yanzu nidai abunda nake soda ke shine kiyi Hakuri abar maganar auren nan Don Allah kinji KO?

Aikam tuni jikinta ya dauki rawa tace Don Allah Alh ka taimaka mani wallahi idan ba auren nan akayi ba, bazani taba samun nutsuwa Da kwanciyar hankali ba a rayuwa ta,

Tanuna Abdul-jabbar tareda cewa wannan yaron Sam bayajin magana ta,

Tun-tuni nake masa maganar aure nan Amma yaki saurarena,
Wai "ace ka haifi yaro da Cikin ka kasayai maka abu sai yaki yimaka toh" "ashikenan, kawai sai tafashe da kuka,

Shikam Abdul-jabbar kirjinsa" ne yabuga yayinda jikinsa" yadauki rawa,

Da sauri yamatsa kusada kafarta cikin tsoro yace Mama kuka kike yimani?

Hannun sa yadora duk akai yace kaichona ni" Abdul-jabbar mahaifiyata kemani kuka? Wayyo Allah Na,

ya kalleta da idanusa dasuka kada sukayi jajir yace ki taimakeni Mama kidaina kukan nan, kinsa cewa kukanki" agareni babbar masifane?

Cikin kuka tace toh" idan banyi kuka ba meka keson nayi? tunda bakajin magana ta,

Wani irin Yasu Abdul-jabbar ya hadiya mai daci sannan yace toh"Mama kidaina kukan hakanan,
kifadi abunda kikeso nayi miki" koda hakan yana nufin daukewar numfashi nane zanyi miki shi insha'Allahu,

Tashare hawayen dagefen zaninta tareda fece majina, sannan tace toh"aini dama "Lariya kawai nakeso ka aura,

wallahi jinake idan har baka aure taba "Lariya ba zuciya ta bugawa zatai,

Da sauri Abdul-jabbar yace.....?




๐Ÿ’žLufhat ce๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page67-70

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)


Dan Allah kuyi hakuri narashin ganin posting din kwata biyu wallahi aikine yai mun yawa nagode,


----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------

only exquisite and whizkid writers are oppw to be pen writers.


โœ๐Ÿพ


Innalillahi'wa'inna'ilaihinraju'una, Mama Zuciyar ki bazata bugaba insha'Allahu badai "Lariya ki kesan Na aura ba?

Da sauri tace "eh yace toh" Zan aure ta tace toh"Allah yai maka Albarka ya kare mani Kai yace Amin Mama,

Alh ya'u nakaka shida Y Y K kallon su" suke cike da tausayin su ,
Musamman ma Y Y K dayake tsanani tausaya ma Amin'ninsa akan wannan aure daba yada tsari,

Alh ya'u shuru yai nazarin yake aransa tabbas abun'nan Na Haj A'i akai sihiri Cikin sa,

Yai nauyayyan ajiyar zuciya yace Haj Aisha ki kwantar da hankalin ki, inda Abdul-jabbar ne zai auri "Laria take KO wa?

murmushi tayi tareda cewa "Lariya ne sunanta yace toh" indai hakan shine farin Cikin ki toh" zaya aureta,

Amma dai sai yadawo daga kos tunda saura sati biyu sutafi,kuma ba wani dadewa zasu yiba tunda duk bai wuce suyi shekara daya ba,

kinga dasun dawo sai "ai maganar auren KO?

DA sauri tace a ah Alh "ai mun'riga munsa rana nan da sati daya muke San "ayi bukin,

Y Y k baisan lokacin da yace what ba?

Shikam Abdul-jabbar daya zaune tunda zu kamar butun-butumi jiyayi kirjinsa yaci gaba da matsananci bugawa,

Alh ya'u Na kaka kam yanzu takara tabbatar da zargin sa na cewa Haj A'isha akwai sihiri atareda "ita

Saboda hahabsai yace haba Haj A'isha wannan wani irin aure haka,

daza'ace za'a yi shi nan da sati daya batare da anshirya komai ba?

tace "eh nidai don Allah Alh ka yaimaka mani nasan kanada halin yin mani wannan alfarma nan,

Yace Haj A'isha bawai Ina maganar cewa banida halin yi maki bane,

Kuma bawai Ina alfahari bane, Abdul-jabbar kadai ba idan sunkai Mutum Dari insha'Allahu inada abunda Zan aurar dasu Rana daya,

Ni Ina magana ne akan gaggawar abun,kin gaggawa " "aikin shedan ne fa?

Kuka ta fashi dashi tace don Allah Alh Ka taimaka mani wlh bakaji yadda nake jibane aran'na,

Da suri Alh ya'u nakaka Yace a ah Haj A'isha kidai Na kukan nan,

Indai auren Abdul-jabbar da wannan "yarinyar ne ki kwantar da hankalin ki insha'Allahu za'ai shi, yanzu ma Zan tafi ne mar masa auren ta" kinji KO"

tace toh" Na gode Allah yakara budi ta mike tareda cewa ni Zan tafi,

yace toh" kijira su agurin Haj zasu zo sumai da ke gida, tace toh" adai- dai lokacin da tafita daga parlor,

Shuru parlor tsawon wani lokaci ba wanda yace komai,

Alh ya"u na ne ya mike ahankali yanufi gurin da Abdul-jabbar yake zaune kan"sa yadafa tareda cewa kiyi hakuri Abdul-jabbar kadauki wannan abun a matsayin kaddara,

saidai Ina gani kamar akwai sihiri ajikin "Haj A'isha' toh" kodai ma mene muciga ba dayi mata Addu'a insha'Allahu Komai zaiyi dai-dai ne kaji ko?

Ahankali yadaga Kai alamar "eh, sannan yace kuje kudau keta Ku kaita gida,

yafadi haka ne dai- dai lokacin da yafita daga parlor,

Da sauri Y Y K ya matsa kusada Abdul-jabbar yafada kafadar sa" yace kayi hakuri Nawa komai yai farko toh" insha'Allahu zaiyi kashi ne kaji KO?

Shikam Abdul-jabbar sai Kai yaketa gyadawa sai kace kadan gare,

tsabar tashin hakalin daya ke ciki yasa shi, yakasa furta koda kalmar a ne,
Y Y k yace tashi muje mukai ta,

Haka suka mike jiki ba kwari suka nufi hanyar fita,

***************
Cikin lokaci kankani baka fara shirin bukin Abdul-jabbar Da Lariya,
Wanda tuni Alh ya'u nakaka yadauki nauyin yin komai,

Abagaren Haj Jumma ma haka shiri takeyi sosai domin taci buri wa bukin Lariya don haka da kare da biri duk ta gayyacesu,


Y Y k da M B suke tsaye akan sha'anin bukin shikam ango ko" ajikinsa domin KO ya dauki auren ne tamkar wasan yara,

Ana saura kwana uku bukin suna zaune su uku suna" fira sai Y Y K yace kai M B bari nakira Dalter boy na yafada masa,
M B yace gaskiya ya kamata,

Shikam Abdul-ganiyyun wato dalter boy mamaki yake haryana tambayar Y Y K wai dama Abdul-jabbar yanada budurwar ne?

shi kam Y Y k dariya yayi yace sai dai kazo tukun na,yace OK yana nan zuwa ana gobe daurin aure, yace toh" sai kazo sukai sallama.

Abdul-jabbar sai faman masifa yake wa Y Y K wai akan wani dalili zayai tafadawa mutane wannan auren da bashi da tsari,

Yace malam idan kanaso ne kaburge ni toh" ka tsaya aure Na da my cool yazo,

Sannan kafadawa duk Wanda zaka fadawa Amma ba wannan auren ba,

Wanda kai daganin sa kasan bana Allah da Aรฑnabi bane abu haka ko"tsari babu yaja tsaki mtswwwww.

**************
Yaune aka daura Abdul-jabbar da Lariya da misalin karfe goma naran Asabar,

Kira'ar sheikh Ahmad Sulaiman ke tashi acikin motar,

Ahankali Dalter boy ke driving dinsu Abdul-jabbar yana kusa dashi, yayin da Y Y k da M B suke zaune abaya suna kan hanyar sune ta koma wa gida,

Y Y k ne ya katse shuru da cewa cikin zolaya oh! shikenan yau wani yazama ango,
yakara she maganar dayin gwalo ga Abdul-jabbar,

Da sauri yace a ah ba ango ba ankwa Mtsww yaja tsaki,

Yace don Allah Dalter boy kabi hanyar cen muje naga my cool ko" zuciya ta nayi fari,

Bamusu Dalter boy yajuya kan motar tareda cewa wacece hakan kuma?
M B yace budurwar sa ce
Yace oh KO" "Humaira da Y Y K ya bani Labarin ta jiya?
M B yace ita fa kaidai, Yace "ai KO" zanso naganta,

Da sauri
Abdul-jabbar yace "ai ko zaka ganta very cute baby,

Y Y yace kajishi saikace wata yar jaririn, ya bashi amsa dacewa "ai jariri yar,ce

da kwatance da Abdul-jabbar yake ma dalter boy har suka karasa unguwar su "Humeeh.

Cikin zolaya Y Y k yace zumuje mufada mata" andauran aure ka ne da "Lariya?

Yace ban saniba Nawa bafa nason walakanci daka ke mun,

M B yace "au dama baifada mata" zayayi aure ba?

Y Y k inafa yafada mata" nayi nayi dashi yafada mata" Amma yaki fada mata",

Dalte boy yace "au haka ne toh" Ku kyalesa ni zanfada mata" yau din'nan,

Abdul-jabbar yace tunda kashe kwaya basai kafada mata" ba din ba, dalter boy yace "aiKo zaka gani,

dai-dai lokacin da Humeeh ta karasa gurinsu ,
Lokaci daya suka fito daga cikin mota,

Cikin jin kunya Humeeh ta gaida su,
Suka amsa fuskarsu dauke da murmushi
gogan'nata,

Abdul-jabbar ne yagaba tarda dalter boy Humeeh ta sake gaida shi, ya amsa tareda tambayan ta ya school? tace lafiya lau,

Shikam Dalter boy aransa sai yaba kyawau Humeeh yake,

yayinda yake mamaki abunda yasa "Mama tace sai Abdul-jabbar ya auri wannan yarinya mai Kama da one,

Maganar Humeeh ce ta katse masa tunanin sa" inda yaji tana cewa Ina zakuje yanzu KO" dama gurina kawai mukazo?

Dalter boy yace "eh dama munzo ne mufada miki,

DA sauri Abdul-jabbar yace....?




๐Ÿ’Lufhat ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐ท ฝ๐ท ฝ๐ท ฝ๐ด€ฝ๐ด€Š๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page76-80

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

edited by Zainuddeen zain

----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------

only exquisite and whizkid writers are oppw to be pen writers.


โœ๐Ÿพ


Umma tana zaune ita kadai atsakar gida tana linkewa "Humeeh school uniform dints kasan cewar "Humeeh bata nan ta tafi islamiyya,

kawai sai taga anshigo mata gida bako sallama,
Ahankali tadaga Kai ta kalleta tace "a ah haba baiwar Allah yazaki shigo Mani gida haka bako sallama?,

Lariya datake sanye da wani matsiyaci dressing ta kalli Umma sama da kasa, ta yamutsa fuska tace sallama tabdi" aini ban sannan ya'akeyin taba, Umma gyada Kai tace tabbas naga alamar bakisan yadda akeyin taba,

Toh" bismillah ga wurin nan ki zauna tanuna mata shimfidar datake zaune akai,

Lariya tace zama? Umma tace eh, taja wani uban tsaki mtswwwww... tace "ah bashi yakawo niba Kuma, Umma tace toh' keh! ko" yarnan meya kawoki toh"?

Tace kinga Malama badon zance yakawo niba nazone infada miki kijawa yar iskar "yarki kune takiyayi "mijina,

Idan Kuma bata" kiyaye "shiba wlh sainai mata" mummunan illa,
Da sauri Umma tace subhanallahi! Nidai ban haifi yar iskaba sannan kuma wanene "mijin naki? tace "Abdul-jabbar idan bata fita harkar Saba tabbas saina nakasa mata rayuwa eheee!

tajuya danufin tafiya Da sauri Umma tace yi hakuri kinji indai "Humaira ce za tarabu da mijiki insha'Allahu kinji KO? fiyuuuu tafice tana cewa oho indai bata rabuda shi" duk abunda yasa meta ita tazajo makan ta domin ninan daki kagan'ni banida mutunci wlh DA SANNU Zan maida "yarki abun kwatance eheeee,

Tun bayan fitar "Lariya Umma take zaune shuru nazari take aranta tabbas wannan "yarinya duk inda tafito toh" ba gidan mutunci tafita ba,

Umma kam jitayi kirjinta yabuga saka makon tuno kalaman "Lariya ga "yarta, ahankali tasaki sanyayyan ajiyar zuciya tareda cewa inda Abdul-jabbar ne toh" Humaira tabarsa tunda bashi kadai ne da namiji ba,


Cikin bacin rai Mama tace keh! Lariya nafa gaji da wannan abunda kikeyi mun haka, KO" agidan ku ankafada miki"haka ake zaman aure, "mijinki bayanan amma ke" kullum cikin yawon bin gari kike toh" wlh bazan cigaba da daukar wannan abun ba,

Lariya ta kalli Mama sama da kasa irin kallon nan Na walakanci mai dauke da harara sannan taja wani uban tsaki mtswwww...tace hmmm wai bazaki cigaba da daukan wannan abunba, yoh Ina abun yake? hmmmm "ai ba'ai komai ba toh" barima kiji in fada miki Haj A'i kike nema kowa? gwanda cigaba da dauka domin ninan dakika ganin yanzu ne zanfara tsulamiki rashin mutunci badai kinci banida tarbiyya ba KO"?
toh" ko" zakiga zallar rashin tarbiyya damani bason wannan shegen "danki nake ba, dama wata muguwar sha'awar sace takamani toh" kuma dayake "shidin Dan bakin Cikine sai yaki yarda naji kalarsa, don haka ke kuma baki'isa ki hanani sha katawa ba eheeeee tafice daga gida,

ita kam Mama kuka tafashe dashi tareda cewa "Oh ni A'isha wannan wata irin matsiface haka waima ya'akai wannan yaron ya auri wannan "yarinyar ne marar mutunci,? Nikam nace toh,

baba Lami ce tafito daga kitchen tace Haj Lafiya kike kuka? Mama tace "aidole nayi kuka saboda Lamarin "yarinyar nan ya'isheni, ni basan ya "akai "ya auri wannan "yarin ba wlh,

itakam baba Lami hakuri kawai take bata, sannan tace "ah Haj aure kam ke kikace dole sai maigida Na ya aure ta,
Mama ta face majina da gefen zaninta" tace toh" dole Kuma yarabuda itaba, domin ni wlh bazan iyaba, haka kawai bakin Cikin Dana bai kasheni basai Na wata yar banza "aizan kirasa nafada masa yara bani da wannan marar tarbiyya "yarinyar,

***************
Da misalin 9:00pm suna zaune Humeeh itada Umma fira suke kadan kadan sai Humeeh ta fahimci kamar wani abu nadamun Ummanta, don haka sai ta kalleta tace Umma tunda nadawo daga islamiyya sainaga kamar wani abuna damunki KO"?

Umma tace Hmmm tabbas Ko" akwai abunda yake damuna, nan dai Umma tafada mata abuda yafaru ta karashe maganar ta dacewa saboda haka kirabu mata da miji tunda ba "shi kadai bane dan namiji a duniya atoh" nibana San tashin hankali kinji KO?

Kai kawa Humeeh ta gyada domin kuwa takasa cewa komai asalima tunda Umma tafara magana kirjinta ke bugawa, aranta ko" fadi take Allah yasa ba "Abdul-jabbar dinta Umma ke magana akai ba,

Umma tace waiko kinji abunda nace kuwa? "eh Umma najiki saidai Ina ganin ba "Abdul-jabbar din'na bane shi "Abdul-jabbar din'na bayada mata bai taba aure bafa shi,

Harara Umma ta watsa mata tace "au shi "Abdul-jabbar din'ne naki da yaushi yazama Naki ban saniba? Ciki Dan jin kunya Humeeh ta sunku yarda Kai kasa,
Umma ta cigaba dacewa ke kinsa waye namiji kuwa? idan yanada mata zaya fada miki ne KO"Kuma idan zaiyi auren sa yafada miki?

tabbas wannan "yarinyar datazo gidan matar "sace Kuma abuda tafada lallai zata iya aikata shi don banga alamar digon mutunci a idanun "taba saboda haka idan Zaki rabu "mata da "mijinta toh" Kira budashi" idan Kuma bazaki rabuda "shiba toh" bismillah tana kaiwa nan, tashi ta shige daki tabar Humeeh zaune kamar anshu kata agurin,

Itakam Humeeh ido ta rintse sosai Ahankali tafurta Allah katadani daga wannan mummunan mafarkin tsawon wani lokaci sannan tabude idanun tana nan inda take zaune hakane yasa tagane tabbas ba mafarki takeba,

Ahankali tace haba my special meyasa zakai Mani haka? can Kuma saita mike kamar wadda aka tsikarama allura, daki tashiga Umma Na kallon ta wayar ta dauko tafito waje ta kunna wayar tayi kasan cewar tundazu daza taje islamiyya take kashita number Abdul-jabbar tayi dialing


Shikam Abdul-jabbar suna zaune shida Dalter boy suna fira saiyaga calling din Mama, yana dauka saiji yai tafashe masada kuka da sauri ya mike tareda cewa ya Salam, Mama meyasa meki kike kuka Allah yasa bani ne sanadin zubar hawayen kiba?

Cikin sheshekar kuka tace toh" idan ba "Kai bane sanadi toh" waye? da
sauri yace oh kaicho na ni Abdul-jabbar shikenan nikuma zamana kenan sa mahaifinyata kuka? lallai kam banji dadin rayuwa ta ba,
kiyi hakuri Mama kifada Mani abuda nakeyi Wanda yasaki kike kuka nikuma insha'Allahu daga yau Na daina kinji?

tace toh" sonake kasaki "Lariya, idanu ya ritse aransa kuma fadi yake Allah kasa mafarkin dana keyine kullum yau zaya zama gaskiya,

Daga can Mama taca kajina kuwa? Dasauri yace "eh Mama meki kace?
tace cewa nai ka Saki Lariya, wani irin sanyine yaji yakwarara Cikin zuciyar sai, Amma don ya tabbatar da cewa da gaske takeyi, saiyai gyaran murya tareda daure fuska kamar yana gabanta yace haba Mama yazakice nasaki "Lariya matata cefa kuma kinsa muna San juna, tace "au abuda zakace Mani kenan KO saboda baka san irin rashin mutunci datake mun bako? toh" wlh idan baka sake taba toh" saidai kanemi wata Uwar Amma bani ba,

DA sauri yace yi Hakuri Mamata "ai duk duniya nan ba wata Uwa dazanje nema bayan ke, indai "Lariya ce yanzu nan Zan saketa bama sai anjima ba Mama ina "Lariyan take? tace barina kirata Yanajin Mama tana kwalawa "Lariya kira "yajin Lariya na cewa Malama Lafiya ki ke mani irin wannan kira haka saikace kin warke makanta?

itadai Mama ba tace komai ba saida kawai tamika mata Waya, "Lariya ta yamutsa fuska tace meye zanyi da waya,? Mama tace anason ayi magana dake takar ba tareda cewa waye? Cikin daka tsawa Abdul-jabbar Yace Uban ki ne Ashe bakida mutunci Maman tawa kike fadawa magana haka?

toh" dama ita ce tasana aure ki" yanzu Kuma tace nasake ki saboda haka ki tattara komatsan kije nasakeki Saki biyu, tsaki tayi mtsww tace toh" donka sakeni saime? Dariya yayi yace sai narabuda jaraba, tsaki mtsww tasakeyi tareda jefawa Mama wayar ta akan ciya tace don kinsa yasake ni toh saime? Mama tace Saina rabuda bakar kadara, tafeta fuuuuu daga falon
Mama tace Allah yaraka taki gona,

baba Lami dake zaune tana sauraren duk abunda ake, batace komai ba sai yanzu tace Hmmm nidama nasan DA SANNU Allah zaya baiyana gaskiya, asauka lafiya dama shi duk abunda akayisa badan Allah ba toh" dama karshan sa kenan,


Da sauri Mama tadauki wayar tace Kai! yace na'am Mama yanzu shikenan hankalin ki ya kwanta? tace "eh Allah yai maka Albarka ya baka abunda kake nema na' alkhairi duniya da lahira kuma Allah yadawo daku Lafiya yace Ameen Mama ta, yace taba baba Lami su gaisa itakam baba Lami hada murnata tayasa narabuwa da "Lariya sukai sallama,

Shikam Abdul-jabbar jiyayi kamar ansauke masa wani katon dutse akai,
don haka yana gama Waya dasu Mama sai yai dialing din Humeeh kasan cewar yaji shigowar calling dinta lokacin dayake Waya da Mama,

A abangaren Humeeh kuwa tana takiran Abdul-jabbar acemata number busy, tana KO" karin sake yin dailing dinsa kenan sai gashi calling dinsa ya shigo,

Da sauri ta dauka tai sallama ya amsa tareda cewa sorry my cool naga kiranki lokaci Ina Waya da Mama ne, toh" yakike ya Umma ta? tace Lafiya lau yace gud than where is my Soyayya?
Shuru tai bata bashi amsa ba yayinda takeji sonshi yan ratsa jikinta,
A

Please Login or Register in order to submit comment